Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE



You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

╨╧рб▒с>■   o■   АААА                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                                ¤   l    

 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~БRoot Entry         └FpWordDocument    1╢0Table        Ё Data
            ■   ье┴ЙИ P┐4НKSKSд1╢Ъ├      дrr____/CЗ╝Cь_╨╩ ╩ ╩ ╩ ╩ ╩ ╩ ╩ ╠ $/▓с
*r__╩ ╩ ____╩ ┐C ╩ C╩ C╩ ╩ _C <╪G▀<╪G▀ RAYUWAR MARYAMU <╪G▀<╪G▀
Story & writing by

MOM MASHKUR

Littafin sadukarwa ne ga mahaifana,da fatan Allah musu rahma=╪O▄

Page 1 _ 2
BISMILLAHIR
RAHMANIR RAHIM

Wata mata na gani,bafulatana mai kimanin shekaru sittin. tana tafiya a dokar daji.gaba ba gida baya ba gida.baka doguwa kyakykyawa,duk da tsufan da tayi hakan bazai hanaka ganin kyanta ba.goye take da yarinya jaririya,mai kwana hamsin a duniya, sai kuma ta dauki gyalenta(mayafi) wanda ya tattauye saboda tsufa da yayi,ta sanya gyalen tayi kamar daurin kirji a saman dan goye hakan ya sanya har kan yarinyar ya rufe.
rike take da babbar bakar leda,me dauke da kayan jaririyar kala bitumen,sai fida da kuma ruwa a daure a farar leda.tafiya take a dokar daji, gaba ba gida baya ba gida,bakajin komai sai kukan tsintsaye. tana tafiya sai jaririyar ta tashi a bacci take ta kuka,sai inna sarai take jijjigata har suka kawo wata bishiya mai inuwa sosai.
inna sarai ta samu wuri ta zauna, ta sauke jaririyar,ta bude ledar ta fito da fida da farar ledar nan me kulle da ruwa.ta bude marfin fidar ta tsiyaya ruwan ta bata tasha,sannan ta kafa mata fidar nan mai madara,aikwa nan take ta fara tsotsa sha take sosai kamar me.aikwa nan take idon inna sarai ya cika da kwallar =╪"▐ tausayinta.bayan ta koshi, sai inna sarai ta dorata a kafada,sai kwa yarinyar tayi gyatsa,ba bata lokaci bacci ya dauketa.da inna sarai ta lura tayi bacci sai ta sauketa,daga kafada ta dorata akan cinya,take ta kallon yarinyar,tana kara ganin tsantsar kamar da take da mahaifinta tasi,u.
sai kuwa wasu hawaye=╪-▐ masu zafi suka cigaba da kwaranya daga idanunta, domin tunawa da tayi da marigayin danta,wanda ya rasu watanni uku da suka wuce.nan ta shiga tuno maganar da sunshine ranar da zai rasu."salamu alaikum"tasi,u yake sallama a tsakar gidan inna sarai."wa alaikumus salam"inna sarai ta amsa ,lokacin da take fitowa daga bandakin da akayi da itacen ridi,hannunta rike da buta."babangida ne "cewar inna sarai cikin yaren fulatanci."Eh inna nine"babangida ya fada.shima duk cikin yaren na fulatanci.

"Karasa ka zauna a tabarma ka jirani alwala zanyi" "toh" yace sannan ya karasa yana zama akan tabarma,ya fiddo wayarsa kamfanin tecno.keypad ce ya kamo wakar dankwairo yana ji.

