Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sun
wake ango da amarya yadda ya kamata har
tsigar nabila yadinga tashi yadda suke manna
sunanta da na mujahid suna fadin auran soyaya
mai dadi a ranta take cewa kukuke ganin auran
soyaya ne.
Duk wannda yaje gun fatin ba wai tsabar kudin
da ake kashewa bane yafi daukan hankalinsa illa
dacewar ango da amarya wato idan ka kalli
mazaunin ango da amarya ka kalli ango ka kalli
amarya sai kaga kamar irin greeting cards
dinnan na turawa wato kyaune da kyau suka
hadu abin har ba'a magana, dole ne dan
bakinciki ya rasa inda zaisa kansa da damuwa
dan na gaba kan yayi gaba.Washegari asabar
akayi dinner party ta tsakar daretsakanin
angwaye da amare su kadai a nanne mujahid
yasa mu gaiyyato yanmatanshi na holewa na
nan kano da na mako a ka cashe, sai a wanan
fatin akaga walwalarshi sosai, yadda yanmata ke
manne ai ya dagawa amarya hankali ta dinga
tambayar kanta menene na sawa zuciyarta
kishin wanda bai damu da ita ba ne.
Soyaya ke kawo kishi.
Duk wani so kuwa tana yiwa mujahid indai
akwaishi a duniya sai dai in babu da asuba
party tashi ga barci a idon nabila ga damuwa da
masifar kishi kamar zuciyarta ta fashe.da zasu
dawo gida yana kwance a kan wata jibgegiyar
jeep ta hadu yana ta dan ne dan nen a hadset
dinsa nabila na zaune gefensa, amir ne zai ja
motar abokinsu salman ne zaune kusa da amir
din a gidan gaba har ya fada mota wata
budurwar mujahid da suka zo tare da salman
daga malesiya ta leko saitin mujahid ta juya baki
cikin harshen larabci ta ce my dear za kazo din
ko.Wani irrin kallo yayi mata yayi murmushi ya
ce duk cikar wayanda suka halarci gun dinner
din ba wacce tafiki daraja bakin dai da na
gayyata kinyi kokari da kika zo dole ne inyi maki
abinda zai faranta ranki kema,tayi dariya ta ce
na gode duk da cewa auran da kayi zai
takurawa rayuwarmu sosai amma ina taya ka
murna auran kyakyawar yarinya da ta dace da
kai sosai ka iya zabe.
Yace ko?
Tace karkayi shakkar hakan.
Yace na gode sai mun hadu.
Tace ok.
Ta zagaya gun salman tace fito mutafi a motar
zainab ba zan gane ba kasar.
Yace shikenan amir na biyoku.
Kai kawai ya gyada mai ya fice shi shi amir
takaicin mujahid ne ya hanashi yin magana.
Har salman suka gama yin magana da mujahid
ya tafi bai ja motar ba, mujahid yace me kake
jira ne amir nagaji da yawo so nake inje inyi
bacci fa?Amir yace kaje kayi bacci ko kaje kayi
wanka katafi gun karuwai?
Mujahid yace to meye?
Amir yaja tsaki ya fisgi mota da karfi suka bar
gun suna tafe yana bambami, mujahid bai sake
cewa komai ba, sai da suka zo kofar gidansu
nabila ta bude kofa zata fita mujahid ya
gallamata harara yace ke wa ya baki izinin fita?
Amir yace bata bukatar neman izininka saboda
baka bata fuskar da zatayi hakan ba, nabila
wuce gidanki ki huta kinji ko?
Tayi murmushi tace nagode amir Allah ya huta
gajiya.
Bayan fitarta mujahid ya tabe baki yace amir so
kake karfi da yaji kasa yarinyar nan ta rainani
ko.
Amir yace bani nake son in sa ta raina ka ba
kaine zakasa ta rainaka daga lokacin da ta gaji
da cin kashin da kake mata.
To wai me nake mata amir?
Ya galla masa hararayace haka ake mu'amala da
macen da za'a aura?
Dan kana shawa karuwarka kamshi suna binka
kamar jela itama haka ya dace kayi mata?
Sanin kankane ita tana da banbanci da karuwa
ya dace ka lura da haka ka dinga tausasa mata
banaso kasa ta tsaneka dan kawai randa reshe
zai juye da mujiya.
Kakamu da sonta a lokacin ita kuma zata rama
abinda kayi mata shiyasa nake so ka dinga
abubuwan a hankali...
Mujahid yace nifa na gaya maka ban iya yar
murya a gun mace ba, yadda na saba tafiyar da
mata itama haka zantafiyar da ita.
Amir yace in tagaji tana iya cewa ba zata zauna
ba.
Kasandai su abba bazasu kara barinka ka zauna
babu mace ba alokacin bazasuce ka kawo mace
da kanka ba duk wadda tasamu baka zasuyi ba
yadda ka iya kuma.A nan nr jikinsa yayi sanyi ya
ce mu bar gun nan dan Allah amir ina da binyi
fa.
Ya bude motar ya dawo gaba, amir ya ja mota
yana fafadin basan abinda kake hange ba da
kake cewa nabila tayi ma kankanta.
Bai ce ko mai ba ya dauke kansa yana lumshe
ido.aranar da zazzabi nabila ta wuni babu party
a washegarin lahadi sai da daddare ne akayi
walima ta maza zalla a gidan su amir, wuni su
inna sukayi da rana amarya na kwance
kawayenta sai kaiwa da dawowa anci ansha anyi
hani'an babu abinda bai wadata ba a gidan
bakin nan , mutane ba abun da suke bada
labari irin facakar likin da ake da naira agun
party da kudin da ake kashewa gun ga
abubuwan ci nan da nasha.
Ranar litinin bayan la'asar akayi sisters day, a
gidan dan hausa washegari talata aka rufe biki
da picnic na zallar yanmata da samari da
yamma daf da magariba suka dawo dare nayi
aka tafi gala night wanda shima yanmata ne da
samari kadai.
Washegari karfe goma shabiyun dare suka
dawo, bikin nabila da mujahid yazamo abin
bada labari sati guda ana shagali ana kashe
kudi sai ranar laraba da safe aka kai nabila
gidan dangin mijinta da sukayi masauki a gidan
alhaji muktar alokacin mujahid na can dakin
amir yana ta bacci shi kadai ya kullo kofa ya
kashe dukkan wayoyinshi dan baison kowa ya
dameshi.
Iyayan nabila suka danka amanarta a hannun
iyayan ango suka amsa da adu'ar Allah ya
taimaka musu su sauke amanar aka basu suka
yi godiya mai yawa da karamci da akayi musu
aka basu ya.
Inna tace mune da godiya da aka nemi diyar
tamu duk wanda yazo yace yana son yar ka da
aure ko shakka babu ya isa masoyinka, domin
shi aure idan akayishi anzama jini daya ne.





Zaharaddeen Shomar

Whatsapp 08168575100




Launin Fata 2-08
Posted by ANaM Dorayi on 09:39 AM, 23-Oct-15
Under: Launin Fata
Jini daya kuwa ba wasa bane, idan mutun
baisonka ba zai so ya kusanceka ba ma
balantana haryace zai hada jini da kai, ba
bakaramar soyayya da girmama mutum akai ba
in akace ana son nashi da aure, mata nawa aka
tsallake aka ce ana son taka.Hajiyar su amir ta ce
gskiya ne inna amma dukda haka mu ne da
godiya ka nema abaka shine darajar da
girmamawar mutum nawa suke nema basu samu
ba mu muka nema aka bamu, duk wanda ka
nema yarsa da aure yabaka lallai ba karamar
soyayya yake maka ba.
Wanda bai kaunar ganinka ma bai son yi
balantana yaso hada jini dakai. Gaba daya aka ce
wannan maganar gaskiya ce.Aka yi addu'a aka ci
gaba da barkwanci kana wata mata ta fito da
wasu madaidaitan farantai guda uku daya
ancikashi da kayan marmari masu kyau irinsu
tuffa da kankana da abarba da lemon zaki
lafiyayu suna ta kamshi, dayan kuma turarukane
masu tsananin kamshi da tsada, dayan kuma
turaren wutane nadaki masu kamshin gaske, a
dan kananun kwalabe masu kyau suma guda
goma gyafe guda an zuba dabino da kwakwa, ta
mikawa dangin amarya tace munsiya bakin
amarya Allah yasa kada tayiwa ango
gaddama.Aka tuntsire da dariya gaba daya suka
dawo da nabila gidansu sai gari ya waye zasuyi
asubanci tafi malesia da angonta. Tun aranar
nabila ke kuka bayan sallar azahar baba mahmud
ya kirata zaure shi kadai ta isa gabansa, ta
durkusa tana sharar kwalla ya ce ki daina kuka
nabila aure gata ne da rahama ba ukuba bane
balantana kiyita kuka haka ni dai abinda nake so
da ke shine kiji tsoron Allah kiyi wa mijinki biyya
dukkan hakkinsa da ya rataya a wuyanki kibashi
idan kinyi haka Allah zai samiki Albarka da
rayuwarki, ki dage kiyi hakuri sosai gaba daya
rayuwar aure hakuri ce rayuwace zakiyita da
mutumin da baki saba dashi ba, kuma zakiyi
abubuwan da baki saba dasu ba a gidan da baki
saba dashi ba, to annan ma hakurine zaiyi
aikinsa har kisaba din. Na gode sosai da biyayyar
da kika yi mun in sha Allahu zakiga alkairi
arayuwarki. Kukan da take ya bashi tausayi sosai
ya kamo hannunta ya shiga da ita cikin gidan
matan gidan na zaune na kallon ikon Allah gashi
basu isa su hana komi ba. * nabila ta gama
sallama da kowa a kano a kano ta dau abin da ta
fi bukata sun bar gida Nigeria zuwa malesia ranar
alhamis da yamma, tunkafin aje a mori amarci da
jin dadin nabila ta kara kyau sai dai rama na
damuwar da mujahid ke kunsa mata da azabar
sonsa dake zuciyarta. Shi da ita da amir suka isa
gidan iyayansa da kannansa mata biyu
kamanninsu daya su suka koma egypt yayin da
amir zai dada kwana biyu kan ya koma Nigeria
gida kano dabo jalla babbar hausa ko da me kazo
anfika. Yayi hakan ne dan ya kara kwantar wa
nabila da hankali ganin irin damuwar da take
ciki.. . Kafin iyayen mujahid yatafi sai da sukayi
mai gargadi sosai a kan ya kula da hakkin
yarinyar nan. Shi yace yana so ba wani ya cusa
mai ita ba, iyayanta kuma suka bashi bawani
dalili da zai sa su wula kanta masu ya. Abba ya
ce idan naji wani labari marar dadi akan zamanku
zaka faskanci fushi na. Takaicin da ya hanashi
sukuni kenan bayan tafiyarsu ya rasa abinda ke
mai dadi a duniya, daga yin auransu har za a
fara ta kura mai kan yarinyar da ba wani
damuwa yayi da ita ba. Ya tashi yayi wanka ya
sanya kaya zuwa kanana ya tsuke sosai ya baza
turare ya fito falo yasami amir kwance yana
kallon wani film yace zan fita zakaje? Amir ya
bishi da kallo ya ce haba lokacin yawo ai baiyi ba
yana da kyau ka koyi zama a gida tunda kasan da
da yanzu ba daya bane . Da baka da mace ba
nauyin kowa a kanka, yanzu kuwa kana da aure
yana cikin hakkin ka da da ya rataya a wuyanka
ka dinga zama a gida kana kana debe wa
matarka kewa, musanman a kasa irin wannan da
bata san kowa ba sai kai. Ya rausayar da kai yana
murmushi yace amma dai kasan ni dalibine har
kokin karatu ba zasu barni in dinga zama ba, ita
din ma makaranta zata rinka xuwa nan da dan
lokaci. Bai jira wani bayanin amir dake bata mai
rai ba ya wuce ya bar gidan, nabila na kicin tana
da dafawa amir abinci yace yunwa yake ji ta
gama ta kawo mai ya dubeta cike da tausayawa
yace kinci naki ne. Ta ce banci ba. A daki zaki ci?
Yace a a ki daure ki ci alamunki sun nuna kina jin
yunwa, idan baki ciba nima ba zan ciba, nasan
ina jin yunwa amma sabodake na tayar da dake
yin girkin yanzu. Ta zame ta zauna a gunta ta
dora kanta a cinyoyinta ta kama sharar kwalla.
Tace idan kasani naci abinci yau gobe da jibi da
sauran ranaku wa zai lallasheni in ci? Banaso in
saba da abin da ba zai dore ba gareni. Nafiso inci
gaba da tafiya yadda mai gidan yatafi da
rayuwarmu a hankali zansaba. Amir yace nabila
nasan dole ki damu kan abinda mujahid yake
miki amma dan Allah ina so ki ci gaba da ba
mara da kunya kiyi hakuri, duk wadannan
abubuwan da mujahid ke maki watarana sai kin
tausaya mai idan yazo hannunki. Tace amir
hakuri yazama dole ga zuciyar da ta kamu da son
wanda bai damu da ita ba, ba zan ce maka ina
bakin ciki da haduwata da mujahid ba saboda
bansan abun da zai faru gobe ba sai Allah, amma
duk da haka ina takaicin kasancewata a wannan
halin ban taba son wani ba sai shi.Amir ya gyara
zama ya ce nabila babu inda aka taba cin nasara
a rayuwa batare da an hada da hakuri ba, ita
nasara ne tana tafiya ki ci gaba da hakuri ki fidda
duk wata da damuwa a kan mujahid watarana
zakiyi mamakinsa. Ke ba matar da za a iya ci
gaba da daukewa kai ba ce musanmam ga
mujahid da yake da fitinar sha'awa, zan gaya
miki sirrin mujahid wanda indai kina mashi shi ya
shiga hannunki ko baya so. Nafarko mujahid
mutum ne mai son tsafta baya son kazanta ko
yaushe cikin kamshi yake yana son duk wanda zai
rabeshi ya zama mai tsafta, ki dage a wannan
zaki ja ra'ayinsa. Na biyu mujahid mutum ne
wanda baya son raini idan har zaki rinka
girmamashi kina nunawa ke ba ko mai bace a
gunsa to kin gama dashi. Sannan mujahid mutum
ne mai son wayayyar mace shiyasa bai son
karamar yarinya, dan kada ta zo mai da raini da
duhun kai, ko da yaushe ki rinka tsukewa cikin
kananan kayan da muka jubgo maki a lefe in zaki
lura hoogs sunfi yawa a lefenki da kaina na saye
su saboda kija ra'ayinsa da su. Ko mujahid bai
niyyar kula mace ba in taja ra'ayinsa da
waddanan kayan sai kiga ya saurareta. * kamkam
ta rike hudubar da amir yayi mata, kwananta
uku ya koma kano ya bar nabila cikin kewar hira
debe kewa da yake mata da shawarwarin da
yake bata. Dk safiya mujahid zai fice bai dawowa
sai yamma, zai bar gidan kalkal ya dawo ya sa
mai kalkal, ko ina na kamshi turaran kamshi
turaran wutar da ta taho da shi da na ruwa dare
da rana yinsa take a gidan, wannan ne abu na
farko da ya fara daukar hankalin mujahid game
da nabila, yana son tsafta da kamshi in ya shigo
kuma zata tareshi a falo a cikin kwalliya ta jan
hankali ta gaidashi ta karbi jakar hannunsa ta
rakashi daki ta fito ta barshi yayi wankansa ya
shirya kaya.. Duk abinda take takan ajiye ta
zauna a falo hanyar da zaifita takan ce mai an
