Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masu taken👇🏻

*RUƊANIN ZUCIYA BIYU*

*SO BAI SAN JINI BA*

Zan sake muku wannan book ɗin na *So bai san jini ba* free, 12/3/2020 idan Allah ya kaimu, ku dai ku kasance dani, domin book ɗin yazo da sabon salon labari, wanda na rubuta shi cikin nutsuwa hikima da basira.

*RUƊANIN ZUCIYA BIYU* Shi kuma zan sake muku shine Bayan na kamalla book ɗina na *Indo a birni* amma shi Ruɗanin zuciya biyu na kuɗi ne, zan sake muku shi a farashi ƙalilan, 200 kawai zaku biya kusha karatu cikin nutsuwa, ku dai ku shirya karku bari a baku labari, domin wannan book ɗin ya haɗa abubuwan al'ajabi da yawa, Soyayya tausayi, ƙiyayya, son Zuciya, da dai sauransu ku dai ku kasance da alƙalamina har zuwa ranar da zan fara sakin wannan book ɗin.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••4️⃣3️⃣ ➡️ 4️⃣4️⃣

"Wai me! wannan yarinyar take muku ne, da gaba ɗaya kuke ƙaunar ta, duk tabi ta lashe muku zuciya, to wlh idan ma iyayenta na can ƙauyen sun asirce kune, to wlh ni nafi ƙarfin su, kuma alƙawari na ɗaukar wa kaina saina kori yarinyar nan daga cikin gidan nan."

Girgiza kansa Habeeb yayi ba tare daya ƙara cewa Momy komai ba, ya fice daga cikin ɗakin cikin ɓacin rai, yana mamakin halin mahaifiyar tashi, yanda ta sauya lokaci ɗaya akan yanda yasan ta a baya.

Ƙwafa Momy tayi tare da cewa.

" Aikin banxa aikin wofi! Yarinyar da tafi ƙarfin iyayen ta, ta addabi garin su, shine ni za'a ɗauko min ita a kawo min cikin gidan, ita Inna har zata biyo ta, a zauna ana cimin mutunci akanta to wlh Abunda baxai yiwu bane idan har Inna ta cigaba da bin bayan yarinyar nan ni kuma na ƙalla da cin ubanta! cikin gidan nan kenan."

Haka Momy ta dinga mita ita ɗaya cikin ɗakin.

Shiko Habeeb shigewa yayi ɗakin su tollet ya shige, ɗaure da towel yayi wanka ya fito, ringine ɗin wayar sa, yaji ɗaga wayar yayi yana murmurshi tare da furta *HASINA* a hankali, ya ɗan juma yana wayar kafin ya katse, shiryawa yayi cikin jallabiya, sannan ya ƙara ƙarfin Ac ya kwanta tare da rufe idonsa yana son hutawa.

A gajiye Sharifa ta shigo cikin gidan, kusa da Indo ta Zauna tana cewa.

" Wash! Allah na wlh na gaji sosai."

Dariya Indo tayi tace.

" Sannu Sharifa, har kin dawo?"

" Na dawo Allah yau na gaji cikin kasuwar nan, kinga kayan ki" (ta turowa Indo kayan gaban ta)

Buɗe kayan Indo tayi tana kallon su tana dariya, cikin murna, dogayen Riguna ne, masu tsadar gaske, tare da riga da siket masu shegen kyau, dariya tayi tace.

" Aradu sunyi kyau Sharifa, sai dai kuma banga atampa ba fa cikin kayan."

Murmurshi sharifa tayi tace.

" To uwar rashin haƙuri, idan Daddy ya dawo zai taho da Atampopi sai mukai ɗinki gobe."

Dariya tayi tare da cewa.

" Yauwa sai yanxu naji magana, Sharifa ya Habibu ya dawo, ɗazu."

" Dan Allah da gaske kike ya Habeeb ya dawo?"

" Allah da gaske nake ya dawo yana sama yace zai huta."

Murmurshi sharifa tayi tace.

" Kaya na sunxo, bari nima naje nayi wanka kafin ya fito."

