Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zageni, Babu laifi nane da nake kulaki, shi mustapha ai da Baya kulaki baki zagesa ba sai Ni, ya karasa maganar cikin, haɗa fuska.

Duk tsiyar Indo da iya shegen ta, sanda taji jikin ta, yayi sanyi, karo na farko da taji tayiwa wani rashin kyautawa, har taji tayi danasani, shuru tayi tare da cewa.

" *KAYI HKR DAN ALLAH BAZAN SAKE BA*.

Ƙin kulata Habeeb yayi, ya kuma kawar da kansa gefe, yace.

" Ki tashi ki fita ki bar min ɗaki na.

Zama Indo tayi daɓas gaban Habeeb tana masa magiya kan yayi hkr, amma ina Habeeb ko kallon ta baiyi ba, bare tasa ran zai kulata.
To fah Indo ta fara ƙula, ganin yanda take bawa Habeeb hkr amma yaƙi kulata, cikin jin haushi tace.

" *Shikenan to, tunda baza kayi hkr ba, inata baka hkr kaki kulani dan ma ka samu na baka hkr, Aradun Allah ban taɓa bawa Kowa hkr ba, har Mama, sai kai Kuma kace baxa kayi hkr ba, sai Kuma ta fashe da kuka tana Cewa, shikenan tunda kaƙi kulani kuma wlh baxan bar nan ba, ina Zaune har sai kace kayi hkr, da makarantar Allo zan tafi, Kuma na fasa zuwa tunda baxa kayi hakuri ba, tana kukan ne take wannan maganar*.

Dariya Habeeb yayi cikin jinjina yarintar Indo, yama rasa dame zai fassara, wannan hali na Indo, da yarintar zai kirasa ko kuma da me zai kira, tunda dai yanxu Indo zatayi shekara goma a duniya, kamar dai ta wuce a kira shi da yarinta, ya kuma fuskanci yarinyar tana da sauƙin kai, idan zaka bita a hankali, tana kuma da fahimta, ya fuskanci Indo tana son mai kulawa da lamarin ta, tunda gashi yanxu har hkr take basa, da ace ni mazaunin kasar nan ne, to tabbas zan iya sauyawa Indo halayyar ta, kuma yarinyar da zata gyaru cikakkiyar mace za'a tayar, murmurshi Habeeb yayi, sannan yaci gaba da maganar zucin sa, zan nemi transfer daga London zuwa ƙasata ta Nigeria, duk wani weekend zan dinga yinsa cikin wannan ƙauyen, domin ganin na inganta rayuwar wannan yarinyar da ake ganin tafi ƙarfin kowa, domin kuwa *BABU GAGARARRE SAI BARARRE DA KUMA WANNAN YARINYAR INDO ZAN NUNAWA MUSTAPHA KUSKUREN SA NA RAINA ƊAN ADAM* .
Kallon sa ya mayar kan Indo yace.

" To tashi nayi hkr, maza kije ki tafi makaranta, idan kin dawo sai muyi video koh.

Mai kuka ce, ta dawo dariya, tashi tayi tana dariya tace.

" Yauwa yaya Habibu ko kai fah, a dai afuwa yana da daɗi, ni videon ma na fasa, bari naje na dawo ka kunna min kallo nayi a wayar ka.

Dariya Habeeb yayi sannan yace.

" Amma dai kije kiyi wanka tukunna, kuma kinga wannan aswakin, ki barsa a bakin ki, kina gogewa har ki dawo.

" *Na shiga Uku ya Habibu wanka Kuma, Ranar da kaxo fah nayi, nidai gaskiya baxanyi wanka ba sai Ranar juma'a*.

" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un yanxu Indo wankan ne, kike yinsa sati sati, Haba, ashe dai gaskiyar mustapha ne, da yace min, abunda yasa baya sonki ke ƙazama ce, kuma bakya jin magana, ashe da gaske yake, tunda yanxu maganar sa, ta zamo gaskiya, kinga Babu ruwana baxan ƙara cewa ya Aure kiba, tunda kinga ita wacce na gaya miki tana sonsa ƴar gaye ne, Kuma kullum sau biyu take wanka, to kinga mai zaiyi dake, mai wanka sati sati, ga mai yin wanka biyu kullum.

Haɗa ranta tamau Indo tayi, shi kansa Habeeb haushin sa, take ji, idan taji ya ambaci sunan wata tana son mustapha, cikin jin haushi tace.

" *YA HABIBU DAN ALLAH NA ROƘE KA*.

Kunshe dariyar sa Habeeb yayi domin kuwa ya harbo jirgin Indo, indai kana son tayi abu cikin gaggawa to kace mata budurwar mustapha ta birni nayi, to yanxu zatace sai tayi wanda yafi nata, kuma daman dan tayi wankan ya mata haka.

" Umhum ina jinki roke ni.

" *DAN GIRMAN ALLAH DAN ANNABI MUHAMMAD (SAW) KA DAINA CEWA WATA TANA SON YA MUSTAPHA, KAGA KAIMA FAH HAR KASA NAJI HAUSHIN KA, SAURA MA KAƊAN NACE MAKA ALLAH YA ISA HAUSHIN DA KASA NAJI, KUMA SAI NA FASA CE MAKA ALLAH YA ISAN, AMMA YANXU ZANJE NAYI WANKAN INA DAI SHIKENAN KOH MAGANA TA ƘARE*

" Dariya Habeeb yayi yace to karya nayi baida budurwar ne, ke dai kawai ki dage, ki fita wanka da wanke baki, ko zamu samu mustapha ya soki.


Magana Indo zatayi Habeeb ya yace Mata.

" Shit maza jeki kiyi shirin makaranta, kar lokaci ya ƙure.

Shigewa Indo tayi, sanda taxo daf da Innah ta sunkuya gaban ta, tare da cewa.

" Allah ya turo miki da malakul maut, ya ɗauke ki mu huta, ni yanxu na gaji da ganin ki, ni bani ashirin nayi kuɗin tara.

Tashi Innah tayi tare da ɗaukar Salati.

" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un yanxu Indo mena tare miki cikin wannan Duniyar, da kike neman Rayuwata, shikenan ni kuma yau baxanyi bacci ba, yarinyar nan tamin baki, nama isa na sake baki ina bacci na jini cikin barzahu, shegiyar yarinya, ja'ira, to bazan mutu ba, yanxu dan ubanki Musa sai naga mutuwar iyayen ki, naga taki naga ta jikokin ki, shegiya mai mungun baki.

Habeeb jin mitar Innah daya sashi fitowa ne, ya tsaya yana cin dariyar ta, Innah da tsoron mutuwar ta.

Ita kuwa Indo, dariya tayi tace.

" Hajiya Innah ina ma zaki ga ƴaƴana bare kuma jikokina, ai kafin nan kin daɗe a lahira, ni ki bani kuɗin na tafi, kar kisa nayi latti.

" Bazan bayar ba, kixo ki ƙwata dan uwarki, a hakan zan baki kuɗina kina neman Rayuwata, to bazan bayar ba.

Ganin da Habeeb yayi, Indo da Innah zasu iya kaiwa magaruba, suna wannan faɗan bai damesu ba, yasa Habeeb Ciro kuɗi Naira dubu dubu ce,a jikin sa, ɗaya ya ɗauko ya cewa, Indo gashi karɓi maza kije kiyi sanji ki ɗauki, hamsin ki dawo min da sanji na, karfa ki hallaka kuɗin nan duka.

Zuwa Indo tayi ta karɓa tare da cewa, yanxu ma zan kawo maka sanjin ka, kafin na wuce makarantar.
Kallon Innah tayi tace, ke Kuma, yau ki jira zuwan malakul maut, dan sai kin mutu mutum ya tsufa ya tsofe amma bai son mutuwa, kuma mutuwa dole ce a kanki, .

