Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jiya tana cemin bari taje ta lika,kiyi sauri kar ki makara"
"Har taci ma ai da sauran lokaci,yanzu bakwai da rabi ma bata karasa ba,danma dai yanzu ba damina bace da malaman sai sun dawo daga gona suke zuwa makarantar, dan dai ma gwamnati ta tsaurara yanzu,makarantatun kauyen ma malaman na kokarin zuwa"wani yaro dan j.s.s. 3 ya fada mai sanye da uniform na yan junior scul.
"to bari in hanzarta"MARYAMU ta fada tana tafiya,domin fitowa daga gidan nasu.
Tafiya take a nutse sanye take da riga da wando da dankwali kayan blue, ne sai farin hijabi,kayan a wanke suke kal kal,sai sandal na roba.
"MARYAMU har kin shirya,akwai layin waina a wurin inna?"wata yar ajin su MARYAMU dake sanye da uniform ta tambaya.
"Eh na shirya,kinsan wurin wainar inna bai rabuwa da layi,sai dai kije ta nema miki alfarma a wurin wadanda ba yan makaranta ba,dan kar kiyi latti.ta fada ba tare da ta jira amsar yarinyar ba,ta shiga gidansu halima.
"Assalamu alaikum"

"Wa alaikumus salam"halima dake fitowa daga bandaki ta amsa mata.
"Yar uwa har kin shirya"cewar halima tana kokarin ajje butar hannunta.
"Kin ganni na shirya,zoki zubo min tuwan nan inci,dan bazan dauki wani kwano ba zuwa gidan mu ba.

"To sarkin yan son burabusko,daman dazu iya ke cemin in kai miki ko zaki ci.
"Ke kuma yar bakin ciki shine kika ki kai min"ta fada tana zaunawa akan wani turmin daka da aka kwantar dashi a wajen.
"Hmmm kedai bari MARYAMU,nida na samu burabuskon nan da taushe naci,kwana nayi ina zuwa bandaki,gashi har yanzu ma be tsaya ba,nasha magani ma amma kamar ban sha ba"
"Hhhhh gskia kin baiwa masai hakkinta" MARYAMU ta fada tana cigaba da dariya.
"Allah shiryeki"ta fada lokacin data zubo mata tuwon.
"Bani inyi sauri inci in tafi'
"Mu tafi dai"
"Au wai kina nufin kina gudawar zaki makaranta,to sai dai kowa ya tafi daban,kar ace ina warin kashi"= MARYAMU ta fada da zolaya.
"Dadinta ma kowa yana yin kashi"hali ta fada tana murguda baki.
"Ba irin naki ba,muje dakin inci mu tafi,wai ina iya take"
"Iya taje karbar kudin daddawa da take bin bashi,shine zata karbo don tayi sautu kasuwa"

Bayan MARYAMU ta gama cin tuwon suka fito domin tafiya makaranta,sun fito kenan suka hadu da iya zata shiga gidan.
"Iya ina kwana"cewar MARYAMU.
"A ah yan makaranta lpy kalaw MARYAMU, an fito"
"Eh mun fito"suka fada suna hada baki.
"To a dawo lafiya ,ayi karatu dakyau "ta fada tana zaro naira ashirin daga cikin kudin dake hannunta.
"Ku ungo kowa goma goma"
"An gode MARYAMU ta fada tana sanya hannu biyu ta karba."
"Sai mun dawo iya"suka Halima ta fada tana kama hannun MARYAMU suka shige gidan su MARYAMUn.
"Assalamu alaikum"
"Wa alaikumus salam" wata mai siyan waina ta amsa.
"Inna zamu wuce"cewar MARYAMU.
"Inna ina kwana"Halima ta fada tana murmushi.
"Lpy alhamdulillah, ku je kar ku makara,ku karbi kudin makarantar"ta fada tana miko musu ashirin goma guda daya,sai biyar biyu.sai kuma alewar tsinke guda biyu.
"An bamu kudin makaranta"MARYAMU ta fada tana daukan akewar ta b dau daya taba halima daya.
"Sai mun dawo"suka fada suna ficewa daga gidan ba tare da sun jira inna sarai ta ce wani abu ba.


Sun fito kofar gida kenan,suka hadu da jummai mai dambu tana kokarin hawa machine.
"Sule tankar kar zaka kaini,wajen yan sanda.ta fada tana daga murya dan su MARYAMU suji.....




