Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan ba
dana bane da babu abin da zai sa in zo a
wulakantani a banza. Kowa ya ci gaba da fadin
albarkacin bakinsa cikin dacin rai tahir yana
tukin mota ya rasa abin da ke mai dadi a duniya
ya rasa da me zaiji da takaicin gidan su Rabi'a
ko takaicin maganganunsu da ba zasu barshi ya
ji da abu daya ba, haka a gidansu aka dinga
yamadidin maganar ana dada zuzuta lamarin
har da masu cewa uban Rabi'a ya zazzagesu,
kai maganganu dai iri iri marasa dadi. Tahir ya
shiga daki ya fidda kayan jikinsa ya yi wanka ya
kwanta kan katifa zuciyarsa ba dadi ya dau
waya ya kira Rabi'a wai ya ji muryarta ko ya ji
sanyi a ransa, amma tana dagawa sai ya ji ta
tana kuka ya rasa abin da zaice sai ya kashe
wayar ya ci gaba da kwanciya yana son yin barci
ya kasa sai juyi. Sai karfe hudu saura kwata ya
fito yana sanye da farar jallabiya ya festo
furaran yayi alwala ya shiga masallaci ya yi
sallar la'asar cikin jam'i ya shiga cikin gidansu
dakin yaya tana zaune kan abin salla itama
sallar ta idar ta zuba mai ido ta ce yanzu za ka
je dauko amaryar ya ce Eh. Ta ce uhum ni ban
taba ganin aure irin wannan ba Allah dai ya
kyauta an gama share gidan. Ya ce Eh cikin
kudin da mahaifiyar Rabi'an ta ban na sai duk
abubuwan da gida ke bukata an gyara gidan
gaba daya. Ta ce shi kenan Allah ya sa an yi a
sa'a. Sallama suka ji ta mahmud yana fadin kai
tahir ai an hutar da kai ga amaryar nan ubanta
ya sawota a mota ya biyoka da ita. Ya dafe kirji
ya ce suna ina? Ya ce suna kofar gida shi ya ce
in ma iso da kai. Hajiya yaya ta mike tana fadin
iko sai Allah. Abba yana tsaye jikin mota yana
hura hanci, rabi'a na tsaye kusa da shi tana
kuka kamar ranta zai fita. Tahir ya durkusa har
kasa ya gaida abba, abba ya ce kai da Allah
mike munafukin banza da wofi an gaya ma nazo
ne dan ina bukatar gaisuwarka, matarka ce na
kawo maka naga kayi nawar zuwa daukar ta
bana son ci gaba da zamanta a gidana. Ya finciki
Rabi'a ya ankadata jikin tahir ya shiga mota ya
ja da karfi ya bada musu kura ya bar gun. Wani
irin gumi ya dinga ketowa tahir, musamman
ganin yadda lokaci guda labarin gidansu abu ga
babban gida, nan da nan aka firfito matan gidan
da yaran aka shiga surutu iri iri kowa da abin da
zaice har sai tahir da Rabi'a suka rasa me
kwakwalensu zasu dauka a ciki ya kama hannu
rabi'a suka shiga dakin hajiya yaya ta dunkule
kanta a hijabi tana kuka na fitar hankali. Hajiya
yaya ta ce ki daina kuka yar nan kin zo gidan
mai sonki ........







Zaharaddeen Shomar

Whatsapp 08168575100




Launin Fata 1-06
Posted by ANaM Dorayi on 04:49 PM, 06-Oct-15
Under: Launin Fata
Insha Allahu zaki ji dadin zama da tahir ba wai
dan ya kasance nawa ba nake yabon shi sai dan
halinsa na amitance, ballantana ke da yake so.
