Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tabi tana kalmar shahada har Allah yayi ikon sa, Allah sarki rai baƙon duniya yau dai ga Inna da bata son mutuwa ta tafi tabar duniyar ta koma zuwa ga mahaliccin ta, kuka Habeeb yasa mai tsuma Zuciya kafin ya durƙusa kasa yana kukan Daddy kuwa zani yaja ya rufe Inna yana Allah ka jiƙan mahaifiyata Allah ka karɓi baƙon cin ta Allah ka yafe mata, hawaye kuwa yana tsere saman fuskar sa.


( Ana son idan mutum yazo mutuwa wanda ke kusa dashi ya dinga kalmar shahada, idan har Allah ya bawa wannan mamacin Sa'a sai kuga shima ya ɗauki wannan kalmar shahada bawai kuta zunduma kuka ba kuna cewa wayyo Allah katanga ta faɗi wayyo mun shiga Uku, wannan duk basu da kyau domin kuwa kuna ƙarawa mamaci azaba ne, gara kayi hawaye ka kuma bishi da addu'a wannan shine gatan da zaka masa)

Kama hanun Habeeb Daddy yayi suka fito waje cikin firgici su kayo kansu ganin yanda Habeeb yake kuka, Mustafa yana kallon halin da Habeeb yake ciki ya tabbatar da cewa Inna ta rasu, zama kawai yayi tare da dafe kansa dake ƙoƙarin barin jikin sa.

" Momy Inna ta tafi ta barmu Inna ta mutu ta barmu da kewarta Momy babu Inna cikin wannan Duniyar.........

Karar da Indo tayi shine ya hana Habeeb karasa maganar tashi, yankan jiki tayi ta faɗi, sukayi kanta da gudu, suna girgiza ta...........




*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*




*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*



*(Ummu Nasmah ce)*
[2/28, 9:48 AM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*••••••5️⃣7️⃣ ➡️ 5️⃣8️⃣

Girgiza Indo Habeeb da Hasina suke cikin tashin Habeeb yake cewa.

" Indo! Indo ki tashi dan Allah karki mutu kema wlh muna son rayuwar ki, idan kin mutu sai nafi kowa baƙin ciki cikin wannan duniyar ƙarshe ma, rayuwata ta ƙare cikin baƙin cikin rashin ki, pls Indo ki tashi dan Allah" yana maganar ne cikin zubar hawaye da ɗimauta yama manta da cewa shi doctor ne, Mustafa da tun ɗazu yake zaune ya rasa me yake yiwa rayuwar sa daɗi domin shi gani yake daɗi shine yake kawo kuka shi so yake ya samu yayi kukan ko zaiji sassauci cikin zuciyarsa amma kukan yaƙi zuwa yasan duk yanda Habeeb suka shaƙu da Inna bai kai yanda shi suka shaƙu ba, shida ko wani weekend cikin Dasina wajen Inna kafin ta dawo birni da zama ko daddy bazai kaisa jin wannan mutuwar ba, cikin ƙarfin hali ya taso yazo har gaban Indo ya sunkuya tare da kai kansa ƙirjin Indo, cikin zaro ido ya ƙara maida kunnen sa sosai, still dai Indo bata motsi, doctor ya fara kwalawa kira cikin sauri yana cewa.

" Doctor! Doctor! Doctor"

Da sauri doctor Ibrahim da doctor Jamil suka nufo su cikin sauri, kan Indo suka sunkuya tare da ƙwalawa nurse kira, emagency aka shigar da Indo, su Habeeb tsayawa sukayi cirko-cirko, cikin tsoron abunda zaije ya dawo, Momy kuwa ita ko a jikin ta, domin ji take dama Indo ce ta mutu tabar Inna, Zama tayi tare da haɗa tagumi tana jinjina mutuwar Inna, doctors duk yanda sukayi ganin Indo ta farfaɗo amma ina abu yaci tura allurai suka mata tare da sa mata drip sannan suka fito da ita zuwa cikin ɗakin hutu, doctor Ibrahim fitowa yayi yana sharce gumi tare da kallon su Daddy yace su biyosa office, bayan sun shiga ne dukansu har Mustafa, doctor Ibrahim ya dubesu tare da cewa.

