Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a gidan radion Kano"
"Eh eh am"ta fada cikin in innaa,da kuma rashin sanin abin cewa .
"Kodai wani abun ne ya faru MARYAMU matar malam audu" ta fada cikin zolaya, amma cikin zuciyarta fal fargaba dan ta lura da canjawar MARYAMUn dan duk lokacin data zolayeta takan ce
"Haba me zanyi dashi Allah kiyaye in auri tsoho.maimakon ta fadi hakan sai tace
"Daman su bishira ne.....kafin takai ga fadar maganar suka tsinkayi muryar jummai mai dambu,wato babar bishira tana kwala kiran inna sarai.
"Sarai sarai,sarai!



'þ
'þ
'þ
'þ<ØGß<ØGßRAYUWAR MARYAMU<ØGß<ØGß



Story & written by


MOM MASHKUR


Page 35 _36





**MANZON ALLAH (S.A *.W* .) *YACE:*
*KU* *KIYAYI* *ZALUNCI,* *DOMIN* *ZALUNCI* *DUFFAINE* *RANAR* *TASHIN* *KIYAMA,* *KU* *KIYAYI* *YIN* *KAURO* *DOMIN* *YIN* *KAURO* *SHI* *YA* *HALAKAR* *DA* _**WANDA* *SUKE* **A* *GABANINKU,* *SHI* *YASA* *SU* *SUKA* *ZUBAR* *DA* *JININSU* *SUKA* *HALATTA* **ABINDA* *AKA* *HARAMTA* *MUSU.*

*MUSLIM**





*RUGAR* *HARDO* **SANI*



Yau tunda assalatu lantana ta tashi ta dakko daron da take zuba kuli kuli tasa a gaba tana kallo,a lokaci guda kuma hawaye yana zuba a idanunta,ta juya ya janyo jarkar man gyada ta jijjiga taji ya kusan kwalba ashirin yau kusan sati biyar kenan amma daga kulin har man gyadar babu wanda yazo ya siya,wanda idan da dane ko sati bayayi yake karewa,saboda gabaki daya fulani and rugagensu da na rugagen dake makotaka dasu dama kauyuka nan suke zuwa siyan mai da karago. wasu sara sukema a wurinta amma yanzu babu wanda zai zo koda siyan kulin naira goma ne,abin na damunta.yau ko baccin kirki ta kasayi saboda tun jiya taje wurin wani malami ya bata lakanin samun kasuwa yace tana zuwa kulin da man zasu kare amma kuma gashi har wuni guda gashi ana neman vwayewar gari ba wanda yazo ya siya.dan kudin hannunta daya rage shine ta raba a biyu takaiwa malamin sauran ta auno gyada wai nufinta idan man da kuli kulin ya kare tayi wani saboda.itace data dawo har da yiwa innar auwalu gorin rashin sana,a,sannan tace mata
"Ko mutum yaso koya ki sai anzo siyan kayana" saboda malamin ya fada mata cewa asiri akayi aka korar mata kasuwa.
"Me yassa wai Jama,a basu fahimci ikon Allah ba"innar auwalu ta fada cikin waka.
"Kedai kika dogara da arzikin miji to gashi yanzu karayar arziki ya sameshi sai asan nayi"
"Haba kekwa lantana nida kikazo kika sameni a gidan mijina,ko na taba fada miki daman dan abin hannunsa nake zaune dashi"
"Allah ne yasan karatun kurma "lantana ta fada tana shiga dakinta.dede nan ta dawo daga tunanin da takeyi, ta sanya hannu ta janyo tukunyar data zuba gyadar data auno,ta haska da fitila "wayyo na shigesu nima karayar kasuwa ta sameni kamar yanda karayar arziki ya samu baban auwalu"ta rushe da wani uban kuka.
Baban auwalu daya fito daga dakinsa zai shiga bandaki rike da buta a hannu,yajiyo kukan lantana sai ya ajje butar da sauri dan shi tunaninsa ko dai kunama ko miciji ne suka cijeta, "lpy lantana"ya fada hankalinsa tashe yana mai bankada labulan dakin ya shiga cikin dakin da Sauri,ya hasketa da touchlight sai ganin lantana yayi da daron karago a gabanta,wani kululun bakinciki ne yazo ya tokare masa makoshi

