Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya danna kofar ya bita
ciki ya maida kofar ya rufe. Rabi'a ta ce a
uzubillahi minashaidanir rajim. Muhamd ya
kyalkyale da dariya ya ce yarinya yau kin zo
hannuna tunda kika zo gidan nan nake fama da
muguwar sha'awar ki a zuciyata. Wannan
fitinannan mijin naki ya kasa ya tsare to yau dai
baya nan ko ki yarda in biya bukatata dake ko
in miki sharrin da ba za ki iya fita ba ta hanyar
cewa ke kika kasie hajiya yaya. . . . . . .
Allahamdu lillah
Allah ya bani ikon kammala littafi na farko sai
kuma Allah ya hadamu a littafi na 2
kukasance dani danjin yanda zata kaya




Zaharaddeen Shoma

Whatsapp 08168575100



LAUNIN FATA
Kashi na biyu 2
Rabi'atu Abubakar Nasidi
Creat by:- Shuraih 99%
@http://fb.com/hausaebooks

Launin Fata 2-01
Posted by ANaM Dorayi on 11:20 AM, 20-Oct-15
Under: Launin Fata
Kan Rabi'a na kasa gabanta na faduwa kamar zai
tsage ya fito tana jin dariyar da muhmd ke
kyalkyalawa yana fadin ko dai ki bani hadin kai
ko in kulla miki sharrin da ba zaki iya fita ba.
Muryarta na rawa ta ce ka ji tsoron Allah ka tuna
ranar da zaka hadu da shi, ni matar dan uwanka
ne bai dace ka nemi yin alfasha da ni ba. . .
Ya ce ke kin san kuwa kyakkyawar surar da kike
da ita? Ko mutum bai niyyar kallanki ba sai ya
kalle kin sha'awarki ta dade tana wahalar da ni
ba zan iya hakuri da ke ba.
Na baki minti 2 ina zuwa ki yi tunani bance dole
sai kin yarda ba amma abin da zai biyo bayan
rashin yardar taki ba zai miki dadi ba.
A hankali ya sulale ya fice daga dakin yayin da
Rabi'a ta sulale itama ta zauna ta kama kai da
hannu 2 2 tana fadin innalillahi wa inna ilaihi
raji'un, wace irin rayuwa na fado haka? Tunanin
abinda ya faru rana ita yau makamancin na jiya
ya fado mata.
Fitowa tayi daga daki ta tsuguna gaban tahir ta ce
me zan fada maka mai gida?
Kan ya yi magana sai ga Dije ta daga labulan ko
sallama babu ta tsaya a kansu ta ce to munafuka
uwar kinibibi me bin miji da rana ko kizo hura
wutar tuwo.
Tahir ya manna mata harara ya ce bata zuwa. Da
jin haka Ali dan dije ya ruga daki gayawa kawu ga
tahir can zagin innarsa dan ta ce Rabi'a tazo ta
hura wuta.
Haka shima kawun ya fado dakin yana huci
kamar wani kumurci dije na ganinsa ta fashe da
kuka ta ce yawwa gara da ka shigo malam ni na
gaji da wulakancin da tahir yake wa kowa a gidan
nan a kan matarsa.
Kawu ya ce dama baka da mutunci ko tahir?
Akan matarka kake zagar mini mata haka?
