Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

korar shaidan, dan ta tabbata shine yake son yayi tasiri akanta.yana son ya sanya gaba ne kawai a tsakaninsu ,domin lallai shaidan makiyinmu ne duk inda yaga wani abu na alkairi zai samemu to tabbas sai yayi yadda ya bata mana zukatanmu Allah mana tsari da shaidan ameen.

Haka ta tattare buhun ta dauko daron alkamar taga har dabobin sun dan tsaga mata shi, ta dauke ta gaggara inda suka zubar.
"Assalamu alaikum" wani yake rafka sallama a kofar gidan inna sarai.
"Wa alaikumus salam"inna sarai ta fada tana nufo zauren.
"Wake magana"
"Me baro ne, ga wannan kayan inji alhaji mutari yace a kawo"
"Masha Allah, shigo min dasu ciki"cewar inna sarai fuskarta da yalwataccen murmushin murna, ta juya domin komawa cikin gidan.

"To" yace yana mai dakko kayan, haka ya dakkosu gaba daya ya ajje mata su a wuri daya.
"Sai an jima"ya fada yana karkade kuran hannunsa.
"Tsaya ina zuwa" tace tana shiga daki, ta bude inda take ajiye kudi ta dakko dari 2 ta bashi.
"ga tukuici kuma ka kara min godiya allah saka masa da alkairi"
"Amma na gode sosai wlh, kuma zaiji in Allah ya yarda"yasa hannu biyu ya karba yana kara godiya.

Bayan fitarshi ta bubbude kayan tana gani, tana yiwa Allah mai iko da hikima godiya, domin shine ya bata.bayan ta gama ganin kayan sai ta dakko tsamiya take gyarwa domin ta musu kunu sai suci da biredi da daddare, sayi tuwon gobe idan Allah ya Kaimu.
"Assalamu alaikum"wani dan matashi ya yi sallama a gidan inna sarai.
"Wa alaikumus salam"shigo mana.
"A bani gyada kwano biyar"
"To maza dakko kwanan awon ka ganshi can akan turmi"
"Gashi"
"Yawwah bude buhun ka rike inke auna maka"haka ya rike mata ta auna masa kwano biyar tana cika mudu sosai, dan bayan ta gama aunawa ma sai da ta tsakura ta kara masa.
"Innar MARYAMU shi yasa mutane suke son zuwa wurinki awo, domin akwai cika kwano bakya tauye mudu ko kadan"ya fada yana murmushi.
"Hakan shine dai dai ai, tunda idan ka rage ma kanka ka daukarwa nauyi dan hakkin wani ne ka rage ,sannan babu kyau rage mudu"
Kedai inna sarai da kike tsoron Allah, amma gashi nan mutane da dama suna tauye mudu a awonsu na kayan abinci"
"Allah yasa suma su gane,domin Allah shine mai shiryarwa ,idan ya shiryar babu mai batarwa, idan ya batar kuma babu mai shiryarwa "
"Amin dn alfarmar annabi muhammad (S.A.W)'
"S.A.W." inna sarai ta fada tana shafa hannayenta duk biyun a fuskarta.
"Ga canjinka "
"Yawwa daman akwai wani canjin ,dana zo na auni kwano uku rannan"
"Ni kake bi canji ,Subhanallah amma ban sani ba wlh"
"Eh bakya nan MARYAMU ce ta auna mini,shine na biyota naira 30 ba wasu masu yawa bane"
"Haba ni nayi mamaki da kace kana bina bashi, dan bana barin kudin mutane akaina ,kuma ba talatin ba ko naira biyar ce ai bashi ce, kuma banda MARYAMU abin ta fada mini shine ta barni da nauyi akaina?"
"Yo yanzu ba sai ki biya ba,bafa wani abu akace ba inna sarai"
"Dan nan kasan bashi kwa kasan hadarin dake cikin cin bashi kwa?,to lokacin manzon Allah (s.a .w) idan mutum ya mutu in za,a sallaci gawarsa sai annabi (s.a.w) ya tambayi mutane shin ana binshi bashi? Idan suka ce 'eh' ana binsa to bazai masa sallah ba, sai yace da mutane ku masa sallah, idan kuma suka ce a,a ba,a binsa to annabi (s.a .w) zai masa sallah ,kaga kenan wannan kadai ya isa ya nuna maka masifar dake cikin bashi, Allah bamu ikon sauke nauyin mutane na bashi akanmu domin Allah baya gafarta zunuban wani akan wani"
"Amin inna sarai gskia naji dadin maganganunki Allah biyaki ,dan yanzu zanje in sauke basukan da suke kaina wanda bani ma da niyyar saukesu"
"Amin ga talatin dinka"
"Yawwa sai anjima to"
"Mu jima da yawa ka gaishe da mutan gidanku"
"Zasuji"





