Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

LAUNIN FATA
Littafi na daya 1
Rabi'atu Abubakar Nasidi
Ebook creator:- Shuraih Usman
@http://fb.com/hausaebooks


Showing posts filed under Launin Fata
Launin Fata 1-01
Posted by ANaM Dorayi on 10:04 AM, 03-Oct-15
Tare da Alkalim
Rabi'at Abubakar Nasidi
Fatan zaku karance da Dan
Uwaku ANaM Dorayi
Falon ya yi tsit gaba daya iyalan gidan na ciki
kowanne kansa a kasa suna sauraron abinda zai
ci gaba da biyo bayan bambamin da dattijo sir
Abdulkareem baba ke zazzagawa diyarsa
Rabi'atul Badawiyya wadda ke durkushe a
gabansa rungume da yarinyar goye da bata
wuce watanni goma ba a duniya. Ya ci gaba da
fadin na taraku ne a nan don ku zama shaida
kamar yadda na taraku a baya kuka zama
shaida a kan abinda na gayawa Rabi ko ba ayi
haka ba? Sai da ya maimaita tambayar babban
cikinsu Rufa'i ya ce an yi haka Abba, duk da
haka muna baka hakuri..... Ya daka mai tsawa
tunda ka tabbatar mini an yi haka bani bukatar
a bani wani hakuri dole a yi abinda na ce. Kar bi
wannan bakar 'yar da ta zo mana da ita ta
rakaka har inda ta yi auran ta mayar musu da
'yarsu. In ba haka ba wannan bata zama min
gida. Ya juya har ya kai bakin kofa ya dawo ya
ce kar in dawo in samu yar nan a gidan nan ran
kowa zai iya baci idan ba a yi abin da na ce ba
a kiyaye. Yana fita Rabi ta dora hannu aka ta
fashe da kuka ta ce ni na shiga uku, yaushe
zanji dadi ne a duniya. Yarinya yar watanni
goma za a kai gidan daba a kaunata ni kaina
ake ba? Gidan da wahalarsa ta sa na fito ba dan
bana son mijina ba. Wacce irin rayuwa za ta yi a
gidan wannan yar. Ko shakka babu ba zan bada
yata ba a kai ta gara in hakura da zaman gidan
nan. Mahaifiyarta ta taso cikin tausayawa ta ce
Rabi rayuwa fa Allah ce duk wanda Allah ya
nufa zai rayu babu wanda ya isa ya hanashi
rayuwa. Ke ko duk duniyar nan zata hadu a kan
bata son rayuwar wani idan Allah ya nufa
rayayye ne zai rayu. Ci gaba da kafiya ga
mahaifinki abu ne da zai ci gaba da kawo illa ga
rayuwarki ba zai bari ki samu nutsuwa da
walwala ba. Idan kika yi hakuri Allah ya ji kanta
ya kaita hannu na gari ki tuna rayuwarki ba
itace rayuwar wannan yarinya ba, idan kin dage
sai kin rayu da ita sai Allah ya karbi rayuwar taki
ta kuma ta na raye tunda rayuwar ta Allah ce
rai da yake jikin mutum kayan aro ne, duk
wanda wa'adi ya cika mai shi zai karbi abinsa
ne kiyi yaya.Rabi ta kalli diyar ta nono na
bakinta, baiwar Allah bata san abin da ake yi ba
tana barci ta dagata ta rungume kam kam tana
kukan da ya baiwa kowa tausayi ta ce nabila zan
bada ke ba dan raina ya so ba sai dan babu
yanda zanyi ina fatan Allah ya kaiki hannu
nagari wanda zai tausaya miki dangin babanki
basa kaunata na san kema ba zasu kaunaceki
ba amma na san rayuwa ta Allah ce.wannan
jarrabawa ce wata rana lbr zata zama, domin
babu wani abu da ya taba dawwama dadi ko
wahala.
A hankali ta maida ita cikin zanin goyonta ta
mikawa yayanta Rufa'i ya karba ya rungumeta a
jikinsa a sanyaye.
Ya ce ki yi hakuri Rabi dole ne komai girman da
uwa bata son rabuwa ballantana yarjaririya
kamar wannan.
Allah yana sane da halin da kike ciki shi ne mai
magani zai miki magani kin sani babu yadda za
mu yi da maganar Abba in banda haka ba mai
rabaki da yarki a yanzu.
Ta zaro yan kayan nabila daga cikin nata ta kulle
a leda ta dauko wata yar sarka ta azurfa siririya
ta rataya mata a wuya ta mike ta shigo daki ta
kwanta.
A wannan lokaci fatanta mutuwa kawai ta zo,
nono na zuba hawaye na zuba dan tsanani sai
ta kama karanta adu'ar.
Allahumma la sahla illa ma ja'altahu salha
wa'anta taj alul hazna iza shi'ata sahla.
A hankali sai barci ya dauketa zuciyarta dauke
da tunanin baya
ASALIN ALHAJI ABDULKAREEN BABA LABARAN
Dan kasar yamen ne, ya zo Nigeria dalilin
kasuwanci, tun yana zuwa ya koma har ya dawo
da iyalansa gaba daya ya gina gidan shi a kano
suke zaune a wanan lokaci yayansu uku.
Hajiya maryam itace matar tasa muhammad
Rufa'i shine na farko sai nafisa sai muhammad
narardin, wadanda ta hafa a can na nan wadda
ta fara haifa itace Asiya sai muhammad Bashir
sai Rabi sannan fatima zahra sai idris dan auta
da suke cewa khalifa.
Duk inda mace mai saukin kai da hakuri ta kai
hajiya maryam ta kai, ko kusa bata dauki duniya
da zafi ba, tana tafiyar da rayuwarta cikin sauki,
yayin da mijinta Alhaji Abdulkareem yake
mafadacin gaske, babu hakuri a harkarsa, duk
wanda yake tare da shi ya san wannan.
Tun daga kan makota da abokan huldarsa a
kasuwa ballantana iyalinsa.
Ya shigo Nigeria da kafar dama bai jima ba ya
shiga sahun masu kudin da ake fadarsu a duk
fadin jihar kano.
Alhaji abdul mutum, ko abokan harkarsa a kasu
sai larabawa yan uwansa.
Saboda yadda ya tsani bakar fata ko mi son da
yake wa abu in har a gun bakin mutum zai saya
to ya hakura. Zirga zirgarsa tsakanin Ngr da
kashashen lrbw irin su Sudan, saudi arabiya,
egypt da malaysia da can kasarsa yemen da
sauransu.
Duk karshen sati ya kan tara iyalinsa kaf a gana
hirar tuna baya a yi raha ayi addu'o'i ga
wadanda suka mutu a ci a sha, kafin a tashi
gargadin da yake musu shi ne baya son hulda
da talaka.
Baya son hulda da bakin mutun idan sun
kaucewa wanan za su zauna lafiya da shi. Idan
ba haka ba zasu gamu da hushinsa wanan
huduba bata yiwa hajiya maryam dadi tana
ganin kuskure ne babba yake dorasu a kai.
Talaka da bakin mutum duk Allah ne ya halicce
su bata isa tayi mai musu ba saboda masifarsa
gaban yayanta sai ya iya rufe ido ya ci mata
mutunci ba damuwarsa bane.
Dan haka duk lokacin da ya gama nashi
hudubar ya tashi in gari ya waye zata tarasu in
bai nan ta ce da su Yanda nake matsayin
mahaifiyarku a gunku nake da hakki kuyi mun
biyaya akan duk wata hanya da nake son kubi
matukar ba ta kaucewa hanyar Allah ba haka
mahaifinku yana da hakkin kuyi mai biyayya. Sai
dai bana jin dadin muguwar da bi'ar da yake
doraku a kai. Ko wannenku a anan yasan Allah
ne ya halacci mai kudi ya halacci farin mutum
ya halacci baki, duk mai hankali da tunani ba
zaiki wani dan bai da dukiya ba, ba zaiki wani
don bai da farar fata ba. Watarana rufa'i ya
kada baki ya ce da ita ummi idan bamu bishi ba
yaya zamuyi? Sanin kankine gaba dayan mu
karkashin sa muke da zarar mun kaucewa
abinda yake so sai ya wulakantamu ya kore mu.
Itama Rabi ta sami bakin magana ta ce ummi
wlh nima raina ba karamin baci yake yi ba in
naji abba yana fadar haka sai in dinga ganin
kamar ba magana bace irin ta dattijo mai ilimi
wanda yasan abun da yake yi ba. Nafisa ta ce
to wai me akeyi da talauci, annabawa ma da
sukafi kowa daraja agun Allah naiman tsari
sukeyi da shi balantana mu? Ni banga laifin
baba ba dan ya ce mugujewa talaka. Ai nufinsa
mu diyansa ne mata kada mu dauko mai talaka.
Haka ku maza kada ku dauko mai aure gidan
talakawa, yanda yake mai kudi yafison harka da
daidai shi, kwarya tabi kwarya. Idris ya tabe
baki yace nima haka dai naganiNura ya ce to
ma in banda abinsu gida kamar namu yadda
abbanmu ke kashe mana kudi gun cin abinci
mai kyau mu sha mai kyau suturu da kayan ado
masu kyau, amma sai mu lalace a auren talaka?
Haba in anyi haka ai anci baya, ina amfanin
shuka idan ba a yi girba ba?
Abba ya sha gaya mana cewa yana kashe
kudinsa a kanmu ne dan mu zame masa riba,
idan mun tashi aure mu na da tagomashin da
zamuyi tsadar da zamu auro mata masu tsada a
gida mai tsada.
Ku kuma mata duk wanda zai zo auranku ko
kallon fatarku yayi ya san an kashe muku kudi
dole sai yana da kudin da zai iya daukarku idan
wanan bai samu ba ina amfanin kudin da yake
narkarwa a kan mu?
Rabi a ta ce kai ni a ganina wannan ba tunani
ne mai kyau ba yaya nura, ni dai a guna talaka
da mai kudi duk daya ne, don a Alkur'ani mai
girma Allah ya ce babu wanda yafi wani a
cikinku a gun Allah sai wanda ya fi tsoron Allah.
Duba da wanan ayar za ku ga cewa fifiko gun
Allah shi ne abin nema a rayuwar mutum ba zai
samu wannan fifikon ba kuwa sai ya kasance
mai tsoron Allah.
Fifikon jinsi ko yare ko dukiya ba sa amfanarwa
mutum komai a ranar lahira matukar bai bi
Allah ba. Nafisa ta zabga mata harara ta ce to
sarkin wa'azi sai ki dauko duro ki hau ki yi ta yi.
Muhamma Bashir ya ce kyaleta ta fadi ra'ayinta
kowa ba ra'ayinsa yake fada ba.
Fatima ta ce ni dai ba ruwana duk wanda Allah
ya bani ina so in mai kudin in talakan mi dai
nafi son in yi auran soyayya ba auran kudi ba.
Babu wani kudi da zai tsolewa gidan nan ido mu
da abbanmu ke buf mana dakin kudi mu debi
yadda muke so mu yi abin da muke so.
To wane kudi zamu je kwa dayi a gidan wasu?
Rufa'i ya ce daga randa abba ya ji kina cewa in
mai kudi in talaka kin daina cin kudinsa dan ba
a banza yake buf muku dakin kudinsa ba yana
son ya fanshe ne a gaba. Ummi duk ta gama
sauraransu ta gyara zama tayi murmushi ta ce a
takaice dai nafisa da nura da Rufa'i ra'ayinku
daya in har zan gaya muku kuji ku sauka daga
ra'ayin mahaifinku dan ku zauna lafiya.
