Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fahimce ni."

" Eh Mamy na gane, kuma insha Allah zanyi amfani da Wannan shawarar taki."

" Yauwa koke fah, yanxu yaushe zasu dawo daga ƙauyen?"

" Bansani ba, amma Momy tace, idan sun dawo zata kira ni."

" Shi kenan hakan ma yayi, yanxu ki tashi kije, ki ɗaura mana abinci, ni bara naje na gyara ɗakin Abban ku."

" To Mamy." RAUDA ta amsa tare da tashi tayi kitchen."

Misalin ƙarfe biyu na azahar, su Indo suka shigo cikin gidan, bayan sunyi parking ne, kowa ya fito, kalle kalle Indo take, cikin ƙauyanci, baki buɗe take kallon fulawin dake, zagaye ƙofar gidan, da gudu tayi gun fulawin tare da taɓa su, tace.

" Lah !! Innah kinga wasu Abu masu ado, Innah sun miki kyau kema, nidai aradu sun min kyau."

Duban ta, itama INNAH takai wajen, tace.

"Sunyi kyau sosai ma, ikon Allah!! Wani abu sai birni, ki duba yanda aka shuka waɗannan Adon kamar zama aka zo duniyar ba za'a mutu ba, yayi kyau."

Mustapha ne yaja suka da ƙarfi tare da hararar ta, ita kuwa Indo ko a jikin ta, bata sanma yana yiba, domin kuwa, ta bada hankalin ta, gabaki ɗaya, wajen wannan fulawin, murmurshi daddy yayi sannan yace.

" Sharifa, maza jeki ki jira Indo, idan ta gama kallon fulawin, sai ku shigo tare, Innah mu shiga cikin gida, zasu taho da sharifa."

Kallon sharifa Innah tayi tace.

" Ke Sharifa, kibi Indo a hankali, banda faɗa banda tsangwama, Wlh ko kallon banxa kika mata naji labari, hmm !sai naci ubanki."

Murmurshi sharifa tayi tace.

" To Innah naji, babu abunda zai shiga tsakanina da ƴar zinaren ki."

Shigewa Innah sukayi da Daddy suka bar Indo tsugunne gaban fulawi, tana famar tsinka.

Murmurshi, sharifa tayi ta ƙaraso gaban Indo ta sunkuya, tace.

" Wai kyau suka miki ne? naga sai tsinka kike, me zakiyi dashi?"

Washe baki Indo tayi tace.

" Zan tarasu ne, naje nata kallon su, shigen irin waɗanda nake ganine a tibin Innah, indiyawa suna bawa masoyan su, nima masoyina zan bawa."

Cikin mamaki Sharifa tace.

" Masoyinki kuma! Waye masoyinki a cikin garin nan?, naga dai baki san kowa ba, cikin garin nan, yanxu kika shigo, kodai ƙauye zaki aikawa saurayin naki?"

" Kiji ki Sharifa da wani zance wani ƙauye kuma, bayan ga nan ya Mustapha na, a cikin gida, nidai shine masoyina kuma shi zan kaiwa fulawar soyayyah."

Razana sharifa tayi, cikin zaro ido tace.

" What! Wani ya Mustapha, ya Mustapha wanda na sani, na cikin gidan nan, shine saurayin naki?"

Indo tana dariya tace.

" Eh mana shine, sai dai fah, yana da baƙin Hali, gashi da masifa, kuma aradu mungu ne, azzalumi, sai dai duk da haka ina sonsa."

Shuru sharifa tayi tare da kama baki tana mamakin rashin hankali Irin na indo, "to idan ba rashin Hankali ba, ina Indo ina ya Mustapha, lallai kam kin jawa kanki wahala wajen ya Mustapha." duk cikin ranta sharifa take wannan maganar.
Sanin rashin hankalin Indo, zata iya zuwa gaban Momy da Daddy tacewa mustapha ga fulawar soyayyah, yasa Sharifa lallaɓa indo ta hanyar cewa.

" Kinga Indo, nikam Ranar da kukayi waya da ya Habeeb, sai naji kamar kina faɗa masa cewa ya mustapha ya miki duka?"

" Eh mana yamin duka, ranar da mukayi faɗa da Garba, kai! Amma gaskiya ya Mustapha baƙin mungu ne Wlh, ya dinga dukana fa kamar ya samu jakar sa, Kuma Allah saina rama, komai daɗewa."