" Sai kixo ki kasheni ai dan uwarki, sai kici kanki ai mayya kawai.

Dariya Habeeb yayi, kawai tare da shigewa ɗakin sa.

Daddare hira sosai Indo da Habeeb suka sha, dan tun zuwan Habeeb mutanen gari suka samu sauƙi wajen Indo, wani sa'in wuni guda zatayi bata fito waje ba, tana maƙale gidan Innah tare da Habeeb.
Innah kuwa yau taki kula Indo, haka itama Indo bata kula Innah ba.

Tsakar dare gari yayi shuru, kowa yayi bacci babu Abunda akeji sai kukan tsuntsaye, Indo dake kwance ɗakin Innah ta tashi tare da ɗauko farin yadin da ta sayo da kuɗin da Habeeb ya bata, dan ƙin kai masa sanji Indo tayi, shima kuma ya manta da ya bata kuɗin, ware yadin Indo tayi tare da rufawa a jikin ta, tayi wajen gadon Innah, sanja Murya Indo tare da taɓa Innah, tashi Innah tayi, haba wa Innah tana buɗe Ido taci karo da mutum lulluɓe da farin yaji, baya Innah taja tare da cewa.

" Waye ne?

Wata irin murya Indo tayi tace.

" Nine mala'ikan mutuwa naxo ne na ɗauki ranki, cikin Aminci, dan haka ki kwantar da hankalin ki.


Rawa jikin Innah ya fara, ja da baya take tana magana da karfi tana cewa.

" Wallahi bani bace wacce zaku ɗauki ranta, wayyo Allah, dan Allah mala'ika ka barni na ɗan kara kwanaki a duniya.
Duk ta gigice ta fita hankalin ta.


Habeeb dake kwance ne yaji ihun Innah ya fito da gudu, cikin tsoron ko wani abune ya sami Innah.

Yana shiga ɗakin yaga Innah takure a gefe sai rawa jikin ta, keyi, haskawa Habeeb yayi da wayar sa, daga ƙafifin ta, ya gane Indo ce, baiyi magana ba, cikin tsabar haushin Indo, saima ɗauketa da wasu tagwayen maruka da yayi tare da nuna ta da yatsa yace


Kuyi haƙuri da wannan wlh naso nayi muku typing yafi haka, sai dai kuma yau muna biki ne, na sister na, kuma wlh bawai ina jin daɗin jiki na bane, mu haɗu daku next page, Ranar Lahadi, in Allah ya kaimu, dan gaskiya bana typing Ranar Asabar.

Gashi yau naso na dawo har cikin dutse, domin ganin halin dasu RAUDA suke ciki, amma ba damuwa mu haɗu next page, tunda Indo ta cinye wannan page d'in ita kaɗai.😄😄😄😄



*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻


*(Ummu Nasmah ce)*
[1/20, 4:14 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*•••••2️⃣3️⃣ ➡️ 2️⃣4️⃣

"kin san me kika aikata kuwa, ki duba kiga yanda jikin wannan baiwar Allah ke rawa, ko kin manta da cewa tana da Hawan jini, so kike ki kasheta, idan mala'ikan bai kasheta ba, aike zaki kasheta, wani irin haline dake wannan, da baki san Wanda ke miki Alkairi ba, tsuka yaja tare da juyawa yayi kan Innah, gani yayi jikin Innah ya sake, da sauri ya kai kunnen sa kan ƙirjin Innah, ajiyar zuciya ya sauƙe jin suma tayi, juyowa yayi ya finciko Indo gaban Innah, Yace, gashi kin kasheta ai kin huta, shikenan Hankalin ki ya kwanta.

Zaro ido Indo tayi, sai kuma ta fashe da kuka, tana Cewa.

