Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

me kuke Anan, yanxu.

Shuru sukayi, suka kasa ce masa game suke yi.
Tsawa ya ƙara daka musu a karo na biyu.

" Ba magana nake muku bane kunyi min shuru.

Cikin rawar murya Sharifa tace.

" Game muke yi.

" Game kuke yi, ya maimaita maganar, amma me nace muku kuke yi daidai wannan lokaci?

" Karatun ƙur'ani ta mayar masa da Amsa.

" Okey shine saboda kun Raina ni, shine kuke Game koh.

" A'a yaya kayi hkr zamu ɗauko littafin yanxu muyi karatun baxamu sake ba.

Shigewa yayi yana cewa.

" Kuma sake kuga matakin da zan ɗauka a kanku cikin gidan nan.

Ajiyar Zuciya Sharifa ta sauke ganin sunsha, dariyar Habeeb taji a daining yana cewa.

" Barrister Mustapha babban yaya, Ango na RAUDA.

Murmurshi RAUDA tayi jin daɗin sunan da Habeeb ya kira, *ANGON RAUDA* Allah ya tabbatar da bakin ka, RAUDA ta ayyana a Zuciyarta.




Wayyo Allah sister's kuyi hkr da wannan, Wlh naso nayi muku typing yafi haka yawa, sai dai uzuri sunyi min yawa yau akaina.


🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻ya Ubangiji ina roƙo gareka daka bayyana ƴar gidan Ladingo, wato Farisa, Allah kasa tana hanun na gari, ba mungu ba, Allah ka bayyana ta cikin gaggawa.
🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻


*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


*(Ummu Nasmah)*
[1/11, 3:49 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*

*D̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞I̸͟͞C̸͟͞A̸͟͞T̸͟͞E̸͟͞D̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty Fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya🙏🏻


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*Ina ƙaunar ku masoyana*

Na gode sosai da ƙaunar ku gareni, kwana biyu kawai da banyi typing ba, kun damu sosai, har ta privet masoya ke min magana, wasu kam ma bansan group ɗinsu ba, gaskiya na gode sosai, hakan ya nuna min yanda kuke ƙaunar wannan book ɗin.


*P*•••••1️⃣5️⃣ ➡️ 1️⃣6️⃣

Yana shiga ɗakin nasa wanka ya faɗa, Bayan ya fito daga tollet ɗinne ya mulke fatar jikin sa, da mai da turare, sannan yasa gajeren wando Wato 3cutter da best sannan ne ya faɗa saman gadon sa, tare da jawo system ɗinsa, ya buɗe, yana jin shigowar, Habeeb bai ɗago kansa ba, shima dai Habeeb bai kulasa ba, saima shigewa wanka da yayi, bayan ya shirya ne, ya dawo saman gadon nasu ya faɗa, tare da rufewa, mustapha system ɗinsa, sai a lokacin mustapha ya ɗago ya kalle sa, yace.

" Ya haka Malam, da rufe min system?

" Saboda Magana nake so muyi dakai.

" Okey ina sauraron ka, Allah yasa mai amfani ce, nasan Halin ka, da zolaya, domin itace ɗabi'ar ka.

Murmurshi Habeeb yayi, tare da cewa.

" Wannan maganar mai muhimmanci ce, mustapha.

"Okey ina sauraron ka.

" meyasa kake nunawa kamar baka san RAUDA na Sonka ba? Wannan yarinyar fah tayi nisa a cikin Sonka, amma kai nunawa kake bakasan tanayi ba, Bayan kuma nasan Kasan tana Sonka, ka sani fah walaƙanta ɗan adam baida amfani duk mai Sonka yafi maƙiyin ka, ko yaya yake, komai kuma muninsa, bare kuma RAUDA bata da wani muni daga fuska har dirin jikin ta.
Why mustapha, Please Answer my Questions?

Cije lips ɗinsa yayi, wanda ya zama masa jiki a rayuwarsa, yana son cije lips ɗinsa, magana ya fara.

