Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasan nabila
tayi mujin nunawa agari mijin takama ko me
yasa yarinyar nan take da yawan sa'a a rayuwa
ne.
Tunanin su kenan, hankalinsu bai gama tashi ba
sai da amir ya fiddo damin kudi ya ajiye a
gabansu ya ce su rabama yara suka fice suka
barsu nan zaune babu mai iya magana.
Inna tashige daki gun nabila tace tabbijan
wanan shine mijin naki, wanan ai ba bahaushe
bane.
Nabila ta ce eh ba bahaushe bane balarabe ne.
Tace masu gari sai kifita kada su gaji da jiranki.
Tuni ta tsala kwalliyarta tafito tana takun kwas
kwas ta wuce su lalididi duk an rude ginin kudi
ga matsanancin bakinciki dake damun
zuciyoyinsu.
Dije tace uhm da can anyi mana yanga da jin kai
balantana yanzu?
Naji baban nata na cewa in an gama bukin
kasar waje zasu tafi ta ci gaba da karatu.
Lubabatu tace ku raba muna kudin nan nasan
inda zani wanan kudin dasu za a tarwatsa
wanan auran ba zai yuwu muna zaune wanan
matsiyaciyar yarinyar ta samu cigaba haka ba.
(KUJI WATA WAUTAR KUMA)
Nabila ta iske mujahid da amir kishingide a
bayan mota yau direba ne ya jawosu, ta rusuna
ta gaidasu, mujahid ya gabatar mata da amir a
matsayin baban amininsa, itama ya gabatar da
ita a matsayin matar da zai aura ga amir din.
Yace to muwuce ko amir.
Amir ya gallamai harara ya ce wane irin zance
ne haka daga zuwan mu zakace mutafi har an
gama hirar.
Ya yatsina fuska kaima kasan ba wani iya hira
nayi irin wannan ba tunda mun gaisa ba shi
kenan sai mu tafi ba.Ranta ya baci har kunyar
amir taji tace to sai anjimaku.
Kansuyi magana ta koma cikin gida, amir yace
wai dan Allah wane irin mutun ne kai?
Matar da za ka aura din ma baka iya zama ka
lallasheta ku shaku da juna ku fahinci juna wane
irin zama ne za ayi irin wannan tsarin naka?
Mujahid ya tsuke fuska yace amir kafin kowa ya
san dalilin wanan neman auran nawa?
Lifiya kalau kasan yanzu ina 25 ba zancen zan yi
aure ba babu yanda zanyi in nemi auran
karamar yarinya kamar wannan ko da auran
zanyi, baban ta fa ya ce mun duka duka
shekararta goma sha shida to me zan tsinta a
jikinta.
Amir yace kai mujahid kada ka auri yarinyar nan
dan ka cutar da ita, nasani ba zata iya tsallake
fadawa cikin kogin soyayarka ba lokaci daya zata
kamu da sonka alhalin ka yadda ka dauketa a
cikin zuciyarka.Ina tausayin yarinyar nan da
wahala ta jurewa tantirancinka da budewar
idonka..
Mujahid yace wai kai meye ka daukeni ne,
abinda nakeso ka gane ina sha'awar sufofin jikin
yarinyar sosai amma ba zan iya anfani da ita a
yanzu ba saboda bata gama cika mace ba.
Shekarunta na da rauni ba za ta iya daukar
rigimata a fannin saduwa ba kaima kasan irin
matan da nake ma'amala dasu ba irin
wadannan matan bane na garinnan, kuma ba
yarinya kamar nabila ba.
Amma nasan in tana gidana akwai lokacin da
zatayi cikar da zan kwanta inyi sadu da ita
yadda nake so.
