Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kin zo da
babban al'amari. Rabi ta ce ki taimakeni dan
Allah ummi. Ummi ta ce duk wannan ba zai
gagare ni ba tunda ina da halin yi tsoro nake ji
kin sani Abba bai son bakin mutum ko yana da
kudi da wahala ya bashi ke bana son fitina. Rabi
ta ce sai mu yi tayin addu'a Allah ya taimakemu
a kansa. Ta ce to shi kenan zan yi tunani.
Gida mai kyan gaske ummi ta sayawa tahir da
mota yar ubansu ta yayi ta dora mai da kudi
har naira miliyan biyu ta ce ya zo kai tsaye
neman auran Rabi'a. Lokacin da ta kirashi take
mai wannan bayanin tahir rudewa yayi ya zauna
sharaf a gabanta yana hawaye ya kasa magana.
Wannan rana ya tabbatar rabi'a da mahaifiyarta
suna kaunarsa ne saboda Allah. Shi kam bai san
da abin da zai saka musu ba. Ummi ta ce kar ka
damu na yi ma haka ne dan kana son Rabi'a
itama tana sonka in dai wadannan abubuwa ne
zasu hana yiwuwar auranka to ko ba zan bari ku
yi asarar junanku ba. Saboda haka kar ka damu
kanka da komai. Tahir kuka ya ke yana godiya
ga ummi ta mike ta shige gida ta barsu shi da
Rabi'a, ta ce tahir mun zama daya ni da kai
zuciyoyinmu sun zama daya. . . Shigowar motar
Abba ya katsewa rabi'a magana direban Abba
ya yi parking ya fito aguje ya bude musu kofa
shi da nura suka fito cikin isa da takama nura
ya ce Abba wai baka raba waccen yarinyar da
wancan bakin yaron ba. Cikin takaici ya ce laifin
umminku ne ita ke bata damar ta yi duk abin
da taga dama, yau fa da safe nake gaya musu
cewa a yammacin nan sultan da nazir zasu zo
gidan nan amma dan wulakanci ta jawo shi yazo
in sultan ya ganta da wannan me zai daukeni?
Nura ya kwala mata kira taho da sauri ta
durkusa, ya buga mata tsawa ya ce munafuka
mike tsaye ba Abba ya rabaki da wancan bakin
yaron ba? Ta waiwaya taga tahir na tahowa ta
ce dan Allah ka yi hakuri wata magana ce ta
kawo shi gunka Abba.To naji magana ce ta
kawoshi gurina wa ya ce ki fito gunsa ke da aka
yi miki miji? Abinda tahir ya fara ji kenan da
sassarfa ya karaso gaban abba ya durkusa ya
gaida shi, ba wanda ya amsa nura ya nuna mai
hanyar fita ya ce dan Allah malam kama
gabanka ko kana ganin iri irinka na shugo mana
gida? Tahir ya ce zan fita dan Allah ka taimaka
ko minti 2 ka bani in ma bayanin abin da ke
tafe da ni. Abba ya wuce yana fadin ka jirani a
nan zan ma gargadin karshe a kan zuwa gidan
nan in baka ji ba zaka gaya musu. Nura ya
bugawa Rabi tsawa ya wuce ciki kar mijinki ya
sameki a nan. Mike ta shiga suka bar tahir tsaye
cikin takaici. Wai shin me mutane suka dauki
dukiya ne. Ya kwashe minti ashirin kafin a aiko
ya shigo falon Abba, yana zaune kan kujera ya
dora kafa daya kan daya yana ma tahir
wulakantancen kallo ya ce to sarkin naci gaya
mini abinda ke tafe da kai kafin ka ji nawa
bayanin. Tahir ya dukar da kai ya ce Abba ka
taimakeni ka bani Rabi ina sonta. Abba ya buga
mai tsawa ya ce baka da hankali ne ina ga kana
da matsala a kwakwalwarka duk abubuwan da
nake gayama ba shiga kunnanka suka yi ba shi
yasa ka kara zuwa guna da batun neman aure
ko? Tahir ya ce abba ka gafarceni in dai kudi ne
nima ina da su a yanzu. Ya ce ina dasu abba.
