Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dawowa gida yayi dole mu dawo, to magani dame kuma zaki tsaremu da tambaya"rakiya ta fada cike da masifa dan batajin zata lamunci wani reni a wurin wani tunda kowa dan kazo nazo ne.
"Ke kika kula tama"amina tayi Saurin fada tana yiwa matar kallon raini.
"Kunsan dawa kuke magana kwa?" Cewar matar tana nuna kanta da yatsa.
"Ina ruwanmu da sanin koke wacece"lantana ta fada tana yin gaba domin tafiya dan ita har ga Allah yunwa takeji ga kishirwa duk da suna tafiya da ruwa amma bai isarsu .
"wai hayaniyar me nakeji tun kafin in shawo kwanar nan zee ta fada yayin da take tunkaro inda suke .aikwa idanunta suka sauka akan su lantana da shugaba.
"Barka da warhaka shugaba" zee ta ce tana dunkule hannu alamar jinjinawa.ai lantana najin an anbaci shugabanci sai ta iyo reverse da Sauri,dan tunda taga zee na jinjinawa matar tasan sun fada matsala.



"""""""""""""'''"""
Inna sarai ta saki baki da mamaki tana kallon dabobin, dan ita dai tasan bata kulle suba a gidan.amma sai batabi takansu ba, sai tayi cikin gida domin tunawa da tayi da hatsin data shanya da kuma alkamarta.

Yalemin kwa tana shiga gidan da abinda idanunta suka mata tarba kenan.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji,un"shine kawai abinda inna sarai keta maimaitawa dan gaba daya abin ya gama daure mata kai.shin sai Yaushene jummai zata dena binta da mugun nufi ne? Ita kenan kullum bata da wani buri ko farincikin daya wuce ta kuntata min nida jikata? Shin mena tsare mata a doron duniyar nan? Wannan sune kalami da tambayoyin da suke yiwa inna sarai kai komo a cikin kwanyarta.kawai sai ta karasa kan dutsen da take zama tayi alwala, ta zauna tare da dafe kanta da gaba daya hannunta, domin tama rasa abin yi ,domin zuwa yanzu ta tabbatar da cewar me jummai tayi.harta ta hakura sai kawai ta tashi taje jikin katangar domin tabbatar da zarginta aikwa tayi ido hudu da inda dabbobin sukayi sufa lokacin da aka jefosu .
"Tabb lallai ma jummai kin cika marar imani,banda rashin imani ki sako min da dabbobi ta katanga, su cinye min hatsi da alkama"inna ta fada rai a matukar bace domin ta fusata ranta yayi mugun baci.

Tana nan tsaye daga karshe sai ta yanke shawarar taje ta gayawa iyar halima, ta fito kenan sai wani bangare na zuciyarta yace kawai ta fara shiga gidan jummai."Assalamu alaikum" inna sarai ta fada yayin da take shigowa cikin gidan dan yanda takejin zuciyarta ma bazata iya tsayawa a bakin zauren ba har sai an amsa mata sallamar ba.

"Wa alaikumus salam" jummai ta fada tana tashi tsaye daga inda take zaune, dan sai taga kamar jefo inna sarai akayi, kuma ma dai batayi tsammanin ganinta ba dan koda za,ayi magana akan dabbobin tasan sai dai ko iya mai daddawa tazo amma ba sarai ba.

"Sarai kece a gidan namu"cewar jummai tana diriricewa dan tama kasa gane mesa gaba daya tsoron sarai ya shigeta abinda bata taba yiba.

"Idonki bai nuna miki ba, da zakike tambayata" inna sarai da ganin wata katuwar kwalla a kife a jikin katangar ya kara fusatata domin zargin da take ya tashi daga zargi ya zama gskia.

"To me yayi zafi haka innar MARYAMU keda fada ba halinki ba"

"Saboda fada ba halina bane shine kuma sai ake cutata ? Dan ansan in a maida komai ba komai ba, to daga yanzu bazan kara yarda da haka ba.name har zaki jefa min dabobi cikin gida su cinyemin hatsin tuwo dan kinsan bazanyi magana ba saboda gudun masifarki? to yau sai kin biyani hatsina kwano biyu da alkama ta kwano uku"

" haba sarai wace irin magana ce wannan kuma? yama za,ayi inyi wannan danyen aikin,kawai idan dabobine suka miki barna kice in biyaki amma bawai kice an jefa miki su cikin gida ba"

"Kalli can kwallar da kika taka kika jefa" inna sarai ta fada tana nuni da yatsanta.

"Haba sarai waccen fa dama a wajen take ,inaga bakya lura da itane inkin shigo gidan nan"ta fada tana inda inda,dan ta manta kwata kwata bata dauke kwallar daga wurin ba.
"Ke. Jummai a haife na haifeki dan haka baki isa ki rena min wayo ba, kuma banda wawta irin taki ai na kulle gidan bare kice a bude na bari ke hatta da inda kika jefasu sukayi sufa naga kurtun kafafunsu"
"Dan Allah innar MARYAMU kiyi hakuri insha Allah bazan sake ba" ta fada gumi na keto mata dan tasan inna sarai ta gama ganota kuma ko ina sukaje itace marar gskia.
"Haba jummai ai ba yau aka fara ba, an dade ana ruwa kasa na shanyewa, amma ba komai na dau hakurin, albarkacin hakurin Allah ya ban wani "inna sarai ta fada tana ficewa daga gidan (tabbas babu wani abu da mutum zai hadiya, mai kuna wurin hadiyarsa ,irin a bata maka rai ,wanda ya bata maka ran zaka iya Ramawa amma ka hadiye hadiyewar nan shi yafi komai wahala a rayuwa ) Allah bamu ikon kwatantawa Amin.
"Nima dai bazan kara ba"jummai dake biye da bayan Inna sarai ta fada.dan sai data biyota har kofar gida,take mata wani zance marar kai da kafa.Sai ga alhaji mukhtar yazo xai wuce (alhaji mukhtar shine mai kudin garin mai alkama, kowa yasan alhaji mukhtar da rabon kudi da sauran duk abinda Allah ya tsagawa mai rabo to zai baka dan abin hannunsa bai tsone masa ido ba) yanzu ma suna tafiya shida wasu mutane guda uku shine suka zo zasu wuce ta kofar gidan Inna sarai.
"Wa nake gani kamar sarai"alhajin ya fada yana murmushi.
"Eh nice alhaji, ina wuni"
"Lpy lau ina maryama"
"Tana lpy"
"Yauwa sarai akwai hatsi rabin buhu, wake kwano goma, sai alkama kwano biyar ,dana raba zakka to kashinki na aiko dazu gidan a rufe bari yanzu inna koma sai a kawo miki"
"To an code Allah kara bude,kai dai baka gajiya alhaji"
"Ai hakkin da ubangiji yace a fitar ne"
"To an gode"
"Ba komai"
"Alhaji mutari in a wuni" jummai da bata gaisheshi ba tun zuwansu wurin ta fada, tana mai durkusawa har kasa.
"Lpy"ya fada yana yin gaba sauran mutanen suka mara masa baya.dan shi tun lokacin da jummai take naman taimako wurinsa ya bata dubu biyu take yawo a gari tana cewa ana ganinshi na Allah to ba haka yake ba, wai ya bata kudinne dan yana son yayi ma,amalar banza da ita kuma tana matar aure.akaje aka fada masa, har sai daya ce zai daureta ayi shari,a sannan ta fadi gskia.

"Alhamdulillah Allah nagode maka"inna sarai ta daga hannu sama>2tana yiwa Allah godiya.
"Ummn sarai rabo ya rantse "cewar jummai ranta fal bakinciki da hassada.
"Kinga amfanin hakuri ko jummai?"
"Hhhhh" jummai ta kwashe da dariya irin ta mahaukata tana kyakyatawa ,sosai===.
"Haba jummai wannan dariyar fa kamar an miki bishara da gidan aljann?"
"Hhhh yo ai ji nayi kina cewa naga amfanin hakuri? Kuma bayan nasan duk randa ya fitar da zakka har dake yake baiwa, kinga wannan baya cikin hakurinki"
"Haka kika ce, amma ni nasan Allah ne ya kawo min mafita, kuma wannan dariya da kike ki daina saboda wani abu da Zan fada miki yanzu da marigayin mijina ya fada min"
"Ina jinki"
"Jummai da kike ji da ganin wannan kasar da muke tafiya akanta a kullum sai ta mana magana sau biyar amma mu bama jin abinda take cewa"
"To mai take cewa,banda abin sarai kasama ace tana magana"
"Cewa take'
1_yakai dan adam kana tafiya akan bayana,Akwai ranar da za,a tsagani a shigo dakai cikina.=-=-=-

2_ya kai dan adam kana cin nau,ikan abinci a bayana,akwai ranar da tsutsace zatake cin naman jikinka, randa aka shigo dakai cikina.=-=-=-

3_ya kai dan adam kana dariya a bayana, akwai ranar da zakayi kuka, randa za,a shigo dakai cikina.=-=-=-

4_ya kai dan adam kana farinciki a bayana ,akwai ranar bakin ciki, ranar da za,a shigo dakai cikina baka bi Allah ba.=-=-=-

5_ya kai dan adam kana sabawa Allah a bayana, to akwai randa da za,a shigo dakai a azabtar dakai randa za,a shigo dakai cikina.=-=-=-

Allah sarki inna sarai ta karasa fada tana hawaye, saboda abu biyu data tuna, na farko ta tuna da wannan magana da kasa keyi a kullum mu kuma bamaji, abu na biyu ta tuna da malam buba makama mai gidanta daya fada mata.


Oh ni mmn AFRAH> abu a gaban bawa bai zoba bai wuce ba=" Allah bamu cikawa da imaani=O


'''''''''''''''''''''''''''''

Haka MUSADDIQ ya taso cikin gata da kulawa ,daga bangarori da dama mahaifansa kakanninsa na wajen uwa dana wajen uba.

Yaro ne fari kyakykyawa dashi mai koshin lafiya , ga MUSADDIQ akwai shiga rai wannan yasa iyayensa daukan dukkan gata suka bashi.MUSADDIQ ya taso baisan koda kyara da akan yiwa yaro ba ,dan haka shi baisan a masa fada ba amma kuma hakan baya hana a nuna masa idan yayi ba dai dai ba. Sai dai bata hanyar fada ko kyara ba ,dan haka MUSADDIQ bai taso da marar tarbiya ba ,sai dai dan gata ne na bugawa a jarida.haka rayuwa taci gaba da kasancewa a cikin wannan gida cikin farinciki da kwanciyar hankali ,har zuwa lokqcin da MUSADDIQ ya kai shekara bakwai a duniya.a lokacin ne kuma mannir ya hadu da wata mata mai suna binta.binta bazawara ce tana zuwa wurin su mannir siyayya , da farko ta nunawa mannir tana sonsa amma sai ya nuna mata baya da ra,ayi. Aikwa binta data kyalla ido taga kyakykyawan mutum mai dukiya sai ta kudurta a ranta kota halin kaka sai ta auri mannir.hakan kwa akayi taje wurin malami ya bata lakanin da tayi amfani dashi wanda lokaci daya mannir ya daura damarar auren binta,wanda aysha sai auren ya fada mata kamar saukar aradu, haka taji abun daga yin aure shekara 8 zay mata kishiya,dan a faninta hakan yayi wuri.(daman duk dadewar mace a gidan miji daya tashi karin aure sai taji ba,a kyauta mata ba, kishi kumallon mata,Allah bamu abokan zama nagari ameen) sai kuma tayi la,akari da daman auren hadi aka musu, may be ya samu wacce yake so ne yanzu.

Duk kuwa da tasan bayan an hada sun sunyi soyayya ,amma sai zuciyarta ta fada mata cewa ba kamar wacce ya gani da kansa ba.dan haka sai ta sanyawa ranta hakuri, ta dage da addu,a akan Allah ya kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali mai dorewa a tsakaninsu ,ya baiwa mijin nasu ikon yin adalci a tsakaninsu.