" Innah ki tashi dan Allah karki mutu, Wlh wasa nake miki, ya Habibu ka tashe ta dan Allah, wayyo Allah na shiga Uku na kashe Innah, shikenan yau kuma ni Indo na shiga Uku, sai kuma ta zauna daɓas a ƙasa, tana cewa,
*Shikenan Babu ni Babu cin taliyar turawa tunda Innah ta mutu, Babu mai bani kuɗin kashewa na jawa kaina Asara, ni Wlh da akwai mai maye mini gurbin Innah bazan yi wannan kukan ba, wayyo Allah na, taliya ta kam shik.........*

Tsawa Habeeb ya daka mata tare da cewa.

" Rufe min baki, dallah dame zanji da ita Innah zanji koda masifar kukan ki, na banxa.

Shuru Indo tayi tare da gallawa Habeeb harara, sai kuma ta tashi ta koma gefe ta zauna, tare da tsurawa Habeeb ido daya ɗauki ruwa yayi kan Innah.

Yayyafawa Innah ruwa Habeeb yayi, kafin Innah taja numfashi mai nauyi, a firgice ta farka tana kalle kalle.
Tausayi Innah ta bawa Habeeb gani yanda take leƙe leƙen cikin ɗakin, cikin taushin murya Habeeb yake ce mata.

" Ki kwantar da hankalin ki, Innah mafarki fa kikayi, ba wani mala'ikan mutuwa daya zo cikin ɗakin nan, ki daina razana dan Allah.

Cikin rawar murya Innah ke cewa.

" Wlh Habibu ba mafarki nake ba, na ganshi cikin ɗakin nan, yace raina zai ɗauka, kuma Wlh bana son na mutu yanxu, ka tashi kawai Habibu mubar gidan nan, nikam na yafe zaman gidan nan.

Ikon Allah cewar Habeeb.

" Haba Innah nace miki mafarki kikayi ko, ga car INDO ki tambaye ta, kiji, itama ihun da kike cikin Bacci ya sata tashi, kinganta can kinsa itama ta kasa bacci kiyi addu'a ki kwanta ta ɓangaren daman ki, babu wani mafarki da zaki ƙara yi.

Saurin kallon Habeeb Indo tayi ganin ya ɓoyewa Innah cewa itace ta mata wannan aikin, sai kuma ta sunkuyar da kanta, ƙasa tuno yanda jikin Innah yake rawa, tana kokarin maida dariyar ta, cikin ta, kar Habeeb ya ƙara jin haushin ta.

" Shikenan Habibu, Indo kixo mu kwanta, amma dai nasan Baccin yau kam na rasashi dan ba iyawa zanyi ba, karna kwanta na ƙara wannan mungun mafarkin.

" Yawwa to ko kefa Innah, kwanta itama Indo zata zo ta kwanta yanxu.
Bayan Innah ta kwanta ne, Habeeb yayi, wajen Indo tare da sunkuyawa daidai kunnen ta, yace.

" Na rantse da Allah kika ƙara tsorata tsohuwar nan, Wlh !! Wlh !! Wlh, kema yau tsakar gida zan wurga ki, na rufewa Innah ƙofar ɗakin ta, naga keda ita wa zai fara mutuwa yau ko kuma naga wanda zaifi wani jikkatuwa tsakanin ku, tunda ke, baki da mutunci.
Tashi kije ku kwanta.

Tura bakin ta Indo tayi ba tare data maidawa Habeeb Amsa ba tana hararar sa ta ƙasan ido, gadon Innah tayi tare da cewa.

" Matsamin na kwanta kuma wlh karki matseni, kuma banda gwarti, dan kina hanani bacci ehe.

Ita dai Innah bata tankawa Indo ba, dan yanxu bata da lokacin faɗa da indo a halin da take ciki, haka suka kwana har gari ya waye ba tare da Innah ta runtsa ba, idonta biyu har garin Allah ya waye.


Da safe Innah ta aika Indo gidan talatu mai ƙosai siyo musu na karin kumallo, karɓa Indo tayi tana kallon Innah tana dariya ta fice daga cikin gidan.