" Saboda bana sonta, bata min ba, nifa kaga RAUDA bata daga cikin kalar matar da nake bukatar aura, sannan kuma bata da aji tunda har zata iya furtawa namiji cewar, tana sonsa, mace mai aji neman ta, ake ace ana sonta ba, ita bace zata nema tace tana son.
Da kake maganar diri, koka manta da cewa shi so Babu ruwan sa, da kyau ko muni, idan kana son mutum baka ganin munin sa dan haka ni kyan mace ko munin ta, baya daga cikin ra'ayina nafi son mace mai kamun kai da nutsuwa tare da ilimin zamani dana Addini, idan har na samu mace mai wannan suffar komin munin ta, zan iya Auren ta, idan har ina sonta, sai amsar tambayar ka, ta ƙarshe itace, bani nace ta soni ba, bare kuma har tayi zurfi cikin soyayya ta, wannan damuwar tace ba tawa ba, idan kana tausayin ts mai zai hana kai ka Taimake ta, ka Aure ta, ai ina ga kamar Babu banbanci tsakanin mustapha da Habeeb, dukan su Abu ɗaya ne, kaga kuwa duk wanda yaso mustapha dole zaiso Habeeb, kodan tsantsar kaman dake tsakanin mu.

Murmurshi Habeeb yayi cikin jinjina tsatstsauran ra'ayi Irin na, Mustapha, shi wlh yana mungun tausayin RAUDA, domin kuwa yasan ba ƙaramin so take yiwa mustapha ba.

" Kai take so ba Habeeb ba, kamar muce kawai ɗaya, amma halayyar mu, ta banbanta, wata ƙil badan kyan fuskar ka take sonka ba, wata ƙil tana sonka dan wani abu dake tattare dakai may be yanayin kane yake burgeta, kokuma Halin ka, ko kuma haka kawai take sonka, amma tunda kace, Allah ya zaɓa muku Abunda yafi Alkairi.

Ameen Mustapha yace tare da jawo system ɗinsa ya buɗe, yana cewa Habeeb.

" Shiyasa fah jiya da kace muje gidan su, ka gaida Mamy nace maka baxan jeba, Saboda wannan shegiyar ƙanwar Tata mai shegen bakin tsiya, kana zuwa zata fara tambayar ka, ya soyayyar ka da RAUDA kamar ni nace mata ina soyayya da RAUDA.

Dariya Habeeb yayi yace.

" Ni kam ai zanje na gaishe ta, dole na, kodan yawan kira na da take a waya, tace min idan ta kira ka, baka dagawa sai kaga dama.

Dariya shima mustapha yayi, tare da cewa.

" Haka tace maka kenan, Duk kiran da zata min akan damuwar ƴarta ne, shiyasa ban damu da ɗaga kiran ta ba.

" Allah sarki Habeeb yace, tana taya ƴarta neman soyayyar kane, shiyasa, kasan uwa da tausayin ɗanta.
Ni ya maganar case ɗin khabeer da uwarsa Momy sarah ne, naji SADIQ yana cewa court ɗinku zai kai su?
Danni rabona da khabeer tun sanda yaje London kamo wani Alhaji.

Ɗago kansa Mustapha yayi, ya kalli Habeeb kafin yace.

" Wlh banda masaniya dan gaskiya na daɗe, rabona da khabeer, tun randa mukaje gaishe sa, daya kwanta rashin lfy, wajen shekara ɗaya kenan.

" Daman can ba shiri kuke ba, kaga bari na kwanta, dan mun daɗe muna hira har 12.

" Allah ya tashe mu, lfy nikam ba yanzu ba, sai na gama aiki na, akwai wani bincike da nake yi.


Itako RAUDA ta kwanta tayi lamo akan gado, ta rasa meke yiwa rayuwar ta daɗi, pic ɗin mustapha ta zubawa ido wanda ta tura a wayar Habeeb, ta daura kan wayar ta, wannan wacce irin soyayya ce nake maka Mustapha, soyayyar ka ta zama cuta ce a gare Ni, why !! why !! why baka sona, menene bandashi menene Aibu na, daka tsaneni haka, Allah ka sassauta min soyayyar mustapha cikin zuciyarta, ko zan samu sauƙin ciwon dake damuna cikin ƙirji na.
Ahaka bacci ɓarawo yayi nasarar capke RAUDA, cikin damuwar da take ciki na tsanar da mustapha ke gwada mata, inji ta da faɗa.

Washe gari da safe, momy ta riga kowa tashi kasancewar zata yiwa Daddy breakfast, zai fita kasuwa da wuri, a kitchen ɗin RAUDA da Sharifa suka taradda Momy, gaishe da Momy sukayi ta amsa tare da cewa.

" Sai yanxu kuka tashi kenan, dana biye ku, yau da saidai Daddyn ku, ya tafi kasuwa ba tare da yayi breakfast ba.

Murmushi RAUDA tayi tace.