Amir yayi tsaki yace nifa duka wannan ba shine
damuwa ta ba ina nufin kada ka tafi da yarinyar
nan ka cutar da rayuwarta ta hanyar kin kulawa
da rayuwarta ta yan da ta dace. Yace a a
wannan kar ya dameka duk abin da nasani na
bukatar rayuwa wanda kudi ke iya saya zan
mata, a bin da nasani yanzu ba zan iya ba shine
zancen soyaya kasan ni bana son raini daga diya
mace,sukuma mata raini garesu da zarar kafito
ka nuna kana sonsu shi ke nan sai su raina ka,
ban saba zuwa ince ina son mace duk macen da
ka ganni da ita ita ta nuna bukatarta a kaina
idan naga tayi mun in amsa tayinta in bata yi
mun ba in fito in gaya mata ta kama gabanta.
Amir yace ni kaina ina ganin bai dace ka auri
yarinyar nan ba kana da wannan tsarin ba.
Yace mutafi dan Allah na gaji da wannan
maganar.
Bakincikin nabila na yau yafi na jiya, inna lilliahi
wa inna iliaihir rajun, ta shigo gidan tana
karantawa ta wuce matan gidan anata kasafin
kudi ta shige daki ta zauna ganin inna bata
dakin yasa tayi tagumi, babu yadda za ayi ta
kubucewa auran mutumin da baya sonta tunda
babanta ne ya kawo shi ya ce ta aureshi, ko zai
dinga yankan naman jikinta ne in an kaita
gidanshi ta amince ya yanka in har ran babanta
mahamud zaiyi fari ta ci gaba, mahmud ko
shine ya haifeta ya ci tayi mai biyaya balantana
ba shi ya haifeta ba yake nuna mata soyayar da
bai nunawa yayan da ya haifa da cikinsa.
Sannan tana matukar son mujahid son da bata
taba tunanin zatayiwa wani da namiji ba a
duniya.




Zaharaddeen Shomar

Whatsapp 08168575100



Launin Fata 2-06
Posted by ANaM Dorayi on 07:13 PM, 22-Oct-15
Under: Launin Fata
Wadannan dalilai 2 suka sa ta amince zata auri
mujahid zata amince da duk wata fitina da zata
gani a gunsa kuma bazata bari wani ya gane a
kwai matsala tsakaninta da mujahid ba.
karfe goma sha 2 dare mujahid ya mike daga kan
gadonsa ya dubi amir wanda yaketa bacci yayi
murmushi yace, da raina da lafiya ban iya ina
kwanciya ina barci nikadai a kan gado.
Ya shige toilet yayi wanka ya tsuke cikin kananan
kaya ya baza turare ya dau key din mota, mai
gadi ya daga mai get ya finciki motarshi ya bar
gidan.
Gidan budurwarshi ilham yaje cikin unity road,
yayi fakin a kofar gidan ya kira ta waya.
Yace ke da waye yanzu?Tace ba kowa sai
kanwata zeenat .
Yace to fito ki bude mun get inan kofar gidanku.
Ta buga tsalle tace dan Allah in zolayata kake
kabari kada kasa zuciyata ta buga, babu wata
macen da take da tagomashin kaje gunta da
kanka sai dai kai aje a sameka.
Yace ke ni bani son surutunki ki zo ki bude mun
get.ta watsar da wayar ta fito sai da ta ganshi ta
yarda shi din ne, aka fara watsewa.
Daya daga cikin abin da yasa mata suke son
mujahid da sha'awarsa ya mugun iya soyaya duk
bacin ran da mace ke ciki idan tazo hannun
mujahid yanzun nan so yayayr sa zai sa ta manta
a duniyar ma da take balantana ta tuna wata
damuwa.
Idan mujahid ta tashi farkon abinda zaiyiwa mace
shine yayi mata wata runguma kamkam wace
zatasa taji kamar numfashinta zai dauke,kana zai
dinga bata hot kis ta ko ina yana mata wata irin
busa a kunne, lokaci guda zakaga mace ta fita
daga haiyyacinta, kuma a tsaye zai mata haka sai
ya gama gala baitar da ita a haka kana ya
kwantar da ita. . . . . . . . . . Abin da bai amince
ya bata lokaci a kai ba shine zancen soyaya.