Tahir ya ce nifa ba zaginta nayi ba kawu yarinyar
nan ba lafiya gareta ba ya dace a dinga sata aikin
da yafi karfinta, amana ce a guna dole ne in kare
mutuncinta daga dukkan abinda zai cutar da
rayuwarta .Kawu tanimu yace af nima zagin nawa
za ka yi to zageni ko ka dakeni karewar zagi
sannan ne nasan ka isa marar mutunci. Tahir ya
zauna kan kujera bai kuma magana ba Dije da
kawu suka kare mai cin mutunci tas a gaban
yayansu yara da manyan kawu ya ce kuma tilas
ne ya bar matarsa ta ci gaba da ayyukan gida
kamar kowace mace dan ba fin matar kowa tayi a
gidan ba har suka gama bala'insu suka fice tahir
bai motsa ba sai hawaye ke zubo mai, Rabi'a na
daki tana nata kukan tabbas zaman gidan yawa
fitina ne, ta mike ta fito falo ta zauna kusa da
tahir ta kamo hannunsa ta ce ka yi hakuri komi
na Allah yana da iyaka watarana duk wanan lbr
zai zama. Ya mike ya barta zaune dan bai son ta
ci gaba da ganin hawayansa, dakin hajiya yaya ya
shiga tana kwance kan gadonta na karfe tana
fama da zazzabi ya zauna kan kujera ya yi
tagumi ta mike zaune da kyar ta ce dan an yi ma
fadan kan abinda kake kake yin kuka, shi kenan
dai kai ba za a fadi gaskiya a kan matarka ba ya
marairaice fuska ya ce don Allah hajiya kada ki
goyi bayan wannan rashin gaskiya a hannunki na
tashi a cikin gidan nan mutanan nan babu
kiyayyar da basu nuna mini ba har Allah ya
rayani ke ma kin san ba kaunata suke ba zasu ci
gaba da yin duk abin da zasu yi ne dan ganin sun
ga bayan zaman lafiyata da kwanciyar hankalina
shi yasa. Shi yasa tun farko ban yi tunanin zama
a gidan nan ba saboda na san abinda zai faru
kenan. Batan fatan ki gaya mini wata maganan
ya kasance ban yi aiki da ita ba shi yasa na zo na
zauna. Duk wanda zai samu sausuce a gunsa a
gidan nan bayanki zan bi, idan ban samu sa'ida
ta bangaranki ba a gunwa zan samu? In har kin
goyi bayan wulakancin da kawu da matarsa suka
yi mini nasan kin yi haka ne dan kece kika haife
shi ni kuwa maraya ne bani da uwa bani da uba
bani da mai goya mini baya kan gaskiyata.
Hankalin hajiya yaya ya tashi da jin kalaman
bakin tahir, ta kama kuka ta ce tahir yau bakinka
ke fadar wadannan kalaman marasa dadi gareni
abinda baka taba yi ba. Ya ce hajiya gaskiya
dama haka take bata taba yiwa wanda ake
fadawa ita dadi ba ki yi hakuri ko da bake kika
haifeni ba ke kika haifi mahaifina. Shima ya kifa
kai a kujera ya shiga kuka, hajiya ta ce ka yi
hakuri tahir nima na san ba a kyauta maka a
gidan nan babu yadda zanyi da tanimu ne nuna
yafi karfina shi da matarsa dije sune kan
jagorancin duk wani rashin gaskiya da son zuciya
da ake yi a gidan nan. Ya mike ya fice a ranar
bakin ciki bai bar shi ya ci abinci ba, Rabi'a tayi
lallashin ta gaji ta sa mai ido.Haka aka ci gaba da
zaman ba dadi kullum cikin bacin rai, damuwar
har tafi ga tahir ita Rabi'a tana dannewa saboda
dai tasan babu inda zata kai karar halin da take
ciki sai gurin Allah, ko ummi dake goyon bayan
auranta da tahir bata sö gaya mata irin wannan
matsalar dan bata son ita dinma ta tsani auran ta
da tahir saukin da take samu ta bangaranta
itama ta rasa. Haka take ta yiwa matan gidan
nan biyayya kan jiki kan karfi amma basu gani
sun hada kai kullum cikin neman abin da zasu
mata wulakanci suke, wai dan kawai mijinta na
sonta yana kula da ita. Duk abinda tayi bata yi
daidai ba aikin tuwan dare kullum mutum biyu ke
yi amma ita bata da ranar hutu kullum sai ta fita
anyi aiki da ita in bta yi ba bala'i. Tahir yayi yayi
ta daina fitowa tana aikin da yafi karfinta duk
abinda zasu fada su yi ta fada ta ce ita dai yayi
hahuri ya kyaleta zaman lafiya yafi zama dan
sarki wata rana sai lbr. Sai da cikinta ya yi wata
biyar ta samu saukin laulayi ta fara samun lafiya
