Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

 YA ZA A YI?
BOOK1
NA KUDI NE LITTAFIN
MASU BUKATAR COMPLETED GA NUNBAR WAYA TA
WhatsApp kawai ban da kiran waya
08089965176
07084653262
BINTA UMAR ABBALE

KUSKURE NE MAI GIRMA A DORA MINI LITTAFINA A WATA TASHAR, KO KUMA A KAI FCEBOK KO WATA MANHAJAR BA TARE DA IZININA BA, WANDA YA AIKATA HAKAN NA BAR SHI DA ALLAH MUTUKAR INA DA HAKKI SAI ALLAH YA SAKA MINI.

1
Tunda na ji Tokar na maganar dawowarsa gida nayi saranda! na riga na san kuma shikkenan ni da samun walwala da farinciki har sai ya tafi ban san me yasa ya tsane ni ba, shiyasa nima kwata-kwata bana 'kaunarsa duk da kasancewar mu 'yan uwan juna na jini, amma tsakanin mu, kamar Annabi da kafiri! bama jituwa kuma duk lokacin da za mu had'u wani guri sai mun yi rikici! kamar masu ya'ki! Ya zage ni Ya ci mutuncina watarana ya kai hannu ya dake ni duk da karfin ba daya bane amma ina kokarin ramawa domin ba na iya hakuri da cizo da yakushi nake kwatar kaina na yi ta kuka ina zaginsa, aikuwa ya sha zubar mini da jinin bakina domin har ha'kora biyu ya fitar mini inda Allah yasa na gefe da gefe ne wannan dalilin yasa na ke bala'in jin haushinsa kuma har yanzu ina kan bakana sai na salwantar masa da wani sashi na jikinsa kamar yanda yasa nayi asarar ha'kora na biyu.

Zaune kawai nake ina tufka da warwara! ta rarrafo tsakar gidan ta fito tana surutai kamar koda yaushe bakinta baya shiru ita kad'ai magana take, idan ba haka ba kuma za ka same ta tana taune-taune! koda kuwa babu komai a bakinta.

Kallonta nayi na sha kunu! domin na riga na san irin soyayyar da take tsakaninta dashi, na san yanzu za ta zo mini da son zuciya to ba zan lamunta ba.

Tasa hannu ta shafa yamulallan gashinta da gabad'aya yake dabaibaye da furfura! ya cukurkud'e! kamar audiga kuma iya tsakiyar kan ne kawai ke da gashi amma gefe da gefe da k'eyar duk sumul kamar ba a ta'ba tsirar gashi a gurin ba, amma saboda fitina irin tata duk sati sai ta sanya ni nayi mata tsifa na wanke mata kan sa'an nan nayi mata sabon kitso.

Ta kalle ni da cewa" Ma'kiyin ki zai dawo shine ki ka fito tsakar gida ki ka zauna kina k'unci! wai ke Jamila yaushe za ki daina nunawa d'an uwanki kiyy.....Katse ta nayi ta hanyar daga mata hannu da cewa; Kin ga Tokar don Allah ki rabu da ni da maganar wannan d'andaban! ni ina ruwana da dawowarsa, abinda na sani shine yana shiga harkata zan keta masa rashin mutunci, domin wallahi na daina raga masa."

Ta ja tsaki tare da sa tsinke tana sakace ramuka da kugunan ha'koranta! aikinta kenan sakace! ta ce" To ai ga ki gashi nan ai, tunda kina ganin za ki iya gwada kwanji dashi."

Zuciyata tayi zafi ruwan hawaye ya ciko idona! na ce" Tokar ban san me yasa ki ke fifita Bahago a kaina ba, alhalin duk ke ki ka haifi iyayenmu! a gabanki fa ya zubar mini da hak'ora har biyu, amma baku d'auki mataki ba, babarsa ma har yanzu ba tace komai ba, kodan
mahaifina yana da kawaici da hakuri ya yi muku shiru shiyasa kuke nuna mana wariyar launan fata! Tokar na jima fa da gane ba kya kaunata saboda ba kya son mahaifiyata duk da irin dawainiya da kaunar Babana yake nuna miki."
Ina maganar hawaye na gararanba a saman fuskata! na cigaba da cewa" Idan na yi magana ko na nemi k'watar ha'kkina a ce bani da kunya! bani da tarbiya wai shin ya kuke so na yi da rayuwata ne? Tokar ina k'ara fad'a miki wallahi ku ja masa kunne babu ruwansa da ni, ba zan shiga harkasa ba to nima kada ya shiga tawa, idan ya yi mini akuyanci! nima zan nuna masa zara! domin nima na iya ta'addacin sai dai ayi mutuwar kasko tsakanina dashi!

Hankalinta a kwance take kallona tare da cigaba da tsokane! dadashinta da tsinke dake hannunta alhalin duka ha'koran dake bakinta sun zube bai fi biyar suka rage ba, amma kullum cikin sakace! su take! duk sun yi jajawur! da ti'kar! goro!

Ganin ta tsira mini ido tana kallona yasa na yun'kura domin barin gurin zuciyata kamar ta tsage! saboda 'bacin rai! kafin na kai ga shiga d'akin Kawu Sammani ya shigo gidan dawowarsa kenan daga kasuwa da hannunsa rike da leda mai zane! kawai sai ji nayi ta fashe! da kuka! da cewa" Jamila na gaji da wannan rashin arzikin naki kawai kin tasa ni a gaba kina zazzaga mini rashin mutunci! kina so ki kashe ni to ta Allah ba taki ba ehe! ba zan mutu ba sai kwana na ya 'kare." Ta kai k'arshen maganar tana goge majinar da ta ziraro mata da hannunta.

Ban damu da maganarta ba domin na san za tayi abinda ya fi haka saboda ganin d'anta ya shigo gidan ta ke wannan maganganun shiyasa kullum gidan yake a rikice! domin ita da kanta take haddasa rigimar ta haifi iyayenmu su uku amma ta ware wad'anda take so a cikinsu kuma tana fifita 'ya'yansu ciki kuwa har da Bahago wanda take ji dashi kamar ta d'auke shi ta goya.

Kawu Sammani ya san halin mahaifiyarsa sai kawai ya girgiza kansa ya kalle ni a lokacin da nake tsaye a jikin bango ina jiran hukuncin da zai yanke, Cikin lumana ya ce." Me ki ka yi mata?"
A sanyaye na ce." Ban yi mata komai ba."
Ta ce." Don Ubanki 'karya nayi miki kenan?"

Shiru nai domin bana so maganar ta yi tsayi!
Ya kalleta a lokacin da take kumfar baki da balolo'ko! duk akan Bahago! Ya ce." Tokar ya isa haka kiyi hakuri ki bar maganar haka, in sha Allah idan ya dawo zan zaunar dasu nayi musu sulhu."

Ta ce." Ai ko ka zaunar dasu wannan mai 'kirar samudawan ba zata saurareka ba domin bakar zuciya ce da ita kamar kafira! idan ba mugun hali ba, ina ita ina yin gaba da wanda ke fita ruwa! da iska! ya nemo mata abinda zata ci, amma har tana kiransa da d'andaba! wannan kalamar ta yi mini ciwo mutuk'a." Ta kai k'arshen maganar tana sake goge majinar da take tsiyaya dakalin hancinta, tafi sati biyu tana mura amma ta'ki shan magani! kuma ta'ki daina kwanciya a farin wata. haka 'ya'yanta suke fama da ita domin muguwar rikitacciya ce, to dukkaninsu lallabata suke domin su rabu lafiya.

Shi dai Kawu Sammani bai ce komai ba ya ajiye mata ledar lemo da ayaba wanda ya siyo mata ya nufi 'bangaransa yana mamakin rikici irin na mahaifiyarsu, haka suke fama da ita kullum ta Allah, burinsu dai suga sun rabu lafiya.

Kallonta nayi tana ta sosa hancinta nan ta janyo wani tasono mai had'e da majina ta lakace! a jikin bango! sannan ta janyo ledar lemon ta d'auko d'aya da ayaba ta bani. Girgiza kaina nayi tare da yatsine fuskata! can 'kasan ma'koshi na ce" Tokar ai ni tuntuni nayi sallama da cin abincin hannunki ko wani naga zakiyi wa kyauta mutukar ina gurin sai na hana shi kar'ba! ace mutum kullum hannunsa a cikin hanci! bayan haka kuma idan tayi bayan gida (kashi) sai tace sai tayi tsarki! da kanta gashi ba wani iyawa tayi ba hannunta duk yayi jirwaye! idan nazo zanyi mata tace bata so Allah ya suturta ban isa naga tsaraicinta ba. haka surukanta suke fama da ita da 'kyar take bari suyi mata wanka! amma kafin hakan akan d'auki sati biyu zuwa uku. sai dai kuma tana da k'ok'arin ibadah! lokacin sallah yanayi zata ja jikinta ta dauro alwala! amma bata bambace! gabas ko'ina kallo take, idan anyi mata magana sai tace ai ko'ina da Allah!
Kallona tayi da fadin." Me ki ka ce?" Da sauri na girgiza kaina " Ban ce komai ba kisha kayanki na gode."
Bakinta ta ta'be da fad'in."Kinyi wa kanki mai ba'kar zuciyar tsiy." Ba tare da nace mata komai ba na dauki buta na shiga band'aki domin gabatar da uzurin da yake damuna.

Koda na fito daga band'akin sai na riski Baba Iyami ta kawo mana abinci a cikin langa mai murfi, dama ita ke bamu na dare Baba Hama matar Kawu Sammani ta bamu na rana. da safe kuma babana ke bamu kudin kunu da kosai, ko kuma idan ya fita gurin sana'arsa ya aiko mana da shayi da biredi har da wainar 'kwai! tunda sana'arsa kenan!

"Ke kuwa Iyami wace irin mugunta ce wannan da zaki bamu dambu! da daddare! gashi babu wani wadataccen ganye da mangyad'a! an baki kudin cefane kinyi abinda ki ka saba."
Tana maganar tana jujjuya dambun kamar zata zubar dashi.

Baba Iyami ranta ya 'baci amma sai ta danne! ba tace komai ba ta kama hanyar gurinta. sai ta d'aga muryarta da cewa" D'anjuma yana samun kudi aure zai yi domin dai ke ba matar rufin asiri bace."
Ni kaina sai da maganar ta bani haushi kawai na bar alwalar da nake na tsaya ina kallonta raina a 'bace!

Iyami ta ce." Tokar idan Danjuma ya yi aure sai me? don Allah ki aura masa mata dubu bai dame ni ba, nifa saboda 'ya'ya nake zaune a gidan nan amma da ban ajiye kowa ba wallahi da tuni nasan inda dare ya yi mini me za a yi da irin wannan auran."

Baki idan yasan abinda zai fada bai san abinda za a mayar masa ba. Tokar ta ji zafin maganganun Iyami! kuka take wurjajan! tana tsitstsine mata wai ta tozartata!

Na ce" Baba Iyami don Allah kiyi hakuri ki tafi gurinki kin dai san halinta zaku iya kwana kuna mayar da magana hakan bai dame ta ba, duk ta watsa zuriarta bata sani ba.

Cikin rawar murya ta ce." Jamila gajiya nayi da cin mutunci wallahi! haba ai ba Danjuma ne autan maza ba, zan iya karkad'e yara na tafi gidanmu tunda nima ba daga sama na fad'o ba." Na ce." Ki dai yi hakuri kada ki sake tanka mata"

Ba ta sake magana ba ta nufi sashenta. ni kuma na d'auki butar domin d'aura alwala kamar yanda nayi niyya. sai na ji tana fadin" Jamila yanzu kina jin Iyami na zagi na tana watsa mini zuria shine ki ke bata ha'kuri! dake za a had'a baki a ci mutuncina ko? dama ai na jima ina kokwanto a kanki domin wannan uwar taki sai da ta gama tallace-tallacen ta sannan 'Danlami ya auro ta, in banda masifa da 'kaddara ina fillo da hada jinsi da wani yare irin bayerabe! ai tunda ki kayi haka na tabbatar da cewa; ke din ba jinina bace."
Ban ce mata komai ba har ta 'karaci! ci mini mutunci tayi shiru! nazo na wuce ta na shiga d'aki na d'auko dadduma da hijab na fito, gefe guda na shimfid'a a nutse na gabatar da sallah ta.

2
Cikin sujjadar 'karshe kuka ya k'wace! mini domin tunda na tayar da sallar nake kokarin danne kukan amma hakan bai samu ba, ganin ina ganawa da mahallici na yasa na kasa daurewa kuka nake sosai ina rokon Allah ya magance mini matsalar da nake fuskanta tare kuma da kyakykyawan zabi nagari. cikin raina naji ina sha'awar aure ko don na samu sauki da salama a rayuwata! domin kwata-kwata bana jin dadin zaman gidan, dalilin cin zarafin da Bahago yake mini uwa uba kuma Tokar a duk lokacin da ta bushi iska sai ta ci mini mutunci da ni da mahaifiyata da tuntuni ta fita ta bar mata gidan saboda tsabar tashin hankali da rashin kwanciyar hankali. gyara
Kwanciya nayi kan daddumar ina nazarin rayuwa! tunda na taso har na zama cikakkiyar budurwa babu wani namiji da ya ta'ba furta kalmar so a gare ni, ni dai nafi tunanin abu daya yasa maza suke guduna rashin kyau! domin zahirin gaskiya ni kaina nasan bana daga cikin mata masu kyawun fuska. 'baka ce ni sosai babu wani abu da yake da haske a jikina sai idona da ha'korana sai kuma faratana su kadai ke da haske a jikina, ni din gabjejiya ce sosai doguwa! mai garin jiki kuma ko'ina na jikina a cike yake mussaman kirjina da kuma kasa ina da hips mai fad'in gaske ga d'uwawu! masu tudun tsiya shiyasa bana sanya mayafi idan zan fita sai da hijabi amma duk da hakan kirar jikina a bayyane take.
Kwata-kwata ban d'auko kammanin mahaifina ba, domin dai gaba da bayansu fulani ne usul shiyasa duk suka kasance farare! domin Tokar tsabar haskenta har d'aukar ido take koda ta tsufa din nan haskenta yana nan. abinda na san na d'auko gashi, domin kaina sunkuf! yake da gashi mai yawa ba'ki'kirin ga santsi da kyalli! mahaifiyata tana da karfin jini sosai shiyasa kaf na kwashe kammaninta kamar tayi kaki ta tofar! wannan dalilin yasa Tokar take gwa'ba mini magana a duk lokacin da tayi ra'ayi sai ta ce tana kokwanto a kaina, wannan kalmar na tayar mini da hankali mutuka!
Kiran sunana na ji tana yi nayi saurin goge hawayen fuskata na amsa tare da daga labulan dakin. ta kalle ni da cewa" Yau ba zakiyi mini shimfidar bane ko mulkin ne ya motsa."
Cike da jin haushinta na ce." Mura fa ki ke yi tun dazu ki ke goge majina kuma ba komai ne ya janyo miki hakan ba sai kwanciya a hasken farin wata don Allah kiyi hakuri ki kwanta a daki tunda dai ba a zafi a garin."
"A'a ba zan zauna na kashe kaina ba a wannan sunkurun! ke da bakya jin zafin sai ki shigo dakin ki kwanta ni dai ba zan kwanta a ciki ba.''

Tunda na ji haka sai kawai na tashi naje na janyo katifar na shimfid'a mata a tsakar gidan kamar yanda ta bu'kata! ta rarrafo ta fito tana surutai! maganar Iyami take yi har yanzu abin yana damunta. cikin raina nace'' Duk abinda Iyami tayi miki ke kika jawo.
Hijab nasa a jikina na kama hanyar fita! da saurin gaske ta ce." Ina kuma zakije yanzu?" Ba tare dana kalleta ba na ce" Shayi zanje na kar'bo gurin Baba."
Shiru tayi ta mayar da kanta kan fillo.
Lokacin dana fita unguwar cike da matasa rukuni-rukuni! kowa yana harkokin gabansa! naji dadin hakan sosai don haka da sauri nake tafiya domin isa can k'arshen layi gurin da tiredar mahaifin nawa take.