Sai yaga mace bata da tagomashin da zai zauna
yana rokonta ta soshi ko wacece ita din kuwa
idan ma ya lura tana da rawan kai ko yanga da
jan aji sai ya san yanda ya rumgumeta ya hadata
da wannan salon nashi kawai sai kaga mace ta
ajiye yangar nan da dukkan jin kan ta rusunar da
kanta gareshi tana rokon suyi soyaya kawai.Idan
mujahid yayi anfani da mace sau daya shi kenan
ya rabata da duk wani jin dadi a gun wani namiji,
bata iya tunanin wani sai shi, shi yasa duk inda
yake zakaga mata na binshi kamar jela.
Wanna ne ya zamo sanadiyar da bai iya bin mata
mace da kansa ya ce yana son ya saba sai dai a
zo gareshi asamu ya kula matsayi ne, domin a
gun mace a ganta da matashi wanda ya isa
matakin rayuwa kamar mujahid ba karamin
cinyewar bane ba karamin daukaka darajarta da
ajin ta na rayuwa bane,kuma duk inda mace ta
kai da dajarabarta mujahid yasan yadda zai kosar
da bukatarta taji ta gamsu, mujahid jarumin
namiji ne shiyasa yake ji da kansa, dan shima
yasan ya gama haduwa.
Dan gatane sosai a gun iyayensa ba su son
damuwarsa shine dalilin da yasa suka hakura ya
nemo matar da yake ra'ayi da kansa ba su bashi
zabin su ba.Lokacin da yake kasarsu bai sa fitinar
mata a ransa ba, sai da yaje maleshiya karatu
matan da kansu suka bude mai ido har ya kware
da neman mata, sabo da dai sun ganshi yaro
matashi mai jini a jika gashi ko a ido yana da
sifar jarumin maza, dan haka ko mace bata dan
danashi ba in ta kalleshi ta san za a huta a
jikinsa, ga uwa uba naira.
Matan wannan zamanin babu abinda suke so a
tare da namiji sai kyau da naira idan namiji ya
mallaki wadannan abubuwan sun amince yayi
musu ko wane irin wulakanci za su bishi a haka
(amma wasu fa hakane ?)
Saboda mujahid bai san zafin naiman kudi ba
ajiye mai su kawai ake shi yasa bai jin zafin yin
kyauta ko da na wace.
Zai baiwa mace in dai zai ji dadi a jikinsa zai cika
mata jaka da naira, tayaya ba za a dinga binsa
ba.
Tun baifi shekara daya a malesiya ba ya zama
kwarare a harkar mata da kora barasa, amma
yasan yanda yake tafiyar da rayuwarsa yanda
yake mu'amala da mata da barasa ba kowanne
zai gane hakan ba.
In ka ganshi ba zaka taba cewa yana wannan
halaiyar ba in gaya maka akayi ka iya cewa
shairi ne wannen ne ma yasa hankalin iyayansa
yake kwance da zamansa a malesiya basu
girgiza hankalinsu ya tashi ba sai watarana da
abbansa ya kai mai ziyarar bazata a gidan da
yake a malesiya ya iske mujahid din kwance a
falonsa daga shi sai wani mi tsitsin pant wata
budurwa tana mai tausa yayin da wata take
dakin baccinsa itama tsirara tana jira a gama da
ta falo a dawo kanta, ga kwalbar barasa birjik ya
sha ta isheshi.
Lokacin da suka hada ido da mahaifin nasa
zatonsa mafarki yake dan haka ya ture hannun
budurwar tasa mai suna laila ya mike zaune
yana mitsitsike idanunsa, abba nashi na tsaye
ya rumgume hannuwa yana kallon dan sa
mujahid.
Duk fitinar mujahid da taurin kansa yana tsoran
iyayansa bai son abin da zai bata musu rai.
Laila ta shiga tambayarsa waye wannan, ya
buga mata tsawa cikin harshen turanci ya ce
mata maza ta bar gidan babanshi ne ya zo.