A bangaren amarya binta kwa abin ba haka yake ba, dan ita kawai burinta ta auri mannir ,Amma ba ruwanta da zaman lafiyar uwargidansa,a cewarta kowa tashi ta fishsheshi.yaranta uku biyu maza daya mace sunanta muhibba , a lokacin muhibba nada shekara biyu dan bata dade da yaye taba.dan daman da cikinta suka rabu da mijinta a dalilin zai kara aure, shine ita kuma tazo zata auri mijin wata.mata kenan sun yarda a u.yiwa wasu Kishiya dasu Amma basu yarda ba ayi musu kishiya da wasu kaji son kai=.

Anyi biki lpy amarya ta tare a gidanta, sannan kuma data tare da yarta muhibba, a cewarta dole suzo suci arziki amma basu barinshi anan dan zama ita da mannir mutukara ba takalmin kaza.dan tayi niyya ma ta barta a gida a kawota daga baya amma kawarta zakiyya ta hanata a cewarta idan ta barta a gida duk randa aka kawota zai ce bai yarda ba, dan daman ba yarsa bace, amma idan taje da ita yanzu yana ridinta ba abinda zai ce.dan yanzu itace da gida sai yanda tayi dashi.


Bayan an an kawo amarya mannir ya tarasb a falonsa a daren, domin yin yan maganganu da kuma yanke kwanakin da zai keyi a kowane dakin.
A haka aysha ta daure ta danne zuciyarta saboda feleken da amarya keyi sai wani lunshe ido take tana budewa.dan hatta da magana da baci ,baci takeyi ita dai aysha taja girmanta ta kame bata tankata ba ,dan mannir din kansa danne zuciyarta take da tuni tahau bugunshi kota ina kodan ta huce, ta samu rangwame a zuciyarta.
>p>p>p>p>p>p>p


Story & written by



MAMAN AFRAH





Page 57_58





KA BAUTAWA ALLAH KAMAR  
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~KANA GANINSA, IDAN KAI BAKA GANINSA ,TO SHI YANA GANINKA.


GODIYA MAI TARIN YAWA GAREKI QUEEN FULANI NAGODE SOSAI DA KAUNA>p>p>p>p
UBANGIJI YA BAIWA BABA LPY=O=O=O
SON SO FISABILILLAHI=ؔ=ؔ=ؔ



"Ina amsawa zee, ya aiki"cewar shugaba data amsa daker tana wani shan kamshi da isa da kuma nuna ita a dole wata mai matsayi ce, dan taji dadin zuwan zee ko ba komai tasan zata yiwa su lantana bayanin wacece ita a maimakon ta musu da kanta .dan gani take hakan tamkar zubda aji ne a wurinsu a matsayinta na wacce take da matsayi .
"Aiki alhamdulillah dan yanzu ma daga wurin aikin nake"zee ta fada tana fadada murmushinta, dan sai ta tuna da farkon zuwanta itama sai da suka sami matsala da shugaba ,kafin daga baya tasan matsayinta gashi yanzu suna shiri ita da shugabar.
"Shin wadannan basu san da wacce suke magana bane ? naga dukkansu kansu na rawa kamar masu tashen balaga"shugaba ta fada tana bin su lantana da kallo daya bayan daya.
"Ayi hakuri shugaba basu san ko ke wacece ba shi yasa, kuma suna cikin sabbin zuwan da aka kawo jiya shisa , ayi musu afuwa"" cewar zee tana hade hannayenta wuri daya alamar roko.

"Gskia ne zee amma wannan rokon su ya kamata suyi da kansu, amma ki fara sanar dasu matsayina tukunna, sai su bada hakuri da hujja"

