Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»Ώ[8/28, 9:08 PM] Aisha A Yabo: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*ILLAR AUREN DOLE*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


*Tare da alk'alamin Aisha A Yabo Fulani,*


*Β© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUMπŸ„*
β˜†We the best β˜†

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* [email protected]

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1

*MANUFARMU ANNABINMU*

*YA RASULILLAHI MANUFARMU KAI A FARKO MANUFARMU KAI A QARSHEN MUNA NEMAN TAIMAKON KA DAN MUTUN CIN NANA FAD'IMA*

*barka da JUMA'ATU BABBAR RANA*


_sadaukarwa ga duk macen da ta tsinci kanta arayuwa ta AUREN DOLE, Allah ya Baku hak'uri da jureyar wannan babbar jarabawar_

*Kira ga iyayanmu, dakuji tsoron Allah ku kuma tausaywa yaranku da Allah ya bamu amanarsu, ku daina tilasta yaranku auren wanda basa so, aure anayin sa ne dan durewar sa har abada, amma ba agina rayuwar aure kan soyayya ba, taya zai d'ure, bak'in cikine zallah aciki, wannan auren zai iya sauya ma tarbiyar yarinya, agyara dab Allah iyaye*πŸ™πŸ»πŸ˜­


*1*

Wata 'yar matashiyar budurwa ce ta k'arasu wajan wata yarinya da za suyi sa'annin juna, tace

"Bistey tun d'azun fa ina can ina yawun nemanki ashe kina nan"

ta fad'a dai dai sanda take zaunawa kan kujeran ruban da aka k'awata wajan cin abincin,

wace aka kira da bistey ta d'ago fuskarta daga duban littafin da ke gabanta, da alama nazari take yi,

cikin murmushi tace "ayya yi hak'uri bistey da zan zo nan malam Hashem ys aiki ki shiyasa nazo nan, amma ai nace Nabila tukur ta fad'a maki"

"ok bamu had'u ba, kinga nifa yunwa nake ji"

ta fad'a tana shafa cikinta cikin ya mutsa fuska,

"Kai bistey idan dai ciki ne sam ba kya wasa da shi, mi zamu ci"?

"ah kema dai kin san bana wuci donot da cok"

"ok ni kam limo kawai zan sha, nan suka kira d'ai daga cikin ma'aikatan wajan suka fad'a mata abunda za akawu.

suna gamawa suka koma aji ganin lokacin komawa yayi, biyu aka tashe su, 'yar b'urb'ura suka shiga kasan cewa ugnuwarsu d'aya.

suna zowa ko wace ta yi hanya layinsu akan sai kuma da yamma idan an had'u islamiya,

tana shiga gidan nasu kai tsaye d'akin mamansu ta shiga fad'awa kan kujera tayi tana fad'in "wash!"

Mama da idar da sallahn ta kenan tana karanta littafin addu'oi ta juyo tana kallonta cikin fad'a tace

"Oh ni Asma'u, wai Balkisu yaushe za kiyi hankali? sabida Allah ki shigo man d'aki ba sallama"

turo baki Balkisu tayi tana cewa "kai Mama na fayi sallama jini bakiyi ba"

"da yaki kurma ce ni ba" murmushi Balkisu tayi tana fad'in "yi hak'uri Mamana na daina insha Allah, wallahi gajiya ce na kwasu,

ga 'yar banzan rana yau da aka kwad'a agarinan"

"Hum kyaji da shi, yanzu kalli ko takalmi baki cire ba kin wani shigo dasu d'aki kamar k'aramar yarinya"

cikin sauri ta zami takalmin tana dariya,

tana ciri Hijab tace mama yunwa nake ji yau mi aka dafa mana"?

"idan kinje kitchen d'in ko mi aka dafa gani za kiyi ai"

tashi tayi ta fita zuwa kitchen d'in da murna ta dawo ta zauna kusa da Mama

"wayyo mamana dad'i na gode maki da kika mana d'an wake, Allah ya k'ara maki lafiya da tsawon rayuwa da ke da Abbana"

cikin murmushi Mama tace "amin d'iyar albarka".


da dare suna zaune tare da Abba da Mama suna fira Abba yace "mai gadon zinari yaushe ne zaku gama makaranta"?