Ta barmar kunya da hauka ake nadeta abin da
yayi kenan, abban nashi ya zare mai ido ya ce
kai shiga hankalinka kada ka wulakanta yar
mutane a banza da me yasa a kirawota, ba ni
ya dace kaji tsoro ba Allah da ya halicceka ya
dace kaji tsoro wanda shine ya haramta abinda
kake aikatawa.
Abin mamaki da takaici ga aban shine yadda ya
ga wata macen ne tafito daga dakin barcin
mujahid tsirara daga ita sai dan pant da bra
tana wata irin karairaya tazo ta dafa shi tace
lfy?
Ya hankadata itama ta fadi kasa.
Abban ya buga mai tsawa yace kai kada ka
karya yar mutane a banza ni kaga tafiyata ka ci
gaba da abinda niyya tunda shi ya dace da
rayuwar musulmi kamar kai.
Yafice daga gidan alokacin yasa aka shirya jirgi
ya bar kasar hankalinsa a tashe game da halin
da ya iske danshi.
Ya dawo da mahaifiyar mujahid labari mara dadi
tace alhaji babu abinyi illa ayiwa yaron nan aure
a kai mai mata can shine zai rabashi da bin
matan banza.
Yace nima tunanin da nake kenan sai dai kinsan
mujahid da taurin kai ya iya cewa baya so?
Sai dai mu bashi damar lallai ya kawo matar da
yake so da kanshi a aura masa ita ko a bashi
duk wacce ta samu.
Mujahid a wannan rana ya kwana ne cikin
matsananciyar damuwa duk yada ya tsani
kwana shi kadai a kangadonsa ba tare da mace
ba haka ya kwana a ranar yana juyi ya tsani
abinda zai bata ran iyayansa.
Duk in da ya dace ya ga mahaifinsa sai da yaje
bai sameshi ba ya tabbatar juyawa yayi ya bar
kasar ya kasa kiranshi a waya dan yana jin
tsoron abin da za a ce da shi.
Gaba daya jikinsa yayi sanyi yasan tilas sai wani
abu mara dadi ya biyo bayan wannan ziyara ta
bazata da aka kawo mai
tundaga ranar ya dan ja baya da mata da
barasa ya rage bai dai daina gaba daya ba.
Aka shafe sati daya bai naimi abba da umminsa
a waya ba shima babu wanda ya nemeshi
alhalin da kullum sunyi magana, in shi bai
nemesu ba su zasu nemeshi suji ko yanada
wata matsala.
Yayin da kullun abbanshi sai ya kirashi da asuba
yace ya tashi yayi salla.
Shi yasa duk yanayin da yake ciki da mace idan
asuba ta doso zai koma cikin natsuwarsa abu a
muryarsa tundaga wannan rana da abba ya
ganshi bai kara kiransa ba, dama amir ya sha
gaya mai idan bai daina abin da yake ba
iyayanshi zasu kamashi watarana.
Yayi dariya a lokacin yace haba kamar wani
yaro?
Amir yace iyayene fa sunfika wayo da iya zaman
duniya duk budewar idanuwannan naka a tafin
hannunsu kake.
Bai dauki maganar amir da wani muhimmanci
ba sannin cewa abin da yake fada ba me wani
muhimmanci ba ne, bai tashi tunawa da haka
ba sai ran da abbanshi ya kamashi dumu dumu,
kuma yayi mai abinda ya tsana wato ashareshi
ba a ce mai komai ba har gara ayi mai fada, ko
a dakeshi ma da wannan shurun da akayi mai
bai san matsayinsa a gunsu ba bai san hukuncin
da aka yanke mai ba.
Ranar da sati biyu ya cika hankalinsa ya gama
tashi abisa dole ya ajiye komai ya nufi kasarsu a
can ya iske amir yayi mamakin hakan zuwansa
bai ba iyayensa mamaki ba shima bai mamakin
kin sakar mai fuska da ummi da Abba sukayi ba
a ranar da ya sauka yana gidansa shi da amir
yayi tagumi gaba daya ransa abace yake, amer
me abba yace maka game dani?
Amir yayi dariya ai kiran da yayi min nakane
saboda kai din yace in ajiye komai inzo yana son
ganina.
Gabanshi ya fadi ya matso kusa da amir yace
me yace maka?
Amir yace abinda nake ma fada a kai baka
daina ba shi ya kirani ya tambayeni dama can
halaiyarka haka take ko daga baya ka fara.
Idanuwan mujahid suka fito waje yace sai kace
me amir?
Ya tamke fuska.
To me zaince inbanda in gaya mai gaskiya,
kokuwa kana ganin zan iya yiwa abba karya ne?
Ya girgiza kai.
A irin fahimtar da abba yayi mun ba zai yuwu in
boye mai gaskiya ba dan ya hadanine da girman
Allah da darajar manzonsa in gaya mai gaskiyar
abin da nasani na halaiyarka matsayina na
amininka wanda yafi kowa sanin sirrinka ciki har
su da suka haifeka.
Na rasa amsar da zan bashi a lokacin yace amir
kaji tsoron Allah ka gaya min gaskiya ka ci
amanata.
Nantake na gaya mai yadda ka koma tun
komawarka malaisiya ban taba ganin
damuwarsa irin wannan rana ba.
Ya jima zaune tsit daga bisani yace amir tunda
kake tare da mujahid kataba jin macen da yace
yanaso?
Nace gaskiya ban taba jiba dan nasan
yammatan dake rububin sonsa, yace akwai
wacce ya taba nuna sha'awar zai aura?
Anan ma nace ban taba gani ba shi da yake
cewa sai ya kai shekaru arba'in zaiyi aure.
Abba yace wannanan karon zan fuskanci abinda
bai so zan masa aure ko yanaso ko baya so ba
zan zuba mai ido dan ina da kudi ba na sakar
mai kudi ya dinga sabon ubangiji da su.
Annan na shiga lallashin abba da yayi hakuri ya
barka ka kawo mata da kanka kada ya ce zai
baka mace da kaanshi, saboda idan yabaka
mace da kanshi abin da zai faru shine matar
tana ganinka zata kamu da sonka kai kuma bai
zamo dole kasota ba zata sha wahalane kawai a
kanka azo a bata goma daya bata gyaru ba, har
gara in kai kanemoi ko baka sonta sosai da
sauki a akan wadanda bakaso kwata kwata.
Abba dai ya amince da hujjata yace zai baka
zabi cikin kankanin lokaci, yace zai aikeni in gaya
ma hakan sai gashi Allah ya kawoka.
Innalillahi wanna ilaihi'raju'un.
Mujahidke fadi yana fadin na shiga uku ni nura
ina ni ina aure yanzu?
Amir yace nura aure lokaci gareshi lokacinka ne
yazo sai dai kayi hakuri.
Kwana sukayi yana nanata maganar da gari ya
waye ya shiga gidansu a dakin mahaifiyarsa ya
iskesu tare da abba yana mata bayani yadda
sukayi da amir a jiya.
Ya zauna a kasa yana gaidasu, abba yace dole
kaji kunya mana, kowa ya gyara ai ya sani haka
in sabanin haka, hakika nayi mamakin haka
saboda ban taba zato ba, bamu kasabawa ba
Allah da ya halicceka ka sabawa ka roke shi
gafara, mu dai hukuncinmu a nan zakayi aure
abokinka amir ya bukaci mu baka zabi to mun
baka watanni uku to kaka wo mana matar da
kake so kuma ka tabbatar kakawo wadda zamu
amince da ita da iyayenta ita ce wadda zata
dace da rayuwarka.
Mujahid ya baro kasarsu ya dawo malesiya da
muguwar damuwa da tunanin yadda zaiyi, zahiri
da badini baya son yin aure a wannan lokacin
dan a ganinsa ba karamin takura zai zamo mai
ba da sa ido.
Bayan wata biyu da yin haka yasa mu hutu baije
kasarsu hutun ba saboda fargabar abinda zaije
ya taras, gashi saura wata daya cikar wa'adin da
abbansa ya dibarmasa baiga ko alamar matar
da zai aura ba shine dalilin da yasa ya nufo
kano hutu.
Aranar da ya sauka kano airport ya hadu da
laila ta dawo daga lagos suka mannewa juna bai
nemi gidansu amir ba inda yake sauka in yazo
kano sai da yayi kwana uku suna lalacewarsu da
laila da kyar ta amince suka rabu kamar zatayi
hauka a kansa ga iya soyayya ga kudi.
Lokacin da ya dora idonsa a kan nabila kai tsaye
ya amincewa zuciyarshi zai aureta, amma fa ba
soyayya ta sosai a ransa dan shi bai iya soyaya
ba zallar sha'awa da fitina a kan mace na
tashan samartaka da naira kadai ne a kansa.
Sai karfe hudun asuba ya saki laila tana
nunfarfashi shikam bacci mai dadi ya shiga yi,
laila na kallonshi kamar zata lasheshi dan
masifar so da sha'awa Laila shaidaniya ce
idonta ya bude sosai da bariki tana harka da
alhazawan birni masu ji da kansu amma babu
wanda ya taba gamsar da ita kamar mujahid,
gata dai yarinya duka bata fi shekara ashirinba
amma ta iya salo salon da wadda ta haifeta a
bariki bata iya shi ba.
Duk wannan shai dancin nata mujahid ya kere
mata gudu ya sha gabanta ta ko ina.
Tana zaune tayi tagumi tana kallon mujahid taji
wayarsa tayi ringing ta dauka taga ansa abbana,
ta girgiza kafadar mujahid da karfi ta tashi da
sauri jin ringing din da yasa a kan wayan
mahaifinsa yasa ya mitsitsike idonsa ya nutsu ya
amsa da sallama.
Abban nasa yace nura katashi kayi sallah
kokuwa kana nan kana ta barcin?
Yace abba bansan na makara ba yanzu zanyi.
Cikin taushin murya yace nura ka rinka rage son
duniya ba ko mai a cikinta sai rudani na rashin
tabbas.
Kayi kokari ka rike addininka da gujewa sabon
Allah, ka tuna komin dadewa.....




Zaharaddeen shomar

Whatsapp 08168575100






Launin Fata 2-07
Posted by ANaM Dorayi on 09:37 AM, 23-Oct-15
Under: Launin Fata
Katuna komin dadewa zamu hadu da Allah kowa
sai yayi bayanin abinda ya aikata da kansa ranar
gaskiya da gaskiya.
Mujahid yayi tsit tana sauraran abbansa jikinsa
gaba daya yayi sanyi har bayan sunyi sallama ya
ajiye wayar bai iya tashi daga gun ba, sai da laila
ta kwanto kan ciyarsa ta bayansa a zaune, yayi
ajiyar zuciya ya mike yayo sallah yayi tagumi laila
tazo gabansa itama tasha kwalliya ta zauna ta
meke kafa tace nura me abbanka ya gaya ma da
ya sauya ka cikin gaugawa haka?
Cikin sanyin murya yace laila abbana yayi mun
nasiha ne na inji tsoran Allah in rike addinina in
daina aikata sabon Allah, kana in dunga tunanin
ranar da zan hadu da Allah.
Zamuyi sallama dake yau dan aure zanyi iyayena
basa son abin da nake.Ta dafe kirji ta
kankameshi tace dan Allah mujahid kada karabu
dani ina sonka fiye da yanda nake son kainama
ka taimaka ka aureni ka cece rayuwata zan bar
wannan harka.Ya mike ya ajiye mata makudan
kudi yace laila kada kisawa zuciyarki zaki sameni
dan ba zaki sameni dinba kiyi hakuri Allah ya
dubi niyarki ta barin sabon Allah ya baki mijin da
ya fini ko mi a rayuwa.
Yafice da ga gidan ya bar laila tana faman kuka
Afalon sashin amir na farko ya iske amir don
kwance yana bacci ya girgiza mai kafada ya mike
zaune cikin magagi yace daman mafarki nake
baka nan?
Yace kai da Alla can sarkin magagi dawo cikin
natsuwarka.Amir ya mitsitsike ido yace nasan da
gaske bakakwa kana gidan nan ba Allah yasa
nabila na da juriya bata da fitinar sha'awarka.
Ya yi tsaki ya shige daki ya fada kan gado sai
bacci.
kanin mahaifin mujahid dake zaune da iyalansa a
nan kano shi ne suka gabatar da komi tare da
Alhaji mukutar na neman aure bisa al'adar
kanawa kenan mahaifin mujahid yaji dadin yanda
kaninsa alhaji muhammadu mustapha ke
bayyana mai nagartar gidan da mujahid ke
neman aure, haka nan mata sun shai da masa
yarinyar kyakyawar gaske ce kamar larabawar ce
suma ko da yake anshaida musu mahaifiyar
yarinyar balarabiyar kasar yemen ce gaba da
baya.Har suka tura masa hotunanta ta wayar
mahaifiyar mujahid tayi farin cikin hakan sosai
haka nan taji tun a hoto tana kaunar yarinyar
basu da fargabar ko mi a kan batun soyayar
dansu a zuciyarta dan sun amince da dansu abin
so ne a duk inda yaje kyawun hali shine abun ji,
sun amince ta hada jini da ita.
Duk shirye shiryen da ake na auran amir ke
gabatar da ko mi ga amarya da kawayenta babu
abin da ya damu ango iyaka yaxo su gaisa yayi
tafiyarsa.Abu biyu ya hadawa nabila soyayya da
damuwa.
Son mujahid na cin zuciyarta tana fama kullun
dare darana da wahalar ciwon sansa, damuwar
rashin kalawarsa da ita ta hanata
sukuni.Kawayenta irinsu fauziya fadi sukeyi
masha Allahu har innice na dace da miji irin
mujahid koda yankan naman jikina ma shi zaiyi
din dan rashin kulawa ai zan zauna dashi.idan
damuwar rashin kulawarsi ta dameka sai ka tuno
kyan kyawun idanunsa su kadai sun isa su
mantar da mace duk wata damuwa da ta
shafeta,balantana in ya budi baki yayi magana
tautausar muryarsa ta ratsa sassan jikin
mace.wannan shine tunanin mafi yawa a cikin
kawayenta, wasu kadan ne da suke ganin jin kan
mujahid yayi yawa.Nabila tana da kyan da namiji
dole ya kalleta ko da bai son mata amma shi ina
kudi dai gasu nan ba matsala.
Ko wayar hannu irin mai masifar tsadan nan ya
aiko mata musanman ya bada oda aka kawo
maiita ya ba amir ya kai mata dan in yana son
magana da ita ya kirata waya ce wadda duk
wanda ya ganta yasan ta hadu.
Lokacin da aka kawo kayan lefen nabila mutanen
gidansu cewa sukayi wata kila mujahid dan
yankan kaine saboda uwar dukiyar da aka kashe
a kayan, sai kace ba asan ciwon kudi ba.
Akwatuna ne set biyu kowanne sai guda shida
ba yawan akwatunan bane abin kallo a a kayan
da aka danno a ciki atamfofin da leshi leshi da
shaddodi kamar suyi magana, gold kuwa wani
karamin kit aka ciko da si abin ya wuce ayi
magana ga hassada sai dai shuru kawai ana
gyada kai.
Lubabatu tayi tagumi tana ta kaicin kudin da ta
kashe a gun bokaye ana ce mata ba za ayi
auren nabila da mujahid ba ko yaushe sai ci
gaba magana take.
Su kansu yan kawo kayan sun fahimci mutanen
gidan ba kaunar nabila suke sosai ba, saboda
basuyi masu tarba da ta dace ba.