"To ranki ya dade
' rakiya,lantana, tare da amina, wannan matar da kuke gani kanwace a wurin mamallakin gidan nan, kuma gaba daya dukkan dukiyar da take cikin wannan katafaren gida nashi ne, sannan kuma itace aka nada a matsayin shugabar wannan gida, dan komai da izininta akeyi a gidan nan, tana zaune ne a garin makka amma sai dai zamanta yafi yawa a gidan nan.akwai bangare ba musamman da aka Gina mata mai kyau, da kuma ma,aikatanta kuma lurane bakuyi ba ko kayan jikinta sun isa isar da sakon wacece ita, dan kuwa babu tantama kamshinta kadai ya tabbatar da isarta, dan haka kuyi bm gaggawar bata hakuri saboda gudu da kuma kaucewa aikin da na sani dan kuwa idan tace ta karawa kowaccenku shekara biyar bi ma,a,na kuyi shekara 10 babu wanda zai canja in kunga bakuyi ba Allah ne beyi ba sannan idan tace a yau mutum zai bar gidan nan to ba makawa sai ya bari sai dai in Allah ne beyi ba, ku gaggauta neman afuwarta"
"Wannan haka yake zee" shugaba ta fada tana wani murmushi mai and kayatarwa dan taji dadin yadda zee tayi bayanin wacece ita.

"Dan Allah shugaba kiyi hakuri wlh rashin sani ne, dan gajiyar da mukayi da kuma yunwa sun rufe mana idanu mun kasa ganin kayan dake jikinki dana sauran mutane a mana afuwa"cewar lantana dake tsugunne dan tunda aka fara cewa zata iya karawa mutum shekaru kota rage jikin lantana yana rawa ta tsugunna a zuciyarta tana addu,a Allah yasa ta rage mata shekarunta"

Haka suka hadu su duka ukun suke baiwa shugaba hakuri, ita kuma sai jinjina kai take kamar kadangaruwa.
"Wato da kun dauka matsayinmu daya daku ko? Shisa kuka dauki girman kai kuka dorawa kanku, to bari kuji abinda baku sani ba, ina da baban iko da dukkan tarin dukiyar cikin gidan nan dan haka kuyi a hankali dan bayan nima akwai wasu shugabannin da suke a kasa na, wadanda na nadasu idan bana nan suke yin dukkan hidindimu"
"Ki kara hakuri ranki dade duk cikin rashin sani ne wlh"rakiya ta karashe kamar tayi kuka dan duk ta kagu a sallamesu subar wajen dan duk ta gaji, ga yunwa dake addabar hanjin su.

"Ku biyoni shashina ku duka ,har dake zed"shugaba ta fada tana yin gaba.
"Su Lantana da suka gama tsurewa jin tace su biyo bayanta,kenan bata hakura ba kome take nufi, har sun shiga kallon kallo a tsakaninsu, amma kuma jin tace har zee sannan kuma zee tana murmushi da daga musu gira ,hakan yasa suka gane ba wani abun marar kyau zata musu ba"


Haka suka bita tana tafiya a hankali kamar bata so ,sannan gashi duk hankalinsu yana can wurin raba abinci, gashi duk sun cinye lokacin a wurin shugaba.haka dai suka daure saboda sun san basu da wata mafita ko yancin kansu da zasu bijirewa umarninta.

Sun yi tafiya mai dan nisa sannan suka iso wani bangare dake can daga gefe guda, gidane na gani na fada amma kuma akwai masu tsaron kofar,su uku duk da dai kofar ta kasance karamar kofa ce bawai get bane.yadda tsarin gidan yake bazaka taba cewa a cikin wannan surkukin dajin yake ba ,sun shigo har cikin gidan sannan hajiya ta shige falonta na alfarma ta barsu nan tsaye, zuwa can wata matashiya ta fito take ce musu su shigo ciki inji shugaba.suka amsa mata sai ta shiga gaba su kuma suna biye da ita, lantana an saki baki ana baiwa ido abinci kafin ciki shima ya samu rabonsa.lol

Sun shigo falon daya sha kayan kawa ko ina, ga manya manyan kujeru, ga freezer dan kareriya a gefe ga kayan kallo nan ,an malale falon da kafet mai laushi da dadin takawa ,ko zee da tayi shekara da shekaru bata taba shigowa falon nan ba,sun sami shugaba ta canja kayan dake jikinta fazu dazu ,zuwa wata doguwar riga mai kyau marar nauyi.tana zaune akan daya daga cikin kujerun da suka kawata falon sai dai kafarta tana kasa akan tuntu.

