You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
gudu kodai yauma macijin ya sake biyoki.
yanzu ke Inna idan macijin ne sai na tsaya har ki iso ban rufe ƙofa ba, ai wlh kafin ki ƙaraso na juma da rufe ƙofar nan sai dai kuma kisan tayi.
Amsa Inna ta mayar mata da cewa.
"Amma dai ke Indo akwai ja'irar yarinyar yanzu dan baki da mutunci sai ki rufe ƙofar ki barni a waje wato idan ma kasheni macijin zaiyi ke baki damu ba, *to bari muga idan na mutu ina zaki dinga samun taliyar turawa kina ci, naga kuma wanda zai dinga karɓa miki faɗa tunda gani nane baƙya ƙaunar yi ina numfashi a duniya*)
Wasu hawaye ne masu zafi suka zubowa Indo ta goge a fili tace.
" Allah sarki Inna, kin tafi kin barni a lokacin da nafi kowa buƙatar ki, baki mutu ba, sai dai kika kawo ni inda zan samu taliyar turawa, sai dai bana buƙatar sa, ke nafi buƙata a yanzu Inna."
Girgiza kanta Mama tayi ta ajiye kayan da take ninkewa ta dawo kusa da Indo ta zauna tana duban tace.
" Yanzu ke Indo ba zakiyi Hkr ba, ki cire damuwa cikin ranki Indo so kike ki sawa kanki cuta, meyasa bazaki ɗauki ƙaddara ba? duk sanda Inna ta faɗo miki cikin ranki ki mata addu'a."
Goge hawayen Indo tayi tace.
" Mama na ɗauki ƙaddara, so nake ki koma dani ƙauye Mama bazan iya zama cikin gidan nan babu Inna ba, hankali na tashi zai dinga yi, Mama nafi son zaman a yanzu fiye da zaman cikin gidan nan domin kuwa wahala zan dinga sha tunda babu Inna kusa dani, dan Allah Mama ki koma dani ƙauye."
Cikin tausayin Indo Mama tace.
" Nima haka naso cikin raina nafi so na koma tare dake domin kuwa na fiskanci cewa Hajiya bata sonki cikin gidan ta, ko daga yanayin yanda take kallon hakan ya nuna min cikin idanunta bata miki kallon soyayya, sai dai bani da ikon da zan saki a gaba mu tafi domin kuwa mahaifin ki shine mai wannan ikon nasan kuma shima bazai yi haka ba, ko dama can da zaki dawo birni ba da Inna zaki dawo akan ke kaɗaice zaki dawo, Inna tace ita lallai ƙafarki ƙafarta, to kinga ai idan muka ce zamu koma dake Alhaji Haruna bazai ji daɗi ba, tunda shine wanda ya ɗauko ki, ke dai ki cigaba da Hkr duk abunda zaki gani ko kiji wanda bai miki daɗi ba cikin gidan nan kiyi hkr dashi komai mai wucewa ne, ki cigaba da yiwa Hajiya A'isha biyayya har Allah ya rabaku, domin ke macece ba mai dauwama a cikin gidan bane."
Sosai Mama take yiwa Indo nasiha har ta samu ta saki jikin ta, sukayi hira, da yamma lis Indo suna Zaune ita da Hasina da Aunty Hindu, tana yiwa Indo tsifar kanta a cewar ta, kitson Indo ya tsufa, sosai Aunty Hindu take son Indo, hira suke gwanin ban sha'awa, suka jiyo sautin motar gidan gwamnati, koda Indo taji tasan motar gidan su zahra ne, cewa Aunty Hindu Indo tayi.
" Ummi bari naje compaunt naji kamar Muryar su Zarah ne bari naje na duba."
Sake mata kai Aunty Hindu tayi tana dariya tace adawo lafiya, Hasina ce tace.
" Ai kuwa ɗazun nan nake zancen ta cikin raina nace Zarah dai shuru ko ta'aziya bata zo mana ashe suna hanya."
Murmurshi Indo tayi tace.
