Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yace " ku ajjeni a waje zafi nakeji "dan har lokacin gumi yake,sannan a lokaci guda jikinsa na karkarwa.

"Hashimu" ya fada a lokacin da wani farin abu kamar kumfa ya fito daga bakinshi,sai yasa hannunshi ya goge "ka kiramin inna"ya fada hawaye na zuba daga idanunsa.wanda koshi bazai ce yasan da zuwan hawayen ba,kawai yaji suna bin kumatunsa.amma ba tasu yake ba,innarsa yakeso ya gani "a bari sai da safe yanzu darene kar a tada mata hankali" hashimu ya fada shima yana hawayen,wanda tunda ya fara daga kofar gida har yanzu be tsaya ba "ita kadai gareni sai sadiya,ka kirawota ita nakeson gani " ya fada yana mai riko hannun hashimu "ka kirawo masa ita tunda yanason ganinta"mai machine din ya fada.

"Toh"ya fada kamar bayason zuwa dan har baiso a fadi silar abin saboda yasan dole sunansa zai fito.wato ace "fada ake da hashimu shine ya shigar masa" dan kowa yasan tasi,u mutum ne marar hayaniya bashi da abokin fada.

"Lpy"sukaji muryar matar hashimun tana tambaya dan bacci take, takejin magana sama sama, shine ta fito aikwa tayi tozali da tasi,u kwance cikin wannan halin."ni ne sila"hashimu ya fada ai nan take sadiya ta tsaya da kukan da take dan tunaninta hashimun ne ya masa raunin kan nasa, dan taga kan da me ma machine dn nan ya haska.sai kawai ya juya domin fita daga gidan,zuwa kirawo inna sarai.". Allah kara afuwa "mai machine din nan ya fada yana bin bayan hashimu, " amin nagode" tasi,u ya fada har lokacin wannan farar kumfar tana fitowa daga bakinsa. "Na wuce Allah kara afuwa"ya Veda hashimu lokacin da suka fito kofar gida yana kokarin hawa machine din, "malam ga Wannan mun gode sosai da taimako"hashimu ya fada yana mika masa dari biyu "wlh ka barshi Allah bashi lpy,kuma Allah ya saka masa" "mun gode" hashimu ya fada yana tafiya dan zuwa gidan inna.

shi kuma mai machine ya kama hanyar rugarsu,yana jimamin abinda ya faru.a bangare guda kuma yana ganin sai kwana ne zai tashi marar lapiyar.domin kuwa akwai wani kawunsu da irin haka ta sameshi,amma shi dutsine aka kwala masa kafin ace sun nemi machina sun tafi baban asibiti a wani gari,har ya fara fidda kumfar nan daga baki.suna zuwa likitan yace ai kwalkwalwarsa ce aka daka dan Wannan kumfar daga kwalkwalwar kanshi yake fitowa,kafin azo ga bashi taimakon gaggawa rai yayi halinsa.

ya dade tsaye a kofar gidan yana tunanin shiga,kafin daga bisani yayi shahada ya shiga.kafin yakai ga yin sallama sai ganin inna yayi gabansa,tana kuka ta nufoshi tana tambayarsa me ya sameshi,domin nafarki tayi yana cikin wani mayuwacin hali.Shine fa ta kasa komawa bacci take kuka tana additional,,a Allah yasa ba wani abinne ya sameshi ba." Bashi lpy ne, shine yace in kiraki "ai kafin me wannan inna ta ware dankwalin kanta irin na tsofaffi ta yafa sun fito suna sauri.


Lokacin da suka isa gidan har tasi,u ya fara fita hayyacinsa "wayyo babangida me ya sameka"ta fada tana kara karfin kukanta dan ganin halin da yake ciki, "innaa" ya fada kamar an fisgo maganar daga bakinshi "gani babangida ko baka ganina"ta mika hannu ta kamo nasa hannun." Inna ga ...sadi..ya nan nasan ...zaki ku...la da ita da abin....da za...ta haifa"ya fada yana mai ciccira kalmomin domin tari daya sarkeshi da kuma kumfarnan data yawaita fitowa sosai,danma sadiya tana goge masa da dankwali."duk da na...san ke...ma baki....da mataimaki....sai tarin ya kuma sarkeshi kumfa mai yawa ta ambulo,sai yaci gaba,sai Allah" inna ga abin...da sa...di...ya za...ta..hai...fa sai idon ya kafe lunfashin ya fara jayuwa da kyar,cikin yana sama yana kasa har rai yayi halinsa....