ta daina zuwa gidansu saboda kowa ya kalleta ya
san bata cikin kwanciyar hankali, a dalilin
ramewar da tayi, sai umminta ke zuwa lokaci
lokaci duk sanda tazo da takaici take fita yadda
rayuwar diyarta ta koma dan bata son nunawa
Rabi damuwarta ne da tuni ta fahimtar da ita
itama auran tahir ya fara fita daga ranta. Da
kuma yawan tausayin da tahir din ke bata, ya
gama kallafa rayuwarsa kan soyayyar Rabi'a
rabasu ba karamin tashin hankali ba ne. Yau
juma'a bayan an sakko daga masallaci tahir na
kwance a falo yana kallon wani nigerian film,
Rabi'a na waje tana fama da fitinar wuta wake
da shinkafa take dafawa na sayarwar dije da take
dora ma yayanta ita dijen zata unguwa ne da
safe har da lekawa dakin Rabi'a ta ce Rabi zani
unguwa hansai zata dora wake dan Allah ki
tayata ki dafa kafin in dawo.Ta ce adawo lfy. Ta
gaji da fifita ice jikakke ne kanta har ciwo yake
saboda hayaki ta dawo daki ta dauki wata roba
tata ta fasa taje ta danna a wuta ta kama ta
dawo ta kwanta tana nishi tausayi mai tsanani ya
kama tahir ya mike yaje gabanta ya tsuguna ya
ce wlh rabi'a ina matukar tausayawa halin da
kike ciki a gidan nan, dole ne in nema mana
mafita zaman gidan nan ba zan ci gaba da
ganinki cikin wahala da damuwa haka ba. Ta ce
ka daina damuwa da yawa na sha gaya maka
cewa ni ina daukar rayuwa ne yadda ta zo mini.
Komi lokaci gare shi, ba 9an ce maka ba ni
damuwa da halin da nake ciki a gidan nan ba yes
na damu amma na san akwai ranar da zai zama
tarihi, idan mutum ya daga hankalinsa kan abin
da lokacin yankewarsa bai yi ba wahala kawai zan
sha a banza. Tahir ya girgiza kai ya ce kai Rabi'a
samun mace irinki sai an tona, na gode Allah da
ya bani ke da ace haka sauran mata suke
kasancewa masu tattalin mazajansu da ba a
samu matsaloli a gidajan aure ba. Ta yi
murmushi ta ce kai ma haka abin yake gareka
maza da yawa da sun kasance masu halayyarka
da mata da yawa ba su dinga kuka da mazajansu
ba. Ya ce Rabi na sha gaya miki ba zan gaji kuma
da gaya miki ba cewar ina sonki son da da ban
taba yiwa wani mahaluki ba ina bakin cikin
abinda zai rabani dake ko na rana daya ne. Ina
kishin in mutu ki auri wani ni kadai na san ni'ima
da gamsuwar da nake samu a tare da ke ta bata
rai ta ce kai sai ana magana mai dadi ka dinga
sako maganar mutuwa, insha Allahu za mu yi
doguwar rayuwa. Ya ce Rayuwa kam ta Allah ce. .
. . Dogon tunanin Rabi'a ya katse anna sai yanzu
idanunta suka cika da kwalla tabbas ta fada cikin
fitina babu mai fitar da ita sai Allah tana rokon
Allah ya tsarer da ita daga sarrin dan ladi
(muhamd kenan) yawancin mutanan gidan da
dan ladi suke kiransa.A hankali ya turo kofar ya
dawo dakin tana mamakin yadda yake iya
shigowa gida irin wannan cike da mutane ba a
ganin shiwarsa ne ko kuwa ana kallonsa son
zuciya ne ya sa aka kyaleshi, an san dai ba dakin
matarsa ba ne kuma yana da mata a gidan me
zai kaishi dakinta alhali mijinta baya nan. Ya
tsaya a gabanta ya ce na baki dogon lokaci da ya
isa ki yi tunanin duk da za ki yi nazo jin amsa. Ta
durkusa a gabansa ta ce ka ji tsoron Allah, ka
sani dan mijina baya nan Allah yana nan kuma
yana kallonka ni matar aure ce duk abin da kayi
da ni sai anyi da matarka. Ya buga mata tsawa
ya ce ke dakata ni zaki yiwa wa'azi. Ya kai hannu
da karfi ya damumi wuyanta tana fadin innalillahi
wa inna ilaihi raji'un. Kamar daga sama sai suka
ji muryar kawu yana fadin danladi. Da sauri ya
saketa kafin ya fita kawu ya shigo falon ya ce kai
lafiya? Tahir din ya dawo ne? Mahmud da ce bai
dawo ba nima shigowa nayi in tambayeta ko ya
dawo ta ce bai dawo ba. Kawu ya ce to kuma
zaman me kayi tun dazu fa naga shigowarka
dakin. Ya jinjina kai muje waje in baka lbr da zai
baka mamaki kawun ko da yaushe takamar tahir