" Ehh Wlh Momy, bayan nayi sallar Asuba ne bacci ya ɗauke Ni, kije ki zamu ƙarasa aikin, fita Momy tayi tana ce musu.

" Kudai yi da jikin ku, dan daddyn ku zai fita kasuwa yau da wuri.

Wajen wanke wanke Sharifa ta shige yayin da RAUDA ta tsaya kan girkin. Cikin 30 minute suka haɗa komai suka jera saman daining, Mustapha da Habeeb tare suka sauƙo, kafin Momy da daddy su fito suma.

Gabaki ɗayan su, a daining suka haɗu yayin da RAUDA tayi seving ɗin su, kafin RAUDA ta iso kan Mustapha, yayi saurin cewa, Sharifa tayi seving ɗinsa, ɗago kanta RAUDA tayi cikin jinjina irin ƙiyayyar da mustapha ke gwada mata, wato tsabar tsana, abincin ma, bazan zuba masa ba, duk motsin Mustapha akan idon RAUDA ne, yayin da shi kuma ko inda take bai kalla ba, bayan sun gama breakfast ɗin ne, RAUDA tacewa daddy,

" Daddy ina son Anjuma zan koma gidan mu.

Kafin Daddy yayi magana Momy ta rigasa ta hanyar Cewa.

" Zaki koma gida kuma RAUDA, keda kikace zakiyi mana sati biyu, kwatakwata fah kwanan ki biyar ne, shine kike zancen komawa gida, kodai akwai Abunda muke miki ne, idan akwai ki faɗa mana.

Cikowa idon RAUDA yayi da hawaye, ita har ga Allah babu wani Abunda suka mata, kawai gajiya tayi da kallon tsana da wulaƙanci da Mustapha ke mata, gara kawai ta koma gidan su, ko zata samu mafita wajen mahaifiyar ta.

" Babu Abunda aka mini Momy kawai dai zan koma gida ne.

" Kin tabbata Babu Abunda aka miki RAUDA, cewar daddy.

" Wlh Babu komai daddy kawai so nake na koma gida.

Ɗago kansa Habeeb yayi yana kallon RAUDA cikin tuhuma, kasancewar yasan dalilin daya sa, zata koma gida, sunkuyar da kanta ƙasa RAUDA tayi, ta ɗauke idon ta, daga na Habeeb, shi Kuma Mustapha yana jinsu, bai ɗago kansa ya kalle su ba, bare ma susa ran zaiyi magana, tashi yayi tare da cewa su Momy.

" Ni zan shige office, Habeeb ka gaida Hajiya Innah idan kaje, sai Allah yayi dawowar ka.

" Okey Babu damuwa zataji. Cewar Habeeb, amma baxaka tsaya mu fita tare ba.

" A'a hanyar mu ba ɗaya ba, kawai Allah ya kiyaye hanya.

Daddy ne, ya tsayar da mustapha ta hanyar cewa.

" Ka tsaya RAUDA ta shirya sai ka sauƙe ta, a gidan su, kafin ka shige office ɗin.

Ɓata ransa mustapha yayi, yace.

" Daddy ni na riga na shirya, zan shige office kuma sauri nake yi, tunda ga Habeeb zai fita bai shirya ba, idan yaso saita jirasa ya sauƙe ta.

Momy ce tace.

" Habeeb baxai sauƙe ta ba, kaiɗin kaine zaka sauƙe ta, ka zauna ka jira ta har ta shirya, sai ku fita tare.

" But amma Momy......

Ɗaga masa hanu Daddy yayi tare da cewa

" Ya isa ka zauna ka jirata, ke kuma RAUDA jeki shirya maza karki ɓata masa lokaci.

Tashi RAUDA tayi tare da haurawa sama yayin da Mustapha ya bita da kallon ƙiyayya, da kuma harara.
Ran Mustapha idan yayi dubu toya ɓaci, akan me za'a zaunar dashi ace dole saiya jira wannan abar, shiya kawota gidan ne, koko zaman sa take cikin gidan, Habeeb ne, yazo daidai kunnen sa ya sunkuya, tare da cewa.

" Ka zauna kayi jiran Amarya yaro, don naga alama momy na sonka da RAUDA, sai kayi hkr, ka zauna jira.

Yana gama fadar haka ya ɗaga kansa tare da haurawa sama, yana yiwa Mustapha dariyar mugunta, harara mustapha ya bi Habeeb dashi ba tare daya tanka masa ba.

Har Habeeb ya fito, Daddy ya basa saƙo wajen Mlm Musa da Hajiya Innah, tare suka fice da daddy suka bar Mustapha Zaune yana jiran RAUDA.
Momy ce ta tashi tare da cewa, bari na haura sama naga maiya tsayar da RAUDA haka tun ɗaxu.

Shidai Mustapha baice komai ba, yana Zaune cikin haɗa fuska, yana ganin RAUDA da Momy suna sauƙowa, ya ɗauko baƙin glass ya manna a idon sa, tare da ficewa waje, cikin motar ya shiga ya zauna jiran ta, har bakin motar Momy ta rako RAUDA, tana cewa.

" To RAUDA ki gaishe da Hajiya Turai ɗin kice Mata, ina zuwa nima insha Allah, Allah ya kiyaye hanya mun gode sosai.

" Zataji RAUDA tacewa Momy, sannan ta buɗe gaban motar ta shiga, jan motar mustapha yayi ba tare daya kalleta ba.
Ƙira'ar malam Ibrahim Abdulrasheed Mustapha ya kunna cikin wayar yana bi a hankali.
Muryar RAUDA yaji tana cewa.

" Ya mustapha meyasa baka sona, menene Aibuna, kasan irin soyayyar da nake maka kuwa.......?

" Enough RAUDA, bana buƙatar jin muryar ki, cikin motar nan.

" Saboda ka tsaneni baka sona koh, dole ai kace nayi shuru, wani irin tsanane wannan, kodan nace ina sonka shine kake wulakanta Ni.

Dariyar takaici Mustapha yayi, tare da yin wani wawan burki, cikin tsawa yace,

" Fita min daga cikin mota, ki fita min nace daga cikin mota, sau nawa zan faɗa miki cewa bana sonki, ko ana soyayyar dole ce, fice min daga cikin mota.

Murmurshi mai ciwo RAUDA tayi tare da sa hannun ta, ta buɗe motar ta fice, cikin tsanar Zuciyarta data ke son Mustapha.

Tsuka mai ƙarfi Mustapha yayi, sannan yaja motar sa, tare da bule RAUDA da ƙura, yayi gaba abunda.

Share guntun hawayen daya cika mata Ido tayi, tare da tare mai adaidaita sahu.


*DASINA*

A hankali INDO take tafiya, ita a dole tasha gayu, ansha lalle da kitso harda, wanka aka sha, tafiya take a hankali, wai zatayi tafiyar ƴan gayu, wani yaro ne ya taho da bokitin ƙullin koko, a kayin sa, sanda yazo daf da INDO cikin tsautsayi, yayi tuntuɓe da ƙaton dutse, sheƙowa ƙullin kokon yayi gaba ɗaya jikin Indo ya wanke mata jiki, tun daga kayi har ƙafifin ta.

" *Kutumar Uba* dan ubanka tsinanne, shine zaka min wanka da ƙullin koko, tsabar kana baƙin cikin nayi wanka, to wlh yau sai naci kutumar ubanka, shaƙo wuyan sa, Indo tayi, haba wa, sai kokuwa, dakuwa suke sosai yayin da yara suka taru a kansu suna rera musu waƙa

" *Ku tasu arna ku tasu ku tasu ba mai raba ku, kai mu raba ace munyi zamba, ku tasu arna, ku tasu dai ba mai raba ku*

Aiko kamar zuga Indo suke yi, ta dage sai jibgar juna suke.

Habeeb da shigowar sa kenan, cikin ƙauyen ya hango yara cike sai zabgar kokuwa ake, parking yayi, tare da fitowa daga cikin motar ya nufo wajen nasu.

" Kai baku da Hankali ne, kuke kokuwa.

Juyowa Indo tayi cikin masifa da rashin Kunya, wa zata gani idan ba Mustaphan ta ba, fit tayi shuru tare da sake yaron tana dariya, tace

" *Tafi abunka kaci albarkacin masoyina mustapha jeka na tafe maka ya Mustapha yaushe ka zoka sannu da zuwa kaga yanxun nan Innah ta shiga cikin gidan mu bari na kira maka ita*.


Zaro ido Habeeb yayi jin ta kirasa da mustapha, kuma masoyina, daga bayan sa yaji yara na cewa lallai yau tasi'u Allah ya ƙwace sa a hanun Indo.

" *INDO Habeeb ya furta sai kuma ya kwashe da dariya tuno labarin Indo da mustapha yake basa, Ashe Itace ALJANAR MUSTAPHA LALLAI BARRISTER MAI ƳAN MATA KALA KALA*.