Haurawa sama Sharifa tayi tare da ledar kayan Indo, su Ishaq ne, suka dawo daga school da gudu Sharif ya faɗa jikin Indo yana cewa.

" Aunty Indo yau kamar kece na gani a makarantar mu, kunyi fannin ƴan Secondary school ss keda ya Mustafa, har zan fito sai uncle din mu ya hanani."

Dariya Indo tayi tace.

" Nice wlh, daman makarantar kuce, nima ai nan Daddy ya saka Ni, ashe zamu dinga tafiya tare, ai da nasan ajin ku aradu da saina shiga."

Ishaq ne yace.

" Lah! Aunty Indo kema yanxu ƴar makarantar muce, to aike Secondary ne, mu kuma primary fa, to yaushe zaki fara zuwa?"

" Oho nima ina na sani, sai sanda Daddy yace na fara tukunna."

Momy da take sauƙowa daga step ta hango su Ishaq maƙale jikin Indo ya sata daka musu tsawa tare da karasowa wajen da sauri, ta kama kunnen su tace.

" Kai! Sharif, me kuka tsaya yi anan to daga yau karna ƙara ganin ku, kusa da wannan abar tsiyar"
Zaro musu Ido tayi tace kunji ko baku jiba.

Da sauri suka haɗa baki wajen cewa.

" Munji Momy bazamu sake ba."

Sake musu kunnen tayi tace.

" Maza ku haura ku cire uniform" maida kallon ta, tayi wajen Indo tace mata.

" Ke kuma ki fita harkar yarana, dan bazaki lalata min tarbiyyar yara ba, ke kin lalace nima kixo ki cuceni ta hanyar koyawa yarana munguwar ɗabi'ar ki."

Shuru Indo tayi tana kallon Momy tare da tunanin meye ne munguwar ɗabi'ar tata, sai kuma ta kawar da kanta daga kallon momy ta tashi tayi ɗakin Inna, tsuka Momy taja sannan ta zauna.

Inna tana shan Baccin ta, Indo ta kwanta Kusa da ita, sai kuma ta shiga tunanin maganganun Momy, tashi Indo tayi kamar wanda aka tsikareta, ta fito ta wuce Momy a falo ta haura sama, ɗakin su Mustafa ta faɗa tana Sallama taji shuru, shiga tayi tana karewa ɗakin kallo yanda yasha ado kamar ɗakin mace, komai a shirye tsaf, a kwance taga Habeeb yana bacci, zama tayi gefen sa, tare da kiran sunan sa, sanda ta kira kusan sau uku sannan Habeeb ya buɗe idonsa.

" Mamana lafiya?"

Tura bakin ta, tayi tace.

" Lafiya lau daman zan tambaye kane?"

Tashi Habeeb yayi yace.

" Naji tashi mu fita waje sai muyi maganar acan ko."

Tashi tayi suka fito, ganin Momy cikin falon yasa Habeeb yin compaunt ɗin gidan, Itama Indo bayansa tabi, Momy kuwa taɓe bakinta tayi, bayan sun shige taci gaba da kallon ta.

Waje Habeeb ya samu ya zauna kan wasu kujerun roba dake zagaye a gefe, itama Indo zama tayi, Habeeb ya dubeta yace.

" Ina sauraron ki Mamana, menene tambayar?"

" Ya Habibu wai da gaske ina da munguwar ɗabi'a ?"


Zaro ido Habeeb yayi yace.

" Wa yace kina da munguwar ɗabi'a ?"

" Momy ce wai karsu ishaq su sake kulani ina da munguwar ɗabi'a "

Girgiza kansa kawai Habeeb yayi cikin ɓacin rai akan abunda Momy takeyi, shidai da baisan Momy da wannan halin ba, to meya sauya Momy haka lokaci ɗaya, kodai akwai Abunda Indo ta mata ne, wanda bata ji daɗin saba? Duban Indo yayi yace.

" Ke baki san meye munguwar ɗabi'a bane?"

" Ya Habibu da na sani ai bazan tambaye kaba, Allah ban sani ba."

Murmurshi Habeeb yayi yace.