Allah sarki rai bakon dny=- Allah jikan mahaifanmu Amin.




Story & writing by

MOM MASHKUR

Page 17_18


A lokacin inna Sarai ji take kamar a lokacin abin ke faruwa,tuno da mutuwar babangida da tayi, duk da cewa kullum mutuwar tana ranta musaman ganin MARYAMU a tare da ita ko in tana kukan yunwa ta rasa abinda zata bata.

Ita bata da nonon da zata bata,nonon ba zuwa zaiyi ba sannan ita ba kiwo take ba bare ta bata nonon akuya,dan yanzu ko kaza bata da ita ,sai dai take bin gidan mutane kamar mai bara, tana rokon su taimaka mata da nonon da zata bata. amma saboda rashin imani tana ganin dabbobin amma masu su suce babu,ko kuma suce ba nonon jijin dabbobin saboda suna zargin cewa ita yarinyar ita ta kashe ubanta,saboda jahilci wai saboda haihuwarta ubanta ya mutu sannan mahifiyarta sadiya ma ta mutu.



daman salamatu makociyarta ke taimaka mata da nonon tana baiwa MARYAMU amma mai gidanta ya hana ta saboda kar idan yarinyar ta kashe inna sarai ta dawo kansu saboda makusantanta take kashewa, a cewarsu ta kashe ubanta tasi,u ta kashe uwarta sadiya wanda kuma ba haka bane kawai shaci fadine da kuma jahilci da yake damunsu.

Dan tun ranar da tasi,u ya rasu take ganin taskun rayuwa,domin kuwa duk da kukan nan da hashimu yake da kuma shine sanadin da aka kwala masa sanda,hakan bai hanasu tashi ba washe gari daga gidan dashi da matarsa, da yarsa, cewarsu kar yayi fatalwa yazo musu cikin dare.

dan wanda zai masa wanka ma rasawa akayi,sai inna saratu da sadiya suka masa ita jikin tsufa ita da tsohon ciki dan lokacin cikinta wata takwas dan yan kwanaki. Da kuka inna ta samu hashimu tace ya taimaka musu susa masa likkafani amma sai ki yayi har sai data tafi gidan liman din sannan shima yazo ya taimaka shima dan yana tsoron kar mutane su daina ganin girmansa dan bawani ilimine dashi ba.haka dae yan tsirarrun mutane suka sallaceshi a kaishi gidanshi na gskia.

anan bayan gidan aka binneshi gaba da gidan, kadan tunda daman gona ce ba wani gari bane ruga ce,dan ko mahaifinsa ma anan aka binneshi.

Inna sarai tayi kukanta sosai a gindin bishiyar nan ta share hawayenta,ta dauki MARYAMU ta goyata wacce har wannan lokacin baccinta take bata san me akeyi ba.ta dauki bakar ledarta taci gaba da tafiya.tayi tafiya sosai ta fara hango bukkoki har ta fara jin kukan jaki,da na shanu sauran dabbobi.sai tabi wata karamar hanya da zata sadata da gidan.

Tun kafin takai gayin sallama,wani katon kare ya tukarota yana haushi,sai ta fara sallama "assalamu alaikum "ga wani yaro ya fito daga daki,zai kai kimanin shekaru shida "magana"yaron yace yana korar Karen. "yahuza ana gida" inna sarai ta fada cikin fulatanci, " eh inna" "to madallah" "ina mutan gidan suke ta fada "innata ta tafi rafi daukan ruwa,innar auwalu kuma ta tafi gari nika


Story & writing by

MOM MASHKUR


Page 19_20


Comment dinku shi zai bani karfin gwiwa kuma hakan zai nuna kuna biye dani nagodee.



Innar auwalu kishiyar innarsa,wato yayar sadiya, kenan wacce suke uwa daya uba daya,sai autansu inusa wanda mahaifiyarsu ta rasu garin haihuwarsa.
Inna sarai ta karasa cikin gidan taga wata tsohuwar fanteka a gindin murhu,ta dauka ta zauna tace "bari in zauna in jira lantanar "shi dai yahuza baiyi magana ba,ya dore wasanshi.


Tana nan zaune har MARYAMU ta motsa alamar tanaso ta tashi daga barcin da takeyi, nan inna larai ta shiga jijjigata cikin ikon Allah ta koma barcin.dan bataso ta tashi ta shanye sauran madarar dan batasan yau ma da yadda lantana zata karbi zuwan nasu ba.can sai ga lantana ta taho dauke da tulun ruwa akanta,sannan da goyon yaro dan kimanin wata hudu a bayanta.sai da inna ta hango goyon yaron take kara jinjina kokari irin na sadiya,lokacin da lantana. ta haifi yaron haka sadiya zata taho tun daga rugar marayo zuwa nan rugar hardo sani.tunda lantana ta haihu kullum sai sadiya tazo wajenta a cewarta basu da uwa sai kansu dole ta taimakawa and yar uwarta kar tayi maraicin uwa tunda ita kadaice yar uwarta.haka zata taho da kafa ta koma da kafa danma tasi,u ya hanata zama amma cewa tayi zaman jego zata mata,shikwa yace itama tana fama da kanta dan lokacin ma cikinta yafi wata shida,haka ta hada kudin da take tarawa idan tayi sana,a ta auni barkono da daddawa da dai sauran kayan hada yaji ta mata dinki kala biyu ta sayi rigunan jariri ta hada takai mata.da takalmi dan madina.

"Hmmm duniya kenan"inna sarai ta fada tana sauke nannauyar ajiyar zuciya. "Salamma alaikum"lantana ta fada lokacin da ta karaso cikin gidan ai tana ganin inna sarai (wato sirikar yar uwarta sadiya) sai ta hade rai ta yiwa inna sarai wani irin kallon wulakanci dan tasan zancen gizo bai wuce na koki.wato magana ce akan talle (ana nufin marainiya),maimakon lantana ta yiwa inna sarai magana sai ta wuce inda randunan su suke ta ajje tulun ruwan data dauko,sannan ta bude randa ta dauki wani Katon kofi ta ciko da ruwa a cikin randa,,ni na daukama inna. sarai zata baiwa,amma me sai naga ta kafa kai sai data shanye ta tass ta ajje kofin takwa saki katuwar gyatsa ji kake=# sai kuma ta turo daurin dankwalinta gaban goshi,ta tsaya tana karewa inna kallo ita jaririyar nan data goyo wadda ita lantana bata san ma sunan da aka sakawa yarinya ba....


"Lantana inna sarai ta kira sunanta cikin sanyin jiki,domin taga abin bana kare bane,duk da ta saba da wulakancin lantana amma ganin yau bata da niyyar mata magana yasa abin yafi kona mata rai.

Ayi hakuri da wannan>ؚB
Story & writing by


MOM MASHKUR


Page 21_22


" Ina jinki" ta fada cikin yatsina fuska "yanzu lantana in dakko hanya tun daga rugar marayo ko baki sanni ba na ratso gidan nan aikya mini magana, ko ruwan da zan sha bazaki iya bani ba, ai bakonka annabinka. Inna sarai ta fada da alama hakan na mata ciwo a ranta dan da ganin fuskarta zaka ga alamar hakan. " wai menene zakizo har gidana kina jifana da maganganu,da kike maganar ban baki ruwa ba yaushe na shigo gidan ma ko so kike in kafa rawar jiki kamar naga uwata" lantana ta fada tana wani zazzara ido kamar tana magana da sa,arta " ni ba haka nake nufi ba"cewar inna dan kawai abar maganar kar taje cin mutuncin yakai ga zagi dan da alamar lantana zata iya fada mata komai

" ai ba maganar da za,a barta ta wuce haka nan bace,har cewa kikai wai kamar ban sanki ba to da allah na tuba a ina na sanki,dama dalilin sadiya ne kuma ta mutu,kinga abinda ya hada ya raba kenan"ta fada tana wani daga kai sama. " yanzu lantana ni kike gayawa wadan nan maganganu,koba komai ai na haifeki "uwata ta dade da mutuwa" ta fada tana dakko kara da wani guntun icce zata saka a murhu ta hada wuta,domin dafa dambu da zatayi na abincin rana, dan da dare innar auwalu ce zatayi tuwo shisa ma ta tafi gari kai nikan tuwo.