" A gaskiya yarinyar nan bata farfaɗo ba duk Abunda muka san zamu iya munyi amma bata dawo cikin hayyacinta ba, da alamu dogon suma tayi sakamokon firgici da ta samu, so munyi mata allura tare da sa mata drip, zamu jira muga nan da 24 hours ko zata farfaɗo, sannan kuma bawai farfaɗowar tata bane abun damuwa yanda zata farfaɗo ɗin, idan har ta sake farfaɗowa a firgice, za ta iya samun heart atack, Abunda kuma bama son ya kasance, so gaskiya tana buƙatar Addu'ar mu gabaki ɗaya."

Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un! Kawai Habeeb yake furtawa tare da wasu hawaye masu zafin gaske, yana cewa.


" shike nan na shiga uku zamu rasa ta itama, doctor Ibrahim ka taimake ni kar Indo ta samu heart atack pls ina cikin ɗimuwa bazan iya taimakon Indo ba domin bazan iya aikata komai ba."


Tsaki Mustafa yaja tare da tashi ya nufi frig ɗin dake cikin office ɗin robar swan water ya ɗauko tare da cup ya tsiyayi ruwan, duka binsa da kallo sukayi, Daddy ne yayi ƙarfin halin cewa.

" Muhammadu me zakayi da ruwa ana magana kayi shuru?"

Dam! Gaban Mustafa ya faɗi jin Daddy ya kirasa da sunan da Inna ke kiran sa, duk da haka bai kula Daddy ba, saima addu'a daya fara jerawa cikin ruwan (fatiha yayi ƙafa 11 nasi 3 falaq 3 ayatul kursiyo 3 amanarrasulu 3) ya fice daga office ɗin riƙe da cup ɗin a hanun sa, ga baki ɗayan su tashi sukayi suka bi bayan sa, su Momy ma dake waje ganin shigewar Mustafa ɗakin da aka kwantar da Indo ga kuma su Daddy sun bisa ya sasu binsu suma Mustafa durƙusawa yayi a gaban Indo tare da zuba ruwan a hanun sa, ya shafa mata a fuskar ta da hanun ta zuwa ƙafafuwan ta, sannan a hankali ya buɗe bakinta yanda ruwan zai shige mata ya dinga zuba mata a hankali kafin ya ajiye cup ɗin ya fice daga cikin ɗakin yayi na Inna nan ma binsa sukayi, gaban Inna ya durƙusa ya yaye mayafin da aka rufeta dashi ya fara cewa.

" Nasan kina jina Inna mayar min da amsa ne kawai bazaki iya ba, tabbas idan nace banji baƙin cikin rabuwa dake ba, nayi ƙarya, Inna ke kakace wacce ko wani jika zaiyi alfahari dake, nasan ɗazu kinso kiji murya ta, sai dai kash na kasa mayar miki da martani sakamokon kuka dake niyar ƙwace min, zanta miki addu'a Inna daga nan har nawa ƙarshen numfashin Allah ya karɓi bakwancin ki Inna, Allah yasa mutuwa ta kasance hutu a gareki Allah ya baki ikon amsa tambayoyin ki cikin sauƙi ya yaye miki duhun kabarin ki, ya haskaka miki shi ya kuma faɗaɗa miki shi" sai yanzu kukan ya ƙwacewa Mustafa, ya zauna daɓas tare da dafe kansa yana kuka mai tsuma Zuciya, zama kusa dashi Habeeb yayi suka haɗa kai sai kuka suke kamar ba maza ba, Daddy ne ya dubesu tare da cewa.

