Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dan kamar wanda ba yan garin mai alkama ba,dan da suka hadu da su bashira ita da habasiyya sosai suka nuna bakin ciki suke hararansu dan sunga sun fisu yin kyau nesa ba kusa ba.

Sai dab da magrib suka dawo gida, a gidan inna sarai suka sauka dan lokacin ma ta dawo daga gidan jummai domin dubo jikinta, amma har yanzu jummai bata saduda ba , dan daker ta amsa gaisuwarta tana wani yatsina tana wani harare harare da zazzare idanu kamar wata tsohuwar mayya.

Wannan dalilin ne yasa da inna sarai ta biyawa iya tace bazata jeba ,ai ta dubata dubiyar hakkin makotaka, kuma tunda ita batasan mutunci ba .haka ta kori su MARYAMU da sukaje dubata.dan haka daga gida ta mata addu,ar samun lpy.ita ma inna sarai haka ta fito daga gidan jiki a sabule dan tana mamakin jummai duk abin nan daya sameta amma ko sanyi jijinta baiyi ba ,da alama ma in ta warke taci gaba da rashin mutunci daga inda ta tsaya.


"""""""""""""''''"""""""""
Wani irin dadin yaji ya ratsa dukkan sassan jikinsa, amon muryarta da yaji shi kadai yasa yaji darsuwar kaunarta a cikin zuciyarshi.
"Hello"ta kara fada dan jin shiru ba,ayi magana ba,kuma ba,a katse wayar ba.hakan ya nuna yana jinta kenan,dan tana jin shuwww na iska a cikin wayar sannan tana jin hawa da sauka na lunfashinsa.
"Hello gani na karaso " mannir ya fada daga dayan bangaren.
"To bari inzo in shigo dakai"ta fada cikin zazzakar muryarta.
"Ok ina jira"ya fada a hankali dan sai yaji gaba daya jikinsa ya mutu bashi da kuzari.
"Daman haka muryar mata take a wayane ko kuma itace muryarta haka?"ya tambayi kansa.nikwa nace kodai ka fara kamuwa=

Haka ta karaso har bakin get din bata ganshi ba.
"Me gadi ina bakon nan yake"ta tambaya a hankali kamar mai ciwon baki
" hajiya wane bako kuma" mai gadin ya fada da alamar tambaya"
"Ya ina tambayarka kana tambayata"ta fada da dan karfi sabanin da da take magana a hankali.
"Ayi hakuri hajiya aysha wlh ba wani bako daya zo"
"Okay" ta fada tana meka hannu ta bude karamar kofar get din ta leka.
"Bismillah ya mannir"ta fada cikin jin kunyar kallon da yake binta dashi tunda ta bude kofar.sanye take da doguwan riga baka da aka kawata ta da fararen stones sai tayi rolling da dankwalin rigar sai takalmi mai dan tudu.rigar tayi matukar amsar jikinta domin aysha badai kyan diri ba.babu kwalliya a fukarta daga powder sai kwalli sai kwa lipstick data shafa a labbanta.
"Ka shigo daga ciki"ta kara fada.
Mannir daya gama shagala da kallonta yayi saurin basarwa ta hanyar fadin.
"Okay ba damuwa"


Haka suka taho ita a gaba shi yana binta a baya, dan ya tsaya sun gaisa da mai gadi ya masa dan ihsani.dan dama akwai sanayya tsakaninshi da mai gadin tunda unguwa daya ne, sannan kuma yana zuwa gidan idan abbansa ya aikoshi ko kuma idan yazo gaishe da baban ayshan.haka suka shigo har wani katafaren falo daya sha kayan alatu , wanda anan suke saukar baki.falon sai kamshin turaren wuta yake ga sanyin a.c sai television da take ta aikinta.dazu da yace zai zo aysha suka dan kara gyara falon ita da wata mai aikinsu,duk dama dai ba wani datti yayi ba suka saka turaren wuta suka kunna ac da tvn.

Bayan ya zauna aysha ta durkusa har kasa ta gaishe shi, cike da kunya dan ita gani take kamar yana mata kallon ita tace tana sonshi a hadasu aure.batasan ba shi yanzu ya rigata fadawa kogin soyayyar ba=9. Haka ya amsa mata gaisuwar cike da fara,a dan daman in yazo gidan wani lokaci idan sun hadu sukan gaisa.