"Yanzu saboda Allah lantana akan kuli kuli kike disgar kuka da asubar fari,ni wlh mms dauka wani abun ne ya sameki"ya fada yana jan tsuka

"Ya kakeso inyi baban auwalu da kayan kulin nan mutane basa zuwa siye,sannan kai yanzu ba wani kudi kake bani ba,kuma nasan ba wanda zai min wannan makarkashiyar sai matarka saboda batason cigaba na"ta karashe cikin kuka

"Ikon Allah wai ke me yasa baki da hankali ne lantana? Ke kwata kwata baki da tawakkali,bakisan komai sai Allah ya Kaddarawa mutum ba yake samun saba,meye na cewa innar auwalu ce ta miki asiri ke kanki kinsan da innar auwalu tana bin makamai da bokaye da bata barki kin shigo gidan nan ba a matsayin matata.

"Ba wani kai daman ka saba bin bayanta,kullum nice marar gskia.

"Ba wani bin bayanta da nake bayan gskia nake bi"
"Ka dai fadane amma ba haka bane"ta fada tana tura daron kuli kulinta kasan gadon karfe.

"Ai tunda kikaci kayan marainiya ba abinda bazaki gani ba,Dan. baki fara ganin komai ba .

"Allah sawaqe bakinka ya sari bayan katanga,sai dai inga alheri wlh,kuma da kake maganar kayan marainiya kayan wa naci? naga kayan yar uwata ne naci,wai ni ina dalili ka dameni da magana shekara da shekaru,mutanan da ba,asan inda sukeba ko sun mutuma wa ya sani,to kai kuma daka tsiyace fa duk kiwon dake gidan nan kama daga tumaki,awakai shanu da kaji,zabbi amma yanxu duk babu sai wannan shegen tsohon machine din kamar anbar maka gado.

"Daman Allah ne ya bani kuma shi zai kara bani Idan yaso,in kuma beso ba ya hanani duk cikin ikonsa ne.kiyi sadaka da kuli kulin mana.

"Bazanyi ba kaima ai na gane bakinciki kake mini "

"Kanki akeji wai mahaukaci ya fada rijiya yace wankana nake "yace yana kokarin ficewa daga dakin.har yaje yayi alwala lantana tana sababi.


*Kauyen mai alkama*



"Kina ina sarai wlh yau mai rabani dake a garin mai alkama ba,ayishi ba"

"Mai kuma ya faru MARYAMU,me kika yiwa masifaffar matar nan yanxu zatazo tagama min tijarar data saba "

"Wlh inna bishira ce ita da habasiyya suka tare mana hanya d...." Zancen ya katse sanadin kiran da jummai mai dambu take yiwa inna sarai.

"Sarai idan bazaki fito ba ni in shigo dakin"

"Haba jummai mai yayi zafi haka,ke kullum idan zaki shigo bazaki yi sallama ba ? Sai dai ki shigo da tashin hankali"

"Ba abinda ya kawoni ba kenan,kona ce miki sallama nazo yi,magana ce akan wannan aljanar jikar taji"

"Karki sake kiranta da aljana,sunanta MARYAMU kin kuma sani,aljana ai ba sunan bil adama bane"

"Haka naga daman fada,ko ma wacece sunanta hakan be daman ba,zuwa bayi inji idan ke kika saka ta suka hadu ita da halima yar gidan mai daddawa suka yiwa bishira shegen duka,sannan suka tura katon gardi ya matse min ya a lungun hanyar makarantar mahammadiyya"

"Haba jummai yanzu banda abinki taya za,ayi in tura su MARYAMU suyi wannan danyan aiki,kuma kinsan bishira ba sa,arsu bace,ta girmesu nesa ba kusa ba,kuma ni bansan abinda ke faruwa ba,sai yanzu MARYAMU take kokarin fada min,bata kai ga fada min ba kika zo"

"Duk ba wannan ba akan me haure zatazo ta takurawa yar gari,kuma mai asali itada ba,a san asalinta ba ,kota wace hanyama aka sameta wayasani,kawai kun dawo mana gari kunzo kun addabi mutane "ta karasa tana wani daga kai sama alamar rashin arziki.