*Ayi* *hakuri* *da* *wannan



'
'
'

Story & written by


MAMAN AFRAH


Page 41_42

*Allah madaukaki sarki yace a cikin hadis qudusi* *yaku wadanda* *kukayi imani kuci daga* *tsarkakan* *abubuwan* *da* *muka* *azurtaku* *dashi kuma kuyi aiki* *nagari*.



Happy new year 2021
Kamar yau 2020 ta kama gashi har ta kare,lallai akwai kalu bale a rayuwar dan adam,allah ka bamu ikon aikata aiki na kwarai.Allah ka sadamu da alkairin dake cikin shekarar ka karemu da dukkan sharrin dake tattare da ita=O=O=O=O



A bisa zato da mutane da dama da suke min akan bice m.shakur,nasan mafi yawa kun santa marubuciyar" two different world" to daga yanzu zan dena rubuta mom mashkur in ke rubuta MAMAN AFRAH ina fatan kun gane=



Wannan shafin naku ne inajin dadin yadda bakwa gajiya wurin min comment

_Queen fulani
_ matar so
__zaitouna_ m. haris
_ _mmn_ twins
_ _pretty_ _mrs_ zdeen
__miss_ husna
_ _hanoupa_ wob
__ _maryam_ Ibrahim
_ _mmn_ sultan
__mmn_ muhammad
Ina gdy da addu,oinku ana tare>>>





"Kai baka isa bafa,ka dauka bagidajiya ka dakko,har zaka wani ce in baka dari biyar,sau nawa ka kayar dani a hanya ? Kuma ma ina sule tankar kar ina mai alkama da zan biya dari biyar"cewar jummai tana wani zazzare ido,tana masifa.
"Idan kin isa kice shege nake,wlh dari biyar zaki bani,kuma da kike maganar faduwa wane shegen yace kiqi gyara zamanki "
"Daman ba iya machine din ba kayi,in zaka karbi dari uku ka karba" ta fada tana mika mishi dari ukun.
"Billahil azim baki isa ba,bayan nace muyi maganar nawa zaki bani kikace mu tafi kawai baki da matsalar kudi,kuma yanzu kizo min da maganar banza,bayan kowa yasan kudin machine din daga mai alakama zuwa nan dari biyar ne,wlh ko kiban hakki na ko kuma ni in kaiki wurin yan sandan su karba min,suma suci rabonsu" ya fada yana kallonta da jajayen idanunsa
"Marbi nan inka cuceni Allah ya saka min,bayan ma baka kowoni wurin yan sandan ba"ta fada tana mika mishi darin biyar.
"Kya nemi inda yan sandan suke,aikin wofi" ya fada yana buga machine dinsa ya barta a wurin.
"Shege da gani ma dan shaye shaye ne,nima kome ya kaini hawan machine dinsa shi daba dan garinmu ba,daga ganinsa ya kawo wani" ta fada tanayin gaba.

"Bayin allah ina ne ofishin yan sanda"jummai ke tambayar wasu samari dake zaune.
"Sun tafi koyan sallama"dayan ya fada yana dauke kansa yaci gaba da danna wayarsa.
"Karku fada din in ku kadaine a garin"ta fada tanayin gaba.
"Baabaa wannan matar fa akwai yan sulalla a hannunta tunda kaga tana neman inda yan sanda =h
'><
'suke" dayan ya fada yana kallon inda jummai tabi.
Tana cikin tafiya ta hadu da wata mata ,ta tambayeta ta kwatanta mata,"idan kika bi lungun nan yana fita zaki ganki a bakin kwalta,to zaki ga wani gini da aka kewaye na siminti daga bangaren hagun wajen asubiti ne"
" daman nan ne,ai nasan asibitin muna zuwa dubiya tsallaka kwalta zanyi kawai ma"
"Eh"
"Ngd"jummai tace tana yin tafiyarta.itama matar tayi tafiyarta.