"Abba saura wata uku insha Allah muyi Kandy"

"madallah Allah ya nuna mana, hadda fa? dan akwanakki kince man saura kad'an ki idar"

"uhm saura hizu goma Sha biyar insha Allah, litattafan ma har mun sauke wasu mun fara harda"

"yayi kyau Allah ya taimaka ina alfahari da ke Balkisu,

ki d'aya muka haifa amma kin zame mana 'ya tamkar dubu, Allah ya maki albarka"

dukan su suka amsa da amin, haka suka cigaba da firan su ciki farin ciki.


suna zaune cikin aji sai hayaniyar d'alibai suke, balkisu da aminiyarta Ummu suna gefe suna karatu,

kafin daga bisani Ummu ta rufi kittafinta tana kallon Balkisu tace "beste kin san mi"?

kad'a kai tayi tana fad'in "Aa sai kin fad'a"

cikin gyara zama tace "yawwa ina gayenan na kusa da gidanmu"?

cikin ya mutsa fuska tace "ni wani gaye na sani na kusa da gidan ku, kawai fad'aman miyi mutuwa yayu"?

duka Ummu ta kaimata abaya "kai wallahi wani lokacin iskancinki yawa ne dashi, daga tambaya sai kiran mutuwa,

kinga iskanci ne duk kinsan wa nake magana, Haris d'an gidan alhajin Allah,

Kin san tun sanda ya ganmu tare ya nace yana sonki,

kuma k'arya ne kice baki gane shi ba,"

"mts to miye idan na gane shi, goya shi zanyi, ni fa bana son kwashe kwashe , ba tara samari 'yan I love you ne agabana ba,

sarai kin sani karatu ne agabana burina na zamo likita, pls karki koma yi mun maganarsa"

Ummu ta kalleta tsantsar gaskiya ta hango acikin kwayar idanunta, cikin girgia kai tace "amma dai kin san na fad'a maki baya da matsala duk na fad'a masa,

ya kuma ce yaji ya gani yana sonki auren ku ba zai hana ki karatu ba,
wallahi yana da kirki sosai Bistey,

Karkiyi wasa da damarki, ki bashi dama dan Allah, kinga ni ya matsa man da zan cin ki"

"Ni fa Biste ba ruwana kawai karma ki k'ara zo man da zan cin sa Allah, taya zan had'a karatu da soyayya"

Ummu za tayi magana Balkisu tayi saurin d'aga mata hannu "dan Allah Biste ki bar maganar nan haka"?

shigowar malami ne ya sa dole ummu tabar zancin.


*Bayan kwana biyu*


Ranar juma'a da wuri aka tashe su makaranta, tana zuwa gida jakarta kawai ta ajiye ko kayan makaranta bata cire ba ta shiga kitchen tana taya Mama aikin abinci,

suna idarwa taje tayi wanka, dama tana fashin sallah wannan yasa kaya kawai tasa riga da sikit na kanti masu yalwa, ta kwanta tana duba wani asamint da aka basu makaranta daga haka barci yayi awun gaba da ita.

"Salamu alaiku" Mama da fitowarta kenan daga ban d'aki taji ana sallama tana ajiye buta ta amsa da


"Amin alaiki Salam, ah maraba ummu yau kece agidan namu"?

cikin murmushi tace "eh wallahi, Mama ina wuni"

"lafiya k'alau Ummu, ya iyayan naki"?
"lafiya k'alau suki sunce a gaishe ki"
"Madallah ina amsawa, shiga k'anwar taki tana ciki barci take"

"to mama" ta amsa tana mai kutsa kai cikin d'akin Balkisu,

tana zuwa ta d'ana mata duka a cinya, zumbur Balkisu ta mik'i tana shafa wajan a tsoraci,

dariyar da Ummu tasa ni ya sa ta saurin duba wajan da take zaune gefin katifa,

"amma wallahi ki d'in ko muguwa ce, Allah ba zan yarda ba sai narama"

ta fad'a tana shirin kaiwa ummu duka, da sauri ummu taja baya tana dariya tace "haba my beste yi hak'uri"

"ai wallahi baki isa ba, sai na rama" nan suka shiga 'yar tsere cikin d'akin, Mama da taji hayaniyar tayi yawa ta lik'o tana fad'in

"kai lafiya, Mike faruwa kuke hayaniya haka"?

cikin turo baki da shagwaba Balkisu tace "Mama tana zuwa fa kawai ta dakeni, shine ba zata bari na rama ba"

"Mts wallahi ku kam Allah ya canza maku hali, ba yanda zaku had'u baku sayar da hali ba"

"wayyo Mama tun fa amakaranta tasan munyi magana zamu je walimar Safiyya Adam 'yar islamiyar mu da zatayi aure,

shine tazo take barci ko shiryawa batayi ba, shiyasa na d'anyi mata duka, kuma fa Mama kad'an nai mata"

"hum ko dai kuka sani, Ke balkisu ki tashi ki shirya ku tafi, ku samu ku dawo da wuri"

"to Mama" ta fad'a tana mai bin hanyar fita,

har takai k'ofa tayi saurin shammatan Ummu ta kai mata duka, ta fita da gudu ta fad'a ban d'aki tana dariya,