Yayi murmushi in kana da kudi ai baka sauya
launin fata daga bakin mutum zuwa farar fata
ba ko? Ko ban gaya ma bana bawa bakar fata
yaya na ba, to tashi ka bani guri, baka da
tagomashin da zaka zama surukina, kuma idan
ka sake zuwa ko kofar gidan nan sai na kulleka
na manta da kai ballantana har ka shigo mini
gida ba da izinina ba kana magana da yata.
Tahir ya shiga magiya abba ya yi mai banza
daga bisani ya danna kararrawa mai gadi ya
shigo aguje ya ce maza ka fice mini da wannan
yaron daga gida, duk ranar da ka kuma barinshi
ya shigo gidan nan a bakin aikinka. Maigadi ya
tusa tahir a gaba ya fitar da shi, kafin tahir ya
isa gida zazzabi da ciwoo kai har sun kamashi,
yana shiga dakinsa ya fada kan katifarsa yana
cizon yatsa, yau yaga wulakanci ganin idonsa, ga
soyayyar Rabi na cinsa a zuci kamar zuciyar zata
fashe. Ya dau waya ya kirata ta daga da sauri
ya gaya mata yanda suka yi da abba ya ce
Rabi'a ki gayawa ummi na gode da kaunar da ta
nuna mini na maido mata gidanta da motarta
da kudinta aure tsakaninmu sai hakuri abba ba
zai bani ke ba.Rabi'a ta ce wli tahir in dai muna
raye ni da kai aure ba fashi, ba zan auri wanda
yake so din ba nima. Zai magana ta ce na fa
gama magana ka zuba ido ka ga abin da zai
biyo baya kawai. Ta kashe wayar ta shiga falon
ummi ta gaya mata yadda tahir suka yi da
abba. Ummi ta ce ai dama na san haka ne zai
faru nayi yadda kike so ne dan kar ranki ya baci
amma na san da wahala a cimma nasara.
Fatima ta shigo da sauri ta ce anti rabi ga sultan
da nazar sun iso. Ta ja tsaki ta ce idan kika kara
yi mini maganarsu sai ranki ya baci. Fatima ta
ce kin san Allah da kin hada ido da sultan za ki
fatattaki tunanin kowane da namiji a zuciyarki,
wlh sultan yadda kika san ba mutum ba don
kyau Taja tsaki ta ce na bar miki ni fa wannan
bakin da ba a so shi nake so. Daukar dala da
gammo kenan. Inji fatima ta fada tana
murmushi. Rabi ta shiga dakinsu ta tsala ado da
wasu shegun riga da wando da anti nafisa ta
sayo musu a indiya sunbi jikinta sun lafe sun
bayyanar da surorin jikinta, gashin nan baki
sidik ya sha gyara ya kwanta a kafadarta ta
zuba turare ta dubi asiya wadda ke nata shirin
ta ce yaya nayi? Asiya ta ce yanzu a haka za ki
je gaban sultan? Ta ce ai ko tahir din da kike so
kullum da hijabi kike zuwa gabansa.......