"""""""""""""""'''''''''
Dan shima mannir gaba daya hankalinshi yana kan amarya binta dake ta bada kamshi ,ga wani uban kwalli na magani da aka bankada a ido mai suna DAUKE HANKALIN MIJI YA DAWO KANKI>z bayan ya gabatar da uwargida a wurin amarya, sai ya gabatar da amarya da diyarta muhibba a wurin uwargida.sosai aysha ta dake zuciyarta ta amshi amarya hannu bibiyu, dan har da cewa muhibba tazo su kwana a dakinta, aikwa amarya da duk zuciyarta ya cika da kunci ganin mai gidan nasu yana nuna kulawa, ba tsangwamawa a wurin uwargidan, sannan itama bata nuna damuwa ko a fuskarta yasa ta cewa la bata yarda da kowa tana mai fakar idon mannir din ta dokawa aysha harara a ranta tana ayyana indai kissa da kisisina ne gidansu kika zo.domin daman binta ta girmi aysha amma kuma bata da wayewa irin na ayshan, dan iya secondary school kawai tayi.dan haka sai maganin tari tayi amfani dashi wajen sanya muhibba barci sukaci amarcin su.





*BAYAN* *SHEKARA* *BIYU
*

Har zuwa wannan lokacin amarya bata samu ciki ba a gidan mannir, bare ayi zancen haihuwa.ita kuma aysha ta haifi danta namiji mai suna abdurrahman suna kiranshi da boy, dan har ta yayeshi ma.A wannan lokacin ne kuma wata asara ta samu mannir na wasu kaya da yayi odarsu daga cairo jirgin ya kama da wuta mutane duk suka rasa rayukansu cikikwa harda amintaccen yaronsa da yaje saro masa kayan.tun daga wannan lokacin kasuwancin mannir ya samu nasaku domin duk kudaden ya narkasu wurin sarin kayan da suka kone a jirgi.sai dai ya danyi sarin kayan kadan ya barwa yaransa, dan duk babu wani kayan azo a gani, dan haka kawai sai ya dakko takardunsa ya fara neman aiki, cikin ikon Allah ya samu aiki a wani babban asibitin gwabnati dake nan cikin kaduna,GENERAL HOSPITAL, sosai ya dukufa a aikinsa baya wasa ga albashi mai tsoka, da gwabnati ke bashi saboda kyau da takardunsa sukayi kuma ya samu kwarewa sosai a aikin. dan idan dai doctor mannir ya yiwa mutum operation to sha allahu a ranar yake dawowa normal ,dan ya kware sosai asibitin ke alfahri dashi.


Wata rana bayan mannir ya tashi daga office zai wuce gida ,suka tsaya bakin titi wurin masu saida dabino da cukui domin su siya saboda yaransa suna so musamman MUSADDIQ da sai yaki cin abinci kawai yake cin dabinon .sai suka tsaya wurin wani dattijo dake aunar da dabinon mannir ya fiddo kudi yaba direban domin ya fita ya siyo,bayan ya auna musu dabino kwano biyu cukui faifai goma , sai dattijon ya tsaya yana hada canjin da zai baiwa direban,sai direban yake fada yana cewa akan me zaike hada musu wasu tsofaffin kudi, duk sun wani yakune, sai dattijon yake cewa haba yaro ai duk kudi kudine kuma muda muke neman sa ai duk tsufansa karba muke indai zai karbu to bamu damu da tsufansa ba.anan direban nan sai cewa yayi wai dattijon nan ya fada masa magana,yana ta cewa ai shima aikin direban sana,a ce haka dai dattijon ya bashi canji maimakon ya tafi ya tsaya yana maganganu,anan wani dake sai da kayan fruits a wurin yake nunawa direban rashin kyautawarsa dan yana ganin ai malam audun ya haifi direban amma sai ya hau zagin mutumin har wasu mutanen suka dan taru suna rabasu, mannir da yake waya tun fitar direbansa,bayan ya gamane ya maida hankalinsa akan jarida ,can sai ya lura da dadewar sabo direba, kamar ance ya dago kansa sai kwa yayi arba da abinda ke faruwa, ya fito daga motar ya doso wurin dake bayajin me suke fada da yana cikin motar sai daya fito ake fada masa abinda yake faruwa anan yaba dattijon hakuri,sabo direba ya dauki ledojin ya sanya a but suka kama hanyar gida.

"Wai kai sabo har yaushe zakayi hankali kasan ya kamata fisabilillahi, yanzu wannan tsohon ka zauna kana sa,insa dashi mutumin ya haifeka ,kai kullum abu kamar karatu ake fada maka ni kullum cikin maka fada kamar wani karamin yaro,gskia na gaji da mutuncina da komai bazaka ke janyomin magana ba ,idan kaci gaba da yin haka to gskia zan sallameka in nemi wani"dr mannir ya karshe ransa a matukar bace dn ya gaji da halin sabo direba.

"Ayi hakuri alhaji hakan bazai sake faruwa ba yanzun ma sharrin shaidan ne"
"Haka kake cewa kullum na gaji da halinka"
"Ayi hakuri dai alhaji"

bayan sunzo gida sabo ya tattaro kayan dr ya shigo dasu bangarensa ya dora akan center table,ya kara gaba, bayan dr ya watsa ruwa aysha ta gabatar masa da abinci yaci don ranar bakinta ne, sai ya baro dinning din ya dawo kan kujera suna kallo suna dan taba hira.can yace ta miko masa wallet dinsa a cikin jakar,aysha ta duba bata gani ba, haka yasa ta miko mishi shima ya duba amma babu ita babu dalilinta, gashi akwai abubuwan a ciki akwai kudi atm dinsa passport dadai wasu muhimman abubuwa.haka ya kira sabo direba yasa ya duba cikin mota amma bai gani ba,ya bashi key din office dinsa yaje ko zai gani Amma babu daga bayama da kansa ya je ya duba amma bai gani ba.



A bangaren malam audu kwa bayan dr mannir ya yiwa sabo magana sun tafi,ya zauna yayi shiru yana tunanin rayuwa ,can sai idanunsa suka sauka akan wallet din da aka yarda a kusa da buhun daya baza dabinonsa, ya tashi da sauri ya dauka ya bude ganin abinda ke ciki razana shi,sai yaga photo alhaji mannir a jiki sai kawai yasa a aljihu ko na kusa dashi, bai nunawa ba saboda halin dan adam.bayan ya tashi daga kasuwa ya koma gida yake baiwa matarsa kande labari (malam audu ne abokin malam buba makama mijin inna sarai da yake zaune a garin kaduna).yace gobe zai idan ya koma wurin sana,arsa idan Allah yasa mutumin yazo nema sai ya bashi.
"Bari in kawo maka abincin malam"
"Kai kande da kin bar abincin nan dan jina nake a kosher"
"Na lura malam tunda gidan aikina suka sallameni daga yin wanke wanken nan, ka rage cin abinci na lura kafison mai dan maiko maiko na gidan yan gayu"kande ta karasa fada tana dariyar wasa.
"Da hakan ma gskia Amma yau din banajin dadin jikina ne shisa"
"Subhanallah to Allah baka lpy"
"Amin"