"kam wallahi yarinya kin d'au bashi" Mama dariya tayi tare da shigewa d'akinta tana cewa "halinku kenan ba kwa had'uwa baku yarda hali ba.

suna fitowa wajan walima Balkisu tace "beste kinga kusa da gidan Yaya Ahmad ne mu biya mu duba shi, jiya ko da yazo gida naji yana fad'awa Mama baya jin dad'i"

"ok muje, Allah ya bashi lafiya"
"Amin".

da sallama suka shiga gidan, Affan kawai suka tarar a tsakar gida, da saurin sa yazo yana masu oyoyo oyoyo,

rungumeshi Balkisu tayi tana shafa kansa yace "my Affan nayi kewarka, ka daina zuwa mana"

cikin shagwaba yace "Aunty Dady ne yace sai munyi Hutu sannan zai kaimu gidan Mama"

"ayya bakomai, ai kun kusa ko"
cikin gyad'a kai yace "eh"

Ummu tace "ina adda Jidda"

"sun fita da Aunty Meena" (k'anwar mamansa)

"Momy fa"?

"tana kitchen" rik'i hannunsa tayi suka wuce kitchen,

"ah 'yan mata adon gari, yau ko ni agidan namu, lallai na taki babba sa'a"

"Kai aunty kin jiki da wata magana, Allah idan wani yaji sai ya zaci bama zuwa"

harararsu tayi kafin tace "yaushe rabun ku da gudanan harfa na manta"

dukansu sukayi dariya, kusan atare sukace "afuwan Aunty makaranta ce ta b'oye mu,

ya jikin Yaya"?
"alhamdulillah yaji sauki, yau dai kam ko masallaci baije ba, kuje yana d'akinsa,

kuma taimaka man mu kaiwa bakin sa dan Allah"

abinci da abunsha suka d'auka zuwa d'akin Yaya Ahmad.

tana ajiye abinci ta matsa kusa da shi ta zauna kamar zata shige jikinsa, "Yaya ina wuni ya jiki"

rik'i hannunta yayi yana cewa "lfy kalau auta, alhamdulillah jiki yayi sauk'i, yasu Mama"?

"lafiya k'alau suki, bamu ma fada zamu zo ba, munzo walima Nan unguwar nace muzo mu duba ka"

"kun kyauta nagodi" Ummu da take zaune gefin kujera ta gaishe shi da jiki, ya amsa cikin fara'a yana tambayar mutan gidansu,

suka gaida bak'in tare da mik'ewa tsaye Yaya zamu tafi Allah ya k'aru sauki"

"haba auta tun yanzu"

cikin shagwaba tace "Yaya bamu fad'awa Mama ba"

"naji duk da haka ku bari ayi magarib sai muje na kaiku, dama ina so na je"

"to Yaya" suka fad'a tare da barin d'akin

d'akin aunty suka shiga suna ta firan su.

d'aya daga cikin abokanan Yaya Ahmad da tun shigowar su Balkisu ya kafeta da idanu,

bayan fitarsu yace "injiniya wad'annan fa"?

"k'anne na ne"
"Allah sarki yara masu hankali"

cikin murmushi Yaya Ahmad yace na gode sosai, nan suka ci gaba da firan su, kafin daga bisani sukayi masa sallama, anayin sallah magarib ya kwashe su a motarsa, sai da suka ajiye Ummu sannan suka wuce gida.


*Karku manta kuna tare da Aisha A Yabo, ta Annabi S.A.W nake maku fatan Alkhairi*
[8/28, 9:08 PM] Aisha A Yabo: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*ILLAR AUREN DOLE*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*Tare da alk'alamin Aisha A Yabo Fulani*


*Β© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUMπŸ„*
β˜†We the best β˜†

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* [email protected]

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1


*MANUFARMU ANNABINMU*

*NA KASA MALLAKAR HAQURINA*

*MADINA TAYI SANSANI AQIRJINA*

*INAMA YAQININA YA GASGATA BURINA*

*KAMAR AJALINA YANA CIKIN RASHIN ZUWA NA MADINA*

*YA ALLAH KA GAFARCEMU KA WANKE DAUDARMU TA RUHI DATA ZUCIYA KA SADAMU DA SHUGABA KALAMUNCE MANA ZIYARAR MAI GIDA KAFIN ZUWAN AJALINMU*

*SOYAYYA NANA FAD'IMA BA AIBU BANE*
*DARAJACE GA MAI RABO*


*Ga ba d'aya nvl dinan sadaukarwa ne ga duk matan da suka tsinci kansu a AUREN DOLE, Allah Ubangiji ya baku hak'uri da juriyar cinye wannan babban jarabawan, Allah ya kawu sauyi da HASKE arayuwarku ta duniya da lahira*πŸ™πŸ»