Yanda tahir ya zauna ya zuba tagumi bai iya
cewa komai ba dan haushi kallon Rabi yake tana
kuka a matsayinsa na namiji bai dace ya yi kuka
ba shima da yayi kukan.A dakin hajiya yaya
Rabi'a ta kwana kuka ta tashi da shi ga kunyar
mutanan gidan da suke lekowa gaisuwar gulma
suna yada mata habaici duk da haka su dinma
tun a ranar suka gano abinda ya sa tahir ya
mannewa Rabi'a matar muhmd zarah ta ce kaga
yarinya kamar aljana dan kyau, tabdijan ai dole
tahir ya kasa sukuni a kan ta. Wata a cikinsu
matar kawu tanimu mai suna dije ta ce nifa tsoro
ta dinga bani ganinta nake kamar ba mutum ba,
cikin dare firgita na dinga yi sai da nayi ta
karanta ayatul kursiyyu naji daidai. Washegari tun
da sassafe tahir ya dau matarsa suka bar gidan
bisa rakiyar hajiya yaya ita kadai gidansu ya yi
kyau sosai ba wani girma gareshi ba amma anyi
mai tsari mai kyau. Hajiya yaya ta yi musu
nasihar zaman lafiya da hakuri da juna ya
daukota a motarshi ya dawo da ita gida ya koma
gun amarya tana kwance bisa gado zazzabi ya
rufeta jikinta yayi zafi zau zau, ya zauna ya kamo
hannunta ya ce nasan daman wannan kukan sai
ya sa miki zazzabi, bari in siyo miki magani.
Bayan ya dawo daga siyan maganin ya shiga kicin
ya dafa mata shayi ya soya kwan ya hado da
bread ya zo ya dagata ya shiga bata a baki da
kyar ta sha kadan ta sha maganin ta koma ta
kwanta, shi kuma ya fita ya sayo mata kayan
sawa kasancewar Abban ta bai kawota da komi
ba. Abin mamaki yana dawowa gida ya iske ummi
da asiya sunzo ya zauna cikin fara'a da
girmamawa ya gaidasu ya dora da godiya bisa
karamcin da aka yi masa. Ummi ta ce ba komi ai
duk yiwa kai ne bata da bukatar komi a gareshi
illa ya ba mara da kunya ya riki amanar Rabi'a.
Ya ce haba ummi wlh idan naci amanar Rabi'a sai
amana ta cini, ai ni tsakanina da rabi'a sai Allah
ki ci gaba da yi mana adu'a.Rabi'a na kwance
kusa da ummi har lokaci idanunta basu daina
hawaye ba bakin cikin abin da abbanta ya yi
mata ya tsaye mata a zuci. Asiya ta matsa daf da
ita tana share mata hawayen ta ce ki yi hakuri
Rabi'a bai dace ki dinga kuka haka ba. Ta ce bari
in yi kuka anti asiya abin kukan ne ya saman,
kina kallon tozartawar da Abba ya yi min. Asiya
ta ce wannan yawan kukan da kike tamkar
butulci ne ga Allah da ya azurtaki da
nagartacciyar uwa mai tsoron Allah wadda babu
son zuciya a cikin dukkan al'amuranta. Idan kin
kalli Abab kin kalli abinda yayi miki ranki ya baci
to kada ki tsananta damuwa har damuwar ta
shiga rayuwarki ki yi sauri ki kalli gata da kaunar
da ummi ta nuna miki, kiyi farin ciki ki godewa
Allah da ya sa kina da rabon auran wanda ranki
ke so sai ki zauna lafiya. Shima Abba wata rana
zai gane kan kuskure yake ya dawo kan hanya.
