Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jinjina ƙarfin hali irin na Innah, ita daya kamata tayiwa Indo faɗa wai itace take ɗaure mata gindi, ya Allah ka shirya min Indo cewar mama.


A hanya Innah da indo suka bi wajen mahauta Innah ta saya musu nama, sanna suka dawo gida, zama sukayi Innah ta dubi Indo tace.

" Ki saurareni da kyau kiji Abunda zan faɗa miki, duk cikin ƙauyen nan duk wanda ya miki ki masa karki bari, aci kashi a kanki, domin kuwa naga an fara samiki ido cikin garin nan.

Dariya Indo tayi tace.

" Innah yo dama wa zan ƙyale, yanxu ma jira nake Allah ya haɗani da garba naci ubansa la'ada waje zaisan yamin Asarar ƙosai da koko na, dan uwarsa.

*Yawan sharhi yawan typing idan kunyi sharhi kaɗan nima kujini shuru sai bayan sati biyu, idan Kuma kunyi sharhi mai yawa kujini kullum tare da typing mai yawa*.


*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*
[1/30, 1:00 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻


TALLAH TALLAH TALLAH

Ina kuke makaranta littattafan Hausa ku matso kusa ga dama ta samu, ni ɗinnan dai *(UMMU NASMAH)* na shirya tsaf domin gabatar muku da sabon Novel ɗina, wanda zai nishaɗantar daku ya faɗakar daku, yasa ku cikin tunanin, mai taken *(RUƊANIN ZUCIYAH BIYU)* Wannan littafin yasha banban da sauran littattafan dana saba gabatar muku, labarin yana tafe da Soyayyah mai ban tausayi, ƙiyayya ƙyama tsangwama, tausayi, littafin zai ruɗa tunanin ku, kudai ku cigaba da biyoni domin karku bari a baku labari da abaku gara ku bayar, karku manta da sunan sa *(RUƊANIN ZUCIYAH BIYU)*
Nice taku mai son farin cikin ku a koda yaushe, *UMMU NASMAH CE*✍🏻


*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}`
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*•••••••2️⃣7️⃣ ➡️ 2️⃣8️⃣

" Kinga Indo tashi maza ki hura wutar nan, yau shinkafa zamuci da jar miya.

Tashi Indo tayi, ta fara kici-kicin hura wuta, domin kuwa Indo babu laifi akwai ƙoƙarin zama tayi girki amma idan taga dama, fah.

Suna aikin su suna taɗi har suka gama, cin abincin sukayi, saida akayi la'asar sannan Indo ta koma gidan su, siɗi siɗi ta shige ta ɗauki allonta tayi makaranta, tun biyar da rabi aka tashe su, tafe Indo take ita da Hansai, suna zance, Hansai ne tace.

" Indo ɗazu da zan tafi makaranta naga lami ta dawo daga tafiyar da tayi, har take cemin Anjuma zata shiga gidan ku.

Tsale Indo ta daka, cikin murna tace.

" Tsakani da Allah Hansai da gaske kike lami ta dawo.

" Wlh da gaske nake, ta dawo na ganta, da idanuna.

"Wayyo Allah daɗi, aminiyata ta dawo, rugawa Indo tayi da gudu tare da mikawa Hansai allonta tace ki kaimin gida.

Lami aminiyar indo ce ita da Hansai, itama lami hatsabibiyace sai dai bata kai Indo ba, shiyasa sukafi shiri da Indo fiye da Hansai.

Aiko Indo kiciɓis sukayi da Lami a ƙofar gidan su, cikin murna suka ɗane juna, Lami tace.

" Ƙawas andaɗe fa ba'a haɗuba, tun ɗazu naje gidan ku, Mama tace kinje makaranta, har gidan Innah naje tace bakya nan.

" Kedai Lami bari Wlh bana jin daɗin garin nan da bakya nan, ayyya Lami ya mustapha na dai har yanzu baixo ba sai sau ɗaya kawai nanma bai daɗe ba ya tafi, amma inaga zan lallaɓa Innah muje Birnin nan, Allah indai har naje baxan dawo ba.

Labarin Habeeb Indo ta dinga bawa Lami, har pictures ɗin da sukayi, ta karasa maganar da cewa.

" Kinga wata shegiyar kama kuwa da suke yi, gashi yana da kirki, sosai ba irin ya mustapha ba, kullum yana cikin haɗiye rai.