Haka nan ta tashi cike da jin kunya ta fita daga falon, can sai gata dauke da tire mai dauke da jug data hada masa lemon tuffa da ayaba da tayi tasa sai tasa kankara da madarar gwangwani a ciki. Sai goran ruwa da lemon five alive sai plastic mai dauke da dambun nama a ciki.tazo gabansa ta ajje a ladabce ta koma ta zauna a kan kujera tana wasa da leban mayafin rigar wanda tayi rolling dashi.
"Ba za,a zubawa yayan ruwan yasha ba, ko sai na roka" ya fada yana kafeta da idanunsa dako kiftawa bai sonyi saboda kallonta.
"Wanne zan zuba maka"
"Wanne zan zuba maka"ya fada yana mai kwaikwayon muryanta.n fuskarta.
"To na bari amma meye a jug din nan"ya fada yana nunawa da yatsansa.
"Lemo ne na hada "
"To zuba min wanda kika hada nasan sai yafi dadi"
"Ya akayi ka san zaiyi dadi"
"Kawai dai"
"To ka bari sai kasha mana"
"Okay"

Yasha lemon sosai dan sai da ya kusan shanyewa sannan yaci danbun kadan, yana ta santi ,tana masa dariya.dan ta fara sakewa dashi saboda ya gabatar mata da kanshi a matsayin masoyi kuma ya aminta ta zama uwar yayansa,kuma itama ta nuna masa amincewarta dan dama aysha wayayya ce kawai dai bata da rawar kai da nuna isa irin na yayan masu kudi.tana da ilimin addini daidai gwargwado ,sannan ga uwa uba ilimin boko dan ta kammala karatunta har matakin degree.






Sun shaku sosai dan soyayya suke nunawa junansu zallah ba algus.aka sanya biki wata biyu kacal.akayi biki sosai dan ba karamin kudi mannir ya fitar ba.aka kai amarya gidan angonta dake anguwar rigasa.

Suna zaune lpy suna soyayya tare da nunawa juna kulawa ,dan kowa kokari yake yaga ya farantawa dan uwansa. karfin gwiwar yin typing ngd>>>
Story & written by


MAMAN AFRAH



page 53 _54



*>2>2>2 Allahummag* *firliy, wali* *walidayya* *warhamhuma* *kama* *rabbayani* *sagira*=O=O=O




Anya daga haduwa da mutum yau ,yau din nan har nayi saurin yadda da ita,karfa inje taci amanata.tunda duduwa ta yaudareni kowama yaudarata zaiyi ,gskia mutum ba abin yarda bane.to kodai in fada mata tunda sun kusa gama zamansu anan su tafi, kuma watakilma idan ta tafi bazamu kara haduwa ba har abada.

"Wai ya kikayi shiru kodai sarkin yan tauri kika tabo kafin ki baro Nigeria" muryar zee ta katse mata zancen zucin da take.
"Lah daman ba komai ne kawai dai ina dan tuna yarana ne"
"Yo kuma banda abinki lantana ai sai kiyi hakuri ki dau dangana ,tunda yanzu kunyi nisa da juna"
"Hakane "ta fada tana yin yake wanda yafi kuka ciwo, dan ita tun ba,aje ko ina ba gaba daya ta saduda da rayuwar data sanya kanta.tabar yaranta gashi gaba daya abinda ta mallaka ya salwanta.

"Wai da wane sarki dan ni har na kagu inji" zee ta kara katse mata dan guntun tunanin data tafi.

"Kawai ki fada mata watakila ma ki samu mafita daga wurinta" wani bangare na zuciyarta ya fada mata hakan.
"Daman wani malami ne da duduwa ta rakani wajensa ,ya bani turaren da zan shafa in mallaki sarkin makka"
"=3 Sarkin makka fa kikace lantana?" Zee ta fada tana zare ido.
"Eh sarkin makka zai zo har inda nake ya aureni kuma in zama tauraruwa a cikin matansa"nan dai ta kwashe komai ta fada mawa zee.
"Lantana tauraruwa matar sarkin makka>#>#" zee ta fada tana kwashewa da dariya sosai har tana rike ciki.
"Haba zainab yanzu meye amfanin dariyar da kike min, kamar kin samu wata mahaukaciya"
"Yi hakuri lantana wlh abinne akwai abin dariya, haba kekwa lantana to ay ko mai aikin gidan sarki baza,a daukeki ba ,bare kuma matarsa matarma kuma tauraruwa, wato duk matan nan nasa larabawa ke zakike haskasu" ta fada tana cigaba da dariya.
"To ni yanzu meye laifina a ciki nifa kawai kudi na biya aka min aiki, dan haka ba abinda nake tsammani sai biyan bukata"
"Lallai lantana an gaisheki to idan har akwai maganin da za,a baki ki auri sarkin makka ,to kwa da tin kan a haifeki wasu matan sun aureshi"
"Aikwa Allah zai saka min hakkina da suka dauka"

"Yanzu ina turaren naki yake"
"Ai tunda naga ba makka muka dosa ba na fasa
shafawa"


Haka zee ita da lantana sukayi ta tattaunawa a wurin , har sai da lantana ta gaji saboda taga kafa duk ta dauke.sai bayan sun koma dakin suka samu duk yan dakin sunyi bacci abinsu anan suka kara tabbatar da sun dade a waje ba.
"Zoki kwanta daga nan gefen shinfidata, tunda kowa ya kwanta kuma kinga babu wuri sai can wajen bakin kofa kuma ba kofar kirki ba"
"To nagode"

Da asuba kiran sallar da wani yake rangadawa ,Shi ya falkar da lantana
Daga wani irin nannauyan bacci daya kamata dan daker ta iya bude idanunta.domin wata hayaniya da taji anayi a dakin ,dan gaba daya tama manta da a inda take sai dataji ana cewa
" ku fito mu fita alwala kar mu rasa ruwa" sannan ne ta fara gane a inda take,kafin daga bisani ta gama wartsakewa .
Fitowa suka dinga yi gaba dayansu daga dakunansu suka tunkari inda aka zuba ruwa a gwangwanaye da kananan butoci.kowa yana dauka yana zuwa ya kama ruwa, dan wasu ma da layi yayi yawa a kofar bandakin nan daga bayan bandakunan suke yin fitsari.haka sukayi alwala sukaje filin da aka shinfida tabarmi da buhunhuna aka hau sahu sahu,sahun gaba guda daya mazane sai sauran duk matane.bayan an idar da sallah lantana ta tsaya tana kallon yawan mutanen dake zaune a sahun sallah basu tashi ba, mamaki take da yawan mutanen da duk matan babu kalar da babu akwai yara yan mata, akwai yaran mata,sannan akwai manyan mata dattijai ne kawai babu.

"Lantana ki tashi kuje za,a raba muku ayyukan da zaku keyi"cewar zee data dafa kafadarta.
"To "ta fada a gefe daya kuma tana tunanin wane irin aikine za,a raba da sassafen nan.
"Zo muje kinga sauran can duk sun tattafi"cewar rakiya tana yin gaba.itama lantana binta tayi har ta taddota sukaci gaba da tafiya a cikin ayari.
"Hmmm nidai Allah yasa abani shara"lantana ta fada tana kallon rakiya."kedai ba sai abinda muka tarar ba,haka kawai mun baro mazajenmu da yayanmu mun taho neman kudi, gashi nan zamuzo mukewa wasu bauta.daman ai in kaki sharar masallaci kayi ta kasuwa"rakiya ta fada tana gyara dankwalinta ta cikin hijabi daya sunce.
"Wai kina nufin da aurenki akanki"cewar lantana da mamaki.
"Eh mana da yardar mijina na taho" rakiya ta bata amsa.
"Wai dan Allah da gske"
"Haba lantana akan me zan miki karya"
"Kinji dadinki ko bayan kin koma gida da mijinki a hannunki"
"Wai daman zawarci kike lantana, in a nufin baki da aure?"
"Hmmm kedai bari rakiya ai wlh duduwa ta gama cutata, bazan taba yafe mata ba"
"Me kike nufi wai bayan ha,intar taki da sukayi kuma nufin akwai wani abu?"
"Wlh tasa na kashe aurena ,dan sai da nasa mijina ya sakeni sannan na taho ,in takai ce miki babu wata sauran igiya a tsakanin nidashi dan duduwa cewa tayi in tabbatar ya sakeni kafin in tafi"
"Tirkashi laifinki ne Allah kyauta ,amma ta gama dake wlh ko ince kin gama da kanki"rakiya ta fada dai dai sun karaso inda aka tarasu.

Nan aka rarrabasu kashi kashi, kowa da aikinsa,
Akwai masu kiwon dabobi, irin dabobin tun daga rago tinkiya akuya dan akuya wato dabobin gida domin a wannan gidan ne ake siyan abin yanka da ake amfani dasu a makka da madina da sallar layya.wadanda idan an yanka ake lodewa a manyan motoci ana kaiwa kauyuka sadaka dan har yan sauran kasashe da suka zo aikin hajji anan abin layyarsu yake dan haka dabobi ne masu yawa a gidan kosassu.
Akwai masu kiwon shanaye.
Akwai masu kiwon tattabaru da zabi su a gidan abincinsu yake ba wurin kiwo suke ba.
Akwai masu kiwon rakuma.
Akwai masu kula da lanbu.
Akwai masu sharar wurin dabbobi da masu noman gonaki.
Lantana tana cikin masu kiwon rakuma dan an nuna musu rakumansu guda hamsin su uku da ita da rakiya da wata da basu santa ba.lokacin da aka raba ayyuka lantana kamar tayi hauka dan bakin ciki abin takaici ma kora rakuman zasu nayi su kaisu can cikin wani kurmusun daji dake cikin gidan.siyi kiwo su kaisu susha ruwa sannan su maidosu su daddauresu.su lantana an zama fatake >.
A yadda aka nunawa kowa aikin da zaikeyi ,sai su lantana suka dawo daki suka karbi abinci sukaci suka dan zauna 8:00 am aka fara kada kararrawa nan kowa ya fara fitowa domin tafiya Wurin aikinsa.daman zee ban ruwan fulawa take tun safe sai takai karfe uku take gamawa, idan ta dawo hallaw karfe hudu ta kara komawa sai magrib sannan zata dawo.hakama sauran sai karfe uku kowa zai dawo kafin a koma na yamma.



"""""""""""""""""
Yau ma kamar kullum haka suka shirya domin zuwa makarantar dare, bayan sun fito suna tafiya suka ga su bishira da habasiyya zasu tafi shagon emeka .
"To munafukai sauran idan kunje makaranta ku gayawa malam aramma mun tafi shagon emeka, wlh mu yiwa yara jini da majina"=Jbishira ta fada tana binsu da kallo daya bayan daya.
"Aikin banza masu zuwa wurin maza"cewar MARYAMU.
"Ke mu kike fadawa haka"cewar bishira.
"An fada din"inji halima
"Dalla rabu dasu halima mu tafi makaranta su basa son karatu"MARYAMU ta fada tana kama hannunta dan su tafi.
"Ke tsaya da suwa kike" bishira ta fada tana kamo kasan hijabin MARYAMU, aikwa MARYAMU ta daga hannu ta mareta,sannan tasa daya hannunta ta hankada habasiyya.
"Duk wacce take son fada ta bari a taso daga makaranta, dan yanzu na dena kyale koma wacece ta shiga harkata"MARYAMU ta fada tana jan hannun halima sukabi hanyar makaranta.suka bar su bishira da sanyin jiki domin kwa sun tsorata da abinda MARYAMU tayi dan daman sun san tana daga musu kafane saboda innarta ta hanata biyasu .
"Mesa ta dena tsoron tayi fada damu"cewar habasiyya tana rike haba.
"Inaga saboda tasan innata bata lpy, bazata iya zuwa gidansu ta yiwa innarta fada ba daman kuma saboda gudun fadan innarta ta hanata.bishira ta fada tana bin bayansu MARYAMU da kallo da suka sha kwana dan tama daina hangosu yanzu.
"Muje shagon emeka mu samo kudin siyan wainar gobe da alawa " habasiyya ta fada tana dariya.
"Wlh kwa dan malam aramma bazai iya samu mu dena zuwa ba" itama bishira ta fada tana dariyar.

Bayan an tashi daga makaranta suka hadu da ishu dan gidan malam aramma, anan yake tambayarsu cewar su bishira basu sake tabasu ba? Aykwa nan suka shiga bashi labarin irin tijarar da inna jummai taje ta yiwa inna sarai.sannan suka bashi labarin yadda bishira ta masa karyar ya matseta a lungu da irin alwashin da inna jummai taci na dakko dan sanda.

Suka dora da bashi labarin halin da inna jummai ta samu kanta a wani dalilin dakko dan sanda a sule tankar kar.

Ishu yasha dariya sosai har yana rike ciki kan dariya, dan yaga sakayyar da Allah ya yiwa su MARYAMU, koma yace harda shi dan da an kamashi kawai sharrin yin yunkurin fyade za,a masa.
"Gobema ta kuma komawa"ishu yace yana kara darawa.
"Wlh kwa"cewar halima tana tayashi dariyar.
"Kema MARYAMU ki daina kyale su bishira, dan idan dai suka san in sun takaleki ba kyalesu zakiyi ba ,to bazasu ke shiga sabgarki ba"
"Ai in gaya maka yanxu ma da muka taho suka raina mana hankali, aikwa MARYAMU ta mari bishira ta hankqda habasiyya, kuma basu rama ba"
"Kingani ko to daga yanzu zasuke tsoronki banzaye masu girman biredi" ya fada yana jan tsaki.
"Halima muje mu tafi gida dare yayi"cewar MARYAMU.
"To sai da safenku"ishu ya fada yana fara yin hanyar da zata sadashi da gidansu.
"Allah kaimu "suka hada baki wurin fada.

Bayan sunzo kowa ya shiga gida , anan baffa ke tambayar halima inda ta tsaya da aka tashi ta fada masa yace kar su sake tsayawa idan an tashi daga makaranta.
"Assalamu alaikum"MARYAMU ke ta sallama ,har saida tayi sau uku inna sarai da bacci ya fara daukanta ta amsa mata.
"Wa alaikumus salam"
"Wai inna har kinyi bacci"
"Wlh kwa"
Wash duk na gaji gashi bacci nakeji" MARYAMU ta fada tana cire hijab dinta.
"Wai da ina kuka tsaya ne MARYAMU?"
"Bayan an tashemu shine ishu ya tsayar damu a hanya yake tambayarmu inna jummai ta dakko dan sandan"
"Kinga MARYAMU ki kiyayeni wlh,akan me an tashi daya makaranta zaku tsaya da daddaren nan da wani namiji ,bayan yanzu daren sanyi duk kafa ta dauke.to ko a birni da sanyi idan dare yayi kafa daukewa take saboda kowa yana gida,kuma ko da daren ba wani darene sosai ba" inna sarai take fada kamar ta ari baki dan tasan ishu saurayine kuma su MARYAMU yarane kar yaje ya kokarin bata musu yara yanzu da zamanin nan ya baci ,duk da ba halinsa bane amma baka shedar mutum sannan shedan ba abinda baya iyawa sai dai addu,a kawai ba abinda ya gagari uabngiji.
"Wlh inna daman dan ya tambayemu Amma da bazamu tsaya ba"
"Ke rufe min baki banda shima ishun wani dukan iskane ya za,ayi yake tambayarku an dakko dan sanda? da an dakko dan sandan ai da an nemoshi duk inda yake a garin nan na mai alkama,tunda shi take zargin an aika ya matse mata diya" ta kare tana bata rai sosai dan MARYAMU ta tsorata dan bataso su fara shigewa ishu dole sai ta dage dan mai ya mace sai da taka tsan tsan.
"Wlh inna bazamu kara tsayawa ba idan an tashi"MARYAMU ta karashe maganar kamar zatayi kuka dan ta tsorata sosai da yadda taga inna sarai ba sababi.nan dai MARYAMU ta bata labarin yadda sukayi dasu bishira.amma duk da hakan inna sarai bata goyi bayan MARYAMU ba tadai ce mata kar tana biyasu dan kar su zama daya domin abokin damo guza.



Haka rayuwa taci gaba da kasancewa yau fari gobe baki, har su MARYAMU suka kammala karatun primary scul. A lokacin MARYAMU nada shekara goma sha daya dan lokacin sai abinda ya karu ba daga nutsuwa da hankali kuma har zuwa wannan lokacin MARYAMU bata da kawar data wuce halima.
Bangaren inna sarai har zuwa wannan lokacin babu abinda ya sauya na daga yan sana,ointa da takeyi dan ita bata yarda MARYAMU tayi tallaba, sannan kuma tsakaninta da iyar halima sai sambarka domin kaman yan uwa haka suka dauki su inna sarai, ba abinda yake tsakaninsu sai alkairi.

Inna jummai an warke ragas sai dai idan tana tafiya tana dan dingisawa ,amma ba wani sosai ba dan duk wanda ya kalleta idan har yasanta a da to zaiga tafiyarta ta sauya.amma rashin mutunci yana nan sai abinda ya kara gaba.dan akwai wata rana data shiga gidan inna sarai taga ta ajje alkama da yawa a daro sannan ga hatsin tuwon su data shanya a buhu, sai jummai taje neman bishira kuma bayan tasan bishira ba wani fiya zuwa gidan take ba.daman gulma tajeyi saboda taji ance baffan halima ya dawo daga neman kudi ya siyo musu tirmin babbar atamfa shine taje dan ta tofa,shine innar ta kyaleta.har innar na ce mata ta fito zata kulle gidan tunda ita batason zaman lpy.

Ai inna sarai na kulle gidan ta tafi gidan barka da gidan makoki sai jummai ta shiga gidanta ta dauki dan akuya da akuya da tunkiya,take jefasu ta katanga suka shiga suka cinye hatsin da alkama. Inna sarai na bude kofa sai ga dabobin na fitowa suna shiga gidan jummai mai dambu.




"""""""""""'''""""""""""
Bayan wata biyu da auren mannir da aysha sai aysha ta fara rashin lpy , mannir ya dauketa ya kaita asibiti gwajin farko aka tabbatar musu da tana dauke da juna biyu na tsawon wata guda. gashi aysha tana da laulayin ciki kullum bata lpy ,sannan komai taci sai ya dawo.dan har sai da takai mannir ya hakura da zuwa kasuwa dan ko yajema baya iya yin komai sai dai ya dawo gida.kawai sai ya barwa yaransa na shagunansa suke cigaba da kula da kayan domin suna da amana

Haka sukayi ta rainon cikinsu har yayi kwari sannan mannir yaci gaba da zuwa kasuwa, ita kuma aka dakko mata yarinya mai suna karima, dan tana tayata ayyukan gida da kuma dauke mata kewa.

A wata ranar juma,a ne aysha ta fara jin nakuda tana jin ciwon kadan kadan har ta dawo daga ya lafa sai ya kara tasowa.lokacin mannir ya tafi gidansu daga can zasu wuce masallaci da abbansa.haka tayi ta daurewa har taji ta kasa daurewar dan sosai ciwon yake tasowa.ta dauki waya ta kira mannir ya dauka kenan sai wani ciwo ya taso mata aikwa ta kwalla wani kara ta saki wayar sai ga karima da gudu daga kitchen.
Shima mannir dake zaune a falon hajja abu da Sauri ya tashi mamanshi tana kiranshi Amma hankalinshi ya tafi ga aysha ,haka hajja abu ta bishi a baya sai tararshi tayi zai tasa motar tayi sauri ta shiga suka tafi gidan mannir din.
Sun sameta ba yadda take dan duk ta galabaita, suka kamata da hajja abu da karima suka sakata a mota ,suka tafi kaita wani private hospital dake kusa dasu na doctor munib nan da nan aka karbeta aka shiga da ita.ba,afi 40 minutes da shiga da itaba wata nurse ta fito rana musu albishir da karuwar da suka samu Allah ya sauketa lpy ta sinbulo kyakykyawan danta kamar balarabe.daga asibitin da aka sallamosu gida suka dawo murna wurin iyaye da yan uwa da abokan arziki abin ba,a cewa komai .musamman mannir da bakinsa yaki rufuwa sai washe baki yake kamar gonar auduga.

Ranar suna yaro yaci sunan abubakar (MUSADDIQ).ansha shagali sosai da sosai dan naira=ص=ش=ض har kuka tayi>(>*




COMMENT
'
'
'
SHARE>>>>



Story & written by


MAMAN AFRAH


PAge 55_56



_Bismillahir_ rahmanir rahim


Innama amruhu iza arada shai, an, an yakula lahu kun faya kun.




Sai wajen yamma sannan suka dawo daga wuraren aiyukansu, su lantana sai da suka je wani katon fili inda zasu daure rakuman nan, dan suna da yawa gashi sunsha wahala sosai dan ma dai rakuman ba wani fada bane dasu, amma gaskia aikin kiwon rakuman akwai wahala dan inda zasu kai rakuman suyi kiwon akwai nisa sosai dan can cikin gidan ne sosai.dan har sai mutum ya dauka yabar gidanne dan qungurmin dajine ga tafiya ,ga kora rakuma abin ba,a cewa komai haka suka kai har karfe uku na yamma sannan sukaji wani karan karfe da ake bugawa wanda duk inda mutum yake a cikin gidan sai yaji karan karfen.dan shi ake bugawa idan lokacin dawowarsu yayi.

Sannan wani abin ma sai dai wanda ya gani, saboda wannan shine karo na farko da suka fara fita kiwon dan haka sukafi jigata sosai.kowane nau,in dabba da akwai bangaren da ake zuwa domin kiwonsu,gashi dajin akwai abin tsoro tartare dashi ga macizai dan a iya yau su lantana sai da suka kashe macizai guda uku manya manya, dan na ukun rakiya taje ta koro wani rakumi da ya ratse ta dawo ,ta hangoshi yana tafiya sululu ya nufi inda su lantana take aikwa ta kwalla kara tare da kiran sunan lantana tana shaida mata ga miciji nan a bayanta.ai lantana najin haka ta fita a guje. to sai wani rakumi daya tsorata da ihun da suka kwasa su duka ukun ,ya fita da gudu,cikin ikon Allah ya take kan micijin=
, su kuma suka karasa shi mis har lahira.


Lokacin da suka fito daga kewayen da ake ajiye rakuman,suka jero su uku lantana,rakiya da kuma amina.suna tafiya suna jan kafa alamar akwai gajiya tattare dasu,musamman ma lantana dan tafi kowa nuna alamar gajiya.
" nida nake rayuwa ma a ruga ,wannan aiki yaban wahala dan Allah balle kuda kuke rayuwa a birni"cewar lantana murya kamar an shake mata makogwaro.
"Hmmmm kedai bari lantana ai abin ba,a cewa komai,duk halin da bawa ya tsinci kansa sai dai godiyar Allah,amma ko a mafarki ban taba zato zanyi irin wannan rayuwar ba"rakiya ta fada idonta cike da kwalla=".
"Nifa gani nake duk halin da muka samu kanmu, mune muka janyowa kanmu,dan da mun zauna a gidajenmu da duk haka bata same Mu ba. Amina ta karashe maganar da iya gskiarta dan ita bata dorawa kowa laifin tafi ganin laifinsu na shegen son kudi da suka baro kasarsu suka taho wata kasa daban.in bandama canjin rayuwa ita wlh ko gaba da gaba bata taba yi da rakumi ba ,balle ya zama abin kiwonta.
"Allah sawaqe to ya bamu iko"rakiya ta fada dai dai sunzo dab da wata kwana da zata kaisu bangaren da suke zaune .
"Kai daga ina kuke? Ko kuma ince meye aikinku?"wata mata katuwa da duk ta girmesu a haife ta jero musu wannan tambayoyin lokaci daya.
"Haba baiwar Allah daga haduwa dake yanzu zaki wani tambayemu ,sai kace wacce kika ajjemu,kowa a gidan nan aiki yake kuma tunda an buga karfe mai nuna alamar lokacin

Please Login or Register in order to submit comment