Zuwa na gurin ke da wuya shima taxi tana sauke shi gabana ya yanke ya fad'i! "Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! itace adduar da nayi. lokacin na dan samu nutsuwa amma dai duk da hakan ban fasa nanata adduar ba, kuma koda wasa ban kalli gurin da yake tsaye ba sai dai ina ganin matasan samarin dake gurin suna ta zuwa gurinsa tare masa barka da zuwa! haka yake da mugun farinjini na maza da mata.
Shima Baba sai washe baki yake dadi duk ya ishe shi! dama mutuminsa ne sosai kuma yana jin maganarsa fiye da ta wanda ya haife shi. da sauri Na ce." Baba ka hada mini shayi da 'kwai."
Kallona ya yi da fadin." Me yasa baki aiko yaro ba Jamila ba kya jin kunyar fitar dare ko?" na ce" Duk sunyi bacci ne." Shiru ya yi mini gabadaya ma hankalinsa na kan Bahago dake kokarin zuwa gurin matasa na take masa ba.
'Dauke kaina nayi tare da jin wani mugun 'bacin rai!

"Ali baka jin tsoron tafiyar dare ko?" ya fad'a da murmushi a fuska ya bar komai gabad'aya hankalinsa yana kansa kwayoyin idanunsa kadai ka duba zasu tabbatar maka da irin k'aunar da yake masa.

Da murmushi a fuskarsa ya rungume shi da fadin." Baba fatan na same ku lafiya?" Ya amsa lafiya lou Aliyu ina fatan kadawo lafiya da alkairai masu yawa." Ya ce." Alhamdulillhi Baba." Ido muka had'a sai nayi saurin kawar da kaina har yanzu babu sassauci a fuskata!
Bai ce mini komai ba wanda daman ban tsammaci maganar tasa ba, ya juya yana sallamar yaran dake gurin da fadin" Gobe su same shi a gida, gabadaya suka watse, gurin ya rage mu kad'ai! da wani dattijo dake zaune da kofin shayi a hannunsa yana kur'ba!

Babana ya kalle ni da cewa" Ba zaku gaisa da juna ba kinyi tsaye kerere! sai kace gunki!" abinda nake ta gudu kenan, domin na san zai iya tsinkani a gabansa tunda dama shima baya son laifinsa, sai na daure zuciyata na kalle shi. "Sannu." Abinda na iya fada kenan na dauke kaina, bai amsa ba ya kama hanyar barin gurin yana fadin." Baba zan shiga gida nayi wanka sai ka shigo." da sauri ya ce." To babu damuwa Ali Allah ya yi maka albarka." ya amsa da amin tare da giftawa ta kusa dani ya wuce.
Ajiyar zuciya na sauke bayan barinsa gurin, na ce." Baba ka had'a mini shayin yunwa nake ji.'' Shiru ya yi mini. na kalli fuskarsa nan na hango damuwa! cikin zuciyata na ce 'Yanzu sa'bani zai fara giftawa a tsakaninmu.

Yana had'a mini shayin yana kara jaddada mini cewa Bahago 'Dan uwana ne muddin ina son ganin farincikinsa dole na kula da zumunci kuma na kiyaye duk abinda zai wargaza shi, ni dai amsawa kawai nake har ya kammala mini komai na kamo hanyar gida ina tunanin yanda zan yi na bashi girma domin dai da awa biyu kacal ya girme ni, an haife shi da safe wajan takwas da rabi ni kuma an haifi ni goma da kwata na safe, dalilin da yasa kenan muke rigima da juna, domin mugun son girma ne dashi, ni kuma nace bai isa ba, tunda rana daya muka diro duniya, banga dalilin da zai sanya yace dole sai na kwanta ya taka ni ba.

Kan shimfid'a ta na same shi a zaune rashe-rashe! a gaban Tokar 'katuwar takarda ce cike da tsire ga lemo da ruwa nan a gefe! hira sukeyi tare da k'yalkyala dariya.
Raina ya 'baci ganinsa akan shimfid'a ta! ban ce komai ba na shiga d'aki na dauko faranti da kofi na fito! ganin suna yi mini wani irin kallo yasa na tsargu! na kalle shi da fadin." Tasar min daga guri."
Ido ya zuba mini fuskarsa babu yabo babu fallasa!
Na ce." Ko ba ka ji ba?" Tsaki yaja tare da cewa" Shiyasa naji zarni ya cika mini hanci! bari na tashi kada na kwashi kwarkwata da kudin cizo."
Na ce." Aikin banza d'an iska kawai kazami!" da sauri ta ce." Meye abin zagi kuma Jamila na fada miki ki daina kiransa da d'an iska." Tafada ranta a 'bace! Na ce" Ai duk abinda zai faru a tsakanina dashi kece sila mai yasa ki ka barshi ya zauna mini a shimfida bayan kin san bani da babban ma'kiyi kamarsa har yana fad'a mini maganar banza wallahi daidai nake dashi."

Ta bud'e baki kenan zatayi magana ya hana ta, sai tayi shiru tana kallona tare da mamular naman dake bakinta.
Ya ce." Kin jima kina kira na da wannan suna wallahi idan baki yi wasa ba sai na lalata miki rayuwa! sai na mayar dake abin kwantace a gari, shegiya mummuna! a haka zaki 'kare babu wani namijin da zai kwashe ki."

Na ce." Na ji dai ni ba fasika bace kuma bana shaye-shaye! bana kuma harkar daba!" Tsaye ya mi'ke sai nayi saurin ja da baya domin na san zai iya kai mini duka! ya cuce ni! aikuwa duk kokarin da nayi gurin kauce masa sai da ya ritsa ni ya ma'kure mini wuya a jikin bango!
blet din dake d'aure a kugunsa yake kokarin kwancewa! ganin haka yasa na kai wa gabansa duka da gwiwata! aikuwa babu shiru ya sake ni yana kallona da mamaki! a tare dashi.
Ina numfarfashi Na ce" Wallahi kafin kayi mini illah ni zan fara yi maka, ni ce ajalinka." Tokar ta zabga salati! tare da fadin." Kece ajalinsa Jamila to kashe shi zakiyi ko me?" murya ta d'aga sosai wanda ya d'auki hankulan jama'ar gidan suka firfito domin jin ba'asi!
[5/29, 8:30 PM] Binta Umar Abbale: 3
"Ke ce ajalinsa Jamila?" maimaita maganar take cikin zuzutawa! tare da rike bakinta tana nuna al'amarin ya girmama! Kawu Sammani ya kalleshi rai a 'bace ya ce."Ali ka dawo ko? wai shin don Allah mai yake damunka ne? mai yasa baka kaunar zaman lafiya muddin kana gari shikkenan bamu da nutsuwa, na tabbatar da cewa; laifin ka ne, domin dai Jamila ba za ta yi wannan furucin ba sai da 'kwakkwaran dalili, wai shin mai yasa kuke nema ku tona mana asiri! me yasa kuke kokarin lalata mana zumuncin mu" Cikin rashin jin dadin al'amarin ya kai 'karshen maganarsa.

Hawaye na zuba a saman fuskata na ce" Wallahi ba laifi na bane asali ma tunda ya dawo ban kula shi ba, kawai saboda nayi maganar ya tashi daga shimfid'ata shikkenan ya hau zagi na, ya ma'kure mini wuya a jikin bango tare da cire blet kamar yanda ya saba zai doke yana fadin sai ya illata mini rayuwa, shine fa Tokar ta juya maganar a kaina."

Kawu Sammani ransa ya sake 'baci! ya kalli mahaifiyarsa dake zaune tana

Please Login or Register in order to submit comment