"Kin fara ko daman abinda ya kawoki kenan,kinzo ki min abinda kika saba,wai jummai mai muka tare muku a garin nan,kuka sako mu a gaba,kullum abu daya kamar cin kwan makauniya,kina sheganta min jika,bayan da ubanta an fada miki ki fita sabgarmu amma kinki nagaji da abin nan da kike mana,sanin kanki ne daga bishira har habasiyya babu wanda zai gwadawa MARYAMU karfi,amma haka na hanata rama abinda duk suka mata saboda gudun abinda zai je yaxo,yanxu mesa baki je gidan iya mai daddawa kin musu ba sai mu mune bamu da kowa,kowane kashi aka kwaso sai akanmu za,a zuba"

"Kinga tsohuwa duk ba wannan ba, gobe zanje in dakko dan sanda duk wanda keda hannu wurin sanya a lalata min ya sai sunanshi ya fito a ciki"

"Kedai jummai wlh baki da haki ki rasa wacce zaki takurawa sai ni da jikata ,a haife na haifeki amma kin maidani kamar sa,arki ,kawai dan mun dawo garinku da zama,to gidanki muka dawo kokwa ko nan gidan kyauta aka bamu ba siya mukayi ba "


"Haba tsohuwa kiyi shiru dan allah da kuka dawo rana daya wa yasan meya raboku da garinku haka kawai zaku kauro mana gari inkwa ke kikayi cikinta kika haihu saboda gudun magana yan uwanki suka koroki,shine kuka dawo mana nan"

"Innalillahi wa inna ilaihir raji,un"inna sarai ta fada tana kuka itama MARYAMU dake tsaye ta jingina kofar daki itama kukan take.

"Inna jummai mai Innata ta miki kike sata kuka?"
MARYAMU ta ta fada itama tana rushewa da kukan "bazaki tambayi ya akayi ba sai kina zagin innata,wlh sune suka tare mana hanya da muka dawo daga makarantar dare,kuma babu abinda muka musu,wai mun cewa malam aramma ta tafi shagon emeka,dan malam aramma ya hana zuwa shagon yace emeka dan iskane ,to shine da malam din bai gansu ba a makaranta yake tambaya an ajin sukace masa sun tafi shagon emeka shine suka tare mu a hanya wai mune muka fada kuma wlh bamu bane,dan ni ko magana banyi ba a lokacin ,kuma ko a hanya ni banyi fada da kowa ba saboda innata ta hanani fada kuma...."


"Ke dallah can rufewa mutane baki, munafuka banda munafurci har akwai wanda yake kai bishira kara a makaranta daya wuceki,banza marar asali"

"Ya isheki jummai !!! Inna sarai ta fada cikin wani irin bacin rai .

"Wlh kimin komai amma zuwa yanzu bazan yarda da wannan kazafin ba,kaf rugagen nan da kauyukan dage makotaka da rugar marayo waye baisan abinda ya faru ba tsakanin tasi,u da fulani ba wanda yayi sanandin mutuwarsa ba,akan me zakuna jifan jikata da wannan suna to wlh ahir Dinki?"

Kedai kin rasa abin fada kuma hakan bazai saka gobe in fasa dakko muku dan sanda ba,kodan gardin da akasa ya matsemin ya a lungu dan iska kawai ku kuma kuka kumbura mata fuska tana nan tayi luhu luhu kamar ansawa fulawa yis.


 inna jummai bafa dan iska bane,ishu ne dan gidan malam aramma,kuma bishira ce ta zageshi bayan ya raba fadan kuma ta dare masa jikinsa tana yakushinsa shine shi kuma ya mareta amma bayan haka ba abinda ya mata"

"Ke idan baki dena samin baki ba a magana sai na kwada miki mari bagidajiya kawai mai ruwan askarawa "

"Kyaleta MARYAMU ta dakko rundunar sojoji ma ba yan sanda ba,indai akan gskia mutum yake ai baya taba tabewa,wane mutum"inna sarai ta fada tana kama hannun MARYAMU suka shige daki suka bar jummai mai dambu na sababi>Ø-Ý





'þ
'þ
'þ<ØGß<ØGßRAYUWAR MARYAMU<ØGß<ØGß


STORY & WRITTEN BY



MOM MASHKUR


PAGE 37 _38


Wannan page din nakune
RAYUWAR MARYAMU FANS inajin dadin comments dinku, kuma na gode da soyayyar da kuke nunawa buk dina Allah barmu tare.san so ana tare>ØÝ>ØÝ>ØÝ


*QALA* *RASULULLAHI* (S.A.W)* *MAN* *AHADASA* *FI* *AMRINA* *HAZA MA* *LAISA* *MINHU* *FAHUWA* *RADDUN.*


Bayan inna sarai takai MARYAMU daki tayi ta lallashinta akan tayi hakuri ta daina kuka,bayan itama kukan take.

