Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

motar hawa bai da ita kuma
malamin makaranta na kasa albashin nasa nawa
ne da zai iya rike yar gidansu da ta saba da jin
dadi ko ta wane fanni? Ko ma me ye dai ummi
tayi na'am da tahir sai dai ko yaushe tana jan
kunnen rabi tana nuna mata cewa kada ta sashi
sosai a ranta abin da zai yiwu shi ake yi, abba ba
zai amince da wanan yaron ba.
Rabi ta ce ummi dan Allah ki daina karyar min da
zuciyata a kan tahir, gwargwadon wayewa ta
addini da ilimin addin yana da shi, haka ilimin
zamanin ma arzikin na Allah ne ai. Ummi ta ce
ba ni za ki gayawa haka ba bani ce mai faìmtar
haka ba abbaku ya dace ki gayawa dan ni tun
kan a haife ki na dade da fahimtar haka.
Ina so ne ki ko yi yadda za ki hakura da Tahir tun
kan Abbanku ya dawo yadda in ya dawo din ya
rabaku ba za ki sha wahala da zuciyarki ba za ki
saba. Wannan ita ce gaskiyar magana. Ta ce
ummi ban san yadda zan iya sabawa da hakan
ba, kamar yadda ban san sanda na fara son tahir
ba.Shi kansa tahir din mamakin yadda ya samu
karbuwa a gidansu Rabi'a yake, shi yana dari dari
ganin matsayinsa bai kai ba Rabi ta nuna ya isa,
tana bashi matsayin da yake ba shi mamaki, har
fushi take in taga ya ki sakin jikinsa, wannan ya
faranta mai rai yana ganin ya tsinci dami a kala
bai san rigimar da take kwance a gidan su rabi
ba. Ana ya gobe abbansu zai dawo daga chaina
gida ya kacame da shirye shirye taryarsu anyi
girke girke kala kala, ana sa ran da magariba
zasu sauka a nan kano. Rabi da asiya anci ado za
a taryar abba, asiya ta ce amma dai yau tahir ba
zai zo ba ko? Kin ba shi dama kullum yana zuwa
gidan nan kun yi mugun sabo da da juna ga
lokacin rabuwa ya zo. Rabi ta ce tabbdijan ke
kina tsamanin akwai wanda zai iya rabani da
tahir? Asiya ta ce ofcourse ko yaya nura ba zai
barki da tahir ba ballantana abbanmu. Ta jinjina
kai ta ce da ace tahir ya ce zaizo yau ba zan
hanashi zuwa ba shin nima ina bukatar ganin
kaya na. Dan ko bai zo yau ba goben nan in Allah
ya kaimu zan gabatar da shi ga abban duk abin
da zai ce ya fada matukar aure zanyi tahir zan
aura. Ni ba auran kudi zan yi ba zanyi auran
soyaýa ne, tahir kuwa yana sona ne saboda Allah
kullum fatanshi Allah ya nuna mai randa zan
zamo matarsa. Asiya ta ce babu abin da ya fi
adu'a muhimmanci, idan Allah ya kaddara taìr
mijinki ne isar Abba ba za ta yi tasiri a kan ku ba.
Ana idar da sallar isha'i jirgin da ya dauko su
abba daga lagos ya sauka a kano, su asiya da
Rabi da fati da idris da direbansu suna jiransu,
kowa a gunsa yake kallo saboda masifar kyansu
akwai daukar hankali, Abba ya dinga rungumar
ya yansa daya bayan daya suka taho gida. Tun a
hanya Abba ya jawo Rabi'a jikinsa ya ce nafisa
ba ta zo ba ko? Ta ce ta yi waya dazun ta ce in
Allah ya kaimu gobe tana hanya. Ya ce Rabi ke
da Asiya kunyi babban kamu. Rabi ta firgita tace
kamar yaya fa. Abba ya dauko wayarsa ta ha6u
ya hasko hoton wani dan ubansun matasì dan
gayu kamar bature ya ce wannan shi ne sultan
dan waziri sarkin Alkahira ne, mahaifinshi
mutumina ne sosai satin da ya wuce sun zo
china sì sultan da mahaifinsa ya ga hotunanku a
jakata ya nuna ki ya ce yana so, na ce na bashi.