" To bari na faɗa miki, na farko shine kin cika yawan faɗa, sannan baƙya hakuri, kina da rigima, ba kuma kya nutsuwa sannan baƙya jin magana, shine fa kawai munguwar ɗabi'a, kuma da zaki gyara ko, ba ƙaramin burge kowa zakiyi ba, ke kanki zakiji ki, kinfi da jin daɗi, kuma ma ba kince min zaki rage yawan rashin jiba, ko kin manta alƙawarin da kika min?"

Tura baki Indo tayi tace.

" Ban manta ba fa ya Habibu kuma Allah na rage, kaga yanxu ma baki na har brush nake, kaga ta buɗe masa haƙori, tace kuma Allah ya Habibu zan daina rashin ji, kuma zan nutsu, to ya Habibu ya ake nutsuwa?"

Dariya sosai Habeeb yayi yace.

" Good question Mamana, kinga ki daina yawan magana, ki kuma daina faɗa ki dinga tsafta, idan manya sunce kiyi, to kiyi idan sunce ki bari to ki bari."

" Allah ya Habibu nama daina su daga yau, zanke jin maganar kowa."

Dariya Habeeb yayi sannan suka cigaba da taɗinsu, suna dariya harda tafawa, a wunin Ranar Habeeb biyewa Indo yayi, suka ta shashanci kamar yara ƙanana.

Da la'asar lis Momy da sharifa na kitchen, ita kuma RAUDA tana cikin ɗaki tana kwance, kasancewar ta dawo daga makaranta a gajiye, Inna Kuma da Indo sai Habeeb suna zaune falo, Mustafa ya shigo, zama yayi kusa da Inna yana cewa.

" Hajiya tsohuwa mai ran ƙarfe, me zan samu ne?"

Hararar Mustafa Inna tayi tace.

" Aiko ina da abun bayarwa bazan baka ba, gara na bawa Habibu tunda ya miki sanin ya kamata."

Gabaki ɗayan su, dariya sukayi Mustafa da Habeeb, Habeeb ne yace.

" Haba Inna Angon naki, zaki ce babu baisan ya kamata ba."

" A'a yanxu bana Auren dashi, gwara na dawo da Auren kanka Habibu sai nafi samun kwanciyar hankali akan wannan ɗan baƙin ran tsiyar."

Fakar idonsu Indo tayi ta ruga ɗaki da gudu, karkashin nan ta ɗauka wanda ta jiƙasa ya jiƙu yasha yauƙi har ya gaji, ta fito da sauri ta laɓe bakin ƙofar ɗakin su, tana jirar Mustafa.

Dariya Mustafa yayi yana cewa.

" Nima bana Auren kije na miki saki uku, saiki tare wajen Habeeb ɗin" ya ƙarasa maganar yana dariya tare da haurawa sama.

Ganin tahowar Mustafa da Indo tayi ya sata kwasa da gudu taje ta kwara wannan ruwan karkashin, ta koma ɗakin nasu da gudu, tare da hararar RAUDA dake kwance tana Bacci ba tare da tasan tana yiba, Allah sarki Mustafa shiko tafiyar sa yake ba tare daya kawo komai cikin ransa ba, taku ɗaya yayi ƙofar ɗakin nasu, ya kawo ƙafarsa ata biyu, yaji wani irin santsi ya ɗebesa, ji kake *Tim* Mustafa ya sauƙa kasan tayels, wani irin ƙarar Azaba Mustafa yasa tana riƙe kunkumin sa, ya runtse idonsa, a firgice suka haura saman cikin gudu, harta RAUDA dake bacci saida wannan ƙarar ya tashe ta, kusan tare suka fito da RAUDA, Habeeb kan Mustafa zaiyi a gigice, Indo tayi karaf tace.

" Ya Habibu rufawa kanka asiri karka taka wajen nan idan ba so kake, kuma kuyi jinya ku biyu ba."

Turus Habeeb ya tsaya yana duban Indo cikin tuhuma yace.

" Me kike nufi da kar muyi jinya mu biyu?" Tare da tsareta da idanun sa cikin tuhuma yake mata tambayar?"