Zaharaddeen Shomar

Whatsapp 08168575100





Launin Fata 1-05
Posted by ANaM Dorayi on 04:45 PM, 06-Oct-15
Under: Launin Fata
Ta ce wata sabuwar soyayya yau zan jewa sultan
da ita amma fa mai ciwo a zuci. Asiya ta gyada
kai tana dariya ta zuba nata kayan irin na rabi'a
amma ita brown ne mai duhu, ban san wadda ta
fi cinyewa ba a ciki. Fatima na can nata hidimar
sanya musu abinci sultan da Nazir na falon abba
na cikin gida kowanne yayi bala'in haduwa,
kananan kaya ne suma a jikinsu iyakar burgewa
da cinyewar da namiji sunyi. Nazir ya fi sultan
son magana da raha sultan na da jan kai da
miskilanci tunda suka gaisa da fatima bai kara yin
magana ba ya dau jarida yana dubawa, nazir ke
janta da wasa itama da yake tana da surutu sai
ta biye mai suka tayi hausa kadan kadan suke
jefota yawanci maganar larabci suke yi. Abba da
nura da rufa'i suka shigo yadda sultan da nazir
ke zaune kan kujera a kasaice shigowar abba
baisa sun motsa ba, shi ne yayi musu sannu da
zuwa cikin fara'a gara ma nazir ya amsa cikin
sakin fuska ya gaida abba ya baiwa rufa'i da
nura hannu sun gaisa, sultan kuwa duk su ne
suka gaida shi. Wai dan kawai yana da farar fata
kuma yana da dukiya ba abin da ya damu abba
da tsananin jin kan sultan sai dai kawai alfahari
yake irin mutanan da yake so sunzo neman
auran yayansa, (ALLAH KARABAMU DA IRIN
WAYANNAN IYAYEN) fatima kanta duk yadda take
yabö kyan sultan da dacewarsa da ajinsa sai da
taji haushin yadda ya yiwa su abba har hasko
yadda tahir ke zubewa kasa yana gaidasu nura
kansu yake balantana Abba da yake yi kamar ya
kwanta su taka ruwan cikinsa. Ta koma ciki ta
barsu suna hira cikin harshen larabci, sama sama
sultan yake magana ba laifi sun danci abinci kana
abba ya mike da kansa ya shigo cikin gida ya sike
rabi'a da asiya a falon ummin ya ji dadin adon
da ya gansu a ciki.Ya ce asiya bani da matsala ta
fanninki ke kuwa Rabi ina sane da abin da ke
zuciyarki, ko da yake nasan kin ci gaba da son
wancan bakin yaron ne dan idanunki basu yi
arba da sultan ba. Na sani daga lokacin da kika
ganshi kin yi bankwana da kowane da namiji sai
shi isarsa da kwarjininsa sun isa su gamsar da
mace tun kan ya kai ga yi mata magana. Amma
duk da haka ina jan kunannki da kakkausar
murya a kan sultan. Kada ki yarda bakinki ya
furta wata magana marar dadi a gareshi ba
wulakantaccen mutum ba ne baki isa ki
wulakantashi ba. Ku taso ku zo suna son ganin
ku. Ya juya Rabi ta bishi da ido tana murmushi.
Ummi ta ce ki yi abin da ya ce ki yi. Ba ta ce ko
mai ba ta yi gaba asiya ta bita da sultan da nazir
ne kadai a falon rabi'a ta yi sallama nazir ya
amsa cikin fara'a ya ce barka da shigowarku
gimbiyoyi. Ta ce yawwa barkanku kuma da zuwa
manyan baki muna murna da zuwanku Nigeria
musamman kuma gidanmu. Nazir ya ce mun
gode Rabi'a ke asiya baki mana barka da zuwa
ba. Ta ce kanwata ta wakilceni. Suka yi dariya
banda sultan wanda yake musu wani irin kallo da
ya kara fusatar da Rabi'a. Tabbas in kyau ne abin
kallo da isa da kasaita da dukiya sultan ya isa a
dube shi, to amma wannan daban so daban har
wannan lokaci da rabi'a tayi ido hudu da sultan
zuciyarta na tare da tahir ba ta jin kuma zata
sauya ra'ayinta saboda kyaun sultan. Wata kila
da tausayi da kaunar tahir bata shiga zuciyarta
ba da ta so sultan dan abin so ne abin haushin
dai shi ne ya cika jin kai da yauki tun a lokacin ta
fara tunanin anya sai yace yana sonta ba tallanta
akai mai ba? Dama haka ake zuwa neman aure?