Yaro ne matashi dan gata shi kadai ne namiji a
gun iyayansa babu duniyar da ba su mallaka
ba, shi kuma abokinsa da suke tare mai suna
nazir ya ce yana son asiya mahaifin nazir shi ne
ministan tsaro na dukka kasar tasu. Gaba daya
kan rabi ya yi dum zuciyarta ta yi bakikkirin da
kyar ta amshi wayar da Abba yake nuna mata
hoton sultan da nazir ta zubawa sultan ido,
karyar mutum ya ce zai kushe sultan kyau dai
na da namiji bata ga abin da ya ragu ga sultan
ba sai dai tuni zuciyarta ta tsumu da tausayin
tahir da kaunasa yadda yake nuna mata bai da
wani gata sai na Allah da manzonsa, matsayinsa
na maraya, bai dogara ga kowa ba sai Allah sai
ita da zuciyarsa ke so fiye da kowace irin mace a
duniya. Lokacin da suka iso gidansu ta mikawa
asiya waya duk walwalwalarta ta koma ciki gaba
daya jikinta ya yi sanyi. Ana zaune a falo suna
cin abinci kowa na raha ban da ita, Abba ya gaji
ya ce Rabi yaya na ga duk jikinki yayi sanyi? Ko
ba ki son sultan ne? Ummi ta ce Ai abba bayan
tafiyarku china ta samu wanda take so. Tun
kafin maganar ta yi nisa ya fi kyau ka baiwa
sultan fatima.Abba ya ajiye cokali ya bata rai ya
ce A ina ta samu wanda ta ke so din? Kafin mu
rabu da su sultan a china sai da muka gama
magana fa yanzu haka wani satin in Allah ya
kaimu za su zo nan kano su gana da su wani
satin a daura aure a yi biki su tafi london inda
sultan da nazir ke aiki, su kuma zasu ci gaba da
karatu. Ummi ta ce to ai dama kama ta ya yi
kafin ku sanya magana ka dawo gida ka tuntubi
su rabin in suna so sun amince. Ya katseta cikin
hushi ya ce saboda su ne suka haifan bani na
haifesu ba, kenan bani da ikon in zartar da
hukunci a kansu sai na yi shawara da su ko? To
bari ku ji wadannan matasa 2 sultan da nazir
banga wani abu na jin dadi duniya wanda ba su
mallaka ba ba zan yarda in yi asararsu a gidana
ba alhali su suka ce suna so ba tallarku na yi
musu ba. Sun yi daidai da ra'ayina ba ruwana
da kuna so da baku so zan aurar da ku garesu
dan ni banga makusa a tare da su ba. Ke asiya
kin ga nazir a waya kin amince da shi ko kema
kina da wanda kika zabawa kanki? Kanta na
kasa kamar tayi kuka ta tsani dabi'ar mahaifinta
na kallafa rai kan abin duniya, duk da ace ma
zai ba da su haka nan ne ba tare da ya nuna
kwadayinsa ga abin duniya ba a zo ana
wulakantasu a kan kudi da sauki bayan kudin
nan kana da su ba rasasu ka yi ba. Sai da ya
maimaita tambayar ta cikin nauyin baki ita ce na
amince Abba ina son ku tayani addu'ar Allah ya
sa son gaskiya yake mini ba son sha'awa ba,
nima Allah ya sa in soshi so na tsakani ga Allah
ba son abin duniya ba. Yaya nura ya fiddo ido
ya ce ke wa kike gayawa haka? Ta ce ka yi
hakuri yaya gaskiya daci gareta. Abba ya ce
Asiya, nasir yana sonki da gaske karki damu. Ba
ta kuma cewa komi ba ya waiwaiya ga Rabi ya
ce to ke kuma fa, shin kin amince da zabin
nawa ko zabinki zaki aura? Cikin makyarkyatar
murya ta ce Abba dan Allah ka yi hakuri ka yafe
min da a ce ban sawa zuciyata son wani ba zan
amince da zabinka dan in samu albarkarka ina
son tahir ka taimakeni ka barni in aure shi.
Abba ya ce uhum Rabi'a da a ce babu fatima a
gidan nan sai in dage sai kin auri sultan, dan ba
zan iya amincewa in rasashi ba, wata garabasa
ce ta zo mini, sai dai duk da haka ki sani zan
amince ki auri zabinki ne idan ya cika sharadina
idan zan bada diyata aure. Kun daf da sanin
sharadin in Allah ya kaimu gobe ki kawo mini shi
in ganshi in ya isa ya zamo surukina sai in baiwa
sultan fatima ta kammala secondary din a
london. In kuwa bai isa ya zamo surukina ba to
kuwa ba makawa sultan ne mijinki.
A dakinsu Rabi'a kuka take tana karawa, Asiya
tace dama kin hakura da tahir, abba ba zai baki
shi ba kar ma ki sha wahalar kawoshi ya
wulakantashi a banza. Fatima ta ce Allah anti ni
ban taba ganin kyawawan maza irin sultan din
nan da nazir ba, a waya fa muka gansu ba a fili
ba, ke kuwa me zaisa ki batawa kanki lokaci kan
wani tahir? Rb ta ce abin da nake so ku gane shi
ne so daban kyan halitta daban, ni son tahir
nake kawai a karan kansa ba launinsa nake
kallo ba. Syy ta sha bambam da abubuwan da
mu tane suke kallo su so mutum. Ina matukar
tausayi Tahir sboda ya kallafa rai akaina, ina son
na aure shi sboda ya fi mini wadannan matasan
da kuke gani kyale kyale ne kawai. Nafi
hangowa kaina zaman lafiya da kwanciyan hkl a
auran thr fiye da auran sultan. Ftm ta mike
zaune ta ce Dan Allah anti Rb me ya sa baki sö
sakin jiki ki mori yaruwa ne? Idan mutum bai
mori lokacinsa na rayuwa ba sai yaushe? Asiya
ta ce ina ma ba haka tsarin bab yake ba da shi
ne zamu more, yanzu ina zancan wani morewa
a tare da mu anan sai da mu dan a samu kudi?
Rabi ta ce ni dai kam gobe zan kai tahir gaban
abba.Asiya ta ce to kuwa ki kwana kina adu'ar
ko abba bai amshi tahir ba kar ya wulakantashi
ta ce Adu'ar ma za tayi tasiri ya amshe shi
insha Allah. Sassafe rabi'a ta kira tahir a waya,
ya daga aguje ya ce Ranki ya dade kin tashi lfya.
Ta yi yar siririyar dariyar da yake mugun so ta
ce lfy kalau tahir Abba na ne ya dawo daga
chana jiya yana son ganinka dan na gabatar mai
da maganarka a matsayin wanda nake son aura.
Numfashinsa yayi kamar zai dauke dan firin
cikin ganin Abbanki saboda wani salo ne na
motsa soyayyar mu ta samu ci gaba. Abinda ya
razanani shine da kika ce kin amince da ni a
matsayin wanda za ki aura, wlh Rabi'a idan na
kalleki na dubi yanayina sai inji na firgice
hankalina ya tashi, sanin cewa ko ta ina aka
biyo kin mini nisa da yawa, in banda Allah shi
ne mai yadda ya so ta ina da matsayi irin naki
zaki kamata ki ce kin amince za ki aura? Bayan
kina sane da cewa ni ba kowa bane ba dan
kowa ba ban ajiye ba ban ba wani ajiya ba. Ta
ce ya isa haka At-tahir ka gama magana da kace
Allah ne mai yadda ya so. Bayan azzahar ka zo
kawai. Bayan sun aje wayar tahir rasa inda zaisa
kansa yayi dan farin ciki wai shi ne zai mallaki
kyakkyawar yarinya irin wanan. Ya shiga gida ya
shaidawa hajiya yaya ya hasko mata hoton rabi
a waya ita kanta.......