" Ni fa ba wani abu bane gani nayi mutum ya faɗi bamu san meya kada shiba haka kawai kaima ka hau ba tare da ka kula ba."

Inna ce tayi carap tace.

" Kuma gaskiya ce maganar Indo, ke dai Allah ya miki Albarka da kika kular damu."

Momy kuwa ta gigice za tayi kan Mustafa dake zaune daɓas cikin azaba ya kasa tashi saima runtse ido da yake, ko kafin Momy ta ƙarasa Habeeb ya lura da ruwan dake kwance ƙasa, yayi saurin cewa Momy.

" Dakata Momy! Kamar ruwa nake gani kwance a ƙasa."

Tsayawa Momy tayi tare da kai duban ta, ƙasa, kusan tare suka sunkuya da Habeeb, hanun su, suka saka sai sukaji yauƙi sosai, saurin duban juna su kayi Momy tace.

" Yauƙi meya kawo yauƙi cikin gidan nan, rabon da muyi amfani da yauƙi ko muyi miyar yauƙi cikin gidan nan, an daɗe, to wa ya zuba yauƙi?"

Saurin duban Indo Habeeb yayi, rashin gaskiya ƙarara ya hango cikin idanunta, ya Kuma san tabas itace kawai zata iya wannan ɗanyen aikin cikin gidan nan, duban Momy yayi yace..................



Kuyi hkr da wannan wlh yau ina busy ne, naso nayi yafi haka yawa.


Please karku manta dani cikin Addu'ar ku🙏🏻


*Vote*
*share*
*and*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


*(Ummu Nasmah ce)*
[2/13, 1:04 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*Jinjina*

Bazan gaji da jinjina gare kuba, waɗannan jarumai, Yaya Mu'az Hassan Tanko Hussaini 80k Yaya Hayat, Ubangiji Allah ya biya muku bukatun ku na Alkairi, ya haskaka muku rayuwar ku, muna matuƙar godiya gare ku, bisa Taya mu posting da kuke, Allah ya saka da Alkairi🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻🤝🏻


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••4️⃣5️⃣ ➡️ 4️⃣6️⃣

" Momy kiyi tunani dai da kyau, ko kinyi amfani da kuɓewa ko karkashi, su Ishaq su gani su ɗauka suyi wasa dashi, kinga dai nan kam kowa da hankalin sa, ba wanda zai ɗauki karkashi harya zubar" Habeeb ya faɗawa Momy haka ne saboda yasan yanda take son Ishaq da Sharif bazai bari ta tsananta bincike ba.

" Babu wani tunanin da zanyi domin kuwa ni banyi amfani da duk abunda ka kira ba, rabona dasu na kusa shekara, sai dai kuma idan aljanu ne, suka zubar."

Takaici da haushi ne, ya ishi Mustafa, cikin ɗaga murya yace.

" Ni! Wannan maganar ta isheni haka, koma waye ya zuba dai yanxu kam ya wuce, tunda dai ya riga da yayi Aikin sa, kuma koma waye ne, zan binciko shi da kaina, kaga Habeeb ni tsallako ka kamani na tashi, ba bincike bane a gaba na."

Harara Habeeb ya aikawa Indo yanda babu wanda zai lura da hakan, sannan ya tsallaka tare da miƙawa Mustafa hanu hanun nasa Mustafa ya kama tare da tashi da ƙyar, a bakin gado ya zauna yana wash, duka biyosa sukayi ɗakin suna masa sannu, RAUDA ce, cikin rau-rau da idanu kamar zatayi kuka tace.

" Sannu ya Mustafa"

Bai ɗaga kai ya kalle ta, ba bare kuma ya amsa, ganin haka da sharifa tayi ya sata juyawa ta fice daga ɗakin ba tare data masa sannu ba, Habeeb ne, ya buɗe jakarsa ya ɗauko magani ya bawa Mustafa tare da ruwa, karɓa Mustafa yayi ya haɗiya, tare da kwantawa yana lunshe idonsa, cikin Azaba, towel Momy ta ɗauko ta sunkuya ta goge masa yauƙin ƙafar tasa, tare da ɗauko karamin baho da ruwa ta wanke ƙafar tas, sannan ta juya, a bakin ƙofa ta taradda RAUDA tana mopping ɗin wajen da aka zubar da karkashin, murmurshi Momy tayi tace.