__________________________


Bana typing Ranar asabar yauma ganin da nayi kwana biyu banyi typing ba, yasa na daure nayi muku🙏🏻

*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah)*
[1/13, 3:29 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take a gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya🙏🏻


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••1️⃣7️⃣ ➡️ 1️⃣8️⃣

Cikin dariya Habeeb yace wa Indo.

" To jeki kira Hajiyan, idan kin kirata sai ki wanke jikin ki koh, dan kin Zama dodo.

Sake baki Indo tayi tana kallon Habeeb cikin mamaki wai yau mustapha ne yake mata magana cikin sakewar fuska, mutumin da baya dariya, kullum cikin faɗa yake, ƙara leƙa fuskar tasa ta Indo tayi.

" Lafiya kike leƙen fuska ta, cewar Habeeb.

Wangale yellown hakwaren ta Indo tayi, tace wa Habeeb, gani nake kamar ba kai bane ya Mustapha, shifa ya Mustapha yana da faɗa kuma kullum cikin haɗewar rai yake, kai kuma naga kana dariya kuma baka faɗa.

Dariya Habeeb yayi Yace.

" Nine mana na sanja miki ne, Hajiya Indo.

" *Aradun Allah ya mustapha ka sauya kodai ka fara sona ne, yanda kake min murmurshin nan dafe ƙirjin ta Indo tayi tace har ji nake wasu kifiyoyin sonka na harbi na, a ƙirji na, Wayyo Allah Wlh ya Mustapha sonka yamin ɗaurin huhun goro ina sonka ya Mustapha na dan Allah kaima kace kana sona ko zanji daɗi*

Dariya sosai Indo ta bawa Habeeb dariya yake sosai, domin shi Wlh yarinyar ma, comedy ɗinta burgesa yake.
Cikin dariyar yace.

" Jeki ki kira Hajiyan ni na wuce, gidan nata idan mun sake haɗuwa zan gaya miki, motarsa ya koma yaja shi zuwa ƙofar gidan Innah.

Da gudu Indo ta shigo cikin gidan har tana tuntuɓe.
" Hajiya Innah !! Hajiya Innah.

Innah da suke zaune da Mama suna firar duniya, tace.

" Lafiya Indo kike min wannan kira kamar wacce kike bina bashi.

Mamace tace.

" Hajiya ai kinsan Halin Indo babu hankali sam a tare da ita, kullum cikin shashanci take, bata da nutsuwa sam.

Tura baki Indo tayi tare da ɗaukar bokiti, tayi wajen randa tana cewa.

" Ya mustapha ne, yaxo, shine yace na mishi kiran sa, idan kinga zaki iya zuwa kije idan kuma bazaki iya ba, Sai ki zauna ni dai wanka na zanyi naje *musha fira da masoyina*.

Salati Mama ta ɗauka tana cewa.

" Lallai Indo rashin kunyar taki ta shahara yanxu gaban mu kike kiran masoyi, Allah ya shirya ki, to waima ke a hakan za'a soki baki da hankali da nutsuwa, ga rashin mutunci, da fitsara, babu wanda baki iya ba, ciki, Babu mai sonki a haka.

Dariya Hajiya Innah tayi tana cewa.

" A'a maryama aiko INDO sai tafi ƴan matan garin nan farin jinin Samari kinga indodo na maza jeki kiyi wankan ki, rabu da maryama.

" Ai nima Innah yau banda lokacin ta, bare naji haushin zancen ta tunda ya Mustapha yamin dariya Kuma yace naxo zaice min yana sona.

Zaro ido Innah tayi tace mustaphan, ne yace miki haka, wannan ɗan bakin Halin tsiyar, ikon Allah, naga wata sabuwar yaudara gurin Muhammadu, anya ma kuwa mustapha ne, yaxo garin nan, gani nayi kwatakwata satin sa ɗaya da zuwa, amma ban sani ba ko ubansa Haruna ne ya aiko sa, maryama bari naje gidan na gani.

" To Innah na gode a huta gajiya.
Cewar Mama.

INDO kuwa wankan ta, ta shige tabar Mama zaune tsakar gida.

Da sallama Innah ta shiga cikin gidan Habeeb ta hango Zaune bakin ƙofar ɗakin ta, daga nesa itama INNAH tayi zaton mustapha ne, sanda ta ƙaraso daf dashi, taji Habeeb ya sureta yana hajijiya da ita, domin tasan shi kaɗai ne, mai mata wannan yahudancin, rufe idonta Innah tayi gam, tana zagin Habeeb.

