Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bani hanya! Tun kafin nabi kanki da wannan motar, kuma nabi kan banza, kinga sai na huta da wannan tsinannan nacin naki dangin Mayu_."

Kaucewa RAUDA tayi daga gaban motar tasa, idanunta na tsiyayar da ruwan hawaye.
Murmurshi yayi tare da cewa.

" Ba yanxu ya kamata ki fara zubar da wadannan hawayen naki ba, ya kamata ki adana su domin kuwa gaba zasu miki amfani mussaman ma idan kika shigo cikin gidana hawayen da zakiyi kukan ma sai kin rasa su, domin suma hawayen daɗi ne yake sawa suzo duk sanda Azaba tayi Azaba to ba'a ganin hawaye a fuskar mutum " yana gama faɗin haka yaja motar sa, tare da bule ta da ƙura, RAUDA Zama tayi daɓas tana hawaye tare da cewa.

_"So baka min adalci ba, zuciyata meyasa zaki kamu da son wanda bai san kina yiba, tabbas kin cuceni da kika kamu da Soyayyar Wanda bai damu da ke ba" tana maganar tana dukan ƙirjin ta da karfi_.

Sanda taci kukan ta, ta ƙoshi sanna ta tashi ta kama hanyar gida.

Mustafa sanda yayi sallar magaruba kafin ya dawo cikin gidan, Momy da Hasina sai Inna suke zaune a falon yayin da Momy da Hasina suke ta famar magana suna dariya sai gefen su kuma RAUDA ce zaune tayi shiru tana tunani, da murmurshi fuskar Mustafa ya nufo Hasina yana cewa.

" Wai wai wai! Yau kuma cikin gidan nan mun banu da magana uwar surutu an shigo" tare da zama gefen su ya cigaba da cewa " Momy karfa ki biyeta ta saki tsamin baki dan wannan ba ƙaramar parrot bane."

Dariya Momy tayi tace.

" Babu wani tsamin baki da ƴata zata sani, ku baku dameni ba sai ita."

Murmurshi yayi yace.

" Nayi shuru tunda haka kika ce Momy" ya ƙarasa maganar yana murmurshi tare da cewa Momy.
" Ina su Ishaq ne?"

" Suna sama yanxu suka haura."

Duban Mustafa Hasina tayi tana dariya tace.

" Alhajin miskilanci, ana yine har yanzu ko an daina?"

Murmurshi ya mata tare da cewa.

" Tunda kinzo saiki saka ido kiyi kallo saiki auna fahimtar ki."

Gabaki ɗaya dariya sukayi har Momy tace.

" Iyayen bawa mutum magana a dunƙule ba, to shi kenan zanyi kallon tunda Allah ya kawo ni gidan."

Dariya kawai Mustafa yayi kafin shima Habeeb suka sauƙo da Indo suna taɗi, kusa da Mustafa Habeeb ya zauna Indo kuma kusa da Inna ta zauna, dariya Habeeb yayi yace.

" Alhajin Allah yaushe ka shigo cikin gidan?"

"Yanzu bari ma ka gani na tashi naje na wanke jikina."

A fito lfy Habeeb ya masa Inna kuwa harara ta sauƙewa Mustafa tace.

" Allah ya tura ƙeya Uban ƴan bakin hali."

Murmurshi kawai Mustafa yayi ba tare daya kula Inna ba, dan yasan neman faɗa take.

Duban Indo Habeeb yayi yace.

" Hajiya Indo Jiya Daddy yace muje na yanka miki uniform zaki fara tafiya school so gobe idan Allah ya kaimu da safe ki shirya keda Aunty ki, zamuje kasuwa ko."

" To ya Habibu Allah ya kaimu" sai kuma tayi shiru tare da jingina jikinta da kujera.

Duban Indo Habeeb yayi yace.

" Mamana lafiyar ki kuwa tun jiya nake ganin sauyi a tattare dake, kamar wacce kike cikin damuwa, me yake damunki?"

" Babu Abunda yake damuna nikam" ta mayar masa amsa.

Murmurshi Habeeb yayi yace.

" Banda dai babu kam, tunda dai gashi yanayin ki ya sauya."

Sharifa dake sauƙowa daga step ne tace.

" Tambaye ta dai ya Habeeb, dan nima tun jiya naga alamar damuwa daga gare ta, na kuma tambaye ta taƙi cemin komai."

Ko kafin Habeeb yayi magana Hasina ta riga sa, dake ita tasan damuwar Indo.

" Kunga tunda tace muku babu komai ai sai kuyi hkr ku ƙyaleta, kinga sweet sis ɗina tashi mu wuce ɗaki kafin su saka miki ciwon kai."

Tashi Indo tayi suka wuce ɗaki, murmurshi kawai Habeeb yayi ba tare da yace komai ba, Momy da RAUDA kuwa kusan tare sukayi tsaki suna bin Indo da mungun kallo, Inna ma dai nata ɗakin ta wuce.

Da daddare Daddy ya kira Mustafa da Habeeb akan zancen Auren su, inda Habeeb ya gabatar da Hasina a matsayin matar da zai aura Mustafa cikin takaici da baƙin ciki ya sanar da Daddy cewa RAUDA ya futar, Daddy yaji daɗin zabin yarannasa sosai, inda yace zaije ya musu tambayar Auren, da suka koma ɗaki sosai Habeeb yayi mamakin Mustafa da yace ya zaɓi RAUDA a matsayin matar Aure, cikin murmurshin takaici mustapha ya ceqa Habeeb.

" Ka daina kiran RAUDA a matsayin zaɓi na, ka kira ta a matsayin zaɓin mahaifiyata, domin kuwa itace kawai take sonta ba niba, ni dai kawai nayi biyayya ne ga umurnin ta, amma hakan ba yana nufin cewa zanyi Rayuwar Aure da RAUDA bane."

Ajiyar Zuciya Habeeb ya sauƙe Sannan yace.

" Nasan da wannan umarnin tun kafin ka sani nayi shuru ne kawai ban sanar da kai ba, sai dan ina tunanin ko Momy zata janye maganar daga baya, ashe bata janye ba, a gaskiya Momy tayi kuskuren haɗa Auren da babu Soyayyar namiji cikin ta, ina ma laifin ace macen ce bata so shi namijin ke so, da ƙiyayyar zata zo da sauƙi, Ubangiji Allah ya kyauta ya daidaita tsakanin ku."

Taɓe bakin sa Mustafa yayi tare da shigewa tollet abunsa.

Washe gari misalin ƙarfe 1 Habeeb da Hasina da Indo suka wuce kasuwa suka yan kowa Indo uniform, daga nan ɗinki suka bayar da zumar a dinka kafin suje su dawo, Hospital suka shige Habeeb ya biya kuɗi akan a yiwa Indo wankin haƙori, tas kuwa aka wanke, haƙorin Indo har wani sheƙi suke, kamar basu taɓa yin yellow ba, Habeeb kuwa sai tsokanar Indo yake har suka dawo wajen mai ɗinkin suka karba daga nan ma SUPER MARKET suka shige suka sayo kayan ciye-ciye kalala Sannan suka dawo gida.

______________________________

Allah sarki rayuwa wai Hausawa suka ce sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba'a jeba, Indo ta fara tafiya makaranta cikin Sa'a da kuma Nasara domin kuwa tafi kowa ganewa cikin ajin nan inda tayi sabuwar ƙawa mai suna Zahra yar gidan deputy governor, sosai jinin su yazo ɗaya da Indo, gashi kuma dukansu gifted ne, haka kuma an sata islamiyya a nan cikin unguwar tasu, hakan sai yasa Indo yanxu bata da lokacin kanta daga ta dawo daga boko sai kuma ta wuce islamiyya, asabar da Lahadi kawai take da time nan ma da daddare bayan isha malamin da Habeeb ya ɗauka mata na lesson yake zuwa, haka kuma aikin gida, takan taya Momy koda ran Momy baiso ba, domin kuwa har yanzu akwai ƙiyayyar Indo cikin Zuciyar Momy.

Yau Indo a gajiye ta shigo gidan, zama tayi kusa da Inna tana dariya tace.

" Hajiya Inna ya naga yau sai famar haɗa rai kike wani abu ne ya faru?"

" Me kuwa zai faru Indo kawai dai yau haka na tashi."

Murmurshi Indo tayi tace.

" Inna kenan, yauwa Inna ya Habeeb ya dawo daga Hospital ɗin nasu kuwa?"


Harara Inna ta watsawa Indo tace.

" Meye kuma wani cospital, ni ki daina min wannan turancin naku."

Dariya sosai Indo keyi tace.

" Kai Inna bafa cospital ba, Hospital ake cewa, ma'ana asibiti nake nufi."

"To bai dawo ba, sai ki tashi kije ki cire kayan makarantar ki samu kici abinci."

Tashi Indo tayi tana dariya ta haura step tana ƙoƙarin cire bag ɗinta, wani irin wawan karo taji tayi da mutum taga-taga Indo tayi zata faɗi a kan step ɗin, cikin jin tausayin ta idan ta faɗi a step ɗin ya sashi saurin tallafo ta jikin sa, runtse idanta Indo tayi tana jiran sarautar Allah, sai taji ta, kwance ƙirjin mutum, shiko wani irin shokin yaji kamar wanda wutar lantarki ta jasa, a hankali Indo ta buɗe idonta, ras ta sauke su fuskar Mustafa ya Wani haɗa rai, kafin ya saketa yana mata mungun kallo tare da cewa.

" Ke dai kullum cikin Hauka kike, sam baki da hankali cikin jikinki" ya ƙarasa maganar tare sauƙe mata ranƙwashi bisa kanta.

Riƙe Inda ya ranƙwashen tan Indo tayi tana hararar Mustafa itama, ido cikin Ido tare da murguɗa masa baki, zaro idanunsa yayi yana nuna kansa da yatsa yace.

" Ni kike harara da murguɗawa baki lallai kuwa yau jikinki zaiyi tsami cikin gidan nan" bakin nata Mustafa ya kama ya murɗe da ƙarfi, sanda hawaye suka zubo fuskar Indo, da ƙyar ya sake mata baki, rugawa da gudu Indo tayi sanda tazo daf kofar ɗakin su tace.

" Allah ya isa mungu azzalumi, Allah ya saka min."

Biyota yayi da gudu, ko kafin ya shigo ta faɗa cikin ɗakin tare da danna key, ƙwafa Mustafa yayi tare da kaɗa kansa ya shige.

Cikin sauri Mustafa ya nufi hanyar waje, Muryar Momy yaji tana cewa.

" Kaga kazo idan fita zakayi ka wucewa RAUDA da waɗannan kayan nata gidan su, tace min daga makaranta gida zata wuce, sai ka miƙa mata su."

Haɗa Ransa Mustafa yayi yace.

" MOMY ba can zanje ba yanzu ni office zan shige kawai ki bayar a kaimata."

" Ban bayar an kai matan ba, ka ɗauka ka kai mata ko kuma ranka ya ɓaci wai Mustafa meyasa kake min musu ne, duk sanda na maka Magana akan RAUDA?"

" Nifa Momy ba musu nake miki ba, kawai ba hanyar zanbi bane."

" To ko ba hanyar zakabi ba, ka ɗauka ka kaimata idan yaso sai ka dawo kayi hanyar taka."

Ɗaukar kayan Mustafa yayi cikin ɓacin rai ya fice, ita kuwa Indo bayan ta cire kayan ta, ta fito cikin sauri tayi kitchen, Momy ta samu tsaye tana aikin yankan koɓewa.

" Sannu da aiki Momy"

Harara Momy ta sauƙewa Indo tace.

" Wai ke bazaki fita cikin sha'anina bane kafin nace ki daina kulani dole ne saikin kulani, koni uwar kice, wani wai sannu kin sani aiki ne da zaki cemin sannu, dallah! Ɗauki Abunda ya kawo ki ki fice daga cikin kitchen ɗin."