" Me kuke yi haka Muhammadu yanzu ka gama nema mata rahama wajen Ubangijin ta shine kuma yanzu zaka zauna ka mata kuka, ko kun manta ba cewa kuka azaba ne ga mamaci karku manta yanzu Inna Addu'ar mu take buƙata ba kuka ba, shine kawai gatan da zamu mata ku tashi muje gida da Inna domin muyi gaggawan kaita makwancin ta, Hasina keda sharifa ku tsaya wajen Indo."

Daina kukan sukayi har Momy da su Hasina, sannan su Sharifa suka koma ɗakin da Indo take suna goge hawayen fuskar su.

Haka suka koma da gawar Inna gida Daddy da kansa ya kira malam musa mahaifin Indo ya sanar dasu rasuwar Inna, Mlm Musa yaji wannan mutuwar sosai, ko mama da taji kuka tayi sosai Kamar itama ranta zai fita, domin kuwa uwa ta ɗauki Inna wacce tayi naƙuda ta haifeta, gabaki ɗaya garin Dasina ya ɗauka da rasuwar Inna, Mlm Musa hkr ya bawa Daddy akan cewa kar akai Inna a jirasu suna zuwa yanzu, dattawan garin Dasina gabaki ɗaya sun taho har maigari Mama da Goggo Hali sai Inna Saude da Lami ƙawar Indo tace itama sai taje ta yiwa indo ta'aziya, cikin 1hours suka iso cikin birni, Mama da Goggo Hali da kuma Inna Saude sune sukayi Inna wanka tare da mata sutura, Allah sarki rai baƙon duniya, haka aka kai Inna makwancin ta ba tare da Indo taga gawar Inna ba, Habeeb da Mustafa sosai suka yiwa Inna Addu'a bisa kabarin ta, ƙofar gidan alhaji Haruna cike yake da mutane ƴan karɓar gaisuwa, cikin gida kuwa Mama ce ta dubi Momy tace.

" Hajiya a'isha banga Indo ba tunda nazo ni?"

Cikin halin ko inkula da halin da Indo take ciki Momy tace.

" Tana asibiti tunda Inna ta rasu ta yanki jiki ta faɗi tana can har yanzu bata farfaɗo ba."

" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un! Allah sarki Indo sabo turken wawa, dole ki faɗi Indo koni uwarki dana haifeki ban miki gata da ƙaunar da Inna take miki ba, Allah ya baki lfy ya baki ikon hkr da rashin Inna."

Taɓe baki Momy tayi tace

" Ameeen." Daga nan bata ƙara cewa Mama komai ba, itama Mama bata ƙara cewa komai ba.
Shigowar Mamy da RAUDA sai Hindatu ƙawar Mamy shine yasa Momy maida hankalin ta, kansu tana dariya kamar ba mutuwa akayi ba, tana cewa.

" Sannun ku da zuwa Hajiya Turai kune tafe yanzu, maraba ku iso ku zauna."

Zama sukayi Mamy tana yiwa su mama wani irin kallon ƙyama, kusa da Momy ta zauna suka gaisa tare da yiwa juna ta'aziya, basu gaishe da Mama ba, sai RAUDA kawai ta gaishe ta, cikin mutunci kuwa Mama ta amsa sannan ta tashi tabar musu wajen tayi wajen su Goggo hali, ta samu Lami tasa Inna Saude a gaba cewa lallai sai an kaita wajen Indo, Mama ce tace tayi hkr sai Daddy ya shigo zata masa magana ya kaisu wajen Indon.

Hajiya Turai duban Momy tayi tace.

" Hajiya A'isha ashe kuma kin rabu da damuwa, tsohuwa ta ƙara gaba."

Dariya Momy tayi tace.

" Ke dai bari kawai daman itace ta takura ni cikin gidan nan, kuma yanzu ta bani iska, duk da naji zafin mutuwar ta, amma dai gaskiya nafi jin daɗin bani iska da tayi, yanzu ne zansan yanda zanyi na kora wannan shegiyar yarinyar ƙauye, kinsan tana can asibiti ta yanki jiki ta faɗi har yanzu bata farfaɗo ba, ni dama shigewa tayi tacan kowa ya huta."