Da kyar rabi'a ta dakatar da hawayanta ummi
tayi musu alkawarin tana tare da su in sha Allahu
ko yaushe suke bukatar wani abu su sanar da ita
cikin sirri zatayi musu kuma duk sanda ta samu
lokaci zata dinga zuwa tana ganinsu, su ma su
dinga zuwa suna gaida Abba ko da zai musu
wulakanci kar su damu watarana sai lbr. Rabi'a
ta marairaice fuska ta ce dan Allah ummi ku bari
sai da yamma. Ta ce yini yanzu ma asibiti na ce
zamu da kyar abba ya bari muka fito dan ya yi
zargin nan za mu zo. Tahir ya rakosu inda suka yi
parking yana godiya da fatan Allah ya sa a gama
da duniya lfy. A bisa hanya ummi na jan mota
asiya na zaune gefenta ummi ta ce, asiya kinga
sirikin mutunci wanda ya san mutuncin mutane
ya san abin da yake. Ba irinsu kabir kaduna ba
kn kin san karshan wancan watan da naje ni
kadai din nan a gaban nafisa lokacin da tayi
rashin lafiya na shiga gidan yana kwance a falo
daga shi sai singileti da gajeran wando, yadda na
yi sallama haka ya amsa min shekeke ko kallon
arziki bai mini ba, na zauna ina zaton ya sha
giyar ne tayi mai karo sai ni nace mai ina kwana,
yana wani mitsitsike ido ya ce lafiya, na ce ina
nafisan ya ce tana ciki, ni dai na shiga ciki na iske
ta kwance tana faman kuka na ce lfy ta ce wai
kwananta 2 a asibiti tun da kabir ya kaita baije ya
duba ta ba da aka sallamota ma sai makociyarta
ma waya ta zo ta daukota da ta zo gida ta mai
magana sai cewa ya yi bai ajiye mata kudin da
zasu isa a yi komi ba me zaije ya yi, ko in yaje
shi zai cire mata ciwon? Na yi murmushi na ce to
mene na damuwa har kina zubda hawayenki a
banza. Ta ce ummi dole in damu ace kana auran
miji bai damu da kai da rayuwarka ba da ka yi
magana sai ya turo ma kudi, kudi su ne maganin
damuwa? Na ce ah su ne mana nafisa. Na yi
mamakin jin wannan maganar ma a bakinki, ke
da abbanki kika ce ni har da kudi ba matsala
dama kin daina kuka kin ci gaba da zaman kudin
da kike tunda fari kin nuna wa kb ku bayin kudi
ne shi yasa ya takaku ya zageku ke da abba ya
biya kudin zagin kuma a zauna lafiya, ni dai ba
zan iya maganin damuwarki ba abba kuma ba zai
kalli matsalarki ba saboda duk wata kb zai jefi
bakinsa da damin kudi. Da na tashi dawowa wai
marar kunyar kb din nan sai ya dauko kudi ya
biyoni da su a gaban direba mannir ya mika mini
na kalle shi a lalace na ce an gaya ma nima
kwadayin kudinka ya kawo ni? Sai ya ce oh haka
ne ashe fa ance ke bakya da son kudi to ki sauka
lafiya ki dinga yiwa mijinki nasihar ya rage son
kudi. Kiji dan girman Allah har yau maganar nan
ciwo take mini da na dawo gida na gayawa abba
yadda muka yi da kb ko a jikinsa sai ma ya nuna
nice mai laifi ni naje gidan kb na gaya mai
magana shi yasa ya samu damar fadar haka. Wlh
asiya ina mamakin abbanku a rayuwata ban ta
ganin mutum mai tsananin son kudin Abba ba
ina tausaya mai randa son kudinshi zai ja mai
fitina ba dai mugun baki nake mai ba. Asiya ta ce
ai ba a zancen mugun baki a magana ta gaskiya
ko yanzu irinsu kb fitina ne a gareshi dan ba
wulakancin da ba sa mishi, ni rannan wani abu
da akayi ya ban kunya shi ne muna hira da nazir
kafin komawarsu london abba ya shigo falo ya
zauna yace nazir dan Allah ka taimaken ka shawo
mini kan sultan ya amince ya auri fatima ban son
ya kubuce daga gidan nan ina son hada jini da
su, nazir ya ce abba dan Allah ka daina zubda
girmanka gun sultan kana rokonshi fatima ba
girman da ta isa aure tayi ba karamar yarinya ce
ko secondary bata gama ba ina ga lokacin
auranta baiyi ba sultan bai son auran karamar
yarinya. Abba dai yamatsawa nazir kan ya nemo
mai sultan a waya su kara magana abin haushi
da nazir ya nemoshi suka gaisa ya ce Abba ke sö
magana da shi sai ya yi tsaki ya ce gaskiya ba ni
son magana da wannan kwadayayyan tsohon,
kudi yake nema duk abinda zaka kai na neman
auranka da asiya ka ninka biyu ka bashi a
madadin wanda yake tunani ya rasa na neman
aurena da Rabi'a ko fatiman da yake nacin na
aura. Daga haka sai ya kashe wayar sai nazir ya
ce kaji ko abba. Anan ne kuma ya tashi jiki ba
nauyi ya fita.Ummi ta ce bakin ciki kamani yake
in ina jin wadannan abubuwan ko talaka futuk da
bai da komi ba zai abin da abba yake a kan kudi
ba, ballantana shi da ya mallaki kudi kamar
wanda zai yi guzurinsu zuwa lahira.sanda suka
isa gida Abba na tare da su nafisa a falo, abba
ya ce har kun dawo? Ummi ta ce eh. Ya tabe
baki ya ce jikina na bani ba asibitin kukaje ba
gidan waccan marar kunyar kuka je? Ummi ta ce
hankalinka ne kan ta shi ya sa kake tunaanin can
muka je. Ya ce ko baki gaya mini ba na san kina
tare da yarki kuma kece kika taimaka mana ta
samu kwarin gwiwar guje mini. Nafisa ta ce Abba
ka daina damun kanka tunda dai ka bata wanda
take so kuma ka barta da shi in tayi ruwa rijiya in
ba tayi ba ma sai. Ya ce kina da gaskiya nafisa na
dai gaya muku kada wani a cikinku ya hada kai
da Rabi'a ya saurareta, duk wanda na samu yayi
haka ba ni ba shi. Asiya ta mike ta bar falon. Yini
guda hirar Rabi'a ake gida suna kalubalantar
auranta da tahir suna ganin ba zai haifar mata
da da mai ido ba. A can kuma sai yamma
zazzabin jikin Rabi ya sauka mai gida tahir na ta
fama da ayyukan gida ya wanke ko ina tas tas ya
goge komi na kyalli ya kunna turaran wuta gida
ya dau kamshi da ya gama ya shirya masu
lafiyayyar jalop din shinkafa da taji kayan hadi da
dankalin turawa da curry sai kamshin girki da
kamshin turare ya hadu. Da ya gama ya hada
mata ruwan wanka duk tana kwance falo tana
kallonsa, ya zo gabanta ya tsaya daga shi sai
farar best da dogon wandon shadda ya ce
gimbiya za ki iya yin wankan ko in yi miki har
yanzu jikinki ba kwari, duk da na ji zazzabin ya
sauka. Ta yi murmushi cikin tausayawa ta ce
haba gara ka yi wanka ka huta tunda safe da
muka zo gidan nan baka huta ba. Yace kar ki
damu in dai a kan hìdimarki ne ba zan gaji ba ko
zan kwana in yini a tsaye tashi in miki wanka nafi
son ki ji dadin jikinki ki san kin zo gidan masoyinki
wanda ya sadaukar da dukkan farin cikinsa a
kanki da lokacinsa. Zuciyarta tayi mata dadi sosai
tayi mai murmushin da yake so ta ce to na gode
zan iya yi da kaina amma dan Allah kaima kaje
kayi wanka ka huta haka kayi min adon
angwanci. Ya yi dariya ya kama hannunta suka
shiga bandaki ya rufo mata ya fito ya zuwa nashi
dakin ya yi wanka ya zabo ado da fararan
kananan kaya ya zuba turaran net work yana
fitowa falo itama tana fitowa falon tana cikin
atamfar super wax cikin sabbin kayan da ummi
suka kawo mata a dazun duk da cewa akwai
rama sosai fuskarta da jikinta amma ta yi kyau.
Jiri ne yake damunta kawai yanzu ta zube kan
kujera ya tsuguna gabanta ya ce ki daure ki ci
abinci yunwa ce ke saki jiri nasan kin kwana kin
wuni ba ki ci abinci ba Daran jiya dake na kwana
na kasa barci yadda naga rana haka daga
dare,ban taba ganin dogon dare irin na jiya ba
saboda Allah Allah nake gari ya waye in daukoki
in dawo da ke gidan nan in samu damar
lallashinki in baki abinci ki ci na miki tausa tunda
a can babu damar da zan miki. Wlh rabi'a daran
jiya kin bani tausayi mai tsanani wannan kukan
da kike ya tayar mini da hankali, ko da yaushe
adu'a ta Allah ya taimakeni ya bani ikon rike miki
amana kin mini halarci mai yawa yaya zanyi in
rike amanarki ne in sauke nauyin amanar da na
dauka. Ta lumshe ido a ranta tana jin wai waye
yafi wani tausayin wani tsakanin ita da tahir.
Hawaye ya taru a idöta ta godewa Allah da ya
bata namijin da yake sonta so na tsakani ga Allah
itama take sonsa don Allah suka yi aure dan
Allah. Ta kamo hannunsa ta ce tahir ina kaunarka
ina sonka. Ya girgiza kai ya ce Allah sarki
Rabi'atul Badawiyya Allah yasa mi ki da Alherin
duniya da lahira. Ta ce amin summa amin.
Abincinma a a baki ya bata, tun tana jin kunya
har ta gaji ta saki jikinta suna hira suna cin
abinci.
zama mai dadin gaske suke yi tahir ya zama
kamar bawa a gun rabi'a duk abinda take so shi
yake mata tausayin da yake ji nata har ya yi
yawa, yana ji da ita kamar kwai. Haka itama
take ji da shi ba su da wata matsala da ke
damunsu komi suke so suna mallakawa junansu
shi. Ranar da suka yi wata 2 da aure da yamma
tahir na kwance a kan gado yana shan lemon
gwangwani Rabi'a ta shigo tana sanye da yallow
din shadda riga da zani kanta ba dankwali
gashin kanta ya sauka a kafadarta ta ajiye tray
din abinci gabansa ta ce yayana ta so ka ci
abinci. Ya kafa mata ido lokacin da ya tashi
zaune ya jawo hannunta ya dorata kan cinyarsa
ya ce kin kara kyau kyanki har ya yi yawa, bana
gajiya da kallon kyakkyawar fuskarki. Ta ce na
gode da son da kake mini. Ya ce ba ki da
bukatar yi mini godiya ni ne da hakkin godiya a
gareki babu abin da ba ki yi mini ba Rabi'atu na
kasance ina burin in yi doguwar rayuwa don in
rayu dake rayuwa mai tsawo, amma ban san
dalili ba sai zuciyata ta dina zartar da ni wasu
abubuwa marasa dadi tana kusanto mini da
nesa kusa tana kusanto mini da rabuwarmu a
kwana kusa ko ta dalilin mutuwa ko ta wani
dalili da ban san shi ba.Ta marairaice fuska ta
ce dan Allah ka daina wadannan zantukan basu
da dadi, so da shauki ke sa kake jin haka insha
Allahu za muyi doguwar rayuwa ni da kai. Ya yi
murmushi rayuwa ta Allah ce mu na tare da
kayan aro Rabi'atu. Ta bude abinci ta ce taso ni
in baka, kana bani tausayi da yawa. Ya ce kin fi
ni zama abin tausayi so da tausayinki har
sunyiwa zuciyata yawa ban san inda zansa
rayuwa ta ba, saukkina daya kina da hankali
Rabi kin san abin da kike yi da wata ce ta samu
dama aa kaina haka ta fahimci sonta yayi mini
yawa haka har bani da katabus sai abinda ta ce
da ni da shikenan sai ta yi ta gasani tana
wahalar da rayuwata. Rabi'a ta ce to wannan ai
shirme ne miji ai shi ne suturar ya mace yana
da daraja mai karfi a gunta, babu dalilin da zata
wahalar da shi in yana sonta. Ya ce gaskiya ne
yau ne zamu je gaida Abba ko. Ta dan bata rai
ta ce mu bari sai gobe duk nishadin da muke
ciki in muka je gidan nan sai mun fito da bacin
rai gashi kai sai ka yi ta cewa sai munje, bana
jin dadin yadda in munje abba ke ma wulakanci.
Ya ce ba komi matata bana jin haushin abba
saboda darajar ya haifeki duk abin da zai mini
na hakura wata rana sai labari. Ba a son ranta
ba bayan sallar isha'i suka shirya a cikin kaya iri
daya dukansu sun yi kiba sun goge sunyi kyau
da gani suna cikin morar amarci da kwanciyar
hankali. Kowanne gwani ne gun farantawa dan
uwansa sai, ita ke tuka motar yayin da tahir ke
zaune gefenta suna hirarsu gwanin ban
sha'awa. Tahir ya ce asiya sun tafi london din
ne? Ta ce eh wannan satin ta tashi dama sai
mijin yana can ko bikin bai zo ba an yi bikin
anan da daurin aure akaa tura mai ita can
yadda abba ke son kenan. Ta yi parking dai dai
lokacin da abba ya ke fitowa daga cikin gidan'
dariya yake yana ganinsu ya murtuke fuska
kamar dama can bai taba dariya ba.Tahir ya isa
gabansa ya durkusa yana gaida shi ya ce tashi
ka sani bana son wannan durkuson munafuncin
idan kana yi ne dan ka burgeni babu abin da
zaka burge ni da shi, sau nawa ma zan gaya
maka ku daina zuwa gidan nan?
