Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ciki tun daga kayan yara yan kanti dana manya da yadika shaddodi,atamfofi jakankunan mata, da takalma na yara da manya da dai sauransu.

Allah ya sanya mishi albarka a ciki,inda yake saidawa yana kara saro wasu kayan da ribar daya samu ,kafin meye wannan har ya shahara kowa yasan shagon mannir mai nera ga araha ,gashi kuma idan kaje duk abinda kaje nema zaka samu riba biyu kenan.


Bayan shekara uku da fara kasuwancin mannir, sai mahaifinsa ya bijiro masa da zancen yin aure.tunda a wannan lokacin mannir yayi kudi sosai yadda ko mahaifinsa baiyi zato ba.saboda baya cin riba,domin kwa yasan haramcin cin riba.


*Fadin* *Allah* *madaukakin* *sarki* *cikin* *suratul* *bakara



Wadanda suke cin riba basa tashi face kamar wadanda shaidan yake dimautarwa,daga shafa yake tashi.wancan.domin lallai ne sunce: ciniki kamar riba yake.kuma Allah ya halalta ciniki, kuma ya haramta riba.To wanda wa,azi daga ubangijinsa yaje masa, sa,annan ya hanu ,to yana da abinda ya shige, kuma al,amarinsa (to ana wakkala shi )zuwa ga Allah kuma wanda ya koma,to wadannan sune abokan wuta,su a cikinta madawwama ne.

Ya ku wadanda sukayi imani, kubi Allah da takawa ,kuma ku bar abinda ya rage daga riba, idan kun kasance masu imani.

Sanin haka da mannir yayi sai yake kokarin kare cinikayyarsa daga cin riba.komai yakan saka riba kadan ,sai Allah yasa masa albarka a kasuwancinsa.gashi yana fidda zakka.

"Mannir ya kamata ace zuwa yanzu ka ajje iyali, dan kwanaki kullum karewa suke, satika suna zuwa suna shudewa, watanni tafiya suke,sannan shekarar ma ta zama,kamar walkiya.wannan kadai ya ishi mutum ya hankalta saboda a kullum yana kusantuwa izuwa kabarinsa, sannan mutuwa dole ce ,yanzu, ko an jima ya kamata mutum ya zama kullum cikin shiri, domin dai ita wannan duniya wurine bana dawwama ba, lallai ya dace mutum ya dauki kansa a cikin duniya kamar bako, matafiyin daya zauna a gindin bishiya.bishiya zai huta sannan yaci gaba da tafiya, Allah sa Mu dace" cewar alhaji sanusi yana kallon dan nasa dake zaune a kasan lallausan kafet din dake shimfide a falon na alhaji sanusi.
"Ameen abba" mannir ya fada,domin jin wannan nasiha ko fadakarwa da mahaifinsa ya nasa duk jikinsa yayi sanyi.

"Yanzu manniru wace yarinya ce ka zaba a matsayin matar aure ?"
" gskia abba....." Sai kuma tayi shiru.
"Amm manniru Shifa aure da kake gani ba abune na wasa ba, ya kamata ka natsu ka zabi abokiyar zama ta kirki,wato ka kuma zabawa yayanka uwa ta gari nagartacciya, wacce zasuyi alfahri da ita domin uwa itace matakin farkio na tarbiyar yaro,domin duk halayyan da yara suka ga mahaifiyarsu nayi suma shi zasuyi me kyau ko akasin haka, dan yaro yafi koyan abinda yaga anayi yi akan wanda aka koya masa ,dan haka kayi zabi mai kyau"
"To abba naji bayaninka amma ni gskia ban fitar da abokiyar zama ba, kawai ba baka zabi, kuma insha Allah duk zabin daka min zanyi alfahri dashi" mannir ya fada yana mammatsa yatsun hannunsa,suna kara kat kat kat.
"To Allah maka albarka, kuma idan na yanke shawara zan kirawoka in fada maka"
"To abba "ya fada yana mikewa zai fita daga falon sai yaga hajja abu mahaifiyarsa tana tahowa ,sai ya dakata da fita.