Ita dai Innah taƙi biyewa Indo yau, bare suyi ɗan Halin da suka saba.


Gidan ƙosan cike yake da yara, kowa na jiran layi, itama Indo ajiye kwanon layin tayi, tare da samun gefe ɗaya ta zauna, kokuwa ne ya tirke tsakanin mariya da Garba, yayin da garba yafi jibgar mariya, anko rabasu garba yaƙi rabuwa, shiga mai taurin kan tsiya, haushin yanda garba ke dukan mariya ne, ya kama Indo, ta tashi taje tsakiyar su, tace.

" Kai garba na sayi faɗan, rabu da ita mu gwabza dani naga jarumtar taka, ɗan mai taurin kan tsiya ka dage sai jibgar ta, kake dan kaga kafi ƙarfin ta.

Sakin mariya Garba yayi yana kallon Indo cikin dariya yace.

" Wanda suka fiki ma na gwabza dasu basu share ba bare kuma ke, idan kin shirya shigo mu fara kiga yanda zanyi dake, idan kina dukan wasu ki share to yau kam kin shigo hanuna, za kuma kiga yanda zaki sha wahala.

" *Dariya Indo tayi tare da sunkuyawa ƙasa ta ɗebo ƙasa, a duka tafukan hannun ta, ta buɗewa Garba tace, ƊAUKI ƊAYA, GANA MASIFA GANA BALA'I, ZAƁI DA WANNE ZAMU GWABZA*.

Na bala'in garba ya ture, ai kuwa take kokuwa ya kaure tsakanin Garba da indo, inda faɗa ya juya salo, ya zamana yanxu Indo ce, ke jibgar Garba, saɓanin ɗazu da garba ke jibgar mariya.
Kokuwa suke sosai, inda garba yaji jiki sosai amma tsabar taurin kai irin na, garba yaƙi haƙura yabar faɗan itama kuwa Indo cewa tayi muddun garba bai haƙura ba, sai dai su wuni suna faɗan, da gyar da suɗin goshi aka raba garba da indo, ɗauko kwanon Indo talatu tayi ba tare da layin Indon yaxo ba, sa mata ƙosan da koko tayi tace gashi ki tafi.

Karɓa Indo tayi tana cewa Garba.

" *Ko wani shege ma waje ya samu, ka dage sai dukan ƴar mutane kake, ɗan iska ƙaton banxa, girman biredi tashin kofin shayi, gobe ka bawa wani labarin Indo*.

Sanda Garba ya tabbatar da indo ta juya tana tafiya, ya taho da gudu ba tare da Indo ta ankara ba, ya ture ta, faɗuwa ƙasa Indo tayi daga ita har koko da ƙosan, shigewa da gudu Garba yayi yana cewa


" Na rama kiji kema idan da daɗi.

" Ihu ne, kawai Indo ba tayi ba, ganin Abunda Garba ya mata, Gashi Kuma ya tsere mata bazata iya kamo sa ba, tashi tayi cikin ƙwafa tare da cewa.

" *Zamu gamu wata rana sai ka gwammace kiɗa da karatu, in kere na yawo zabo na yawa wata rana za'a haɗu*
Ɗaukar kwanon nata tayi, ta koma gidan Innah.

Ganin mutum Innah tayi a kanta, da kwano riƙe hanun nata, duk tayi futufutu da jikin ta, kallon ta Innah tayi tace.

" Aya na ganki haka kamar an koroki, wai wanka kikayi da ƙasa ne, duba kiga yanda kika yi wata kala duk kin ɓata jikin da datti.

" Tura bakin ta Indo tayi wanda ya zamo mata sana'a tace.

" Faɗa mukayi da Garba, na masa shegen duka, shine da yaji haushi, ban ankara ba ya ture min koko da ƙosan ya zube ƙasa ko kaɗan bai saura ba.

