Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saratu wani suna ya dace a sawa yarnan?
Ta ce na taba jin tahir yana son suna nabila.
Yace shikenan angama magana sunan wanan
yarinyar nabila, Allah ya rayata Allah ya sa mata
albarka.
Saratu tace amin.
Ya mika mata ita zai fita sai ga ummin Rabi'a
tare da fatema da bashir da nafisa.
Rabi'a ta mike ta rumgume ummi tana kuka,
itama ummi kukan ta kama yi Bashir yace to
meye abin kuka kamar wada akayi muku
mutuwa.Nafisa ma haka tace, fateema ce mai
tayasu kukan, ummi tace an yi yanka ne?
Rabi ta ce a a.
Tace to akwai rago a mota saboda haka na ce
bashir sayo wa za a yiwa magana a yanka.
Tace bari na kira saratu a tambayeta.
Matan gida suka fito tsakar gida ana shewa da
yada magana a wulakance suka masa gaisuwar su
ummi, nafisa tace gaskiya ummi tafiya zanyi bana
son harka tatsiya wannan ba xan iya zama a
gidan nan ba inna cigaba da zama ina ganin
wadannan abubuwan rigima za'ayi dani.
Ummi tace muma tafiya zamuyi kinsan abba yana
nan banda kinxo ma da ba zai barmu mu zo ba.
Baba ibrahim ne ya yanka ragon shida bashir
sukayi komaidole su ummi suka tsaya har akayi
azahar ta ba rabi'a kudi masu yawa ta duk
abinda bata dashi ta siya kada ta yarda ta bar
gidan nan abba yaga gaxawarta suyi mata dariya
shida su nura da nafisa.
Da sukayi waya da asiya daga london ma haka ta
gaya mata tace kin burgeni Rabi'a hakurin da
kikayi ba xai fadi kasa a banxa ba isha'allahu sai
kinga sakamakon hakuri domin Alla (s w a) shi
yayi alkawarin yana tare da masu hakuri.
Tace anty asiya kina zaune lfy da nazir ko?
Tace eh muna xaune lfy da nazir don yana sona
ma iyaka abba ya yi min illar da yasaba yimana a
gun surikansa ma'ana ya nuna kwadayinsa a fili
ga nazir, ko haka wani dan sabani ya hadamu
dashi sai ya nuna mini kwadayin ubana, wanda
hakan ba karamin ciwo yake yimun ba.
Ko da yaushe sai na tunaki tare da jin jina maki
da kika tsaya kan ra'ayinki kin samu soyayya mai
tsarki a gun mijinki wanda babu al'gus a
cikinta.Lokacin da tahir ya cika shekara daya cif
bai dawo ba mutanen gida suka fara yan
tsegumgumi akan xamar matar shi cikin gida.
Wasu suna cewa a sallameta ta tafi gidansu wasu
suna cewa a kai kara kotu a raba auran harda
masu cewa idan anraba auran su suna so kowa
dai yana kawo nasa son zuciyar, wani abun in
rabi'a taji tayi kuka wani abun tayi dariya.
Takan raba dare akullum tana adu'ar in har
mijinta yana raye Allah ya dawo mata dashi.Don
har yanxu babu namijin da take so take kauna
sai shi, tayi kuka tayi kuka kamar kwayan idonta
zai zazzago, saboda rashin mijinta abin
alfaharinta.
Wani lokacin idan nabila tana kuka sai ta dinga
ganin kamar kukan maraicin rashin uba take.
Sai itama ta kama kuka ta dau yar ta rungume
tana fadin yi hakuri nabila ba ke kadai zakiyi
kuka ba tare zamuyi kukan rashin mahaifinki
jarumin namiji daya tamkar da dubu mai tausayi
da kulawa.
Sai tayi mai isarta take hakura tashare hawayenta
tunda babu mai lallashinta.
Sau daya taje gidansu ta kai ma abbanta yar ya
karbeta yace dubi sanadin auran bakin mutum
kin haifo bakar ya saboda taurin kai irin naki duk
zuri'ar mu ba baki sai wanan yar.