Dariya sosai Mamy take harda shewa tace.

" Ba dole ta faɗi ba taga asirin ta zai tonu, za'a koma ƙauye wacce ta shigo da ita birnin ta wula, Allah dai ya kyauta amma dai karki barta ta ƙara wani zamani cikin gidan nan."

Takaici da haushin iyayen nata shine yasa RAUDA tashi ta fice tabar musu wajen Ishaq ta kamo tace yaje ya mata magana da ya Mustafa ta masa ta'aziya, da gudu kuwa Ishaq ya fita, gun Habeeb yaje yana cewa ya Habeeb ina ya Mustafa, sai yanzu Habeeb ya lura cewa Mustafa baya wajen, dudduba Wajen yayi yaga babu Mustafa har wajen su Daddy yaje baya nan, cewa ba Ishaq yayi yaje yace Mustafa yana zuwa, zama yayi yana mamakin ina Mustafa ya shige.

Mustafa kuwa asibiti ya koma, domin kuwa haka kawai ya tsinci kansa da son sanin halin da Indo take ciki, su Hasina suna zaune sunyi tagumi babu mai cewa ɗan uwansa komai, Mustafa ya shigo, zama yayi gefen gadon yana ƙarewa Indo kallo, kafin ya fara tofa mata addu'a, yana cikin tofa mata Addu'ar ne Sharifa taga hanun Indo ya fara motsi, da sauri ta karasa tana cewa

" ya Mustafa hanunta yana motsi."

Duban hanun nata yayi ya cigaba da addu'a yana roƙa mata sauƙi wajen Ubangijin ta, (ƴan uwana mu kasance masu yawan addu'a ga mu kanmu da ƴan uwan mu, domin kuwa shi alƙur'ani waraka ce ga dukkan ciwo da damuwa) a hankali Indo take buɗe idanunta harta buɗe su duka amma idanunta na zubar da ruwan hawaye tana kiran sunan Inna, riƙo hanunta Mustafa yayi yace.

" Ki daina kukan haka ki yiwa Inna Addu'a kinji."

Fisge hanunta Indo tayi tana cewa.

" Na daina kuka fa kace! Ta yaya zan daina kuka bayan na rabu da gatana uwata wacce take sona a kowanne Hali, wacce ta ɗauki damuwata nata haka ma farin ciki na, ta maidashi nasa, take min duk abunda nake so koda kuwa ranta baya sonsa, tana take laifi na, ta mayar dashi ba laifi ba, take bani duk wani Abunda nake so muddun kuwa tana dashi, ka faɗa min! Taya zan daina kuka! Ta ƙarasa maganar tana sakin wani irin kuka mai taɓa ZUCIYA tana dafe ƙirjin ta, ta cigaba da cewa "zuciyata zafi take min ji nake kamar zata bar jikina, ina ma ni mutuwa ta ɗauka tabar Inna, Ina kin tafi kin barni cikin ƙunci da damuwa banda wani farin ciki a yanzu, ku tashi ku kaini naje muyi bankwana da Inna nayiwa gawarta kallon karshe, duk da har abada hoton fuskar ki bazai taɓa goguwa cikin idanuna ba."


Allah sarki Indo ta bawa kowa tausayi a wajen babu wanda yace mata an binne Inna gudun faruwar wani abun, da kanshi Mustafa yaje ya karbo sallama wajen doctor, suka tafi gida, tunda suka shigo cikin gidan Indo bin kowa take da kallo ba tare da tayi Magana ba ɗakin Inna ta wuce su Mama ta samu zaune, da gudu Lami ta faɗa jikin Indo ta saki kuka tana Cewa.

" INDO Innan mu ta mutu ta barmu, Inna tana sonmu tana karɓa mana faɗa ta bamu kuɗi, idan mukayi fushi ta rarrashe mu, yanzu kuma ta tafi ta barmu."