matarsa shi bai san wace irin mace yake zaune
da ita ba. Zaunn fa ake jugum jugum a gidan ana
jimamin mutuwar hajiya yaya amma kawu tanimu
kamar ba mahaifiyarshi ta rasu ba, yana can gun
danladi suna kulle kullen sharrin su a kan baiwar
Allah Rabi'a zafi 2 ne ya haduwa Rbi'a a wannan
dare koma 3 ga dai tashin hakali bacewar mijinta
ga mutuwar hajiya yaya wadda a gunta kadai
take samun sauki a gidan ga wata sabuwar fitinar
da muhamd ya bullo mata da ita. Ta kasa zaune
ta kasa tsaye duk iya kwarewa da sata irin na
barci a wannan rana hakuri yayi ya tafi ba tare
da ya sace Rabi'a ba dan bata runtsa ba har gari
ya waye. Bayan ta idar da sallar asuba ta fito
sanye da hijabinta zuwa dakin hajiya yaya inda
matan gidan suke zaune ana shirye shiryen
jana'izar hajiya yaya gaba dayansu kallon banza
suke mata kadan ne suka amsa gaisuwarta, tun a
daran jiya dije da ladidi sun yada cewa Rabi'a
mayya ce ta lashe hajiya yaya. Wasu daga cikinsu
suka fara cewa mu ma idan ba mu bi a hankali
ba sai ta lashe mu mu da yayan mu idan muka
ba hali sai mu bar mata gidan.Duk da mutuwar
ba a fasa wannan gutsiri tsoma ba a cikin gidan,
lamarin da ya sa zaman gidan ya dinga yiwa Rabi
tsanani, da kunci dama dai tana sumun sauki ne
idan an kuntata mata zata kalli mijinta mai sonta
da tausayinta ta ji sanyi a ranta ta maida komi
ba komai ba to gashi yanzu babu shi babu mai
lallashinta, mutanan gidan basu kaunarta ba tare
da ta yi musu komi ba masu kaunarta dinma
tsoron kawu tanimu da dije ba zai bari su jata a
jiki ba. Bayan an kai hajiya yaya an rufe ta dawo
daki ta kwanta tana hawaye ta dauko waya ta
kira umminta ta sanar mata mutuwar hajiya yaya
da bacewar tahir tun safiyar yau. Ummi ta ce to
ki yi shuru ki daina kuka zan zo an jima. Ta tsara
Abba da cewa zata dubo kawarta a asbiti, fatima
ta nace zata rakata bashir ya tukosu a mota da
yake yazo gida hutu. Daga bashir har fatima babu
wanda ya taba zuwa gidan tunda rabi ta zo
ummi ce kadai ke zuwa itama daga baya ta daina
zuwan saboda bata jin dadin yanayi da take iske
diyar ta in tazo. Basìr ya yi parking a nesa da
gidan kadan ya dubi ummi lokacin da take fita
daga motar ya ce yanzu wannan ne gidan da
Rabi'a take? Ta tsuke fuska ta ce to menene ba
rayuwa ba ce. Fatima ta tabe baki ta ce auran
soyayya kenan ya yi amfani. Ummi ta ce kwarai
kuwa yayi amfani dan tana cikin kwanciyar
hankali da mijinta. Suka yi ta'aziya ga mazan
dake zaune a kofar gida tana cikin . Suka yi
ta'aziya ga mazan dake zaune a kofar gida ana
zaman makoki suka shigo cikin gidan wadda ke
cike da mata wasu sunyi jugum jugum wasu kuwa
hirasu suke.Rabi'a tana daki ita kadai jin
sallamarsu ta fito ta fito ta rakasu daki daki suka
yi gaisuwa sai wani irin kallo ake musu sun haska
gidan gaba daya, lokaci guda kamshin jikinsu ya
cika gidan suka dawo dakin Rabi'a tana kokarin
danne damuwarta amma ina kallo daya kayi
mata zaka shaida muguwar damuwar da ke
damunta. Fatima ta ce anti Rabi dan Allah tunda
tahir baya nan gashi mutanan gidan nan ba
kaunarki suke ba ki dawo gida ki yi zamanki ki
haihu ka da ki zo haihuwa su illataki. Ta girgiza
kai ta ce fatima aure na da tahir bai zamo auran
nadama ba a guna, har yau babu namijin da
nake so sai mijina tahir soyayyar da nake masa
yanzu ta ninka wadda kika san ina yi masa kafin
mu yi aure. Babu wata wahala da zata sa in gudu
in bar ladana, wannan wahalar insha Allahu dadi
ce a gaba dan ance bayan wuya sai dadi. Ina so
ku ci gaba da tayani addu'a Allah ya bayyana
mini tahir, ba zan iya barin dakina da nake da
yanci in tafi in da bani da yanci ba. Ummi ta ce
kina da gaskiya Rabi'a insha Allahu tahir zai dawo
ku ci gaba da kyakkyawan zamanku. Bashir dai
tagumi yayi ya kasa cewa komi.