Shewa Lami tasa tare da cewa,

" Ke ƙawata, kwantar da hankalin ki, ba sai kinje ba, tunda Innah tana cikin garin nan dole zaizo shi, dan haka sa ranki a inuwa, amma gaskiya naso haɗuwa da wannan Habibun, yanxu dai ba wannan ba, ina zamuje neman magana kinsan an daɗe ba'ayi ba.

Shuru Indo tayi tana tunani, sai can tace.

" Muje shagon Mlm Ibrahim ko zamu samu Garba, muci ubansa daman ina da cikin sa.

" Muje Lami tace tare da kama Hanun Indo suka tafi.

Aiko Garba dake zaune yana jirawa babansa shago, ya hango su Indo suna, zuwa, tashi Garba yayi ya ruga da gudu domin kuwa yasan muddun ya shiga hanun su Indo ya shiga Uku, rufa masa baya suma sukayi da gudu, amma ina kafin su iso Garba ya tsere musu.

Haushi ne ya kama Indo cikin takaici, ta dubi Lami tace.

" Shege ya gudu, Ranar mafah haka yamin ya tsere Min.

Kallon shagon su Garba Lami tayi tace.

" Kinga Abunda zamuyi kawai mu ɗebi, biskit da minti muyi gaba, shi kuma shikenan, ki barsa.

Haka kuwa akayi suka shiga shagon suka ɗebi biskit da minti, sukayi tafiyar su, Indo kam a hanya, ta rabawa yara wanda ta ɗiba ko ɗaya bata ciba.
Lami ce ta kalleta tace.

" Ya kika rabar da naki baki ciba, bakya sone.

" Ina so mana kawai dai bazan ciba ne, nasan yau sai baban garba ya kaimu ƙara wajen mai gari, akan kayansa, kinga basu da hujjar da zasuce na biyasu kayan su, sai suje su nemi yaran dana bawa su karbi Kayan su a hanun su.

" Amma dai ke Indo akwai shasha, yo su kuma yara ina ruwan su, aida kici da karki ci, akan kene kika ci, garama kici idan yaso a miki hukunci da tushe.

" Kan Uba cewar Indo, uban waye ya isa ya hukunta ni akan abunda banci ba, to wlh ba'a isa ba, *Uwar kuturu ma tayi kaɗan balle na makaho* idan kuma akace za'a hukunta ni to wlh shima kansa mai garin saiya gane kurensa.

" Mtss matsalata dake Indo rashin wayo sai kitayi ni wlh saina ci, sai dai duk abunda zai faru ya faru.

" Na Yadda banda wayon kuma wlh karkici kema ki rabawa yara, kamar yanda nayi idan kuma kikaci to wlh duk hukuncin da mai gari ya yanke mana, akanki ne ke ɗaya, dan wlh *Banci kaza ba baxanyi aman gashi ba*

" Mtss sai kuma kiyi, tafiyar ta, Lami tayi tabar Indo tsaye a wajen.

Itama Indo tsukar tayi, ta tafi tana zagin Lami cikin ranta.

Gidan su, ta shige Mama ta samu zaune tana talge, kusa da jummalo ta zauna dake zaune tana, karkarwar zazzaɓi, sai hawaye dake zuba cikin idanunta, kallon jummalo tayi tace.

" Sannu jummalo ya jikin naki.

Hawaye ne, ya gangaro fiskar jummalo tace.

" Mutuwa zanyi Indo, dan Allah ki nutsu ki daina ɓatawa Mama rai kinga ni zan tafi na barki da Mama, dan Allah ki daina ɓata mata rai.

Kallon ta Indo tayi, sai kuma ta tuntsire da dariya, tace.

" Kai jummalo duk zafin ciwon ne, haka, wlh yau da Innah kika faɗawa Maganar nan da kinsha zagi.
Tana maganar ne, sai kuma taga Idon jummalo yana juyewa, sai kuma ta fara wani irin nishi, tsoro da Indo tajini yasata kwalawa mama dake madafi kira.

" Mun shiga Uku mama kixo jummalo zata mutu, wai daman da gaske kike mutuwar, zakiyi, wayyo Allah.

Da gudu Mama ta fito daga madafi, tayo kan jummalo tana girgiza ta, himar dinta mama ta dauko, tasa Indo ta kama mata, jummalo suka fito da niyar zuwa chemist amma ina kafin su ƙarasa fita daga gidan jummalo rai yayi halinsu, kallon Indo Mama tayi taga ita bata sanma jummalo ta rasu ba, cikin dauriya da ƙarfin hali tace.

" Mu koma Indo mu ajiye ta, tayi bacci jikinta yayi sauƙi.