Zaharaddeen Shomar

Whatsapp number : 08168575100



Launin Fata 1-04
Posted by ANaM Dorayi on 09:22 AM, 06-Oct-15
Under: Launin Fata
Tare da Alkalamin
Rabi'at Abubakar Nasidi
Ita kanta firgita ta yi ta ce kai tahir ina kai ina
wannan balarabiyar 'yar? Wlh ka rufawa kan ka
asiri kada ka dauko abinda yafi karfinka, ina ka
ga kudin da zaka auri wannan yar, ina kaga inda
zaka ajiye ta? Ya ce yaya wannan yarinyar tana
sona za ta iya zama duk inda na ajiye ta. Bata da
girman kai da son duniya zata baki mamaki in
kinganta. Ta ce ni dai kam da zaka bi shawarata
da ka hakura da yarinyar nan ka nemi daidai da
kai ka aura. Ya ce yaya kiyi mini addu'a kawai ba
zan iya rabuwa da yarinyar nan ba ko zan aure
ta ta dinga tattakani ne. Yaya ta bishi da kallo
yana jinjina kai. Karfe 2 daidai suna kofar gidansu
Rabi'a shi da abokinsa Ibrahim. Gwargwadon
halin da suke da shi da wayewarsu sunyi ado sun
yi kyau suna ta kamshin turare. Ibrahim ya dubi
gidansu Rabi'a ya ce anya tahir yarinyar nan da
gaske tana sonka? Me kagani Ibrahm? Dubi fa
gidansu kana da abinda zaka nemi aure a
wannan gidan? Tahir ya yi dariyar nishadi ya ce
Ibrahim lallai bani da kudin da zan kawo wannan
gidan dan suna da komi. Allah da yake da kowa
da komi shi ya sanya soyayya ta a zuciyar Rabi ba
tare da na isa ta so ni ba. Ya ciro waya ya kirata
ya ce gasu sun zo nan da nan ta fito ta ci uwar
kwalliya da atamfa english ban iya bayyana kyan
da tayi. Dole ne Rabi ta firgita duk wanda ya
hada ido da ita tayi kyau matuka duk da cewa ta
lullube jikinta da babban mayafi ta dauki rayuwa
da sauki da yawa. Ta shigar da su ta falon baki
na abbansu ta sanya musu abinci suka kwashi
girki suna hira kana ta shiga cikin gida ta ce da
abban ga tahir ya zo.Ya ce je ki shigo da shi nan.
Abba na kishingide a kasaitaccen falonsa na cikin
gida wanda ya fi kowanne falo a gidan. Tahir gani
yake babu a kure a falon ummi da suke zama su
yi hira ba da wancan falon na baki, yau da ya
shigo wannan falon na Abba ai kauyanci suka
nuna sosai shi da Ibrahim saki baki suka yi galala
suna kallo duniya, tun daga nan Abba ya fara jan
tsaki ya murtuke fuska. Jikin Rabi ya kara yin
sanyi ta zauna daf da kafar Abba yayin da su
tahir suka zube kasa suka gaidashi ya amsa a
lalace ya mike zaune sosai ya ce ke wai ina taìr
dinne kin zaunar dani kina bata min lokaci. Cikin
in ina ta nuna tahir da yatsa ta ce ga shi nan.
Cikin tsawa ya ce wa?
Ya nuna shi da yatsa.
Ta ce Eh shi ne Abba.
Ya ce amma lallai sai yau na san baki da hankali
da tunani.
Ya maido idonsa ga Tahir ya ce kai yaro sunanka
Tahir ko?
Ya ce Eh abba suna na kenan.
Ya ce waye mahaifinka a garin nan.
Tahir ya dauko tariin gidansu tiryan tiryan ya
fadawa abba.
Abba ya ce idan ita Rabi mace ce tana da
karancin tunani a matsayinta na mace mai raunin
shekaru kai ya dace a ce tunaninka ya dara nata.