Haka ranar zazzabi da ciwon kai suka rufe malam audu, dan koda safe ma bai samu zuwa wurin sana,arsa ba.haka ya kwanta jinya satinsa biyu a kwance yasha wahala sosai, dan har kande ta fidda rai dashi ,sai kuma Allah ya tashi kafadunsa.bayan yaci gaba da zuwa kasuwa tsawon kwana uku baiga mutumin nan mai wallet din nan yazo ba ,gashi bai san inda zai sameshi ba,shikwa mannir yama hakura da nema dan yasan duk wanda ya tsinci wallet din bazai taba bashi ba,dan bayan kudin Nigeria ma har da dollars a ciki.sannan tunaninsa bai taba bashi ya yarda a wurin masu dabino ba.

ranar nan zasu wuce sai mannir yace sabo ya fita ya siyo dabino da cukui,aikwa malam audu yana ganin sabo direba ya shaidashi dan daman suna yawan zuwa ga kuma abinda ya faru ranar nan,bayan ya bashi dabinon da cukui sai yabi shi wajen motar ya zagaya inda alhaji mannir yake,yake kwankwasa glass din, sabo da har zai shiga mota ya hango abinda malam audu yake,sai ya dakata da shiga motar.
"Haba malam yanzu barar ma da zakayi har sai ka kwankwasa kofa?
kallo daya malam audu ya yiwa sabo ya dauke kansa,dan da shi yayi niyyar bawa wallet din amma ganin bashi da nutsuwa,da alama amanar ma ba ita gareshi ba.
"Sannu baba kana bukatar wani abun ne?" Mannir daya bude kofar yake tambaya cikin girmamawa.
"Eh ina bukatar ka sauke nauyin dake kai nane"
"Nauyin me baba"
"Gashi"yasa hannu a aljihunsa ya fiddo wallet din ya mika masa.
"Wallet dina"mannir ya fada cike da mamaki.
"Wallet fa kace alhaji"sabo direba ya fada shima da mamaki a fuskarsa dan tunda yaga mannir ya bude kofar sai yaja ya tsaya.sai yanzu da aka ambaci wallet ya karaso wurinsu.
"Rannan ka yardata anan, to ni kuma satina biyu a kwance ba lpy tun ranar dana tsinta ,sannan idan ma lpy ta kalau bansan inda zan sameka ba"
"Kai Amma nagode baba ,dan har ba gaji da nema na hakura"
"Ba komai ai hakkin kane, idanma na rike a duniya to tabbas zan biyaka da ladana ranar kiyama"
"Hakane ngd amma wasu basa lura da hakan,dan duk wanda ya tsinta gani zaiyi ya zama nasa kawai"alhaji mannir ya karasa fada yana fiddo kudi daga aljihunsa ya irga dubu ashirin ya mikawa malam audu.
"Ka barshi wlh bazan karba ba, ni dan Allah nayi"
"Kai amma ngd Allah biyaka"
"Amin "ya fada tare da juyawa ya koma bakin sana,arsa dan har mutum uku suna jiransa.


Bayan sun hau hanya mannir ya bude wallet dinsa yana kallo da mamaki dan kamar yanzu ta fadi,dan komai yana nan yadda yake ba,a taba komai ba.
"Mutumin nan yana da tsoron Allah gskia alhaji"
"Hakane ay shisa ba,ason wulakanta mutum,kaga da mugune sai yayi amfani da cin zarafin daka masa rannan ya rike wallet din,amma dake yana da amana baiyi hakan ba .
"Kuma ko kudin daka bashi yaki amsa"
"Eh mana gashi dai yana da bukatarsu amma wadatar zuci ta sanya yaki karba.


suna isa gida sabo direba ya fito ya tura get din sannan ya dawo yaja motar suka shiga ciki yayi parking alhajin ya fita shi kuma ya take masa baya da kayan zuwa sashensa.