"Ku zauna "
"To shugaba"suka hada baki wurin fada.sun zauna kowa yayi shiru kamar wasu kurame ,lantana kwa idonta akan fanka dake wulgawa ,dan akwai inji a gidan dake basu wuta.ita dai lantana tayi nisa wurin tunani akan yadda dakin da suka kwana jiya yake.sannan tana tuna badan bakinciki irin na duduwa ba, da yanzu itama tana can gidan sarkin makka,tana tunanin ma inda zata zauna yafi wannan da komai.
"Ku zo muje "wacce ta shigo dasu dazu ta fada tana yin gaba.
Wani daki ta kaisu acan. bangaren ma,aikatanta, suka zauna akan tabarma ta kawo musu lafiyayyen abinci har da nama a ciki da ruwa, haka suka zauna sukaci suka koshi suka sha ruwa sukayi hamdala.bayan sun gama haka suka zauna a dakin har sai da wacce ta kawosu ta dawo ta nuna musu bandaki, suka kama ruwa sukayi alwala suka gabatar da sallar la,asar.suka zauna suna dan tattaunawa.
"Kunga lokacin komawa wurin aikinmu yayi , kar fa muje a mana wani abin"rakiya ta fada fuskarta da alamar damuwa.
"Tabb ai Allah ya ciyar damu yau, dan kuwa aikin nan dai yabi ruwa dan duk wanda shugaba ta tsayar dashi to koda lokacin aikine babu mai tuhumarshi dan kuwa sai ta bada umarnin a maye gurbin mutum da wasu,wato wanda zasu karbeshi su masa aikin dan haka kar ku damu"zee ta karasa fada tana kara mike kafafunta.
"Aikwa in hakane mu gaba ta kaimu gobarar titi"amina ta fada tana murmushi.
"Ai ni jina nake kamar wacce aka yiwa albishir da aljanna, da aka dauke mana aikin nan, dan kuwa daman ko mun koma banajin zan iya tabuka wani abin kirki a wurin rakuman nan, ga abinci mai rai da lafia kai Allah yiwa matar nan albarka"lantana tq fada tana kishigida.
"Inama ta dauke mu aikin bangarenta da mun mugun more wlh"cewar zee itama tana kwantawa tayi filo da hannunta.
"Allahumma ameen "rakiya ta fada tana daga hannunta sama alamar roko>2
"Dan duk wanda yake aiki a bangaren shugaba babu yunwa ko wahala a tare dashi"cewar zee.
"Gskia fa kiga dai yadda wacce ta kawo mana abincin nan take kamar ba yar aiki ba"lantana ta fada da alamar mamaki a fuskarta.
"Hmmm kai kwa sai ka gama yaki da rakumai azo a baka dan abinci kadan"rakiya ta fada tana tabe baki.
"Allah dai ya kyauta."amina da tayi shiru ta fada.

Haka suka zauna a dakin nan suna hutawa jefi jefi kuma suna hira ,har zuwa lokacin sallar magriba.bayan sunyi sallah wannan da ta gabatar musu da abinci dazu ta kara zuwa ta kawo musu wani abincin ,mai rai har da lafiyarsa suka zauna suka cika cikinsu dan har saura suka bari sosai bayan sun gama sai ga wacce ta kawo abincin tazo ta kwashe, dan har zee tana cewa ta bari zasu kwashe amma taki tace aikinta ne.bayan ta fita lantana take cewa
"Kai Amma taji dadinta ace kawai kawo abinci ne aikinka ai ka huta, ga abinci ishashshe da wurin kwana mai kyau.ba irin namu ba"
"Kema dai kya fada duk da cewar ku yau kadai kuka fara aikin"cewar zee
"Hmmm zee kenan kefa baiwa shukoki ruwane kawai aikinki ,ammafa kiwon nan namu sai hamdala kawai"inji rakiya
"Hakane kam Allah dai ya iya mana dan kam abin ba sauki, dan baiwa shukokin ma ruwa akwai wahala tunda suna da yawa kuma ba wuri daya bane"
"Wahala kowacce ba sauqi kam"amina ta fada
"Assalamu alaikum"mai kawo musu abincin tayi sallama.
"Wa alaikumus salam" suka hada baki wurin amsa mata.
"Wai shugaba tace idan dame bukatar yin wanka ga bandaki nan, idan kuma ba me bukata tace muje in maidaku bangarenta zata muku magana"
"A,a zamuyi wankan"kowacce ke fada da murna dan dama suna bukatar su watsa ruwan babu hali ne.
"To idan kun gama kunyi Sallar ishsha,i zan zo domin rakaku wajenta "
"To muna godiya"





""""""""""""""""""""""
Haba innar MARYAMU ki daina kuka mana nasan kin tuna da marigayi ne, Allah jikanshi da rahma yasa ya huta"jummai ta fada tana goge hawayen da itama yake gangaro mata daga idanunta, dan wannan maganar da inna sarai ta fada mata na cewar kasa tana yiwa dan adam magana a kullum ya tsorata ta, ita da tabi ta gallabi mutane da halinta bare azo ga maganar sallah da bata damu da yinta ba.dan idan jummai tayi kokari tayi sallar asuba da safe, sai ta hada azahar da la,asar in taga da sarari ta hada magriba da ishsha,i in kuma taga uzurin gabanta ya mata yawa to sai ko gobe, amma fa ba ramawa zatayi ba a,a an wuce wurin.
"Kuka ya zama dole jummai ,domin muda ranmu abin tausayi kullum muna kara kusantuwa ne zuwa ga kabarinmu,domin mutuwa ta zama dole a garemu yanxu ko anjima, dole mutuwa na tafe in kinga bamu mutu ba to tabbas lokacin ne beyi ba.Amma dole wataran sai mun mutu dan yadda mutual ta tsallakemu ta dauki wani to ba shakka wataran zata tsallake wani tazo ta daukemu,dole wataran sai mun zama gawa(saboda fadin Allah madaukaki, kowace rai sai ta dandani mutuwa=D) ,wato sai mun koma ga mahaliccin Mu kuma duk abubuwan da muka aikata sai an tambaye mu .tabb lallai akwai aiki a gabanmu amma mukan manta da mutuwa muke aikata abubuwan sabo (lallai dan adam yana cikin halaka,sai dai wadanda sukayi imani ,kuma sukayi aiki mai kyau,kuma sukayi wasiyya da gskia,sannan sukayi wasiyya da hakuri).

"Kai hakika sarai kinyi sa,ar miji mai ilimi da dinbin sanin ya kamata, daya nuna miki hanya mikakkiya,wato ya sanar dake ilimin addini domin ki kyautata lahirarki,sai dai muce Allah jikan malam buba da rahma dan nima gashi na karu sosai kuma in Allah ya yarda zan gyara sallata na da nake kwangenta dan duk rashin ilimi ne yake kawo wani abin,insha Allah daga yanzu zanke shigowa kina dan tunatar dani wani abun dangane da addini dan Mu ba arabi ba boko gashi kuma kauyen namu ba makarantar matan aure akeyi ba sai ta yara"
Hakane gskia kika fada dan malam yayi iya kokarinsa na ganin ya koya min ilimin addini ,kuma alhamdulillah dan ba abinda zance sai godiya ga Allah, da kuma yi masa addu, ar dacewa da aljanna firdausi,sannan ba wani abu kina shigowa zanke koya miki dede gwargwadon abinda na iya"
To na gode sosai"
"Ba komai jummai, ai yiwa kaine ke kina da lada nima kuma ina da lada"
"Riba biyu kenan, ka koya ka samu kada kuma"
"Hakane ai shi addinin muslunci akwai garabasa,bari in shiga gida"
To innar MARYAMU, nina gidan zan shiga sai an jima"
"Mu jima da yawa"inna sarai ta fada tana shigewa cikin gidanta.

Tana shigowa sai idonta ya sauka akan daron data zuba alkama da kuma buhun shanyar hatsinta, sai kawai taji wani haushin jummai a ranta,wani bangare na zuciyarta yana dada gaya mata abinda jummai ta mata bata kyauta ba ,ba komai bane sai kyashi da kuma tsana, nan take taji ranta ya kara baci sai kawai ta fara fadar (a,uzubillahi minash shaidanir rajiim) saboda

Please Login or Register in order to submit comment