Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kusa da ita yakan ji wani irin yanayi haka zai kasance yana tunanin ta, soyayyar ta kuwa kullum ƙara ƙarfi take cikin zuciyarsa, amma da zarar sun haɗu kuma sai faɗa ne zai biyo baya, haka kuma a wajen Indo duk sanda ta haɗa ido da Mustafa takan jin gabanta ya faɗi ko da kuskure ya riƙe hanunta sai taji wani shirking a jikinta.

🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌🕌

Yau ta kasance juma'a haji babbar rana, Mustafa da Habeeb daga masallaci gidan su suka wuce kasancewar yau ne ranar da zasuyi Family meeting, sun sami kowa ya hallara wajen har Daddy da su RAUDA Hasina Sharifa hatta autan momy ba'a barsu a baya ba, Indo KUWA tana maƙale gefen Aunty Hindu, bayan gaisuwa Daddy yasa Mustafa ya buɗe taron da addu'a kafin Daddy Yayi gyaran murya tare da cewa.

"Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah daya tara waje ɗaya, dukanku nan kunsan wacce ta tara mu a wajen nan, sai dai babu wanda yasan dalilin ta na haɗamu wannan waje, Hindatu muna sauraronki ki sanar damu dalilin ki na haɗamu a wajen nan"

Gyaran murya Aunty Hindu tayi kafin ta fara magana.

" Yaya ba wani abu yasa nace a haɗa wannan family waje ɗaya ba, sai dan wata alfarma da muke nema gareku, nida mijina mun zauna mun tattauna akan wannan baiwar Allah wato Indo, SAKAMAKON komawar mu Egypt daya taso yasa muka yanke shawarar cewa mai zai hana a bamu Indo mu tafi da ita idan yaso sai mu jona mata University ɗin ta acan ta cigaba, tunda kaga yanzu babu kowa gaban mu, zamuji daɗi idan muna kallonta gaban mu."

Shuru Daddy Yayi yana tunanin wannan alfarmar Aunty Hindu, domin kuwa shi yafi so Indo ta zauna a ƙasar ta haihuwa, kuma gabansa ko yanzu ma daya bari Indo take Zaune gaban Aunty Hindu Saboda cika wasiyyar Inna na cewa abar Indo ta zauna gaban Hindu har lokacin da zafin mutuwar ta ya kau mata, ɗago kansa Daddy Yayi ya dubi Aunty Hindu Yace.

" Shikenan maganar koko akwai wata idan akwai wata ki faɗa kafin na amsa miki su duka."

Tunda aka fara maganar Dukansu suka nutsu suna sauraron Aunty Hindu da Daddy, duk da shi Mustafa bai ji daɗin maganar Aunty Hindu na cewa zata koma da Indo Egypt, Yayi shuru ne kawai yana jiran yaji amsar da Daddy zai bata, Aunty Hindu ce tace.

" Magana ta biyu itace akan *BARRISTER UMAR JIJJI* Yaya mun tattauna da Barrister sosai ga lamarin Indo a Inda yake sanar dani cewa yana sonta, zai kuma nemi Soyayyar ta, idan harta amince masa, zai turo iyayen sa su nema masa aurenta, kuma gaskiya yaya naji daɗin hakan domin kuwa Barrister Umar mutumin kirki ne kuma ina da kyau tabbacin cewa idan har Indo ta auresa zataji daɗi ta kuma samu nutsuwa, sai dai na sanar dashi cewa ya turo iyayan nasa kawai gareka domin na fiskanci akwai Soyayya tsakanin su idan ka nutsu kayi duba ga shaƙuwar da take tsakanin su, kaga idan an basa zata cigaba da karatun ta harta gama kafin ayi Maganar Aure Allah yasa banyi kuskure ba"

Gabaki ɗayan su ukun a firgice suka juyo suke kallon Aunty Hindu, mussaman Indo da bata san wata soyayya dake tsakanin ta da BARRISTER UMAR ba da har ake mata Maganar Aure, Habeeb kuwa wani irin maƙoƙon ɗaci ya haɗiye cikin wuyansa yana jin wata munguwar tsanar Barrister Umar, Mustafa Sarkin rashin haƙuri, tashi yayi tsaye idanunsa rufe domin kuwa baya kallon gabansa Magana ya fara cikin ɓacin rai da kaushin murya.

" AUNTY Hindu Babu soyayya tsakanin UMAR JIJJI da Indo ki sanar dashi cewa ya fita rayuwarta domin kuwa bata dace dashi ba, kuma nima zan sanar dashi, idan kuma yaƙi ta lallami to kuwa zaiji ta tsiya wlh."

Gabaki ɗayan su wajen tsayawa sukayi suna kallon Mustafa cikin mamakin kalaman sa, Aunty Hindu ce tace.


" Meye ya haramta Soyayya tsakanin Umar JIJJI abokin ka da Indo, tunda bata dace dashi ba, dawa ta *DACE* sanar dani?