Gidan kyawawa ake kiran gidan tun daga titi ka
tambaya inkiyarsu kenan, kowanne na takama
da kyau na a gayawa duniyar farare ne kai kai
kamar a taba jikinsu jini ya fito, duk wanda ka
gani sai ka zata yafi duk yan gidan kyau sai kaga
wani sai kaga yafi shi kyau.
Babu abin da ya damu umminsu da cin buri a
kansu, rigimar tana gun abbansu wanda ya dau
burin duniya ya dora musu kamar shi ne ya
fara haihuwar yaya masu kyau.
Mutanan unguwarsu kaf sun san dabi'arsa ta
girman kai da daukan dan adam ba a bakin
komai ba shi yasa basa ma shiga harkarsa
gaisuwa ma sai sama sama.
Duk abinda aka gaya mai ba zasu je baba zai
bar matarsa ta je ba haka diyansa .
Hajiya maryam na son hulda da mutaner yaki
yarda duk randa yaga wani bakuwar fuska a
gidannsa sai ya kare mata cin fuska tas a gaban
bakon dole ta hakura c mai shiga gidanta ita c
ta zuwa gidan kowa a matkotan sai gidajan
abokanan sa masu kudi dai dai da su.
Abin yana mata ciwo sai dai da yake babu
yadda ta iya, fadan da yafi karfinka sai ka mai
da shi wasa dan ka zauna lafiya.
Rufa'i na da sassaucin ra'ayi akan ra'ayin
mahaifinsa a boye yana hulda da ckaken
talakawa a makaranta har yanata bakake yana
yi saboda ra'ayinsa na kashin kansa yafi
sha'awar mace chaculate colour ba fara kal ba.
Nura shi ne mai ra'ayin rikau irin na mahaifinsu
shi yasa suka fi daidaitawa yafi sakar masa kudi
nura dan duniya ne dan fafa na gani kasheni a
dinka sutura a hau mota ana zaga gari idonsa
ya bude sosai da bariki duk wannan bai damu
mahaifinsu ba tunda dai bai jajibo mai talaka da
bakin fata ba an gama haka nafisa yar lelen
abbansu ce tafi kowa iya jin kai da yanga a
gidan dukansu suna da kyaun ta ya hadu da
gayu idan ta dau ado ta shiga mota tana tukawa
kai kace tauraruwa zahra cikin taurari haka take
zama cikin sauran mata karya ne nafisa ta wuce
guri ba ta ja hankalin mutane an maida hankali
ga kallonta ba.
Fatima ke take mata baya a nan inda halinsu ya
bambanta shi ne fatima bata tsani talaka da
bakar fata ba jin kansu dayanga ne iri
daya.Masu halayyar mahaifiyarsu a gidan Rabi
da Asiya suna adawa karara da Nafisa Bashir da
irdis ra'ayin ba ruwanmu ne .. ..
Rufaida da nura sun gama karatun su ne a
malaisia sna aiki a nan kano duk karkashin
kamfanin abbansu a baya musu rowar kudi duk
abinda iyalan sa ke so an gama, matsalarsa
daya fada shima sai ka saba masa.
Kai tsaye a iya cewa basu da matsala a rayuwa
ta fannin kudi dai kam.
Sai a wannaan shekarar akayi auran Rufa'i da
irin diyar da abba yake so, diyar kakadan a
karasu ta yemen a nan Nigeria, gata farar fata
ga uwa uba dukiya. Sunanta zainab suna mugun
sö juna ita da rufa'i haka iyayansu na son hajiya
maryam ce kadai yarinyar bata kwanta mata a
rai sosai ba.
Saboda lokacin da aka fara maganar auran sai
rufa'i ya dauko ya kawota dan ta gaida
iyayensa.
Hajiya maryam na zaune a kan kujera a falonta
suka shigo suna manne da hannun juna shi da
ita har shi rufa'in na dan jajjanyewa saboda
kunyar umminsa ita kuwa zainab ko a jikinta sai
dada mannewa take a jikinsa tana shagwaba.