"Assalamu alaikum"hajja abu ta fada tana shigowa dauke da tea flacks da karamin farantin tangaran mai dauke da karamin kofin tangaran din sai tea spoon a cikin kofin.
"Wa alaikumus salam"cewar mannir ya nufi mahaifiyarsa zai karbi kayan hannun nata domin ya karasa dasu kan karamin center table ya ajje.
"Matsa kaban wuri, zaka rage min ladana"ta fada tana dariya tare da matsawa dan kar ya karba.
"To mama nima ba aljannata ba nake nema"ya fada da alamar baci a cikin maganar yana wani kumbura baki kamar wani karamin yaro(wa yaga sakatare>Ø-Ý).
"Sai ka bari sai ina wani aikin daba na abbanka ba, sai ka karba"ta fada tana zuba ruwan zafin cikin kofin domin hadawa alhaji coffee.
"Shima ai ya kusa ya kaura gidansa matarsa take samun lada akanshi"alhaji ya fada yana dariyarsu ta manya.
"Wayyo abba kar ka fada mata"ya fada yana ficewa daga falon dan kar mamansa ta zolayeshi.
"Bani insha labari da dumi duminsa "ta fada tana zama kusa dashi akan kujerar da yake.
"Tabb ai sai kin bani goran albishir mai tsoka
"Amma dai har gidansu yarinyar zaka fada min"cewar hajja abu tana kashe ido daya=Ø Þ
"Ke dai rike goranki dan nima na kagu in bada labari , dan nasan sai ki tarki tafiya bangarenki domin dakko goron albishir din"

"To ina jinka nina na matsu inji"
"Danki ya ban dama in zaba masa matar aure"
"Kai alhamdulillah"ta fada tana daga hannayenta sama.


_Bayan_ _mako_ _daya_

Mannir ne zaune a falon mahaifinsa, yana zaune a kasa kan kafet su kuma iyayen suna kan kujera.

"Mannir daman na kiraka ne akan maganar zabin daka bani in maka na abokiyar zama, to alhamdulillah komai ya kammala dan na Sami mahifin yarinyar da maganar kuma alhamdulillah mun gama magana, dan ya samu yarinyar itama ta amince da wannan hadin,yanzu abinda ya rage shine kaje ku sasanta kanku ,ba Kowa bace face illa aysha yar gidan alhaji suraj aminina kuma makocina, kasanta tunda gida ukune a tsakanin gidan nan da nasu gidan" alhaji sanusi ya karshe maganar yana kallon tilon dan nasa domin ganin yadda zai karbi maganar, duk da dai shine ya bashi zabi to zai iya gani a fuskatsa idan zabin bai masa ba, duk da yasan hakan da wuya.itama dai hajja abu murmushi ne kwance a fuskarta, na zabin da aka yiwa tilon danta, duk da tun jiya mahaifinsa ya sanar da ita.
"Gskia abba hakan yayi wlh Allah ya bada tsawon rai, kuma insha Allahu zan karbi zabinka da hannu biyu, kuma bazan taba baka kunya ba abba" mannir ya fada yana dago kanshi yana kallon fuskar mahaifansa dake cike da murmushi.
"To alhamdulillah komai yayi Allah sanya albarka yasa ayi a sa,a"cewar hajja abu tana kallon dan nata da shima murmushi da annashuwa suka kasa barin tasa fuskar.