Har aka share makikin hajiya yaya tahir bai dawo
ba kana danladi bai daina yiwa Rabi'a barazanar
ko ta yarda da shi ko kuma ya shirya mata
sharrin da ba zata iya fita ba. Yau da ya lallabo
ya shigo dakin tsakiyar dare dama ba wani barci
take ba tana zaune kan abin salla ta idar da
nafilfilnta tana adu'o'i ya zuba mata harara ya ce
ke in dai fa kina cikin gidan nan sai na cimma
bukata a kanki. Ta yarfa mai itama hararar ta ce
to wai waye ya hanaka yin abin da kake so? Na
sai dai tunda kai baka jin tsoron Allah ka iya
fyade? Kuma kasan ba fin karfinka zanyi ba,
mene ne na zama neman yarda ta? Ba sai ka yi
min fyade ba. Haka kika ce ko? Ta ce eh haka na
ce. Ya kyalkyale da dariya ya ce yaro dai yaro ne
tabbas kuma na iya fyade yau za ki ga fyade yau
zaki gane kuranki tausayinki nake ji shi yasa nake
lallabaki. Ta ce karya kake kace kana jin
tausayina. Babu rashin tausayi da yafi abinda
kake nuna mini ka ki ka barni inji da bakin cikin
bacewar mijina babu wanda ya damu a cikinku
saboda ba kaunarsa kuke ba. Kullum sai ka zo ka
daga mini hankali to ka sani ban hanaka aikata
abinda ka so da ni ba sai dai wlh ba zan yi
kaffarar wannan rantsuwa ba in har ka isa gareni
ka keta mini mutuncina sai na luma maka wuka a
ciki, sharrin da kace zaka yi mini na kashe hajiya
yaya kisan ya tabbata a kanka in yaso nima a
kasheni. Abin mamaki sai taga jikinsa ya yi sanyi
baice da ita komi ba ya juya ya bar dakin. Ta
fada kan gado ta runtse ido tana mai godiya ga
Allah da ya bata karfin halin da ta yi maganin
iskancinsa. Duk abinda take fada karfin hali ne
da karfin adu'ar da take ba abin da zata iya.
Tabbas in banda karfin addu'a da tuni danladi ya
samu kaiwa gareta a yadda yake nuna zalamarsa
karara a kanta ko kunyar mutannan gidan baya ji
su kuma da yake munafukai ne ana jin tsoronsa
babu wanda ya tba magana akan haka sai abinda
bai dace a yi magana a kansa ba sai suka iya.
Tun da aka gama zaman makokin hajiya yaya aka
sake sabon babin yiwa Rabi'a wukanci a gidan
ganin ba idon tahir dama dai dije da ladidi na
raga mata ne saboda shi tun tasowar tahir a
gidan duk abinda na ke masa yana kauda kansa
a kan Rabi ne kawai bai da hakuri. Ita kuma ta
kudiri niyyar babu inda zataje tana nan tana
adu'ar duk inda mijinta ya shiga Allah ya dawo
mata da shi su ci gaba da zaman soyayyarsu.