Juyawa sukayi suka kwantar da jummalo, Mama tacewa Indo taje ta mata kiran Innah.
INDO na fita Mama ta fashe da kuka, tare da rungumo jummalo a jikinta tana mata addu'a.

Indo bata wani juma ba, suka shigo tare da Innah, da sauri Innah ta ƙaraso gaban Mama ganinta tana kuka tace.

" Mairo lfy meya faru, kike wannan ajiyar Zuciya haka.

" Innah jummalo ta rasu, ta tafi ta barni Innah.

Daɓas Innah ta zauna a ƙasa tare da sakin kukan itama, sai aka rasa waye zai bawa wani hakuri tsakanin su.

Allah sarki Indo, wato duk inda dan uwa yake yana son ɗan Uwansa, kasa kuka Indo tayi, ta zauna itama kusa da jummalo, sai kuma ta tashi ta fice da gudu, ashe Baba ta kira, tare suka dawo Baba yaxo ya same su sai sharbar kuka suke.

" Haƙuri Baba ya basu tare da musu nuni da cewa, jummalo yanxu bata buƙatar kuka a garesu, addu'a take bukata, Allah sarki rai baƙon duniya, jummalo kwanan keso tayi, Indo da Innah kuwa kwana sukayi basuyi bacci ba, washe gari da misalin karfe goma aka kai jummalo makwancin ta, Indo tasha kuka Ranar har idanun ta suka kasa buɗuwa, Innah ce ta kira Baba tace yaje ya nemi waya ya sanar da Haruna rasuwar jummalo.

Haka kuwa akayi Baba ya kira Abokinsa Haruna ya sanar masa.


*DUTSE LOCAL GOVERNMENT*

Hira suke ciki falon dukan su, suna zaune, har Habeeb, mustapha ne kawai baya cikin su, duban Momy Habeeb yayi yace.

" Momy akwai maganar fah da nake son na sanar dake, shi Daddy na sanar masa.

" Okey ina sauraron ka Habeeb.

" Momy daman ina son jibi idan Allah ya kaimu zan koma London, saboda ina son zan sanar dasu cewa nabar aiki dasu zan dawo gida na cigaba da aiki, so idan na koma zan tattaro duk wani abu da yake nawa na dawo, bazanfi sati biyu ba zan dawo insha Allah.

Murmurshi Momy tayi cikin murna tace.

"Alhamdulillah, daman Abunda nake so kenan Habeeb, nafi son aikin ka, anan gida Nigeria, naji daɗin wannan Albishir da kaxo min dashi, Allah kuma ya kaimu jibin lfy.

Murmurshi Habeeb yayi ya amsawa Momy da ameen sannan ya dubi, RAUDA yace.

" Ke Malama, wai yau bazamu ci abinci a cikin gidan nan bane, naga kamar baku da niyar yi.

Dariya RAUDA tayi tace.

" Kai dai kace yunwa kake ji kawai idan banda haka yaushe ma akayi breakfast, ta inda ya mustapha yafika kenan, shi babu ruwan sa, da yawan ci.

Dariya shima Habeeb yayi yace.

Wai damma shi mustapha baya gari, da yau mun gwada mun gani nida shi waya fi wani ci.

Kallon mamaki RAUDA tayiwa Habeeb, cikin Zuciyarta tace, haba shiyasa tun daya fita jiya shigota gidan nan banga ya dawo ba, ashe tafiya yayi, na shiga Uku anya wannan maganin namu akwai Sa'a cikin sa, kuwa.

Sharifa ce, tace.

" Momy da gaske ya mustapha tafiya yayi Babu Sallama yau.

Murmurshi Momy tayi tace Sharifa.

" Ehh shima baisan da tafiyar ba, sai da ya fita office ake sanar dashi, yaje inugu zasu gana da wani Criminal amma ina ga ya dawo gobe insha Allah.

" Allah ya kaimu Momy ya dawo dashi lfy.

Da ameen Dukansu suka amsa sannan Habeeb yace shi zai shiga ya kwanta.

Tashi RAUDA tayi cikin ɓacin rai tayi kitchen ita da sharifa suka bar Momy zaune a wajen.

Da dare bayan daddy ya dawo sunci abincin dare yake sanar da Momy mutuwar jummalo, sosai Momy ta taji mutuwar a jikinta, shi kanshi Habeeb yaji mutuwar domin yasan jummalo zuwan sa da yayi, yarinya ce mai nutsu da tarbiyya, gata da tausayin iyayen ta, daddy ne yacewa Momy.

" A'ishah inaga Ranar Laraba, zaku shirya gaba ɗaya zamu tafi dasina ta'aziya, da jibi nayi niyan mu tafi, to sai kuma gashi Habeeb zai koma jibin shiyasa nace, gara mu bari idan ya tafi mu kuma washe gari sai mu tafi shi mustapha munyi waya dash daga inugu zai wuce Dasina zamu haɗu acan.

" Shikenan Alhaji Allah ya kaimu jibin idan yaso saimu wuce dukan mu, har RAUDA.

Nisawa RAUDA tayi tace.

" MOMY ai ina da school babu Halin naje, zan dai koma gida idan kun dawo saina dawo nima.

" Okey Allah ya kaimu cewar Momy.

Haka kuwa akayi Ranar talata Habeeb ya wuce London tare da bawa Sharifa sakon idan taje, dasina Innah ta nuna mata Indo tace yana gaishe ta, Kuma yana mata ta'aziya, idan kuma ta samu network ta kirasa a waya ta haɗasa da Indo.

Ranar Laraba da safe su Momy suka ɗauki hanyar DASINA, daddy ne yayi waya da mustapha yake tambayar sa yaushe zai iso Dasina, sanar dashi yayi cewa sai gobe idan Allah ya kaimu, sannan daddy ya kashe wayar sa, RAUDA suka fara sauƙewa a ƙofar gidan su, kafin suka ɗauki hanya, tare da direban Daddy....................


Dan Allah kuyi hkr da wannan wlh yau ina da makaranta, shiyasa ban samu nayi muku typing mai yawa ba.


*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*

*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*


*(Ummu Nasmah ce)*
[1/31, 6:20 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻

*بسم الله الرحمن الرحيم*
____________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

*P*•••••••2️⃣9️⃣ ➡️ 3️⃣0️⃣

Sha biyu dai-dai su Momy suka iso cikin ƙauyen DASINA, cincirindon mutane, suka hango sun taru, daga nesa Momy ta hango yara biyu tsakiya sai famar dakuwa suke yi, Daddy ne yace direba yayi parking, parking yayi, ko kafin Daddy ya fito Momy ta rigasa, cikin sauri ta karasa wajen, Indo ce da Garba suke famar dakuwa, yayin da Indo tayiwa garba duka, ta ɗane ruwan cikin sa, sai dukan sa, take.

" Subhanallah Momy ta furta, tare da kamo hanun Indo da niyar janyeta daga jikin Garba.

Ƙwace hanunta Indo cikin masifa tace.

" Babu ruwan ki dani, ki barni naci ubansa, wlh ko gaba aka ambaci sunana saika gudu.

Kallon mamaki Momy ke bin Indo dashi, yarinya ƴar ƙarama da ita, ta dage sai dukan ƙaton namiji take, cewa Momy tayi.

" Haba baiwar Allah, kina mace kina faɗa da namiji, ki tashi kansa nace, wannan ai rashin Hankali ne, wawiya kawai, kina mace kin zauna sai kokuwa kike da namiji.

Indo dai taƙi ɗaga Garba Kuma a hakan take yiwa Momy tsiwa.

" Ni dai wlh ba wawiya bace, kiji mata dai, daga zuwan ki, baki san meya haɗamu ba, ki hau zagina, shi namijin cewa akayi mace baza tayi faɗa dashi ba, ni bana son shishshigi, kuma niba marar Hankali bace, da hankali na ehhe😏.

Salati Momy ta ɗauka tare da riƙe baki, tana jinjina fitsaranci irin na wannan yarinyar, gaskiya ita tunda Uwar ta, ta haifeta bata taɓa ganin marar kunyar yarinya irin wannan ba, a take a wajen tsanar Indo ya ɗarsu a zuciyar momy.

Ƙara sowa Daddy sukayi shida Ishaq, yana Cewa.

" A'ishah yaya dai, muna jiranki mun jiki shuru, har yanzu basu rabu bane.

Kaɗa kanta Momy tayi tace, waɗannan ba masu rabuwa bane, Alhaji muje kawai.

" A'a A'ishah ya zakice haka, baki rabasu ba dai, ƙarasawa Daddy yayi, ya kama, hanun Indo yace, tashi a kansa kinji ƴata, babu kyau faɗa, maza tashi.

Kallon Daddy Indo tayi sai kuma ta tashi akan garba tana nunasa da yatsa tana cewa.