shirya mai abinci randa yaga dama ya ci kadan
ya tashi randa bai da ra'ayi ya ce ya gode ya
koashi abincin da take bata lokaci sosai gun
dafashi ta sha wahala amma wanda akayi danshi
in ya zo sai yace ya koshi, idan ya fita da
yamman nan bai dawowa gida sai tsakar dare
yana dan lekawa dakinta kana yawuce nasa dakin
ya yi bacci. Kusan kullun abbansa ko umman sa
sun kirashi a waya suna tambayar lafiyar nabila
ya yace kalau take itama in sun kirata sun
tambayeta haka take gaya musu har ta shafe
wata uku a gidan bata taba nuna musu tana da
matsala da mujinta ba, haka shima baba
mahmud daga gida kano ko yaushe yana mata
waya su gaisa haka amir shi da yake yasan komai
shi yake dada yi mata nasiha da ban hakuri.Ta
kance dashi amir ka dai na bani hakuri hakuri
yazama dole ina hakuri da mujahid hakurin da
ban taba tunanin zan yishi da da namiji saboda
son da nake mashi.
Amma nasan da cewa gaskiyane da hausawa
kance mai hakuri zai dafa dutse har yasha
romansa.
Ni na dora nawa dutsen a wuta ina ta dafa shi
watarana in har muna raye zai dahu nasani.
Tana yawan baiwa amir tausayi.
Idan ya ma mujahid magana sai ya rufeshi da
fada sai yace wai me kake so in mata ne goya
ta zanyi, sanin kanka ne ba zan zauna inlalace
gun yar karamar yarinya haka ba mai zan tsinta
a jikin nata?
Aure ne aka ce sai nayi kuma nayi ina
gargadinka da ka kama bakinka kada kasake ka
gayawa abbanmu abinda kasan zaimin fada.
Amir yayi murmushi in har ba kan gaskiya kake
tafiya ba abba da kansa zai gano haka ba sai na
fadi mai ba.
Hatta abinci da abinsha din da mujahid ke so
amir ke gayawa nabila yana cewa ta daure tana
yi mashi in yau baiciba gobe zaici in har yana
yin dadi zai daina cin abincin kowa sai nata.
Ranar da ta cika wata uku cif a gidan tana
zaune da sassafe ta fito da wasu rantsantsun
body hoogs haduwa rigane da wando sun matse
jikinta kam kam Duka surorinta sun bayyana ta
saki gashin kanta a kafada, duk da ba wani jin
dadin kasan mujahid ya mallaka mata ta fannin
soyayya ba amma jikinta ba karamin kyau yayi
ba, fatarta ta kara gogewa da haske sosai irin
kalar nan mai tsada.
Jikinta da falon na wani irin bacci mai dadin
gaske, wani yaron mujahid mai hidimar gidan ya
kwankwasa kofa ta mike ta bude yagaida ita ya
miko mata wasu takardu yace wanine ya kawo
yace abawa mai gida.
Ta karbi ta juyo ne suka hada ido da oga
mujahid yana tsaye kofar dakin baccinsa ya
zuba mata ido zuciya ta gama kule shi ganin irin
kallon da yaron yake mata na zalam, ta iso
gabansa ta tsuguna ta gaida shi ta mike mai
takardun, ya danna mata harara ya ce dama
haka kikeyi da ma'aikatan gidan nan?
Ta ce me nayi kuma?
Yace me kikayi me yasa ya kwankwasa kofar
baki lullube jikinki ba kika fita a haka ya gama
ganinki.
Cikin sanyin murya ta ce ka yi hakuri zan kiyaye
a gaba.
A nan ne jikin mujahid ya yi sanyi har yanzu
idonsa a kan ta yake, wannan itace rana ta
farko da ya kare mata kallo da bai taba yi mata
ba.
Ya fara fahimtar abinda bai fahimta tana da shi
ba, ya kasa dauke idonsa a kanta ko ranar da
ya fara ganinta har yace yana sonta bai mata
irin wannan kallon ba.
Ya gyada kai yace tashi ki zauna.
Ta mike ko ina na jikinta rawa yake, yarinya
danya sharaf tana kan gabar budurci komi na
jikinta ya bude ta cika taf ya haramtawa kansa
halal dinsa wai dan kawai ta raina shi.
Har ya kai bakin kofa yaji tace ga abincinka ka
daure dan Allah ka ci.
Ya waigo suka hada ido tayi shirin maida nata
idon kasa yayi ajiyar zuciya ya koma kan tebur
yace to zo ki zuba mini.
Ta taso tayi sauri ta zuba mai, yana mamakin
yadda ta haddace abincikan da yafi so ta iya
dafasu yadda yake bukata, yaci sosai yana yi
yana satar kallonta idan sun hada ido sai yasha
mur ya dauke kanshi, har abin ya fara bata
dariya tsammaninsa bata wayo ne saboda yana
daukarta yarinya mai karancin wayewa a
wannan fannin.
Bai san tana da nata wayon ba duk yadda yake
tunaninta ba haka take ba, a kansa ta zama mai
hakuri da kauda kai, saboda babu wani tsari da
zuciyarta zata iya a kansa a dalilin tsananin son
da take masa.
A gabansa ne bakinta ke mutuwa tsiwarta ba
zatayi tasiri a kansa ba da zarar taganshi jikinta
mutuwa yake shi kadai ne namijin da ya isa tayi
mai komai yana so da baya so dan zuciyarsa
tayi haske.
Bayan ya gama cin abinci ya mike ta amshi
jakarshi zata rakashi waje, ya manna mata
harara yace a hakan zaki kara fita ko Ta dubi
jikinta kana tashiga daki ta dauko zani ta lullube
jikinta tayi ajiyar zuciya haka kawai yau yasamu
kansa da son kallonta.
Jikinsa yayi sanyi da ya shiga mota ta mika mai
jakar ta rusuna tace adawo lfy Allah ya kiyaye
hanya.
Rana ta farko da taga yayi mata murmushi ya
ce amin yi maza ki koma ciki bana so ana
kallonki.
Itama murmushi tayi masa ta ce to.
Murmushin da ya tsaya mai a zuciya har ya
shiga makaranta yana tunanin fiskarta yadda
murmushin yai bala'in yi mata kyau tunaninsa
shine dama yarinyar nan tana da kyau haka.
Gaskiya za a huta a jikinta sai da muwarsa ita ce
kada tazo ta raina shi, ko da yake ya fahimci
tana da ladabi da hakuri duk dauke mata kan
da yake dare da safe in dai zai shigo gidan sai
tayi mai adu'ar Allah ya bada sa'a bai taba
mata kallon rahama ba sai yau duk da haka
bata fasa ba.
Yana shirin fitowa daga motar sa wata
budurwarsa mimi ta iso da sauri ta karbi jakarsa
ta bude hannu suka rumgumi juna yace nayi
mising dinki mimi kamar nabiki kasarku yaushe
kika dawo?
Ta lankasar da kanta a kirjinsa tace nasan ban
isa ka bini ba shiyasa bansa ran zaka bini din
ba, yau da asuba na dawo gidanka nayi niyar
zuwa fatyz ta ce mun kayi aure kuma ka gargadi
dukan yanmatanka kada wadda ta kara zuwa
gidanka yanzu kana da mata, bakincikin hakan
yasa na nufo makarantar nan yanzu saboda na
baro gida cike da kewarka, ina kishin ruwan
kirjinka da soyayyarka, ka taimake ni.
Mujahid ya lumshe ido ya maida ta cikin mota
ya shige ya suka nufi inda zasu huta, soyaya ta
fitar hankali sukayi a wannan rana suka sha giya
yadda suke so tun safiya sai tsakiyar dare suka
rabu, mujahid yayi bacinsa ya isheshi ya tashi
yayi wanka, ya fiddo wasu kayan a motarsa ya
bazo turare ya dawo gida yana wani shan
kamshi kamar ba shi ba.
A falo ya iske nabila tana zaune tayi tagumi
lokaci baiyi ba ta sani da zata gaji da zaman
hakuri da take a gidan mujahid amma yau
hankalinta ya fara tashi.
Tun safe yayi mata murmushi jikinta ya sauya
zuciyarta ta tsumu da son ya rinka kasancewa
da ita kamar kowanne mata da mijin ta wuni
cikin wannan halin, da yamma ta sauko harabar
cikin gidan ta zauna tana karanta wani littafi na
hausa da tayo guzirin abinta daga gida sanin irin
zaman da zatayi kadaici da kewa suna damunta
na rashin abokin hira.
Wata sisi ta shigo gidan tana takun kwas kwas
kamar zata karye, ta tambayi yaron gidan ima
ko mai gidan na nan, ya ce baya nan amma ga
matarsa can, ya nuna mata nabila ta iso
gabanta tana wani irin kallo cikinharshen turanci
tace tana son zama ta jira mujahid a nan. Cikin
takaici nabila tace ba zai yuwu ba nan gidan
matar aure ne ba gidan karuwa ba, ta yi sauri
ta fice ranta ya baci, haushi ya kamata ta ce
koda yaushe nan fa take zuwa ta jirashi nabila
ta buga mata tsawa ta ce idan bata fita ba sai
tasa an mata duka, ta fice tana fadin sai ta
gayawa mujahid din.
Nabila ta mike ta koma cikin daki ta kwanta a
gado ta matse idonta yaushe ne lokacin da
mujahid zai saurareta duk da cewa bata taba
aure ba amma ta san ba haka ake zaman aure
ba ta dafa abinci ba a ranar saboda tsabar
sanyin da jikinta yayi tun bata fi sati a gidan ba
ta san mujahid mayan mata ne ita da take
zaman halal din sa bai kula ta ba.
Riga da zani na atanfa ne a jikinta ba wani
make up a fuskarta sai dai daddadan kanshin
nan na kullum wanda mujahid ke matukar so.
Daga zaunan da take ta ce mai sannu da
zuwa.....



Zanaraddeen Shomar

Whatsapp 08168575100




Launin Fata 2-09
Posted by ANaM Dorayi on 09:40 AM, 23-Oct-15
Under: Launin Fata
Tausayinta ya kama shi ya matso daf da ita ya ce
baki da lafiya ne yau?
Lafiyata kalau.
Ta bashi amsa a takaice.
Bai ce komai ba ya wuce dakinsa baccine har
yanzu a idonsa ko kayan jikinsa bai cire ba
takalminsa ma na kafarsa,cikin karuwansa na
makarantarsu tana juriyar shanye fitinar sa
batsaa raki in zai kwana yana takarta ba zata
kosa ba, irin wadan nan matan sun fi burge shi.
Nabila ta kasa juriya ga halin da take ciki ta
dubi a gogo ta jawo waya ta kirawo numbar
amir.
Bayan sun gaisa ta ce Dan Allah kazo ka tafi
dani gida ban iya ci gaba da zama a garin nan
ban san kowa ba sai mujahid shi kuma bai da
lokacina duk lokacinsa na makarantunsa ne da
holewa da karuwansa, na yi iya kokari na in
shawo kansa in jawo hankalinsa da duk abinda
ka nuna mini da wanda nimaa na sani banyi na
sara ba.
Na hakura dashi izawa wannan lokacin na san
ba zan sami nasara a kansa ba na hakura in sha
Allahu hakuri zai zame mun maganin ciwon sasa
da ke damun zuciya ta.
Amir yayi murmushi yace na yarda ke yarinyace
nabila kuruciya na damunki yanda na fahimci
kina son mujahid ko shekara goma ina zaton
zaki kina jiran lokacin da zai shigo hannunki ba
zaki kosa ba.
Sai gashi watanni uku kacal kina fadin kin
hakura?
Nasha gaya maki ba a cin nasara sai anyi
hakuri, shi kuma hakuri da kike ganinsa shine
abinda yafi komai wahala kafin ayishi sai ansha
wahala, wannan hakurin shine zai mallaka maki
mujahid kuma shine zai rike maki zuciyarsa a
gaba duk inda ya shiga yana tare da tunaninki.
Nabila nasan nura tun shi bai gama sanin kansa
ba, na san abinda yake so da wanda baya so,
da ace nasan ba zaki iya jan hankalinsa ya shigo
hannunki ba da ba zan bari ki zauna da shi ba
har yanzu ko anyi auran naku sai na san yanda
nayi kika dawo gida.
Amma da yake nasan ke irin matar da yake
matukar so ne kuma nasan shi mayan mata ne
shine dalilin da yasa iyayansa suka takura yayi
aure bai da hakuri a kan mace macen kuma
irinki.
Kada kiyi gajen hakuri ki maida aikinki baya
kada ki bari ki rasa masoyinki wanda zuciyarki
take so daga baya kizo kiyi nadama.
Kici gaba da hakuri wata rana zaki ci riba.
Kuma duk yanda kike shan damuwa ta
bangaren shi kada ki sake ki kai karan mujahid
baya so a hadashi da iyayensa, ni kadai ne zan
kai kararsa ga iyayensa, ya hakura dan ni babu
yanda zaiyi dani.
Bayan sun ajiye wayar ta mike ta shiga dakin
nasa ta durkusa dai dai kansa tana kallonsa ko
mai kyau yakewa mujahid hatta bacci inyanayi
kamar karya tashi, ta shafi sajen fuskarsa sai
taji yayi ajiyar zuciya ta matsa da sauri a zatonta
farkawa zaiyi ya mareta ya ce ta raina shi.
Lallai fauzeeya tayi gaskiya da tace babu wanda
zata so bayan mujahid sabo da shine wanda
zuciyarta ta fara so, rabuwa dashi zai haifar da
damuwa mai tsanani a zuciyarta.
Yazama wajibi taci gaba da hakuri dashi har
zuwa lokacin da zata samu zuciyarsa.
Idan bata bar gidanshi dan damuwar shi
damuwar da zata shiga a gidansu inda bata
ganinsa sai ta ninka wadda take ciki a yanzu.
Saboda nandin gidansa da take yana kwashe
mata rabin damuwar da duk damuwar da take
ciki idan mujahid ya shigo zuciyarta sai tayi
haske taji dadi ta dinga tunanin wanne irin so
take wa gayen nan ne?
da gari ya waye ta shirya mai abinci mai rai da
lafiya yau ma sai ta sanya a tamfa riga da zani
ta kulle kanta tsam batayi wata kwalliya ta a zo
a gani ba..
Mujahid ya fito daga dakinsa cikin kananan kaya
(giant sosai) ya fidda space din idonsa ya
dubeta a yatsune ya amsa gaisuwarta yace
daman wadannan kayan kika saba sawa?
Ta sunkuyar da kanta kasa tace naji kace in
daina sawa ma aikatan gidannan na kallo na.
Yayi murmushi yace ai ba ina nufin ki daina
sawa gaba

Please Login or Register in order to submit comment