" Basa nan ai sunje sunyi tafiya Kano jiya suka dawo Aunty Sharifa ai ta kira min ita munyi waya."
Tana gama faɗin haka Indo ta fice zuwa compaunt ɗin, aikuwa zarahn ce, da gudu Indo taje ta rungume Zarah tana cewa.
" Ƙawata kece tafe sannu da zuwa, yaushe kuka dawo?"
Dariya Zarah tayi tace mune tafe dai baki ga momma bane"
Sam Indo bata kula da momma ba sai yanzu tana dariya ta ƙarasa wajen momma tana cewa.
" Momma ai ban ganki ba, sai yanzu sannu da zuwa."
Dariya ita ma momma tayi tace.
" Ina kuwa zaki ganni hankalin ki ya tafi wajen ƙawarki, ina su Ishaq?"
Tana murmurshi Indo tace.
" Suna ciki momma mu ƙarasa, gashi kuwa Mamana tazo Allah yayi zaku gana"
Tare suka ƙarasa cikin falon, sosai momma tayiwa Momy ta'aziyar Inna, sai dai bata samu Daddy ba, ya fita Indo Mama taje ta kira suka gaisa da momma, sun ɗan juma Zarah taso su sami ishashshen lokaci da Indo sai dai babu halin hakan gashi sunyi hutun makaranta bare tace zasu haɗu a can, sallama momma ta musu tare da sawa aka sauƙe musu kayan abinci mota guda, kuɗi momma ta bawa Mama dubu ɗari tace babu yawa tayi Hkr sosai mama tayi godiya har compaunt Indo ta raka su, Mustafa da yayi parking ne yake karewa motocin dake cikin gidan kallo cikin mamakin wasu baƙi ne suka zo gidan, daga nesa Mustafa ya hango kamar Hajiya Zubaida, ƙara buɗe idanunsa Mustafa yayi sosai tabbas dai Hajiya Zubaida ce, to me kuma ya kawo ta cikin gidan mu, haɗa fuska Mustafa yayi dan karma ta kulasa, itama dai momma gani take kamar Barrister Mustafa, sanda suka zo daf da juna kafin momma ta gane cewa Mustafa ne, ganin da gaske Mustafa zai shige bai mata magana ba, yasa momma tare sa tana cewa.
" BARRISTER yau kuma ni zaka gani ka wuce ba tare daka kulani ba?"
Cikin haɗa fuska Mustafa yace.
" Barrister Zubaida, daman akwai dokar da tace idan na ganki dole sai na miki magana, ko kin manta da cewa na tsani mata irinki mai take mutuncin mace ƴar uwata, wacce sam bata kishin jinsin ta, oh ashe daman kina da ƴarinya mace kike wannan rashin imanin"
Duban Mustafa momma tayi cikin jin Zafin maganganun sa, tayi murmurshin dole tace.
" Ya kamata kake manta Abunda ya faru a baya tunda dai gashi har kayi nasara a kanmu so meye na fushi mune waɗanda ya kamata ace munyi fushi dakai da kayi Nasara a kanmu, duk da wancan lokacin kaƙi karɓar aikina yanzu ma ina da aiki a karo na biyu, wanda zan baka maƙudan kuɗaɗe, muddun zaka karɓi Case ɗin."
Murmurshi Mustafa yayi kafin yace.
" Baki da wata dukiya wacce zata ruɗeni a wajen ki, wacce har ki iya siyata dan haka kibi wani sarkin ba niba."
Yana gama faɗin haka ya juya yayi cikin gida.
Habeeb daya naɗe hanu yana tsaye yana jin duk abunda suke tattaunawa, Habeeb sam baiji daɗin Abunda Mustafa yayiwa Barrister Zubaida ba, domin kuwa shi yasan komai da ya faru tsakanin su da Mustafa, ƙarasawa Habeeb yayi wajen nasu yanda yaga ita Zarah ta hasala ranta ya ɓaci ganin yanda Mustafa yake gayawa mahaifiyar ta Magana duk sanda suka haɗu, wannan ba shine karo na farko ba, hakan ne yasa zarah tsanar Mustafa duk da momma ta sanar da ita Abunda ya faru, itama Indo kallo take binsu dashi cikin sarƙaƙiya tare da jin haushin Mustafa.
" Sorry Barrister Zubaida, kin san halin mutumin naki so karki wani damu da Halin sa, kallon Zarah yayi yace kiyi hkr kema karkiji haushin sa, haka shi yake bai cika yafiya ba."
Murmurshi momma tayi tace.
" Karka damu Habeeb" tana faɗin haka ta shige cikin mota cikin zafin rai, itama Zarah shiga tayi tana cewa Indo.
" Ni da gidan ku har abada Indo bazan ƙara tako inda aka ciwa mahaifiyata mutunci ba"
Cikin rau-rau da ido Indo tace.
" Please Zahra ni me na Miki ba laifi na ba kice bazaki ƙara zuwa gidan nan ba, nima ai ba gidan mu bane"
Zarah dai bata cewa Indo komai ba suka ja motar su suka tafi, Indo wani irin murɗan baƙin ciki taji har wani ɗaci take ji cikin ranta Abunda Mustafa ya Aikata mata, ya wulaƙanta mata baƙi waɗanda suke darajata da mutunta ta, waɗanda suka ɗauke ta ɗaya da ƴarsu ta cikin su, juyawa tayi cikin gidan a hasale har bata ganin gabanta zabar ɓacin rai, a falo kuwa ta same su, tsayawa tayi kan Mustafa cikin faɗa da ɗaga murya tace.
" Wani irin mutum ne kai wanda sam baka da kawaici cikin rayuwar ka, meye wannan baiwar Allah ta maka kake wulaƙanta ta a gaban ƴarta, yanda kaci mutumcin wannan matar kaima Allah ya kawo wanda zai tozarta ka cikin al'um..........."
Bata ƙarasa ba taji wani kyakkyawan mari saman fuskar ta, danƙo gashin ta Mustafa yayi yana cewa.
" Ni sa'an kine dan ubanki koko ni sa'an wasan kine banza daƙiƙiya ƴar ƙauye, jaka har zaki tsaya a kaina kina son gaya min Magana, ita Barrister Zubaida ƙanwar uwarki ce ko ta ubanki, da har zaki tsaya a kaina kina neman zagi na, naga alamar har yanzu baki san ni waye bane" ya ƙarasa maganar yana gwara Indo da gini, tare da murɗe mata hanu, hanun sa yasa still ya daki bakin Indo da ƙarfi sai kuwa ga jini, wani irin ƙara Indo tasa tare da fara zagin Mustafa.
" Allah ya isa tsakani na dakai baƙin mungu wlh yau ko kasheni zakayi cikin gidan nan saina faɗa maka cewa Allah ya haɗaka kaima da wanda zai wulaƙanta ka cikin al'umma, ka kasheni na faɗa!" Ta karasa maganar cikin ƙara wanda yasa Mama da Aunty Hindu dake ɗaki fitowa da gudu, ran Mustafa Idan yayi dubu to ya ɓaci kan Indo ya nufo gadan-gadan da niyar ya ɓallata kowa ya huta, cikin Zafin nama Habeeb yasha gaban sa, yana cewa.
" Haba Bros Haba dan Allah yanzu kai saika biyewa Indo Idan ita bata da hankali ai kai kana dashi, bana son kana biyewa Indo karka manta da cewa yarinya ce ƙarama wacce kayi ƙanwa da ita wajen ta uku ko biyu."
Harara Mustafa ya sauƙewa Habeeb yana cewa, kauce daga gabana ka bani hanya naje naci uban wannan yarinyar ko zan huce, daga bayan su sukaji Muryar Aunty Hindu tana cewa kauce ka basa hanya ya kashe ta ma ƙarshe kenan tunda shi baida mutunci, duban Momy tayi tace yanzu ke A'isha kina Zaune kina gani ɗanki zai kashe ƴar mutane kin kasa yin magana".
Mama kuwa batayi magana ba domin tasan halin Indo ba daɗi take dashi ba, bare kuma dama can inuwar su bata zuwa ɗaya da Mustafa.
*Vote*
*Share*
*And*
*Comment*
*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*
*(Ummu Nasmah ce)*
[3/3, 1:21 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻
*Na*
*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*
*(մʍʍմ ηαςʍα)*
👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻
*Marubuciyar*
*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*
*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*
*Aunty fauza ƴar Amana*
Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.
*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*
*Aunty Hauwa Maman Uswan*
Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻
*Babu komai fa masoyana karku damu komai ya wuce, yanzu ma na fara muku typing ɗin Indo karkiji komai ana mungun tare*😄❤
*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________
*P*••••••6️⃣1️⃣ ➡️ 6️⃣2️⃣
Cikin ƙaraji Indo ta ce ni yama kasheni na huta, tun da nake a rayuwata ban taɓa cin karo da mutumin daya tsaneni ba Irin ka, ka kasheni sai ka huta, *NA TSANEKA! NA TSANEKA*" Ta ƙarasa maganar tana kuka mai tsuma Zuciya, tare da haurawa sama da gudu.
Duban Mustafa Aunty Hindu tayi tace.
" Ka kyauta, daɗin me kaji daka daki baiwar Allah, ba laifin ka bane laifin mahaifiyar kace da ta zuba maka Ido kake jibgar yarinya, kuma indai mugunta kasa a gaba, kaje kayi idan da akwai riba" itama tana gama faɗin haka ta juya, Momy kuwa ko a jikinta bata tankawa Aunty Hindu ba, ta cigaba da kallon ta, Shima Habeeb haurawa yayi sama, ƙwafa Mustafa yayi tare da zama yana cije lips ɗinsa, Habeeb kuwa ɗakin su Indo ya tura, tana kwance ruf da ciki tana cin uban kuka bakinta kuwa ya kumbura suntun, sai kuka take, sunan ta Habeeb ya kira, shuru tayi da kukan ba tare da ta amsa ba, Habeeb bai damu da rashin ansawar ta ba yace.
" Meyasa bakya jin magana ta, sau nawa nake ce miki ki daina yiwa Mustafa rashin kunya, ban faɗa miki ba nace ki daina shiga cikin sha'anin sa tunda yace baya sonki cikin rayuwar sa, amma kin ƙi gashi kuma jikin ki yana faɗa miki daman Hausawa sunce *duk wanda baiji bari ba zaiji hoho* karki fasa shiga rayuwar sa, kece cikin wahala" ya ƙarasa maganar yana nuna Indo da yatsa.
Tashi Indo tayi tana sharce hawayen ta, cikin Muryar kuka tace.
" Yanzu ya Habeeb duk abunda ya Mustafa yayi baka gani ba, a gaban ka fa ya zagi momma kana kallo matar da tazo har gidan nan domin ta'aziya shine ya cimata mutunci, amma wai laifi na kake gani shi baida laifi kenan?"
Cikin tsawa Habeeb yace.
" Ina ruwan! Ki da Abunda ya yiwa Barrister Zubaida kin san meyake tsakanin su, kin san meta masa, ke kanki da kinsan Abunda yake tsakanin su, bazaki damu ba bare har kiyi tunanin shiga tsakanin su, ba yau suka fara gayawa juna magana ba, ita kanta Barrister Zubaida ta ɗagawa Mustafa ƙafa ne yau kawai saboda cikin gidan su tazo, ina ruwanki da shiga Abunda bai shafeki ba."
" Ya Habeeb ban gane abunda kake nufi ba, wani irin hali momma take dashi? wanda har zaka ce ya Mustafa baida laifi duk irin wannan cin mutuncin da ya mata a gaban ƴarta."
