Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zama kamar ba,ayi ba" "hakane nagode" "bari inna in tatso madara idan kunje gida sai ki bata" lah ki barshi dan banajin zan iya Kara karbar wani abu da zai fito daga gidanku" inna sarai ta fada "haba inna ai ba,a maida hannun kyauta bayaba" "da in baiwa MARYAMU madarar gidan nan naku gwara ta wuni da yunwa.

Anan inna sarai ta baiwa innar auwalu labarin abinda ya faru, tsakaninta da lantana.
"Oh ai inna lantana ta wuce haka daman bazata taba karbar yarinyar nan ba,dan saboda karta karbeta shi yasa bata je gidan mutuwar sadiya ba,tun ranar kwana uku da ta dawo"cewar innar auwalu tana kallon inna sarai.
"Ikon Allah, wai daman dan karta karbi MARYAMU taki komawa wurin mutuwar" "eh wlh dan ran kwana bakwai ma tana kallo na shirya nida mai gidan namu, amma ta zauna wai ita mai da karago zatayi,yace mata ta hau ya mana goyon biyu muje in akayi addu,ar sadakar sai mu dawo amma taki tayi zamanta muka tafi." "To ai shikenan kanta ta yiwa,nasan dai itama ba a duniyar zata dawwama ba dole wataran ta tafi inda sadiya ta tafi" inna sarai ta fada tana gyara mayafinta dan ya rufe MARYAMU saboda rana.


"Amma inna ki daure ki karbi madarar nan,wlh a jikin akuyata zan tatsar miki ba ta wani ba,dan Allah ki barni in sami ladan marainiyar Allah" "ba komai dan kince akuyar kice,kuma ina gudun daukan alhakinta ,kar mu tafi take kuka a hanya,kuma bani da abinda zan bata" " bari in tatso miki"ta koma cikin gidan da dan sauri"
"Manafuki dai yana wuta"lantana ta fada tana sudar hannun da taci dambu dashi, lokacin da innar auwalu ta shigo cikin gidan.tayi banza da ita dan ganinta take ita da tinkiya banbancinsu kadanne.ta wuce jigon akuyarta wacce bata dade sosai da haihuwa ba, nonon akuyar a ciccike,haka ta tatsa da yawa ta zuba a wata yar jarka mai marfi ta taho ta kawo wa inna Sarai.

"Gashi inna"ta fada yayin da take mika mata " yawwa nagode yarinyar arziki Allah raya miki yaranki" ta karba ta saka jarkar a cikin bakar ledar "aamin"sukayi sallama inna sarai ta tafi ita kuma innar auwalu ta koma cikin gida.

"Ni yanxu ina zan nufa?" Inna sarai tawa kanta wannan tambayar, rugar marayo zan Loma ko kuma wani wurin daban zan tafi? dan wlh bazan iya zama garin da zanke daukan alhakin marainiyar nan ba,gashi bani da inda zanje,wata zuciyar tace,ki tafi rakumi mana.wata zuciyar tace karki je rakumi dan iya tsahare bazata yarda ki rabeta ba>��>��>��nima zan tsaya nan kafin inna sarai ta yanke hukuncin inda zasu nufa ita da tauraruwar MARYAMU.



'�
'�
'�
'�NAGODEE >��>��>��<�G�<�G�RAYUWAR MARYAMU<�G�<�G�


Story & written by


MOM MASHKUR


Page 29_30


Happy birthday mY MUNIB <؂�<�m�<�l�<�a�<�w�Allah yiwa rayuwa albarka =�O�=�O�=�O�



Tana ta tafiya MARYAMU ta farka a barci take kuka, nan inna sarai ta samu inuwa ta zauna,ta sakkota daga bayanta ta zuba madarar a fida, ta bata tasha ta koshi.nan yarinya take ta watsa kafa har da dariyar kuda,inna sarai ta daga ta take mata rawa,dan sai taji farinciki da MARYAMU ta samu madarar da tasha.nan take taji bata jin yunwar da take ji,dan a yau ko ruwa bata saka a bakinta ba,gashi yanzu har la,asar tayi ita kuma ko sallar azzahar batayi ba.


Tana cikin tafiya har ta iso wata ruga,dan ga bukkoki nan tana hangowa,ta karasa wani gida daya fi kusa "Assalamu alaikum"ta fada lokacin da take tsaye daga jikin wani kara da aka tara shi gefe guda."wa alaikumus salam lale marhabin "cewar wata mata da ta fito daga cikin wani daki "yawwa " inji inna sarai
"Sannu bakuwa karaso mana"matar ta fada tana karkade tabarmar kaba domin ta shimfidawa inna sarai "Toh"inna Sarai tace "zauna ga wuri " "Yawwa nagode"ta fada tana mai zaunawa akan tabarmar da aka shimfida mata. matar ta kawo mata ruwa mai sanyi na randa a kofin silba,ta ajje mata "bismillah ga ruwa" Ngd"inna sarai ta fada yayin data dauki kofin silba tayi bismillah ta kafa kai tasha.bayan tasha ruwan nan suka shiga gaggaisawa duk cikin yaren fulatanci. anan inna Sarai take ce mata daman hanya ce ta biyota dan Allah zatayi sallah,"bakomai wlh ga buta"ta bata butar karfe mai cike da ruwa,sannan ta nuna mata bandakin.


Inna Sarai ta kama ruwa, tayi alwala ta gabatar da sallolinta,matar nan ta kawo mata kwanan silba da kuma kwarya da aka rufe da faifai, " baiwar Allah ga abinci" "toh harda wahala kuma"inna sarai ta fada tana murmushi "wlh ba komai ai naga alama ba,a kusa kike ba,dan da alamar kinsha tafiya " "nakwa gode da karramawa wlh,Allah ya biyaki"
"Amin amin " haka inna sarai ta bude kwanan silbar nan danwake ne da mai da yaji sai kuma fura a kwaryar nan,taci ta koshi tasha fura dan batayi fulako ba.domin idan tayi fulako ma bata da abinda zataci in taje gida.

Bayan ta gama ta kara yiwa matar godiya a bisa karamcin data mata,sannan ta mata sallama ta tashi zata tafi,ita kuma ta rakota suna hira kamar daman sun saba "yarinyar nan jikarki ce kika taho da ita" matar take tambayarta "eh jikata ce amma marainiya ce ba uwa ba uba" "Allah Sarki"ta fada cikin nuna tausayawa.

ta rakota bakin hanya ta juya ta tafi,inna sarai taci gaba da tafiya kenan sai ga machine ya taho ta koma gefe da niyyar ratsewa sai taji ance "inna"dagowar da zatayi sai taga mijin lantana "na,am baban auwalu" sai ya tsaya domin su gaisa "tace ina wuninku"lpy" suka amsa a tare" to wa nake gani kamar sarai "mutumin nan na bayan machine din ya fada nice malam Audu" "lallai saduwa tayi wuya " cewar malam audu yana sakkowa daga bayan machine "gskia dai daman kana nan" "wlh ina nan kawai dai ina can kaduna inda nake rani,dan bana shekarata kusan bakwai banzo ganin gida ba,kuma ban fi sati biyu da dawowa ba " "Allah sarki ni ince ka dade baka gewaya wajen namu ba " cewar inna sarai "daman ina sanya ran kafin in koma nan da sati biyu zan ziyarceku"malam audu ya fada "Allah sarki Allah kaimu " 'amin "ta "inna daga can gidan kikene "baban auwalu ya tambayeta "eh"ta bashi amsa a gajarce "to madallah,amma inna ina ganin ki hakura da zuwa wajen lantana haka,domin wahalar tayi yawa wlh domin ba canja ta,ayi zatai ba" "ai daga yanzu bazan kara zuwa ba" "yawwa inna dan lokacin da naje nace ki bamu yarinyar nan in anyi bakwai baki ga cin mutuncin data min ba, wai naje na tambayi yarinya bada izininta ba,to idan na karbota sai inzo in riketa sosai ta tada min hankali kamar ba yar zumunta ba"


"Hmmm ai amana batace haka ba komai lantana ta gani wurin sadiya tace tana so to sadiya kwa zata bar mata shi har abada,duk kayan kwallar(kayan lefe) sadiya lantana ce ta dauke mafi yawansu kai har daki take zuwa ta bude loka ta dauki abinda takeso koda sadiyar bata nan idan zata fita tace min idan sadiya tazo ince ta dau kaya,wlh idan na fadawa sadiya ko bacin rai bata nunawa sai dai tace Allah sarki lantana ai da ta bari na dawo mun gaisa,amma yau sakayyar da lantana zata yiwa sadiya kenan "inna sarai ta fada abin na mata ciwo "Allah kyauta "cewar baban auwalu.