Da dare suna dan tattaunawa da aysha dan ranar ma ya kasance girkinta, sai yake bata labarin yadda ya samu wallet dinsa, ta tayashi murna kafin daga bisani ta bashi shawara akan ya dauki mutumin koda gadi ne tunda gashi mai gadin nasu ciwon kafa ya dameshi dan yau ma kwanansa biyu da tafiya garinsu,yace su samu wani kafin Allah ya bashi lpy.sosai mannir yaji dadin shawarar data bashi aikwa washe gari yajewa malam audu da maganar ,yaji dadi sosai amma kuma ya fada masa yana da mata baya barta ita kadai ba tunda Allah bai basu haihuwa ba.mannir yace zaiyi shawara da iyalansa yaji ko suna da bukatar karin mai aiki.bayan ya tara matan nasa ya rattabo musu bayani sai kwa suka amince akan malam audu ya dawo da matarsa gidan tana musu aiki shi yana gadi aka basu daki ciki da falo da bandaki a ciki acan bangaren masu aiki amma shi dakin daga can gefe yake dana masu aikin sai dai duk a part daya ne.wannan shine sanadin haduwar malam audu da alhaji mannir.





Ya samu shekaru biyar yana aikin a general hospital din , kafin daga baya akayi mishi transfer zuwa asibitin aminu kano, dake garin kano ta dabo tunbin giwa.har wannan lokacin kuma aysha bata sake haihuwa ba ,binta ce ta haifi yaranta yan biyu duk mata hassana da husaina, yanzu suna da shekara 3, MUSADDIQ nada shekara 14, boy 7,muhibba nada 9.har wannan lokacin babu wani jituwa tsakanin aysha da binta ita dai aysha tana kama girmanta sannan kuma ta dauki duk yayan binta duk dayane da nata ,sai dai ita binta a nata bangaren abin ba haka yake ba, a gaban mannir zata nunawa yayan kulawa amma a bayan idonsa kyama take nuna musu saboda tana ganin duk maza ne amma ita nata mata.yanzu kimanin shekara biyar da dawowarsu kano da zama dan tunda aka mashi transfer ya siyi dankareran gida anguwar nasarawa, dan Haka har su kande aka dawo kano ko kuma ince da dukkan ma,aikatansu suka dawo.yanzu MUSADDIQ ya kammala karatunsa na secondary school ,yama samu admission yana shirin tafiya India domin cigaba da karatunsa,muhibba tana s.s two boy yana s.s one sai hassana da husaina da suke primary 2.




"Hajiya na kammala aikin"cewar karima tana rissinawa.
"Kin tabbatar komai yayi tsaf"
"Komai yayi hajiya babu inda baiyi tass ba"
"Kin shiryawa yan biyun sarari kayan gugar nan a cikin kayansu?"
"Duk na kammala komai a ma,ajjinsa hajiya"
"Ok abinda nake sonki dashi ,ungo wannan kudin kije kasuwa ki siyo kayan kamshi ,daddawa ,kuka, ammm kimma san duk abubuwan da zaki hado na kayan gargajiyar nan, dan nida ba amfani nake dasu ba bana rike sunayensu mantawa nake, karki manta wannan abun da ake jikawa asanya idan za,ayi danwake yama sunashi?
"ta karasa fada tana yatsina fuska.
"Kanwa hajiya"karima ta fada tana danne dariyar dakeson kwace mata.
"Koma dai meye ke kika sanshi, ki hau napep dan sabo lokacin dakko yara a scul yayi bazai samu damar kai ki ba kuma karki dade dan zaku hadawa alhaji abinci ,na sanki da shiririta"
"To hajiya an gama insha allahu bazan dade ba"
"Kibi ta kicin ki cewa kuku yayi sauri ya gama min abinda na sakashi"
"To hajiya"






'
'
'
'
'
'
'
'
'
'
'====







Story & written by



MAMAN AFRAH




Page 59____60







Bayan su zee sun gama wankan kowacce ta maida kayanta data cire, suka daura alwala suka gabatar da Sallar ishsha,i suna nan zaune zuwa can sai ga matar nan ta dawo ta tambayesu sun kammala suka amsa mata da eh sun gama.haka ta musu jagora har zuwa bangaren shugaba, sun sameta a zaune sai wata yar budurwa dake mata tausa,tana mammatsa mata kafafu.bayan sunyi sallama an amsa musu suka mata sannu da hutawa da kuma mika godiya na alkairin data musu.ta nuna musu hakan ba komai bane ,duk taimakonsu tayi .