Haka jummai tabi ta wannan lungun dazai sadata da bakin kwalta inda police station din da zata kai kara yake.ta shigo tsakiyar lungun da duk ba mutane duk suna cikin gida,sai wani yaro yana daukan ruwa a karamar jarka,bayan ya gama ciki jarkar jummai dake jin kishi ga rana tayi,taje gindin famfon nan ta ajje jakarta yar pos me zip guda daya,ta wanke hannunta ta hade hannun biyu ta sunkuya a famfom take sanya bakinta take shan ruwan a tafin hannun nata.wannan saurayin dake biye da ita bata sani ba ya fito faga maboyarsa a guje ya dauke pos din ya zura a guje kamar walkiya,kafin jummai ta farga har yasha kwana,ihu take tana kiran jama,a ku taimaka min zai gudu da kudi= amma ina ba wanda ya fito tsabagen takaici a wurin ta zauna take hawaye, sai ga wani mutum yazo wucewa,
"Baiwar Allah lpy kike kwa,ya kika zauna ruwa yana jikaki? Yakai hannu ya kashe famfon, Sai asan nan ma jummai ta lura da famfon data bari a bude,ruwan yana gangarowa inda tayi zaman yan bori yana jikata.

"Dan Allah malam ka temakeni,wlh wani saurayi ne ya dauke min jakar kudina ya gudu"
"Kekwa baiwar Allah garin ya haka ta faru?"
"Wlh jakata na ajje anan zansha ruwa yazo ya dauke ya gudu"
"Tap bata garine Allah dai ya shirya,sai dai kiyi na annabawa,dan wannan bazai tsaya inda za,a ganshi ba"yayi gaba abinshi.
"Na shiga uku na lalace,wayyo ya zanyi"
Ta fada tana tashi tabi hanyar daya bi,amma ko mai kamarshi bata gani ba,haka ta dawo ta nufi wurin yan sanda domin su mata bincike su gano wanda ya dauki jakarta> tirkashi=.

Wasu yan sanda na hango su biyu a tsaye a bakin wani office suna tattaunawa,sai suka hango jummai na tahowa.
"Yallabai ga wata mata nan kuma da alama daga kauyen garin nan take,kaga tunda d.p.o baya nan ma kwashi rabonmu"
"Eh kaga ko karyawa bamuyi ba,ga wacce zamu wanka" dayan ya fada.
"Assalamu alaikum"jummai ta fada a tsorace dan da gansu da uniform dinsu sai taji wani mugun tsoro ya saukar mata
"Barkanki da zuwa,wurin yan sanda"daya ya fada a maimakon amsa sallama.
"Ftn kinzo akan gskiarki,dan idan bincike ya nuna baki da gskia to sai na daureki har igiya tayi saura" dayan ya fada yana bata rai sosai, dama ya fadi hakan ne dan ya tsorata ta yadda zasu ji dadin cin kudinta,dan yaga gaba daya a tsorace take kamar ace kamota ta zuga a guje.

"Ina kwananku yallabai"jummai ta tsugunna har kasa ta gaishesu.

"Tashi, tashi bar gaisuwar nan, muje daga ciki"daya ya fada yana yin gaba,shi kuma dayan yabi bayan jummai suka sakata a tsakiya,dan sun kosa ayi komai a gama kafin d.p.o ya dawo daga inda yaje,su karbi rabonsu karya kawo musu matsala.