Habeeb ne daya fito cikin shirin sa, na komawa, cikin dutse ya girgiza kansa, yana jin Ikon Allah wajen Indo, wato ita duk Inda taje sai ta saida hali, Allah ya kyauta ya kuma shirye ki,.

Cikin masifa Innah ke cewa.

" Kan bala'i wato shi garban ne, ya zubar min da koko da ƙosan nawa da ubansa, to kuwa tashi zanyi naje har wajen shi uban nashi naji idan shine ya turo sa, tashi muje ki raka ni Indo.

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

" Haba yanxu ke idan an barki sai kije, kinsan Abunda ita indon ta masa ne, kuma idan banda Indo da rashin hankali kina mace ina ke ina faɗa da namiji, Babu kyauma ai, hararar Indo yayi yace, kindai ji jiki Wlh, tunda ke baza kiyi Hankali ba.

Tashi Innah tayi tana cewa.

" to Uban ƴan iya magana, a ina akace mace baza tayi faɗa da namiji ba, to tayi faɗan ke Indo, daga yau cikin garin nan, duk Uban da ya miki ki takasa ko ubanwaye ne, kuwa.

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

" Allah ya baki hkr Innah nikam ba baƙon zafi bane, tafiya ma zanyi yanxu, kallon Indo yayi Yace, muje ki rakani gidan ku, na gaisa da Mama da baba na wuce ina son shiga cikin dutse da wuri, ke kuma Innah shigewa zanyi daga can baxan dawo ba.

" Bazaka tsaya kayi karin kumallo ba, zaka wuce da wuri haka.

Dariya Habeeb yayi yace.

" Dame zanyi karin kumallon Innah, bayan anyi tanbola da koko da ƙosan.

Shikenan to ka gaishe da iyayen naka, ka cewa wannan ɗan baƙin Halin, ya aiko min da saƙona dan ubansa.

Dariya Habeeb yayi cikin zolaya yace.

" Babu ruwana tsakanin ki da mustapha sai Allah dan haka bazan shiga tsakanin kuba.

" Karka shiga tsakanin namu, yanxu nasan idan ka tafi sai kuma tsawon rai kafin na ƙara ganin ka Habibu, sai kuma tasa kuka, Habibu Allah dai ya ƙaddara saduwar mu.

Murmurshi Habeeb yayi tare da cewa.

" Bazan dade ba, Innah idan na koma can wajen aikin nawa ma, bazan daɗe ba, zan ajiye musu Aikin su, na dawo gida na cigaba da aiki na, so bazan fi wata Uku ko huɗu ba, zan dawo insha Allah.

Shikenan Habibu Allah ya kiyaye hanya ya tsare, ya sanyawa Rayuwar ku, albarka.

Ita kuwa Indo haɗa fuska tayi jin ance Habeeb zai tafi, dariya Habeeb yayi tare da cewa.

" Haba indodo na, meye na haɗa fuskar kuma bayan baxan daɗe ba, zan dawo.

" Ya Habibu bana son ka tafi, amma tunda kace bazaka juma ba, shikenan, idan kaje ka cewa ya mustapha ina gaishe shi, kace masa ina sonsa kullum da sonsa nake kwana nake tashi.

Murmurshi Habeeb yayi yace.

" Insha Allah kuma zan isar miki da saƙon ki, Indo ki daure kike zuwa makaranta kinji, ki rage yawan rashin ji sannan kullum kike wanke bakinki kina gogewa kinji indona.

" Ya Habibu xan rage, koda ƙaɗanne, zan kuma ke zuwa makaranta kullum, kuma kullum zanke wanke baki na.

Bayan Habeeb sun shiga cikin gidan su Indo, ya gaishe da iyayen ta, duk da ma bai samu Baba ba, dubu ashirin ya ajiyewa Mama tana godiya tare da cewa ya gaishe da Hajiya A'ishah.