Washe gari ya kama juma,a bayan ya dawo daga kasuwa misalin karfe biyar na yamma bayan yaci abinci sai ya shiga bangarensa dake dauke da falo da bedroom sai bayi a ciki ,yayi wanka ya shirya tsaf cikin wata dakakjiyar shadda light blue ,ya dauki hula data dace da kayan ya saka, sannan ya dakko bakin takalmi yasa sai ya dakko agogo ya daura a tsintsiyar hannunsa ya feshe jikinsa da turaruka masu kamshi mai kwantar da hankali, ya tsaya ya karewa kansa kallo a madubin dake jikin bangon falonsa wanda duk tsawon mutum sai yaga har kafarsa a ciki.
Fitowa yayi ya shiga bangaren mamansa inda ya isketa a falonta tana kallo tana shan kayan marmari dake ajje a gabanta.
"Assalamu alaikum"
"Wa alaikumus salam" ta amsa masa sallamar fuskarta a sake.
"Mama hutawa ake" ya karshe yana zaunawa akan 2 seater din da tafi kusanci dashi akan sauran kujerun da suka yiwa falon kawanya.
"Eh hutawa nake, sai ina kuma akasha wannan kwalliya daga dawowa kasuwa" ta fada cikin zolaya ba ya bayan tasan insane yake da niyyar zuwa, dan ita ta bashi no aysha da safe tace abbansa yace ya kirata ya sanar mata zuwanshi, to bayan ya kirata ta gaisheshi shine Ya sanar mata da zuwanshi bayan sallar isha,I
"Ba Inda zani daman wanka kawai nayi, ai kinsan ina kwalliya ba sai ina da wurin zuwa ba" ya fada yana murmushi.
"Kodan wurin sarakkuwar tawa za,aje aka sha kwalliya haka "
"Ashe kinsani mama"ya karashe yana dariya.
"Na sani man" itama ta fada tana dariyar.
Haka sukaci gaba da hirarsu ta uwa da danta ita tana shan fruit shi kuma yana shan lemon gwangwani, har aka kira sallar magriba ya fito domin zuwa masallaci.har ya fita ya tuna bai dakko carbinsa dan dannawa ba, ya koma ya dakkoshi akan tv stand daya dora, ya fice ya tafi masallaci.
Bayan an idar da sallar haka ya zauna yana ta istigfari domin rage zunubai, saboda manzo (s.a.w) yana istigfari sau 70 a kowace rana. Haka ya zauna har akayi sallar isha,i sannan ya fito daga masallacin ya nufo gida.
Dakinsa ya koma ya kara fesa turare sannan ya dakko wata leda mai kyalkyali, dake dauke da sweet da snack masu dadi ya fito ya kama hanyar gidan su aysha.

Tafiya kadan ta kawo shi kofar get din gidansu, domin a kafarsa ya taho bai dakko mota ba tunda kusa ne.
Yana zuwa kofar get din ya fiddo wayrshi ya kirata, aysha dake zaune ta tashi cikin sanyin jikinta ta dakko wayarta dan har ma kiran ya kusa yankewa ta danna ok cikin sanyin murya kamar wacce batason yin magana tace.
"Hello"



"""""""""""""""""""""""""

haka su MARYAMU suka fito daga gidan iya domin tafiya makaranta, sun iso tsakiyar gari inda motocin garin guda biyu ke lodi akwai golf sai kuma babbar mota mu kalli juna,sun gota motar kenan suka hango inna sarai na kokarin shiga mu kalli juna ,aikwa suka tafi suna kiran sunanta.

Inna, inna"
Inna sarai dataji kiran da batayi zata ba dan ta dauka sun tafi makaranta.
"Na,am ,wai daman baku tafi yakul dinba(scul)" ta karashe tana binsu da kallo.aikwa suka kwashe da dariya, kai hatta fasinjojin yan boko na cikin motar wadanda suka san me take nufi dariyar suke =ØÞ .inna sarai kwa tace to koshi baturen kirkirar sunan yayi bawai dan yasan me ake nufi ba.ta fada tana samun wuri ta zauna abinta.
"Gskia ne inna mai funkaso"wani ya fada yana cigaba da dariya.
"Inna karki manta da sakon mu na yalo da goba cewar halima tana kokarin danne dariyarta.

"Anki a siyo din duk mai son zigege ya kawo kudinsa" cewar inna tana bata rai dan ita bataga abin dariya har haka ba.
"Haba innata ta kaina, kar muyi haka man kema da kin fada da hausa ai amma idan na girma na iya turanci sosai zn koya miki"MARYAMU ta fada tana rausayar da kai.
"Ku kama hanya ku tafi dan makara sai dai kar a kara"cewar inna sarai tana balgatar goranta.
"Ina zamu tafi yakul din cewar halima"tana kallon MARYAMU yamu sai kwa suka fara daria suna tafiya rike da hannun juna.
"Yan karshen bokon zamani kawai" inna ta fada tana dariya.
Haka motarsu ta cika=ØŽÞ suka kama hanyar babura a sauka lafiya =ØKÜ


12 :5 pm
Lokacin ne aka taso su MARYAMU daga yakul suka kamo hanya suna ta sauri gudu gudu dan sun san zuwa yanzu baffa ya dade da karasowa.dan halima daker ta iya hakura aka tashi daga makarantar ,dan gaba daya hankalinta yana gida wurin baffanta.
Ganin yadda halima take murna a makaranta tana fadawa kawayenta yau baffanta zai dawo.Hakan yasa MARYAMU jin itama da babanta yana nan da idan zai dawo daga legas itama zatake fadawa kawayenta, dan inna tace legas yake tafiya neman kudi.sai jikinta yayi sanyi amma kafin meye wannan har ta manta tana uzurin gabanta yarinta kenan.