"Meke tafe dake"suka hada baki wajen fada
"Yallabai daman kara na kawo,s
Wani ne ya dauke min jakar kudina" ta fada tana hawaye dan gaba daya a tsorace take,kuma tama manta meya rabota da garinsu,wato kawo karar su inna sarai dan ita yanzu jakar kudinta ne a gabanta kudin mutane da zata kaiwa me daukan adashe dubu ashirin,da kudinta dubu goma sha biyar na ridi data saida da kudin bishira data ke tara mata,dubu hudu ga kudin dambu,kai gaba daya tattalin arzikinta yana cikin jakar nan.
"O my God>&
B&"dayan ya fada yana zaunawa daga tsayen da yake,ya zauna akan benci ,dan jin babu kudin ma sai an nemo a inda aka dauke.ta bata musu plan din da suke.
"Yana ina? Inkin ganshi zaki iya ganeshi?" Ya jefo mata tambayoyin a lokaci guda.
"A ah Yallabai kafin in kalleshi in shaidashi ya gudu sai bayanshi na gani amma na shaida rigarsa,shudiya ce"ta fada da sauri dan zuwa yanzu,jikinta kar karwa yake sosai saboda tsoron yan sandan nan ga wata yunwa data addabi yayan hanjinta ko karyawa bata tsaya yiba tana saurin dakko dan sanda,gashi yanzu tanajin kiran sallar azzahar a masallaci dake Bayan police station din.
"Ke banda kin rena mana hankali kizo wurinmu kawo karan wanda baki sani ba,baki san inda za,a sameshi ba"dan sandan ya fada yana matsowa gabanta,ya mata wani kikam dan yanda yaga ta tsorata so yake ya sanya tayi fitsari a wando.
"Dan Allah kuyi hkr wlh na janye karan"ta fada duk ta hads xufa duk da ranar bata zafi saboda lokacin sanyine.wlh sai kin shiga cell na thirty minutes ya fada yana korata cell din,yasa kwado ya rufe.bayan ya rufe ya jiyo abokin aikinsa na magana,a waya
"Ok sir Allah bata lpy,to insha Allah.
"Matar oga ce (d.p.o) ce take nakuda sun tafi kaita asibin,yace a Kula da komai"
"Ok" yace yana kishingida.
Jummai tana cikin cell abin duniya ya isheta,ga yunwa da dana sanin zuwanta police station ya isheta ga batan jakarta,Amma tasan duk alhakin su inna sarai ne,tunda tasan basu da lefin komai, itake sanya bishira da habasiyya su ringa jan su MARYAMU da fada kuma tayi sharrin an matse yarta ne a lungu dan idan yan sanda sunzo su ,sanya mai gari ya koresu daga mai alkama, dan bata kaunar ganinsu saboda kyan MARYAMU gani take kamar idan sun zo yanmatanci samari zasuke ta zuwa wurin MARYAMU su bar yarta baka mummuna,sai gashi ido ya juye da mujiya.(hassada mugun ciwo).

Misalin karfe biyar suka tina da ita a cell dan sun manta ma da ita,dan sunci doya da kwai a wurin wata mai kawo musu bashi sai wata su hada mata kudinta.suna zaune suna ta yin sulhun kararrakin da aka kawo har sauran yan sandan da sukazo daga baya,wanda basa nan jummai tazo station din,suna ta karbar cin hancin suna rabawa suna soke kayansu a aljihu,dan har sannan d.p.o din bai dawo ba,dan c.s. ma aka yiwa matar tasa.
Garamm aka bude kofar cell din,jummai dake kwance xuwa wannan lokacin duk ta gama galabaita da yunwa,tana tunanin da a gida take da tacj dambunta ta koshi,amma yanzu ko ruwa bata samu ba.
"Ke dalla malama taso ki kama gabanki,ku kun rainawa kakinmu hankali komai ma ku kawo mana kara, da abu mai muhimmanci da wanda bai kamata a kawo ba kuzo ku damu mutane,to da kina da kwandala ma da sauki amma haka nan zagadam zagadam kizo zowa matane,tashi mana"

"To yallabai" ta tashi daker ta saka takalmanta ,dana kalleta naga har ta fada kadan,sai taban tausayi= haka ta fito dan sandan ya kulle cell din ya biyo bayanta,daya daga cikinsu yace "ke mantawa ma akayi dake,gashi kuma ba,a samu na kullewa ba,bare akaishi a ganki a ciki a tina dake jeki an sallameki"
"To" ta fada tana kokarin fita daga station din.
"Tab yau da oga yazo ya tarar da ita da duk sai rayukanmu sun baci"daya ya fada yana cin goron daya fiddo a aljuhunsa.




_KANO_ STATE


wata mata na gani zaune akan kujera tana rike da remote a hannunta,da take kokarin canja canel dashi, daya hannunta rike da glass cup da take shan lemo, kafarta daya akan daya tana girgiza kafar,wayarta dake kan center table tayi kara, amma memakon ta dauka sai naji ta kwala kiran
"Karima,karima "take fadar sunan kamar bataso, tana wani yatsina fuska.
"Na,am hajiya"wata budurwa ta fito sanye da doguwar rigar atamfa duk ta kode hannunta jike da ruwa da alama tana wani aikin ne daya danganci amfani da ruwa,
"Miko min wayata"
"To hajiya ta fada "tana goge hannunta a a jikin rigarta,ta dakko wayar ta dan risina ta mika mata da hannu biyu.
"Ke bakya komai da sauri gashi nan kiran ya katse,kamar wanda zakiwa mutum aiki kyauta,karfa ki manta biyanki nake "ta fada tana jan tsaki
"Ayi hakuri hajiya"ta koma gefe ta tsaya.
Wayar ce ta sake daukan kara a karo na biyu,ta mika hannu kamar bataso, ta daukota daga kan kujera inda ta ajjeta kusa da ita.ta danna ok ta kara a kunnenta.