" Sannu RAUDA Allah ya miki Albarka."

Da ameen RAUDA ta amsa sannan Momy ta shige, Inna kuwa a cikin sai sannu take yiwa Mustafa ta kasa dainawa, tana cewa.

" Sannu Muhammadu, ko wani mungun ne, yayi wannan aikin sai Allah, Allah dai ya toni asirin sa, koma waye, bari kaga naje na dafa ruwan zafi nazo na gasa maka ƙugunnaka."

Shi Mustafa koma kallon Inna baiyi ba, bare ya bata amsa, saima Habeeb ne ya zaro ido yace.

" Inna wani ruwan zafi kuma? muna zaune lfy ga magani tasha, to mudai bama bukatar ruwan zafi, muna da magani ya ishe mu."

" To likita bokan Turai to tun kafin a haifi ubanku ake amfani da ruwan zafi, wajen maganin ɗumuwa wai kaima ɗan zamani, zaka wani kira min magani, sai kuje kuta amfani da maganin naku ai" tana gama faɗin haka Inna ta fice.

Dariya Habeeb yayi tare da duban Mustafa yace.

" Sannu Bros, Allah kasha wahala, sosai faɗuwa saman tayels ai akwai Azaba.

" Kai dai bari Bros Habeeb wlh ji nayi kamar wanda ake zare min rai, kaji kunkumi na kuwa, rufin asirin ma, ban faɗi akan ƙafata ba, Allah inaga da karyewa zanyi."

" Sannu bari naje na haɗa maka ruwan zafi kayi wanka, tunda Inna daga wasa tayi fushi tace ta fasa tausaka, ni bari naje na haɗa maka."

Dariya Mustafa yayi yace.

" Rabu da Inna, ni jeka haɗa min ko zanji sassauci."

Shigewa tollet ɗin Habeeb yayi yana dariya.

Dariya sosai Indo takeyi tana riƙe cikin ta, domin kuwa ko banxa yau ta rama dukan ta, na ƙauye daya mata, tana cikin dariyar ne, Sharifa ta shigo cikin ɗakin duban Indo tayi tace.

" Ke kuma dariyar me kike haka, kamar wacce aka miki Albishir da gidan Aljanna?"

" Babu komai fa, kawai wani abu na tuno shiyasa nake dariya."

Kaɗa kanta Sharifa tayi ta zauna tana ɗaukar wayar ta, tare da cewa.

" Ki tashi kije ki ɗauki kayan ki, ki sasu cikin drower."

Da to Indo ta amsa tana dariya ta tashi ta nufi drower, shigowar Habeeb cikin ɗakin yasa Sharifa ɗaga ido tana kallon sa, bai kalli Sharifa ba, ya nufi Indo tare da hama Hanun ta, sukayi waje, kallo Sharifa ta bisu dashi har suka fice, RAUDA dake tsaye tsakiyar falo taga Habeeb sun wuce riƙe da hanun Indo, ta bi bayan su da sauri, Habeeb bai sake Indo ba, saida sukaje garden ɗin gidan sannan ya sake ta, RAUDA samun waje tayi ta ɓuya inda bazasu ganta ba, duban Indo Habeeb yayi yace.

" Meyasa kika watsa masa yauƙi a ƙofar ɗaki?"

" Ya Habibu ni kuma na watsa masa yauƙi?"

" Eh ke ina kallon ki, ai sanda kika watsa masa" Habeeb ya gayawa Indo haka dan ta faɗa masa gaskiya.

Shuru Indo tayi tana tura baki taƙi magana.
Kallon ta Habeeb yayi yace.


" Okey bazaki sanar dani ba ko? Shikenan bari naje na sanar da Momy cewa kece kika watsa yauƙin."

Magana tayi tana haɗa rai tace.

" To ba shi bane yake min mugunta, ranar a ƙauye yamin duka harda kunbura min jiki, ranar kuma a falo ya dakeni, shine shekaran jiya kuma ya zageni, ni kuma shine na rasa da Abunda zan rama shine na zuba masa karkashi ya faɗi, shima yaji in akwai daɗi."