Namiji ne mai jin kai da isa magana ma tsada
take mai? Nazir ya ja hannun Asiya suka fice
waje, suka yi tsit, sultan ya kafawa rabi'a ido bai
san ma me zaice da ita ba. Saboda wannan shi
ne karo na farko da ya taba zuwa gun wata
budurwa da kansa sunan neman aure ya yi
yammata kala kala a kasarsu da kasashen da
yake zuwa musamman london inda rayuwarsa
tafi yawa duk wata mace ko sultan yaje inda take
ba sai dai ita ta zo inda yake. Babu abinda
iyayansa suka fi so sai ya yi aure, baiga matar da
zata da ce da rayuwarsa ba ne sai sanda yaga
Rabi a hoto, ta burge shi sosai, sai dai ya yi ta
jinjina yanda zaizo gaban mace ya yadda ajinsa
yana mata hirar soyayya. Zuwa can ya budi baki
da kyar ya ce Rabi'atu abbanku ya miki bayanina
da dalilin zuwana ko? Ta dubi kwayar idanunsa
masu kyan gaske ta ce Eh, ya yi mini sai dai ban
amince ba. Sultan ya fiddo ido cikin mamaki ya
ce kamar yaya? Ta ce eh kwarai kuwa ban
amince ba. Saboda ban miki ba? Ya yi tambayar
cikin lallon raini da wulakanci. Ta ce ba wai ba ka
yi mini ba ne ba yadda za a yi mace ta dubi
kamarka ta ce bai mata ba, sai dai kafin kai na
mallaka zuciyata ga wani nayi mai alkawarin
kaina ba zan iya janyewa in saba mai alkawari
ba. Cikin takaici sultan ya ce amma Abbanku ya
san da wannan bai gaya min ba, ya bari na baro
ayyukana tun daga london na zo nan? Ta ce Eh
to lokacin da ya yi ma alkawarin zai baka aurena
a china bai san na tsaida zuciyata ga wani ba
amma lokacin da ya dawo ya kawo mini lbr ka na
gabatar mai da wanda nake so. Ka yi hakuri ba
wai bani sonka bane ina duba girman da darajar
alkawari kuma na gode da ka ce kana sona Allah
ya baka wadda ta fini. Daga haka bata jira komai
ba ta mike ta fice ta shige dakinsu ta kulle ba
tare da wani ya ganta ba. Sultan kuwa bin
bayanta ya yi da ido zuciyarsa ta yi bakikkirin
ransa ya baci ainun. Tunda yake bai taba ganin
wulakanci irin wannan ba, kamar shi mace
karamar yarinya zata yiwa haka kawai dan ya ce
yana sonta? Ya mike hannayensa zube a aljihun
wandonsa ya fito ya tsaya a kofar falon, abba
yashigo daga get ya hangoshi gabansa ya fadi
jikinsa ya bashi ko yarinyar nan ta batawa sultan
rai, da sauri ya karaso ya ce sultan lfy? Wani irin
mununan kallo ya yi ma Abba ya ce mene ne
yasa ka sani na zo gidanka alhali yarka tana da
wanda take so. Abban ya zaro ido ya ce haka ta
gaya maka? Ya ce da haka ta tabbatar mini da
bakinta, ban ji haushinta ba dan nafi son a gaya
mini gaskiya fiye da a yaudareni, kai ne ka bani
haushi da ka bata mini lokaci. Abba ya ce dan
Allah dan annabi ka yi hakuri sultan yarinya ce
mai taurin kan tsiya amma zanyi maganinta bata
isa ta yi ma wulakanci ta zauna lafiya ba. Sultan
ya ce hakan ba zai amfani ba dan na hakura da
ita har abada ka bata wanda take so kawai. Ya
wuce ya bar Abba tsaye sororo don takaici sai ya
wuce cikin gida yana kwalama Rabi'a kira, ummi
fito tana fadin lfy. Abba ya ce ina munafukar
yarinyar nan kin daure mata gindi ta wulakanta
mani mutane to yau sai ta gane kuranta. Rabi na
fitowa daga daki Abba ya rufeta da duka yana
bambani sai da yayi mata lilis ya fice ya barta
tana kuka.