Rufa'i ya zauna kan kujerar zaman mutum 2 sai
ta zauna a jikinsa ta lankwashe a kafadarsa a
haka ta gaida ummi.
Haushi ya kama ummi ta mike ta bar musu
falon, har zainab ta nunawa Rufa'i rashin jin
dadinta da haka ya ce kar ta damu kunya ce da
umminsa saboda shi dan fari ne.
Suka bar maganar a haka bayan ya kai zainab
gida ya dawo ummi ta dube shi ta ce wannan
yarinyar itace irin yayan da abcnku ko yaushe
yake burin ku auro saboda farar fata ce
kyakyawa, kana iyayanta na da kudi kuma
sanannu mutane ne bai damu da cewa tana da
tarbiyya ko babu ba. Yaya tarbiyar gidansu da
iyayanta suke?
Shi fari da dukiya kadai ya dame shi wannan
kuskure ne da ba za ka fahimce shi ba sai nan
gaba.
Rufa'i bai faìmci abinda ummi take son ya
fahimta ba saboda son da yakewa zainab, dan
haka ya share batun ummi ya ci gaba da
harkokin gabansa.Lokacin da aka yi daurin aure
da biki abbansu ya gina mai gida na kece raini a
tsadadiyar unguwar nan Nasarawa GRA da sai
masu kudin gaske ke iya zama a cikinta. Ya ce
kuma kada a kawo zainab da ko allura sun
gama shirya gidansu.
Amma ina sai mahaifin zainb ya ce tuni ya gama
shiryawa yarsa gida da komai ango ne zai biyota
gidanta dake sultan road duk a kano.
Su yi hakuri haka tsarinsu yake gida ne na bada
labarin kyansa da tsaruwarsa ba zai taba
yiwuwa ba an kashe kudi iyaka.
Duk saboda buri da son duniya wannan bai
damu Abba da rufa'i ba suka bi a haka, ga
gidansu ga komi ya bi zainab gidanta bayan an
gama biki an kaita.
Wannan ma ya bata ran ummi amma ba ta ce
komai ba ta sa musu ido.
Matsalar zainab ta farko da rufa'i ya fara
fuskanta bata iya komi ba sai soyayya.
Yar gata ce yar shagwaba da ma tun ran da za
a kawota har gida ubanta ya kirashi ya ce to fa
shi yarsa ba ta saba da wahala ba, kuma
tattalin farinciki ta ake a gidansu dole ya dora a
inda suka tsaya. Ita kadai ce diyarsu mace suna
sonta fiye da zatonsu.
Sun bashi i ta ne don ta nuna shi take so fiye
da kowane namiji su kuma ra'ayinta shi suke bi.
Basu son diyarsu ta shiga wata matsala dole ne
ya kiyaye da wannan tun daga wannan lokaci
jikin rufa'i yayi sanyi ya jiyo kamshin gaskiya a
maganganun mahaifiyarsa da tace aure a gidan
tarbiyya ya fi aure a gidan dukiya tarbiyya ita ce
zata dore dukiya fararriya ce kararriya.
Bai gaya mata yadda suka yi da iyayen zainb sai
abbansu ya gaya mawa, shi abban ya rufe shi
da fada ya ce ni bani son irin wannan korafin
menene a ciki don sun ce yarsu yar gata ce?
Shin ba yar gatan bace?
Idan c yar gatan ce ba ma ba zata dace da kai
ba.
Rufa'i ya tafi a kan haka bai fara gane kuranshi
ba sai da zainb ta yi sati 2 a gidansa kullum
umminsa ke aiko direba da abinci safe da rana
da daddare, zainab bata san komi ba sai dai ta
ci ta kwanta hatta pant dinta shi ke wanke mata
tun randa ya zo ya iske mai wanki na shanyar
pant da bra dinta a harabar gidan ran sa ya
baci sosai ya ga ina mai wanki ina ganin sirrin
matarsa?Da ya yi mata magana sai cewa tayi
bata iya wanki ba ko a gidan su wanke mata
ake yi, ala dole ya shiga wanke mata da kansa
duk sanda ta yi wanka nan zata bar mai a toilet
ya wanke ko da kuwa da jinin haila a jiki.
Wannan lamari ya dagawa Rufa'i hankali ya
HUrasa wanda zai gayawa lokacin da zainb ta yi
sati 2 a gidansa umi ta kirashi ta ce to kai abinci
ya kare matarsa ta gama hutawa in zata dinga
dafawa to in kuma siya zai dinga yi to.
A ranar ya shaidawa zainb ya da ce ta fara girki
ta galla mai harara ta ce kaga na yi ma kama
da mai shiga kicin?
Ni ko ruwan tea ban taba dafawa ba ban san
yadda ake dafawa ba ma ga masu aiki nan?
Ya ce girkin masu aiki zan ci?
Ta ce idan ba za ka ci girkin masu aiki ba ga
restaurant nan kala kala ka iya dinaga sayowa.
Haushi ya turnuke shi ya ce ban saba ganin ana
sayen abinci ba a gidanmu ni ma ba zan iya ba
da mutuncina da komai ba zai yiwu in dinga
yawan siyan abinci ba....

Zaharaddeen shomar
Whatspp num; 08168575100


Launin Fata 1-02
Posted by ANaM Dorayi on 09:03 AM, 04-Oct-15
Under: Launin Fata
Kuma ni ban saon cin abincin yan aiki ba har yau
ummana bata daina shiga kicin ba duk kuwa da
cewa muna da yan aiki.
Ta ja tsaki ta tabe baki ta ce wannan matsalar ka
ce babu abin da ya daman.
A ranar dan takaici rufa'i bai yi barci ba bai
kwana kuma a dakin zainb ba, wani abin haushin
gari na wayewa ta yi tafiyarta gidansu ta
shaidawa iyayanta wulakancin da Rufa'i ya yi
mata a jiya.
Yana gida yana mamakin halin zainb yana
tambayar kansa haka ake zaman auran dama.
Sai ga mahaifinta ya zo har gidan ya same shi da
fada inda yake shiga ba nan yake fita ba.
Ya ce kai ni fa ban baka diya ta dan ta zamo
baiwa ta rinka maka bauta ba.
Shi yasa na aje mata yan aiki su yi mata duk abin
da take so, bance ka biya ba ni zan biyasu ina
dalilin matsa mata kace sai tayi wani girki?
Wadannan 'yan aikin da na ajiye mata babu wani
kalar abinci da ba za su iya dafawa ba.
Fadan da ya fi karfin mutum dole ya mai da shi
wasa haka rufa'i ya bada hakuri aka ce kuma
dole shi zai je ya dauko zainb.Da yaje haka
mamanta itama ta dora kan fadan baban zainb,
zainb din ta bishi ita kuma da yanga da
shagwaba haka ya bisu yadda suke so dan
babanshi ya ce ita ce matar da ta dace da shi.
Ba a duban tarbiyya da shari'a sai dukiya da
launin fata kawai da yare.
Duk abinda zai dace da rayuwa, addini da
shari'ar mu ta musulunci sun zo mana da shi.
Daga lokacin da mutum ya kauce ya bi rudin
duniya da soye soyen zuciyarsa sai yaga bacin rai
a lokacin da mutum zaiyi aure abin duba shine
abinda zai dace da rayuwa kan tsarin shari'ar
musulunci da addini.
Ba abin da zuciya take so take farautar nema ba,
rufa'i dai ya san ya yi auran soyayya, soyayya
akwaita zainb ta iya soyayya tana sonshi a
shimfida gwanace tana gamsar da shi.
Sauran ma'amalolin rayuwa kuwa kullum aya take
gasa masa a hannu, bai isa tayi ba daidai ba ya
yi magana, ta kan rufeshi da fada ta gaya ma
iyayanta su kare mai tas bai da bakin magana.
Da ya gaji da tsiyarsu haka ya sa mata ido take
cin karanta ba babbaka bai da bakin kai kararta
gun umminsa dariya zata yi mai, mahaifinsa da
zai gayawa fada zai kara mai yace ya fiye korafi
zaman aure dan hakuri ne ya ce dubi dukiyar da
mahaifinta yake jibge muku duk wata ga kudi a
kai akai, koda daina aiki kayi dukiyar mahaifin
zainb zata rike ku.
Lamarin Abba ya dinga ba Rufa'i mamaki, abban
baida wata magana sai kudi, kudi dai.
Gidan rufa'i kenan. Nafisa kuwa lokacin da ta
kammala karatunta a jami'ar ahamadu bello ta
zaria ta dawo tare da wani hamshakin dan
kasuwa dake zaune a kaduna amma fa kamar
shanshani yake kan yawo bai iya zaman sati biyu
a Nigeria yana yawon kasashen duniya sunansa
kabir, matashi ne mai tashen naira shekarunsa
kusan arba'in bai taba sha'awar aure ba sai da
ya dora idonsa kan nafisa lokacin da tazo bikin
yaye su nafisan bisa gayyatar da wani abokinsa
yayi masa.
Ya ruf sosai a kan nafisa tayi daidai da duk wani
ra'ayi nasa da bukatarsa a kan diya mace.
Kabir gogaggen matashi ne dan duniya na gaske,
yadda kasan sauyi riga ka cire kasa wata haka ya
mai da diya mace, kasuwancinsa ya kawo mai
kudi sosai, yana shigo da motoci ne da tayoyi da
duk wani abinda mota ke bukata daga kashashen
duniya kana yana kwangilar kayan gine gine na
zamani daga Al-kaira.
Bai dauki kudi abikin komai ba, yanzun nan sai
ya yi wa mutum kyautar da zata firgitashi.
Bai san ajiye kudi ba in ya samu kudi ya kashe
yayi bushasha kawai ya sani.
Motocin da yake hawa yan ubansu ne na yayi,
wani lokacin mota sabuwar yayi a gunsa ake fara
ganinta.
Abokansa sun dauka itama nafisan holewar za a
yi da ita ya ce wannan matar Aure ce in ta
amince, ya sha yanga kafin ta amince din kuwa
ya hanata sakat sai da ta kawo shi ga babansu.
Bai samu fara'a sosai ba saboda na farko dai
bakin fata ne sannan ba dan boko ba ne.
Jikin kabir yayi sanyi ya tafi ba kwarin gwiwa
abban ya ce nafisa ina ke ina son bakar fata?
Ta marairaice ta ce Abba babanshi ne baki
mahaifiyarsa shuwa ce kuma yana da kudi.
Ba a son ran Abba sosai ba ya amince da auran,
kabir ya fahimci mahaifin nafisa na da shegen
son kudi shi dama kudi ba matsalarsa ba ne dan
haka ya saki jiki ya dinga jibge musu dukiya ya
shirya mata gida kamar Aljannar duniya a malali
low cost a nan cikin garin kaduna.
Lefen da yayi mata akwati set ashirin kaya masu
tsadar tsiya, ga motoci guda 2 na kece raini, duk
wata karya an kare ta a neman auren nafisa,
tana son kabir saboda dan gayu ne dan fafa dan
karya, ga iya magana, idan yana tsara mace sai
ya kashe mata baki ta kasa magana shi kuma
yana son ta saboda kyan ta da gayunta da iya
yanga.
Cikinsu babu wanda ya yi tunanin tarbiyya ko
bincike kan wani abu da shari'a ta gindaya a yi
yayin neman aure.
Rayuwa kawai aka sa gaba ummi bata ce ko mai
ba sanin ba yanda za a yi da maganar
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment