Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ba
kallon su kawai take suna hidimarsu.
Akayi biki na kece raini, abba na alfahari yayanshi
na da sa'a ya kance shiyasa ya kashe musu kudi
dan a kalle su da daraja, ina talaka ina gidana?
Ummi ta yi murmushi kawai tana kallonshi kamar
bai san abinda yake yi ba.
Ya dau rayuwar duniya ya sa a gaba kamar ba za
a mutu ba, aka kai nafisa kaduna cikin gata da
daula kb kamar ya hadiye ta don so, ta kwashi
fiye da watanni tare ta kb ana shan soyayya ba
matsalar ko mai, lokacin da tayi shekara daya
nafisa ta fara fuskantar matsala daga gun kabir.
Matsalar farko ita ce yawon dare kabir sai ya kai
karfe 2 na dare bai dawo gida ba, in tayi magana
ya ce shi fa daman bai iya zama a gida ba kamar
mace, tayi fushin ta gaji ta dawo lallashi bai
daina ba sai ta kai ta kawo ya fara kwana a waje.
Wata rana ya fita tun sassaè bai dawo ba sai da
ya kwana 2 bakinciki ya damu nafisa gashi ya
hanata aiki ballantana ta dinga fita ya ce bai
amince da aiki ba, tana kwance a daki taji tsiwar
motarsa ta mike ta fito suka hadu a baban
falonta ya fadi kan kujera da kwalabar giya a
hannunsa ko minti 2 baiyi ba sai barci nafisa na
tsaye ta zuba mai ido ta dauko kwalbar giya tana
juyawa dan giya ta aura?Ta jefar da kwalbar ta
fashe ta koma daki ta kwanta tana kuka ta fara
tunanin makomarta a gun KB, kudi dai shi suke
so ita da mahaifinta akwasu babu matsala, duk
abin da take son in dai kudi na siya kabir zai
mance da su akasan matashi. Tun tana da
watanni 2 a gidan sa kb ya fito karara ya ce mata
shi baya son haihuwa dole ne ta yarda a juya
mata mahaifa c zata samu ciki ya rusa mai tsari
ba. Duk da cewa itama ba damuwar ta ta hauhu
ba, amma taji tsarin be mata ba, da ta nuna mai
haka sai cewa ya yi shi fa mace ba ackin komai
take a gunsa ba yana da damar auran 3 irin ta
lokaci guda ya ajiye su yi mai duk abin da yake
so ba ta isa ta sauya mai tsari. In har tana son
zaman lfy ta yi yanda yake so kawai. Sai ta bishi
a haka ya dauketa ya kaita asibiti dan ajuya mata
mahaifa, likitan da zai yi aikin ya dubi kabir ya ce
to bamu guri ko? Kabir ya galla mai harara ya ce
in baku guri kamar yaya? Matata ce fa me zaka yi
mata wanda ya haramta in gani? Likita ya ce
aikin za ayi kuma aiki ne da yake bukatar
nutsuwa ba a son motsi. Da kyar ya amince ya
fita din dan dai yana son a yi aikin. Likita ya dubi
nafisa ya ce da amincewarki za a yi miki wannan
aikin? Alhalin da kuruciyarki da komi? KB namiji
ne a yanzu duniya da kudi da tashan da yake ji
na lafiya da karfi a matsayinsa na matashi ya sa
yake ganin bai dace ya haihu ba. Haihuwa zata
bata mai tsarinsa, daga lokacin da ya gama duk
wadannan abubuwan hankali ya dawo jikinsa ya
faìmci inda rayuwa ta sa gaba to zai auro matar
da zata haihu ne ke kuma ya cuce ki kenan har
abada. Nafisa na sharar kwalla ta ce Dan Allah
likita ka taimake ni ka ce da KB ka yi aikin nan ka
yi mini allurar da zan shekara 5 ban haihu c idan
yaga cn samu ciki ba shi kenan ko nawa kake so
zan baka. Haka aka yi likita ya dannawa nafisa
allura ya ce da kabir an gama aikin... Nafisa tayi
doguwar ajiyar zuciya ta mike ta dawo fal ohar
yanzu barci kb yake ta dau jakarsa da yake fita
da ita ta hannu ta bude ta fiddo matsayacin hoto
mace ce tsirara haihuwar uwarta kyakyawar
gaske, jikin nafisa ya kama rawa, ganin badalar
ta yi yawa ta sake danna wani gun sai ga filin
sosai yana juyawa mijinta ne kb da waccan
yarinyar da ta fara ganin hotonta tsirara
haihuwar uwarta suna aikata masha'ar yarinyar. .
. Yana wani irin. . . Da. . . Ya rike mata. . . .
Alamun yana cikin wani hali. Jikin nafisa ya hau
rawa hankalinta ya yi mugun tashi, a rayuwar da
tayi gwargwadon wayewarta da budewar
idanunwanta ta ga masha'a iri iri amma bata
taba ganin rabin wannan ba. Ta yi sauri ta kashe
wayar gaba daya, ta zauna sharaf gaba dayan
jikinta ya saki a kan kujera kanta ya yi mata
dumm ta rasa tunanin da zata yi.Shin mene ne
kb ya rasa a gunta da yake neman mata? Tamike
ta shige dakin ta ta tsaya gaban makeken
gadonta tana kallon kanta, ita dai ta sani duk
wani abu da namiji yake nema a jikin mace tana
da shi kuma iya kokarinta na farantawa kabir a
fannin sha'awa tana yi saboda tun randa ta shigo
gidansa ta fahimci shi mutum ne makalin mace,
yana da masifar sha'awa bai iya hakuri akan
mace, dole take amfani a bubuwan da zasu kara
mata kuzari da ni'ima dan ta samu juriyar da
zata iya shanye fitina kabir duk dan kada ya nemi
matan banza ashe duk a banza tayi. Tun tana
A.B.U zaria ta tsani namiji mai neman mata duk
burinta bai wuce ta auri namiji mai kudi wanda
zata fantama ta huta ba. Amma ba ta son dan
giya mai neman mata ashe shi zata fado
hannunsa. Kome ya hanata fahimtar haka tun a
da (RABI'ATU NASIDI TA CE KUDI NE) hakane yan
uwa?
Kb ya boye mata halinsa a zaman da suka yi na
shekara daya bata taba ganinshi da giya ba kuma
bata taba ganinshi da mace ba haka kam ya aure
ta bai taba nuna mata wani iskanci ba. Ashe kura
ce lullube da fatar akuya, ta dawo falo ta kara
bude jakar kb sai kuma ta ci karo da pant da bra
wadanda ba na ta ba, da ace su ta fara gani sai
ta rufe tunda ta ga waccen badala me zai
firgitata cikin pant da bra kuma?
Tabbas wannan aike ne a kayo mata dan ta gani,
yarinyar da kb ya kasance da ita a jiya ita ta aiko
mata da wannan sakon, ita ta hana kb dawowa
gida a daran jiya. Ta maida idonta kan kb yana ta
faman barcinsa bai san abin da take ba ta
daddage ta girgizashi da karfi ya farka nan take
cikin matsanancin haushi. Dama abinda ake bata
mai rai kenan a tashe shi yana barci, ya buga
mata tsawa ya ce ubanwa ya ce ki tasheni ina
barci? Ashe baki da hankali?Ta zuba mai wata
uwar harara ta dauko wayarsa ta kunna mai film
din sa ta haska mai ai yana gani ya mika
fuskarsa ta rine da bala'i ya ce ubanwa ya ce ki
daukar mini waya? Sau nawa nake gaya miki ki
daina taba mini waya? Ta ce an taba din sanin
baka da gaskiya ne ya sa kake tsoron in taba ma
waya, ashe kai dan iska ne ban sani ba?
Mazinaci, mashayin giya! Kb ya fincikota ya shake
mata wuya ya shiga lodarta yana fadin ni kike
zagi? Ke har kin isa ki zageni? Kin isa ki hanani
abin da na yi niyya? Ina ce kudi na kashe na
auro ki? Ubanki bai baiwa kowa dansa sai mai
kudi dan na aureki sai in zauna dake ke daya. Ya
yi mata lilis ya dau motarsa ya bar mata gidan,
itama ta nufo kano gidan iyayenta cikin tashin
hankali, Abbansu baya nan sai ummi ta fada
mata abinda ya faru. Ummi ta ce ai auran mai
kudin kenan ga ribarsa nan kin gani sai ki jira mai
daure muku gindi ya zo. Abba ya zo ya ji cin
mutuncin da Kb ya yi ma yar lelensa a ranar ya
nufi kaduna ya taki sa'a ya iske kabir a gida, ko
kallon arziki baiwa Abba ba ya ce kaga ni fa dan
na auri nafisa bata isa ta hanani abin da na ga
dama ba. Dan me yasa za ta yi mini bincike
dama mai bincike yana cike da ganin bacin rai sai
ta kiyaye dan gaba. Abba ya ce kai bana son
rashin kunya ka bawa yata takarda ko mu hadu a
kotu. Kb ya mike ya shige daki ya fito da wata
yar akwati cike da kudi sabbi kai yan naira 1000,
bandir bandir ya ajiye a gaban Abba ya ce ba ni
da niyyar sakin matata ba zan hanata zama a
gidansu ba, duk sanda ta gaji da zaman ta iya
dawowa ga kudi nan ka kai mata tunda ita kudi
ne a gabanta ni kudi ba matsala ta bane. Ya
koma daki ya danno kofa ya bar abba zaune
turus daga bisani ya dauko akwatin kudi ya dawo
kano ya ba nafisa da ummi lbr yadda suka yi da
kb. Ya ce Nafisa hakuri za ki yi ki koma gidan kb
tun da dai muna samun kudi a jikinsa ki ci gaba
da hakuri da halayansa. Ummi ta ce tabdijan
yanzu duk wannan wulakancin da ya yi maka bai
sa kun dauke hankalin ku daga kan abin duniya
ba, shin meye baka da shi ne Abba da kake
kwadayin abin wani?Abba ya buga mata tsawa ya
ce ke baki da wayo ne? An gaya miki dukiya tana
wa mutum yawa ne? Yanzu ne lokacin da mutum
zai yi tattalin rayuwarsa saboda gaba kafin
lokacin ya kure maka. Nan gaba ka yi
kwanciyarka a gida ka ci duniyarka da tsinke.
Ummi ta girgiza kai ta ce Allah ya kyauta. Tun
nafisa na jin zafin KB har hubdubobin mahaifinta
suka shigi zuciyarta da karfi ta manta son abin
duniya ya rufe mata ido, ta kira kb a waya da
kanta ta ce ya zo ya dauke ta zata dawo, ya ce
da shi ya kaita, in zata dawo ta dawo in ba zata
dawo ba tayi ta zama shi dai ba zai fasa dana
matar duk da yaga tayi masa ba. Bakin ciki
kamar ya kashe nafisa haka ta koma bisa
hudubobin mahaifinta. Dama aure ne aka yi shi
bisa sha'awar suffofin jiki lokacin da kowa ya
gane waye dan uwansa salo ya sauya. In kida ya
sauya rawa ma sauyawa take. Gidan nafisa
kenan.
Yayin da nura da ya kasance ba zancen aure a
ranshi sai tsabar duniyanci da son jin dadi, babu
takurawa a tsarin mahaifinsu kowanen da yana
tafiya ne kan abin da yaga dama, ko Abba zai
takurawa kowa a kan batun aure ba zai
takurawa nura ba saboda yafi amfani da
ra'ayinsa da abinda yake so. Asiya da Rabi
halayyarsu daya basa tare da Abbansu ko kadan
ra'ayinsa bai musu ba sunfi shiri da umminsu
tafi jansu a jiki tare suke duk wata shawara da
za su yi, tare suka yi candy lokacin bashir yana
jami'ar malasia yana karatu asiya na son tafiya
jamiar bayero ta nan kano yayin da Rabi tafi son
shiga legal ta karanta fannin shiyar usulunci.
Wata rana da yamma sun fito zasu kasuwa ita
da asiya,da fatima Asiya ta lullube jikinta da
farar lafeaya fatima ta yafa mayafi ita kam Rabi
hijabi ta sa har iya kwaurinta ta dau nikab ta
kara saboda bata son kallo a kofar gida suka
gamu da Abbansu ya ce ina zaku haka ke kika
rufe fuskarki kamar wata dodo? Cire shi da Allah
sokuwa wadda har yanzu bata gano inda duniya
ta sa gaba ba, ke dai ga alamu bazan ci ribar
kudin da na ke kashewa a kanki ba. A sanyaye
Rabi ta fidda nikab ranta a bace ya ce bani shi
nan, dube ki kamar wadda aka haifa a daji.Suka
shiga mota tana mamakin halin mahaifinsu ba
abinda ya yi mai zafi da tsarin kan shi dan
kuwai ya sami kudi ya maida yayansa kamar
wasu hannun jarin da zai dinga samun kudin
shiga da su. Ya aurar da nafisa ga mai kudi
maganar haihuwa bai damu ba ya ba Rufa'i
diyar masu kudi itama iyayanta sun ce haihuwa
ba yanzu ba duk bai damu ba. A kofar shiga
sahad store na zoo Road wani matashi baki sidik
ya kafawa Rabi ido har ta rasa meye abin kallo
ne a jikinta, ita ba wata shiga tayi ta fitina ko
jan hankali ba tayi tsaki ta wuce gaba ta tsani a
dinga kallonta haka. Har suka gama siyan abin
da zasu siya suka fito wannan matashin yana
tsaye inda yake wannan karon ma ita yake ta
aiki kallo. Daf da shi direbansu yayi parking za
su shiga mota ya karaso kusa da rabi yayi musu
sallama. Fatima ta galla mai harara ta ce malam
lafiya? Asiya ta ce haba fati me ye haka mutum
yayi mana sallama ba ki amsa ba ki haushi da
fada? Ta ce walaikumussalam. Yayi murmushi
ya ce barkanku da yamma. Ta amsa
Alhamdulillahi kana lafiya. Ya ce lafiya kalau dan
Allah waccan yar uwar taki neke son magana da
ita in ba zata damu ba. Asiya ta ce gaskiza
yanzu muna sauri ne sai dai ka iya gaya mata
abinda kake son gaya mata a cikin minti 2. Ya ce
hakan ma na gode. Ya dubi rabi ya ce baiwar
Allah dan Allah gidanku nake son in sani. Ta
dago kyawawan idanuwanta ta dube shi, ta ce
ko zan san dalilin da yasa kake son sanin
gidanmu? Ya ce eh, bahaushe kance in kaga
kare na shinshinar talalmi dauka zai yi, niyyar
Alheri ce ta shiga zuciya ta ayanzu yanzu a kanki
shi ne nake son gabatar da kaina in na san
gidan ku kumma in an bani izinin in zo saboda
nan ba gurin magana bane. Rabi'atu ta dube shi
ta yi jim bakin mutum ya je gidansu. Ai sai Abba
ya kusan dukanta ita kuma ba ta iya wulakanci
ba kawai sai ta yi kundunbala ta gaya mai
kwatancan gidansu ta bashi izinin yazo har ta
gaya mai sunanta.Godiya mai yawa ya mata
tashiga mota suka tafi, duk da sassaucin ra'ayin
Asiya sai da ta ce mata kin yi wauta Rabi,
maganin kar ayi kada a fara, kema kin san in
Abba ya ganki da wannan mutumin kin banu. Ta
ce to ya zanyi? Bana son wulakanta mutane, kai
tsaye kaga mutum a hanya ka wulakantashi
akwai matsala saboda baka san wane irin
mutum ne ba. Fatima ta ce ke dai anti Rabi da
kin sani hakuri kika bashi da wukancin da Abba
zai mashi gara ki bashi hakurin ki sani ko kun
rage saura ku biyu kacal ke da shi a duniya
Abba ba zai baki shi ba. Ta ce a a dama nima
kun ji na ce ina sonsa ne? Nufina idan ya zo in
bashi hakuri cikin ruwan sanyi a rabu lafiya.
Asiya ta ce to Allah ya sa a rabu lafiyan lamarin
Abban ne akwai wahala ****
A ranar Abba bai dawo gida da wuri ba sai
kusan goman dare yayin da tun bayan sallar
isha'i aka aiko ana sallama da Rabi'atu. Ummi
ta rike baki ta ce Oh yau na ji abinda ban taba
ji c waye ya samu nasara a kanki Rabi'a. Fatima
ta ce wlh ummi wani bakin mutum ne ya ganmu
dazun a sahad store ya ce yana sonta ta yi mai
kwatancan gidan nan dan kawai ta sa Abba ya
zo yana fada, da ganinshi kuma kinga talaka...

Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100


Launin Fata 1-03
Posted by ANaM Dorayi on 01:09 PM, 04-Oct-15
Under: Launin Fata
Ummi ta zabga mata harara ta ce to sai me dan
talaka ne kuma baki? Na sha nuna muku cewa
akidar da mahaifinku yake kai ba akida ce ta
gaskiya ba. Tashi kije ku gaisa Rabi. Rabi ta mike
sanye da hijabin da ta yi sallar isha'i ta fito kofar
gidansu inda ta iske shi yaune akan farin mashin
din (vespa) ta dan rusuna ta gaidashi ya amsa
cikin fara'a ya ce ba ki tambayan suna na ba
Rabi'atu. Tayi murmushi ta ce na san zaka gaya
min ba sai na tambaye ka ba. Ya ce haka ne to
sunana Tahir sunan mahaifina Al-amin,
mahaifiyata kuwa sunanku daya Rabi'atu shi yasa
kika kara shiga raina. Sai dai Allah ya yi mata
rasuwa tun ina da shekara 5 a duniya na girma
ne a hannun kakata wadda ta haifi mahaifina.
Shama shekararsa daya kenan da rasuwa sai
kannansa da yayyansa da muke tare da su gida
daya kowanen da iyalansa, kasancewar gidanmu
babban gida ne sosai. Ta ce Allah sarki Allah ya
jikansu. Yace Amin na gode Rabi. Ta ce ina jin
tausayin maraya rashin iyaye yana da ciwo sosai
ko don ni ina da kwalafuci da son iyaye ne? Ya
girgiza kai ya ce E haka ne Rabi'atu iyaye suna da
shiga rai kinga ni ban san mahaifiyata ba, lokacin
da Allah ya karbi rayuwarta ban yi wayon da zan
tantance da ita in shaku da ita ba amma duk da
haka zuciyata tana matukar sonta, idan naga mai
sunan ta sai inji ina kaunarta ina bata girma na
musamman. Lokacin da idanuwana suka yi arba
da ke dazun na yaba sosai da yadda na ganki
cikin sutura ta mutunnci har na dinga tunanin ko
ke matar aure ce ke, direbanku na tambaya cikin
hikima ba tare da ya gano manufa ta ba ya
shaida mini cewa ke ba matar aure ba ce jikina a
sanyaye na nufo ku na yi muku magana duba da
yanayinku kufini karfi talaka kamata ya doshe ku
da batun soyayya to amma abin mamaki sai
zuciyata ta kasa juriyar kyale ku ku tafi na
tabbatar in har kuka tafi ban yi muku magana ba
na yi wa kaina ganganci. Duk da cewa bani da
tabbacin zaku saurare ni, bahaushe kance da
rashin kira karan bebe ya bata haka na daure na
karfafi zuciyata da add'ar neman nasara ban taba
zaton zaku saurareni ba sai gashi kun saurare
nin, har sai da na dinga tunanin ko dai mafarki
nake yi ne? Kalaman tahir suka dinga ratsa
gabban jikin Rabi tana tsoron dawowar babanta
bakinta ya mata nauyi ta kasa yi mai bayanin da
ta fito da shi a bakinta, lokaci guda tausayi da
kauna suka yi tasiri a zuciyarta suka dan jima
suna hira bai tambaye ta matsayinsa a zuciyarta
ba saboda fargabar amsar da zata ba shi. Ya yi
mata sallama ta koma cikin gida tana murna
Abban bai dawo ya iskesu ba. A falon ummi ta
iske Asiya da ummin suna hira ta zare hijabinta
ta zauna, Asiya ta ce in ce ko kin mai bayanin ba
zai samu aure a irin gidan nan ba?Rabi'a ta
waiwayo suka hada ido ta ce tahir ya bani tausayi
sosai ban mai wannan bayanin ba. Asiya ta ce
kada ki bari ba zuciyarki ki wahala a banza Abba
ko ya sha giyar wake ba zai yarda ki auri bakin
mutum ba ko da yana da kudi kuwa. Ki dubi
mijin anti nafisa fari ne kal kai kamar a taba
jikinsa jini ya fito, babanshi ne kawai baki amma
da kyar abba ya yarda da auransu kuma dan
yaga irin wanda yake so ne, bai san ciwon kudi
ba in banda haka da bai bashi ita ba. Ummi ta
ce watan wata rana fa dole abba ya ga sauyin da
baya son gani a gidan nan. Rabi ta mike ta shige
daki.
Tahir ya kamu da son rabi soyayya mai tsananin
gaske ta yadda har yake jin kamar in babu ita ba
zai iya ci gaba da rayuwa ba son da ya shige shi
mai karfin gaske ne, cikin kwanaki 2 rayuwarsa ta
sauya zuwa tunanin mai wahalar da zuciya.
Yanayin Rabin da yake so yanayi ne na mata
masu tsadar gaske yanayin gidansu tun daga get
zaka fahimci ba gida ne na zuwan talaka baYa yi
mamakin yadda ta karbe shi kamar ya isa ya zo
neman auran nata bayan shi kansa ya san bai isa
komai ba. Tahir ya tashi a cikin maraicin uwa bai
samu kulawa sosai ba kasancewar yana da
mahassada da yawa ta bangaran matan babansa
kafin rasuwar baban nasa a dalilini suna ganin
baban nashi na sonsa fiye da dukkan yayansu shi
kuma maraicin tahir din yake dubawa da
nutsuwarsa, tun tahir na dan karami yake
fuskantar hassada daga matan ubansa da yan
gidansu, haka dai ya rayu yau wuya gobe dadi,
yayi diploma dinsa a fannin education a jami'ar
bayero yanzu haka yana koyarwa a nan kano.
Shekarunsa na haihuwa ashirin da bakwai,
rayuwarsa na cike da nutsuwa da sanin abin da
yake bashi da hayaniya da neman rigima, dai dai
gwargwado yana taimakon kakarsa da ta rike shi
da yan uwansa gun uwa. Tun da ya hadu da Rabi
ya dauke ta ya manna a ransa yake jin jikinsa ba
dadi yau da yake ba aiki da ya shiga dakin
kakarsa hajiya yaya tana zaune kan sallaya tana
lazimi ta idar da sallar walaha.Ya zauna kan wata
tsohuwar kujera katako ya zabga tagumi sai da ta
gama ta jawo wani dogon kofi da koko a ciki ta
tura mai ta ce ban karbar maka kosai ba dan kar
ya huce bari in amso maka gun tabawa yanzu. Ya
dubeta a wahalce ya ce bar kosan nan yaya
kokon ya isheni. Tayi mai wani irin kallo ta ce ban
gane maka ba. Cikin yan kwanakin nan duk ka
sauya ko ba ka jin dadi ne? Ya ce lafiyata lau
yaya wata yarinya na gani ina so sai dai tafi
karfina. Ta koma ta zauna tana kallonsa ta ce
lokaci da dama na sha tuna maka cewa kai
maraya ne, dan abin da kake samu na alcshinka
zai isheka rayuwa idan har ka dauko dai dai da
kai. Ya yi ajiyar zuciya ya ce yaya so ba haka
yake ba? Babu ruwan so da mai kudi ko talaka
ba ruwansa da mai iyaye ko maraya zai shiga
zuciya ne an sanya ko ba sanya ba. Ta ce to
shikenan yanzu ka san abin yi tunda kai da kanka
kasan tafi karfinka, amma kake dada sonta, idan
so cuta ne hakuri magani ne? Ya ce yaya hakuri
ba ya yin tasiri ga zuciyar da tayi nisan shakuwa
da soyaýar gaggawa irin wa6an. Ta ce idan hakuri
bai yi tasiri ba wahala ta yi tasiri ko? Ta fice ta
bar shi nan zaune bai san abin yi ba. Da yamma
ya yi kundunbala ya kara nufar gidansu Rabi,
yayi sa'a ya hadu da su ita da Asiya da Fatima a
hanya sun dawo daga islamiya da fara'a sosai
suka amshieshi, Asiya da Fatima suka yi gaba
suka bar su tsaye a gun. Tahir ya ce Rabi'a
soyayyarki ta rabani da duk wani zaman lafiya da
nake da shi a rayuwata gashi kuma ga dukkan
alamu ke ba ki san ina yi ba. Ta ce Ah haba yaya
zaka ce haka? Ya ce dole in fada mana tun da
baki amsa tayin soyayya, ita ba a binta a hankali
idan kace zaka yi a bari ya huce sai ta zamo
rabon wani ba naka ba. Tayi murmushi to ka dai
yi hakuri da sannu zaka ji komai. Ya ce to hakuri
ya zama dole tunda haka kike so a yi, Allah ya sa
in ji Alheri.Suka jima suna ìra tana cike da
fargabar kar babanta ko yaya Nura su zo su
sameta ta yi sa'a har suka yi sallama ya tafi ba
wanda ya zo. Tun shigowa gida ummi ta ce da ita
Rabi ki sallami yaron nan kada wata ran Abbanku
ya zo ya yi mai wulakanci. Asiya ta ce mini dan
mutunci ne da ganinsa salihin mai kamun kai, bai
dace Abba ya mai wulakanci ba gara ku rabu
lafiya. A sanyaye ta ce ummi ni fa ina sönsa dan
ni dan mutunci kawai nake so ba mai dukiya ba
dukiyar da kake da ita ta isheni rayuwa har in
taimaki wani ma, babu dalilin da zai kai ni
kwadayin abin duniya guna wanda zan aura.
Ummi ta yi murmushi ta ce inama abbanku zai
barki ki tafi kan ra'ayinki da kin samu rayuwa
mai kyau da kwanciyar hankali gidan mijinki.
Yanzu ina amfanin rayuwar takaicin nafisa ke yi?
Ko da yaushe ina jin tana bugowa Abba waya
tana gaya mai matsalolin mijinta. Ba abinda ya
ajiye sai shan giya da neman mata idan tayi
magana ya lakada mata duka, abin da ya dame
shi in ubanta yaje ya danne mai baki da kudi ya
dawo? Kuma yayi kicin kicin cewa ba zata haihu
ba bai son haihuwa, dan mutunci mai tarbiya zai
yi haka? Duk wanda ya biyewa kyale kyalen
duniya a aure sai yayi nadama wlh. Idan aka yi
soyayya da aure a tsarin da shari'a ta zo da shi
da aeini aka so juna saboda Allah aka auri juna
saboda Allah, aka zauna dan Allah da manzönsa
wlh ko babu da ko kwandala rayuwarku za ta yi
albarka za ku samu zaman lafiya da kwanciyar
hankali, babu wani abu da zai zamo barazana ga
rayuwarku wanda zai hanaku kwanciyar hankali.
Ba wani abu ne ke bani takaici ba ga auran
nafisa neman matan da mijinta yake abin tsoron
shine kada ya kwaso cuta tana zamanta ya zuba
mata sun riga sun nuna mai kwadayinsu ita da
abbanku har bai shayin ya takata dan ya san zai
biya kudin takawar da ya yi mata. Haka yayanku
Rufa'i shima bai da kwanciyar hankali a gidansa
bai isa ya gayawa matarsa ta yi ba sai dai ita ta
gaya mai ita da iyayanta, yana namiji tana mace
ta ce lokacin haihuwa bai yi ba ya yarda a haka
saboda duk wata duk wani abin bukatar rayuwa
ana jifansa da wasu makudan kudade.An dora
rayuwa kan tafarkin son duniya da kwadayi dadin
da ake son a ji ya ki samuwa. Ina amfaninsa?
Rabi'a ta yi tagumi ta ce ummi ba wani
taimakoko da zaki iya yi mini Abba ya fahimci
ra'ayina da nasu ya sha bambam?
Ta ce uhum Rabi'a kin san halin sa da zarar na yi
magana raina sai ya fi baci fiye da kowa sai dai
addu'a.
Bayan kwana 2 da yin wannan abba da Rufa'i da
nura suka tafi kasar chaina shigo da wasu kaya
kamfaninsu, za su yi watanni 3 a can, hakan ya
baiwa Rabi damar cwa tahir damar zuwa gidansu
duk lokacin da ya ga dama.
Har falon ummi take shigo da shi a shirya mai
abinci, su sha hirarsu sosai ta soyaya.
Lokaci guda ta nuna mai tana sonshi zata aure
shi, haka itama ummi ta yi na'am da shi Asiya
ma tana kaunarsa a gun fatima da idris ne bai
samun fuska a ganinsu ko ba ra'ayin rikau na
abbansu tahir bai da matsayin da zai zo gidansu
neman aure.
Mutumin da ko

Please Login or Register in order to submit comment