"Assalamu alaikum" suka fada a tare lokacin da suke shigowa cikin gidan, ganin iya tana dauke da tiren data jera kwanukan baffa na cin abinci, ga kuma takalminsa a kofar dakin yasa suka fara tsalle suna cewa.
"Ga baffa , ga baffa"
Shima baffa najin maganar tagwayensa, dan haka yakan kirasu, sai ya fito daga daki yazo gurinsu suka tafi suka rungumeshi suna murna.
"To ya isa haka kar ku kayar da baffan naku"iya ta fada tana musu dariya.
"Maza kuzo in baku tsarabarku ya fada yana kama hannyensu suka shiga daki.
"Baffa ina wuni, sannu da zuwa "suka fada a tare bayan sun tsugunna har kasa (yana da kyau iyaye mata mu kula da wannan a tarbiyar yaranmu,idan iyayensu maza sukayi tafiya ko suka fita unguwa zuwa wani waje,kai koma ina ne ki koya musu idan babanku ya dawo ku ce masa sannu da zuwa da Allah kiyaye hanya lokacin da zasu fita ,aikinmu. Ne iyaye mata hakan tarbiya ce, tun yaro yana mantawa wataran zai tuna,koda kinji shigowar uban kafin ya karaso ki tuna musu.Allah bamu ikon tarbiyantar da yarnmu.ameen).
"Ke MARYAMU tunda ke fara ce ki dauki shudayen, ke kuma halima ki dauki jajayen zasufi haskaki"iya ta fada tana basu kayan fakistan na gwanjo da baffa ya siyo musu iri daya ,kala ce kawai ta banbanta,da takalmin soso sai hijab dinkakku sai kuma alawowi da biskit da sauran kayan makulashe.sai kuma hijab din iya da sabulun wanka dana wanki da klin sai shinkafar Hausa kwano uku da wake rabin kwano.

Haka aka kaiwa iya tsaraba bayan ta dawo daga kasuwa, da taje masa sannu da zuwa ta mass godiya da addu,a taji dadi sosai, dan baffa da iyar halima sun dauketa kamar uwa, sannan sun dauki MARYAMU kamar yar da suka haifa.




Masoyana comment naku shike kara min karfin Hausa


<ØGß<ØGßRAYUWAR MARYAMU<ØGß<ØGß



Story & written by


MAMAN AFRAH>ØpÝ


Page 51 _52



*Hadisil* *qudusi* *Allah* *madaukakin* *sarki* *yace* :



_Yaku bayina dukkaninku_ _mayunwata ne sai wanda_ na ciyar, ku nemi _ciyarwata,_ in _ciyar_ daku.


Godiya da yabo mai tarin yawa gareki, masoyiyar kwarai sakon soyayyarki ya iso gareni *ZAITUNA* *IBRAHIM* *SHARGALLE* nagode da kaunarki gareni nima ina qaunarki sosai ina godiya da addu,arki gareni son so=دÜ=ؘÜ>ØpÝ=Ø
Þ.