Babu shakka cikin Zuciyar Mustafa domin kuwa a yanzu ya shirya bayyana sirrin Zuciyar sa, Saboda yaga wankin hula na ƙoƙarin kaisa dare gara kawai ya faɗa a wuce wajen.

" *Nine Wanda na dace da Indo ba Umar ba, nine Wanda na juma ina ajiyar Soyayyar ta cikin zuciyata tun kafin takai ga wannan matakin, Aunty Hindu SHATUU BUGUN NUMFASHI NANE INA SONTA FIYE DA YANDA NAKE SON KAINA HAKA KUMA INA DA TABBACIN CEWA ITAMA TANA SONA TUN ƘARAMAR TA* wannan shine hujja ta."

A matukar razane Habeeb ya miƙe Indo RAUDA suna masa wani irin kallo na ka haukace ne, RAUDA kuwa wani jirine yake neman yardar ita, saurin komawa tayi ta dafe kanta, jan hanun Indo Habeeb yayi har gaban Mustafa yace.

" Kasan me kake cewa kuwa, ko ka manta waye kake zancen cewa kana so, *INDO CE FA WANNAN ƘAZAMAR ƘAUYEN WACCE KAKE KIRA DA ALJANA WACCE KAKE CEWA ALLAH YA SAUWAƘE KA SOTA, WACCE KAKE ƘYAMAR TA, ITACE YANZU ZAKA DAWO KACE KANA SO*........


MURYAR Momy Habeeb yaji ta katse sa ta hanyar cewa.

" Ka rufe Min baki haka Babu wata Soyayyar tsakanin *GUDAN JININA DA WANNAN TAMBAƊAƊƊIYAR ƘAUYEN WACCE TA FITINI GARIN SU TA FITINI IYAYEN TA, TA GAGARESU SUKA HAƊO MU DA ITA BABU JININI BABU ITA,* koda wasa Mustafa karna ƙara ji ka ambaci kalmar soyayya tsakanin da wannan abar ƙyamar." Ta ƙarasa maganar tana huci.

Runtse idonsa Mustafa Yayi yana jin zafin kalaman Momy, amma sai dai duk abunda zai faru bazai taɓa rabuwa da Indo ba komai tsanani komai wahala, duban Momy Habeeb yayi tare da cewa.

" Momy ba cewa zakiyi Babu junin ki babu Indo cewa zakiyi babu Mustafa babu Indo domin kuwa shi Mustafa yana Auren ƴar gwal ɗinki bazaki so a mata kishiya ba, Momy jininki yana tare da Indo kuma bana tunanin zai iya rayuwa ba tare da ita ba, ki janye kalamanki Momy pls."

INDO dake sandare tana sauraron sune ta juya a guje ta fice daga gidan cikin matsanancin kuka, Daddy kuwa gyaran murya yayi tare da cewa kowa ya shiga hankalinsa ya nemi waje ya zauna.


________________________________________

Kash mai karatu anan na kawo ƙarshen wannan littafin kashi na farko, sai mu tara daku a kashi na biyu mai taken *SO BAI SAN JINI BA* cigaban *INDO A BIRNI* domin jin yanda zata kasance nanda wasu ƴan kwanaki, akwai tambayoyi kashi kashi da kuke buƙatar amsar su, wanda dole sai kun kasance dani cikin *SO BAI SAN JINI BA* anan ne zaku samu amsar ku.

1 shin Indo zata so Mustafa kuwa harta yarda ta auresa, duk da ɓakar ƙiyayyar daya nuna mata a baya?

2 shin Habeeb yana nasarar samun soyayyar Indo kuwa, gashi dai ya mata Hallaci cikin Rayuwar ta, shin zata duba wannan hallacin ta amshi soyayyar sa?

3 shin Indo zata amince da Soyayyar Barrister Umar kuwa idan har ta amince da Soyayyar sa ya Rayuwar Mustafa da Habeeb zata kasance?


4 gefe ɗaya kuma ga Momy, shin Momy zata yarda ɗanta ya auri Indo KUWA?

6 shin Daddy zai amince da komawar Indo Egypt kuwa idan ya amince ya rayuwarta zata kasance a Egypt?

Shin wake nasarar samun Indo?

Kudai ku biyoni cikin BOOK 2 SO BAI SAN JINI BA CIGABAN INDO A BIRNI DOMIN JIN YADDA ZATA KASANCE. Duk wanda yaji ance SO BAI SAN JINI BA yasan dole Akwai gurmi.

Kafin na shiga BOOK 2 ina son ku sanar dani me kuka fahimta game da wannan littafin, wani irin saƙone yake ciki, jin ra'ayin ku shine zaisa na samu ƙarfin gwiwwar cigaba da Wannan book ɗin sai naji daga gare ku.


Karku manta taken sa *SO BAI SAN JINI BA*


*Vote*
*Share*
*And*
*Comment*


*Alƙalamin Rasheedat Usman✍🏻*



*(Ummu Nasmah ce)*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment