Join Our WhatsApp Group

Subscribe for N1000/month for downloading access and an ad-free site. Contact WhatsApp +2348140419490 if you can't pay / subscribe. SUBSCRIBE

FATTOMAH BOOK 1 Complete Hausa Novel Document by FATTOMAH BOOK 1


FATTOMAH BOOK 1

Cover Design Copyright and attribute to Marus Graphics

Uploaded by @Taskar

Total Words: 42519



FATTOMAH BOOK 1

Reading Time: 3 Hours

Added On: 25, Jul 2024

Author: Nanameera ,

Ebook Compiler : Admin

Author Group : MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION

Author Phone : 09086030007, 07041901078

Book License : Free

Category: Love Novels

File Size: 222.12 kb

File Type: txt

Views: 279+

Download: 195+

Last download: less than 1 second ago

Description/Story: [5/3, 4:20 PM] Nanameera: *FATTOMAH*

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION






*Nanameera ce#*







*ALHAMDULILLAH!! ALHAMDULILLAH!! I'm so grateful to Allah subhanahu wata'ala for giving me the privilege to finished my book SHEIKH HEESHAM, I'm so grateful to my lovely fans I really luv you from the bottom of my heart nd my Role model Na'ima Sulaiman Sarauta(Nimcyluv) my regards to yhu Aunty nimcy. Now I'm back with another unconditional love book FATTOMAH don't miss it dears*



Page 1-2.



Hadari ne haɗaɗɗe a sararin samaniya banda guguwar iska babu abinda ake iya ji dubbannin mutane suna tattara kayansu domin kada ruwan saman ya iskesu domin a wannan lokaci ana tsaka da damuna ne babu tabbacin idan ruwan ya sauka ya dakata da wuri, cikin wannan yanayin take tafiya kamar wacce kwai ya fashewa a jiki, bakinta sai rawar sanyi yake da alama tana matuƙar jin sanyin da yake tashi. Yarinya ce ƙarama dan bazata shige 15-16yrs ba amma yanayin halittar jikinta zaka ɗauka takai irin 18yrs ɗin nan, tsayawa tayi da tafiyar ta durƙushe nan wajen tana riƙe ƙafarta sosai takejin ciwo a cikin ƙafar gashi kuma bata kusa zuwa gida ba babu kuɗi a hannunta bare tayi tunanin hawa ko keke napep ne dazai kaita gida, tana nan wajen durƙushe kusan 8mins wani mutum yazo shigewa har ya yi gaba sai kuma ya dawo ya tsaya yana kalllonta batareda ta san yana yiba


"Keee me kike yi anan kina ganin hadari ya haɗo?"


Sai a sannan ta ɗago runannun idanuwanta ta kalleshi amma ta gagara furta koda kalma ɗaya domin zuwa wannan lokacin jikinta banda rawa babu abinda yake wanda ke nuni da cewa ciwonta na gab da tashi, girgiza kai mutumin ya yi ya ce "ke kam kurma ce ko bebiya?" ba tare da ta ce komai ba ta miƙe tana dafe kanta wanda yake barazanar tsagewa a kowane lokaci. Gaba tayi mutumin ya bita da kallo yana mamakin hali irin nata to kodai bata ji ne???? ɗaga kafaɗarsa ya yi alamar bai dameshi ba sannan ya cigaba da tafiyarsa. Da sallama ta shige tsakar gidan nasu wanda bashi da girma ko kaɗan tana zuwa ta zauna gefen mahaifiyarta tana lumshe idanuwanta wanda take jin suna yi mata nauyi a kowane lokaci,


"Fattum jikin ne?"

Hawaye na gangarowa kan kuncinta ta ɗaga mata kai ajiyar zuciya ta sauke cikeda damuwa ta ce" sannu kinji Allah ya baki lafiya ya rabaki da wannan ciwon da yake damunki" shiru Fattomah ta yi ta kwanta kan cinyar mahaifiyarta nan da nan bacci ya ɗauketa. Zaune suke akan tabarma suna cin abinci cikeda kulawa ya ce" Faɗimatoh ya jikin naki?" tana kallonsa ta ce" Abbana da sauƙi kawai ƙafar ce har yanzu tana yi mini ciwo sosai" "Allah ya yaye miki gabaɗaya in Sha Allah" jinjina kanta tayi ta ce" Allah yasa Abba" ganin ba cin abincin take ba yasa ta ce" Fattum bafa kya cin abincin" turo baki gaba tayi cikeda shagwaɓa ta ce" koba na ƙoshi ba Ammi" girgiza kai Ammi ta yi ta ce"A'a me kika ci da zaki ƙoshi?, ki daure ki ci ko kaɗan ne kinga zaki sha magani" ranta a haɗe ta kalli Ammi sai kuma ta ɗauke kanta tana ƙunƙuni wanda basu san abinda take cewa ba


"Faɗimatoh ki ɗauki abinci ki ci kinji"


Kwaɓe fuska ta yi cikeda zallar shagwaɓa ta ce" ayyah Abbana wlh na ƙoshi sosai I'm full fa" numfasawa ya yi ya ce"kin tabbata?" da sauri ta gyada masa kai ya ce" shikenan ki je kisha magungunanki sai ki kwanta ki samu hutu" babu musu ta miƙe ta shige wani ɗaki wanda ya kasance ɗakinta ne. Tana shiga ta zauna kan katifar da take shimfide a ɗakin wata leda ta jawo ta buɗe tana ƙarewa magungunan ciki kallo sachet ɗin PCM ta buɗe ta ɓalla har ta kai bakinta sai kuma ta yi saurin yarda shi tana ƙoƙarin yin amai, yana ɗaya daga abinda Fattomah ta tsana a rayuwarta kenan wato sha magani duk irin lalurar da take tofa bazata sha magani ba kuma bazata yarda ayi mata allura ba saidai idan Abbanta ne zai kai ta ko kuma ya zaunar da ita ya bata maganin toh shine zata yarda tasha shima kuma tana kuka. Harhaɗa magungunan tayi duka cikin ledarsu ta ajiye daga gefen katifar ta koma tayi kwanciyarta.



Kalle-kalle ta shiga yi ganin yanda ko'ina na tsakar gidan nasu ya jiƙe ta tabbata jiya da daddare ba ƙaramin ruwan sama akayi ba, wata ƙara ta fasa ta tsuguna nan bakin ƙofar ɗakinta ta rushe da kuka da sauri Ammi ta taso daga wajen gawayin da take kunnawa daidai nan shima Abba ya shigo daga waje, sosai take kuka kamar wacce aka cewa iyayenta sun mutu Abba ya ce"lafiya Faɗimatoh?" sake rushewa tayi da kuka ba tare da ta basu amsaba girgiza kai Ammi tayi ta ce" kodai jikin naki ne?" kallonsu duka tayi sai kuma ta fashe da wani sabon kukan tana ƙoƙarin birgima a ƙasa, tsayawa sukayi duka suna kalllonta dan ita Ammi ma ta ɗauka aljanu ne suka shiga jikinta Saida tayi mai isarta sannan ta fara sauke ajiyar zuciya


"Yanzu faɗa mana ke dawa?"

Kallon Abbanata ta yi cikin sheshsheƙar kuka ta ce"Ab... Abba.. Abbana koba takalmina bane ya jiƙe a tsakar gida da ruwan sama...." Sake rushewa tayi da wani kukan ita kuwa Ammi tsabar baƙin ciki kasa magana tayi kawai ta juya ta koma kan Abinda take, cikeda nuna kulawa da kuma rarrashi ya ce" shikenan kiyi haƙuri zan siyo miki wani sabon takalmin amma fa sai kinyi shiru da bakin ki, kuma kinje kinyi sallah" goge fuskarta ta shiga yi tana gamawa ta miƙe tana sake kallon tsakar gidan dan ita idan da abinda ta tsana tofa bai shige ganin waje a jiƙe ba shiyasa kullum takalmanta suna cikin ɗaki dan duk randa akayi rashin sa'a suka jiƙe tofa sai hankalin kowa ya tashi, a hankali kamar wacce ke taka kashi haka ta ƙarasa ta ɗauki takalmin nata ta sanya sannan ta ɗauki buta, girgiza kansa ya yi ya ce" Allah Ubangiji ya shiryeki Faɗimatoh".



Shiryawa tayi cikin uniform ɗinta ta fito tana kallon Ammi ta ce" nikam Ammi tafiya zanyi karna makara Kinga yau nice da duty" kallonta Ammi ta yi ta ce"amma dai kin tsaya ki fara cin abinci ko Fattum?" Girgiza kanta ta yi tana sanya takalminta ta ce"kawai saina dawo zanci ai yau bazamu kai 4pm ba" shuru Ammi ta yi dan tasan tunda ta ce haka ko za'a kasheta bazata ci abincin ba, Saida ta gama sanya takalminta ta ɗauke jakarta tana kallonta ta ce"zan tafi ki yimin addu'a Ammina" murmushi ta yi ta ce" Allah ya kiyaye hanya ya tsaremin ke ya kareki daga dukkan abun ƙi Faɗimatoh" murmushinta mai kyau tayi ta ce" Ameen Ammina saina dawo" bye bye tayi mata sannan ta juya ta fita tanajin nutsuwa na saukar mata tabbas tana matuƙar so da ƙaunar iyayenta kamar yanda suma suke nuna mata soyayya.


Malamin Geography ne ya shigo musu dole kowa ya yi shiru domin ko kaɗan baya ɗaukan nonsense shiyasa duk irin surutun da suke da zarar ya shigo kowacce zata shiga taitayinta banda Fattum dan daman ita duk wani malami da ake jin tsoronsa tofa ita shine abin rainawarta kwata-kwata bata ɗaukesa mutum ba shiyasa kullum cikin hukuntata yake amma kamar abanxa dan hazaka ɗauka ita yake yiwa wannan hukuncin ba. Yauma kamar kullum yana shigowa ta kwanta kan desk ɗinta wanda suke zaune su uku tanaji ya ce kowa ya ɗauko littafinsa kuma karya zo ya tarar dakai baka rubutu amma tayi kwanciyarta abinta, desk ɗinta taji an daka cikin baccin daya fara ɗaukanta ta buɗe idanunta tana murzasu ta kalleshi, yanda ya haɗe fuska kamar wani mala'ika sai abin ya bata dariya, cikin kakkausar murya ya ce


"Get out!!"

Kallonsa ta tsaya tanayi kamar ma bata gane abinda yake nufi ba, kalllonta ya yi ganin yar ƙaramar yarinya na neman raina masa hankali ya ce cikeda masifa" I'm talking to a doll?" shuru ta kuma yi masa for the second time, a fusace ya fincikota daga kan desk ɗin ta waɗo nan ƙasa amma ko kaɗan babu alamun zatayi kuka dukda saurin kuka irin nata, dawowa ajin ya yi da wani sanda na bishiya yana zuwa ya dinga ɗaukanta da ita ko ta'ina amma ko tari batayi ba sai sauke ajiyar zuciya ta dinga yi Saida ya gaji dan kansa sannan ya rabu da ita ya koma gefe yana sauke numfashi, duk ɗaliban da suke cikin ajin sunyi shuru sai binta suke da kallo ganin yanda tayi shuru amma fuskarta tayi jajawur wanda shine zai tabbatar maka da cewa taji dukan a jikinta kawai dai taurin kanta yasa bazata yi kukan ba. Kusan 5mins...


Read / Download FATTOMAH BOOK 1

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .

START READING

OR

Login Register

Please Login or Register in order to submit comment

Releted Novels

Releted Album