Yanzu saboda Allah ka dubi kamar wannan da
zankadediyar yarinya kamar wannan kana
matsayi irin naka bakin mutum bakin ma kuma
talaka ka ce kana so a baka ka aura? Na farko
baka da gidan zama kace a gidan iyayanka na
gado za a sammaka dakin zama, baka da ko
motar hawa sai machine' kana koyarwa kana
daukan albashi a wata a haka kake ganin zaka iya
rike min wannan yariyar wadda abincin da zataci
na kwana bakwai zai iya kashe albashinka na
wata 3, ba wai dan yawan abincin ba sai dan
tsadarsa,(Babdijan Abba kadau duniya dazafi,
cewar ANaM)
Kuma suturar da take sawa albashinka na wata
shida ne zai iya sayan kala daya kana nan cikin
ya san 2. Ballantana a gangaro motar da take
hawa in zata fita wadda har ka mutu albashinka
in zaka daina ci ka daina sha kana tarawa ba
zaka iya saya mata motar da take hawa a gidan
nan ba. Haka kayan kwalliyar da take amfani da
su ba zaka iya saya mata ba. Ballantana a zo ga
batun lafiyarta in bata da lafiya ina fita da ita ne
kasar waje a dubata, babu asibitin da ya yi mini
a nan kai kuwa ko a nan dinma asibitocin da ba
zaka iya biya ba sun fi yawa. To ina ga in anzo
raguwar bukatu na rayuwa. Ni kuma kaga ba zan
yarda in saida akuya ta dawo tana ci mini danga
ba. Yayana tun suna kanana nake kashe musu
kudi in wadata su da abinci mai kyau, abin sha
mai kyau, sutura mai kyau, makaranta mai kyau,
asibiti mai kyau, makaranta mai kyau, asibiti mai
kyau, mahalli mai kyau in shekara goma sha
takwas ko ashirin ina wannan rana tsaka in dau
yata in ba namiji da ba zai iya dorawa inda na
tsaya ba? Sai dai ta koma ta ci baya a gidansa ko
kuwa ni inci gaba da bata abin da ta saba rayuwa
da shi a gidana? Ya girgiza kai impossible, kai
kanka ka san ina da gaskiya saboda haka da
Allah daga yau ki yiyaye Rabi'a ba sa'ar auranka
ba ce ko ta ina. Na yi ma wannan bayani ne dan
ita ta kawoka gabana a wautarta zanbi abinda
take so. In da a kofar gida na ganka kamar kai
bakin mutum talaka ka ce ka zo gidana neman
aure da yau a kulle zaka kwana. Saboda kazo
mini da rainin wayo. Tashi maza ka kama
gabanka. Tunda tahir ya sunkuyar da kai yana
sauraron Abba bai dago ba ko motsi bai yi ba sai
da ya gama haka shima ibrahim tare suka mike
suka ce mun gode Abba mun barka lfy. Ya bisu
da kallo yana murmushi ya ce Allah sarki
matashin kwai mai wautar karo da dutseRabi na
zaune kan kujera ta kifa kanta a cinya tana jin cin
fuskar da abba ya karewa masoyinta, tsananin
kunya ya hanata dago kai tana ji su tahir suka
fice daga falon, bata san me zata ce da su ba,
kila tahir yace ta kawo su ne dan a wulakantasu
dama dai ta san hakan ce zata faru. Abba ya sa
hannu ya dago kanta ya ce Rabi ni kam kin bani
mamaki dan Allah ina ke ina wannan bakin
mutumin? Shin kina duban kanki sosai kuwa? Ki
dubi baiwar kyakkyawar haliuar da Allah ya yi
miki amma ki lalace gun wannan yaron? Da
bakinsa fa ya ce mini bai da gidan kansa in na
bashi ke a gidan iyayansa zai zauna bai da motar
da zai dinga kaiki in da zaki in bukatar fita ta
taso. Haba Rabi'atu duk abinda kike so zai iya yi
miki ki lalace gun wannan? Ta fashe da kuka ta
ce Abba wai shin wake ba da arziki ne in ba Allah
ba? Akwai wanda aka haifa da arziki? Ko kuwa
akwai wanda zai tafi lahira da kudi? Kowa a nan
duniya ya samu kuma nan zai barsu. Rabon bawa
da arziki mutuwa, babu mai fidda rai da rahamar
Allah, Allah shi ne mai bayarwa Abba. Abba ya ce
uhum wannan wa'azin da kike mini na nufinin ke
dai kina nan kan bakanki kina son tahir ko? Ta ce
dan Allah ni dai ka yi hakuri ka taimakeni ka bani
shi ina sonshi. Ya tsuke fuska ya ce Rabi'a in har
kina son zaman lafiya ki daina batun wannan
yaron. In har kinga kin aureshi sai dai bayan
raina ko kuma kin gujeni saboda shi kin bar gidan
nan amma ba da yawuna ba.
A kofar gidan su Rabi ya tsaya ya rike kai da
hannu idanunsa sun yi jazir ya ce ibrahim ya ya
zanyi da son da nake wa yarinyar nan ne?