Rigima ta yi rigima a gidansu Rabi, babu yadda
Abba bai yi da sultan ba kan ya karbi fatima ya
ce bai so ya hakura da neman aure sam shi ba
zai juri wulakanci ba dama haka mata suke in
akace ana sonsu? Nazir ma ya yi kokarin nuna
mai cewa ba haka abin yake ba ya ce sam ina
shi yayi ya gama, nazir bai ji dadin lamarin ba
yadda asiya ta amince da shi suke shimfida
soyayya har ansa ranar aure sati 3 kacal haka ya
so a yi bikin gaba daya da amininsa abin zaifi
armashi. Rabi ta ci zagi a gun Abbansu fadi yake
taja mai asara, ko da ace baya neman kudi yayi
abinda zai samu a gun sultan da nazir ya
isheshi rayuwa amma da yake ita mai kashin
tsiya ce tayi mai abin da ya sa har fatiman ma
yace bai so in banda ummi da Asiya ba mai
goyawa Rabi'a baya duk yan gidansu haushinta
suke ji da ganin wautarta, ba kamar yaya nura
da yake j kamar ya shake Rabi ta mutu ya huta
da ganinta haka nafisa gara gara ma bashar ya
ce a kyaleta ta auri wanda take so ai jiki magayi
ne. Da haushi ya ishi Abba sai ya ce Rabi'a ta
turo mai bakin yaron da ta nacewa, ta kira tahir
a waya ta ce ya zo babanta zai ganshi.A guje za
zo ya iske shi a harabar gidansa ya fadi kasa
kamar zai kwanta mai ya gaidashi abban yayi
mai wani matsiyacin kallo wai a kan wannan aka
wulakanta sultan ya ce. Kai anya ba asiri ka
yiwa Rabi ba ta fifita soyayyarka a kan kowa?
Tahir ya ce wlh ba haka ba ne Abba soyayya ce
kawai daga Allah. Ya ja tsaki ya ce kai rufe mini
baki munafukin banza da wofi ban yarda ba da
abinda ka yiwa yata. Abinda zan gaya ma shi ne
tunda Rabi ta manne bata da mijin aure sai kai
na baka ita goben nan in Allah ya kaimu kazo da
waliyyinka da sadaki a daura muku aure ka
dauketa ku tafi bana bukatar ci gaba da zaman
ta a gidana tunda ba za ta yi abinda nake so
ba. Ta hir yana mutuwar son Rabi'a fiye da
yadda yake son kansa a duniya yana jin babu
abinda zai fi mai dadi kamar a ce an bashi
auran Rabi'a to amma ba a irin wannan yanayin
ba. Duk auran da aka yi ba bisa son ran iyaye
ba akwai matsala. Jiki a sanyaye ya ce ka yi
hakuri abba albarkar da muke nema a auran ba
zata samu ba matukar babu son ku a ciki na
hakura da rabi ka bata wanda kafi so. Abba ya
buga mai tsawa ya ce tashi ka bani guri bana
son munafunci har ni zaka yiwa dadin baki,
bayan ka gama kangarar mata da kunne bata jin
maganar kowa sai taka, ni dai babu ruwana da
ita da auran ta da kai duk wani hali da
rayuwarta zata shiga ba abinda yayi min zafi. Ya
mike ya shige cikin gida ya bar tahir zube a kasa
har lokacin da Rabi ta ji shuru yayi yawa ta fito
ganin zaman da yayi ya fadar mata da gaba,
muryarta na rawa ta ce lafiya tahir. Ya runtse
ido hawaye na zuba idonsa ya bayyana mata
yadda suka yi da abba ya kare da fadin wlh
Rabi'a zuciyata bata da karfi kan dukkan abin da
ya shafe ki da ace zan iya hakuri da ke da. . . .
Ta sa hannu ta toshe mai baki ta ce mene ne
dan abba ya fadi haka, ciki da gaskiya wuka
bata huda shi ka kwantar da hankalinnka tunda
muna son juna ne dan Allah, kuma zamu auri
juna don Allah, babu abin da zai faru da
auranmu sai alheri.
Hajiya yaya ta dubi tahir bayan ya gama kora
mata jawabi ta ce tun farko sai da na gaya ma
yarinyar nan ba matar talaka ba ce ka hakura
ka ki, tunda ya ce haka zan ma kawunanka da
Alhaji isa magana kuje tare da su a daura auran
Allah ya kyauta. Kwanan farin ciki da damuwa
tahir ya yi yana farin cikin auran masoyiyarsa
wai gobe ya war haka in isuna raye rabi ta zama
matarsa yana jin abin ne kamar a mafarki
kamar zai farka yaga ba haka ba a gefe guda
yana jin damuwar yadda lamarin ya kasance.