<╪G▀<╪G▀RAYUWAR MARYAMU <╪G▀<╪G▀

Story &writing by

MOM MASHKUR

Page 3_4

Tazo ta tada sallar magriba,har ta idar tasi,u (babangida) yana kishingide,sai dai ya kashe wakar daya kunna ya ajje wayar a gabansa.yayi shiru kamar mai tunani.inna sarai tace "babangida" taji yayi shiru"ta kuma cewa "babangida ko bacci ne ya daukeka"dake ya juya mata baya.sai ta kai hannu ta tabashi aikwa sai yayi saurin juyowa, yace "to inna har kin idar da sallar ?" sai tayi shiru tana kallonsa kamar tana nazarin wani abu a tattare dashi,sai ya sunkuyar da kansa kasa.
Inna sarai tace cikin fulatanci "wai nikam babangida me yake damunka"ina lura dakai jiyama da kazo gidan nan,duk jikin ka sanyi Kalau.kodai kulun ce ba lafiya" matarsa kenan sunanta hauwa ake kiranta da kulu.duk da tasi,u ya kasance bafulatani,kuma ansan fulani akwaisu da kunya=╪H▐ amma hakan bai hana inna sarai sakewa da danta ba.saboda shi kadai gareta, duk da ya kasance da na uku a wurinta amma duk sauran sun rasu baban namiji ne sunanshi sale ya rasu bayan an haifeshi da kwana uku daman bezo da lafiya ba.sai ta kuma haifar zainabu itama tana yar shekara biyar ta rasu.
Sai kuma ta haifi tasi,u wanda har ta cire rai da kara haihuwa, domin kwa bayan rasuwar zainabu sai da ta kwashe kusan shekaru goma sha 18 sannan ta samu cikin tasi,u sunsha farinciki ita da mijinta malam buba makama wanda a wancen lokacin yana da rufin asiri.kafin Allah ya karbi ransa a lokacin tasi,u yana da shekaru goma,malam din kamar yadda kowa ke kiranshi.domin malami yana koyar da karatu ne anan rugar marayo da kuma sauran rugar dake makotaka da rugar marayo din.
Malam buba ya rasu sanadiyar ciwon cikin da yayi na kwanaki biyu, inna sarai taji mutuwar mijinta sosai saboda soyayyar dake tsakaninsu, sannan shi kadai take dashi a duniya. domin marainiya ce ba uwa ba uba,sannan ba yan uwa ita kadai mahaifiyarta ta haifeta,sai wacce suke uba daya sunanta iya tsahare tana aure a wani kyauye mai suna rakumi.iya tsahare ta tsani inna sarai

<╪G▀<╪G▀RAYUWAR MARYAMU <╪G▀<╪G▀

Story & writing by

MOM MASHKUR.


page 5_6

Tsana ce wadda tun tasowar su,take nuna mata,haka babarta ta nuna mata.wanda hakan ba hali ne mai kyau ba. sai dai ita inna sarai bata nuna damuwa akan hakan domin ba irin tarbiyar da mahaifiyarta ta mata ba.wannan kenan

Bayan rasuwar malam buba,su inna sarai sun shiga damuwa sosai ,saboda babu abinda ya bari sai wata gonarsa da yake nomawa, itama gonar ya siyar da rabi rabin ce tashi.

Sai gidan da suke ciki wanda gida ne na kasa daki daya sai kuma bukka,da kuma rumbu wanda suke ajje kayan amfanin gona a ciki.

Inna sarai tana dorawa tasi,u tallar kayan miya,ita kuma tana saidawa a gida da manja,da yan kulle kulle na gida.ta hakane suke dan samu abinda zasu rufawa kansu asiri.har tasi,u yakai shekaru goma sha bakwai a lokacin ne ya fara bin dan makotansu hashimu zuwa legos neman kudi.

Yana aykin karfi sannan yana dako, da dai sauran aiyuka wanda yake ganin zai iya hi.kuma alhamdulillah yana samun alheri,tunda ko gida ya tashi zuwa yakan siyo klin me yar dama da sabulun wanki,da gishiri dan leda ya kawo a rabawa makota da abokan arxiki.A haka har ya shafe shekara guda, yana zuwa birnin na legos neman kudi.daga nan sai aka fara gulma ana cewa mahaifiyar tasi,u ta fifita neman kudi akan aure sunnar ma,aiki. kunsan su kauye da rugage akwai auren wuri=╪▐.

domin shi hashimun da matarsa, har da dansa. daga lokacin ne da tasi,u ya dawo daga legos ganin gida inna sarai ta hanashi komawa.tace ya bari sai anyi bikinsa ya koma sannan babu mai cewa bashi aure yana tafiya neman kudi,tace "yanzu zakaji ana cewa fasikanci kake idan kaje can"sai aka hada dan abinda ya samu da wanda inna sarai take dan tarawa aka fara shirye shiryen auren tasi,u da budurwarsa sadiya wacce suke soyayya.

sorry=╪O▄=╪O▄=╪O▄ayi hakuri da wannan

<╪G▀<╪G▀ RAYUWAR MARYAMU<╪G▀<╪G▀


Story & writing by


MOM MASHKUR

Page 7_8

Ansha biki sosai,biki irin na fulani ansha fura da nono =╪▐. amma bikin daga Jama,ar gari sai yan unguwa wato babu wani dan uwa na inna sarai, sai makociyarta salamatu babar hashimu wacce ita ce ta zame wa inna sarai kamar yar uwa.

saboda zaman na amana da sukeyi,da kuma mutunta juna.har akayi biki aka watse amma iya tsahare babu ita babu dalilinta kuma inna saratu har kauyen rakumi tasa dan mashine ya kai ta, ta fada mata bikin na tasi,u.
amma bata zo ba,itama inna sarai bata tofawa kowa ba,koda an tambayeta ita sai tace bata da lpy.shima malam buba dangin nasa sun kasance dangin takanda, sai dai muce Allah jikan rai.
an kawo amarya sadiya gidan angonta,nan cikin gidan inna sarai,inda tasi u (babangida) ya gyara dakin kasar nan, sai ya kewaye musu da kara, ya musu bandakin na iccen ridi.an kawo amarya sadiya dakinta,sai fatan allah basu zaman lpy.

Zama tsakanin inna sarai da sadiya zamane akeyinsa mai tsafta,domin inna sarai bata da fada ta dauki sadiya da tasi,u duk daya ne a wurinta. itama sadiya yarinya ce mai biyayya ta dauki inna sarai tamkar mahaifiyarta,tunda daman mahaifiyarta ta rasu wajen haihuwar autansu inusaa, sai mahaifinsu kawai ne a raye.na (sanya sunan matar tasi u hauwa kulu to na canja na sanya sadiya ina ftn mai karatu ya fahimta).

Cigaba da Labari

inna sarai tace"to idan ba sadiyar ce ba lpy ba,to ko kaine ba lpy babangida"
tasi,u yayi shiru sai kuma yace"wlh inna nima bansan me yake damuna ba, kawai dai inajin jikina ba dadi" inna sarai tace"toh allah sawaqe,amma banajin dadin ganinka a haka" "lah ba komai fa inna" cewar tasi,u.

"kona zuba maka tuwon burabusko,gashinan har daman shanu"inna ta tambayeshi.yace "kai a koshe nake yanzu inna" inna sarai tace "to ai shikenan,nima salamatu ta aiko mini dashi" shi dai tasi,u baiyi magana ba sai ta sake cewa" to ko sadiya zaka kaiwa ko zataci ita"tace "gaskia inna ba lallai taci ba,saboda fitowar nan tawa na siyo mata dambu na kai mata.kuma kinsan ita ba gwanar cin tuwon burabusko bace, sai dae ki ajje min da safe nazo inci dumame"

Inna sarai tace "kaji ja,iri dumaman matar taka fa=╪▐"shima dariya yayi yace "sai ta cinye kayanta"yana mai tashi ya dau wayarsa akan tabarma,yace bari inje inyi sallah naga lokaci yayi" tace "to babangida" har ya fara tafiya tace masa" in kayi sallar gida zaka wuce"yace eh gida zan wuce"(yanzu ba anan gidan inna sarai suke da zama ba,a gidan abokinsa hashimu suke tare da hashim).

<╪G▀<╪G▀ RAYUWAR MARYAMU <╪G▀<╪G▀


Story & writing by

MOM MASHKUR

page 9_10

"idan naje gida zamu fita kallon shadi (wani wasa ne da fulani keyi da sanduna kamar fada ko ince gasa ce) nida hashimu" inna sarai tace" shadi kuma babangida a ina za,ayi shadi yau"yace a rugar baduku "tace to Allah kiyaye amma kar kuyi dare dan allah" " yace insha allahu inna"

bayan yaje gida, ya tadda sadiya har ta kwanta,yace "sadiyayye har an kwanta" tace wlh kasan sanyi wajen itama abokiyar hirar tawa ta shiga daki "(aisha matar hashimu)shima dazu ya dawo yana tambayarka"yace " yace ai gani na dawo daman shadi zamuje kallo" ku ko sanyin nan bakwaji"duk cikin fulatanci suke maganar nice ke fassarawa >╪*▌ "ina kika sakamin rigar sanyina" yace yana mai dubawa cikin lokar kayanshi. "tana kan igiya dana wanketa dazu, dana kwaso kayan wankin naji bata karasa bushewa ba"yace toh nagode matar aljanna, Allah dai ya saukeki lafiya inga abinda za,a haifa min"ummmm ta fada tana rufe fuskarta da tafukan hannayenta. alamar kunya shi kuma yake mata dariya.ya fita ya dauko rigar sanyin yasa,ya dauki takalmin roba sau ciki ya sanya, ya dauki sandarsa ya fito kofar daki.

Sadiya ta yunkura ta mike faker,saboda tsufa da cikin nata yayi ta biyo bayan tasi,u ta tsaya daga bayanshi, tana kallon bayanshi.kamar ance juya daman a jikinsa yaji kamar ana kallonsa,"ko kema zaki kallon shadin sadiyaye"ya fada yana dariya itama dariyar tayi " yoni yanzu ina zan iya zuwa Banda gidan inna" ta fada tana mai jingina da bango "baka ganin yanda nake "ta kuma fada tana kallon jikinta zuwa cikinta "sai in goyaki" ya fada kamar mai rada "kai malam in zaka ka taho mu tafi kar a fara muna hanya"sukaji muryar hashimu yana magana "da ita zan tafi" cewar tasi,u "to na tafi sai kun karaso, dan nasan nan da shekarama bakwa karasa ba"hashimu ya fada da zolaya yana kama hanyar fita daga gidan."zan kamaka" tasi,u ya fada cikin wasa.
"Sai kun dawo,a dawo lafiya" ta fada kamar batason yin maganar "amin sadiyayye"yace yana tafiya har zai fita daga gidan sai ya juyo aikwa ya ganta tsaye, yadda ya barta sai ya daga mata hannu,alamar bye bye=╪K▄.itama ta daga masa,ya juya ya fita daga gidan yanajin jikinsa ba dadi.

Can yaga hashimu yana tsaye m,yana jiransa ya tsayar da sandarsa ya dafeta da tafin hannu yana zuwa yace masa "toh muje mana"hashimu beyi magana ba ya bishi suka fara tafiya.maimakon subi hanya sai hashimu yaga tasi,u ya kama hanyar gidan innarsa,wato inna sarai "kai wa ina muka dosa ne" hashimu ya tambayeshi "inna zanwa sallama"ya fada ba tare daya kalli koda inda hashimun yake ba "jeka ka dawo ina jiranka" ya fada yana mai zama akan tayar kofar gidan.be masa magana ba,ya shige cikin gidan.

"Salamu alaikum" "wa alaikumus salam"inna ta amsa sallamar daga cikin dakinta "babangida"cewar inna tana me tashi daga gadon karfe "kai amma dakin nan naki inna akwai dumi" "gaskia akwai dumi babangida ai saboda wutar nan da nake kawowa daki" "kamar in fasa zuwa wurin shadin nan in zauna muyi hira"inna dariya tayi kawai tace"babangida kenan " "ga matar ka nan da tsohon ciki, in har firar ce kaje kuyi da ita mana yar amana"inna ai wannan amanar taki ce"tayi dariya tace "amma ka fini karfin rikon"murmushi yayi kawai.sai kuma yace "inna ko bana raye ai kece zaki kula da sadiya" "me ya kawo maganar mutuwa" duk da Allah ne yasan gawar fari dan nan.muma zaman jiranta muke=╪"▐ sai yace "allah jikan baffana ya hadamu a gdn ajannah"amin"inna tace daker saboda ya tada mata mikin mutuwar mijinta.

"to innata sai mun dawo " "adawo lpy ta fada tana kallonsa" Har ya fita daga dakin ya dawo "zan dawo da safe ki ajjemin burabuskon nan.

<╪G▀<╪G▀ RAYUWAR MARYAMU <╪G▀<╪G▀

Story & writing by


MOM MASHKUR


Page 11_12


MUNA JAJANTAWA KATSINAWA ABINDA YA FARU A JAHAR SU,WATO JAHAR KATSINA.UBANGIJI YA KUBUTO DASU YA ALLAH KADA KA BASU IKON KASHE SU,KO CUTAR DASU.=╪O▄=╪O▄=╪O▄


ina mika dinbin godiya ga QUEEN MEEMI BASHIR marubuciyar RAI DA SO,LABARIN HUSNA,RAHEENA.da dai sauran littattafanta ngd sosai da gudunmuwarki gareni, Allah kara daukaki ya daukakaki ya raya Zuri,a=╪O▄



Inna sarai tace "Toh Allah kaimu goben da abin aro" yace "ameen" ya fita daga gidan da sauri dan tunowa da yayi da hashimu na jiransa,a
kofar gida.
Aikwa yana fitowa ya fara fada "malam kasan dadewa zakayi ka barni ina jira,da nasan zaka jima dana yi tafiyata" tasi,u yace "yi hakuri abokina" hashimu dae tafiya ya farayi ba tare da ya kara mishi magana ba.sai ya kara cewa " wai kodae me machine zamu samu ya kaimu tunda bamu fito da wuri ba" sai a sannan hashimu yayi dariya yace "yawwa ko kaifa na sadiya"

sun shawo kwana kenan sukaga me machine suka tsayar ya musu goyon biyu,suka kama hanya suna tafiya suna haduwa da mutane,wasu a kafa wasu a machine.sun isa suka tadda an fara wasan,nan sukayi kallo har aka gama.bayan an tashi suka kamo hanya a kafa dake basu kadai bane akwai yan rugarsu, akwai yan wata rugar dake kusa da tasu suna cikin tafiya a daji sai ake tada zancen yadda shadin ya kasance aikwa sai aka fara musu,wasu suce "ga wanda yayi nasara "wasu suce " anyi galaba akan wane"duk musun nan da ake tasi,u beyi magana ba da hashimu akeyi.

Abu kamar wasa sai ya zama fada,aka fara cacar baki sosai,wasu daga ciki suna rabawa tasi,u yana janye hashimu amma hashimu yana komawa har takai sun fara doke doke da sanduna (kunsan bafulatani baya rabuwa da sanda) lol tsakanin hashimu da wasu su biyu daga cikin ayarin da suka taho dasu.tun ana rabiya har tasi,u yaga sun rufarwa hashimu,su biyu shi daya.sai tasi,u ya shiga fadan,shigarshi da wuya dayan ya daga sandar kafin tasi,u ya kare dukan da sandarsa ,ya sakar masa duka a tsakiyar kansa da karfi,nan take jiri ya daukeshi ya fadi a wurin

<╪G▀<╪G▀ RAYUWAR MARYAMU <╪G▀<╪G▀

Story & writing by

MOM MASHKUR


Page 13_14


A nan take hashimu yayi kanshi ,yana kiran sunan shi,su kuma wanda ake fadan dasu suka fara tafiya.ko a jikinsu Wanda ya kwala masa sandar ne ke cewa " da kasan kai ragone baka da karfi kake tarewa wani fada" suka tafi abinsu,sai sauran mutanen da suka tsaya suka kewaye tasi,u suna masa sannu.

shi kuma tasi,u murmushi yayi yana kokarin tashi zaune,sai hashimu ya kama hannunsa ya taimaka masa ya tashi zaune."hashimu inason insha ruwa" tasi  u ya fada sai wani cikin mutanen nan ya miko ruwa a cikin jarka,wanda ke rataye da tsumma a wuyanshi.

Aikwa yasha ruwan nan sosai,bayan ya gama sha ya mika musu jarkar,aikuwa nan take ya fara gumi sosai gumi yake zubowa daga jikinsa " ya kamata mu tafi gida " inji tasi,u " ka bari ka dan huta " cewar hashimu " A ah mu tafi kawai "tasi,u ya fada yana kokarin tashi tsaye,aikwa jiri yake dibansa.

sai daya cikin mutanan da suka tsaya yace " kunji karan machine yana tahowa ku bari, ya karaso sai ya rage masa hanya "hashimu yace to idan da mutum a bayanfa " sai tasi,u yace " kawai kazo mu tafi "ya fara tafiya taku daya biyu ana ukun sai ya jiri ya daukeshi ya tafi zai fadi,hashimu yayi saurin tareshi shida daya cikin mutanen nan.dai dai nan machine din nan ya karaso,mutum biyu. ne aka mai tukawa da kuma wani a bayanshi .suna zuwa suka tsaya ganin mutane a wurin da kuma hasken fitulu,sai direban yace" lpy dai ko "sai yaga mutum a zaune ya jingina da wani a kusa dashi.anan wani ke labarta musuw abinda ya faru sai na bayan machine dn ya sauka yace " ka hau ya kaika gida bazaka iya tafiya ba ni sai in tafi a kasa "sai direban yace "ya yau sai dan uwan nasa ya hau bayanshi in kaisu " suka hau dan tasi,u sai da hashimu ya tallafeshi sannan ya iya hawa machine din.

Sun fara tafiya me machine din yace " wace ruga zan kai ku " "rugar marayo " hashimu yace yana mai sauke ajiyar zuciya. " "kai amma basu kyauta ba gskia " me machine din ya fada yana me jajantawa "wlh ni bansan me zan cewa innarsa ba,mun taho lpy mu koma a haka " tasi,u ya fada yana mai jin zafin dukan da suka yiwa abokin nashi.da yasan haka zai faru da bai zo kallon shadin ba, balle har yayi musu ya kaisu ga fada yanzu gashi ya janyo sun yiwa abokinsa lahani.ya fadi hakan cikin zuciyarsa.

"Kaddara" tasi,u yace lokacin da yake kokarin zaunawa dai dai akan machine din,dan gaba daya ya kwanto jikin hashimu shi kadai yasan

<╪G▀<╪G▀ RAUWAR MARYAMU <╪G▀<╪G▀

Story & writing by


MOM MASHKUR

Page 15_16

Amma hakan be samu ba, dan kuwa kasawa yayi sai jikin hashimun ya kara komawa ya jingina.Sun kusa isa rugar tasu tasi,u ya fara karkarwa kamar mai zazzafan zazzabi,haka ya ringa karkarwar har suka iso cikin rugar,dan lokacin ma kafa duk ta dauke, dan kusan sha biyu na dare.danma an gama wasan shadin da wuri, don wataran sai wajen karfe uku na daresuke dawowa.

A nan hashimu yake nuna masa hanyar gidan nashi,inda suke zaune da tasi,u da matarsa daya basu daki,tun bayan da dakin nasu ya zube da damina sanadin wani ruwa da akayi mai yawa.inda Allah yasa ba wanda ya fadowa.

A dai dai kofar gidan me machine din ya tsaya,inda hashimu ya nuna masa,nan hashimu n ya sauka amma sai yaga tasi,u ya langare alamar bazai iya tsaiwa da kansa ba "tasi,u "hashimu ya kirashi yana mai jijjigashi. " na am" ya amsa daker dan har zuwa lokacin jikinsa bai bar karkarwa ba,sannan ji yake gaba daya bashi da karfi ga kuma kansa dake barazanar rabewa gida biyu,wani irin ciwo yake ji daga tsakiyar kansa.

" ku kamani" ya fada saboda ba abinda zai iya yiwa kansa, in ka dauke numfashin da yakeyi kamar inji na zuko masa.sai mai machine din yace " mu saukeshi inda in haska kan nashi In gani " suka kamashi cali cali suka saukeshi daga machine din.suka zaunar dashi aka jinginashi da dangan kara, wanda aka kewaye gidan dashi.mai machine din ya fiddo torch light daga aljihunsa,nan take ya kunna yana mai haska kan tasi,u a lokaci guda suna kokarin gano ciwan da aka ji masa INNALILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI,UN Sukayi saurin fada a tare,ganin yadda kan yayi,domin kwa tsakiyar kan tayi wani irin lobawa.ai hashimu bai san lokacin da hawayen tausayin abokinshi ya fara kwaranya daga idanunsa ba.
<╪G▀<╪G▀ RAYUWAR MARYAMU <╪G▀<╪G▀


Story & writing by

MOM MASHKUR

Page 17_18


A lokacin inna Sarai ji take kamar a lokacin abin ke faruwa,tuno da mutuwar babangida da tayi, duk da cewa kullum mutuwar tana ranta musaman ganin MARYAMU a tare da ita ko in tana kukan yunwa ta rasa abinda zata bata.

Ita bata da nonon da zata bata,nonon ba zuwa zaiyi ba sannan ita ba kiwo take ba bare ta bata nonon akuya,dan yanzu ko kaza bata da ita ,sai dai take bin gidan mutane kamar mai bara, tana rokon su taimaka mata da nonon da zata bata. amma saboda rashin imani tana ganin dabbobin amma masu su suce babu,ko kuma suce ba nonon jijin dabbobin saboda suna zargin cewa ita yarinyar ita ta kashe ubanta,saboda jahilci wai saboda haihuwarta ubanta ya mutu sannan mahifiyarta sadiya ma ta mutu.



daman salamatu makociyarta ke taimaka mata da nonon tana baiwa MARYAMU amma mai gidanta ya hana ta saboda kar idan yarinyar ta kashe inna sarai ta dawo kansu saboda makusantanta take kashewa, a cewarsu ta kashe ubanta tasi,u ta kashe uwarta sadiya wanda kuma ba haka bane kawai shaci fadine da kuma jahilci da yake damunsu.

Dan tun ranar da tasi,u ya rasu take ganin taskun rayuwa,domin kuwa duk da kukan nan da hashimu yake da kuma shine sanadin da aka kwala masa sanda,hakan bai hanasu tashi ba washe gari daga gidan dashi da matarsa, da yarsa, cewarsu kar yayi fatalwa yazo musu cikin dare.

dan wanda zai masa wanka ma rasawa akayi,sai inna saratu da sadiya suka masa ita jikin tsufa ita da tsohon ciki dan lokacin cikinta wata takwas dan yan kwanaki. Da kuka inna ta samu hashimu tace ya taimaka musu susa masa likkafani amma sai ki yayi har sai data tafi gidan liman din sannan shima yazo ya taimaka shima dan yana tsoron kar mutane su daina ganin girmansa dan bawani ilimine dashi ba.haka dae yan tsirarrun mutane suka sallaceshi a kaishi gidanshi na gskia.

anan bayan gidan aka binneshi gaba da gidan, kadan tunda daman gona ce ba wani gari bane ruga ce,dan ko mahaifinsa ma anan aka binneshi.

Inna sarai tayi kukanta sosai a gindin bishiyar nan ta share hawayenta,ta dauki MARYAMU ta goyata wacce har wannan lokacin baccinta take bata san me akeyi ba.ta dauki bakar ledarta taci gaba da tafiya.tayi tafiya sosai ta fara hango bukkoki har ta fara jin kukan jaki,da na shanu sauran dabbobi.sai tabi wata karamar hanya da zata sadata da gidan.

Tun kafin takai gayin sallama,wani katon kare ya tukarota yana haushi,sai ta fara sallama "assalamu alaikum "ga wani yaro ya fito daga daki,zai kai kimanin shekaru shida "magana"yaron yace yana korar Karen. "yahuza ana gida" inna sarai ta fada cikin fulatanci, " eh inna" "to madallah" "ina mutan gidan suke ta fada "innata ta tafi rafi daukan ruwa,innar auwalu kuma ta tafi gari nika
" Wayyo Allah na sun maka lahani "hashimu ya fada," kar ka damu" ya fada yana mai cije lebe saboda yadda yake jin kan nasa yana,wani irin zugi." mu kamashi mu shiga dashi ciki mana " mai machine din ya fada " wlh tunanin yadda zan tunkari matarsa dashi a haka nakeyi " " ya za,ayi da ikon Allah " mai machine din yace " haka Allah ya kaddara min " cewar tasi,u haka suka masa cali cali suka shiga dashi cikin gidan,a lokacin sadiya ta fito daga bandaki,da taje tayi fitsari ta fito, dan dama ba bacci take ba,dan duk ranar da suka tafi kallon shadin nan bata yin bacci sai dai barawo.

Tsayawa tayi tana kallonsu tama kasa gane wanda aka kamo,dan gaba daya ta rude fatanta kawai Allah yasa ba hashimu bane dan ta kasa danganta hakan ga tasi,unta.ita tunaninta. ma mutuwa mutumin yayi.ganin sun doshi kofar dakinta yasa ta kara rudewa,dan ta kasa koda motsawa daga inda take, ba tun shigowarsu.

"ki kwantar da hankalinki sadiya " tasi,u ya fada cikin dauriya ai sai sadiya ta taho da sauri tana mai fashewa da kuka,gaba daya jikinta karkarwa yake.saboda tasan ba karamin abu bane zaisa tasi,unta ya kasa tafiya da kanshi ba.zasu shiga dashi daki

Please Login or Register in order to submit comment