Duk bacin ran da take sha a gidan dai dai da
rana daya tahir bai taba fita daga ranta ba,
kullum ta zo kwanciya barci sai ta yi kukan rashin
sa a kusa. Sai ta tuna wani abu wanda ta yi ya
tsaye mata a rai na faranta wa a iya zamansu da
tahir ba za ta iya fadar wani lokaci da wanda ya
bata mata rai da gangan ba. Sai dai cikin rashin
sani da sabani na zaman yau da gobe, wanda
soyayya komi karfinta ba ta iya maganinsa. Ko ta
yini da karfin hali in dare yayi sai ta yi kukan
zuciyarta na son tahir saboda kyawawan
dabi'unsa da hakurinsa da soyayyar da yake
mata da uwa uba addini. Ta daukarwa kanta
alkawarin ba zata nuna gazawarta a gun abbanta
ba ya samu abin yi mata dariya, ummi ta aiko
mata da kudi masu yawa da kayan abinci a boye
ta ce duk abinda take so tayo mata waya. Itama
ba ta son Abban ya gane karayarta ta gargadi
fatima da bashir.....


Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100



Launin Fata 2-02
Posted by ANaM Dorayi on 11:21 AM, 20-Oct-15
Under: Launin Fata
Kada wanda ya gayawa abban bacewar tahir.
Dan haka Abba bai san abinda ake yi ba, tun
tana bakin cikin abinda ake mata a gidan nasu
har ta fara sabawa matsalarsu ta daina damunta,
aiki ne in an sa ta wanda ta ga zata iya tayi
wanda ba zata iya ba sai ta shige dakinta ta
kullo, Dije tayi masifar ta ta gama wanda taji ta ji
wanda ba ta ji ba oho. Abincin da take dafawa
kansa ba ci take ba yadda ya kama ta ballantana
nasu. Abinda ta fahinta shi ne suna so ta bar
gidan, hakan ya bata kwarin gwiwar ci gaba da
zama a gidan ko da yaushe haka za a yi tayi
mata habaici da cin fuska iri iri bata taba
tankawa wani ba. A haka har cikinta ya shiga
watanni haihuwa a lokacin nan watannin tahir
hudu da bacewa, duk abinda za a bukata ummi a
kawo mata ta shaida mata da taji nakuda ta yo
mata waya zata taho da nurse. Sai da ta shafe
wata na goma kana a wata safiyar juma'a ta
tashi da ciwon haihuwa. Tun tana karama Rabi
tana da dauriyar ciwo, haka ta yini ita daya a
daki tana fama sai daf da la'asar ta kira umminta
awaya ta gaya mata halin da take ciki. A kai rashi
sa'a Abba yana gida ta ce zata je gaida kawar
babarta ya ce sai dai gobe yau yana da baki baya
son su zo basa nan, hankalin ummi ya tashi ta
san ba yadda za a yi abba ya bari taje gun Rabi'a
in ta gaya mai gaskiyar lamarin, ta kira fatima ta
gaya mata ta ce to ummi duk ba ita ta jawo
kanta ba.Ta ja tsaki ta mike ta rasa a bin yi ta
kira Rabi'a Rabi'a ta kasa daga waya saboda tana
cikin mawuyacin hali ga haihuwa shima. Ta gaji
taje ta samu Abba a falo ta fito ta gaya mai
gaskiya. Ya mike zaune ya galla mata harara ya
ce amma ke baki da da tunani yarinyar da ta
nuna mijinta ya fimu ita zan bawa wani taimako
a gidana. Ummi ta marairaice murya ta ce Abba
Rabi'a bata nuna mijinta ya fimu ba ka yi hakuri
ka barni in je. Ya ce to ina mijin nata ta kasa
magana ya ce to ba inda zaki je. Ya mike ya
ficewarsa ya bar ummi kamar ta hadiyi zuciya
dan takaici sai tayi alwala ta yi sallah la'asar tana
adu'a Allah ya sauki yarta lafiya ta ce ko naje ko
banje ba babu abin da zai sauya.Rabi'a na daki
ita kaidai duk da mawuyacin halin da take ciki
bakinta bai daina furta salati ba, karfe 5 na
yamma ta haifo santaleliyar diyarta mai kama da
tahir sak har fatar. Ga dai Rabi'a fara kal amma
yarta baka sai dai hasken fuska irin na jarirai, da
yar da mahaifar haka suka fado gaba dayan