"Ki daina kuka MARYAMU,komai kika ga ya sami bawa daga ubangiji ne, kuma babu wani dan adam da zai yiwa mutum abu face sai Allah ya Kaddara"


"Inna haka kullum za,ake zaginki kina kuka kuma duk ba wani abu kike yi ba"

"Komai zai wuce MARYAMU zai zama kamar ba,ayi ba ,kinji ko" ta gyada mata kai tana sanya bayan hannunta ta goge hawayen fuskarta.

"Maza tashi ki cire hijabinki,ki dakko ga rigar sanyinki can ki saka"

"To amma bazansa hular sanyi ba ko inna ?"

"Ba dole kisa hular sanyi ba so kike ki kwanta da dankwali,cikin dare ya badi daga kanki,duk ki ringa yaba Min wannan gashin naki da kika ki zuwa a miki kitso ,sai dai kiyi ta yawo dashi abu ba kadan ba,ni sai in rasa ya kikeji abu gashi har baya kuma ba kitsawa"

"Zanje amini kitsan "ta fada tana zunbura baki, dan in akwai abinda MARYAMU taki jininsa to kitso ne,saboda tsawan gashinta idan ana mata har gajiya take da zama,dan kafin akai karshen bedo daya hmm abin ba,a magana.

"Idan kinyi iyo fitsarin ki ciko min butar ki shigo min da ita,kar in tashi da asuba ruwan inji yayi sanyi,Amma in a daki ne sanyin ba kamar ruwan ya kwana a waje ba.
"To"
"Ki saka labulan ya rufu sosai ,sai ki rufe kofar ,ki miko min mansiletana in shafa, hancina duk ya toshe ,kuma ki kashe radion nan ki dauketa ki dora akan kabet din nan"

"Ina mansiketan yake?"

"Duba cikin kwadon kayan kwalliyarki,inajin yana ciki"

"Baki gani ba"

"Gashi na ganshi"
"Miko kizo ki kwanta "

"Ungo"ta mika mata tana hawa kan gadon ta kwanta a kusa da innar "

"Yanzu inna idan inna jummai ta dakko dan sandan gobe ya zamuyi? kar tasa su tafi dani"

"Haba MARYAMU ba wanda zai tafi dake ai da a tafi dake gwara ni a tafi dani, dan ma bazasu tafi dake ba saboda ke yarinya ce,kuma suma sai sunyi bincike suke yin hukunci"

"Wai inna mesa muka bar gidan mu muka dawo nan garin,indai inna jummai na fada sai tace mun dawo musu garinsu'

Nan take hawaye suka zubowa inna sarai,Amma maimakon ta goge sai ta barshi a haka,dama a duhu ne sun kashe fitilar da zasu kwanta ,balle ma MARYAMU taga hawayen nata.domin tinawa da tayi da dalilin da yasa suka baro rugar su,wato rugar marayo.

"Zan fada miki,amma ba yanzu ba"

"Sai yaushe"

"Sai wataran "

Shiru ya biyo baya ita inna sarai na addu,ar Allah yasa kar MARYAMU ta baro mata wata tambayar,ita kuma MARYAMU bacci ya dauketa.asuba ta gari tauraruwarmu.