"Wai ke baiwar Allah baza kici abaincin naki ba kowa yaci ya barki, to tun wuri ma gwara ki manta da gida kiyi abinda ya kawoki dan matukar baki musu iya adadin shekarun da suka kamata kiyi ba babu inda zasu barki ki dara daga wannan bakin gidan" cewar wata mata dake shinfida zannuwanta a kasa da alama wurin kwanciyarta ne.
"Ni wlh na kada gane wane irin abinci ne wannan, sannan da kike maganar wasu shekaru ni ba muyi zance da wani cewa zanzo inyi rayuwa anan ba, kuma ma ni bangane me zanyi ba danni wlh duk a tunanina idan na isa makka sai dai in ci shinkafa kaza da madarar kwali kamar yadda ake bani labari amma sai na ganni a dokar jeji sabanin makka"lantana ta karasa fada idanunta na cika da kwalla dan ganin burinta bai cika ba ,kuma bata ga alamar zai cika ba.
"Gskia ne" yan dakin suka fada suna kwashewa da wata irin dariya data saka wani kululun bakin ciki yazo ya tokarewa lantana a makoshi dn ganin sun maisheta mahaukaciya.
"Haba bayin Allah maimakon ku mata bayani kwa ke mata dariya"cewar wata daya daga cikin wadanda aka kawosu dakin dasu lantana.
"Ni sunana zainab ana kirana da zee, ni yar kasar niger ce kuma wani dan uwana ne nasa ya min hanya aka dauki sunana a yan tahowa makka aikatau, amma makar gobnati wacce sai kaje kayi aikin tsawon lokaci suna rike kudin aikin naka, ma,ana sai sun dauki tun daga kudin passport kawo kudin jirgi da sauransu. sannan za,a fara biyanka kudin aikinka kaima ka dan tara wani abu.to sai wasu daga cikin shuwagaban ninsu suke kara shekaru akan wanda mutum zaiyi, dan kinga ni yanzu mun shiga shekara ta biyar a wurin nan amma har yanzu bamu da ko kwandala na kanmu ba domin me wannan gidan duk watan duniya sai ya biya duk wani ma,aikaci a gidan nan amma da yake ba da kudinmu muka zo ba ko kwandala bata zuwa hannunmu, amma in mun cika shekara biyar in muna da rabo su kaimu can kauyukan da suke makotaka da makka muke aiki muna samun dan abin tarawa ko mu samu shiga har cikin makka muna aiki a gidan larabawa muna samun kudade da diloli muna aikawa yan uwanmu kafin a kamamu a matsayin takaru"zee ta karashe maganarta tana kallonsu.

"Ni sunana rakiya ni yar Nigeria ce a garin sokoto nake .Eh to nima dai akan hakan muka taho, amma mu shekara uku suka ce zamuyi,kuma daman munyi na,am da duk inda aka kaimu zamuyi aiki tukutu.cewar wacce ta bukaci a yiwa lantana bayanin.
"Wlh tallahi ni ba da kudin kowa na taho ba da kudina na taho"cewar lantana da zuwa yanzu hawaye ya gama wanke mata fuska dan kiris ya rage ta gano an yaudareta.
"Kamar ya kudinki"cewar zee tana karkata kai ,tana jiran karin bayani
"Eh wlh kudina ne, na sai da duk wani abu dana mallaka ........nan dai ta kwashe komai ta fada musu yadda kawarta ta bata shawara da yadda tasa wani ya shige mata gaba duk ta labarta musu amma bata fada musu zancen boka ba na mallakar sarkin makka da zatayi=ØJÞ.

"Kai Amma gskia wannan mutane sun cuceki ,dan banace ta cuceki ba saboda hada baki sukayi suka zuraki a mazurari sukaci kudinki sai ki rungumi Kaddara" rakiya ta fada tana nuna jin tausayin lantana har cikin ranta.
"Daman hanyar makkar bashi ya miki amma bada kudinki aka biya miki ba"zee ta fada tana mai daukan kokonta ta fita domin ta wanke dan duk wanda ya cinye abincinsa sai ya wanke kokon yaje ya maida.
"Kaji kadan kaji da yawa" cewar wata cikin mutanen dake cikin daki.

Haka lantana ta cinye wannan abinci da batasan ko da sunanshi ba, amma tsabar yunwar dake barazanar cinye yayan hanjinta yasa ta cinye dan ba yadda zata iya.haka ta dauki kokon ta cewa rakiya ta rakata ta wanke ta maida Inca ake maidawa.
"Gskia bazan iya ba lantana , dan wlh tsoron gidan nan nake, kinga duk kafa ta dauke kowa ya shiga daki sai mutane jefi jefi gashi mu baki ba wani kan gidan muka sani ba, kema da kin cinye tun dadewa da kowa yaci da kin huta da fita yanzu.
"Haba dan Allah rakiya" cewar lantana da take tsaye bakin tangamemiyar kofar dakin da aka dinka katon buhu akayi labule dashi.kawai sai ta tuno da yar uwarta dariya (babar MARYAMU ) lokacin suna gidansu idan tana jin fitsari da daddare , sadiya take tasa daga bacci ta rakata ,gashi dai lantana ce Babba amma sadiya ita ke rakata ita kuma sadiyar idab zataje lantana bata rakata. "Allah sarki yar uwata " lantana ta fadi hakan a zuciyarta.
"Kinga muje nima inaso zanyi fitsari" zee ta fada tana yin gaba lantana tabita a baya.