" Ka sauƙe ni dan ubanka Haruna, kaji ɗan iskan Yaro zai ƙarasa ni.

Cikin dariya Habeeb ya sauƙe Innah tare da cewa.

" Missing ɗinki nayi fah Amarya ta, an juma ba'a haɗuba, yanxu na ganki kuma ai dole na juyaki.

Dariya Innah tayi tace.

" Ja'iri Habibu aini nasan babu mai min wannan iya shegen sai kai, yaushe ka dawo ƙasar, kullum saina tambayi Muhammadu, kai sai yace min ai baka da Ranar zuwa ɗan albarka Ashe kaine kake tafe, ni fah nayi mamaki da naji Indo tace min Muhammadu ne yaxo.

Dariya Habeeb yayi yace.

" Nine nan Innah nayi nayi mustapha mu taho tare wlh wannan bawan Allah yaƙi, wai ba yanxu ba, ko dai kina basa ciwon kaine Innah.

" Toni ina ruwa na, dashi idan yana soma karya ƙara zuwa waje na, daga nan har abada, dan ubansa.

Dariya Habeeb yayi Yace.

" Ni Babu ruwana a tsakanin ku, kunfi kusa, nine bare tsakanin ku, bari naje nayi wanka, akwai kaya cikin but ɗin mota, bari nayi wanka saina nemo yara su kwashe, yace akwai wanda za'a kai gidan Mlm Musa.

To saika fito cewar Innah, ɗakin da mustapha yake sauƙa inda yaxo garin shima Habeeb nan ya sauƙa.
Wanka Habeeb yayi tare da kwantawa baccin gajiya.

Wanka Indo tasha fes da ita, ta taho gidan Innah, Innah tana zaune tsakar ɗakinta Indo ta shigo tana leke leƙen ta ina zata ga mustapha, ɗakin Innah taxo ta zauna tare da cewa Innah, ina yaya Mustapha yake.

Dariya Innah tayi, tace.

" To shasha wannan ba Muhammadun bane, Habibu ne, ɗan uwan haihuwar sa, kamace kawai suke, sai banbancin hali da suke dashi.

" *Haba haba daman dai akwai walakin goro a miya, nidai nasan mustapha bai taɓa min dariya ba, wannan kuwa yana dariya, harma da kula mutum, kallon jikin ta, tayi yanda tasha wanka harda ɗige ɗige da tasha a fuskar ta, sai kuma tasa kuka 😩 tace yanxu kenan nayi wankan banxa, wlh danasani banyi wannan wankan ba*.

Dariya sosai Innah tayi tace.

" Yanxu ke INDO baza kiyi wanka danjin daɗin jikin kiba, sai dan wani, amma dai kinji kunya Wlh.

Ƙara sautin kukan ta Indo tayi, tsakanin ta da Allah take kuka tana yiwa Innah masifa, cikin ɗaga murya.

" *Ni ki ƙyaleni nayi kuka na, Wlh banyi niyan ƙara wanka ba, sai wani sati Ranar juma'a shine ya cuceni yasani nayi, har yasa naji kifiyar Son ya Mustapha ta sokeni ashe ba shi bane, Kuma wlh wankan Allah ya isa nayi, tunda banyi niya ba, kuma Innah kiga fah yanda na zage nayiwa fuska ta kwalliya, duk dan ya Mustapha yace nayi kyau*.

Habeeb da tun sanda yaji hayaniyar Indo ta hanasa bacci ya fito, ya tsaya gefe yana kallon shirmen Indo, shi Wlh burgesa take idan tana wasu abubuwan.

" To kukan ya isa haka.
Taji Muryar Habeeb daga bayan su.

Tsale Indo tayi ta diro gaban Habeeb tana ƙara sautin kukan ta, tana cewa.

" *Baxan yi shuru ba Wlh yau wuni zanyi ina kuka, kuma Na wuni ina zan Allah ya isa, dan ancuce ni Wlh.*

" 😆 Ikon Allah yau ni Habeeb ina ganin ikon Allah, to naji, idan kin wuni kina kuka ai kanki ma wuni zaiyi yana miki ciwo, to wai Allah ya isan wa kika jawa shi?.


" *Kai kai na jawa Wlh, tunda kaine kayi kama da ya Mustapha na, shine harda cemin kaine ya Mustapha, ashe ƙarya kake min, KUMA NA

Please Login or Register in order to submit comment