" Good! Zargina ya kasance gaskiya, to waima tukanna a ina kika samu karkashin?"

" Randa ya kaini makaranta ne, ya tsaya ya shiga wani kanti, shine ni kuma naga mai karkashin na fita na roƙesa, shine sai ya bani biyu."

Rufe baki RAUDA dake maƙale jikin bango tayi tana zaro ido, a hankali yanda bazasu ganta ba ta juya tayi cikin gida domin kai rahoto.

Girgiza kansa Habeeb yayi, cikin mamakin halin Indo, zama yayi sannan yace mata itama ta zauna, zama Indo tayi, Habeeb ya dubeta tare da cewa.

" Zan roƙeki a karo na uku na kuma saka miki doka cikin gidan nan, idan baki daina ba, Allah babu ruwana da ke cikin gidan nan, bazan kuma sake kulaki ba."

Shuru tayi tana haɗa rai, kafin Habeeb ya cigaba da cewa.


" Daga yau babu ruwan ki da Mustafa, karki ƙara shiga harkokin sa, in kin gansa ki gaishe shi kawai idan kuma ya saki aiki ki masa ki daina raina sa doka ta ɗaya kenan, doka ta biyu, karki yadda ki dinga yiwa Momy Rashin kunya, duk abunda ta miki wanda bakiji daɗin saba, ki bata hkr kiyi shuru, karkice zaki mayar mata magana, doka ta uku, kinga ki daina cewa kina son Mustafa domin yanxu ke karatu kika saka a gaba ba soyayya, ba kinga yanxu ke karatu ne ya kamace ki ba soyayya ba, idan kin nutsu kinyi karatu zaki taimaki rayuwar ki, domin kuwa gaba zaki zama cikakkiyar mutum, zaki taimaki kanki da iyayen ki, ki nutsu dan Allah ki gyara rayuwar ki, ki zamo kamar kowace ƴa wacce ko wacce uku take alfahari da ita" karo na farko da Habeeb ya kira sunan Indo na gaskiya yace " A'isha ki dubeni da kai ki kuma kalli ƙwayar idona ina son ki ajiye wannan Abunda zan faɗa miki cikin zuciyarki da ƙwaƙwalwar ki, na tabbata gaba sai kin tuno dashi duk sanda Hankali ya mamaye jikinki, *KI SANI CEWA MAI SONKI DA GASKIYA SHINE WANDA ZAI GAYA MIKI GASKIYA CIKIN RAYUWAR KI, YA KUMA NUNA MIKI HANYA MAI KYAU A'ISHA MAI SONKI DA GASKIYA BAZAI TAƁA KYAMAR KIBA KO YAYA KIKE, KI SAKA ARANKI CEWA NI HABEEB MASOYINKI NE NA GASKIYA, BANA JIN DAƊI IDAN HAR MUTANE SUNA AIBATAKI, PLEASE DAN ALLAH BADAN NIBA KI GYARA HALINKI*."

Shuru Indo tayi Yayin da jikin ta yayi mungun sanyi, tabbas maganganun Habeeb sun shiga jikin ta, babu mutumin daya taɓa maganganu masu ratsa jiki sai yau duban Habeeb tayi cikin sanyin murya wanda bansan Indo tana dashi ba tace.

" *YA HABIBU IN SHA ALLAH BAZAN SAKE ABUNDA NAKE BA ZAN SANJA DAGA YAU, ZAN KUMA YI KARATU KAMAR YANDA KA UMURCE NI, DAGA YAU BAZAN SAKE FAƊA DA KOWA BA NA DAINA KAYI HKR*."

Murmurshi Habeeb cikin jin daɗi yace.

" Good ƙanwata, na gode yanxu tashi ki koma ciki Allah ya miki Albarka."