"Sarai ina labarin dan nawa"malam audu ya fada yana dariya(malam audu abokin mijin inna sarai ne wato malam buba) amma ba ruga daya suke ba.
Maimakon inna Sarai ta bashi amsa sai kawai yaga tana share hawaye "allah sarki tasi,u kake tambaya "cewar baban auwalu ba tare da malam audu ya bashi amsa ba yaci gaba"ai tasi,u allah yayi masa rasuwa watanni uku da suka wuce" "innalillahi wa innaa ilaihir raji,un Allahu akbar wlh ban sani ba"cewar malam audu yana jinjina al,amarin.nan dai baban auwalu ya shiga bashi labarin komai har mutuwar sadiya matar ta tasi,u da kuma halin da Inna sarai ke ciki a rugar marayo.


"Kai subhanallah,lallai sarai kinga tashin hankali wlh,ita kuma yarinya Allah rayata,ke kuma Allah baki ikon cin jarabawa, dan wannan gaba daya jarabawa ce. "Amin"suka amsa ita da baban auwalu.

" Tunda yanzu gaku daman inaso in samu wanda zai min cinikin gonar wajen marigayi daya bari,rabi ce amma kuma tana da girma sosai,malam audu kai ka santa,to inaso a siyar da ita domin zan tashi daga rugar marayo, in koma wani wurin da baza,a tsangwame niba kodan saboda MARYAMU in sayi wurin zama, inyi jarin sana,a sannan in siyawa MARYAMU madarar bature ta gwangwani.



<؂�<؂�<�m�<�l�<�G�<�G�RAYUWAR MARYAMU<�G�<�G�


Story & written by


MOM MASHKUR


31 _32




"Allah sarki sarai gskia kinyi tunani,kuma insha Allah komai zai zo da sauki,gobe idan Allah ya kaimu zan samu mai siya aje aga gonar a taya,idan tayin ya miki sai a siyar da ita.
"Ba komai malam audu duk yadda aka taya indai ya maka to ka sallama musu, dama ni ba aikina bane bansan kudin gonar nan ba,dan haka na wakilta ka "
"To insha allahu zan rike amana,zamuje da shedu da komai ayi ciniki,kuma mai siyan gonar ma bazaiyi wahala,saboda gonar wurine mai kyau kasar wurin mai kyau ce"malam audu ya fada yana cire wata kaya data makale a jikin babbar rigarsa.
"Kuma malam kana ganin za,a samu mai siya acan rugar marayo din,ko kuma da mai siyen za,aje can rugar"
"Eh to kaima baban auwalu kayi magana,amma ni ina ganin aje da mai siyan yunda yan rugar marayo suna nuna musu kyama,ina ganin bazasu yarda su siya ba,zadai mu gayawa hardon rugar cewa za,a siyar da gonar marigayi malam buba makama dan kar yaji yawai,yanzu daukana zakayi a machine muje wurin wani mutumena idan zai siya mini"
"To shikenan Allah yasa haka shi yafi alkairi"
"Amin"inna sarai da baban auwalu suka Amsa a tare
"sarai muje gida kici abinci kidan huta,in yaso idan munje wurin mutumin nan wanda zan masa tallan gonan mun dawo,sai baban auwalu ya kai ki gida a machine"
"Nikam a koshe nake wlh wancan gidan da kuke hangowa,ta nuna gidan data baro yanzu,can na ratsa domin nayi sallah matar gidan mai kirki ta gabatar min da abinci naci na koshi ba tare da tasan koni wacece ba"
"gskia toh ai can gidan ne gidan malam audun"cewar baban auwalu yana yiwa inna sarai dariya=��.
"Ikon Allah,kaga hikimar ubangiji ko,gskia matar nan tana da kirki kaga da rashin kirkima ta mini yanzu in muka koma da mai gidan sai taji kunya=�H� shisa akeso mutum ya kyautata ma,a mala da mutane "inna sarai ta fada tana yabawa da karamci irin na matar malam audu.
"Allah sarki ai kande haka take da kirki,koda acr ace abincin da zataci ne kawai a gidan to zata hakura ta baiwa baki"
"Amma na yabawa kokarinta"inna sarai tace tana jijjiga MARYAMU
"Mu karasa gidan ki sauketa ki bata madarar tasha,karki barmin matata da yunwa"malam audu ya fada yana dariyar su ta dattijai.
"Gskia dai"shima baban auwalu ya fada yana dariyar.
"To MARYAMU me gidanki ya bada umarnin aje a baki abincinki,duk da dai tsohone sai dai kici kudinshi ba aurenshi zaki ba" inna sarai ta fada tana dariya, sai kuma ta bisu a baya domin komawa gidan na malam audu.

"Amma sarai ki bari ki kwana anan,gobe idan Allah ya kaimu sai baban auwalu ya kaiki gidan, tunda ba wani abu zakiyi a gidan ba,kinga goben sai ya kai ki koda hantsine"
"Eh to banki ta taka ba, amma kamata yayi in tafi gida saboda,ni da nake shirin tashi daga gidan inje in kikkintsa abubuwa ko ya ka gani"
"Kema da gskiar ki,to amma shi cinikin ba lallaine a gama a goben ba kamar yadda kika bukata,sannan kuma dole sai an samu inda za,a siya miki,kuma ba lallai ne tayin da za,a yiwa gonar ya zama wanda za,a sallama ba,dan idan akaga anaso a siyar za,ayi tayin wulakanci ,duk da na yadda da mutumin da zan tallatawa amma sai anbi komai a sannu"

"Amma kuma kawai sai inzo in kwana haka ake"

"Ai Bamako kwana daya ba,da son samune ma ki zauna har a gama komai, a sama miki inda zaki koma,dan insha allahu bazan koma rani ba, har sai naga komai ya kammala,wato in nace komai ina nufin har sai an samu an siyawa amaryata MARYAMU Abin da za,ake bata duk da kince na mata tsufa=�t�<��� ya karashe yana dariya"

"Gskia malam nima haka nace" baban auwalu ya fada shima cikin raha"

"Yo malam audu kai in an baka tsaleliyar mata kamar MARYAMU Sai ka karba"inna sarai ma ta fada tana dariya

"Me zai hana sai inki karba ai taimaka mata zanyi"

"A ah gskia bazan baka MARYAMU ba,ka zauna da kandenka amma MARYAMU ta mai rabo ce"

"Haka kika ce"

"Eh"
"To ai shikenan"
"Da yafi dai malam dan naga inna ba baka jikar nan tata zatayi ba "baban auwalu ya fada yana dariya,dan wasan nasu ya bashi dariya,yarinyar
dake goye mai kwanaki hamsin akewa zancen mijin aure,kodan girman dan mutum ba wuya kamar yau ne ya fada a zuciyarshi.

"Yanxu dai ki kin yarda zaki zauna anan din,har a gama komai "

"Nifa malam audu baki nayi ba, kawai dai ai da nauyi,kuma ban dauko kayan sawana ba,sai na MARYAMU kala biyu shima dan na dauka lantana zata karbeta ne "

"Babu maganar nauyi dan nine nace ki zauna,kuma gidan nan dai gidana ne,sannan in maganar kande kike wlh bata da wata matsala,dan dazuma da tasan ke matar malam buba ce bazata barki ki tafi ba, har sai na dawo,Dan haka kibar maganar jin nauyi"
"To shikenan zan zauna,amma dai zuwa gobe zan koma,hakan ma dan kar kaga ban kyauta maka ba"
"To hakan yayi,ni saboda MARYAMU ma kinga anan akwai madarar da zakina bata,sabanin can da babu wanda zai baki koda kuwa da kudinki bare kyauta"malam audu ya fada dai dai lokacin da suka karaso kofar gidan nashi.