" Bance tana da mungun Hali ba, sai dai abinda take wani lokacin bata kyautawa, Barrister Zubaida, ƙanin ta, ya taɓa yiwa wata yarinya fyaɗe ko nace sunyi mata fyaɗe, ƴar talaka lis ce yarinyar wanda basu da cin yau bare na gobe, iyayen yarinyar hankalinsu ya tashi sosai, har takai ga sun kai ƙara human Right, su kuma human Right suka shigar da ƙara kotu, a lokacin Hajiya Zubaida lowyer ce Babba, amma taƙi shigawa ɗan uwanta Case, gashi suna da kuɗi sosai mahaifinsu babba ne a cikin siyasar ƙasar nan, hakan ce tasa suka nemi Mustafa suka yaudare sa da cewa sharri aka yiwa ƙanin nata ba shine yayi fyaɗen ba, suka sashi ya karɓi Case ɗin, dake shi lowyer ne mai zaman kansa, yayi duk wani bincike bai gane cewa Sadiq shine yayi fyaɗen ba, suka shiga kotu, Mustafa yayi duk yanda zai yi yasa aka kori ƙarar, kinsan meya faru?"
Girgiza kanta Indo tayi alamun bata sani ba.
" Wannan ƙanin Barrister Zubaida shine yayi fyaɗen, gashi kuma an riga an kori ƙara a kotu, sosai Mustafa yaji zafin yaudarar sa da sukayi, gashi kuma ba'a juma da ƙorar ƙarar ba Allah yayiwa yarinya da aka yiwa fyaɗen rasuwa, daga baya Mustafa ya kasa Hkr gani yake kamar Allah bazai barshi akan haƙƙin wannan yarinyar Mustafa shida kansa ya shigar dasu Hajiya Zubaida ƙara akan abiwa yarinyar haƙƙin ta tare da hujja mai ƙarfi mustafa ya shiga kuto ko a karo na biyun Hajiya Zubaida da kanta ta tsayawa ɗan uwanta a kotu, kan cewa sam ba shi ya aikata wannan laifin ba, sai dai Mustafa ya fita hujja, wanda hakan yasa alƙali ɗaure ƙanin Barrister Zubaida har na tsawon shekaru goma a gidan kaso, ki faɗa min wake da laifi tsakanin su?, ki daina shiga Abunda bai shafeki ba, wanda baki da masaniya akai sam Mustafa baida laifi cikin wannan lamarin, laifin sa ɗaya kasa manta abunda ya faru shiyasa ko da yake jibgar ki banyi magana domin kuwa baki da gaskiya ko kaɗan".
Jikin Indo sosai yayi sanyi, amma sai dai har yanzu tana jin haushi da tsanar Mustafa cikin ranta, bata kuma ɗaga kanta ba har Habeeb ya fita daga ɗakin.
Koda daddare Mama sosai ta yiwa ƴarta nasiha, tare da mata faɗa akan ta daina yiwa Mustafa rashin kunya ta daina shiga sha'anin sa muddun bai sata a ciki ba, sosai dai Mama ta yiwa Indo faɗa.
Washegari kuwa mama da su Baba suka ɗaga zuwa Dasina, Indo ji tayi kamar tabi su amma sai dai babu halin hakan.
Sati Uku da rasuwar Inna Aunty Hindu suka koma gidan su dake gida dubu nan cikin Jigawa, amma sai dai bata koma da Indo ba, Hasina ce kawai suka tafi tare, aka bar Indo da sharifa.
A hankali rayuwa take tafiya, jituwa kuwa sam babu tsakanin Mustafa da Indo, yau Watan Inna shida da rasuwa a yaune Kuma aka saka Ranar Auren su Mustafa da Habeeb sati biyu rak, Aunty Hindu da kanta tazo ta ɗauki Indo tace sai bayan biki zata dawo.
Da sauri ta fito hanun ta riƙe da school bag ɗin ta, tana cewa.
" Aunty Hasina kiyi sauri kizo ki sauƙe ni zanyi let fa."
Fitowa Hasina tayi tana dariya tace.
" Muje na sauƙe ki kafin ki cinye ni"
Dariya Indo tayi tana yiwa Aunty Hindu sai ta dawo ta fice.