Bayan zee tayi fitsarin ita kuma lantana ta wanke kokon abincinta ta mayar, sai suka tsaya a waje suke tattaunawa.
"To keda lantana banda abinki garin yaya har kika bari wannan kawar taki ta miki salalan tsiya har haka"
"Hmmmm kema dai kya fada zee kawai dai taje sun rabani da komai,
nawa gashi sarkin ma ban samu gani ba.nidai da in kara yarda da kawa har duniya ta nade"
"Haba ke kuwa lantana ay ba duka aka taru aka zama daya ba ,idan wani ya kika da wuni wani da kwana zai soka' zee ta fada domin ita kaifi daya ce dan gskia ta tausayawa lantana yaudarar da kawarta ta mata ,gashi zata dandani wahala a bakin gida kamar yadda suke kiran gidan.
"Hakane maganarki zee amma na tsorata sosai da dan adam "nikwa mmn AFRAH nace hmmm tunda kema kika ci amanar yar uwarki ay dole amana ta ciki hajiya lantana>Ø-Ý
"Karki damu akwai Allah"
"Hakane kam"
"To amma ke ya kikaji da kika ga kun doso wannan hanya lantana"
"Hmmm kedai bari zee a lokacin da muka hau jirgi sosai nake cikin farinciki , duk da ina cikin tsoro hakan bai hanani jina kamar an min albishir da aljanna ba. Har aka fara sanarwa cewa jirginmu zai sauka,to daman tun a Nigeria da muka shiga jirgi an raba mana wani abu kamar tuta yar karama, sai akace idan mun sauka a jiddah duk mai yar tutar nan ya taru a wuri guda,to ashe tutar shedar wadanda zasu kauyen nan ce kuma a cikinmu ma akwai wadanda aka ware aka tafi dasu to su ina ganin wani wuri mai dan gwabi gwabi aka kaisu dan ban kara ganinsu a cikinmu ba. A lokacin da aka kawo wasu motoci masu kyau da sanyin raba a cikinsu, duk muka shiga aka tafi damu,har aka kaimu wani gari amma ba makka bace kuma ba madina bace amma ba kyauye bane ,ai ina ganin mun tsaya na dakko kwallar turare na wanda zan sanya saboda sarki"
"Ban fahinta ba daman dazu naji kin kira sarki to dan kar in katse miki hanzari shisa ban tanka miki ba, wane sarki?"





""""""""'"""""""""""""""""
Washe gari ya kama asabar ranar kasuwar kauyen mai alkama, kuma ranar babu makarantar boko sai makarantar dare dan haka su MARYAMU ita da halima a gidan inna sukayi bitar karatunsu, sannan suka yi tilawa har suka kammala, inna sarai kwa tana gyaran alkama da zatayi funkaso a kasuwa dan gobe lahdi kasuwar gujungu, dan alkamar ma yawa gareta saboda kasuwar tana da girma sosai kuma tana ciniki dan funkason inna sarai badai laushi ba, ya tashi yayi kyau gwanin sha,awa ga taushe yasha naman rago da kayan kamshi abin sai wanda yaci zai adar.gashi tana sanya kalolin maggi masu dadin dandano sannan kuma Allah yana daukaka sana,arta saboda rikon marainiyar da take dan rikon maraya akwai ganin bude sosai a rayuwa .tunda gata dai dattijuwa amma kuma tana kokarinta na ganin ta kula da komai na yarinyar, ba kamar waccen uwarta ta hajiya lantana ba=ØJÞ data kwashe komai na mahaifiyar yarinyar tayi awon gaba dashi ba.


