Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

koma
gidanmu ko dan ka huta da wulakancin Abba. Ya
toshe mata baki a sanyaye ya ce ki daina
damuwa na gaya miki lamarin abba bai taba
damuna ba na san komi lokaci gareshi, kada in
kara jin kin yi batun rabuwar mu a kan lamarin
Abba. Ta sake shi ta koma ta kwanta lamo ya
wuce cikin dakinsa ya zauna yayi tagumi bai son
Rabi ta dameshi da tambayoyin da bai son amsar
su ba. Baya son gaya mata gaskiyar lamarin ne
saboda daga hankalinta za ta yi duk abinda zai
daga mata hakali kuwa baya sonshi. Haka ya yini
sukuku ba kuzari abinci ma kasa ci ya yi da
yamma Rabi'a ta gaji ta saka mai kuka ta ce wlh
da abin da Abba ya gaya ma wanda ya dameka
ka boye mini idan ka boye mini dan in damu
damuwa ba zata bar zuciyata ba tunda kana tare
da damuwa garama ka fito fili ka gaya mini mu
san abin yi. Babu mafita na yin haka dan haka ya
gaya mata yadda suka yi da Abba. Ta dafe kirji ta
ce innalillahi wa inna ilaihi raji'un garin yaya ka
bashi takardun gidan? Ya ce to Rabi'a idan ban
bashi ba ya ya zanyi? Ko kinga ina da karfin da
zanja da Abba ne? Ta ce idan Abba ya fi karfinka
ai baifi karfin hukuma ba ko? Ya ce haba Rabi
Allah ya sauwake in kai Abba ga hukuma idan
nayi haka ai na bar abin fadi har ga jikokin mu,
akan gida da mota in kai wanda ya haifi matata
kara? Ta lankwasas da kai ta ce kana da hujjoji
masu karfi da hukuma zata maido ma gidan nan
da motarka hannunka. Ya ce ki bar wannan
maganar Rabi'a abu ne da ba zai yiwu ba kina
darajar da zanwa Abba komi saboda ke. Ta ce to
yanzu ina zamu zauna? Ya ce ba komi kafin wata
2 da ya dibar mana Allah zai bamu inda zamu
zauna din. Ta mike tsaye ta shiga kai komo a
dakin zuciyarta ta gama baci in ranta yayi dubu
ya baci sai yau ta tabbatar da kiyayyar da
Abbansu ke wa auranta da tahir ba kiyayyar wasa
ba ce. Duk abinda zai yi yaga bayansu shi yake
nema, ta yaya za ai bashi ya sai gida da mota ba
ba da kudinsa aka saya ba ya kwace? Kwana
tahir ya yi a ranar yana lallashinta tana kukan
bakin ciki.Yayin da ita kuma ummi ta fada cikin
bala'in Abba domin yana shiga gidan ya hauta da
masifa ya ce dama ni na san duk munafuncin
yana gunki kika dau gida kika ba ma wannan
matsiyacin yaron to na kwace kuma wlh idan na
kara jin kin basu wani a bakin auranki. Ummi ta
saki baki tana kallon Abba tana mamakin yadda
ya ji wannan sirrin takaici yasa ta rasa abinda za
ta yi ma wace irin rigima ce wannan. Kwana 2 da
yin haka Rabi'a tana cikin matsananciyar damuwa
ko abinci bata iya ci sosai har tahir ya fara gajiya
da lalalshi ya shiga yi mata fada ya ce yaya kike
so in yi da raina ne? Menene dan an karbi gida
da mota da can nasan da su ne? Ran da yake
jikinmu wata rana rasa shi zamu yi ballantana
abin duniya Allah shi ya san yadda zai yi da mu.
Ta kwanta lamo tana hawaye ya yi ficewarsa ya
barta nan' zuciyarta ta dinga tashi ta amayar da
dan shayin da ta sha nan da nan sai zazzabi. Tun
tahir bai kulata ba har zuciyasa ta kasa juriyi ya
daukota suka je asibiti a can ne likita ya tabbatar
musu tana da shigar ciki wata daya amma ta
rage damuwa cikin baida kwari zai iya faduwa.