Hawayen ta Indo ta share tana ɗaga jikinta daga na Lami tace.

" Zo muje ki rakani na yiwa Inna bankwana ina son na ganta kafin su binne ta, na mata Addu'a."

Tashi Mama tayi ta kamo hanun Indo ta Ajiye ta, ta fara mata magana cikin rarrashi.

" Indo kiyi hkr ki daina wannan kukan haka, Inna ta rasu bazamu iya dawo da ita ba, gatan da za ki yiwa shine addu'a, kuka ba naki bane da kiyi kuka da kar kiyi Inna dai ba dawowa zatayi ba, yanzu ki Zauna kiyi mata addu'a, an kai gawarta makwancin ta tun ɗazu......"

INDO bata jira Mama ta gama magana ba ta fita da gudu ko takalmi babu ƙafarta, fitowa Mama tayi da Inna Saude suka bi bayan ta, su Momy ma tashi sukayi suna binsu da kallo, Indo kuwa babu Inda ta tsaya sai wajen Daddy, faɗawa tayi jikin Daddy ta saki kuka mai tsuma Zuciya tana cewa.

" Daddy meyasa kuka binne Inna ta, ba tare da kun jira na ganta ba, meyasa Daddy" ta ƙarasa maganar tana sharce majina idanunta kuwa sun kunbura suntum daƙyar take iya buɗesu, cikin tausayin halin da take ciki Daddy ya mata magana cikin muryar rarrashi.

" Kiyi hkr dole yasa muka kai Indo ba tare da mun tsaya kinga gawarta ba, nasan wannan mutuwar kece a kayiwa amma kiyi hkr ki sawa Zuciyar ki dangana, ki ta yiwa Inna addu'a shine gatanta gareki."

" Daddy bazan iya hkrn rashin Inna ba, meyasa kowa yake bani hkr babu wanda ya bawa ita mutuwar hkr sanda tazo ɗauke min Inna, Daddy nima bazan yi hkr ba, kawai ku dawo min da Inna na."

Cikin hasala Baba dake zaune gefe yace.

" Kar Allah yasa ki hkr dan gidan ku, iskancin banza kawai, ana rarrashin ki kina yiwa mutane iya shege, tashi kibar wajen nan tunda bazaki iya hkr ba shashashar banza, kedai har abada bazaki taɓa Hankali ba" Baba ya ƙarasa maganar cikin faɗa.

Habeeb wani irin zafi yaji cikin Zuciyar sa, yanda Baba ke yiwa Indo faɗa baiga damuwar da take ciki ba, tashi Mustafa yayi yaje ya kamo hanun Indo ba tare daya kula kowa ba, yayi cikin gida da ita, juyawa suma su mama sukayi, Daddy ne ya dubi Baba yace.

" Mlm Musa bai kamata kana yiwa yarinyar nan faɗa ba, kasan yanda suka saba da Inna dole ne ta shiga cikin ɗimuwa, rarrashin ta, ya kamata ayi bawai a mata faɗa, har mu samu ta dawo dai-dai."

" Haka ne Alhaji Haruna kasan wani lokacin Indo tana da ban haushi, amm nikan ya banga Hindu ta iso ba har yanzu?"

" Ɗazo na sanar da mijin nata kamal amma nace karya sanar da ita sai sunzo saboda gudun damuwa kasan tana da Hawan jini, zuwan su zai kai gobe kasan sai sunyi visa."


" Allah ya kaimu" Baba ya furta yana tagumi, Alhaji Ahmed mahaifin RAUDA dake gefe ya dubi Daddy yace.

" Gashi kuwa mummunan Hawan jini ne da ita, Allah dai ya bata dangana."

" Ameeen" Daddy ya furta.


Ɗakin su Mustafa ya wurga Indo cikin hasala shima ya hau mata sababi.