Wannan karon Indo bata damu da zagin da Momy ta mata ba, domin kuwa idan da sabo yanxu ta saba da zagin Momy ɗaukar abincin ta, Indo tayi ta fice daga kitchen ɗin, Hasina da sharifa ta tarar cikin falon kusa dasu ta zauna taci abincin, suna taɗi.

Shiko Mustafa a ƙofar gidan su, RAUDA ya tsaya ya miƙawa mai gadi kayan RAUDA yace gashi ya shigar musu gida sannan ya wuce abunsa, mai gadi kuwa har cikin falo ya kaiwa mami kayan, tambayar sa tayi waye ya basa, ya amsa mata da Mustafa, wani ashar mamy ta sauƙe tare da cewa.

" Amma wannan yaron akwai shege mai taurin kan tsiya, Wato shi yafi ƙarfin ya kawo min kayan har cikin ɗaki gara ya bawa mai gadi ya kawo, badai an kusa Auren ba, zanyi maganin wannan taurin kayin naka daga kai har Uwar taka.............


Kuyi manage da wannan bani da times ne sosai kwanan nan, ayyuka sun min yawa ga school.


*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*
[2/21, 4:52 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••5️⃣1️⃣ ➡️ 5️⃣2️⃣

Haka Mamy ta gama mitar ta ita kaɗai ta gaji tayi shiru.

Yau Indo ana gida Babu islamiyya kasancewar yau Alhamis, tana cikin su Sharifa da Hasina, sai zance suke, har la'asar lokacin shiga kitchen yayi, tare suka shiga dukan su, komai tare suke basa ware Indo kasancewar ta ƙarama a tsakanin su, Sharifa ce ta dubi Indo tace.

" Indo yau fa kece zakiyi girkin nan, ehe kiyi mu gani ko kina gane yanda mukeyi kullum dan kinsan ya Mustafa yana son matar da ta iya girki sosai" Sharifa ta ƙarasa maganar cikin zolaya.

Haɗa fuska Indo tayi tace.

" Allah ya sauwaƙa ni bana son ya Mustafa yanxu, Allah na tsanesa dama rashin Hankali yasa nake cewa ina sonshi, mungu ne kuma azzalumi."

Zaro ido Sharifa tayi tana kallon Indo kafin tace.

" Oh yanxu kina da hankali kenan, ya Mustafa da kullum kike kira kina so yanxu kice bakya sonsa."

Murmurshi Indo tayi tana duban Sharifa kafin tace.

" Aunty Sharifa kenan, nayi Hankali yanxu Aunty Sharifa, na fara sanin menene ciwon kaina, menene kuma rayuwa, kuma duk ta sanadiyyar ku na fara sanin hakan, da ke da ya Habeeb da Aunty Hasina, sai aminiyata Zahra, kune kuka fara nuna min rayuwa da kuma nutsuwa, har nazo na fara fuskanta, zan iya miki rantsuwa da Allah cewa bana son ya Mustafa, dama kwalliyar sane kawai yake burgeni ko a da ma rashin Hankali yasa nake cewa ina sonsa, kwalliyar sa kai yake burgeni ni kuma saina ɗauki hakan a matsayin soyayya, ya Habeeb shine wanda ya banbance min haka ya nuna min yanda zan gane Soyayyar gaskiya tun daga nan na fuskanci cewa bana son ya Mustafa, na kuma fuskanci hakan, dan haka ni babu Soyayyar ya Mustafa cikin raina."

Ga baki ɗayan su shuru sukayi suna mamakin sanjawar Indo lokaci ɗaya mussaman Sharifa da tafi Hasina sanin waye Indo, cikin Zuciyar Sharifa take cewa, (Allah buwayi gagara misali, lallai ilimi haske ne cikin rayuwar ɗan adam da kuma zama cikin wayayyun mutane, ya kan sa mutum ya sauya ɗabi'un sa, wai yau Indo ce tasan ciwon kanta, tabbas yarinyar tana da good brench ikon Allah)
Hasina ce ta dawo da sharifa daga duniyar tunanin da ta lula ta hanyar cewa.