Har gari ya waye bai gasgata kansa ba sai da
Rabi'a ta kirashi a waya tana kuka ta ce babanta
ya matsa mata da zagi da duka har ya fasa
mata jiki ya ce ta gaya mai kada ya bari karfe
taran safiyar ta wuce bai zo ba an daura auran
ya tafi da ita ba. Zuciyarsa ta yi mai kunci ya ce
ki yi hakuri Rabi'a ko mai mai wucewa ne komi
yayi farko zai yi karshe, wata rana lbr zai zama
ni dai babu abin da zance muku ke da ummi sai
godiya. Kun nuna mini kauna ta hakika kuma ta
gaskiya insha Allahu za ki yi alfahari da aure na.
Kyakkyawan zaton da kike mini na zan rike ki
amana har kika sadaukar da rayuwarki gareni
ba zan baki kunya ba. Ta ce Allah ya sa taìr
mahaifina baya son auranmu saboda hujjarsa
marar tushe ballantana makama, Allah ya sa in
kasance mai farin ciki da auranka, Allah yasa in
karyata maganar nan da ake cewa da namiji ba
dan goyo bane. Ya ce kada wani tunani marar
dadi ya shiga zuciyarki a kan auran mu ki ci
gaba da kyautata mini zato kamar yadda kika
saba insha Allahu za ki samu farin ciki fiye da
yadda kike zato a kaina. Suna aje wayar ya tashi
ya shiga gidan kawunsa tanimu ya yi mai tuni
kan zuwan dauri daurin auransu, kawu ya ja
tsaki ya ce ni bana son inje in da za a
wulakantani.Tun kana karami kake da wannan
dabi'ar duk abin da za ka yi sai ka zo da fitina
da iya yi kamar kai din wani na daban ne.
Yammata babu irin wanda babu a gidan nan da
unguwar nan dan iya yi ka ce ba su yi maka ba
katafi inda za a wukantamu muce ba zamu ba a
ce kai maraya ne mun ki kula da kai don
iyayanka basu gidan duniya. Zuciyar tahir ta
kara baci abin ya yi mai yawa, sai da ya tuno
matar da zai aura kana ya ji sanyi a ransa ya ga
wannan duk ba komi ba ne. Da zarar an daura
auran na ba shi matarsa an gama. A can
gidansu Rabi ma dai rigimar ce a kwance tun da
gari ya waye Abba yakewa rabi'a bambamin
masifa da ma kwana tayi ba ta yi barci ba tana
fargabar yaddalamarin zai kasance duk irin
zumudin son da takewa tahir da burin auransa
da take hankalin ta gagara kwanciya yayi saboda
yadda lamarin ya kasance, bai wa kowa dadi ba
a gidan. Wayewar gari wannan rana tun da
sassafe ya kira duka yayansa a waya har da
nafisa da ke kaduna da bashar da ke zariya
makaranta ya ce lallai yana son ganinsu kafin
karfe tara, duk sun san rigimar mahaifinsu karfe
bakwai da rabi basar ya iso nafisa kuwa takwas
da rabi ta zo. Abba na zaune kan kujerar zaman
mutum 3, ummi na gefensa ta yi tagumi rufa'i
na gefen Abba, nura ya harde a gefe daya
bashir na kusa da Rabi'a wanda ke ta kure a
gefe ta hada kai da gwiwa idanunta sun
kumbura sun yi jawur kamar ta shekara tana
kuka. Nafisa ta fi kowa jin haushin Rabi'a dan
bata ga dalilin da zata jefa kanta a wahala ba ga
dadi hutu na kiranta bayan kudi ga sarauta.