Dan itama suna zaman hakuri ne daga ita har me gidan,dan lantana bata da kirki inda halinsu yasha banban da yar uwarta sadiya kenan.sadiya akwai kirki ladabi biyayya ga uwa uba girmama na gaba.sannan kamarsu daya da lantana amma ita sadiya fara ce sosai,shisa MARYAMU farin mahaifiyarta ta dakko amma kamar su daya da mahaifinta tasi,u.

"Allah jikanta" inji inna sarai " kuma naji mai rabawa ta raba, amma kinsan ai yar uwarki ta bar jaririyar data haifa ko ita dinma baki da hadi da ita" "naga kema jikarki ce diyar danki 'lantana ta fada tana liqa rigana (madambaci) "Allah ya rayata take kai mana niqa idan tazo nan rugar da yawo"ta fada tana murmushin mugunta dan ta fadi abinda ke ranta,kuma daman ta matsu azo wurin dan tasan meya kawo innar wurinta tunda ba Wannan ne karo na farko data dakko talle (marainiya) ta kawo mata ita ba,domin ta karbeta ta hada da danta ta shayarsu dasu.

Wancen lokacin ma ta mata wulakanci son ranta yadda ko a hanya batajin inna sarai zata mata magana ba,amma saboda rashin zuciya irin na matar yau ma shine ta dawo mata da yarinyar. " wai kuwa lantana kina da hankali" cewar inna sarai " siyamin in kina da kudi" lantana tace tana dora tukunyarta ta dambu akan wuta."Allah kyauta"inna sarai ta fada ganin abin bana kare bane.


Story & writing by


MOM MASHKUR

Page 23_24


JIN JINA DA GODIYA GAREKU

DUNIYAR KARATU GROUP
MAMAN OSMAN NOVEL GROUP
RAYUWAR MARYAMU FANS
JEDDAH ALIYU FANS
SON BANZA ASSO OF NIGERIA
ZEE AMMAN KHADY GROUP
TASKAR MRS OMAR
QUEEN MEEMI NOVEL GROUP MUSAMMAN WASU MEMBERS NA GROUP DIN
MOM MUHSINA,HADIZA AMINU,MISS HUSNA,MISS HEEDA,KULCHUMI,MUFEEDA,OUM HYDAR,
MAMAN SHURAIM HJY FAUZY,AMRAH,MMN WALIDA,SAI FRETTY MRS ZDEEN
DA DAI SAURAN GROUP S NGD DA KAUNA.


 yanzu dai dan girman Allah ki duba maganar dana zo miki da ita lantana" Inna sarai ta fada tana karya murya dan lantanar taji tausayin yarinyar ta karbeta."ina jinki inna duk da nasan zancen gizo bai wuce na koki " ta fada tana iza wutar murhun data ga tana hayaki " hmmn magana ce akan MARYAMU " to to, to"ta fada tana dariya "ai sai kiyi bayani inna wlh ni duk tunani na zancen talle(marainiya)ce shisa nake ta Wannan fadan ba dan komai ba, kinsan nima shayarwar nan nake shi yasa wlh amma ai diyar sadiya yata ce badan goyon da nake ba ni zan dauketa"ta fada tana samun guri ta zauna a kasa kusa da inna " yahuza ajje kayan wasan naka ka dakkowa inna ruwa a randa" ta fada tana sakko dan bayanta daya tashi yana kuka ta fiddo nono ta saka masa a baki.

" Gashi "yahuza ya fada yana miko mata ruwan daya dakko a kofi.ta karba tana mikawa inna sarai wacce har lokacin ta kasa magana, sai bakinta data bari a sake saboda mamakin abin da lantanar keyi.inna sarai ta karbi ruwan ta ajje akan wani dutsi dake gefe "kina cewa ba,a baki ruwa ba kuma an baki kn ajje"cewar lantana "umm yanzu ba ruwanne a gabana ba, maganar da zamuyi tafi muhimmanci" inna ta fada tana kunce MARYAMU daga bayanta saboda kuka da ta fara,domin ta tashi daga bacci "talle an tashi "inji lantana ta fada yayin da take kokarin zaunar da yaron dan yana zama amma be wani ninaba, "yi shiru MARYAMU kinji ongo"cewar inna sarai yayin da take kokarin bata fida mai madara dan bata na
ma da yawa ta kusan shanyeta dazu data bata,daman a hanyarsu ta tahowa taga wani saurayi yana kiwo ta rokeshi daya sammata nono zata baiwa jaririya,shine ya karbi fidar ya tatsa mata.dan koda safe data rasa abinda zata bata sai koko ta zubawa ruwa yadan tsinke ta bata tasha,shine tausayinta ya kamata ta dakkota ta kawowa lantana ko zata tausaya mata ta karbeta


Dan wadan nan mutane na rugarsu bata ga ranar da zasu dena nuna musu kyama ba,saboda MARYAMU dan takai ta kawo yanzu ko barka ko biki ba,a gayyatar ta kai ko haihuwa akayi idan taje barka ba,a bata yaro kai koda barka ta bayar ba,a karbar abin hannunta.dan ana gudun MARYAMU karta kashe su wai ta kashe iyayenta sabida farar kafarta.hatta kayan miyar da inna sarai ke saidawa da manja an daina siya saboda MARYAMU yanzu abinda baiwa MARYAMU ma neman gagararta yake, bare wanda zata sanya a cikinta."wai tukunnama wacece MARYAMUN naji kin kira talle da MARYAMU"lantana ta fada tana wani zara ido kamar wacce ta yiwa sarki karya



'
'
Story & writing by

MOM MASHKUR


Page 25 _26


WANNAN SHAFIN NAKI NE =؋MARYAM IBRAHIM=؋ TA GROUP DIN RAYUWAR MARYAMU, NAGODE SOSAI DA KULAWA.GA SHAFIN DA KIKE NEMA KISHA SHA,ANINKI.>p>p>p




"To da ke tunaninki wacece MARYAMU" inna sarai ta fada tana kallonta da kuma son ta gano manufarta.
" wai kina nufin Wannan yarinyar ce MARYAMUN da kika ce zamuyi maganarta, dama MARYAMU aka sakawa yar sadiya,ni wlh na dauka wata MARYAMU babbace zamuyi wata magana,dan na daukama ko kuli kulina zata sara" lantana ta fada cikinta mamaki daya baibaye mata zuciya.
"Kuli kuli kuma lantana?" Inji inna sarai "eh mana"lantana ta fada. "Kuma a rasa wanda zai kawo miki abokin cinikin kuli kuli sai ni"inna sarai ta fada tana nuna kanta da yatsa.
"Yo idan Allah yasoka da ciniki duk inda yake ai sai yazo gareka"cewar lantana cikin fada fada dan yanzu ta gama gane inna sarai magana tazo mata da ita akan talle (marainiya) wato MARYAMU.



"Yanzu dai inajinki da wacce kika zo"lantana ta fada tare da mikewa domin sauke dambun data dora ya nuna."to ai sai kin dawo kin zauna zamuyi maganar kokwa" inna sarai ta ce yayinda da take ta jijjiga MARYAMU dake kuka,dan kukan na taba zuciyar inna sarai saboda tasan koshine batayi da madarar data bata ba,shisa take faman kuka."zaki iya maganarki ni dambun nan ma zan karkasa,dan yunwa nake ji kamar me.cewar lantana tana jera Kwanikan da zata kasa dambu.

"Lantana dago ki kalleni dan Allah"
Inna sarai ta fada lokacin da hawayen halin da suka samu kansu ita da marainiyar Allah(MARYAMU) yake ita rashin danta tasi,u ne ya sanyata a halin da take ciki,da yana raye tabbas bamai wulakanta ta=- haka kamar yadda mutanen rugarsu suke mata da kuma lantana dan sunga bata da kowa=F
@&
Ita kuma MARYAMU rashin iyaye,musamman mahaifiyarta sadiya,da sadiya tana raye lallai ba mai neman nonon lantana, bare aje ga bata na akuya." Ya ilahi" me ya kawo kuka kuma kamar gidan mutuwa inna"lantana ta fada baki cike da dambun data afa a baki wai nan tabin manda akayi= shine aka cika hannu akaci "haba lantana sai yaushe ne zaki tausayawa yarinyar nan ki karbeta,ni wlh ko da bazaki iya shayar da ita ba zuwa a yayeta ba,to dan Allah ko wata takwas ne ki barta tayi,nasan zuwa Wannan lokacin tana cin abinci,tana shan koko.kuma nasan zuwa lokacin na samu yadda zany,wlh ko rugar tamu sai in bari saboda RAYUWAR MARYAMU".

"Sannan na samu inda zan koma,na samu tsayayyar sana,a wacce zan iya siya mata koda madarar bature ta gwangwani ba ta akuya ba,wacce ko roka nayi ba,a bani ke koda siya zanyi wlh bame saidamina dan yau ma koko na karawa ruwa na bata " ta fada tana share hawayenta da gefen gyalenta.

Wanda zuwa lokacin jikin lantana ya danyi sanyi,amma ba sosai ba dan ba alamar saduda a tare da ita."nifa inna duk abin nan da kike ba,aje ga haka ba,meye kuka"lantana ta dawo kusan inna Sarai dauke da dan chaina, wanda ta zuba mata danbu a ciki."abin yama wuce haka lantana ya kikeso inyi da yarinyar nan idan tana kuka rasa me zan mata nake ko cikin dare haka zatayi ta kuka kuma wlh ba komai ke damunta ba sai yunwa sai dai nima intayin kuka=-.

"Da ace bana shayarwa zan dauketa in shayar da ita,amma nima goyo nake to ya kikeso inyi da nawa dan" cewar lantana" ni wlh bawai sai kin bata nonanki ba,tunda kina ganin bazaki iya shayar dasu su biyu ba,to ita kike na akuya tunda kuna da kiwo gasu nan,amma ni acan bana samu wlh lantana" inna sarai ta fada

"Bazaki fahimta ba nifa bazan karbeta ba na gaya miki tun ran sadakar ukun mutuwar sadiya,bayan nan ma zuwanki nawa gidan nan wai akan me zakina zuwa har gidana jina daga mun hankali,duk akan jaririya bandama gudun wahala da kikeyi mezai sanya kike neman kai da jikar da ita tilo kike da ita"
"Mubar maganar nan,kuma har duniya ta nade bazan kara kawo MARYAMU wurinki da sunan ki shayar da iyaba,nima ina zuwa ne dan nasan bata da uwar data fiki,daman tunda mahaifinki ya tsawatar miki akan ki karbeta kika ki kuma yace bashi bake,amma hakan besa kin karbeta ba ai banga wanda zaisa ki karbeta ba tunda ke baki da imani"

"Anki a karbetan ni naga mata da karfin hali wlh, kamar ni na kashe mata uwar zaki damu da sai na bata no no"

Bata bukata ki rike kayanki,abu guda na sani shine da ace kece kika mutu kika bar jaririya wlh nasan sadiya sai ta shayar da abinda kika bari koda kuwa goyon tagwaye take,kuma sai ta nunawa yaron so da kulawa fiye da wanda zata nunawa yayanta"inna sarai ta fada tana goya MARYAMU dan tayi barci saboda kukan da tayi.
"Wannan kuma fadarki ce" lantana ta fada tana daukan danta dake kuka,wanda ta kwantar a kasa kan dangoyo .
"Zo yaka,yo kake kuka ga gyatumarka a kusa kai ba maraya ba"ta fada da gayya dan ta konawa inna sarai rai."gashi innar rugar marayo ki bata"
yahuza ne yake mikawa inna sarai madara a cikin wani koko,yayin da sarai ranta yakai kololuwar tashi ta sunkuya daukan ledar kayan MARYAMU.




COMMENTS DINKU SHINE KWARIN GWIWAR YAWAN TYPING NA



Story & written by



MOM MASHKUR


Page 27_28


Jinjinar ban girma gareki
=M=M=M=M=M=M=M=M
maman muhibba
marubuciyar DASHEN ALLAH na gode sosai da qauna Allah raya yara=O



" ki karba ki bata innar rugar marayo" ta tsinkayi muryar yahuza yana cigaba da mata magana, da kamar bazata kalleshi ba,sai kuma ta waiwaya ta ganshi yana miko mata karamin koko mai madara a ciki.nan take taji idanunta yana cikowa da hawaye ganin yaro karami yasan abinda ya kamata sabanin mahaifiyarsa.
"Yahuza ka je ka ajje min zanje in dawo tunda kaga yanzu MARYAMUN tayi bacci,idan na dawo zan karba in bata ta sha" fada ta tana mai shafa kan yaron tare da masa murmushin yake don kawai ta kara mishi kwarin gwiwa,saboda wataran dan shi yaro komai yana ajjewane a kwalkwalwarsa.matukar ta gwasileshi to wataran ma zai ji shayin taimakawa wani,dan gudun kar a mishi abinda inna sarai ta mishi.

"To jarababbe me shegen iyayi kinga Wannan da mace ne wlh da kissa da kisisinar da zaiyi sai Allah kiyaye" lantana ta fada tana munashi da yatsa=Ftare da aika mishi da harara tamkar idanunta zasu fado kasa=@.

Ita dai inna sarai bata kara bi takan taba ta juya domin ficewa daga gidan, sai ga innar auwalu ta taho kanta dauke da kwarya mai nika a ciki.
"Assalamu alaikum " tace tana nufo tsakar gidan amma lantana ko ta amsa mata sallamar,itama inna sarai da hankalinta yayi gaba bata bi takan innar auwalu ba."inna ina wuni"innar auwalu ta durkusa tana gaisheta "lpy"kawai tace tana mai cigaba da tafiya abinta, da sauri innar auwalu ta ajje kwaryar garin tabi inna sarai tana kiranta. " inna tsaya mana dan Allah" cewar innar auwalu tana mai sassarfa dan ta taddo inna Sarai,"gulma ajali in ba,ayi ba a mutu" lantana ke fada da karfi yadda innar auwalu zata jiyota.

"Bani da lokacinki, sakarai wacce bata san inda ke mata ciwo ba " innar auwalu tace tana cigaba da tafiya,har tazo inda inna sarai ta tsaya.
"Haba inna ya zaki tafi da ranar nan kamar wanda ake korarki" "kawai dai akwai abinda zanyi a gida shi yasa"
" A ah inna ki bari rana ta danyi sanyi mana,duo da nasan ba dan zakiyi komai a gida zaki yafi ba,sai dan lantana ce ta miki abinda ta saba,amma kiyi hakuri wataran sai Labari" "hmmm yar nan kenan labarin ma ba,a jiba wataran"inna sarai tace tana kulle ledar hannunta mai kayan MARYAMU a ciki. "Dan Allah inna ki daina dakko yar nan kina zuwa tana wulakantaku wlh lantana ba zata karbi tallen nan ba (marainiya) da zata karbeta da ta karbeta tun dadewa.
"Ba komai insha Allah daman bazan kara kawota ba,da sunan ta bata nono,tunda bazan rabata da ita ba dole idan ta girma wataran ta nemeta tunda ba wasu yan uwan gareta ba,daga kakanta na wajen uwa sai ko inusa kanin mahaifiyarta,dan ni yar uwata ba,a sakata a layi ba dan mutuwar nan ma sai ran uku taje tamin gaisuwa yadda wasu keyi su tafi itama haka yazo a machine,tamin gaisuwar wai mai machine yana jiranta,ta tafi har yau kwa ban sake ganinta ba".

"Kiyi hakuri Inna komai tsanani yana tare da sauki,komai zai wuce insha Allah,zai

Please Login or Register in order to submit comment