" Kinga ɗaura girkin nan maza kar dare yayi mana."

Ɗaurawa Indo tayi suna kallon ta, harta kamalla cikin mamaki yanda Indo tayi girkin ta tsaf Kamar yanda su Hasina keyi, lallai Indo tana da ƙwaƙwalwa, dariya Sharifa tayi tana zolayar Indo tace.

" Masha Allah! Sweetie na ta iya girki, Allah komai yayi dai-dai kinyi ƙoƙari."

Dariya Itama Indo tayi tace.

" Aunty Sharifa ke da kinyi zaton bazan iya bane cap ai Babu kalan abincin da bazan iya ba cikin gidan nan."

Dariya dukansu sukayi cikin haɗin baki su kace.

" Ai kuwa munga alama, gashi kin bamu mamaki."

Ɗaukar abincin sukayi suka jera su saman daining, sannan suka wuce ɗaki wanka.

Zaune yake cikin office tun ɗazu yake jin alamun mararsa na ƙullewa, Sanin abun zai iya tashi masa haiƙan ya sashi tashi cikin sauri ya fice daga office ɗin, motar sa ya shiga yaja da ƙarfi yana cije lips ɗinsa Allah ne kawai ya iso da Mustafa gida lfy, domin kuwa shi kaɗai yasan abinda yake ji, babu kowa cikin falon da ƙyar ya haura step ɗin, yana shiga ɗakin ya zuɓe saman bed sai kuma ya fara mutsu-mutsu yana cizon lips ɗinsa, tare da riƙe marar tasa dake sara masa.

Indo da ta fito daga bedroom ɗin su zatayi na Inna sai taga ƙofar ɗakin su Habeeb buɗe, hakanne ya sata kutsa kanta cikin ɗakin domin ita a zaton ta ya Habeeb ne ya dawo daga Hospital, sallama tayi kusan baki uku jin babu wanda ya amsa mata ka wai sai ta shige cikin bedroom ɗin, zaro ido tayi ganin Mustafa kwance dai mutsu-mutsu yake, ga hawaye kwance fuskar sa, Indo Sarkin tausayi, da sauri ta ƙarasa bakin bed ɗin tana cewa.

" Ya Mustafa meya sameka, baka da lafiya ne?"

Shuru Mustafa ya mata ba tare daya amsa mata ba, yana cigaba da mutsu-mutsun sa, cikin azaba domin baida bakin magana a yanxu, da ƙyar ya ɗago hanunsa yana mata nuni da drower alamun ta ɗauko masa drog ɗin sa, ita kuwa Indo bata gane me yake nufi ba, haurawa saman bed ɗin tayi ta kamo hanun Mustafa tana cewa.

" Ya Mustafa sannu kona kira Momy ta kaika asibiti, kaga baka da lfy har kuka kake yi."

Mustafa baiyi magana ba saima jawo Indo da yayi jikin sa tare da ƙanƙameta gam yana ƙoƙarin zura hannun sa cikin rigar ta, ƙoƙarin ƙwace kanta Indo take tana cewa.

" Ya Mustafa meye haka, ka sakeni dan Allah naje na kira maka Momy ta kaika asibiti, malamin islamiyyar mu yace haramun ne namiji yake taɓa jikin mace" tana maganar ne tana ƙoƙarin ƙwace jikin ta daga garesa, shiko Mustafa baima san tana yiba shidai burin sa, kawai ya kamo breast ɗinta da suka fara ɗan tasowa, domin kuwa Mustafa baya cikin hankalin sa.