Aranar mahassada irinsu Dije kamarsu hadiyi
zuciyarsu su mutu.Washegari aka fara buki
aranar ne iyayen mujahid da manyan abokansa
suka iso kano duk dacewa anyi abubuwan ne a
kuraran lokaci duk da hakan abubuwan suntafi
cikin burgewa da ban sha'awa.
Masu bakin ciki sai dai rusa kuka kawai duk duk
yanda suke zaton daukakar nabila ta samu ya
wuce nan, mutum ba zai gama fahimtar hakan
ba sai aranar alhamis din nan da aka shiga
gaggarumin fatin manyan baki da kowa da kowa
ya halarta su dije sunce ba inda zasu basu saba
ganin irin wannan watsewarba, yaya da iyaye
sai tafiya wai party daga baya kuma suka gagara
dai basu iya zama ayi babu su suka shiga wata
jibgegiyar mota mai numfashi sanyin AC na
ratsasu aka kaisu wani kayatacen hotel a nan
kano inda akayi party.
Anan sukaga mahaifiyar mujahid da mahaifinsa
da wasu daga cikin yan uwansa, fararan kaya
ango da amarya suka sa babu walwala sosai a
tare da mujahid saboda bai sami gayyato yan
matanshi ba a dalilin zuwan iyayensa wanda
baiyi zaton zai gansu sun zo ba,da yake auren
da matar duka ba damunsa sukayi ba sai ya sa
bai yi wani shiri ga bikin ba duk da haka duk
wanda yaje bukin nan yasan ana kashe naira
kuma an burge iyakar burgewa ango da amarya
sunyi kyau har sun gaji yanda ango bai da
walwala haka amarya zuciyarta ke cike da
damuwa, amma bata bari damuwar ta bayyana
a fiskarta ba dan kar babanta muhmud ya
fahimci cewa bata son auran ya shiga damuwa,
duk abin da zai bata ran bawan Allah nan bata
sonshi saboda darajarsa da kimarsa a gunta
shida mahaifiyarsa shiyasa ta sadaukar da
rayuwarta kun faranta musu kamar yadda suka
ji tausayinta lokacin da take neman taimako.Duk
lokacin da tuno iyayenta sai tayi kuka, tunaninta
a kansu ba mai kyau bane, gani take sun watsar
da ita ne kowanne ya kama gabansa ko ta rayu
ko ta mutu oho bata taba furtawa inna wannan
tunanin nata ba dan kar ta sauyata daga haka a
haka take son ta tafi tana musu addu'a ne
saboda arzikin haihuwa kawai kauna da soyaya
sai baba muhmud da inna.
Tunanin da kenan fati har aka tashi zuciyarta
babu dadi, da suka dawo gidansu fauziya inda
suke zaman amarci da kawayensu ta kwanta
lamo bisa gado gobe ne juma'a za a daura
musu aure da mujahid na mijin da bai damu da
ita ba zai aure ne dan wani dalili nashi nakanshi
ba dan soyaya ba.A daidai lokacin da zuciyarta
takeyi kamar ta fashe dan tsananin soyaya..
Yanmata kawayenta sha'aninsu kawai suke biki
yana musu dadi saboda iyayen kudin da aka
sakar musu wautarta suke gani yadda bata da
walwala da gani kasan tana tare da damuwa,
fauziyya har ta gaji da yi mata nasiha ta sa
mata ido.washegari da safe aka daura auren
nabila da muhmud nuraddin (mujahid) bisa
sadaki naira dubu dari biyar wanda ango yabiya
da kansa kamar yadda shari'a tazo dashi,
sauran hidindimun auren kaf iyayensa da alhaji
mukatar suka yi mai.
Tuni sun shaida wa iyayen amarya da ko tsinke
komi suna da shi amarya kawai suke bukata.
Da yanmacin ranar mafatin suka tafi launchin ne
na cin abincin rana harda yaya a sani abacha
stadiym, makada da mawaka sun sha kudi

Please Login or Register in order to submit comment