"Hello" ta fada cikin kashe murya
"Hajiya "alhaji ya fada daga dayan bangaren .
"Na,am alhajina barka da rana, ya kake ya aiki"
"Lpy alhamdulillah sai dai kewarki"
"Allah sarki alhajina,nima nayi kewarka"
"Banga alama ba, dan da kinyi kewata dakin kirani a waya"
"Wlh abubuwa ne suka sha min kai"ta fada tana ringisawa akan lallausan kujeran da take kai"
"Ok ba damuwa,daman kira nayi in ji lapiyarki"ya fada yana dafe goshinsa saboda gajiya.
"Ammm nace, da yamma zaka dawone ko sai dare saboda abincinka "
"Sai da magriba zan dawo saboda ina da ayyuka a office,yaran basu taso bane daga scul"
"Eh basu taso ba, kasan yanzu sha biyu tayi,me za,a dafa maka "ta fada tana wani kashe ido kamar yana ganinta.
"A dafa min tuwon tsari miyar kubewa kinsan nafison abincin gargajiya,sai a min pepper soup,sannan amin fruit salad, a dafa naman kai asa daddawa sosai"
"Ok karka samu damuwa alhajina"
"Sai na dawo" ya fada yana hanging call din.
"Ke karima"
"Na,am hajiya" t karima da har lokacin take tsaye kikam ta fada tana matsowa kusa da ita.
"Kije part dinku ki kira min kande,kice tazo yanzu"
"An gama hajiya" karima ta fada tana kokarin fita.
"Karima "
"Na,am hajiya"karima ta fada tana dawowa hajiyar ta risina.
"Kin gama wankin toilet dinneh "Eh hajiya saura na dakin muhibba "
"Gaskia baki da sauri,kirawo kanden kizo ki karasa, zan aike ki"
"Toh hajiya"




MAMAN AFRAH=

'
'
'
'



Story & written by

MAMAN AFRAH=




Page 43 _44


*Innallaha wa* *mala,* *ikatihi* *yusalluna* *alannabiy* *ya* *ayyuhallazina* *amanu* *sallu* *alaihi,* *wa* *sallimu* *taslima.*(allahuma salli ala sayyadina muhammadin wa sallim>2>2>2).




NO EDITING <
@&


Tun bayan tafiyar MARYAMU makaranta take cikin zulumi da tunani,domin tasan dole yau zasu fuskanci bacin rai domin duk da suna da gskia,idan har taje ta baiwa yan sanda kudi shikenan ita zasu baiwa gskia, sai dai in an hadu da masu gskia kuma masu tsoron Allah.
"Ummm Allah mun gode maka da irin rayuwar da muke cikin,sannan ina kara gode maka da kasa ina raye da bansan ya MARYAMU zatayi da rayuwarta ba,duk da nasan idan bana raye ma zaka iya bata kyakykyawar rayuwa
Duk hakan yana cikin ganin damarka,alhamdulillah"ta fada tana tashi tayi alwala tayi kabbara domin yin sallar walaha da ta zame mata jiki,da a kullum sai ta gabatar da ita.domin inna sarai akwai ibada,kamar ba a ruga ta taso ba,saboda malam buba makama Allah jikan rai ya bata ilimin addini sosai,kuma alhamdulillah tana aiki dashi.

Bayan ta idar da sallah ta daga hannunta sama>2
"Ya Allah ka shige mana gaba a lamarin nan,Allah kai ne gatanmu kai kadai muke dashi,ya Allah karka barmu da kanmu ka zama gatanmu a ko ina ,kuma a kowane hali,Allah ka shiga tsakanin nagari da mugu Allah ka bamu nasara akan jummai ya allah ka rabamu da mugun nufinta akanmu ameen" ta fada tana shafa hannunta a fuskarta.