A nutse bakinsa ɗauke da Sallama ya shigo ɗakin, turus ya tsaya yana kollon Mustafa na kokuwa da Indo, wani irin maƙoƙon baƙin ciki ne ya tsayawa Habeeb a rai, da sauri ya ƙarasa wajen nasu, cikin zafin nama ya fisgo Indo da ƙarfi, ya wullo ta ƙasa yana mata mungun kallo, shiko Mustafa ɗago kansa yayi da ƙyar ya kalli Habeeb kafin ya ƙara danƙe marar sa, yana juyi, hanun Indo Habeeb yaja sannan ya wurga ta waje yana nunata da yatsa, simi-simi Indo ta shige bedroom ɗin su ta faɗa bisa bed sai kuma ta saki kuka mai sauti.

Komawa ɗakin Habeeb yayi, tare da buɗe drower ya ɗaukowa Mustafa drog ɗin sa da ruwa ya tallafo sa, sannan ya basa yasha, cikin minti biyar ya fara haɗa gumi sai kuma bacci mai nauyi ya ɗebesa, ficewa daga ɗakin Habeeb yayi ya faɗa nasu Indo cikin faɗa, Allah yaso babu Kowa cikin ɗakin su Hasina sunyi bedroom ɗin Inna, harara Habeeb ya zabgawa Indo kafin yace.

" Kukan munafurcin me kike, ki faɗa min meya kaiki bedroom ɗin mu, ki faɗa min! Nace?" Ya ƙarasa maganar cikin tsawa.

Ja da baya Indo tayi tana riƙe bakin ta, sa kuka ke ƙoƙarin ƙwace mata, cikin tsorata da lamarin ya Habeeb ga Idonsa sun koma red colour mutum da bai taɓa mata tsawa ba, shine yau yake mata, mutumin dako laifi tayi sai dai ya mata faɗa cikin nasiha, shine yau yake mata wannan ihun a kai, cikin tsoro tace.

" Na Na Naje neman kane shine na gansa yana kwance baida lfy shine nace kona kira masa Momy ta kaisa asibiti, shine ya jawo ni jikinsa."

" Ya jawo ki jikinsa koko ki haura bed ɗin har ya samu damar jawo ki, ba nace ki daina shiga bedroom ɗin mu ba, har sai kinyi sallama an miki izini ba?"

" Ka faɗa min kayi hkr bazan sake ba."

Ƙwafa Habeeb yayi sannan ya fice daga cikin ɗakin, koda daddare da suka zo cin abinci babu Mustafa domin kuwa bai tashi ba, da Daddy yace a kirasa sai Habeeb yace kar a tashe shi baya jin daɗin jikin sa, Indo kuwa tana gefe jikin Inna sai satar kallon ya Habeeb take, ganin yayi banza da ita kamar babu ita a wajen ko inda take bai kalla ba, idanunta ne ya ciko da ƙwalla tayi saurin gogewa, bata san kuma duk abunda take Habeeb yana kallon ta, ta kasan idanunsa, sosai ta basa tausayi ganin yanda take goge hawaye a ɓoye, duk da haka yayi fuska bai kulata ba, Daddy ne yace.

" Habeeb yaya maganar ginin da zaku tayar ne, a nan cikin Estate ɗin, naji har yanxu kunyi shuru bakwa magana?"

" Daddy ai jibi za'a fara ginin in sha Allah mun gama magana dasu, zasu mana part biyu."

" Okey yayi Allah ya taimaka, jiya Daddyn Hasina ya kira ni kan cewa yaushe za'a tsaida ranar Auren amma nace masa suyi hkr har ku kammala ginin gidan ku, ya kuma fuskance ni, ita kuma Hasina ashe tunda tazo bata je wajen ƴan uwan mahaifinta ba? sai jiya Alhaji Ibrahim ɗin ke sanar dani."

Dariya Habeeb yayi yace

" Daddy gobe take da niyar zuwa daman taje tayi sati daya a can."

" Okey Allah ya kaimu" Daddy ya furta tare da wucewa bedroom ɗin sa, Momy ma bata juma ba, ta wuce nata bedroom ɗin, Indo ma bin Inna tayi tace nan duniya ɗakin Inna zata kwana, tambayar ta Hasina tayi ko sun mata laifi, tace babu komai ita dai kawai zata kwana ɗakin Inna ne , ina itace tace su rabu da ita yau taga alamar Yan iskan tane suke kusa da ita, dariya sukayi kafin suma suka shige nasu bedroom ɗin, a ɗaki Inna ritsa Indo tayi tace ta faɗa mata ko akwai Abunda aka mata ne, taga kamar taci kuka amma Indo tace nan duniya babu komai haka dole Inna ta ƙyaleta.