Labarin samuwar wannan ciki ya tafi da
damuwar dake zuciyar tahir farin ciki ya kama shi
zai yi da dama shi haka yake bai cika sa abin
duniya a ranshi ya dameshi, duk lokacin da wata
damuwa ta yi mai yawa sai ya shiga adu'a. Ya ci
gaba da tattalinta kamar kwai bai da magana sai
ta cikin nata, ala dole ta rage damuwa, ya
gargadeta a kan kada ta gayawa kowa abin da
Abba yayi musu baya son wani ya ce zai baiwa
Abba hakuri shi ma zai yi kokari samun nasa. Kar
ummi tazo gidan Rabi'a Abba ya hanata zuwa ko
ina sai ita Rabi'a ta saci jiki ta zo ta gaya mata
yadda Abba ya yi musu kukan da Rabin ke yi ya
ba ummi tausayi da yawa itama sai da ta yi
hawaye ta ce Ba komi rabi'a ki ci gaba da zama
lafiya da mijinki da yi mai biyayya Allah yana tare
da masu hakuri. Allah ya baki miji nutsatse mai
mutunci in shi kadai ke mutunta Abba da ni duk
wulakancin da abba ke mai bai dubawa.Tunda
Abba ya wulakantashi a kan dukiya insha Allahu
sai ya ci moriyar dukiyarsa wata rana Abbba ya
ce a bakin aure na in na sake baku wani gidan,
dana siya muku wani. Rabi'a ta firgita sosai da jin
wannan maganar har ta dawo gida kuka take yi.
Hajiya yaya kadai tahir ya gayawa abinda
surukinsa ya yi masa ya ce ya samu madaidaicin
gida a nan kasan layinsu zai kama haya. Ta rike
baki ta ce haba dai haya har me kake samu a
wata da zaka dinga iya biyan kudin haya ga
dawainiyar matarka wadda ko yaushe kake
karewa kan hidimarta, ka dauko yar masu kudi
da bata cin abinci irin namu sai mai tsada, bata
da sutura irin tamu sai mai tsada ubanta bai
kaunarka. Duk zuri'ar gidan nan wanda ya tashi
aure daidai dashi yake nemowa gashi kowa yana
zaune lafiya banda kai kaima da dai dai kai ka
dauko da baka ga wanan takaicin ba.Saboda haka
zancan kama haya bai taso ba ga dakin
mahaifinka ciki da falo har da bandaki a ciki yafi
kowanne sashe kyau a gidan nan ka kara gyarawa
ka zauna, in kuma matarka tafi karfin zama da
mu ne shi kenan. Ana wata ga wata, maganar
hajiya yaya tafi karfin musu a gun tahir ita ce ta
haifi mahaifinsa, lokacin da mahaifinsa zai rasu
wasiyya 2 ya bar masa. Na farko ya ce ya guji
duniya da kwadayin abinda ke cikinta da son
zuciya ya ji tsoron Allah duk abinda zai yi ya tuna
zai mutu ya hadu da Allah. Na 2 shi ne lallai duk
abinda zai yi ya yi shawara da hajiya yaya in ya
saba mata shi ya sabawa. Gumi ya dinga
tsayayowa taìr yana mumfashi da kyar bai kaunar
kawo matarsa gidan nan saboda shi ma ba
kaunarsa mutan gidan ke yi ba suna cewa ya fiye
sanabe da iyayi ga jin kan to ina ga matarsa, duk
abin da zai takura rayuwar matarsa baya so.
Haka ya amsawa hajiya yaya taso ya nufo gida ya
saidawa Rabi'a yadda sukayi ta ce c komi ai kowa
da halin sa zai zauna, da muje gidan haya ai gara
can din.
A ransa ya ce tabdijan baki san matsalar dake
kwance a gidan mu ba ne. A kai akai Abba ya
dinga kiran tahir a waya yana shaida mai
wa'adinsu ya kusa ciki ya ce ina sane Abba
zamu tashi. Abba ya zubo ido yaga Rabi'a ta
dawo gida ya ji shiru, ya gaji yaje gidan da
kansa lokacin tahir baya nan yana makaranta,
tunda ta ganshi ta san ba alheri ne ya kawo shi
ba, bata amrheshi da walwala ba ya shiga har
falonta ya zauna bayan sun gaisa ya ce dubeki
dubi yadda kika koma kin yi fari fat kamar
aljana sai dogon hanci kamar talakan bature kin
lalatar da kanki a kan wannan matsiyacin yaron
da bai da komi ki kwashe kayanki ki koma gida.
Ta ce nifa Abba ina son mijina ko ba shi da ko
mi ina sonshi haka kuma zanci gaba da zama da
shi a haka? Ya ja tsaki ya ce sai ki yi ta zama
wahala ce bata isheki ba na tabbatar kwadayi
ne ya kai tahir ga auranki yanzu da na toshe
mai hanyar da zai samu abin da yake samu ba
abinda zai saka miki da shi sai saki. Ta yi tsit ya
karaci kame kamen fadansa marar dalili ya tashi
ya tafi yana mamakin halin Rabi'a.Bata gayawa
tahir zuwan Abba ba dan abin kunya ne a
gareta a ce babu wanda ya zama fitina ga
auranta sai mahaifinta. Bayan kwana biyu suka
tattara kayansu suka koma gidansu tahir, dakin
ya gyarashi sosai ya fashe simintin kasa ya yi
mai tayar silif ma mai tsada ya sa ya sa har da
bandakin ya sa AC da duk wani abin kawata
daki, sauran kayansu ya sa a dakinshi na zaure
da ya tashi ya rufe, falon da dakin baæin nasu
ya yi kyau sosai amma duk da haka da ummi ta
saci jiki ta zo sai tausayinsu ya kamata ta hango
ita daular da ta ke ciki a gidansu kamar Aljannar
duniya kullum dada kayatar da shi ake amma ji
muhallin da yarta ke ciki wani tsukakken falo da
daki daya kawai da toilet ko kicin babu. Bata
yarda Rabi'a ta gane damuwar ta ba dan kar ta
karyar mata da zuciya amma tana fitowa kuka
ta kama yi a mota musamman da ta tuna da
kallon banzan da mutanan gidan ke yi mata
suna yada kananan maganganu a tsakar gida.
Bata ga alamar za a zauna lafiya a wannan gida
ba.
Tun a washegarin ranar da suka tare da safe
Rabi'a ta shiga dakin hajiya yaya dan gaida ita
hajiya ta ce Rabi'a zaman duniya iyawa ne
matan aure sun kai goma sha 2 a cikin gidan
nan kce ta sha 3 dole sai kin iya da kanki duk
wanda ya ce zo mu zauna kamar ya ce zo mu
saba ne, duk kusancin harshe da hakori wata
rana sabawa suke ballantana mutum da
mutum. Da safe da rana kowa girkinsa yake
amma da daddare tare ake yin tuwo gaba daya
gidan, zaki shiga cikin wannan tsarin kuma. Rabi
ta dawo daki ta zuba tagumi, bakin cikin
Abbansu ya kara dawo ma a sabo fil haka kawai
suna zansu lfy ya kwace musu gidansu ya jefosu
a wahala da bacin rai. Ba wai dan zai amfana da
gidan ba sai dan ya kunsa musu bakin ciki da
damuwa, to tabbas sai ta bashi kunya babu
wata wahala da zata sa ta koma gidansu ta rabu
da mijinta dan yana sonta yana tattalin farin
cikinta itama shi kadai take so. Tunanin da ya
dauke hankalinta shi ya ja har tahir ya shigo
bata ji ba sai ji tayi ya rumgumota ta baya ya ce
wannan tagumi fa na meye? Ta yi ajiyar zuciya
ta ce ba komai.Yace haba mutum ya zuba
tagumi irin wannan kuma ya ce ba komi
matsalolin gidan nan sun fara damun ki ko? Ta
ce a a. Ya ce ki yi hakuri in sha Allahu ba zamu
dade a gidan nan ba ni dai ina godiya da kaunar
da kike mini ba dan na isa ki soni ba ina godiya
da juriyar da kike da duk wani hali da ke
riskarki a dalikin aure na. Ta mike tana fadin
godiyar ta isa haka. Ya damko ha6unta ya ce
me kike söci in dafa miki? Ta ce um um ni zan
dafa kada ka manta gidan nan ba irin can ba ne
akwai idanuwan mutune sosai a kanmu dole mu
hakura da rayuwar da muka saba. Kamar amsa
ga abinda take fada kawai sai ganin yarinya
suka yi budurwa katuwa ta daga musu labule
babu ko sallama ballantana neman izinin
shigowa, a kalla zata kai shekara goma sha 7
ransa ya yi mugun baci ya saki Rabi'a ya buga
mata tsawa ya ce ke lfy za ki shigowa mutane
daki babu sallama? Ta turbune fuska ta ce
hajiya ce ta ce in kirawoka. Ya ja tsaki ya ce je ki
ce ina zuwa.
Rabi'a ta shige daki ta kwanta tana tambayar
kanta irin rayuwar da zasu yi a gidan nan kenan.
Tahir ya shiga dakin hajiya yaya ransa a bace ya
zauna ya gaida ita, ta bata rai ta ce dan na aika
kiranka shi ne kake mata bambamin masifa, kai
ko kunya baka ji da safiyar nan ka kulle da
mace a daki, wa kaga yana wanna tabarar a
gidan nan? Kunya tasa ya sunkuyar da kansa ya
rasa abinda zai ce, tabdijan komi sa ido ne
kenan a gidan nan, ta tura mai kwanan sha cike
da kunun tsamiya da kosai mai zafi ta ce gashi
nan ku je ku karya dan naga alama matar taka
dan kosa ce ga alama girkinma kai ke yi mata.
Ya dauko ya dawo daki Rabi'a ke kokarin janshi
da hira shi kuwa damuwa ta hanashi sakat.
laulayi ya sa Rabi'a a gaba ga takaicin da take
kunsa a zaman gidansu tahir, da takura tana
fama da barci da kasala ga yawan aikin matan
gidan sun debi ido sun sa mata komi tayi a
kyara da hantara take. Lokaci guda ta rame tayi
wani irin hankalin tahir duk ya tashi wani lokacin
in ya zauna a gabanta har kuka yake mata
abinda ita kuma bata so.
Yau satinsu hudu daidai da dawowa gidan, taliya
ta dafa jalup da rana ta ji attaruhu da albasa
saboda bakinta ba dadi tana cikin ci yaron Dje
salhu ya shigo dakin yana gatsine gatsine na
rashin kunya ya ce Rabi wai ki zo in ji
ummanmu. Ta ce to je ka ce ina zuwa. Ba ta je
c sai da ta gama cin abincinta tana shiga dakin
jije ta zabga mata harara ta ce aikin banza da
wofi dan kina cin taliya zaki ma salihu tsawa kice
ya fita daga dakinki, taliyar banza da wofi. Ta
rike baki tana kallon salihu wanda ya yi kicin
kicin da fuska tana harararta yara kanana suna
mata wulakanci da rashin kunya kawai dan
iyayansu sun daure musu gindi. Ta ce salihu
yaushe na maka tsawa? Dje ta ce ya miki karya
marar kunya kawai. Kishiyar ta ladidi tana zaune
a gefe ta tabe baki ta ce zaki daina ganin laifinta
tahir ne da yake nuna mata kamar tafi kowa a
gidan nan dan yana auran yar masu kudi sai
kace baki ga wani irin kallo da yakewa mutane,
baka isa tahir ya gaida kai ba kamar ba mu ne
muka ci kashinsa da fitsarinsa ba.
Dije ta ce to ai aikin banza yake surukin nasa ba
wulakantashi yake ba, ina ce ba shi ne ya
korosu ba suka dawo tahir din, baya da kuma
yake yafi karfin ya zauna da mu a gidan nan.
Wannan surukin nasa har wani abin takama ne
a gunsa? Suka yi tsaki. Dije ta ce ni tashi wanke
wanke na ne sumaýa bata yi ba ta tafi unguwa
ki yi mini kuma kin san ke ce zaki yi tankadan
tuwo amma kika nade a daki ke ga yar gata.
Ladidi ta ce anya kya sa ta wanke wanke kuwa?
Shekaran jiya fa dan kawai na sata iza wuta
tahir ya shigo ya sameta a gaban murhu tana
fifita makirar yarinyar nan tana gani mijinta sai
ta fara matsar ido wai ita hayaki ya dameta. Da
yake ba shi da kunya sai ya zo gabanta ya tsaya
ina hangoshi daga daki ya amsì maficin ya fifita
wutar ya janye ta suka yi daki har da turo kofa
a ranar sai ni nayi towon gaba daya bai bari ta
tayani ba. Da takaici ya isheni na kasa hakuri da
safe na yi mai magana na nuna mai bai dace ya
dinga nuna wa matarsa tafi kowa a gidan nan
ba yadda ake ya haka mu ma muke yaya daukar
cikiou aka yi yadda aka dau nata haihuwarmu
akai yadda aka haifeta muma ba daga sama
muka fadoba ,ba daga bola aka tsintomu ba
kowa fa yana son hutun nan.
Da budar ckin marar kunya sai ya ce gaskiya sai
dai mu yi hakuri matarshi yarinya ce bata saba
da wahala ba zata iya aikace aikacen gidan nan
ba sa6an juna 2 gareta tana bukatar hutu. Dije
ta tare ta wai sai kikace mishi me? Ko kuwa ido
kika sa mai ya ke rashin kunya. Ta ce to mai
zance mai dije fadan da yafi karfinka wasa kake
mai da shi ni dai na ce to ba zan kara sa matar
shi aiki ba kada wata rana wani abu ya sameta
a ce nice' dan naga kamar kwai haka yake ji da
ita. Dije ta ce tabdijan ashe lallai za a yi ta wlh
bai yiwuwa dan mu ma c cyi cne haka iyayanmu
ba bayi ba ne. Ga hadiza nan shekarar ta sha 5
kacal aka kawo ta gidan nan amma tas take
zama tayi tuwon gidan nan mijinta bai taba
cewa tana da ciki ko bata sa ba whala ba kuma
itama yar gta ce haka hansai sai ita yar gwal in
iar tana gidan nan sai tayi abin da kowa ke yi.
Rabi'a ta mike ta fita jiri na dibarta sama sama
ga wani azababban bacci tana ji ta shiga wanke
wanke, ga manyan tukwane bakikkirin Dije ta ce
a wanke mata su tas saboda rashin sabo kusan
awa 2 tayi tana wanke waken tana nishi ta share
tsakar gidan kana ta dauko tankaden garin
masara amai ya dinga taso mata, jiri na daukar
ta ta ajiye gari ta tashi da gudu ta shige daki ta
fada toilet ta dinga kwarara amai kamar yayan
hanjinta zasu fito. Tahir ya shigo tun daga falo
ya jiyo kakari ya shiga da gudu ya iske rabi'a
cikin mawuyacin hali sai da ta gama ya daukota
ya rungume kamar zai yi kuka ya fito da ita falo
ganin tana gumi ya tayar da inji da sauri ya
kunna mata fanka. A tsakar gida Dije ta fito
daga daki ta iske tumaki na cin garin nan da
nan idanunta suka rine da bala'i dama mai
neman kuka ballantana anjefata da kashin
awaki.. Ta fusata ta nufi dakin Rabi'a tana fadin
dan wulakanci da rainin hankali in baki
tankadan ki ajiye tumaki su cinye mini ai gara ki
ce ba za ki yi ba,ta hankada kofar ta shiga tahir
na zaune dirshan ya dora Rabi'a a cinyarsa ya
fitar mata da riga daga ita sai bra. Wai duk da
wannan abin da dije ta gani bata fasa zazzaga
masifa ba fadi take ai dama nasan kai ka hana
ta yin abinda na sata. Bakin ciki da kunya suka
kama su Rabi'a ta mike tana duddukawa ta
shige cikin daki yayin da tahir ya mike cikin
matsanancin haushi ya ce baki ga bata da lafiya
ba ne. Ta ce karya take dan ta ganka ne tun
safe take harkokinta. Ya ce to ni dai gaskiya ban
yarda da wannan tsarin ba. Dije ta fidda
dankwalinta ta ci damara tana fadin tunda baka
yarda ba sai ka zo ka dakeni sanan ne zan san
ka isa marar kunya. . . . Yara ne suka ruga waje
suka fadawa kawu tanimu ana fada dije da
tahir. Ya taso da sauri ya shigo gidan cikin
matsanancin haushi yadda dije ta shigo cikin
dakin shima haka ya danna kai ya riski tahir
yana fadin ni dai bance zan dake ki ba ina dai
so in gaya miki ne daga yau matata ta daina
bautar dafa ma yayanku abinci ana yi mata
wulakanci.Kawu tanimu ya ce sannu me mata?
Kai yanzu har ka yi girman da kasan dadin mace
zaka zagi iyayanka a kan mace? Wuce muje gun
hajiya in ita ta baka damar.........








Zaharaddeen Shomar

Whatsapp 08168575100







Launin Fata 1-08
Posted by ANaM Dorayi on 11:14 AM, 20-Oct-15
Under: Launin Fata
Wuce muje gun hajiya in ita ta baka damar ka
wulakantamu a kan matarka sai mu tashi mu bar
muku gidan ka zauna kai da matar taka in nine
na haifeka ka yiwa matata haka, kai ka iya duka
binda a kai maka ka ce an nuna ma bambanci
dan kai maraya ne kai kuma ka iya yin duk abin
da ka ga dama. Tahir ya mitsittsike idanunsa ya
wuce gaba suka shiga dakin hajiya yaya tana
zaune kan gado har yanzu bata da lfy amma dai
jikin da sauki. Kawu tanimu ya ce dije gayawa
hajiya abin da ya faru. Ta karkace ko tsoro Allah
bata ji ba ta sharo karya tana matsar ido ta ce
hajiya ni daman tun randa uban yar nan ya
sawota a gaba dan abin kunya ya kawota gidan
nan jikina ya bani in har a gidan nan zata zauna
sai an samu matsala gaskiya ni ba za zauna
yarinya tana mini kallon banza mijinta ya nuna
mata bamu da kima ba, ba mu isa mu sata ko
hanata mijinta sai ya zagi mutum, zamu bar ma
tahir da matarsa gidan.
Hajiya ta ce ya isa Dije duk abin bai kai zafin
haka ba, kai tahir abin da zan gaya ma shine ba
a kanka aka fara aure ba kuma ba kanka za a
kare ba, a ciki gidan nan ka girma tunda ka taso
baka ga wanda yake wa iyayansa rashin kunya a
kan matarsa ba. Kawu tanimu ya ce yawwa gara
a gaya masa dan naga alama watarana sai ya
kamani da kokawa a kan matarsa. Hajiya ta ce
ya wuce ke kuma dije ki ji tsoron Allah kin kusa
yin jika da rabi'a banga dalilin da zaisa ta tsole
miki ido kina damuwa da ita ba ki rike ta amana
kuma kin haifi yayan nan gasu nan a gabanki sai
kuma Allah ya kai naki yayan inda za a rike
amanarsu a kula dasu kana taimakon dan wani
ne dan gyara rayuwar naka. Saboda baka san
inda Allah zai kai naka ba kaima a gaban ko
baka mutu ba imma kana rayan.Tunda tahir ya
fita a ranar bai dawo ba sai sha dayan dare,
Rabi'a tana zaune a falonta ta zuba kwalliya da
shadda maroon colour, abinka da farar mace sai
kalar tayi amta kyau ainun duk bacin ran da
tahir yake ciki sai da ya neme shi ya rasa ya
ajiye ledar da ya siyo mata gashasshan nama ya
jawota da karfi ya rungumeta yana shafa cikinta
ya ce cikin nan girma yake Rabi'a sai kyau yake
kara miki wata matar in tana da ciki sai tayi
muni ke kuwa kyau kike karawa. Ta lumshe ido
ta narke a jikinsa ta ce nayi fushi. Ya ce me na
yi gimbiya ki rufawa rayuwata asiri komi zai iya
faruwa da ni in kika juya mini baya. Ta yi
murmushi me yasa kaje ka dade a waje? Yana
shafa gashin kanta ya ce ki yi hakuri Rabi'a tuna
takaicin abin da ke faruwa a gidan nan ya yi
mini yawa, ina bakin cikin yadda kika fada
wahala a dalilin aure na. Nasan Abba da yan
uwanki na can na fadin dama ga abinda suke
jiye miki nan. Gaba daya sai in dinga ganin ban
kyautawa rayuwarki ba. Ta rufe mai baki ta ce
haba mijina duk wanda yaga laifinka a kan
wannan ya kasance mai tsananin son zuciya.Ko
kadan ban dau wannan lamarin a matsayin abin
da zai zama matsala ga auran mu ba ni dai
abinda nake so da kai ka dinga dauke idonka a
kan duk abinda zaka ga an yi mini a gidan nan
wanda baya yi maka kadi. Saboda yin
maganarka ba zai kawo masalaha a cikin lamarin
ba sai dai ya kara lalata al'amarin. Su gani suke
ma asiri nayi maka kake mini irin wannan son
kasan yanzu an daina ganin namiji na son
matarsa irin haka. Ya ja tsaki ya ce yi shuru
Rabi'a duk wadannan hujjojin da kike zana mini
basu da tushe ballantana makama, babu wani
dalilin da wani zai sa ma ido danshi bai kula da
matarsa ya ce kai ba zaka kula da taka matar
ba, ko kuma wata dan mijinta bai kula da ita ta
ce ke mijinki ba zai kula da ke ba. Soyayyar da
nake miki Rabi'a tafi karfin in boye a cikin kasan
goman ban fito miki da kashi biyar ba kashi uku
ce idan na fito da ita gaba daya sai ki yi
tsammanin na haukace ni kuma duk abinda zai
faru da ni sai dai ya faru wallahi ba zan fasa
kulawa da ke ba.Rabi'a ta rasa abinda zata gaya
mai ya fahimce ta dole ta sa mai ido ya ci gaba
da baýana mata matsayin ta a zuciyarsa abin
har ya kaishi ga kwalla. Tun abin yana ba Rabi'a
tausayi da sha'awa har abin ya koma bata
tsoro. A wannaan dare ta ga wata irin soyayya
mai wahalar sha'ani a gun tahir kukan da ya yi
mata na soyayya daga daran zuwa wayewar gari
ya yi matukar firgitata jikinta rawa ya dinga yi
ta dinga ganin ko dai ya zautu ne. Tunda ya
aure ta take ganin soyayya iri iri agunsa, amma
bata taba ganin yayi mata abin da ya yi mata
yau ba kuma ya tashi jikinsa a sanyaye kamar
an mai mutuwa. Wajan karfe bakwai na safe
yana kwance kan doguwar kujera da carbi a
hannunsa yana ja farar jallabiyya ce a jikinsa
duk inda Rabi'a tayi sai ya bita da kallo, ta gaji
ta zo gabansa ta zauna ta ce dan Allah ka gaya
mini abinda ke damunka wanan kallon naka
yana firgita ni da yawa. Ya mike ya fice ya ce
mata ina zuwa. Shuru shuru tahir bai dawo ba
mamaki ya isheta ta ta ci gaba da ayyukanta,
dan har sha 2 rana tahir bai dawo ba, azahar
tayi la'asar ma shiru.
Ta shiga dakin hajiya yaya ta isketa jikinta ya
tsananta ta kasa gaya mata ta dawo daki ta yi
ta gumi duk gidan ba wanda zata tinkara da
maganar tahir sai hajiya gashi ita kuma ba
lafiya. Hankalinta bai gama tashi ba sai da dare
ya yi tahir bai dawo ba ta kira wayarsa taji ta a
daki kan mudubi tun tana dauriya har takama
kuka ta kasa zaune ta kasa tsaye, ta shiga dakin
hajiya yaya ta zauna tana kuka hajiya ta bude
ido ta ce Rabi'a matso ki min adu'a kirjina ya yi
min nauyi da yawa. Jikinta na rawa ta matsa daf
da ita ta hadu da muhamd dan wan tahir ya ce
ke lfy? Ta ce shigo dan Allah kaga hajiya. Ya bita
yana fadin me hajiya ta yi ita da na barta tana
magana sosai. Yana taba hajiya ya ce innalillaì
wa inna ilaihi raji'un.
Ke din nan mayya ce kashe hajiya kikayi dan
dana fita na barta tana hira a zaune na barta
kin shigo kin kashe ta. Kafafun Rabi'a da suka
kama rawa sai ta zube a gun tuni mutanan
gidan suka hallara a dakin. Rab'a ta sulale ta
bar dakin ana ta koke koke ta shige dakinta zata
rufe kofa kenan muhmd

Please Login or Register in order to submit comment