Bayan sun dan zauna na dan wani lokaci sai ta fara musu jawabi kamar haka.
"ba komai bane yasa na taimaka muku ba sai dan nima inason akwai wata bukata daga wurin wasu daga cikinku ,amma ba yanzu zan fada muku ba,sai lokaci yayi zan sanar daku ,nidai fatana ku bani hadin kai a dukkan maganan da nakeso na fada muku ba" ta fada tana binsu daya bayan daya da kallo.
"Hajiya ai ba komai dukkanmu a karkashinki muke dan haka babu wani musu da zamuyi da umarninki"cewar zee cike da girmamawa.
"Wannan haka yake shugaba"amina rakiya da kuma lantana suka hada baki Wurin fada.
" ba wani abu ku koma shashin ku da zarar na shirya fada muku maganar zan neme ku"
" to shugaba"
"Ga wannan kwa yi amfani dashi"ta mika musu b babban leda cike da kayan makulashe.
"Muna gdy sosai da sosai Allah kara girma "
"Amin "cewar wacce ke matsawa shugaba kafa a fili, a zuciyarta kwa tana tausaya musu dan tasan kudurin shugaba akansu, suma ma,aikatanta sai wanda Allah ya tseratar.


Fitowa sukayi daga bangaren shugaba zuwa bangarensu, zakatansu cike da murna, dan sai suka kasa tantance abinda shugabar tasu take bukata wanda bazata fada musu yanzu ba .sai daga baya dan su duk tunaninsu aiki takeso ta daukesu a bangarenta, dan kowacce fatanta Allah yasa a daukesu gaba daya, ammq a zuciyar kowaccensu tana addu ,a Allah yasa kada aqi dauka da ita, dan hausawa sunce so sone amma wai son kai yafi.


Lokacin da suka iso bangaren su sai suka zarce dakinsu, anan kowa yake murna da ganinsu dan kowa labarin zuwansu gidan shugaba ya iskeshi, dan kuwa nan akazo aka samu wasu aka maye gurbin aikin su lantana dasu.dan haka kowa yasan daga inda suka dawo ,anan kowa yake tofa albarkacin bakinsa wasu na cewa daman sune wasu nason suji yadda abin ya kasance,ma ana yadda akayi suka je gidan shugaba har ta sanya aka maye gurbin aikinsu da wasu daga cikinsu.nan suka shiga basu labari amma kuma sun boye cewar shugaba tace zata nemesu,hakan kwa yana cikin shawarar da zee ta kawo musu a ganinta idan suka bayyana hakan wasu yan bakin cikin zasu iya yin duk yadda zasuyi suga basu samu wannan cigaban ba.
Bayan sunyi shirin kwanciya suka fiddo ledar da shugaba ta basu ,suka fiddo kayan dake ciki suka raba gida biyar kowa ta dauki kashi daya ,kashi dayan kuma suka baiwa ya yan dakinsu suka rarraba.

Washe gari ma haka kowa ya tafi wurin aikinsa, su lantana haka kowa ya kunshe dan abin da shugaba ta bashi ya tafi dashi domin rage zafin yunwa.basu dawo ba sai karfe uku kamar yadda aka buga karfen nan jiya yau ma haka sukaji karansa, wannan yasa suka koro rakumansu zuwa madaurinsu.sannan suka kamo hanya domin tafiya bangarensu ,da sukazo dai dai inda suka hadu da shugaba jiya sai suka tsaya suna ciccira idanu yau ko allah zai sanya su sake haduwa da ita.amma ko mai kama da ita basu gani ba,haka suka kama hanyar karasawa cikin gida dan kar su rasa dan abincin da ake rabawa.bayan sun gama cin abinci sunyi sallar la,asar dan acan suke sallar azahar,sai kowa ya kama hanya domin zuwa wurin aikinsa.