"Assalamu alaikum"iyar halima ke sallama a gidan inna sarai.
"Wa alaikumus salam ,shigo mana iyar halima" inna sarai ta fada tana daga cikin daki.
"Sarai a daki kike"
"Eh wlh kin ganni ina jiran tsammani "
"Tsammani kuma, namefa"
"Kinjiki kema iyar halima da wani abu,yo tsammanin mekwa zanyi in banda na zuwan dan sanda"
"Lallai ma inna sarai yanzu har bata lokacin ki kikeyi ,akan wannan marar hankalin da sanin ya kamata"
"Hmmm haba iyar halima ba dole ba na,ringa tunani saboda bani da abin da zanyi shara,a duk da ina da gskia amma yawancin mutanen yanzu ba gskia bace a gabansu abin duniyane a gabansu,haka ina ji ina gani wanda ya daki tasi,u akanshi wanda hakan yayi sanadin mutuwarshi,har yau da idona ban ganshi ba,balle ayi zancen yin shari,a saboda bani da gata kuma bani da wanda zai tsaye min,haka na hakura ba tare da an daukar min fansar abinda aka min ba" ta fada hawaye na zuba daga idonta=-
"Allah sarki kiyi hakuri sarai,akwai Allah ai, kuma ba anan zamu dawwama ba,komai daren dadewa zamu koma ga Allah"iya ta fada itama idonta na kawo kwalla=" domin tana tausayin inna sarai.
"Ba komai mu fawwalawa Allah komai shi zai shige mana gaba" cewar inna sarai tana share hawayenta,dan dan kukan da ta danyi ya sanya taji zuciyarta sakayau,kukama rahma ne.
"Bari inje in bada nikan wake saboda alalar rana,tunda yau jummai bata nan bare tayi dambu, cinikin nawa zaifi na kullum"
"To nima yanzu tashi zanyi in gyara alkamar can akai min nika da yamma,a siyo min kayan taushe, gobe juma,a kasuwar babura"inna sarai ta fada tana kokarin tashi daga zaunan da take.
"To sai an jima yadda ta iyu,bari in tafi yan makaranta sun kusan tasowa"
"To iyar halima an gode"
"Bakomai ai inna sarai"


*Bayan* *awa* *uku*


"Assalamu alaikum"
"Wa alaikumus salam,lale marhabin da da yan makarantar bokoko"
"Ni gskia inna ki daina cewa bokoko,ki ke cewa boko dan in aka ce bokoko ana nufin bokoko a wuta fa" MARYAMU ta fada tana bubbuga kafa a kasa, tare da zunburo karamin bakinta .
"To shikenan yan makarantar boko"inna sarai ta fada tana dariya.
"Yawwa innata ai kema bakyaso in shiga wuta ba"ta fada tana dariya har beauty point dinta suna lobawa.
"To maza a cire inifom din azo ayi sallah aci abinci"
"Inna uniform ake cewa fa"
"Ke rabu dani da wannan kwakwasa gwallan naku, ai nayi kokarima nida ba yar boko ba"
"Gskia inna"
"Kema kin san dede ai"
"Wai ni inna jummai ta dakko dan sandan"ta fada fuskarta da damuwa
"A ah me kika gani"
"Da safe da zamu tafi makaranta muka ganta ,ta hau machine har tana ce masa wurin yan sanda zai kaita"
"To dae bata dawo ba har yanzu,jeki kiyi abinda zai fishsheki,Allah ya fita"inna ta fada a fili amma a badini fargabarta ta yawaita dan tasan kudirin jummai ba mai kyau bane.
"To"ta fada tana shiga daki,can sai gata ta fito daure da zani.

"Yanzu hallaw wani wankan zakiyi bayan kinyi da kinyi da safe,ke ko sanyin nan da akeyi bakyaji,maimakon kici kiyi sallah kici abincinki"
"Gskia inna wanka zanyi tunda ga ruwan zafi,sai inyi sallah"
"Haka kika iya kullum wanka kamar agwagwa yo ni ina dalili,keba wata budurwa ba,ga shegen iyayi wankan ma tun baki cika shekaru bakwai ba kinki inke miki saidai kiyi da kanki ,dan ma dai kina fita sosai,kuma na miki zancen abinci kikace kiyi wanKa kiyi sallah abincin fa"
"Me kika dafa"
"Wake da shinkafa da mai da yaji,nasan kinason shi sosai,ke har da salak na bayar aka siyo a kofar shagon emeka"
"Yawwa innata"ta fada tana tafiya tana tsalle.


Shiru, shiru har la,asar inna sarai bata ji ance anzo da dan sanda ba,sai da taga har rana na neman fadawa, sannan ta fito daga gidan domin kirawo MARYAMU a gidan iya mai daddawa tazo ta siyo mata yis da fulawa wanda zata kwaba funkason da zatayi a kasuwa.ta fito kenan taga wata amalanken shanu ta tsaya a kofar gidan jummai mai dambu yara duk sun kewaye amalanken ana cewa " ga gidan nan" usaini baban bishira daya taho domin zuwa gida yaga dandazon yara da amalanke, ana nuna gidansa,sai da yara suka ganshi suka fara cewa "ga mai gidan nan" me amalanken ya miko mishi hannu suka gaisa har zauwa lokacin baban bishira bai ga wanda ke cikin amalanken ba. "daman marar lafiya ce na kawo, ta taho ne daga sule tankar kar a kafa" inna sarai dake kokarin shiga gidan iya mai daddawa ta dakata, yaci gaba da cewa "shine tazo wurin masu mashina wai a kawota mai alkama,a hakikanin gskia inaga bata da lpy,ko kuma tafiyar da tayi daga sule tankar kar din ne kafa yasa ta galabaita,nidai ban sani ba.tunda ta wuce kauyuka uku kafin tazo wurin da masu mashinan suke inda suke daukan wanda zai shiga kauyukan da suke cikin lungu"
"Dan Allah dakata malam wai maganar wa kake? " baban bishira ya fada yana kanne ido daya dan dayan bai gani sosai.
"Gatanan a bayan amalanken,mai machine din ne ta hayo dan koyo,kuma ga tafiyar yashi(rerai) shine suka fadi shi ya kukkuje kuma kansa ya bugu,ita kuma ta samu inajin gocewar kashine,shine aka kirawoni na dakkota, sai ka sallaman jaka biyu da rabi 300" ya karashe yana cin magani danma kar a nemi ragi=.




Baban bishira daya leka bayan amalanken yaga jummai , sai ya kama haba ya saki baki, a haka mai amalanken ya gama bayani danshi gaba daya abin ya daure mishi kai.matar daya tafi kona gawayi (sana,ar sa kenan ya sare bishiya ya ya koneta ta zama gawayi) da sassafe ya bari a gida,shine yanzu ake masa wanna bayanin,to me yakai jummai sule tankar kar? Yayiwa kansa tambayar a zuciyarsa.
"Ka sauketa ka biyani kudina in tafi"
Inna sarai dake tsaye har lokacin,sai kwallar da idonta ya kawo, "Allah mai yadda yaso"ta fada tana since gefen zaninta ta irga dari uku ta karasa ta mikawa mai amalanken .
"Yawwa iya kin kawo taimakon gaggawa"ya fada yana irga kudin ya saka kudin a ljuhunsa.
"Inna sarai harda wahala haka"baban bishira ya fada yana kinkimo jummai daga amalanken,daman jiki ba jiki ba ,sai shegiyar masifa.haka ya shiga da ita gidan ya ajjeta akan wata tabarma daya gani a shimfide,duk ta wani hada uban gumi.
"Me kikje yi sule tankar kar ?" usaini ya jefo mata tambayar,yana kallonta.
"Dan Allah baban bishira ka samo me gyara" ta fada cikin azaba dan ita kawai jinsu take, amma tana tunanin ma kafarta ba gocewar kashi bane karaya ce. Kallonta yayi cikin tausayawa, duk da bai isa da ita ba abinda taga dama takeyi amma ya tausaya mata sosai, dan shi duk tunaninsa bata da lpy ta tafi asibitin sule tankar kar din."to amma me yasata tafiyar kasa a maimakon ta hau machine tin daga sulen?" Ya yiwa kansa wannan tambayar lokacin da yake fitowa daga gidan, domin kirawo mai gyara.

Bayan mai gyara yazo ya gyara mata kafar ,dan har da targade a hannun.sai dai muce Allah kiyaye gaba jummai=




Wasu motoci na gani guda uku dogaye, sun dakko mutane suna ta tafiya a sahara, kowace mota cike take da mutane.motoncin farare ne amma saboda yadda sukayi bududu da kura da jar kasa zaka dauka jajaye ne, duk ilahirin mutanen dake cikin kowace mota matane kalilane maza suma daga direbobin motar saikwa maza sai maza uku uku,ma,ana kowacce mota na dauke da mass hudu har direban mortar.

Kowace mota dana duba mutanen cikinta sai inga iya mazan ne kawai suke dan cin wani abun, sannan ga ruwan gora a suna korawa.Amma su matan basa cin komai hasalima

Please Login or Register in order to submit comment