Ya jefa mata abinta kan cinyarta ya mike yana
tsaki zai fita ummi tayi murmushi tace wannan
yar tazamo abin alfahari a gidan nan tunda ita ce
jika ta farko a gidan nan kuma insha Allahu sai
anyi alfahari da ita har kai kanka.
Domin ka ba Rufa'i diyar fararan mutane ita da
iyayenta sun ce ba zata haihu ba, Rufa' bai ajiye
mana jika a gidan nan ba, nafisa ka aurar da ita
ga mai kudi (half case) ya ce bai yarda da
haihuwa ba bai son yaya bata ajiye mana jika a
gidan nanba, ga asiya can a london a gaba na a
gabanka yace ba zai rufe mana ko mai ba zai
mata allurar hana haihuwa saboda bai shirya
haihuwa yanxu ba.
Abba yaja tsaki yace shine me?
Dan rufa'i da nafisa da asiya ba su haihu ba har
wani abu ne?
Tace wani abune mana.
Kai yanzu da me kake takama in ba da yayanka
ba.
Kamayar dasu hannun jari da kake samun kudi
shiga da su in har haihuwa ba wani abu bace ba
xakayi takama dasu ba.
Yayi mata wani lalatacen kallo ya wuce bai kuma
cewa komi ba lamarin baiwa rabi'a dadi ba ta
kama sharar kwalla.
Ummi tace ki daina bata hawayenki a banza, in
sha Allahu sai abba ya ci gajiyar wannan yar da
ubanta sai ya gano kuskuren da yake tafkawa.
Har rabi'a ta baro gidansu a ranar bata daina
kuka ba shine dalilin da yasa bata kara zuwa
ba.Sai ummi ke zuwa ganinsu tana kawo musu
duk abin da suke bukata ita da fateema bashir in
yaxo hutu shima rufa'i yazo musu sau daya, nura
ko ko hanyar gidan bai taba yowa ba, halaiyarsu
daya da abba ta kyamar bakin mutum da talaka
kamar su sukayi kansu a fararan kuma su ne
suka baiwa kansu arzikin. * nabila na da wata 5
ta iya xama sosai, rabi'a ta gaji da zaman da
take yi haka ta fara zuwa islamiyar matan aure
dake bayan gidansu ta asabar da lahadi. Ranar
wata laraba wuraren karfe 8 na dare, danladi ya
shigo dakin ta yana salama a hankali babu
mahalukin da ta tsana irin daladi ta ajiye littafi
arba'una hadis da take dubawa ta kwantar da
nabila cikin net dinta ta kura mai ido lokaci daya
yake zama kujera tace lafiya? Yayi wani munafikin
murmushi yace ita ta kawo haka. Tace to tashi
kafitan min daga daki ko nayi maka ihu. Ya bushe
da dariya yace idan kinyi mini ihu abin kanki zai
kare gara na kirufa wa kanki asiri ki tsaya kiji
abinda nazo na fada maki. Ta saki baki tana
kallon shi tace to koma me zaka fada mini ban ga
dalilin da zaka shigo min daki awanan lokacin
kanka tsaye haka ba. Kada ka manta nanfa dakin
matar aure ne, idan akayi ma haka dakin
matarka ranka ba zai so ba, akwai hadisin
manzon rahama (s a w) da yake cewa imanin
dayanku baya cika har sai ya sowa dan uwansa
abinda ya ke sowa kansa. Ina nasiha gareka
mhmd kaji tsoron Allah ka dinga tuna gamuwarka
da Allah. Ka daina barin shaidan na wasa da
hankalinka da zuciyarka, kasani duk abinda kayi
sai anyi maka shi. Alokacin ne ta tabbatar jikinsa
yayi sanyi tasan inda ba a kaunar tahir a gidan
nan ba ya xa ayi manyan gidan nan susawa
danladi ido yana haike mata haka. Ko a tsakar
gida yasameta ta ayyukan da ta saba sai ya dinga
yi mata maganganun da basu kamata ba ko
matarsa tana gurin ba abin da ya dameshi,
amma duk cikin gidan ba bu wanda ya taba ko
da kalubalantarsa kan haka balantana a samu
wanda zai tsawatar masa. Batasan wane irin
tunani yayi ba sai yatashi ya fice, tabishi da ido
daga bisani tayi tagumi hawaye nazuba a idonta
ta dauki nabila ta kamkameta tana fadin tahir ina
kashiga ne ka barni cikin fitinar yan uwanka?
Tatashi tasawa kofarta key dan kada ya dawo *
tunda tahaihu tayi 40 ayyukan gidan suka ninka
na da ta daina sa lamuransu a ranta tana
damuwa, damuwar rashin sanin inda yake kadai
ya isheta ta kan goya yarta tayi ta fama da
ayyuka tun safe har yamma, in badare yayi ba
bata samun hutu. Sukance mai kankanba da
iyayin tsiya bai nan tayi aiki a kan dole. Tana
tsugunne tana tatar koko da hantsi daladi ya
shigo ya tsaya a kanta sai dije nagefe har
matarshi lubabatu suna hira yace oh malama
rabi tata ake ne? Ko daga kai batayi ba ta
dubeshi tama ci gaba da aikinta, yayi magana
tayi mai banza. Sai kawai lubabatu matar tasa ta
fashe da kuka. ta tashi tashiga dakin mahaifiyar
danladi shi kuma ya kada kansa yayi waje, yayin
da duka matan gidan sukabi bayan lubabatu tana
gaban innar danladi tana kuka tace inna nikam
nagaji da wulakancin da danladi yake yi mun a
kan wanan kodadiyar yarinyar da watakila ma
mayyace.
Idan so yake ya aure ta ya fito fili mana ya fada?
Nanfa matan gidan kowa ya ta fadin albarkacin
bakinsa wasu na fadin ba laifin daladi bane laifin
Rabi'a ne ita ke masa kisisina har taja ra'ayinsa
yarinya sai shegen feleken tsiya, yanda ta mallake
tahir haka takeso tayiwa danladi shima in ya
aureta a nemesa a rasa.
Innarsa tace Allah ya sauwake ki share hawayenki
zai gamu dani.
Yini guda ranar maganar da akeyi kenan
mamakin yanda aka lankayawa rabi sheri ya
isheta tana fadin wannan rashin tsoron Allah da
yawa yake, mutane sun san gaskiya kiri kiri
amma dan son zuciya da tsoro su take.
Danladi bai dawo gidan sai dare bai nufi dakin
kowa ba sai dakin Rabi'a sai ya tsaya a bakin
kofa ya kwankwasa mata kofa tace waye?
Yace nine danladi.
Tace kakoma ba zan bude ba.
Yace kidubi girman Allah ki bude da kanki idan
kinki budewa zan karya kofar.
Ta taso ta bude tana sanye da doguwar riga ta
dora dogon hijabi akan fiskarta murtuk kamar
bata taba yin dariya ba, ta jingina da kofa tace
lfy.
Sai tayi mai kwarjinin da bata taba yi mai ba ya
shiga inda inda sai taja tsaki tace idan har wanan
inda indar ce tasaka bugun kofa ka kama
gabanka dan bani da lokacin sauraranka.
Yace ah ba haka bane kin gane Rabi dan Allah ki
tausaya min ki bani hadin kai na rasa yanda
zanyi da sha'awarki da ke damuna in ma kin
yarda zamuyi aure zanyi muki duk abinda kike so
tunda kinga har yanzu tahir bai dawo ba.
Tayi masa wani wulakantacen kallo tace an dai
sha haushi an kuma fadi ba nauyi.
Ni ba yar iska bace na tabbatar da haka, auran
tahir dake kaina yana nan bangaji dashi ba ko zai
kai shekara goma bai dawo ba ina nan ina
jiransa, in har da yardata xakayi fasikanci dani to
ba ka isaba in kuma fyade zakayi mun kafili ga
mai doki.
Tuni dai kana sane da sharadin da na gindaya
ma duk sanda kasake kayi mini fyade kuma wlh
da gaske nake karka dauka barazana ce in kuma
ba kayarda ba kana ganin wasa ne ka gwada
kasha mamaki.
Ta maida kofar ta rufe da karfi ta barshi nan
tsaye ransa gaba daya ya baci ya shige dakin dije
yana banbami ya fada mata wulakancin da rabi
take masa dan yanuna yana sonta.
Ta ce rabu da shasha ta tsaya jiran mijin da babu
tabbacin rayuwarsa idan gari ya waye zansa a
rubuta takarda ka ba babanta kace tahir ne ya
aiko da ita daga inda yatafi yace a ba matarsa ka
nuna mai cewa zatafi daukar sakon da
muhinmanci idan shi ya bata da kansa saboda
shi tafi ganin darajarsa.
Ta kadar xata kumshi sako ne daga tahir yana
bada umurni daga matarshi rabi'a idan ta sami
muji tayi aure ya sauwake mata saboda bai san
ranar da zai dawo ba.
Ihu daladi yayi da tafi yana yiwa dije jinjina yana
fadin shike nan kinga an huta ta hakura dan dole
ta tafi gidansu daga can dan dole ta aureni ko
dan yarta.
(kaji wauta).
Irin wuraren karfe taran safiya rabi'a na falonta
tana wa nabila wanka baba ibirahim yayi sallama
rabi na ganin mutuncin dattajon sosai da
girmansa saboda yana tausaya mata da
kaunarta, ta lullube jinta da mayafi ta leko
rumgume da nabila ya amshe ta........


Zaharaddeen Shomar
Whatsapp 08168575100



Launin Fata 2-03
Posted by ANaM Dorayi on 07:08 PM, 22-Oct-15
Under: Launin Fata
Ya rungume, Rabi rabi ta durkusa har kasa ta
gaidashi ya amsa.
Yace rabi'a yau Allah ya amsa adu'ar mu ina
zaune da safiyar nan wani matashi yazo yace
mini sun hadu da tahir can wanigari cikin mali ya
bashi takarda yace a kawo miki ina ganin ta
gaisuwace dan muna yace a gaidamu yana nan
tafe.
Shiyasa nace ba zan baiwa kowa ya kawo miki da
kaina zan kawota in miki wannan albishi da kaina.
Hannun rabi'a narawa gabanta na faduwa ta
amshi takardar da hannu bib biyu tayiwa baba
ibrahim godiya mai yawa, yace ba ko mai rabi
Allah yayi maki albarka.
Ya mika mata nabila ya juya tana rawan jiki ta
yage ambulan abun da tagani anrubuta ne yasa
ta yanke jiki ta fadi kasa maga shiyan.
Ga abin da takardar ta kunsa.
BAYAN SALAMA IRIN TA ADDININ MUSULINCI,
DAGA MIJINKI TAHIR ZUWAGA MATATA RABI'A NA
BARKI GIDA CIKIN KUNCI GA TAFIYA TA TSAWAITA
INA GUDUN CUTAR DA RAYUWARKI A MATSAYINKI
NA KARAMAR YARINYA DAN HAKA NA YANKE
IGIYAR AURENA DAYA DAKE NA BAKI DAMA IN KIN
SAMI MIJI KIYI AURE.
Rufe idon da rabi tayi adu'a take Allah ya karbi
rayuwarta ta huta da wanan tashin hankalin da
take ciki tajima kwance dif nabila nata bugun
kirjinta tana cewa ma ma ma.
Da yake ta dan fara iya magana a lokacin
watanninta bakwai da haihuwa.
Zuwa can ta mike ta kara karanta takardar ta
nemi hawaye a idonta ta rasa sai dai kanta dake
sarawa kamar zai fashe, idanunta sunyi jawur
zuciyarta na faman turiri.
Ta dunga karanta adu'ar. Allahumma ajirni fiy
masibatiy wa akh lufniy khairan minha.
Ta daga hannuwanta biyu sama tace Allah na
tuba kayafe mini, Allah banyi bakin ciki da duk
abin da ka kaddara zai saman ba dan na
kasance butulu gareka da baiwar salihin miji na
gari wanda yake tsoronka sai dan zuciyata bata
da karfin kan duk abinda ya shafe shi, bani da
juriyar da zan iya shanye damuwar rabuwa da
mijina ban zubar da hawaye ba.
Da bazanyi kuka ba saboda nasan Allah ne ya
azurtani dashi alokacin da basanshi ba.
Allah na gode maka Allah kasa haka shi yafi
zama alkhairi garayuwata.
Ta mike tayo alwala tayi sallah raka'a 2 alokacin
karfe goma dai dai na safiya ta bude alkur'ani
mai girma ta dinga rero kira'a cikin suratul
bakara.
Sai alokacin hawaye ya dinga zubo mata idan
tayi kamar tayi shuru in ta kalli nabila sai
zuciyarta ta kara karaya, tausayin yarinyar ya
kara kamata hankalinta ya tashi ta kamota ta
rumgume ta ce wanan yarinya kin shigo duniya
cikin garari bansan yadda rayuwarki zata
kasance ba, nan gidan ba a kaunarmu gidan mu
mahaifina baya kaunar babanki nasan ba zai
bari ki zauna a gidanshi ba.
Nan kuma ba zaki rayu cikin farinciki ba, amma
akwai Allah yana sane damu shi yasan yanda
zaiyi damu.Su dije da danladi suka zuba ido
kwana daya biyu uku har saty basu ga rabi'a ta
kwashe kayan ta ta bar gidan ba, kuma bata
nuna wata damuwa ba a fuskarta, ta ci gaba da
ayyukanta na yau da kullum yadda ta saba.
Ranar da saty biyun ta cika har daki dije ta
isketa da yamma tace wai ke wace irin bakar
mayya ce?
Mijin nan naki ya gaji da tsotseshin da kike yi ya
gudu ya barki baki tafi gidanku ba, ya aiko maki
da takarda nanma dan naci baki tafi ba sai
yaushe?
Tace zan tafi ne umma sai nagama idda.
Taja tsaki ta fice tana fadin aikin banza mayya
kawai.
Lokacin ne rabi ta fara sabon tunani akan
takardar da aka kawo mata ta saki daga mijinta
masoyi nagaskiya tahir.
Shi kansa babfa ibrahim lullube mai maganar
akayi, baisan abin da maganar ta kunsa ba, ya
yadda ya kawo wa rabi yana murna anfara
samun lbr tahir haka yake tsanman gaskiyar
lamarin harcikin xuciyarsa.
Sai da maganar ta yadu a cikin gidan kunya ta
ishesa yaxo har dakin rabi yana hawaye da
idonsa yace nayi bakin ciki ace nine na kawo
takarda da hannuna.
Itama ta kama kuka tace dan Allah kayi hakuri
kadaina kuka baffa aure rai gareshi zaman lfy
da soyaya basa mutuwar aure idan wa'adinsa
ya cika haka rashin zaman lfy da kiyaya basa
kashe aure idan lokacinsa bayyi ba.
Rabi'a ta mike ta dauko takardar wadda ta
adana can kasan kayanta tasake karantawa tana
nazarin rubutun duk da cewa zuciyarta na
tsananin yi mats kunci.
Rubutm kam yana mata kama da na mijinta ta
mayar ta ninke takarda.
Ta kwanta tana tunani watarana da tahir
yasameta a kicin tana girki da tsakiyar rana ya
dawo daga makaranta yace gimbiyata me ake
dafa mana gaba daya unguwa ta kama da
kamshi haka.
Tace ah ni fa bani son zolaya.
Yace karkiyi zaton haka zolaya nake sauri ki
zubo mini yawu na sai tsinkewa yake.
Suna cin abinci suna fira yace mata Rabi'a anya
macen da ta kware a girki mijinta zai iya fushi
da ita.
Ta tun tsire da dariya tace in nace santy kake yi
fushi me zai hana in tayi laifi yayi fushi kuwa?
Yace kai koyayi sai ya huce kuma ina tabbatar
maki iya girki gamace yana ja mata wata daraja
ta musamman a gun mijinta yana kara dankon
soyaya tsananin mace da mijinta yana kara
kankame igiyar auransu.
Tace gaskiya santi kake.
Yace idan ma santy nayi banyi laifi ba Rabi'atu
kin cancanci ayi santi a kanki ta kowanne fanni,
dukkan mutun 9 yake bai cika goma ba, amma
ke din nan banga ta inda kika raga ba, igiyoyin
aure da ana daura goma ko dari zan daurata a
tsakanin nida ke bama ukun ba.
Auran mu da ni dake mutu karaba takalmin
kaza..
Mutu karaba takalmin kaza.
Kalmar da ta maimaitawa kenan to amma me
yakawo takardar saki?
Kaddara mana.
Ta ba kanta amsa.
watanni ukun da shari'a ta aje a matsayin idda
suka cika Rabi'a na dakinta a lokacin watannin
nabila goma da haihuwa.
Tana cikin tsananin fitina da zalamar mahmud a
lokacin ne ta yanke shawarar komawa gidansu
duk abinda Abbanta zai mata ya mata idan ta ci
gaba da zama a gidan mahmud zai yi galaba a
kanta wataran kuma ma meye amfanin zaman
natan?Rabi'a tayi ajiyar zuciya ta tashi tayo
alwala ta dau alkur'ani mai tsarki tafara karatun
suratul an'am, batasan taci gaba da kuka dan
kuka bai da an fani a gareta ba zai mata magani
matsalartar da take fuskanta ba a
rayuwarta.......
A falo Rufai tausayin yar labubuwar yarinyar
nan Nabila ya cikashi shi kansa ya rasa abinda
zai yi yarinya yar wata goma a rabata uwarta,
yatsaya cak kowa ya kasa magana ko nura duk
yanda yake bin ra'ayin abbansu sai da ransa ya
baci kan wanan rashin tausayin da ya nunawa
diyar rabi'a.
(KAR KU MANTA AN KOMA KAN ZARAN LABARIN
DA MUKA BARI TUN FARKO).
Ummi tace rufa'i katafi ka kaita in abbanku ya
dawo baka kaitaba wata sabuwar fitinarce ba
barinta zaiyi gidan nan ba.
Bashar yace to dolene Rabin sai ta zauna a
gidan nan.
Gidan wa zata zauna in bata zauna a nan ba,
zata cigaba da rayuwa cikin fushin mahaifinta ne
saboda yarta?
Hakuri xatayi Allah ne yasan yanda zaiyi da
rayuwar yar.
Fatima tamike ta amshi nabila ta rumgume har
yanzu bacci take ta dauki kayanta dake cikin
laida poly bag tace muje mu kaita yaya.
Bai ce ko mai ba ya wuce suka shiga mota zuwa
gidan su tahir.
Baffa ibrahim suka samu a kofar gidan suna fira
suka gaisa Rufa'i ya gabatar da abinda ke tafe
dasu duk son zuciyar danladi sai da yaga wautar
mahaifin rabi'a ya sa hannu ya amshi nabila
daga hannun fatima yace kace mun gode zamu
rike ta in sha Allahu.
Baffa ibrahim bakin cikine yasa ma yarasa
abinda ma zaice har su rufa'i suka wuce baice
komai ba.
Sai mahmud ne yace zan rike yarinyar nan
baffa.
Baffa ya girgida kai yana kallon nabila wadda ta
kwanta lamo jikin mahmud kamar tasan abinda
ke faruwa a kanta yace ba ruko ne masalar ba
kasan halin matan nan gidan nan.
Yace ba komai baffa tunda sukayi haka insha
Allahu wannan yarinya tana cikin kulawata da
amanata.
Baffa yace Allah ya tayaka riko Allah yayi ma
jagoranci kan kyakyawan aniyarka.
Ya shige gida rungume da nabila da kayanta ba
kowa a tsakar gidan matar tasama bata nan ya
zauna a daki ya dauko alawa ya dinga lasa mata
a baki zuciyar mahmud ta karaya tausayin
yarinyar ya dameshi da yawa.
Ya tuna sandasuka sa aka rubuta ta kardar saki
akan baiwar Allah rabi'a dan kawai ynason ya
aureta lokaci daya zuciyarsa ta sauya gumi ya
dinga keto masa ya fara tunanin meye
makomarsa kan wanan lamarin da ya aikata?
BAYAN SHEKARA GOMA SHA BIYAR.
Yadda Allah yaso haka rayuwa ke tafiya maka
haka mutane keso ko akasin haka.
Abubuwan da suka auku cikin shekaru goma
shabiyar suna cike da tarihin Rabi'a da diyarta
nabila da mahaifin nabila wato tahir.
Watanni shida bayan kai nabila gidansu tahir
lokaci guda abban rabi'a ya gudiri niyar komawa
garinsu yamen da xama sakamakon wata
gagarumar harka da ta fado hannunsa daga
manyan masu fada aji a kasar tasu, lokacin da
ta tara iyalansu ya saida musu bako zaiyi
halinsa, kowane ya girgiza amma ba kamar
Rabi'a wadda kukan da take na rabuwa da
yarta ne.
Nan tasan muddin suka koma yemen da zama
sunyi bankwana da yarta da mijinta wadda har
wannan lokacin bata fidda ran rabuwarsu ba
tunda komi na Allah ne tun lokacin da aka
rabata da nabila watanni shida da suka shude
ta tsananta da adu'ar Allah ya bata hakuri da
juriyar kan jarabawar da yayi mata.
Cikin ikon Allah tana samun saukin damuwarta
kuma tundaga wanan lokacin ne suka shirya
sosai da abbanta kusan yanzu yafi nuna
kulawarsa akanta fiye da kowane dansa.
Yayin da ita bata damu da hakan ba har abada
tasan ba zata daina ganin bakinsa ba akan
bakincikin da ya kullawa rayuwarta.
Daga baya ma tunanin da ya dinga shiga
zucuyarta shine anya ba damuwa ce tasa tahir
ya bar gida ya buya awani gurin ba.
Kuma ba kowane ya haddasa musu wannan
damuwar ba sai mahaifinta wanda yanuna ma
tahir zahirin kiyaya ko kunya baiji.
Bayan an gama shrye shiryen barin kano ana
yagobe zasu tashi ajirgi zuwa yemen tana zaune
a dakin ummi ta fahimci kukan da take, ummi
tace kiyi hakuri Rabi'a kije kiga nabila tafiya ba
mutuwa ba ce komawar mu yemen bashine
rabuwar mu da nabila har har abada ba.
Cikin kukan tace nabila ba ina gudun yanayin da
zan ganta a ciki, hankalina zai dada tashi ne fiye
da yan zu na hakura da nabila na san mun rabu
kenan Allah ne ya kaddara auranmu da tahir
dan in haifi nabila na gode masa.
Ta mike tafice tashiga cikin dakinsu ta kwanta
fatyma tashigo tace anty in baki so kitafi ki bar
nabila a kano me zai hana kiyi zamanki a kano?
In zauna a kano gidan wa?
Hakuri in biku yemen shi yafiye min alkairi,
haduwa ta nabila na san yadda Allah yayi.
Washegari da sassafe suka bar kano da zazzabi
mai zafi a jikin rabi wani abin ta kaici har da
abba a lallashinta kamar bashi ne ya ja mata
duk wata damuwa da take ciki ba.
Suka bar kano nabila na hannun inna mahaifiyar
mahmud babu abin da ta nema ta rasa duk
abin da takeso mahmud ke mata sai ya zamo
kamar mahaifinta ba ya yarda kowa ya taba ta
a gidan, saboda tsoron matarsa babu mai taba
ta mutanen gidan har mamakin son da mahmud
ke ma nabila suke.
Lokaci guda mahmud ya maida kansa dan kirki
ya daina tunanin auran Rabi'a balantana
sha'awarta da aikata fasikanci.
Lokacin da damuwarsa kan abin da ya aikata ya
dameshi sai ya yanke shawarar yaje gidansu
Rabi'a ya roki gafarta ya bayyana mata gaskiyar
lamari cewa wannan takarda fa ba tahir ne ya
aiko da ita ba.
Yana zuwa gidan ya iske mumunan labari cewa
su rabi'a sunyi kaura sun koma kasar
mahaifinsu ta haihuwa wato yemen.
Makocinsu aminin abba ne wanda aka daura
auran rabi'a a gabansa yayi wa mahmud
wannan bayanin lokacin da yaje gidan.
Tunda mahmud ya sunkuyar da kai zuface kawai
ke tsatsafo mai yana tunanin inda zaiga rabi'a
ya sauke nauyin hakkin da ya dauka, sai da
alhaji garba ya gama bayani kana ya dago kai
ya tambaye shi ko yasan inda suke a yemen
din?
Ya jin jina kai yace wlh ban taba zuwa kasar
yemen ba sai dai yayi min kwatancen garinsu da
unguwarsu kuma ina da number wayarsa,
nanda karshen shekara zani in kana bukatar
zuwa sai muje.
Mahmud ya dawo gida cikin ma tsananciyar
damuwa tun tuni gidansu a ke tsegumin cewa
makauniyar soyayar da ta kama tahir ta kama
mahmud tunda gashi ta bar gidan amma gaba
daya ya rasa sukuni sai ramewa yake yana fama
da tunani gaba daya yanayinsa ya sauya.
Ya dauko yarta ya manta a zuciyarsa babu dan
gata duk fadin gidan agunsa sai ita, yayansa ma
2 gasu nan bai damu da su ba yanda ya damu
da yar Rabi'a wato nabila, lubabatu matarsa tayi
masifar tayi bala'in har sakinta yayi akan
maganar nabila ta tsani nabila yadda ta tsani
mutuwarta amma ina mahmud yafi karfinta
babu yadda ta iya dashi.
Dole ta hakura ta dawo ta zauna ta hadiye kin
da takewa nabila dan in har yana gida to yana
manne da nabila itama tasaba dashi bata iya
bacci sai a jikinsa, kullun da safe in zai fita da
wayo suke rabuwa shi ke mata komai in bai nan
kuma tana hannun innarsa.
Itama tana son yarinyar tana yi mata gata,
nabila ta zamo yar gata fiye da kowane yaro a
gidan nan a gidan ba bu wanda ya taba zaton
faruwarsa.
Dama haka sha'anin ubangiji yake shi ke jujjuya
lamuransa yadda yaso a lokacin da ya so, yawan
kudin da aka kiyasta masa zai kashe yayin tafiya
yemen bai firgitashi ta fasa zuwa ba.Yayi
alkawarin zaije ko da zai dawo baya da ko
kwandala sai dai ya neme gafarar rabi'a kan
abin da yayi mata.
Mafarkan da yake yi da ita suna dada firgita shi
har kuka yake wani lokacin lamarin dake kara
tada hankalin matarsa kullum gidansu surutun
kenan Rabi'a mayya ce ta lashe mahmud kullun
yana tunaninta yana son yarta fiye da kowa.
Sai dai yana jinsu yana ta shirin tafiya yemen
kawai sai anawata sai ga watagaf da shekarar da
zata kare yaje ya tambayi Alhaji garba batun
tafiya ya tarar Allah yayi masa rasuwa, a dalilin
hadarin mota da ya rutsa dashi a kan hanyar
dutse zuwa kano kuma shima ta aziya yaje suna
dawowa matarsu ta fadi sai gawarsu aka kawo
gida.
Alokacin da aka korowa mahmud wanan bayani
zubewa yayi a gun yayi zaman dirshan ya daga
hannunsa sama yace ya Allah dukan dan adam
ajizi ne mai kuskure nasan ina aikata kuskure a
rayuwata na gano kuskure na na nemi hanyar
da zannemibaiwarka Rabi in roketa gafara ban
samu ba Allah ka yafe mini ka kaddara saduwar
mu in nemi gafararta.
A takaice nabila bata taso cikin maraicin iyaye ta
sha wahala amma gatan da mahmud ke nuna
mata yafi gaban a bayyana, mahassada na ci
gaba da hassadar su hassada naci gaba da
zama taki ga mai rabo.
Har wanan lokacin ba a samu labarin tahir ba
shekaru goma sha biyar kenan......




Zaharaddeen shomar
Whatsapp 08168575100




Launin Fata 2-04
Posted by ANaM Dorayi on 07:05 PM, 22-Oct-15
Under: Launin Fata
Da bacewarsa yayin da har wanan lokacin
mahmud bai daina fatan

Please Login or Register in order to submit comment