Su lantana sun kora rakuman nan har sai da suka danganasu da wurin kiwonsu ,amma kuma sai suka lura babu abinci sosai a wurin dan haka suka kara luntumawa can cikin dajin sosai dan su samu abinci yadda zai ishesu.sun samu wurin da ciyawa take da yawa da kuma kaya sai suka barsu a wurin suke kiwonsu,zuwa can sai rakiya ta hangi wani wurin an kewayeshi da katanga sai ta ta nunawa sauran suma suka gani,sai rakiya tace lantana tazo suje suka menene a ciki ,sai suka bar amina take kula da kiwon. lantana da rakiya suka tafi domin su gano ko menene.suna zuwa sai suka ga ashe shuke shuke ne a ciki aikwa suka dunguma har ciki sai sannan suka kara cika da mamaki dan kuwa lanbu ne Katon gaske mai cike da shuke shuke tun daga lemon zaki na tsami, ayaba goba karas kai babu abinda babu sannan ga ruwa nan yana ta gudana a wurin da basu gama tantance daga inda ruwan yake ba.haka suka sille hijabansu suka cicciri abunda sukaga ya musu sunayi suna tsoro kar azo a kamasu bayan sun cira da yawa sai lantana ta cire wata roba da take rataye a wuyan lantana, suka cika da ruwa, ai kafa me naci ban baki ba suka zuba a guje sune basu tsaya ba sai sai a wurin amina ,nan suka nuna mata abinda suka samo, suka zauna cike da murna suka wanke suka ci suka koshi dan dama abincin da aka raba ba wani isar su yake ba. Haka sukaci gaba da kiwonsu har sukaji ana buga karfen dake nuna alamar lokacin tashi yayi ,suka kamo hanya suka dawo suka maida rakuman suka kama hanya suka dawo gida.



*BAYAN* *SATI* *BIYU*


Har zuwa wannan lokacin shugaba bata aiko kiran su lantana ba. Haka su zee suka cigaba da zuba ido, da kasa kunnuwa domin jin kira daga shugaba amma har lokacin shiru kakeji wai malam yaci shirwa.sai daga baya ma sukaji labarin wai bata nan ma wasu suce ta tafi makka wasu suce ta tafi Nigeria,su amina sunsha mamakin jin cewa wai ta tafi Nigeria sai suke tunanin dama tana zuwa Nigeria? to me zai kaita Nigeria kuma? Nace amsar na wurin shugaba.sune basu kara jin duriyar shugaba ba har sai bayan sati bakwai ma,ana wata biyu ba sati daya ,dan zuwa wannan lokacin su lantana duk sun fita hayyacinsu sunyi baki sun rame ,har gwara ma zee da yake ita ta saba shekara da shekaru.

A wannan lokacin ne sukaji ana cewa shugaba ta dawo ,amma kuma bata nemesu ba,sai kawai suka fidda rai da cewar zata nemesun.

Bayan kwana uku da dawowar shugaba ,su lantana suna zaune a dakinsu tsakanin magriba da ishsha,i sai ga sako daga shugaba,yar aikenta tazo wai ana kiran zee da sauran mutum uku da sukaje wurin shugaba.lokacin da aka fadi sakon zee bata nan tana wani daki dake kusa da nasu taje wurin kawayenta hira,sai lantana da amina dan rakiya tana bayan dakinsu tana wanki,murna wurin su lantana kamar an musu albishir da wata gagarumar kyauta haka lantana ta kirawo sauran suka hadu da yar aiken suka kama hanya domin zuwa can bangaren shugabar.


Yar aiken ta musu iso har can inda suka samu shugaba kwanaki da sukazo, sai dai abin mamaki suna zuwa sai sukaga an nuna musu wani korido wanda da sukabi mai musu ison sai sukaga ta kaisu wani daki sannan ta kara kaisu wani dakin dake can ciki.suka samu wuri suka zauna a kasa duk da daman ba kujeru a dakin sai cafet sai tuntu kawai a dakin.suna nan zaune kusan minti talatin sai sukaji an bude wata kofa dake cikin dakin, sai sukaga shugaba ta bayyana,sai suka mimmike alamar girmamawa.
"Barka da fitowa

Please Login or Register in order to submit comment