Mustafa bai farka ba sai wajen goma na dare, wanka yayi tare da zuwa ya zauna ko mai bai shafa ba, kansa ya riƙe yana tuno Abunda ya faru ɗazu tiryan-tiryan pic ɗin abun ke faɗo masa, da ƙarfi yace "NO!"

Ɗago kansa Habeeb yayi ya kalle sa, kafin ya kawar da kansa yana cewa.

" Ya kamata ace na baka shawara wacce kullum nake son furta maka ita nake tsoron girman kanka zai hana ka ɗauka" Habeeb bai saurari me Mustafa zaice ba ya cigaba da cewa " ya kamata ka riƙe RAUDA matsayin matar so, tunda tana sonka kuma bata da wani aibu duk abunda mace mai ji da kanta take dashi itama RAUDA tana dashi, ka manta da........

Da katar da Habeeb Mustafa yayi ta hanyar ɗaga masa hanu alamun yabar maganar baya so, murmurshi Habeeb yayi tare da kauda kansa ya kuma yi shurun ba tare daya ƙara cewa komai ba.

Wasa wasa yau kimanin kwanaki biyar Habeeb baya kula Indo ko kallon ta baya yi, Indo ta damu sosai da sauya mata da Habeeb yayi, gashi kuma tunda wannan abun ya shiga tsakanin ta, da Mustafa bata ƙara sashi cikin idanunta ba.

Zaune take a makaranta sun fito break ita ɗaya kusa da bishiyar maina ta tafka tagumi, Zarah da tazo kusa da itane ta zauna tare da dafa kafaɗar Indo tace.

" Lafiya ƙawata tun ɗazu nake neman ki cikin makarantar nan ashe nan kika taho?"

"Eh" kawai Indo tace mata a takaice.

Zahra ƙara cewa Indo tayi.

" A'isha Meya same ki naga kamar ranki a ɓace yake?"

" Nace miki babu! Ko kin isheni da tambaya."

Murmurshi Zahra tayi kafin tace.

" Allah ya baki haƙuri ni a nawa tunanin mun riga da mun zama ɗaya haka kuma damuwar mu ma zata kasance ɗaya, ashe abun ba haka yake ba a wajen ki, Nice kawai na ɗauke ki aminya wacce nake iya sanar dake damuwata ba tare da shamaki ba."

Sanyi jikin Indo yayi, ta kamo hanun Zahra tana tace.

" Sam ba haka bane ƙawata baki da shamaki da damuwa ta, kawai raina ne yake ɓace sakamakon daina kulani da Ya Habeeb yayi, sam banjin daɗin haka mussaman yanda ya Habeeb ya dauke ni tamkar ƙanwar sa wacce suka fito ciki ɗaya, amma yau fushi yake dani kwana biyar kenan baya kulani, abun yana damuna sosai cikin zuciyata."

Cikin mamaki Zahra tace.

" What! Ya Habeeb shine yake fushi dake har ya kai 5dys bai miki magana ba, wani irin laifi kika masa haka mai girma A'isha da har zaiyi fushi dake haka?"

Cikin zubar da hawaye Indo take mayar Zahra abunda ya faru.

" Gaskiya A'isha laifin kine taya har zai jawo ki jikinsa ba tare da kece kika haura bed ɗin ba, gaskiya laifin kine."

Duban Zahra Indo tayi tace.

" Kina nufin kema kina zargi na kenan?"

" Ko kaɗan bana zargin ki, A'isha, kawai na baki laifin kine na kuskuren kusantar sa da kikayi, sanda kika gansa haka kamata yayi kije ki sanar da mahaifiyar sa, ba wai ki tsaya kusa

Please Login or Register in order to submit comment