A bangaren jummai mai danbu kwa bayan tazo kofar fita daga cikin gidan, ita kuma iya mai daddawa ta kawo kai zataje gidan na inna sarai.
"Daman nasan sai ke wannan aikin,dan babu mai shiga gidan baiwar Allah n nan da daren nan yake mata tijara in ba ke ba" cewar iya mai daddawa dafa katangar da hannunta daya, "wai dan Allah jummai mesa bakyason zaman lafiya mai matar nan ta tsare miki ne,ko akanki take zaune ? Kawai dan zaman wuri daya ya hadaku,zaman wuri dayan ma makota katanga daya sai kibi ki addabeta ita da jikarta me suka tsare miki keda yar taki a garin mai alkama,da kuka hana rayuwarsu sakat kullum jiya iyau.
"Kin gama ? Nace kin gama koda saura"ta fada tana gyara mayafinta daya koma gefe daya yana kokarin faduwa daga jikinta.
"Ban gama ba din,kedai wlh jummai kiji tsoron Allah,dan ba anan za,a dawwama ba"
"In banji tsoron Allah ba tsoronki zanji? Ko kin dauka kema barinki zanyi to yanzuma dana fito da baki zo bama gidanki zanje,tunda duk zaman da mukayi shekara da shekaru har wannan tsohuwar data dawo garin nan daga baya zata shiga tsakaninmu,har a hada baki dake ki tura yarki halima su hadu da wannan yarinya marar galihu MARYAMU su yiwa bishira dukan kawo wuka, har ku tura katon gardi ya matse min ya' a lungu zai keta mata mutinci Allah ya kubuto da ita,to ku sani ta Allah ba taku ba,kuma wannan magana ko me garin nan tafi karfinsa ya raba mana ita sai dai hukumar yan sanda,dan gobe sai kunje hilis sezin (police station) kun wuni koma ku kwana yo wayasan iyakar kwanakin da zakuyi acan ma,sannan suci tararku ta sanyawa a yiwa yarinya fyade"

"Karki fasa niyyarki dan girman Allah yanxuma ki tafi ki dakko su, an daketan koma me kikace anyi mata to anyi,ki kaimu kotu ma ba wurin yan sanda ba, ni nafi kowama da na tsaya ina saurarenki marar hankali kawai"iya mai daddawa ta fada tana shigewa gidan inna sarai.

"Zakuga ga kotu kwa ganin idanku."ta juya ta shige gidanta tana sababi.
"Assalamu alaikum" iya mai daddawa taketa sallama har ta karaso kofar dakin inna sarai,tana kokarin juyawa ta tafi a tunaninta ko sunyi barci.inna sarai da bacci ya kauracewa idonta tana tunanin yadda za,ayi gobe su da jummai taji muryar iya mai daddawa na sallama tazo ta bude kofa.
"Iyar halima shugo mana"
"To aida juyawa ma zanyi na dauka kunyi barci"
"MARYAMU tayi bacci nice dai idona biyu,daman nasan sai kin fito maimakon kiyi zamanki da sanyin nan kika fito,wannan abu na koda yaushe me gari ma ya gaji da rabiya da shiga tsakani ai sai dai muyi ta addu,a Allah ya kawo mana karshen wannan masifa"
"Hakan shine dai yafi dan abin yafi karfin mutum sai dai Allah mana maganin abin"iya ta fada tana zaunawa a kujera yar tsugunno.
"Hmmm ai abin na jummai kullum gaba yake sai dai Allah ya kyauta"
"Hakane kuma duk halima ta min bayanin abinda ya faru"
"Wlh nima MARYAMU ta fada min,kinsan su bishira ne da tsokana,kuma koda MARYAMU ta kyalesu tofa halima bazata kyalesu ba"
"Ai kema inna ke kika hana MARYAMU take yin fada kuma wannan kamar kin tauyetane,dan da ace tana lakada musu duka da abin da sauki baza suna takalar fadan ba"
"Hakane maganarki amma bazaki gane ba,banason MARYAMU take fada dan idan fadan ya jawo mai gari ya koremu daga garin nan wlh bamu da inda zamuje,kuma muba wani namiji da zai tsaye mana garemu ba,malam audu ne kuma kinsan shi a kaduna yake ba anan kusa yake ba yau kusan shekara biyar bai zo nan ba,kinga kwa gwara muyi hakuri da halin da muka samu kanmu kafin Allah ya kawo mana mafita"

"Wannan ma hakane,to Allah ya kyauta ya mana maganin abin"
"Amin"
"Bari inje in kwanta kafin muga yadda goben zatayi in muna da kwana"iya ta fada tana tashi domin tafiya gidanta.
"Allah ya kaimu da abin aro"cewar inna sarai tana tashi itama domin ta rufe musu kofa dan sanyi ya sakko sosai dan ma akwai garwashi a dakin.



*Rugar* *hardo* *sani


"Nifa sai dai ka saken dan wlh gobe tafiya babu fashi sai dai dan bakinciki ya mutu" cewar lantana tana gyara daurin zaninta.
"Ai daman ni bada izini na kikayi shirye shiryenki ba,shisa yanzu kuma dole ki karbi kudinki a hannun wadanda kika kaiwa ki zauna kiyi zaman aure"baban auwalu ya fada ransa a bace yaga abin na lantana nema yake ya wuce gona da iri,dan gskia shifa bayajin zai iya barin mace ta tafi makka aikatau da aurensa akanta hakan ba mai yiyuwa bane tabbas!
"Nifa nace banyi ko dole ne,dan na fada maka tafiya ba fashi ,ko ka sakeni ko ka rike sakinka ba fasa tafiya zanyi ba,dan daga nan gobe sai dutse gadawur dan jirginmu yana can yana jiranmu,tafiya neman kudi dole bazan zauna talauci ya min kanta ba dan in baka saken bama hakan bazai hanani auren balaraben makka"ta fada wani murmushin yana subuce mata dan har ta fara hangota itada sarkin makka =Ø3Þ suna angwancewa ya fifita ta akan sauran matansa tana haifa masa ya'ya' larabawa.dan kamar yadda kawarta duduwa ta kawo mata wannan shawara,ta tafiya saudi arabia aikatau,kuma ita ta tasa ta saida gaba daya kadarorinta,harda wata gonarta da take tinkaho da ita da kiwonta da duk wani abu data mallaka ta hada duk ta siyar ta biya kudin komai da komai na tafiya yanzu gobe zasuje dutse babban birnin jihar jigawa domin jirginsu zai tashi jibi da karfe takwas na safe.


"Ki tabbatar ya sake ki lantana kafin ki tafi, dan idan sarkin makka ya aureki>Ø-Ýto daga baya idan yaji da aure akanki to watakila asa a ratayeki,saboda kinyi aure akan aure,gwara kije a bazawararki yar gidana"duduwa ta fada tana mika mata hannu suka tafa suna dariya.duduwa kawar lantana ce da sukayi kuruciya tare,bayan tayi aure ta fito zawarci,daga zawarcin ta wuce yawon duniya,kusan shekara uku bata gida shine yanzu labarin mutuwar mahaifinta ya risketa shine tazo bayan anyi sadakar bakwai taje gidan lantana,shine tazo mata da shawarar tafiya aikatau saudiya,ta zo da wani mutum har gida aka gama maganar ya shigewa lantana gaba akayi komai da komai,suma sukaci rabansu shida duduwa,sannan duduwa ta kaita wajen wani malami ko ince rikakken boka' ya bata magani wani turare wanda yake a karamar kwalba yace, "da zarar ta shiga makkatul mukarrama ta shafa sai ta ambaci sunan sarkin makkar sau uku,tokwa duk inda take sarki sai ya nemota ya aureta,itada Nigeria sai ko ziyara, yasa a kawoki a jirginsa ziyara"haka suka kamo hanya suka dawo yanzu gobe zata tafi shine ake hawa sama da baban auwalu dan yace bazai sake ta ba,kuma shi baima amince ba da tafiyar daman bada yawunsa ba tayi shirinta.

"Dan Allah baban auwalu kar kayi sakin nan,duk abinda zata fada maka"cewar innar auwalu
"To yar bakinciki,dan kar in tafi cin shinkafa kaza shine kike bakinciki to wlh nan gani nan bari"
"Allah baki hakuri lantana ba nufina ba kenan,gani nayi mata nawa suke tafiya aikatau kuma da aurensu Amma ke kice sai an sakeki kamar wanda kika kaura har abada."

"Hhhh lallai innar auwalu,to da wa yace miki dawowa zanyi ai sai ko ziyara,kuma koda ace zan dawo ma ba fata ba ai nafi karfin zaman aure da wannan "ta fada tana nuna baban auwalu da duk haushinta ya gama cika masa ciki.
"Dan Allah Inna kiyi hakuri mana,in kinje kiyi ko shekara dayane ki dawo"yahuza danta ya fada idaonsa cike da kwallah dan yasan shirin na innarsa bana dawowa bane,Amma ko yaya lantana mahaifiyarsa ce kuma bayaso ta tafi karma taje ta bata.

"Kai dalla can rufe min baki,banason wannan kidahumin uban naka da talauci ya yiwa baban kamu,nikwa nida talauci munyi hannun riga,Allah ya tsari gatari da saran shuka"

"Nifa dan yayanki nake zaune dake lantana hakinki daman ya dade da isata Amma tunda bakiji maganar mahaifinki ba ,bakiji ta babban danki ba,wane ni ga fili ga mai doki =ØEÞ
@&þduk wanda yakiji bayaki gani ba,kije na sakeki saki biyu,sai ki hada da dayan dana taba miki kinga uku kenan"
"Ayyiriririii "ta rangada guda mai karfin gaske ,tana mai jin farincikin mutuwar aurenta da baban auwalu a bangare daya tana jin nishadi zata kasance mata kuma tauraruwa a gurin sarkin makka>Ø#Ý>Ø#Ý>Ø#Ý





'þ
'þ
'þ
'þ<ØGß<ØGßRAYUWAR MARYAMU<ØGß<ØGß



Story & written by


MOM MASHKUR



Page 39 _40

QALA RASULULLAHI (S.A.W):
MAN KANA YU,UMINU BILLAHI WAL YAUMIL AKHIRI FALYAKUL KAIRAN AULIYASMUT >ØÝ>ØÝ>ØÝ>ØÝ>ØÝ>ØÝ>ØÝ




A yau ne jirgin su lantana ya tashi 'þzuwa kasa mai tsarki,sai dai muce saduwar alkairi.sai mun hadu acan lantana=ØKÜ.

A bangaren su inna sarai kwa,washe gari da safe ta dora kaskon wainarta yar tanderu,mai so da kuli a bashi,mai so da taushe shima a zuba masa.manya wanda bazasu shigo cikin gida ba MARYAMU take karbo kwanikansu ,a zuba musu,amma inna sarai koda wasa bata taba barin MARYAMU tayi tallaba.

Ita take yin waina kullum da safe ana zuwa ana siya,sannan tana zuwa irin kasuwannin kauye tana yin funkaso da taushe.
Ranar litinin taje kasuwar sule tankarkar,ranar juma,a babura,ranar lahdi kuma sai taje gujungu,wannan sana,a da ita innq sarai take fadi tashi da ita take musu yan hidindimun yau da kullum.sannan tana daukan gyada buhhuna tana baiwa yan mai da karago idan sunyi mai sai su bata kudin su sake karbar wata,hakan da Allah yasa mata albarka shine jummai ke mata bakinciki da hassada,har ma da wasu mazauna garin na mai alkama.suna gani itada ba yar gari ba tazo tafi an gari samun budi da rufin asiri,kuma hakan ba karamin sauki bane a wurin masu amfani da gyadar domin da sai sun bada sako kasuwa amma yanzu abu har gida wannan kenan.

"MARYAMU zoki dauki wainar mass kici, idan kin gama shirin makarantar "inna sarai ta fada tana zubawa wani waina, daya bata dari uku zata zuba masa waina, sai kuma taushe a wani kwanan daban.

"Wai MARYAMU bada ke nake ba" inna sarai ta fada da dan karfi dan MARYAMU tajiyota .
"To"MARYAMU ta fada tana kunkuni dan batason cin abinci.
"Ina kike wai ga yara nan yan makaranta sai ca suke in basu kar su makara,amma ke kin shiga daki kinki fitowa.
"Sorry innancy"ta fada tana dariyar wasa,lokacin data fito tana zige zif din jakarta.
"Ke soron gidanku wlh MARYAMU ki kiyaye ni,yar bokon karshen zamani kawai"inna sarai ta fada tana dariyar itama har wasu daga cikin masu siyan wainar suna tayata .
"Inna nifa banason wainar nan,ta ginsheni idan na dawo naci abinci da rana"
"Wai nikam MARYAMU so kike cutar yunwa ta kamaki, jiyama fa haka kika tafi makarantar dare bakici abinci ba,haka kika kwanta.
"Tuwan me kikayi inna"
"Ban sani ba,kedai MARYAMU wlh halin zolayarki sai ke,ba a gabanki na tuka tuwon masara ba?"
"Oh na tuna, tunda bana burabusko bane shikenan"ta fada tana yatsina fuska.
Nan danan idon inna Sarai ya kawo kwalla,saboda tunawa da tayi da inda MARYAMU tayi gadon,son tuwon burabuskom,a wajen mahaifinta tasi,u, a gefe daya kuma tana tuna ranar da zai mutu,yake ce mata.
"Zan dawo da safe ki ajjemin burabuskon nan"
Bata ankara ba taji kwallar na gangarowa,sai tasa gefan fallan zanin data yafa akanta ta goge ba tare da kowa ya lura.
"Kije gidan iyar halima,ki karbo kici shi tayi

Please Login or Register in order to submit comment