Kuma duk abinda ta dauka din matukar ba MARYAMU ce tace ta yafe mata ba, to sai Allah ya musu hisabi kan haka domin ba komai taci ba face wuta.saboda fadin Allah madaukakin sarki:
(Wadanda suke cin dukiyar maraya da zalunci , ba komai sukeci ba a cikin cikinsu face wuta, kuma suna a cikin wutar sa,ira).
Amma yanzu karancin imani yayi yawa mutane basu dauki cin dukiyar maraya a bakin komai ba ,basu san hakkinsa bane kai bama dukiyar maraya ba hatta shi kanshi marayan ba,a daukeshi a bakin komai ba wani daga lokacin daya rasa daya daga cikin mahaifansa koma dukansu to a sannan ne yake fara sanin menene kalmar maraici.Allah ka bamu ikon baiwa yaranmu tarbiya ingantacciya domin itace ginshikin rayuwarsu koda bama raye ,tarbiya da ilmin adddini, dana zamani ,zasu taka muhimmiyar rawa a tare dasu.

"Kuje ku wanke hannunku kuzo kuci abinci tunda na gama gyaran alkamar in Dubai muku abinci" cewar inna ta fada tana zuba musu dan wake da mai da yaji.
"To inna ay ko saboda corona virus ma wanke hannunmu, tunda ana fada mana a makarantar boko"halima ta fada tana dariya.
"Ke dalla rabu dani da maganar korola biris din nan, daman tun kan zuwan korola muna wanke hannunmu domin sunnar annabinmu ne wankin hannu da kuma bismillah kafin cin abinci"
"Inna bafa korola biris ake cewa ba, corona virus ake cewa"MARYAMU ta fada tana dariyar maganar inna sarai.
"Ke tunda ba maganar Allah da annabi bace ki dena gyara min, aya ko hadisi zaki gyara min ba karatun bature ba"ta fada tana ajje musu dan waken ta shige daki abinta.

Bayan ta fito daga dakin ta gansu suna cin abincin amma kowacce da inda ta mike kafar ta daban inda abincin yake daban.
"Haba diyan nan mesa kullum idan kuna cin abinci bakwa gyara zamanku kuyi zaman cin abinci? Ku nade kafafunku kusa abinci a tsakiyarku kuyi bismillah sannan kuke ci, kuma ku dena surutu idan kuna cin abinci dan ba dabi,ar cin abinci bane kuna magana sai kunje kun kwaru,kullum ana fada muku amma in kuna ci sai an kara tuna muku? To daga yau ba tini saidai kuji rankwashi irin ba wanda innarku jummai ke muku aka"ta karashe tana musu dariya dan ganin sun nutsu sun maida hankali.
"Daga yau ma bazamu sake ba"cewar MARYAMU.
"Insha Allah"halima ma ta fada domin sunji zancen rankwashi.

Haka suka nutsu sukaci abincinsu , sannan sukayi Sallah sai sukayi fita zuwa gidan iya mai daddawa.
"Assalamu alaikum"
"Wa alaikumus salam yan matan inna sarai masu komai dozin"cewar iya dake fidda alala daga gwangwanaye tana yankawa tana sanyawa a fanteka.
"Iya alalarce har aka sauketa" halima ta fada tana cire hijabinta ta rataye a igiya.
"Aikwa nayi ranama nake ga tunda har anyi sallar azzahar yanzu"
"Kuma yau kasuwa ba"maryamu ta fada tana zama a kan kujera yar tsugunno.
"Yanzu mutane zasu fara shigowa siya, yan cin kasuwa"halima ta fada itama tana samun wuri ta zauna.
"Iya ina baffa"cewar "MARYAMU.
"Wlh kwa nima tunda safe ban ganshi ba"Halima ta fada tana kallon iya.
"Ya tafi ruga gaisuwar abikinsa daya rasu baya nan.
"Shisa bamu ganshi ba"suka hada baki wurin fada.



Da yamma su MARYAMU sukayi kwalliya suka saka kayan da baffa ya siyo musu, sunyi kyau sosai musamman MARYAMU dan sosai hasken fatarta ya fito, suka fito dan zuwa kallon wasan birrika da akeyi ranar kasuwa da wasan miciji. haka yan garin suke kallonsu kamar wasu baki

Please Login or Register in order to submit comment