Da ameen Indo ta amsa sannan ta shige cikin sanyin jiki, a falo ta taradda Momy tsaye rike da ƙogu tana jiran shigowar Indo RAUDA na tsaye gefen ta, Inna kuwa tana zaune gefe Indo na shigowa Momy ta finciko ta, tare da ɗauketa da tagwayen maruka, a har zuƙe Inna ta tashi tayi kan Momy, sarin shan gaban Inna Indo tayi, tana girgiza mata kai tare da cewa.

" Karkice komai Inna ki barta ta hukunta ni idan na mata laifi ne, Inna duk abunda za'a min cikin gidan nan, na rokeki da Allah karki ƙara magana, Inna na sauya a Indon da kika sani da, Inna ko kin manta Maganar Mamana sanda zamu taho garin nan, cewa tayi bani da wata uwar da ta wuce Momy yanxu, dan haka ki barta tayi hukunci gare ni."


Sake baki Inna tayi tana kallon Indo a fiska dai indon da ta sani ne, amma a kalamai kuma ba Indo da ta sani bane, " ikon Allah Inna ta furta, tare da ɗaga hanu tana cewa, alhamdulillah! Abunda nake faɗawa iyayen ki kenan suyi hkr wata rana Allah zai shirye ki, gashi kuma yau lokacin yaxo" shigewa Inna tayi ɗaki tana cewa Momy " ke kuma kinji kunya Wlh ki rasa wa zakisa a gaba sai wannan ƙaramar yarinyar."

Taɓe baki Momy tayi tana cewa Indo.

" Wani sabon salon iskancin kika ɗauko kenan, shegiya mayya, wato bari ki kashe min ɗa ko harda zuba masa karkashi, Allah bai kashe sa ba, ke baki isa ki kashe shiba, ɓace min a nan kafin na illata ki, munafuka kawai."

Shigewa Indo tayi ba tare da tacewa Momy komai ba, RAUDA ce ta dubi Momy tace.

" Munafurci ne fa Momy, Allah Momy bana ƙaunar yarinyar nan."

" Yo to nima RAUDA ƙaunar ta nake ne, dole tasa take zaune cikin gidan nan badan ina soba wlh, kinga wuce gije ki ƙarasa girkin nan, na gaji."

To RAUDA tace tare da shigewa kitchen ɗin, Indo kuwa tayi cikin ɗakin su, ta buɗe drower ta kintsa kayan ta, sannan ta zauna gefen kujera guda ɗaya dake cikin ɗakin tayi tagumi tana tunanin maganganun Habeeb, a fili tace.

" Mutum Shida kawai ke sona cikin gidan nan Inna Sharifa ya Habibu Daddy sai su Sharif, ya Habibu in sha Allah bazan baka kunya ba, na sanja daga yau."

haka Indo ta wuni cikin sanyin jiki ranar, da daddare Bayan dawowar Daddy suna zaune Momy tace RAUDA taje ta dauki abincin Mustafa ta kaimasa ɗaki bazai iya saukowa ba, tashi RAUDA tayi cikin sauri ta haura cikin ɗakin su, ta ɗauko maganin da Mamy ta ta dawo cikin kitchen ɗin, buɗe kololin abincin tayi cikin tsarguwa tana leƙe-leƙe ta zuba maganin cikin abincin, haurawa tayi cikin sallama,ta shiga ɗakin, amsawa Mustafa yayi, Habeeb dake kwance ya zurawa system ido, murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

" Ƴar ƙanwata kece tafe?"

" Nice ya Habeeb ai nayi fushi da kai tunda ka dawo ko Magana Babu."

Dariya Habeeb yayi yace.

" Sorry sis ai kinga tunda na dawo bakya nan kina school ɗazu Kuma ina busy, just sorry."

" Shi kenan ina tsaraba ta?"

" Tana cikin jaka, sai da safe zan bawa kowa tashi."

Murmurshi RAUDA tayi tare da cewa"Allah ya kaimu" duban Mustafa tayi tace.

" Ya Mustafa wai ga Abinci inji Momy?"

Sai yanxu Mustafa ya ɗago kai ya kalli RAUDA yace.

" Ki mayar da abincin nan, kice na koshi yanxu nasha yoghout bana jin yunwa sai dai kuma indan Habeeb zaici sai

Please Login or Register in order to submit comment