A makarantar Hasina ta sauƙe ta sannan ta juya, cikin Class ɗin su ta shiga Ss3 dake ma sun kusa fara jarabawar barin Secondary School, Zarah Indo ta samu tana zaune a sit ɗin su dake yanzu ta ɗan sanjawa Indo tun abunda ya faru tsakanin su da Mustafa, hanu Indo ta miƙawa Zarah sukayi musabaha, daga nan bata ƙara cewa Zarah komai ba, ganin da zarah tayi Indo bata da niyar kulata yasa ta cewa Indo.
" A'ishatu Musa meya sameki naga yau kamar kin sanja min?"
Ɗago kanta Indo tayi tace.
" Bangane na sanja miki ba, na sanja miki ko kin sanja min? Me kike so na miki Zarah kin daina min magana sosai kin rage shiga harkata so kike ni nata bin ki kina min wulaƙanci, an miki laifi a gidan mu, bani na miki ba, amma na baki Hkr kika ƙi haƙura kuma nima kinsan dai gidan nan ba gidan mu bane amma na baki hkr kika ƙi to ya kike so na miki Banda nima na fita harkar ki."
Murmurshi Zarah tayi tace.
" Ƙawata ba dai fushi ba, wlh raina ne ya ɓaci sosai amma komai ya wuce, kiyi hkr ka kinji bestie na"
Dariya itama Indo Tayi tace.
" Babu komai ƙawata ya wuce nima a waje na"
Sosai suka ta taɗin su kamar babu abunda ya taɓa shiga tsakanin su.
"Mustafa wai ya haka ne kam, tun jiya nake maka Maganar wani hole ya kamata ace mun kama na diner amma kayi burus dani ka ƙi Magana."
Tsuka Mustafa yaja ba tare daya ɗago ya dubi Habeeb ba yace.
" Naga alamar tun jiya bakin ka yake ciwon magana to Allah ya yaye maka."
Haushi ne ya kama Habeeb yace.
" Baƙar magana zaka faɗa min saboda ina ta binka akan harkar bikin ka, to Allah ya baka hkr."
Murmurshi Mustafa yayi yace.
" Meye kuma abun fushi Bros, nima fa ban ɗauki wannan auren da zanyi ba Aure, kaine zakayi Aure ba niba kaida zaka Auri zaɓin ka, dan kaje ka kama hole ɗinka ni babu wani kuɗina da zan kashe kan wannan banzar yarinyar wacce bata da wani daraja cikin idanuna, Wlh Habeeb ni tausayin ta nake ji muddun ta shigo cikin gida na, badai Momy tace sai anyi Auren ba, to ayi."
"Mtss haba Mustafa wai meyasa bazaka ɗauki ƙaddarar ka ba, ka Rungumi zaɓin mahaifiyar ka, sai Allah ya sa maka Soyayyar ta cikin ranka ya kuma Albarkaci auren muddun ka yiwa mahaifiyar ka biyayya da kake maganar kai bazaka kashe kuɗin kaba ai bance ka kawo sisin kwabon ka ba ni zanyi komai a aljihu na."
Dariya sosai Mustafa yayi yana yiwa Habeeb kallon sakarai yace.
" Ubangiji Allah karya taɓa samin soyayyar ta cikin zuciyata, kai kasan yanda na tsani YARINYAR nan kuwa kaga tunda kaga zaka iya ɗaukar ɗawainiya bismillah kaga ba sai naje ba, sai su saka a tsakiyar su tunda Abunda yayi Mustafa ai shine yayi Habeeb ko? ni sai yanzu ma ka tuno min da cewa Momy tace lallai sai dai naje na bata kuɗin da zatayi hidimar bikin, ni da zaka taimake ni ma na baka ka kai mata ba saina jeba, dan wlh banson zuwa gidan su, nasan kuma munafuka zata sanar da Momy cewa banje ba."
" Mtsss kazo ka jani ka sani dole na kai maka ubana tunda nine mijin nata, kuma wlh kasa a ranka sai kaje dener" yana gama faɗin haka Habeeb ya fice yana hararar Mustafa.
Murmurshi Mustafa yayi shima ya tashi ya shiga wanka da niyar yaje ya miƙa mata kuɗin ya wuce office.
A falo Habeeb ya ci karo da Momy da sharifa suna ta rigima akan cewa zata gidan su Hasina ta kwana ita kuma Momy ta hana, duban Sharifa Habeeb yayi yace
" Sarkin ƙorafi ta cikin gidan nan meya faru haka kike haɗa baki?"
Ƙara haɗa bakin Sharifa tayi tana cewa.
" Ya Habeeb kaga jiya Hasina ta kira ni........" Bata ƙarasa maganar ba Habeeb ya bige bakinta yace.
" Aunty zaki ce ba Hasina gatsal ba dan gidan ku" ya ƙarasa maganar yana zaro mata Ido.
Dariya sharifa tayi tace.
" To Aunty Hasina ina shike nan, tace zan rakata kasuwa shine nacewa Momy zan kwana idan naje, taƙi yadda."
Dariya Habeeb yayi yana duban Momy yace.
" To Momy gareki kiyi kibarta zuwa gobe da safe ta dawo pls MOMYN mu."
MOMY cewa tayi.
" Ba fa zata kwana ba, ita kaɗai take tayani aiki cikin gidan nan idan taje ta kwana da wa zanyi aikin."
" To Momy ai nace miki da wuri zan dawo da sassafe ma."
Daƙyar dai Momy ta yarda Sharifa tayi kwana ɗaya.
Dariya Habeeb yayi tare da cewa.
" Muje na sauƙe ki to tunda kin shirya saina wuce daman zanje na ɗauko Indo a school Idan mun ɗauko ta, sai na sauke ku nayi tafiya ta."
Harara Momy ta watsawa Habeeb tana cewa.
" INDO dai Indo dai cikin bakin ka kullum, kamar wanda kuka fito ciki ɗaya shashasha marar lissafi ka zaune sai bautawa yarinya ƙarama kake."
Tana gama faɗin haka ta haura sama tana cigaba da mita, shidai Habeeb baice komai ba saima cewa Sharifa da yayi muje, tsalle Sharifa tayi tace.
" Yauwa yayana muje daɗi na dakai akwai tausayawa na ƙasa dakai ba Irin ɗayan ba, kullum rai a haɗe kamar an aiko masa da saƙon mutuwa."
Zaro ido Habeeb yayi tare da cewa.
" Me kika ce, to bari mu juya wajen ɗayan saiki maimaita a gaban sa kafin mu wuce, tunda ke baki da kunya."
Dariya sharifa tayi tace.
" Rufa min asiri ya Habeeb ai yana ji yau saiya kusa kasheni cikin gidan nan."
Dariya shima Habeeb yayi yace" matsoraciya kawai" suka wuce suna wasa da dariya da Habeeb kamar ba kanwar sa ba.
"Mamy ya maganar Family And friends ɗin nan ne da kika ce za'ayi kuma kinga yau saura 10 days Auren fa."
Duban ta Momy tayi tace.
" Ina sane za'ayi shima, sannan gobe yani zata zota ta fara miki gyaran jiki da wasu abubuwan, sannan Asabe ta aiko min da wasu magungunan mata, zaki fara amfani dasu yau, dubu ashirin na karɓosu wajen ta"
" Shike nan ba damuwa kice gobe su Aunty yana mutan Barno ana hanya"
Ehh Mamy tace, kafin suka cigaba da zancen yanda bikin zai kasance.
Mustafa daya juma cikin gidan nasu tsaye compaunt ɗin, baiga kamal ba mai masa iso cikin gidan, gashi kuma shi baida numbern RAUDA, wajen mai gadi ya nufa tare da cewa ya taimaka ya masa magana da RAUDA, tashi Baba mai gadi yayi ya shiga kira masa ita shi kuma ya koma mota.
Da sallama Baba mai gadi ya shiga bayan sun gaisa ne ya sanar dasu cewa Mustafa yana jiran Indo a compaunt, duban Baba mai gadi Mamy tayi tace" kaje kace mishi ya iso" da to Baba ya amsa sannan