Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haduwa da Rabi'a ba ya
roki gafararta.
Nabila ta tashi a gidan tamkar wata tauraruwa
zarah cikin taurari saboda tsabar kyanta.
Ba fara bace kalkal wankan tarwadace mai haske,
tana da matukar kyan fuska da kyan diri ga wayo
da iya magana.
Tun tasowarta abin da ta dauka shine
mahaifiyarta ta rasu tasan inna itace kakarta
mahmud shi ta dauka mahaifinta, tun kan ta
mallaki hankalin kanta mahmud ya gargadi kowa
a gidan kada wanda ya sake ya bayyana wa
nabila ainihin lbr ta, duk wanda yayi haka zai
fuskanci bacin rai kusan a rayuwa irin tasu babu
abinda ta nema ta rasa tana da kokari sosai a
makaranta.
Rayuwar mahmud ta sami cigaba yana daga cikin
masu fada aji a cikin family dinsu, ya gina baban
gidansa a nan kano ya maida matarsa can har ya
kara auran wata matar sunanta ummulkhairi,
amma dai ita nabila tana gun inna har yanxu
nabila tana da tsiwa sosai ba ta fiye barin ta
kwana ba da yawa suna sonta ne saboda kyanta
da tsiwarta matan gidansu irinsu dije da ladidi
sun tsaneta ainun ganin yadda take da farin jini
dun tsiwar nan tata bata hana mutane su sota
ba.
Su kansu din tsoranta suke ji basa iya taka ta da
sun gaya mata zata mayar saboda gaba daya sun
gama nuna mata basu kaunarta ita kuma ba
tsoron kowa take ji ba a gidan tana abin da ta
gadama ne.
Shekaranta goma sha daya kacal ta gama primary
a ta sha biyun tana secondary wanan shekara ta
sha shida ga watan haihuwarta tayi candy tana
zaman jiran sakamako jarrabawar tawanda zai
bata damar shiga jami'a kamar yadda take ta
buri.
Tun tana yar mitsitsiyarta take da son karatu duk
jarabawarta ta daya take zuwa duk sanda tayi na
biyu da kuka da ciwon kai har da zazzabi take
kwana.
A da kamarsu daya da mahaifinta tahir daga
baya ta juye kamanin mahaifiyarta sak.
Tun tana da shekaru goma sha biyu a duniya tayi
saukar karatun alkur'ani mai tsarki, rayuwar
nabila tana da ban sha'awa sosai duk tsiwarta
bata da raina na gaba da ita sai in fa na gaba da
ita ne ya yadda girmanshi ya neni nuna mata san
zuciya da fin karfi to anan fa babu ragowa
tsakaninsu.
Yau satin su biyu da yin candy da yammacin
lahadi tana kwance a kan gadon inna ta sha
kwalliya da wani dan ubansun matereal ruwan
powder yayi mata kyau iya kyau, tana ta zuba
kamshin turare ta da tafeso.
Alhaji mahmud ya shugo dakin ganinta a kwance
ya bata rai wai ke me yasa naxo gidan nan a
kwance zan ganki, kamar wata mara lfy.
Ta mike zaune cikin shagwaba tace to me zanyi
abba? Yace bazaki je kina tayasu aikin girki ba
kema ki dinga koya.
Ta bata rai tace nifa baba ba sai na koya wani
girki ba tunda ba aure zanyi yanxu ba.
Inna ta harareta tace ba aure zakiyi ba to me
zakiyi?
Ki kina nufin duk makarantar da kikayi bata isa
ba sai kinyi wata.
Tace inna ni fa karatu yanzu na fara yinshiduka
shekaru goma sha shida a dinga maganar aure.
Baba mahmud yace ke nabila shiga hankalinki ki
saurara kiji abin da zan gaya miki.
Tunda take bata taba ganin ya bata ranshi a
kanta haka ba, duk lokacin da zai mata magana
zai matane cikin lallashi, lallai yau tasan maganar
ta gaske ce ta sauko daga gado ta lankwashe
kafafu a gabansa.
Yace ke nabila ada nayi niyar na barki kiyi
karatunki iya yadda kike so amma yanzu lamari
ya sauya.
Akwai kanin abokina mai suna mujahid yana
karatune a malaisiya yazo hutu nan kano zai
koma nan da sati biyu a jiya da suka zo gidan
nan ya ganki yace yanaso, abokij yayansa alhaji
mukutar shine ya nema mai auranki a guna kai
tsaye nace na bashi.
A razane ta dago kai suka hada ido tace eh?
Ya amsa yace eh nace na baiwa mujahid ke kuma
za a daura auranku nan da sati daya, wani satin
in ya zagayo insha Allahu za ayi biki ku tafi
malesiya inda zai ci gaba da karatunsa na likitanci
ke kuma xai nema miki makarantar da tadace da
ke kema ki ci gaba da naki karatun kan fannin
duk da kike so kuma kika zaba, na amsa na bashi
ke saboda dalilai uku na farko nasan na isa dake
kina mini kaunar da zakiyi mini biyaya kan duk
abinda na umurceki, nabiyu nasan tun kina
karama baki da burin da ya wuce karatu.
Sai na uku na amince da mijahid saboda yaron
arziki ne mai mutunci dan masu mutunci, kuma
mai ilimi, wanda yake da ilimi shi yasan darajar
ilimi.
Ki tashi ki shirya anjima zai zo ku gaisa. Ya mike
ya fice ya barta zaune ga badaya gwiwowinta
sunyi sanyi, ta waiwayo ga inna tace inna kinji
wani hukunci da baba ya yanke min kai tsaye.
Inna tayi murmushi irin tasu ta manya tace uhum
nabila yasan ya isa ne wanda bai isa ba ai ba
zaiyi haka ba.
Tace inna da ma haka ake bada mutum aure
batare da anji ra ayinsa ba yana so ko bai so ba?
Ba tare da an bada dama ya ga mijin da za a
bashi ba?
Nan ma murmushi tayi ta ce eh haka ne kuma
da ba haka ba ne?
Me kike nufi inna?Nabila ina nufin eh ana haka
abawa mace miji batare da ta ganshi tana son shi
ko a a ba.
Kuma ana bawa mace dama ta zabi duk mijin da
take so a aura mata musanman a zamani irin
wannan da ake kiranshi wayayen zamani wanda
aka ci gaba ma alokacinmu idan za ayi auran
yarinya ba ruwan iyaye da batun soyaya ya rinya
ba zata ga mijin auranta ba sai tayi kwana uku ko
ma bakwai a gidan mijin ta.
Haka shima mijin ba zai ga matarshi ba sai anyi
wadan nan kwanakin.
Tace inna to tunda zamani ya sauya ba a wancen
zamanin muke ba ya dace baba ya tambaye ni
ko?
Tace eh ya dace yayi hakan amma tunda baiyi ba
yana da hakkin kiyi mai biyyayya.
Wai shin ma in tambayeki nabila.
Cikin sanyin murya tace ina jinki inna.
Kinsan wacece mahaifiyarki?
Girgiza kai tayi tace bansantaba inna, ba zan
santaba tunda kince tun ina yar karama tarasu.
Ta girgiza kai cike da tausayi ta dafa kafadarta ta
ce nabila ba zai yiwu muci gaba da boye maki
abinda ya dace ki sani ba game da rayuwarki,
dan haka ba gaba da boyuwa zaiyi din ba, dakiji
a wani gun inda zakiyi muna mumunan fahimta
gara kiji daga bakina a ta kaice dai nabila
mahaifiyarki nanan a raye bata mutuba.
Afirgice ta ce inna karki razanar da zuciyata....
Ta katseta tace ba razanar dake zanyi ba nabila
gaskiya zan gaya miki duk abinda zakiji daga
bakina ki dauka gaskiya ne ba wanda zai gaya
miki fin hakan sai dai daidai da haka ko ma kasa
da shi.
Inna tas duk la barin iyayan nabila na gaskiya ta
gaya mata.
Babu abin da ta boye mata, nabila ta daskare a
gurin tana mamakin kasancewarta ba diyar
babanta mahmud wanda ya haifa a cikinsa ba kai
amma ya cika masoyi a gareta na gaskiya.
Ta mike bata ce da inna ko mai ba ta dau
hijabinta ta fice a kofar gida ta iske baba
mahmud tare da mutane suna hira ba abin da ya
dameta da mutane ta fada jikinsa tana wani irin
kuka mai firgitarwa, yariketa jikinsa na rawa yace
lafiya nabila?
Ganin ta kasa magana yasa ya jata cikin gida
dakin inna me ya samu nabila ko dai dan na
mata maganar aure ne?Inna ta ce ba haka bane
na gaya mata lbr iyayanta na asali ne.
Ya ce haba inna me yasa kikayi haka, bayan
kinsan zai jefata tunanin da zai din ga wahalar da
rayuwarta ne?
Tace yin haka ya zama wajibi a wannan sirri ne
da ba zai iya cigaba da boyuwa ba.
Jinsa daga bakinmu yafi ta jiyoshi a wani guri.
Ya zauna kan kujera har lokacin nabila na manne
jikinsa tana kuka ya share mata hawaye ya ce
nabila ki daina kuka kasancewata ba ni na haifeki
ba ba zai zamo illa ga rayuwarki ba, zakici gaba
darayuwa dai dai da yadda kike yi, in har
mahaifinki na raye zaki gansu insha Allahu. Nabila
kuka take tana karawa ta kara magana, inna bata
kuma cewa kmi ba sai aikin lallashin tunanin
nabila shine duk soyayar nan ta baba mahmud
gunta bashi ya haifeta ba. Ita kuwa mai tayiwa
mahaifiyarta da ta tafi ta barta tsawon wanan
shekaru ko sau daya bata zo ta ganta ba. Har
bayan sallar isha i kuka take tana zaune kan
sallaya, Aliyu ya shigo yace ance tana da bako a
waje tace ya tambayo sunansa ya ce ance mujhid
ne. Gabanta na faduwa ta mike ta kara gyara
jikinta ta daura kallabi da a tamfa super tayi kyau
iyaka, ta yafa karamin mayafinta iya kafada ta
sako takalmi mai tsini tafito zure tana takun kwas
kwas kai kace wata kasaitaciyar liyafa zata. Wata
yar ubansun mota ta hango irin new modern din
jeep din nan lafiyaya tana zuba kyalli tundaga
nesa take juyo wani tautausan kamshi mai ratsa
zuciya na tashi. Ta isa gun jikinta ba kwari ta
tsaya daidai saitin da mai motar zai hangota,
mujahid na kwance a mazaunin direba ya
kwantar da kujera music ne mai taushi ke tashi,
yana sanye ne da baki da farin kananan kaya
duk duk yanda naso kwatanta mujahid a kyau da
komi abin ba zai taba yuwuwa ba. Ko wanda bai
san duniya da abinda ta kunsa ba yasan mujahid
ya hadu dogo ne sosai mai jiki madaidaici
ma'ana shi ba mai kiba ba kuma ba shi da rama.
Inda kyanshi ya tattara shine a fuskarsa, ya
mallaki fuskar da duk namijin da ya mallaki irinta
ya isa yayi yanga kowane mutum akwai inda ya
cika akwai ya tauye, a iya gane gane nabila na
maza a kanobata taba ganin namijin da ya kama
kafar mujahid a kyau ba.Komi nashi yayi mata
nantake taji nunfashinta na neman daukewa
lokacin da ya warware mata kwala kwalan
idanunsa yana mata wani irin kallo wanda bata
taba gani a gun wani da namiji ba.
Itama shi take kallo har ta gaza ta mai da
idanunta kasa ta cikin sanyin murya tace sannu
da zuwa.
Wato tunda tafito tasan yau tayi arba da
kyakyawan namiji amma ba ta gama tabbatar da
haduwarsa ba sai da ya budi baki ya amsa mata
sallama da sannu da zuwan da ta yi mishi.
Ya buda mata mota kusa dashi yace ta zagayo ta
zauna.
Tashiga tana sa kanta a motar wani sansanyan
kamshi da sanyin Ac suka ratsata tayi ajiyar
zuciya har saida mujahid ya kalleta.
Ta gaida shi ya amsa bata yi mamaki ba da taji
hausar sa bata fita sosai yafi kama da larabawa.
Yace nabila ko?
Tayi karfin halin amsawa eh haka sunana yake.
Kiran sunan ta da yayi ya shigo da sabuwar
faduwar gaba da sanyi a jikinta ta ce,
subhanallahi wane irin mutum ne yau na hadu
dashi kuma.
Yace nabila menene burinki na rayuwa a yanzu?
Ba tambayar da ya dace ya fara yi mata kenan
ba a ganinta, kumababu wani namiji da zai yi
mata irin wannan tambayar bata gwasileshi ba
kai a ganinta shisshige ne yazo mata da shi
amma ina mujahid ya wuce haka a gunta.
Shi kadai ne da bakinta ya fara mutuwa a
gabansa, ta kasa katabus kanta na kasa kamar ba
ita ba.
Da kyar ta tattaro natsuwarta tace bani da burin
da ya wuce karatu mai zurfi.
Murmushi yayi wanda yayi masifar kara mai
kyau, ya lumshe ido yace haka babanki ya fada
mana a jiya lokacin da na shaida mai ina sonki.
A lokacin mu munganki ke baki ganmuba muna
tsaye mu da babanki da abokin yaya Alhaji
mukutar wanda nake sauka a gidanshi idan nazo
hutu nan kano.
To sai dai bai fada mini mai kike son karantawa
ba, ina son ji daga bakinki.
Tace to ina son zama lauya ina son zama likita ina
son zama malamar makaranta masana koyarwa.
Yace na yaba ma zaben ki duka din da kika zaba
zasu dace dake duk da haka nafi maki sha'awar
likita.
Tayi murmushi ta ce ko?
Yace yes.
Tace dalili fa?
Yace sai nan gaba zakiji.
Ta ce ba damuwa.
Yace nabila.
Sunana mahmad nuraddin ana kirana da mujahid
saboda suna daya da mahaifina, mu larabawar
kasar egypt ne, ina da iyaye a nan kano shine
abinda yake kawoni kano lokaci lokaci yin hutu.
Shekaruna na haihuwa duka ashirin da biyar
bansan da lilin da yasa iyayena keso inyi aure ba.
Ko da yake suna burin mu cika musu gida da
jikoki ne inaga shi yasa suka damu da aure na
inaso ki bani hadinkai muyi aure ko mai zan maki
iyayena ma zasuyi maki, amma karki damu da
soyaya ta dan gaskiya na ce ina sonki ne zan
aureki dan in huta da fadan da iyayena ke mini
kan maganar aure ba wai dan lokacin auren yayi
gareni ba.
Bani so su bani matar da bani ra ayinta shi yasa
nace ina sonki.
Gaba daya sanyin Ac din dake motar sai ya
zamewa nabila hucin wuta sabo da gumin da ya
jikata.
Wane irin al'amari ne kuma wannan mai kama
da almara, cikin sarkewar murya tace kana nufin
ba sona kake da gaske baza ka aureni dan gudun
kar iyayenka su baka macen da baka ra'ayi?
Ya kara kashe murya yace no karki damu kanki
da batun soyaya aguna ina da wani irin hali game
da mu'amala da mata sai nan gaba zaki fahinci
hakan ke dai in kin amince da aure na shikenan.
Ta maida kanta kasa tana tunani saboda
al'amarin da yazo rayuwarta, ya duba agogo yace
ni zan koma dan ina so inyi asubanci tafiya
maiduguri ina ga wani abokina.
Ya dora mata rafar dubu dai dai sababi yace ki
sha lemo na shiga wani super market da niyar
inyi maki tsaraba bansan me kike so ba.
Muryarta na rawa tace dan Allah ka bar kudinnan
sunmin yawa.
Dan Allah karki damu dauka ai ba rokana kikayi
ba nine nayi niyya yaron gidan ma zan iya yimai
kyautar da tafi haka ballanta na yarinyar da zan
aura.Lokacin da nabila ta shugo gida tunaninta ta
gayawa innarta cin fuskar da mujahid yayi mata,
wai kamarta yau da take ji da kanta mujahid dan
yana ganin ya isa a soshi ya budi baki yace kar ta
damu da neman soyayarsa ya nemi auranta ne
dan iyayanshi sun damu suna son yayi aure bai
son a hada shi da wanda bai ra'ayi.
Sai kuma tayi tunanin inna fa mahaifiya ce ga
mahmud bawan Allah da ya riketa tsakani da
Allah ya ke kaunarta dan Allah har bata iya sanin
ba shi ne ya haifeta ba saboda tsantsar kauna da
soyayar da yake mata, sai a wanan rana da hali
yayi aka fada mata.
In banda taji daga majiya mai tushe bakin da ba
zai yi mata karya ba da ba zata taba yarda cewa
ba mahmud ya haifeta, kaunar da yake nuna
mata ko yayan cikinsa ba a ga yana musu haka
ba.
Wanan tunani ya sa jikin nabila ya dada sanyi, ta
ajiyewa inna kudinin da mujahid ya bata ta koma
gefe ta yi tagumi.
Inna tace yaya na ganki cikin damuwa baki sonshi
ne?
Nanda nan ta saki fuska tace ina sonshi mana
inna nidai ina tunanin rabuwa dake ne zuwa
rayuwar da baka saba da ita ba, a gidan da baka
saba dashi ba cikin mutanen da baka saba dasu
ba.
Inna tayi murmushi tace nabila tun kina da
watanni goma kike hannuna babu wani abu naki
da zai buya gareni ko motsi kikayi nasan abinda
kike nufi idan har wannan yaro bai maki ba.Ko
wane motsi kikayi nasan abinda kike nufi idan
har wannan yaron bai maki ba kina da damar ki
ce baki so ba zan bari ayi maki auran dole ba
duniya na iya zagin mu a ce dan ba iyayenki ya
sa muka tilastaki yin abinda ba ki so.
Nabila tace dan Allah inna daina wannan
maganar karki sani kuka, wannan mujahid din da
baba ya ban namiji ne wanda babu macen da ta
isa tace bata son shi.
Duk yadda ake son namiji ya wuce nan zancen
ince bana sonshi ma bai taso ba ni ban ni ban
taba kallon wani namiji da sunan soyayya ba.
Saboda ba soyayar ce a gaba na ba, ban san
yadda ake soyaya ba tun da ban taba kamuwa da
son wani ba amma wallahi inna ina hada ido da
mujahid na ji gaba daya yanayi na ya sauya na
tsinci kaina a tunanin da ban taba shiga ba.
Ko da ban san meye so ba na san na kamu da
son mujahid ta farat daya.
To wlh inna ba mujahid ba ko wane irin mutum
baba ya kawo ya ce na aura zan aureshi na gode
wa Allah da ya nu feki da bayyana mini gaskiya
lamari a kan rayuwata, hakan ba zai sauya
matsayin baba a guna ba illa ya kara daukaka
darajarshi a zuciyata ta yadda zan sadaukar da
zuciyata inyi mai biyya bakin rai bakin fama.
Saboda haka dan Allah inna ko da wasa kada
kinunawa baba bana son mujahid don ina sonshi
din.
Ko da bai kai matsayin da za a soshi ba zai ci
darajar baba in soshi in aure shi in zauna dashi,
balantana kuma mutum ne shi din mai daraja
namba daya cikin maza.
Inna ta ce to Alhamdulillahi ina jin dadin yadda
kike da wayo da hankali nabila, Allah ya yi miki
albarka amma me ya sa kika karbar mai kudi
masu yawa haka?
Tace shi ya bani inna na ce ya barshi ya ce sai na
amsa.
Alwala tayi shafa'i da wutiri ta hau katifarta ta
rufe idonta kamar tayi baci, tayi haka ne dan
bata son hirarsu da inna yau tunani ne kawai a
gabanta ta fado wata sabuwar rayuwa da bata
taba shiga cikinta ba.
Lallai mujahid ya isa namiji duniya da za a soshi
illar daya ya fito ya fada mata baya soyaya a
gabansa zai aureta ne kawai dan ta zame mai
garkuwa daga auran dolen da iyayensa zasu iya
mai in bai kawo matar aure ba.
Shin ina makomar rayuwarta a gaba lokacin da
mujahid zai gaji da ita tunda baso na hakika yake
mata ba.
Tana jin inna na fadin ho yar nema yau ba za a
karanta mini lattafi ba a kai barci?ba ta ko motsa
ba tana ji ta gama tata hidimar ita ma ta kwanta.
Tam bayoyi ne barkatai ta kema zuciyarta babu
amsa, da gari ya waye haka ta tashi sukuku jiki
ba kwari, gashi ba makaranta balantana aje a
shiga kawaye dauke mata kewa da rage damuwa.
Inna na kallonta da yake bata son matsa mata ba
tace da ita ko mai ba wuraren karfe goman safe
baba mahmud ya iso gidan bayan sun gama
gaisawa da ragowar matan ya shigo dakin inna,
nabila ta gaidashi zata tashi ya janyo hannunta
yace haba yar lele na ya naga duk kinyi sanyi
yau? Ko baki son mujahid din ne?nikuwa gani
nake kamar zai dace da rayuwarki zai kula min
dake.
Tace baba ina sonshi ba abin da yake damuna.
Yace alhadulillah nasan dama ba zaki bani kunya
ba nabila ta sai a fara shirin rabuwa da inna dan
in an jima zasu kawo kudin aure da kayan lefe.
Inna ta ce da wurwuri haka?
Yace eh ai na gaya muku ba ma zauni bane kasar
zasu bari nan da sati biyu.
Gaban nabila na faduwa ta tashi ta shiga daki ta
kwanta tana jin yadda baban ta yake bayyanawa
inna kirkin mujahid da kyakyawan dabi'unsa.
Bayan tafiyar baban nata ta shaidawa inna zata
gidan miniyarta fauziya da sukayi candy tare bata
da aminiyar da ta wuce fauziya gidansu na
karshen layinsu inna tace adawo lafiya amarsu ta
ango.
Ta zunburi baki ta fice.
Fauziya na ganinta tace yanzu fa nake shirin
zuwa gidanku....






Zaharaddeen Shomar

Whatsapp 08168575100






Launin Fata 2-05
Posted by ANaM Dorayi on 07:06 PM, 22-Oct-15
Under: Launin Fata
Nabila ta wuce suka gaisa da ummansu fauziya
suka shige dakin su fauzeeya tazu ba mata ido
tace ke yaya na ganki haka duk idonki yayi ja lfy?
Nabila tace fauzeeya ina fa lafiya yau saura
kwana shida a daura mini aure.
Fuzeeya tace da B.U.K ko A.B.U zaria ko?in ba
dasu za a daura maki aure ki tafi can ba wane
irin aure ne haka bashiri kamar auran baby
wasan yara.
Tace kinsan Allah aure za a daura mini fuzeeya
baba ne ya badani kai tsaye ni kuma na amince.
Fauzeeya ta fido ido tace dan Allah in gaske kike
bani lbr yadda akayi in zolaya ta kike ki bari
kawai muyi wata hirar.
Nabila ta bata rai tace kin taba ganin nayi maki
irin wanan wasan?
Ta zaiyana mata duk abubuwan da suka faru.
Fauzeeya ta kasa magana dan mamaki sai da
nabila tace fauzeeya bansan yadda soyayya take
ba amma ko shakka babu nasan na kamu da
son mujahid ta farat daya.
Sai dai abin takaici mujahid ba sona yake ba,
kuma da ganin idontasa kinga tantirin wayayen
mutum budewar idonsa sunyi yawa ina gudun
shiga wata rayuwa da ban saba shiga ba.
Fauzeeya tace tabdijan ai wlh tun wuri ki fitar da
batun damuwa a zuciyarki ki natsu kisan yadda
zaki cunkusa mashi soyayyarki a cikin zuciyarsa
ya soki.Tayaya zanyi haka fauzeeya?
Na gaya maki yace yana sonane ba dan wai
yana sona din ba sai dan ya kubutar da kansa
daga auran dolen da iyayensa zasu iya yi masa.
Fauziya tace baki da wayo nabila shi mujahid
yana gudun iyayensa suyi masa auren dole,
kenan yana nufin kema dole yayi ma kansa zai
aure ki.idan wacen yarinyar da iyayensa zasu
iya bashi dole ce ke din wayasa yace yana sonki,
ai idan hakane da yayiwa kansa auran dole gara
iyayensa su mai.
Tunda har ya kai idanunsa kanki in dai zuciyarsa
ce ta kawata masa wani abu naki har yaji zai iya
zaman aure dake.
Zai iya yiwa soyayyar bata gama ratsashi ba
kamar yadda ya gaya miki, dama wata soyayar
tana shiga zuciyar mutum ne a hankali yayin da
wata zatashiga da karfinta. to shi nashi salon
soyayar kenan na tabbatar idan babu rami babu
abinda zai kawo magaar rami, idan babu so ko
kaka babu abin da zai kawo maganar aure.
Baya sonki zai sha'awar zama dake, zama kuma
na aure, zaman da ba asan iya kacinsa ba sai
Allah.
Wata kila shi irin mazannan ne da basu son
raini, yana ganin ke karamar yarinya ce idan ya
fito maki da soyaya fili kya iya rainashi.
Saboda haka ki kwantar da hankalinki nasan
tunda kika ce mujahid na da kyau ya hadu lallai
ya hadun saboda ban taba jin kince wane ya
hadun ba.Mujahid zai soki in dai har kincika
mace zaki iya samowa kanki soyaya a zuciyarsa.
Ko waye mujahid ko wane irin kyau gareshi wlh
nasan ba zai fi karfinki ba, ba zaifiki kyau ba sai
dai yafiki gogewar fata na jin dadi da yanayin
gurin da yake rayuwa da ilimi da wayewa da
budewar ido Nabila tayi gauran numfashi tace
fauzeeya dan bakiga mujahid din bane shiyasa
kikecewa ba zai fini kyau ba ke na gaya maki
tunda nake fa ni ban taba ganin kyakyawan
namiji irinsa ba duk yanda naso kwatanta shi ba
zai kwatantu ba.
Ni dai nasan na gamu da gamo natun da na
dora idona a kan mujahid ban kara samun
kwanciyar hankali da natsuwa ba gashi abin
mamaki bai ji nauyin ya fito ya nuna min ba
matsuwa yayi da sona ba.Fauzeeya tace na gaya
maki kada ki bari wanan ya dameki namiji ne
fa, tunda ya amince zai aureki ai an gama
magana kuma sai ya furta da kanshi tunda ba
wanine yayi masa tallarki ba ba wani ya tursasa
shi ba.
Duk abubuwan da fauzeeya ke so nabila ta gane
jinta kawai take bata gamsu ba ta dawo gida
cikin sanyin jiki lokaci guda kowa a gidan ta
sauya duk wanan surutun da tsiwar sukai ta
koma ta koma zama shuru har bata so ayi mata
magana tafi son tayi zamanta ita daya tana
tunanin mujahid.
Tunani mai dadi kuma mara dadi idan ta tuno
kyanshi da haduwarshi taji dadi in ta tuno yace
ba dan yana sonta zai aureta ba sai dan wani
dalili gaba daya sai taji hankalinta ya kuma tashi
tana tunanin makomarta a irin soyayar da ta
damki zuciyarta kai tsaye.
baba mahmud ya shaidawa duk mutanen
gidansu cewa nabila tasamu mijin aure za ayi
aure ne nan da sati 2 kuma anjima zai zo ya
gaisa dasu.
Abinka da gidan yawa nan da nan aka shiga
tsegumin wane irin aure ne haka kamar auren
yartsana yau she mijin samu babu wanda
yasani har aka yanke lokacin aure.
Ladidi tace duk kinibibin mahmud ne da ya dau
son duniya ya daura a kan wanan mara kunyar
da bata ganin kan kowa da gashi, shi zai nemo
miji ya kawo mata.
Dije ta ja tsaki tace ai mu rabi ta tafi ta barmu
da irin jaraba, yarinya tasa ba mai kallon yayan
mu, duk wanda zai magana sai dai yayi a kanta.
Ta dunka yanga tana yauki kamar kilaki.
Lubabatu tace uhum an gama feleken karatu ne
da ba cewa sai anyi digirin da girgir ba?
Mu yayan mu ba yaya bane sai ita?
Dije tace wai ke haka aka bar mahmud, tun
uwarta tana gidan ta gama dashi da ta tashi
tafiya ta hada jinin sa da na yarta ta yadda ta
fidda son kowa a zuciyarsa sai na yarta yake
mata son da bayawa ya yansa da ya haifa kila
har uwarsa da ta kawoshi duniya.
Lubabatu tafi kowa jin haushi al'amarin shi yasa
ta kasa zama tunda aka kawo maganar auran
nabila.Tun safiya ake ta ya madidin maganar
nan har yamma lokacin da baba mahmud yazo
yasa yara keta share gidan ana gyarawa, ta kai
ci ya kara isar matan gidan sai dai babu yadda
suka iya babu wanda ya isa ya kawo wa
mahmud raini, basu isa yace za ayi suce a a ba.
Kar fe biyar dai dai na yamma Mujahid da
abokinsa amir suka iso gidan dan gaida
surukansu a cikin motar da yazo jiya suka zo,
tuni yara sukayi dafifi suna kallon motar da
masu motar wasu suka ruga suka gayawa
iyayansu ai mijin nabila bature ne ba bahaushe
ba, nanfa suka shiga rarraba idanu manyan
kaya su mujahid suka sa tun suna kofar gida
kamshin turaransu ya bay baye gidan, baba
mahmud ya yo masu jagora suka shigo cikin
takun isa da kasaita, gaba daya matan gidan na
tsakar gidan, da yayan su nabila ce kawai
kwance a dakin tana shakar kamshin mujahid ta
lumshe ido wata zazzafar soyaya ta kara
kwarara a cikin zuciyarta tamike ta leko ta
window.Sai a yau ta kara tantance waye mujahid
da ta ganshi a cikin haske kai subhanallahi
wannan mutum da kyau yake.
Dije da ladidi da lubabatu sai share zufa kawai
suke dan tsananin bakin ciki ko gaisuwar da su
mujahid ke musu basu iya amsawa ba, iyakar
burgewa kam duk hassadar mutum

Please Login or Register in order to submit comment