Tahir ya ce dan Allah ka yi hakuri. Abba ya ja
tsaki ya yi tafiyarsa ya barsu nan tsugune,
Rabi'a ta ce dama na gaya ma, kace sai mun zo,
mun zo an wulakantamu sai mu koma ko?
Ya ce ba wani abu ummi zata faranta mana rai
a cikin. Ta ce ita din ma a tsorace take hira
damu dan kar Abba ya yi mata fadan dan ya
raba yan gidan nan da mu. Ummi ta nuna farin
cikinta sosai da ganinsu ta sa musu albarka ta
ce kin san kuwa matar Rufa'i tana gidansu?
Ta ce subuhanallahi yaya akayi haka? Ta tabe
baki ta ce wai ke duk abinda ba a yi shi dan
Allah ba akwai inda zaije?
Wai wancan satin ne shi Rufa'i ya dawo daga
portharcourt ya iske babu abinci a gidan kin san
Rufa'i bai da hakuri in yana jin yunwa ko a
gidan nan ba a fada dashi sai in ba a gama
abinci da wuri ba, ya ce garin yaya aka bar gida
babu abinci?
Ta ce masu aikin dafa abincin da ka basu nan
daya ta tafi ganin gida daya bata da lafiya itama
tana gidansu. Haushi ya sa ya kwanta a falo
yana tunanin abincin da yake ci ma cikin lalura
yanzu babu?
Sai gata ta fito daga daki ta ci uwar kwalliya wai
ya tashi ya kaita unguwa. Kin san zuciyar mai
tsumma a kusa take ya ce gidan ubanwa zata?
Daga fadin haka sai ta sa kuka wai ya zagi
ubanta, shi kuwa ya ce ya zaga din iyayan nata
da basu koya mata tarbiyyar komi ba sai abinda
taga dama take?
Abinci wannan ba zata iya dafawa miji ba sai dai
ya ci na yan aiki, ba za ta iya kula da gidan ta
ba komi sai dai ayi mata?
Shi kam bai taba ganin irin wannan tsari ba. Ta
fashe da kuka ta ce wai dama so yake ya ci
mata mutunci kuma ya yi da yar halak, iyaye
kuma ba nata ya zaga ba nasa ya zaga dama
can ya san bata da tarbiyar ai ya auro ta, ya ce
ta kama bakinta in ta sake ta zage shi sai ya
tattakata ai da budar bakinta sai cewa tayi an
zage ka kai din banza kai din wofi har me ka isa
ka yi in an zageka?
,Sai kuwa ya zage karfinsa ya nada mata duka,
ta nufi gidansu a lokacin babanta ya zo gidan
nan nan da kansa in kinji cin mutuncin da ya
karewa Abbanku da shi Rufa'in kya rike baki.
Rabi'a ta ce kash abin bai yi dadi ba to yanzu
me ake ciki?
Ta ce ina ai bai fita daga gidan nan ba baban
nata sai da Rufa'i ya bashi takardar yar maza
Rufa'i ya je ya kwashe duk abinda ya sani nasa
ne ko su watso mai waje, ya isa ya wulakanta
musu ya ya ci arzikin yar tana sonshi ta ce kar a
kulle shi yau da yaga wulakanci in sun kulle shi
a bursin sai kamanninsa sun sauya an mantada
shi, ke ranar nayi kallo, bai bani haushi ba
saboda na san duk wanda ya hau motar
kwadayi tashar wulakanci zata kaishi suka ce
Allah ya kyauta. Ta ce amin ku tashi ku tafi kar
Abban ya dawo ya same ku.
A gurin nura Abba ya samu lbr ummi ce ta
sayawa tahir gida da mota da kudin da ya yi
ìdimar auran rabi'a ai kuwa ya tada tashin
hankalin sai ya kwace ai duk kudin da fa ummin
ke samu nasa ne, dama yana jin takaicin yaea
suke zaune lfy. Ason ransa ana kai Rabi'a ta
gamu da matsalar da dole ta rabu da auran ta
dawo gida ya bata wanda yafi so sai gashi duk
tafi ya yan da ya aurar inda yake so kwanciyar
hankali da samun zaman lafiya. Ballantana a
bangaran soyayya, samun namijin arziki wanda
ya san hakkin aure irin tahir za a jima. Yana
tattalin zuciyarta kamar kwai, duk inda yake
hankalinsa na kanta. Duk sonsa da abu in har
Rabi'a ta nuna bata so ko da wasa ne ya bashi
har abada, in kuwa ta ce wasa to shi kenan ya
shiga rudani bai samu nutsuwa sai yaga ta dawo
normal, sanin hakan ya sa ko bata da lafiya
bata yarda ya gane dan bata jin dadin yadda
yake daga hankalinsan a kan dukkan abin da ya
shafeta. Abba bai nunawa ummi komi ba ya sa
idris ya rakashi gidansu Ribi'a a safiyar wata
lahhadi. Bai shiga ba ya aika aka kira mai tahir
ya fito cikin rawar jiki ya fadi ya gaida shi ya ce
lfy Abba baka aika na zo c ka zo da kanka. Ya
buga mai harara ya ce mike tsaye ka karkade
kunnuwanka da kyau ka ji abinda ke tafe da ni.
Lfy ba zata sa nazo gidan ka ba kamar yadda ka
dade da sanin ba zan kaunace ka ba. Nazo ne
dan in tabbatar baka manta da zuwa na ba
kuma ba zaka yi wasa da abinda na gaya maka
ba. Tahir ya ce ba wani abu Abba ai dama kai
ba abokin wasa na ba ne. Ya ja........





Zaharaddeen Shomar

Whatsapp 08168575100




Launin Fata 1-07
Posted by ANaM Dorayi on 11:10 AM, 20-Oct-15
Under: Launin Fata
Ya ja tsaki ya ce wannan gidan da kake ciki bana
wadda tayi muku kyautarsa ba ne gidana ne
motar da ta ba ka ma ba tata ba ce tawa ce
kudin da ta tara ma su ne nata suma da na
wane sai ka biyani. Wannan ita ya shafa, abinda
nake so da kai ka shiga ka fito mini da takardun
gidana da mukullin motata ga idris zaija na baku
wata 2 ku nemi gida ku tashi nan ba gidan
zamanku bane, idan wata 2 suka cika baku tashi
ba zaku sha mamaki. Dama can na barku kun
dana ne dan ku mori amarci sai ku san abin yi.
Yadda Tahir ke tsaye gumi ne kawai ke tsiyayo
mai tun daga goshi har sassan jikinsa, bai taba
jin fin karfi irin wannan ba, Abba ya buga mai
tsawa ya ce zaka shiga ka fito mini da kayana ko
kuwa? Ya juya jikinsa ba kwari yaje ya dauko
takardun gida da makullin mota har kasa ya
durkusa ya ba Abba ya ce A sauka lafiya Abba na
gode. Harara ya galla mai ya mikawa idris
mukullin mota ya ce jamin ita mu tafi. Hatta idris
din duk yadda ya tsani tahir sai da yaji jikinsa ya
yi sanyi saboda tausayin da tahir din ya bashi,
Abba ya shiga mota ya ja, idris shi ma ya ja
motar da da take maunin ta tahir. Tahir ya dawo
cikin gida ya iske Rabi'a a zaune a falo tayi
tagumi bata san me ke faruwa ba, amma tunda
idris ya shigo ya ce mata Abba ne ya zo da kansa
gidansu ta san wani tashin hankali ne ya
tunkarosu. Tana ganinshi ta mike ta rungumeshi
tana kuka ta ce cin mutuncin abba ne yau ya
biyoka hir gida? Nasan dai alheri ba zai kawo
Abba gidan mu ba. In banda ina sonka bani son
rabuwa da kai da na hakura da kai na

Please Login or Register in order to submit comment