Cikin jimami da bacin rai Habeeb da INDO suka rabu, yana ɗaga mata hanu tana daga masa, har yayi mata nisa, juyawa Indo tayi gidan su da niyar taje ta tafi makarantar Boko.


*DUTSE LOCAL GOVERNMENT*


Zaune suke sun gama breakfast kasancewar yau Daddy na gida bazai fita kasuwa ba, kallon Mustapha dake zaune yana game a wayar sa Daddy yayi tare da kiran sunan sa, amsawa yayi tare da kallon Daddy.

" Mustapha ka shirya kaje gidan Alhaji ka karɓo min saƙo, kuɗi zai baka, idan ka karɓa ka shige bank ka ajiye min su cikin account ɗina, zai baka 20millions.

Amsawa mustapha yayi da to, amma bawai zuciyarsa na ƙaunar zuwa gidan su RAUDA ba.

Momy ce tace.

" Yawwa bari na baka saƙo ka kaiwa RAUDA, daman akwai sarƙar da na saya mata, tunda zakaje saika tafi mata dashi koh.

Haɗa Ransa Mustapha yayi Yace.

Ki ajiye kawai Momy duk sanda taxo kya bata, karna manta ta cikin motata.


" Bazan ajiye sai taxo ba, kai mata zakayi yanxu, ka manta kuma mu gani, sarkar ce, zaka manta, inbanda baka son kaimata ne

Tashi mustapha yayi, cikin jin haushin aikan da Momy ta masa wajen RAUDA ya haura sama, yana mita cikin ransa, tare da jin haushin RAUDA, shidai har ga Allah haka kawai baya ƙaunar RAUDA cikin rayuwar sa, kuma bawai tana da wani Aibu bane ko wani mungun hali, a'a bata da ko ɗaya, shi kansa yasan RAUDA macece mai nutsuwa tare da biyayya ga duk na sama da ita, tana da kyawun ta dai-dai gwargwado, a fili yace.

" Ajine kawai bata dashi,
Tunda har zata iya furtawa namiji cewa tana sonsa, ai macen da takai mace, ita ake zuwa ace ana so, ba itace zata ke bin namiji ba, ko ita wannan INDOn da take cemin tana sona, daman can ita ba nutsuwa gareta ba, bare kuma a samu Class tare da, ita, ita ɗayan ta, ma Aljana ce, ita za'a iya mata uxirin rashin Hankali da rashin lafiya na aljanu da take fama dashi, amma ke RAUDA kina mace mai Class, har kin kai 3 Hundred level a JSU kixo kina zubar da ajinki wajen maza, banza jarababbiya kawai, tsuka yaja tare da shigewa tollet.

Ita kuwa Momy da gangan ta aiki mustapha wajen RAUDA, duk neman yanda zata haɗa kansu, har shakuwa ta shiga tsakanin su, yanda zata samu sauƙi wajen haɗa su, aure.
Sharifa Momy ta daga tace ta shigar da kwanuka kitchen, sannan ita kuma ta tashi domin zuwa gyarawa Daddy ɗakin sa, kasancewar shi Daddy yace baya buƙatar ƴar aiki cikin gidan sa.

Cikin shirin sa, Mustapha ya fito, yana sanye da ƙananan kaya, Baƙin wandon jeans, da Red colourn riga, gashin kanshi kuwa kwance kasancewar mustapha ba ma'abocin Aski bane, sai Uban gyara da kuma mayuka da yake amfani dasu, wa kansa, toshe idanun sa, yayi da baƙin glass, ɗakin Momy ya nufa, bata ciki, fitowa yayi ya shiga na Daddy, tana gyaran ɗakin ya sameta, ki bani aiken naki Momy zan wuce.

Murmurshi Momy tayi sannan, ta fito daga ɗakin Daddyn nasu, shi kuma mustapha na biye da ita har cikin ɗakin ta, bakin gadon ta ya zauna kafin, Momy ta ɗauko sarƙar tare da Zama kusa

Please Login or Register in order to submit comment