Dariya ce, taso ƙwacewa sharifa, sai ta ƙunshe ta, tace.

" To yanxu ke dan Allah mutumin daya miki wannan dukan ne, zaki basa fulawar soyayyah, duk yanda kike da ajin nan, aisai ya raina ki, haba ƙawata, ki kama ajin ki, dan Allah karya raina ki, kinsan me zai faru yanxu?"

" A'a ban sani ba saikin faɗa." Indo ta ƙarasa maganar tana tura baki.

" Kinga karki yadda ki basa wannan fulawar, domin idan yaga yana dukan ki, kina binsa, to wlh kullum ya dinga dukan ki, kenan yana raina ki, kinga ni kuma bana son haka ta kasance, tunda kinga yanxu kin zama ƙawata, bazan so Abunda za'a raina kiba."

Shuru Indo tayi, tana tunani, sai can ta ɗago kanta tace.

" Kuma fah haka ne, amma ai zan rama nima ba barinsa nayi ba."

" Eh ko zaki raman dai, yau Kam karki basa fulawar nan, har sai kin rama tukunna."

" Na yadda to, amma dai zan ɗauki, guda ɗaya na dinga kallo, suna min kyau ne."

" To shi kenan ɗauki mu tafi."

Ɗauka Indo tayi, sannan suka wuce cikin gidan, a falo suka taradda su Momy kowa yana zaune cikin gajiya, sai Mustapha kawai da ya haura sama, shine baya falon, ɗakin dake ƙasa a falon Daddy yace.

" Wannan ɗakin shine, wanda Innah zata zauna a cikin sa, A'ishah ku gyara ɗakin keda sharifa, ita kuma indo zata haura sama, su Zauna tare da sharifa, tunda daman bed biyu ne cikin ɗakin."

Da to Momy ta amsa, sannan ta tashi tayi, ɗakin tana cewa Sharifa ta shiga kitchen ta ɗaura musu girki.
Daddy ne, yace.

" Kubar girkin nan, kawai bari mustapha ya fito yaje ya mana ordern abinci. "

Innah ce, takai duban ta, gefen ta, sai taga wayam Babu Indo, duba tsakiyar falon tayi, nan ma wayam Babu Indo.

" Kai wai ina Indo ce, bandan ta, ba fah."

Daga bayan kujerar da Innah take suka ji Muryar Indo na cewa.

" Gani nan a bayan ki, Innah, *Wallahi sanyi nake sha Allah wannan abun ƙasan sanyi garesa, shiyasa ma na kwanta, naji sanyin da kyau, Wlh Indo ƴan birnin nan wayo suke mana, suna shan daɗi Abunsu, to Innah shi wannan wani irin suminti ne, mai kwalliya*."


Leƙa inda take maganar sukayi, tana kwance abunta ƙasan tayels sai birgima take tana taɓa shi, ita a dole tana jin sanyi.
Murmurshi daddy yayi, domin kuwa, yarinta ce tsantsa ke ɗawainiya da Indo.

" Kinga Indo taso maza karki ɗebi mura, zoki zauna nan."

Tashi tayi tana dariya ta dawo kusa da Innah tana taɓa kujera, dannawa tayi da hanunta taji hanunta ya nutse cikin, dariya tasa, tace.

" Lah ! Wallahi Innah shima laushi garesa, da ƙarfi ta faɗa kan gurar, tana famar dariya."

Ƙauyanci kala-kala Indo ta nuna sa, a falon, Momy ce ta fito daga ɗakin da Daddy yace na Innah ne, Bayan ta gama gyarasa, zuwa tayi tace.

" Innah an gama gyara ɗakin ki shiga muje, na nuna miki Bayan gida da yanda zakiyi amfani dashi."

"To Innah." tace sannan ta tashi tabi bayan Momy, itama Indo tashi tayi zata bi bayan Innah, Sharifa ta riƙo hanunta tace.

" Ki tashi muma muje namu ɗakin, tare zamuke kwana ai, muje muma muyi wanka."

Sama suka haura ita da sharifa, suna shiga ɗakin Indo ta fara kalle-kalle cikin ƙauyanci, tace.

" *Jar Uba! Chap! Lallai fah Yanxu Sharifa nan ɗakin kine duka ke ɗaya, kuma duka kayan ɗakin naki ne, harda gado biyu, duka naki ne*?"

Murmurshi sharifa tayi tace.

" Eh nawa ne duka amma akwai ƴar abokin Daddy da take zuwa ta juma a nan, tare muke kwana, so yanxu ɗakin ya zama namu mu biyu harda ke."

" *Wayyo daɗi nima zan fara kwana a gado mai laushi, to amma sharifa na tambaye ki mana*?"

" Ina jinki menene tambayar.?

" *Naji kince ƴar abokin daddy tana zuwa ta kwana, to ita ɗin bata da gidan uba ne, sai taxo nan ta kwana*."

Dariya sosai Sharifa tayi, sannan tace.

" Kinga yanxu kinga ba wannan bane a gaban mu, muje banɗaki, na wanke miki wannan gashin naki, sai kiyi brush, sannan kiyi wanka."

Taɓe bakin ta, Indo tayi sannan tabi bayan Sharifa, sosai Sharifa ta wankewa Indo gashin kanta, sunayi Indo na taɓe-taɓen kayan tollet ɗin, sannan ta bata maclean da brush tace, ta wanke haƙwaran ta, da farko Indo ƙin karɓa tayi saida suka kai ruwa rana takunna da lallashi, Sharifa ta samu ta Indo ta karɓa, tana nuna mata yanda zatayi.

" Allah Sharifa zaƙi ne, da wannan abun kamar na shanye kunfan."

" Karfa kisha Indo, datti ne, idan kuma kinsha to cikin ki zai kunbura, Babu ruwa na."


" To mema yayi zafi, bazan shaba, hanyar lafiya a bita da shekaru."

Sharifa tasa Indo ta wanke bakin ta, wajen sau biyar, sannan ya ɗan fita, soso da sabulu ta bata tace tayi wanka, sannan ta fito ta barta cikin tollet ɗin tare da bata towel tace, idan ta gama ta ɗaura.

Wanka Indo tayi tas ta fito kuma ɗaure da towel ɗin, gam a ƙirjinta, hand Drayer Sharifa ta ɗauka ta jawa Indo gashin ta, cikin minti biyar gashin ya bushe tare da laushi, mai ta bata ta shafa, sannan Sharifa ta ɗauko wata, doguwar rigar ta, wanda daman ta mata kaɗan ta, bawa Indo ta saka, tare da feshe ta, da turare, fes Indo ta fito Abunda gwanin sha'awa Babu wannan ƙazantar, hakwaren ta ma sun ɗanyi haske Babu laifi, bari Indo Sharifa tayi, wajen mirro sai kallon kanta take cikin madubi, ta shige tollet Itama.

" *Aradu kayan birni akwai kyau, cankaɗi kuga yanda wannan riga tamin kyau, shin-shina jikin ta, tayi, tace, kuma fan ƙamshi nake, kuga yanda gashi nama yayi kyau*."

Surutun ta Indo take yi har sharifa ta fito daga tollet, ta shirya suka fice zuwa fallo, da gudu Indo ta ƙarasa wajen Innah tana cewa.

" *Ya kika ganni Innah, wallahi nayi kyau, koh ban yiba Innah*."

Dariya Innah tayi tace.

" Ai kyau kamma ba'a magana, waye ya baki kaya?"

" Innah sharifa ce, ta bani, harda turare ta samin, kinga Innah harda baki na, ta goge min."

" Allah dai ya miki albarka sharifatu, kedai bakiyi baƙin halin uwarki ba."

Suna cikin zancen, mustapha ya shigo Hanun sa, ɗauke da ledar take away da Daddy ya aike sa, a tsakiyar falon ya ajiye yana cewa Innah.

" Ki dai dinga zama a hankali karki karya mana kujera, ba'a saba zama ba, anfi gane ƴar tsugunno."

" Dan ƙaniyar ka, ba'a Zauna a hankalin ba, kaji ja'iri kawai."

" Dariya Mustapha yayi tare da Zama ya ɗauki take away ɗaya, yace."

" Haura ki cewa Momy ganan take away ɗin na kawo, dan gaskiya ni yunwa nake ji, bazan iya Hkr har sai sun fito ba."

Muryar Indo sukaji tana cewa.

" *Su aci-ci kenan arnan ci, ciccika rumbu, ashe dai cikin zanine da mutum bamu sani ba*."

Zaro ido mustapha yayi yace.

" *Ke Jakar Ƙauye da wa kike*?"

Mur guɗa baki Indo tayi tace.

" *Da wanda ya tsargu nake, wanda bazai iya jira kowa ya fito aci abinci ba, dashi nake*."

Tashi mustapha yayi yawo kan Indo, a fusace,
Bayan Innah Indo tayi da gudu, tana dariya.
Har bayan Innah mustapha yawo, zai fisgo Indo yana cewa.

" Na taɓa wasa da kene, wawiya ƙaramar ƙauye."

Buge hanun mustapha Innah tayi, tace.

" Karka kuskura ka taɓa ta, ta, dan naga san baƙar muguntar ka, daman can ba ƙaunar ta, kake ba, kuma ƙarya tayi kai ɗin ba aci-cin bane."

Mustapha bai saurari Innah ba, ya finciko Indo, ɗaga hanu yayi zai sauƙe mata mari yaji Muryar Daddy yana cewa.

" Kul karka fara, me ta maka daga zuwan yarinya zaka fara dukan ta."

" Alhamdulillah! Gara da Allah ya kawo ka, to ka shiga tsakanina da wannan ɗan iskan ɗanna ka, ya fita idona dana Indo, karya kuskura ya samin yarinya a gaba."


Murmurshi daddy yayi yace.

" Muhammad ka daina saurin hanu, fah, idan ta maka laifi ka fara mata faɗa kamin duka, kaji koh."

" Naji Daddy" mustapha ya furta, cikin takaici ya haura sama, da kuma haushin Innah.

MOMY tana sauƙowa tana waya.

" Eh Hajiya Turai, mun dawo ɗazu, na nemi number RAUDA switch Off, so ki sanar mata cewa, mun dawo, zansa driver yazo ya ɗauke ta, da daddare idan Allah ya kaimu."

Sallama naji Momy tayi, sannan ta katse kiran, zama Momy tayi ta buɗe ledar take away d'in, plet tasa Sharifa ta ɗauko, ta sawa kowa ta basa, jalop ɗin shinkafa ce, taji vegetables, da kuma rabin kaza a kanta, loma ɗaya Innah ta kai bakin ta, ta tofar tana cewa.

" Wlh bazan ci Abincin nan, bai min ba, aje a nemo min tuwo duk inda yake, shi zanci."

Da sauri Momy ta ɗago ta kalli Innah, sai kuma tace.

" To Innah, bari na tashi na tuƙa miki tuwon yanxu."

Indo kuwa cin abincin ta, take Hankali kwance tana ƙutsurar kaza, tace.

" *Amma dai Innah baki san daɗi ba, yanxu ga wannan me zakiyi da tuwo, Wlh Momy karki mata tuwo wahalar dake zatayi, idan baza taci wannan din ba, ku barta ta kwana da yunwa*."


Zaro ido Daddy yayi yace.............




Wayyo Allah typing wahala.


*Vote*
*Share*
*And*
*Comments*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*

*(Ummu Nasmah ce)*
[2/9, 12:39 PM] Ummu Nasmah: 💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻

*I͓̽N͓̽D͓̽O͓̽ A͓̽ B͓̽I͓̽R͓̽N͓̽I͓̽*
💅🏻💅🏻💅🏻💅🏻


*Na*

*r̸a̸s̸h̸e̸e̸d̸a̸t̸ u̸s̸m̸a̸n̸*

*(մʍʍմ ηαςʍα)*



👸🏻 *mᎪKᎪmᎪᏒ ᏦᎪᎥᏁuᎳᎪ*👸🏻


*Marubuciyar*

*Sauyin Rayuwa*
*Nasmah ko Nasirah*
*Sara da Sassaka*


*D̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞i̸͟͞c̸͟͞a̸͟͞t̸͟͞e̸͟͞d̸͟͞ t̸͟͞o̸͟͞*

*Aunty fauza ƴar Amana*

Uwa mabada Mama ƙaunar ki daban take gareni domin keɗin shugaba ce dake Adalci ga duk na ƙasa dake.
Allah yabar ƙauna.


*S͢p͢e͢c͢i͢a͢l͢ G͢i͢f͢t͢ t͢o͢*

*Aunty Hauwa Maman Uswan*

Ina roƙar Ubangiji daya Albarkaci Rayuwar zuri'ar ki baki ɗaya 🙏🏻



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*



*Ina ku ke masoyan wannan shaharariyar ƙungiyar mai tarin Albarka, wace taga jiya taga yau, mai shirin ganin gobe da yardar Ubangiji, watau 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION dake group ɗin WOMEN24 TV WHATSAPP GROUP, kamar yanda a komai namu ku ke bamu goyan baya, yanzun ma muna neman wanan goyan bayan na ku wajan ganin kun zaɓi wanan kungiyar taku mai tarin Albarka a wannan gasar da za'ayi ta gaba ɗaya ƙungiyoyin social media,wanan gasar a group ɗin WOMEN24 TV WHATSAPP GROUP kaɗai za'ayi kamar yanda kuke sonmu da ƙaunar mu, yanzu ma ta hanyar zaɓen mu ne za mu gane wannan amanar da ke tsakaninmu tana nan har yanzun, wanda mun San ku masoyyanmu ne na haƙiƙa ba za ku bamu kunya ba, za mu ci gaba da suburbuɗo muku book ɗinmu kyauta kamar yanda aka saba mu dai fatanmu ku zaɓe mu, Allah ya bar so da ƙaunar da ke tsakaninmu.*



*Nasan akwai wnda za su ce basa group din WOMAN24 TV WHATSAPP GROUP ai da mun zaɓeku, tau ƴar uwa ga dama ta samu in kina son ki shiga wanan group don zaɓen wanan kungiya ta 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION ko bayan an gama zaɓe ki ci gaba da moriyar wanan group din a kan 200 kacal👌🏿ga yanda abin yake*👇🏻





*INA KUKE MASOYA LITATAFAN 🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION YAU ALLAH YA KAWOMU YANDA ZA KU NUNA MANA SOYAYYAR DA KUKE MANA NAKA SAI NAKA DADIN ZAMA SAI BARE MUNA MAI FARIN CINKIN SANAR DAKU CEWA MUN SHIGA GASAR WOMEN24 TV WHATSAPP MUNA NEMAN GOYAN BAYANKU DAN GANIN ALLAH YA TAIMAKA MUN LASHE WANAN GASAR AMAN SAI DA GOYAN BAYAN,KU WAJAN ZABAR WANAN KUNGIYAR TAKU MAI ALBARKA SAI MUN JIKU ONE LOVE MY LOVELY SISTER'S*😍


Kusan cewa kungiyarmu *🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* sun cikin gangarimin gasar da award Wanda *women24 TV WhatsApp group* zasu gudanar

Awannan gasar ne za'asamu ƙungiyar da tafi kowacce ƙungiya yawan fans da Kuma bin ka'idan rubutu

Dan kisamu damar zabar kungiyarmu *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* za ki tuntuɓi wannan numban 09030159301 Dan su sakaki a *WOMEN24 TV WHATSAPP GROUP* ananne za'ayi zaɓen ƙungiyar da tafi kowacce ƙungiya yawan mabiya ita zata lashe wanan gasar.

*Women24 Tv*

Ba zaɓe kaɗai za kiyi ba,

za ki ƙaru da abubuwa da yawa Kamar haka

*Yanda ake girke-girke,*
*yanda za ki gyara jikinki,*
*yanda za kiyi makeup,*
*yanda za ki ɗaura ɗan kwali.*

Kuma suna shirye-shiryen nan na *arewa24 tv* kamar su

*TARKON ƘAUNA,*
*DAƊIN KOWA,*
*KWANA CHASA'IN,*
*JAMAI RAJA,*
*SAPNE SUHANE,*
*GIDAN BADAMASI,*
*RUƊIN ZUCIYA,*
*BAGHYA LAKSHMI,*
*AKUSHI DA RUFI,*
*AUDIO NOVEL,*
*HAUSA NOVELS.*

Kada kimanta da ranan zaɓe in kin shiga group ɗin ki zaɓi *🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* tananne za ku iya nuna mana irin son da kukema ƙungiyarmu da littattafanmu.



Karku manta fa masoyanmu idan kun zaɓi labarinmu za kuyi comments ne, wannan shi ne zai nuna mana cikakkiyar ƙaunar da kuke mana, *Mun gode, Mun gode.*


Allah yabar Ƙauna da zumunci.

*P*••••••3️⃣9️⃣ ➡️ 4️⃣0️⃣

" Ƙa niyar ki A'ishatu Innan ne za'a ƙyale Saboda ke kin samu kin cika cikin ki ko."

Tura bakin ta Indo tayi tace.

" To Daddy ita Inna ga abinci mai daɗi sai tace sai tuwo, kullum shi take ci a cikin garin mu, Allah ke Inna ƴar ƙauye ne."

Dariya Daddy yayi sosai yace.

" To A'ishatu da ɗin innan ƴar ina ne? idan ba ƙauye ba, dukan mu, ai ƴan ƙauye ne, har ke ma."

" Chap! Nidai Daddy, yanxu ba ƴar ƙauye bace aradu, dane nake ƴar ƙauye, amma yanzu ni ƴar Birni ne."

Dariya Daddy yayi yana kallon inna yace.

" To inna kinji Abunda ƴar jikarki ke furtawa, wai ita ba ƴar ƙauye bane."

Murmurshi Inna tayi tace.

" Rabu da ita ja'ira tunda ita ta koshi ai kowa ma ya kwana da yunwa bai dameta ba, indai Indo ce, ƙauye kuma shine gatan ki, Birnin dai a sama kika tsince sa."


Ita dai Momy bata ce komai ba, a cikin zancen su, sai ma hararar Indo, da take yi ƙasa-ƙasa, tashi tayi, ta shiga cikin kitchen, ta kama aikin tuwo, domin kuwa ta ƙudurta cikin ranta cewa (idan tayi tuwon nan shine za'a ci har dare bazata sake wani girkin ba).

Sharifa ce ta dubi Daddy tace.

" Daddy ka bamu kuɗi muje kasuwa, mu sayawa Indo kaya? tunda kaga bata da wasu kaya masu kyau."

Murmurshi Daddy ya sake yana kallon sharifa, yace.

" Babu damuwa wannan ai magana mai ƙyau kikayi, (ATM CARD ɗin sa Daddy ya ciro ya miƙawa Sharifa) gashi kije ku sayi Abunda ya kamata, sai ki dawo min da ATM card ɗin, Inna kuma idan na fita kasuwa gobe zan dawo mata da Atampopi zuwa less sai a nemi mai ɗinka musu har ita ma Indo zan kawo mata, koda yake, kinga bani ATM card ɗin nan, ku bari sai gobe da safe kuje yanxu bazai yiwu ba, dare yayi."

Godiya Sharifa ta yiwa Daddy tare da miƙa masa ATM card din sannan ta taɓa Indo, murya ƙasa-ƙasa tace.

" Ki cewa Daddy kin gode mana."

" Daddy na gode, Daddy za'a saya min harda, Irin wannan rigar da sharifa ta bani? wlh Daddy gare ta Daddy."

" Murmurshi daddy yayi yace.

" Komai kike so za'a saya miki Indo, duk abunda kike so ki sanar dani ko MOMYN Ku zamu baki in sha Allah."

Tsalle Indo tayi tana murna tana cewa.

" Yauwa! Daddyn mu, godiya nake dubu dubu, yanzu Daddy komai nake so zaka bani da gaske?"

Kaɗa kansa Daddy yayi yace.

" Eh mana zan baki komai kike so, indai baifi ƙarfi na ba."

Tashi Sharifa tayi ta kama hanun Indo tace.

" Tashi muje ɗaki na kira miki ya Habeeb."

Tashi Indo tayi tana dariya tabi bayan Sharifa, a ɗakin zama sukayi saman bed Sharifa ta dannawa Habeeb kira, a lokacin da sharifa ta kira Habeeb yana zaune bedroom ɗin sa, ya gama haɗa kayan sa, zai dawo gida Nigeria gobe, katse kiran Sharifa yayi sannan ya kira, ɗauka Sharifa tayi tare da cewa.

"Barka ya Habeeb, ya London?"

"Alhamdulillah! London gamu cikin ta, gobe ma nake son dawowa, da naso na shige Egypt wajen Aunty Hindu, to kuma ina tunanin hakan bazai samu ba, daman *HASINA* zan bi mu taho tare, amma munyi waya kawai zata taho jibi."

" Wow! Yaya kace muna da babbar baƙuwa, wlh ya Habeeb naji daɗin wannan Albishir ɗin, Aunty HASINA zata zota."