Ibrahim ya ce yaya za kayi kuwa ban da ka
hakura? Ka taba ganin an yi hakuri da soyaya
Ibrahim? Tahir ya yi tambayar cikin yanayi na
tanyin kai da karaya. Ibrahim ya gyada kai ya ce
eh kwarai kuwa soyayya kuwa ita ce a kai hakuri
da ita dan kuwa ba ta da magani sai hakuri.
Hausawa ma kance. In so cuta ne hakuri magani
ne.Bai da ce ka bari maganar nan ta dame ka
ba. Ni da kai mun san haka na iya faruwa idan
ka kalli Rabi da gidansu da yanayin rayuwar da
suke ciki zaka tabatar gaskiya mahaifinta ya
gaya ma? Cikin abinda ya lissafa wanne ba haka
ba? Saboda haka ina baka shawarar ka hakura
da Rabi'a ko misali ya baka da wahala
albashinka ya rike ta. Maganganun ibrahim na
kara dagawa tahir hankali ya ce mu tafi kar
zuciyata ta buga.
Dakin ummi ta shiga ta isketa ta idar da salla ta
zube a gabanta tana kuka ta gaya mata
wulakancin da abba ya ma tahir. Ummi ta aje
carbi ta ce wannan kenan da kike bata
hawayenki kike a banza kan abinda kinfi kowa
sanin faruwarsa. Ta ce ummi ni yaya zan yi ne?
Ummi ta ce hakuri mana? Sanin kanki ne fitina
ce babba in har kika ce zaki yiwa abba
gaddama. Ta mike ta shige dakinsu Abba kuma
ya shigo da bambami ya ce maryam kece kika
baiwa Rabi damar tayi soyayya da irin mutanan
da kun san bani ra'ayin su ko? Ta ce duk sun
zuciyar mutum ya san wani bai da ikon cusa son
wani a zubiyar wani sai yadda Allah ya nufa bai
ki ba ka iya bada shawarar a hada wane da
wance aure, Allah ya sa soyaya a tsakaninsu
duk da haka in sun so juna baka isa ka ce kai
ne ka sa musu son junansu ba kowa ya san
hukuncin Allah ne. Abba ya ce to naji ba kece
kika sa sonta a zuciyarta ba amma dai kece
ganin bana nan kika bata damar sauraronsa har
ta shaku da shi take ganin ya dace ta aureshi
alhali kun san ko na sha giyar wake ba zan
yarda in ba shi ita ba. Ta ce Alhaji auran fari
shari'a ta yarda iyaye su zabawa yayansu mijin
aure. Amma shari'ar ba ta haramtawa yar ta
kawo wanda take so ba matukar an yarda da
sana'arsa da addininsa saboda gaskiyar magana
ni bani tare da kai kan wannan bahagon ra'ayin
naka' tana son shi, shi ma yana sonta yaro ne
mai mutunci mai kamun kai, ya mallaki abinda
masu kudin ba su mallaka ba. Ya ce ke da Allah
rufe mini baki kin yi aikin banza ke da ita, ko da
aka kula soyaya bana nan ai yanzu na dawo
kuma an nemeni idan an isa a kaita gidansa ba
da sa hannuna ba mana kara kawo mini zancan
wannan yaron daga yau na soke shi a gidan nan
in ba haka ba za ku fuskanci bacin raina. Na
bawa sultan Rabi dole shi zata aura baku isa ku
bata mini tsari ba.
Tsakiyar dare Rabi ta kira tahir a waya yana jin
muryarta ya yi wata boyayyar ajiyar zuciya mai
dauke da damuwa ya ce Rabi me ya hanaki
bacci har yanzu? Abin da abba na ya yi maka
banji dadi lamarin ba. . . Ya katse ta daina bani
hakuri dan kuwa ba laifi yayi mini ba gaskiya ya
gaya mini, ya tunasar da ni abin da tunvni na
san da shi makuwar soyayya ce ta sa ta kasa yin
tasiri a zuciyata in ankarar da kaina hakan.
Rabi'atu hakika bani da kalmar da zan iya yi
miki godiya da ita saboda kin bani matsayin da
ban kai shi ba a zuciyarki. Wanan kadai ya isa
yasa in ci gaba da ganin girman mahaifinki ba
zan kullaceshi a zuciyata ba, saboda ya haifo ya
mai mutunci mai daraja wadda tasan abin da
take. Rabi'a a rayuwa irin tamu da yadda
zamani ke tafiya da mu samun mace kamarki
wadda ta kai matsayi irin naki ta saurari namiji
mai matsayi irin nawa zai yi wahala. Duk
abubuwan da abba ya lissafa ba zan iya rike ki
da su ba haka yake' babu uban da zai so yarsa
tana cikin jin dadi ya kaita ga wahala. Idan jin
dadin bai dara na gidansu ba to bai dace ya yi
kasa da na gidansu ba, ke wadanda ma basu da
halin wadata yayansu da abubuwan jin dadin
rayuwar fatansu su kai yayansu in da zasu huta.
A duniya babu wanda bai son ya ji dadi sai dai
in bai samu ba. Rabi'a ta ce tahir bana son
wadannan maganganun naka, kara bata min rai
suke zamu auri juna tunda muna son juna insha
Allahu a duniya babu namijin da nake son aura
sai kai, kuma kai din zan aura,dame zan auri ya
irinki? Ke daga baya fa nima naga wautata, ko
ba a gwadaba linzami ai yafi karfin bakin kaza.
Ta ce tahir idan ka fasa aurena ne ka gaya mini?
Duk maganganun dai a kaina ake kuma na ce
naji na gani ka daina damun kanka. Ya ce Rabi'a
ki dubi yanayin rayuwarki tana da nisan gaske
da tawa. Ta ce da can baka san da hakan ba
kace kana sona kana son mu yi aure ka cusa
soyayyarka a zuciyata a lokacin da ban taba
soyayya ba ban taba san wani namiji ba. Ka
amince da abinda na gaya ma kawai (ta kashe
wayarta). Shi da ita babu wanda ya yi barci a
ranar kowa tunaninsa daban ne da safe ta shiga
dakin ummi suka gaisa ta ce ummi ina son ki
taimakeni daga auran miji irin na yaya nafisa,
zuwa auran mijin da zai dace da rayuwata.
Ummi ta ce Rabi'a bani da karfin da zan yi haka
ko da kuwa ba irin wannan ra'ayin ne da
babanku ba ina son ki kyautatawa sultan zato ba
duka aka taru aka zama daya ba, masu dukiya
da yawa mutanan arziki sun wa addini hidima
sosai a zamanin manzon Allah (S A W) sayyadina
Abubakar saddik (R A) Mai dukiya ne shi ne
wanda aka ce da za a tara imanin duk mutanan
duniya ba zai kai rabin imaninsa ba haka
Abdulrahman bin Auf (R.A) mai dukiya ne shi ne
sahabin farko na sababbai goma da aka yiwa
albishir da alanna tun suna duniya. Kasancewar
sultan mai dukiya ba shi ke nuna bai da kirki
ba, akwai talakan da ga talauci ga shi bai da
hali na gari ga girman kai bai ba komai fa sai
munin hali. Dan kabir mijin nafisa ya zamo haka
bai yiwuwa a ce sultan haka yake. Abin da yasa
kika ga nima ina kalubalantar lamarin halayyar
da Abban naku ke nuna wa ce bana so. Komi
girman ka a idon mutum matukar ka nuna ka
damu da abin hannunsa ba zai ci gaba da
kallonka da daraja ba. Ance idan kana son Allah
ya soka to ka guji duniya. Idan kana son mutane
su soka to ka guji abin hannunsu. Wannan ita ce
gaskiyar magana mama dai wane taimako kike
so in yi miki. Rabi ta gyara zama ta ce yawwa
ummi so nake ki taimakeki ki sayawa tahir gida
ki bashi mota kudin da yake dan tarawa zai sayi
nasa gidan sai ya yi hidimar neman aure na da
su, nima zan sai da duk golds dina in ba shi
kudin ya ba Abba tunda dai Abba kudi ne kawai
a gabansa ba mutunci ba. Ummi ta yi shiru
kanta na kasa zuwa can ta ce Rabi'a

Please Login or Register in order to submit comment