" Daga kai har Zainabu munafukar data turo ka, sai naci ubanku, ka faɗa mata itama saura ita, ba ita bane munafuka, har zata zugaka, tace maka munyi sadaka da mintin ka, to munyi sai axo a daure mu.

Jan Hanun ta Daddy yayi ya fitar da ita daga wajen yace maza tafi gidanku kiyi hkr ya isa haka, Momy dai bin Indo take da kallon mamaki da kuma tsana, harta bacewa kallonta, jin ihun yara da sukayi suna cewa, jama'a Indo ta kashe garba baya motsi wlh, da sauri su Daddy suka ƙarasa kan Garba, da gudu wani yaro ya tafi kiran baban Garba, taɓa ƙirjin Garba daddy yayi, yaji ai suma yayi, ana haka mahaifin garba ya iso wajen, masifa yage da zage-zage, dakatar dashi daddy yayi yace.

" Kayi hkr Mlm Usman, suma yaronka yayi ba mutuwa, ba, ruwa aka mikowa Daddy ya zubawa, garba, sai kuwa gashi yaja numfashi tare da tashi a firgice.

Sai a lokacin Mlm Usman ya gane Daddy, hanu ya mika masa yana cewa.

"Alhaji Haruna kaine cikin garin namu, ai ban gane kaba, tsabar bala'in wannan yarinyar, yarinya ta zamewa garin mu, masifa kullum da maganar da take jawo mana, to wlh tunda abun nata ya fara kaiwa da neman rai mai gari shine kawai zai rabamu da ita, tunda ta gagari iyayen ta.

Murmurshi Daddy yayi tare da cewa.

" Haba Mlm Usman meyayi zafi haka harda kai ƙara wajen mai gari dan Allah kayi hkr kabar maganar haka ta wuce, ƴar waye ce yarinyar?

" Ƴar waye kuwa bayan ƴar Amininka Mlm Musa, Allah saina kai su ƙara kagama tafiyata, shigewa Mlm Usman yayi, ba tare daya saurari me Daddy zaice ba.

Kallon Daddy Momy tayi, tace.

" Yanxu wannan ƴar Mlm Musa ce, Lallai toka ta haifi wuta, bayin Allah da haihuwar hatsabibiyar yarinya.

" Ya Isa haka wannan maganar A'ishah, Allah ya shirye ta ya kamata ki furta, bawai kike ambaton magana marar daɗi ba, shige mu tafi.

Komawa mota sukayi, ita dai Momy tana mamakin wai Indo ƴar Maryam ce, har suka isa gidan Innah basu sameta ba, domin kuwa tana gidan su Indo, wajen Mama, sai Daddy ne yace wata kila tana gidan rasuwar, bari naje na duba mu gani.

Zagawa ƙofar gidan su Indo daddy yayi, ya samu su Mlm Musa zaune a kofar gidan nasa su wajen huɗu, dake ana ɗan zuwa masa ta'aziya, kasancewar yau satin jummalo da Rasuwa.
Nlm Musa yaji daɗin zuwan aminin nasa, cikin murnar ganin juna sukayi musabaha, daddy ne yace.

"Musa ashe Jummalo kuma taxo ƙa'ida, Allah ya jiƙanta da rahama yasa ta huta.

" Ameen Alhaji Haruna, lokaci, yayi babu yanda muka iya, sai dai mu bita da addu'a.

Daddy ne yace.

" Naso muxo tun washe garin ranar da ka sanar dani, sai kuma Allah bai nufa ba, Innah ma naga bata cikin gidan nata.

Murmurshi Baba yayi yace.

" Ai Babu komai Haruna gaisuwa bata ruɓa, Innah tana cikin gida, mu karasa cikin gidan.

Shiga cikin gidan sukayi, suka taradda Innah da Mama, sai Goggo haule addar Mama, suna zaune, Goggo taji daɗin ganin ɗanta, bayan an gaggaisa ne, Innah take tambayar sa, Momy, sanar da ita yayi cewa ai sunxo suna gidanta, faɗa Innah tahau yi, tana cewa, meyasa basu sauƙa a nan ba, zasu shige cikin gidan ta, to maza yace su karaso nan.
Murmurshi daddy yayi kasancewar yasan halin mahaifiyar tasa, ya tashi yaje ya cika umurnin ta, tare suka dawo daddy ya zauna a wajen su Baba, tare da sawa aka sauke musu kayan Abincin daya kawo musu.

Da Sallama Momy suka shiga, amsa musu Mama tayi tare cewa.

" Barka da zuwa Hajiya A'ishah, lale maraba.

Zama Momy tayi cikin fara'a, sannan suka gaisa da Mama ta mata ta'aziya.
Maida hankalin ta, wajen Innah Momy tayi cikin darajawa ta gaisheta.

Amsawa Innah tayi tare da tambayar ta, mustapha da Habeeb.

" Innah Habeeb ya koma, London, mustapha Kuma yana inugu amma idan Allah ya kaimu gobe zaizo.

Allah ya kaimu Innah tace, sannan Momy ta gaishe da Goggo haule.

Ruwa da abinci Mama ta gabatar musu.

Ishaq kallon wani iri yake yiwa shinkafar, domin kuwa shi gaskiya ji yake bazai iya cin abincin ba, Sharifa Sharif Momy sukan duk sunci, amma ishaq yaƙi ci, Momy sarai ta gane nufin Ishaq wato dai abincin ne bai masa ba, shiyasa yaƙi yaci.

Daddy ma an fitar musu nasu abincin waje shida direban sa.

Kamar munafuka Indo ta shigo cikin gidan tana raɓe raɓe, tsawa Mama ta daka mata tace.

" Ke Indo, tsayuwar me kike anan baki ga mutane bane da bazaki gaishe suba.

Tura baki Indo tayi, sannan tace, to sannun ku ina wuni.

Tsabar haushi Momy bata amsa ba, sai Sharifa ce, ta amsa da lafiya.

Duban Indo Mama tayi tace.

" Ina sugern dana aike ki yake tun ɗazu sai yanxu kika ga damar dawowa.

Kame kame Indo ta fara cikin kuma tura baki take cewa mama.

" To ba, Garba bane, ina cikin tafiyata, ya tare Ni, yake cemin wai saina biyasa mintinsa da muka ɗaukar masa a shagon babansa, na rantse da Allah Mama ban kulasa ba, naci gaba da tafiya ta, shine fah ya jawo min rigata, nikuma shine na kamasa da faɗa bayan mun gama faɗan ne, na nemi kuɗin aiken da kika min na rasa wallahi Mama nidai banso yin faɗa ba, shine yasani.

" Innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un innalillahi wa'inna'ilaihirraji'un, nikam na shiga Uku dake Indo, yanxu kenan ban isa na aikeki ba, Indo, kullum sai kin ɓatar min da kuɗi, ki kuma jawo min magana cikin gari, da wanne kike so naji ne, da zafin mutuwar jummalo zanji koko da masifar da kike ɗauko min iy............

Dakatar da Mama Innah tayi itama cikin faɗa tana cewa.

" Ya isheki haka mairo, sai wani innalillahi kike ambata kamar wacce kika gamu da masifa, to ya isheki haka, shi garban kinsan meya mata, nawa nema kuɗin da kika aiketan ina Murtala uku ce, kike famar tada jijiyar wuya, to ahir ɗinki na kara jin kinyi magana, itace ta kashe jummalo da kike cewa da zafin me zakiji, zonan ƴar Albarka, ta kira Indo.

Tahowa Indo tayi, ta zauna kusa da Innah, tare da kwantar da kafaɗar ta, akan na Innah.

Kallon mamaki Momy suke bin Innah dashi, yanda take ta ɗaurewa karya gindi, wata irin tsanar Indo ne, ya kara ɗarsuwa a cikin Zuciyar Momy.

Mama kam ta kasa magana tsabar haushin daya isheta, danta fiskanci Innah itace take ƙara, lalata tarbiyyar Indo, gashi kuma bata isa tayi magana ba.

A gidan Innah su Momy suka kwana, da safe ma da koko da ƙosai suka karya, dole ce tasa Ishaq yaci badan yana soba.

Da sassafe Baba da Daddy suna Zaune kofar gida suna taɗin yaushe gamo, suka ga, Dogarin sarki, bayan sun gaisa ne yake sanar da Baba cewa mai gari na neman sa a fada shida Indo da misalin ƙarfe goma na safe.
Amsawa Baba yayi da to, domin kuwa yasan Indo ce, yauma ta ɗauko masa magana.

Nisawa Daddy yayi tare da fara bawa Baba lbrn Abunda ya faru jiya shigowar su garin ya ƙarasa zancen da cewa, ina ga akan maganar mai gari yake neman ku, amma bazamu yanke hukunci, ba, sai munje munji kiran shi mai garin.

" Wlh Alhaji Haruna, na gaji da yarinyar

Please Login or Register in order to submit comment