Asiya ce ke taya rabi'a kuka yayin da fatima dan
haushi tayi kwanciyarta a gefe, idris kuwa da
yafi kowa tsanar rabi'a kan maganar bai zauna
ba a falon. Abba ya ce dukanku kowa ya san
abin da ke faruwa kan maganar auran Rabi da
tahir ko? Gaba daya suka amsa eh mun sani
abba. Ya ce to Alhamdulillahi gaskiyar magana
ita ce bana son auranta da tahir kamar yadda
kowa a cikinku ya dade da sanin ra'ayina, ban
taba tsammanin akwai wata ya da zata yi mini
gaddamar da rabi tayi mini ba na yi iya kokarina
in nuna mata illar da nake hango mata kan
lamarin amma taki. To na taraku ne dan ku
shaida na bawa tahir Rabi'a duniya da lahira
kuma na fidda hannu a kanta, bance ba ta cikin
yayana ba yata ce, amma babu hannuna cikin
duk wata matsala da zata same ta idan auransu
ya yi dadi ita dadin ya shafa. Bana bukatar in ji
ko mi in san komi a kai, idan matsala ce ta taso
nan ma kada ta nufo gidan nan, farin cikinta
nata ne ita kadai matsalarta ma tata ce. Basar
ya ce Abba ka yi hakuri ka sassauta wannan
hukuncin na ka, duk lokacin da iyaye suka ce
sunfidda hannunsu kan matsalar dan su fushi
suke da shi kenan. Fushin iyaye masifa ne ga
dansu saboda girman darajar da suke da ita a
kansa fushin ba zaisa ya gyaru ba sai dai ya
kara shiga wa matsalar kenan. Abba ya ce kai
rufe mini baki ba kiranku na yi don in nemi
shawararku kan lamarin ba na kiraku ne don ku
zama shaida saboda gaba. Bana son wani
cikinku ya kara bani hakuri a kai, yadda ita bata
hakura ta yi biyaýa ga umarnina ba ta dage kan
ra'ayinta sai ni na janye nawa ra'ayin nabi
yadda take so haka nima babu wanda zai sa in
yi abinda ban yi niyya ba. Asiya ta duka ta ce
duk haka abba ka gafarcen mu ci gaba da
tayata adu'ar Allah ya sa haka shi yafi alheri,
babu wanda ya san abin da zai faru gobe sai
Allah. Nafisa ta zabga mata harara ta ce wai ku
da kuke fadin haka me yasa ita baku tursasata
ta yi biyaýa ga Abba ba a matsayinsa na
mahaifinta sai shine zai mata biyayya a
matsayinta na yar da ya haifa? Duk ummi na
jinsu ko tari bata yi ba, idanunta kan Rabi'a
wadda tun tana kuka har ta goge hawayen ta a
ranta ta ce ko mi na Allah ne insha Allah komi
zaizo mata da sauki. Karfe tara minti biyar tahir
ya zo tare da kawu tanimu da alhaji isa abokin
mahaifinsa da abokinsa ibrahim sai dan wan
babansa muhamd, tahir dama ya san ba zasu
samu tarbar arziki a gidan ba, har falo aka
shigar da su, ummi da Rabi'a da asiya da fatima
da nafisa suka shige cikin gida suka barsu a falo
nan take aka daura aure bisa sadaki naira dubu
dari, in banda limamin unguwar da makotansu
abokan abba Alhaji garba babu wanda abba ya
gayyato su ma rufa'i ne ya matsa mai ya kira su
dan su shaida auran.Abba na bambami ya ce ni
bana son kiran kowa in sha kunya harka ta
matsiyata wa zai gayyato masu arziki ya sha
kunya a banza. Motar da ummi ta ba tahir suka
zo sai ya jawosu a motar mota ce mai kyan
gaske da tsada amma duk da haka kallon banza
Abba ya yiwa motar lokacin da aka gama daurin
auran suka fito ya ce dube su da Allah, kayan
da ango tahir ya sa sun isa a dubeshi a
matsayin rayuwar da yake kai amma a gun
Abba a talauce ya zo ransa a bace yake sosai ko
ganin tahir bai son yi. Sadakima da Alhaji isa ya
mikawa liman ya amsa ya mikawa abba cewa ya
yi ba zai karba ba a kira Rabi a bata abin ta
kuma su tafi yanzu yanzu ba zata yini a gidan sa
ba. Anan ne liman ya ce ko kadan haka ba zai
yiwu ba ya bari tahir ya kai mutanansa ya dawo
da yamma ya dau matarsa. Abba dole ya yarda
da haka tahir yaga cin fuska a wannan rana
yaga wulakanci na karshe suka baro gidansu ran
su ya baci sosai a hanyarsu ta komawa gida
mahmud yake ta bambami ya ce wlh da
wannan wulakancin yarinyar nan ko yar gold ce
na hakura da ita sai dai santa ya kasheni,
mutane kawai dan suna da kudi sai su dau
kansu a wata tsiya. Kawu tanimu ya yi tsaki ya
ce ai wlh dan kar a ce mini naki zuwa ne

Please Login or Register in order to submit comment