" To iya gama uwar ƴan son baƙi, ki jirata tana hanya jibi."

Dariya sharifa tayi tace.

" Ya Habeeb ai baƙo abun sone Wlh, yauwa Ya ganan Indo tace na bata za kuyi magana."

Cikin mamaki Habeeb yace.

" Indo Kuma! naji kamar Mustafa yace min kun dawo daga ƙauye, ko ke an barki a ƙauye ne?"

Dariya sharifa tayi tace.

" Ni dai ya Habeeb ina cikin dutse, a shango Estate, dan haka ga Indo ka tambaye ta, meya kawo ta, cikin dutse?"
Miƙawa Indo wayar Sharifa tayi tana dariya.


" Hello ya Habibu, shine ina ranar ka kashe wayar ka, bamu gama magana ba ko?"

Murmurshi mai sauti Habeeb yayi yace.

" Haba Mama na, ni na isa na kashewa uwata waya, kawai dai network ne ya katse ranar, ya akayi na jiki cikin gidan mu?"

Dariya Indo tayi tana cewa.

"Ai ya Habibu na dawo birni nima da zama, Daddy ya ɗauko mu, nida Inna yace muma mun dawo nan da zama, yace nima na zama ƴarsa, kuma yace komai zai dinga bani."

" Masha Allah! Congratulation! To fa, yau kuma ga *INDO A BIRNI* kice ƙawata ta dawo gidan mu da zama, gaskiya naji daɗin wannan lamarin, sosai, to nima Albishir."

Dariya Indo ta tuntsire dashi har tana kwanciya saman gado tace.

" Goro fari tas ya Habibu na."


" In sha Allah gobe ina hanya nima zan dawo musha hirar yaushe gamo, nasha labari."

Dariya tayi tace.

" Ai ya Habibu ba labari bama labarai zaka sha, Allah akwai labarai kala-kala."

Murmurshi Habeeb yayi yace.

" Kice na kwanke kunne na, domin naji daɗin jin labarai."

Murmurshi sharifa tayi tana mamaki yaushe ya Habeeb sukayi sabo da Indo haka.

Indo sun daɗe suna hira da Habeeb, sanda aka fara kiran sallah magrib sannan Sharifa karɓe wayar, saka Indo a gaba Sharifa tayi saida sukayi sallah tare, da daddare, bayan sun gama cin abinci, Momy ta dubi Mustafa tace.

" Mustafa ka tashi kaje ka ɗauko min RAUDA a can gidan su, yanxu ta kira ni, tana jiran azo a ɗauke ta."

" Momy ina driver gidan su? da dole saini zanje na ɗauko ta, gaskiya Momy ta biyo driver gidan su, ya kawota."

" Kai Mustafa! ina cewa kaje ka ɗauko ta, kana cemin drivern gidan su ya ɗauko ta, nasan da drivern gidan nasu ai nace kai kaje ka ɗauko ta, ka tashi kaje ka ɗauko min ita kafin ranka ya ɓaci."

Inna ce, ta dube sa, tace.

" Muhammadu kaji tsoron Allah ka daina yiwa uwar ka, jayayya idan iyaye sun bada umarni bi ake, sai a samu albarka ko baka so ka tashi kaje maza."

Harara Mustafa ya dakawa Inna yace.

" Ke kuma yaushe kika fara wa'azi? daman kin iya wa'azin ne, kika bar wannan yarinyar ta lalace."

Baki Indo ta murguɗawa Mustafa, tana juya masa Indo tace.

" Ni dai ba lalacacciya bace ehe, sai dai idan mutum shine lalacacce."


Kallon Indo Mustafa yayi yana huci yace.

" Da wa kike wannan maganar?"

Murguɗa masa baki ta ƙara yi, tsawa ya daka mata yace.

" Nace da Uban wa kike wannan maganar."


Ƙara murguɗa masa baki tayi tace.

" Da *Uban wanda ya tsargu nake*."

Zaro ido Momy tayi tana kallon Indo cikin tsana.

Wo ho ho yau dai ran maza ya ɓaci, cikin ɓacin rai Mustafa yake takawa gaban Indo kamar wani zaki yaga nama, ita kuwa Indo tana maƙale jikin Inna ko a jikin ta, da ƙarfi! Ya fisgo ta, a

Please Login or Register in order to submit comment