"Assalamu alaikum"suka fada su ukun a dai dai mashigar gidan.

"Assalamu alaikum"
Suka kara fada ,amma shiru ba amsa. Bismillah ku shigo malam audu ya fada yana shiga cikin gidan. "Kande, kande " malam audu audu yake kiranta "ehemm "kande tayi gyaran murya daga cikin bandaki. "To to, to ashe magewayi kika shiga "malam audu ya fada yana shinfida wata tabarma daya dauko a jingine a jikin maina, ya shinfida daga gefen wacce ya gani a shinfide.
"Zauna sarai kafin kanden ta fito man,kaima baban auwalu bismillah" suka zauna gaba dayansu,can sai ga kande ta fito daga bandaki,hannunta rike da buta,tasa kasa ta wanke hannunta sannan ta nufo inda suke fuska a sake,take cewa "lale marhabin sannunku da zuwa,bakuwata barka da dawowa "tana dariya "ashe kin ganeta "cewar malam audu "haba yanzu fa ta fita na kasa shaidata,yo ai ko nan da shekara ta dawo zan shaidata,idanuna garau suke =�@�ta fada cikin zolaya."Hmmm hakan dai bazai hana na auro amarya ba kwanan nan" "Allah kawota ta fada tana samun wuri ta zauna kusa da inna sarai. "Bari dai in baku ruwa "ta tashi ta nufi daki ta dakko ruwa ta kawo musu. Anan malam audu ya shiga bata labarin wacece inna sarai, kuma halin da suke ciki a rugar ita da MARYAMU, da kuma zaman da zatayi a gidan zuwa gobe,da kuma abinda za,ayi goben na batun sai da gona.

Allah sarki kande har da kukanta,ta tausayawa MARYAMU matuka da inna sarai na halin da suka tsinci kansu.anan ta mata gaisuwar rashin malam buba da marigayi tasi ,u da kuma gaisuwar surukarta sadiya wato mahaifiyar MARYAMU. anan ta dora da cewa "wlh da nasan kece da bazan barki ki tafi ba, har sai malam ya dawo,dan yana cewa zamu rugar ya ganoku kuma in miki gaisuwa malam dan lokacin daya rasu mun tafi rani,shima malam acan wani dan nan wajejen nan ya fada masa shine ya taho yayi gaisuwa,gashi mun shafe shekaru bama nan,wlh bamu da labarin mutuwar tasi,u ma data sadiya,duk da bamu taba haduwa ba amma inajin labarinki a wurin malam" kande ta fada tana share hawaye>�&�
@&�"lah ba komai wlh,ai rashin sani yafi dare duhu,ni na gode ma da karamcin da kuka mini, a lokacin da kowa yake kyamarmu nida marainiyar Allah "inna sarai ta fada idanunta na kawo kwallah=�"� "sai dai ince Allah biyaku da mafifincin alkairin da kuka mini,Allah baku ladan zumunci amin =�O�




'�
'�
'�
'�<�G�<�G�RAYUWAR MARYAMU <�G�<�G�


Story & written by


MOM MASHKUR


Page 33 _ 34


WASHE GARI


Da sanyin safiya baban auwalu yazo gidan malam audu,suka tafi rugar marayo,domin haduwa da mutumin nan mai siyan gona,bayan sunje jiya da yamma sun mishi bayani ya kuma nuna yanaso ya siya,sai yace gobe zasuje ya gani sai, dillalai su yiwa gonar kudi idan yaga ya zai siya a yadda dilllalan suka yanke to zai bada kudi hannu,idan kuma bai mishi ba, to sai su samu wanda zai siya.to shine yau zasuje can rugar marayo inda mai siyan gonar ma zai je domin a karkare ciniki.


*BAYAN* *SHEKARA* *TAKWAS*


*KAUYEN* *MAI* *ALKAMA*

Kauye ne dake karkashin karamar hukumar sule tankarkar,dake jahar jigawa.sannan akwai kananun kauyuka da suke makotaka da kauyen ba mai alkama,wanda basu kai shi girma ba,cikikwa har da kauyen rakumi,sannan akwai rugage da suka hada da rugar marayo,rugar hardo sani da dai sauransu.shi wannan kauyen na mai alkama anan ne malam audu ya siyawa inna sarai gidan da zasu zauna itada MARYAMU,cikin kudin gonar da aka saida mata,sannan ya siyo manyan gwangwanayen madara na yara domin ake shayar da MARYAMU,sannan ta dauki jari da zatake sana,a dashi sauran kuma ta baiwa malam audu ya siyawa MARYAMU ko karamar gonace,a ajje har lokacin da zata girma saboda gadon tane na wajen mahaifinta,dan abinda sadiya ta bari na kayan daki da kayan saw a,duka lantana taxo da amalanken shanu ta tada fitina wai kayan yar uwartane,itakwa inna sarai ta barta ta kwashe,ta fada mata kayan Marainiya ne amma ta kekashe kasa tace inna sarai keson danne kayan.haka ta tattara duka ta tafi dashi,Allah shiryeki lantana.


Kauyen mai alkama Kauye ne da yake da dan girma,kuma a garin akwai kasuwa da take ci duk ranar asabar.A cikin garin mai alkama akwai makarantar boko tun daga primary zuwa j.s.s 3 day ne,sannan suna da makarantar allo inda wannan makarantar allon itace a matsayin islamiya,dan yara maza da mata anan suke daukan karatu.suna hura wuta a makarantar idan da sanyine,domin bawai ajijiwa bane,kawai filine aka ware,sai su shimfida tabarmi kowa ya zauna bangaren maza daban na mata daban.

Yau ma kamar kullum bayan an taso su ita da kawarta halima wacce ake kira da (hali) suna tafiya suna nuna karantun da aka dora musu yau "gskia MARYAMU sai dai idan nazo gidanku ki tuna min domin ni wlh ban iya ba, da ace aya biyu ake dorawa da sai inke kokarin biyawa ina bada harda,amma dan muguntar malamin nan sai ya dora aya 4 kuma idan baka bashi harda ba ya dakeka,ke koda tini ya wuce uku sai ya maka bulala gskia ni na gaji " hali ta karasa mganar kamar zatayi kuka dan tasan kashinta ya bushe Matukar asabar tazo bata iya karatun harda ba.

"Nace zan koya miki gobe idan mun dawo daga makarantar boko sai kizo gidan mu muyi karatun tare,nima ran juma,a sai inje gidanku mu nina"MARYAMU ta fada tana dafa kafadarta,itama hali ta dafa kafadarta suke tafiya.

Yarane yan kimanin shekaru takwas,kusan kansu daya farace da kuma baka.MARYAMU kenan da kawarta halima,makotane dan katagarsu ajinsu daya a makarantar boko wato primary 2 yanzu suna shirin yin jarabawar karshen zango na uku domin shiga aji uku kunsan makarantar kauye >�*�yara kanana sai Kaga sun gama primary scul.

"Kema hali idan kika dage iya karatun nan zakiyi"
Hmmm haka kike gani dan kinga ke kina da kokarinki,shi yasa nikwa banni "
"Hhhh kina da abin dariya nima ba kokari gareni ba dagewa nake �kema idan kina dagewa zakina bada harda kema kamar ni"MARYAMU ta fada tana mai nuna kanta.

"Na shigesu wlh ga bishira nan da habasiyya"
"Dallah can banza meye na cewa kin shigesu,ni ba yarinyar da nake tsoro wlh ko dambe za,ayi sai dai ayi daman zun s���� 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~�aba mahaukata"hali ta karasa tare da jan wata tsuka
"Nifa banason muke fadan nan, kuma kinsan ba tsoro nakeji ba kawai dai banason ake kaiwa inna karata ana cewa munyi fada kinga ta hanani kula su bishira muyi fada.
"To tunda su suke janmu da fada,ai bama kyalesu....naganar tata ta katse dai dai karasowar su habasi da bishira ,dan ganin sun zo sun sha gabansu,ma,ana sun tare hanyar da zasu bi su wuce.

"Wace yar kazar ubance a cikinku ta cewa malam aramma na tafi shagon emeka "bishira ta fada tana kama kugunta da hannu biyu.

"Wlh kema bishira ke kike tambayarsu,akwai wanda zai mana wannan gulmarne inba wadan nan ba" cewar hali tana nunnunasu da yatsa.

"Ke habasi matsa Mu wuce dan shiru shiru ba tsoro bane gudun Maganane" halima ta fada tana me cin damara da dankwalinta data daura akan hijabinta.

"Dan Allah hali ki kyalesu,kar muyi fada dasu tunda munsan bamu muka fadawa malam dinba ai shikenan"MARYAMU ta fada cikin sanyin murya da sanyin halinta,dan bata son tashin hankali,domin yanzu daga sunyi fadan su bishira zasuje gidajensu su fadawa iyayensu,su kuma iyayen suje su samu innarta wato inna sarai suci mata mutunci.

Ke dalla rufewa mutane baki ,me kama da aljannu, ni ko kallonki banasonyi saboda kar inkeyin mafarki,wannan fari kamar yan yalabijin din nan da muke gani masu gashi har gadon baya"habasi ta fada tana kokorin cin kwalar halima,aikwa aka fara dambe nan fada ya kaure,yi ake tumumur tumumur,habasiyya sau biyu tana shan kada,ita kuma bishira ta kama MARYAMU tana dukanta,amma MARYAMU ko sau daya bata kai hannu ba,halima takai habasiyya ai habasi na mikewa sai ta ari na kare,taga uwar bari.bayan habasiyya ta gudu sai halima ta koma kan bishira aka fara gabzuwa kamar yan dambe,Allah sarki MARYAMU sai rabasu take amma basu rabu ba.har sai da allah ya kawo wani saurayi yazo wucewa,ya shiga rabasu,halima ta kale bishira amma bishira taki hakura.

"Ke ba na rabaku ba"ya fada yana wani cin magani.
"Anki a rabu din kai ubanane"ta fada tana rike tsantsa .

"Ke karki min rashin kunya,yanzun nan in babballaki ,in taken rashin kunya kike na dameki na shanye"
"Kar ka fasa ballanin dan....=�I�ta dura wani zagi mai maiko,nima rufe kunnena nayi saboda tsaro.
Ai beyi wata wata ba ya kwasheta da wani mari,wanda yasa taga gilmawar wani haske,kamar wuta.aikwa tayi kokan kura ta dane jikinshi da makale wuyansa,tana yagonshi har da cizo, da yaga tana karkace masa jiki kamar wanda mage ko kare ya yayyyaga,dan inaga tafi wata va yankan farce lol
Sai ya bambareta ta warbar da ita,ya hada hannayenta wuri daya ya rike.
"Kuyi tafiyarku MARYAMU,wannan mai gadon masifar bazata barku ba.suka juya sukayi tafiyarsu,shima ya hankadeta ya juya ya tafi.bishira da taga haka sai ta dage karfinta
"Banza dan iska sai na maka sharri" ya dawo da baya "karya kike karamar yar iska,dan kina zuwa shagon wancan inyamurin yana lallatsaki kin dauka kowa ma haka yake ? Banza kwaila kawai"ya fada yana mai cigaba da tafiyarsa.


Lokacin dasu MARYAMU sukazo kofar gidajensu,sai suka yiwa juna sai da safe,dan ko a hanya kasa yiwa juna magana sukayi,kawai tafiya suke ita MARYAMU tana tunanin abinda zaije yazo,ita kuma halima tana ta maida numfashin damben da sukayi.haka kowacce ta shiga gidansu.

"Assalamu alaikum"

"Wa alaikumus salam,yan makarnta an dawo " Inna sarai ta fada tana tashi zaune daga kishingidan da take, takai hannu ta rage sautin radion da takeji.
"Eh mun dawo inna"ta fada tana zama akan kujerar yar tsugunno da take kusa da tabamar da inna take kai a gaban kaskon da ta kawo garwashi dakin saboda sanyin da akeyi.
"Kun dade yau ,dan har an fara taskar labarai

Please Login or Register in order to submit comment