" Wani irin Zuciya ce dake da bata hkr, ƴaƴan da ta haifa ma sunyi hkr da rashin ta bare kuma ke, ana rarrashin ki kina ƙi, to idan ba zakiyi hkrn ba, ya zakiyi zaki dawo mata da rai ne ko kiyi hkr ko kar kiyi Inna dai ta mutu kuma babu mai dawo da ita sai dai tarihi, idan kinga dama kita kuka daga nan har taki mutuwar tazo ta sameki" yana gama faɗin haka ya fice a fusace, kuka Indo tasa tana cewa.

" Shike nan na shiga Uku Inna kin mutu kin barni gashi har an fara zagina, dan Allah Inna ki dawo" birgima take tana kukan, Sharifa ce ta sunkuya kanta tana cigaba da rarrashin ta, daƙyar suka samu Indo tayi shiru sai kuma ajiyar Zuciya da take.

Sai da magaruba su Mamy suka yiwa Momy sallama suka tafi, Daddy kuwa sun jima a waje har 10:30pm suka shigo, tare suka kwana da Baba ɗaki ɗaya, daman saura kam tunda aka dawo daga maƙabarta suka juya Dasina.

Su Mama ɗakin Inna suka kwana, Indo kuwa tana bayan Sharifa a maƙale dan ko cikin dare ance bacci ɓarawo ne, amma dai ranar ita Indo bai sace ta ba, haka ta kwana tana tunanin Inna wani tayi kuka wani kuma tayi ajiyar Zuciya mussaman idan ta tuno rayuwar su ta ƙauye haka ta kwana cikin tunani.

Washegari misalin ƙarfe 1 na rana jirgin su Aunty Hindu ya sauƙa, Idi drever shine yaje da Mustafa suka ɗauko ta, tun a hanya Aunty Hindu taga face ɗin Mustafa babu walwala ba kamar yanda ta sansa ba, tun ƙofar gidan da Aunty Hindu ta hango a cike da mutane ta fara tambayar Mustafa me yake faruwa, Mustafa baice mata Inna ce ta rasu ba, saima cemata da yayi babu komai, get aka wangale musu suka shiga cikin gidan, cikin sauri Aunty Hindu tayi cikin gidan, domin ita dai bata yadda ba, duk da taga yayan nata a waje amma hankalin ta bai kwanta ba, dam gaban Aunty Hindu ya buga ganin Mama meron Dasina zaune cikin falon ga kuma su Inna Saude, dube-dube ta fara bata hango Inna cikin falon ba, a fili ta furta.

" Allah yasa ba Inna bace ta Rasu."

Daga bayan ta Daddy yace "Zauna Hindu"

Zama Aunty Hindu tayi tana dube-dube, Kafin Daddy ya dubeta yace.

" Hindatu kinsan dai Allah shine yake bayarwa ko?" ɗagawa Daddy kai tayi alamar ehh.

" To alhamdulillah! Sai nake ga ai wanda ya maka kyauta ya karɓi abunsa ya fika sonsa ne, bai kamata miji haushi ba ko ranmu ya ɓaci, Hindatu ki ɗauki ƙaddara na rashin Inna da mukayi mu cigaba da aika mata addu'a zuwa makwancin ta, ina ga wannan shine dai-dai."

Dafe kanta Aunty Hindu tayi idanunta na zubar da hawaye take furta innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un!

Tafi minti goma a haka kafin tace.................


________________________________

Masu min tambaya da bincike akan cewa meyasa na kashe Inna, zan baku amsar ku yanzu, akwai waɗanda suka biyoni ta private da yawa wasu suce min bai kamata na kashe Inna ba, wasu kuma suce min meyasa na kasheta, to ina son kusan wani Abu👇🏻

Ita mutuwa babu ruwan ta da baka da kowa koda kuwa wannan mutumin shine kaɗai gatan ka indai tazo Sai ta ɗauke sa, koda kuwa mutumin shine kaɗai gatan ka a duniya, zata ɗauke sa, kuma haka Allah bazai bar bawansa ya wulaƙanta ba, dan ya rasa wannan gatan nasa ita mutuwa dole ce,dan haka maganar bai kamata Inna ta mutu ba bai taso ba, karku manta da mutuwa tana ɗauke uwa da Uba lokaci ɗaya ta rabasu da ƴaƴansu babu ruwan ta da wannan ƙaunar da take tsakanin su kuma su rayu.
kudai ku cigaba da biyoni cikin labarin domin jin yanda rayuwar Indo zata kasance bayan Inna.


Ina Alfahari daku masoyana a koda yaushe😘


*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*



*(Ummu Nasmah ce)*[3/2, 3:29 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*WLH DA NIYATA NA DAINA RUBUTA WANNAN BOOK ƊIN, DOMIN KUWA AN ƁATA MIN RAINA FIYE DA TUNANIN KU, IDAN HAR KA TAMBAYI MUTUM BOOK TA PRIVET SAI KIYI HKR, KI JIRA WATAƘIL BATA ONLINE WATA ƘIL KUMA MESSAGE NE SUKA MATA YAWA SHIYASA BATA MAYAR MIKI AMSA BA, AMMA TSABAR RAININ HANKALI ZAKI WANI CEMIN WAI INA DA GIRMAN KAI, IDAN MA NA KUƊI NE NA FAƊA MATA ITA ZATA IYA BIYA KO NAWA NE, TUNDA TAGA YANZU WRITER'S KUƊI MUKA SAKA A RANMU MUN MAIDA SOCIAL MEDIA KASUWANCI, SAI KI FAƊA MIN WAYE BAYA SON KUƊI KO KUMA A INANE BA'A NEMAN KUƊI, DA KIKE WANNAN MAGANAR WACE WRITER'S KIKA TAƁA SAWA DATA, KOKO TUN FARKON BOOK ƊINA KINJI NACE NA KUƊI NE, BABU KOMAI KANKI KIKA YIWA KIJE GABA ZAKI HAƊU DA DAI-DAI KE NA BARKI DA ALLAH*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*•••••••5️⃣9️⃣ ➡️ 6️⃣0️⃣

"Naji zafin mutuwar Inna sai dai kuma nafi jin Zafin rashin ganawar da ba muyi ba da ita har ta koma ga mahaliccin ta, shekara 6 rabona da nasa mahaifiyata cikin idanuna, hakan ne idan na tuno nake jin zafi cikin zuciyata, nasan mutuwa rigar kowa ce, jiranta yake sai dai naso ace nasa Inna cikin idanuna koda sau ɗaya ne, Allah ya jiƙanki da rahama Inna yasa can yafi miki nan" ta ƙarasa maganar tana goge hawayen cikin idanunta, Aunty Hindu ta bawa kowa mamaki domin kuwa tafi kowa ɗaukar ƙaddara, da dauriya.

Wunin Ranar Aunty Hindu tare suka yisa dasu Mama Momy kam dama bata cika shiga cikin su ba, Indo kuwa ɗaki ta wuni cikin tunani, lokaci ɗaya tayi wani irin faɗawa idanunta su faɗa suma, hawaye kuwa har yanzu yaƙi barin idanunta ba.

Yau Litinin akayi sadakar bakwai ɗin Inna, kowa yayi haƙuri ya dangana ya barwa Ubangijin sa lamarin sa, haka Indo itama ta haƙura amma har yanzu taƙi sakewa jikin a sanyaye yake, su Mama sai haɗa kayan su suke zasu koma ƙauye gobe, Indo ce ta shigo cikin ɗakin tana ƙarewa kayan Inna kallo, wani zanin Inna ta hango, sai ta tuno, randa Ilu ya biyota da gudu ta faɗa gidan Inna, itama Inna ta bi bayan ta da gudu tana sababi har Indo take cewa ( lafiya Indo kike

Please Login or Register in order to submit comment