Rabi'a ta godewa Allah jikinta sai rawa yake bata
san yanda ake komi na haihuwa c ga ya na
kwance a tayal tana ta tsala ihu. A tsakar gida su
dije na zaune a na ta shewa hansai ta ce kai ku
dakata ni fa kukan jariri nake ji. Ladidi a ce kar
dai waccan munafukar yar ce ta haihu. Dije ta ce
anya kuwa zata iya haihuwa ita kadai haihuwar
fari saratu ta ce tabdijan Rabin mugun abin da ke
cikinta yayi yawa sai ta haihu mana. Bata gama
rufe baki c suka ga rabi'a ta fito daga daki duk
jikinta jini ta iso gabansu ta ce dan Allah ku
taimaka mini ana haihu. Dije ta yi mata wani
matsayacin kallo ta ce aikin banza sai yanzu kika
san da neman taimakon namu? Saratu ta ce to
yaya za mu yi dole a yankewa ya cibiya dan kar a
samu a bakin duniya. Dije ta ce tabdijan sai kije
ki yanke ni dai ba ruwana tunda ta iya haihuwa
da kanta har yanke cibiyar ma sai ta yi. Saratu ta
jima tana tausayin Rabi'a bala'in dije take gudu,
ita da hadiza suka shiga dakin Rabi'a suka yi
mata duk abin da ya da ce.Har kwana bakwai ta
cika abba bai bar su ummi sun zo ganin Rabi'a
ba ran ummi gaba daya ya gama baci, hatta
fatima na son ganin yar uwarta sai dai waya duk
hakurin ummi sai da suka yi rigima da abba ta yi
kuka mai yawan gaske shi kuwa ko a jikinsa ya ce
ai tunda rabi'a ta auri bakin mutum talaka ba
shiga lamarinta sai dai bai hanata zuwa gidansa
ba amma shi da iyalansa ba zasu je inda take ba.
A waya ummi suna magana da rabi'a tana kuka
ta ce Rabi abbanku ya hanamu zuwa mu ganki ta
ce subhanallahi shi ya kike kuku ummi? Ta ce to
ya ba zanyi kuka ba rabi'atu ko a gidan da ake
kaunarki kike zan so in ganki in ga lafiyarki da
abinda kika haifa ballantana a gida irin wannan
ko mutum shiga ya yi ya fita a wannan gida ya
san ba a kaunarki, haihuwa ko ta nawa zaki yi
kina bukatar kulawarmu ballantana haihuwar fari
da baki san komi ba akai ba? Rabi'a ta ce dan
Allah ummi ki daina kuka, wannan kukan naki shi
zai tayar mini da hankali fiye da rashin
zuwanku.tun da Allah ya saukeni lafiya Allah ya
sa tausayina a zuciyar wata baiwar Allah a gidan
nan sunanta saratu matar wan mahaifin tahir ce
tana kula dani yanda ya dace. ummi tace
Alhamdulillah dama haka sha'anin ubangiji yake,
ki kara hakuri kan wnda kike yi insha Allahu
alheri zai zame miki, Allah yana tare da masu
hakuri kamar yada ya fada a cikin alkur'ani
maigirm. bayansuyi salama rabi'a ta ajiye waya
jikinta a sanyaye ta dauki bebi ta wanda ke cikin
kayaan sanyi yana ta kamshin turare, hawaye ya
dunga zuba a idon rabi tunda ta haihu sai yau
tayi kukan bakincikin gorin da ake mata a gidan
nan ya isheta, su dije sun sami nayi har waka ake
mata atsakar gida wai bata da kowa tun da ta
haihu ba wanda yaxo daga gidansu gidan nasu
ma bakaunarta ake ba. maganar bata taba
damunta ba sai yau takai idanunta ga yar bebin
ta maikama da mahaifinta tahir sak, ta tuna wa
tarana da tahir ya sameta kwance tana shan ice
cream yace haba rabi'a yaya kina da ciki kike
shan kayan sanyi?Saratu ta shigo tare da baffa
ibrahim babban wan mahaifinsu tahir ta ajiye
baby da sauri tasauko kasa ta gaida shi ya ce kiyi
hakuri ki daina kuka yar nan insha Allahu Allah
zai bayyanar da mijinki muna ta adu'a.
Saratu ta miko mai yar yace akwai wani suna da
tahir ya taba nuna miki yana sha'awar sawa idan
ya haifi mace?
Ta girgiza kai ya ce to ke kina da zabi?
Nanma girgiza kai tayi.
Ya ce

Please Login or Register in order to submit comment