*3*

Bayan sa jingini yake jikin bungon suron, duka hannayinsa cikin aljihunsa, ya zubawa k'ofar da zata fito ido ciki da zak'uwa,

sai dai sautin kukanta yasa komai nasa ya tsaya cak, ga ba d'aya sai yaji jikinsa yayi sanyi,

tsaye ta masa k'im tana jiran taji da me yazo kafin ta wanke shi,

zuba mata idanu yayi ciki da damuwar ganin hawayen da ke zuba afuskarta, cikin sanyin murya yace

"kiyi hak'uri ban zace zuwan nawa zai saki damuwa harda kuka ba, dan Allah kiyi hak'uri kinji"?

har cikin jinin jikinta taji muryar na ratsata, wani irin sanyi taji da natsuwa, sai ta tsinci kanta da had'iye kukan ba tare da ta shiryawa hakan ba,

"kinji kiyi hak'uri"
ta sake tsintar muryarsa mai dad'i da sanyi,

cikin inda inda tace "u..u..m.m.b.b.a.k.m"

ajiyar zuciya yayi kafin ya koma cewa "ba dai zuwana ya saki kuka ba ko"?

sunkuyar da kai tayi tana wasa da k'asan mayafinta, ba tare da ta iya cewa uffan ba,

murmushi yayi kafin yace "duk da baki ban amsa ba, alhamdulillah naji dad'i sosai da kika daina kukan, da fatan kina lafiya"?

"lafiya k'alau" ta bashi amsa cikin yin k'asa da murya hakanan ta tsinci kanta da jin kunyarsa,

"am sunana Mahamod abdulnasir, ina zaune ..... magana ta gaskiya ina ganinki ne aduk sanda zakije islamiya,

ganin farko da na maki naji kin mun ma'ana ina sonki, so ba na wasa ko yaudara ba, so ne na aure,

ya nayinki tarbiyarki sune suka yi jagura wa zuciyata ta fad'a sonki, har dai na bin cika gidanku cikin yardar Allah na samu"

yaja numfashi kafin ya cigaba da cewa "Balkisu gani agaban ki da k'ok'on barana, da fatan zan samu kyakyawan masauki a zuciyar ki,

ba koma zan b'oye maki ba, ni d'in talaka, d'an gilulu ne ni"

ya k'arasa maganar cikin wasa,

shiru tayi ta kasa cewa komai, sai dai har ranta tana jin saukar muryarsa mai dad'i tare da dad'ad'an kalamai,

jin shirun yayi yawa yace "oh Balkisu dan Allah kice wani abu dan Allah kinji"?

barin wajan tayi da gudu tana murmushi,

da murmushi afuskarsa ya bita da kallo aransa yana addu'a Allah yasa Balkisu rabunsa ce, dan yana jinta har cikin jinin jikinsa,

ba dan yaso ba ya tafi aransa yana jin lallai goben ma sai ya dawo dan yaji ina aka kwana.

abakin k'ofa ta tsaya, sai da ta dai daita na tsuwarta sannan ta shiga gida.


kallon mamaki ya bita da shi, ganin yanayin da ta fita ba da shi ta dawo ba,

sai sussuna kai takeyi, mik'ewa yayi tsaye yana fad'in "to Mama auta ta dawo zan tafi"

cikin murmushi tace "Allah ya tsare agaida kishiyata da mai gidan kwali"

"zasu ji insha Allah"
"Yaya ina gaida yara da aunty"

cikin mamaki ya kalleta "iyye autar Mama yau ba ko rakiya ko"?

b'oye fuskarta tayi tana dariya tace "Aa Yaya, dama fa tasuwa zanyi"

ta fad'a tana mik'ewa tsaye, Mama tace maza koma ki zauna, kai kuma sauka lafiya"

cikin dariya yace "oh Mama duk tsarunne yasa aka hanata rakiya, to na tafi ina gaida baba idan ya dawo"

itama cikin dariya ts bashi amsa "zaiji"

har cikin ranta taji dad'in da Mama ta hanata binsa, dan bata san mi zata ce masa ba,

yana fita tayi saurin yiwa Mama sai da safe, dan bata so ta yi mata tambaya akan bak'onta,

"yau ba za ajira Baban ba"

"Mama barci nake ji"

"to Allah ya tashemu lafiya"

"Amin Mama" ta fad'a tana mai shigewa d'akinta.

ranar kam barci tayi mai ciki da mafarkin Mahamod, dan kuwa ba k'aramin shiga ranta yayi ba.

washe gari haka ta tashi cikin farin ciki da tunanin Mahamod, cikin sauri ta shirya, koda Ummu tazo har ta kimtsa,

rik'i baki tayi tana fad'in "ah Lallai yau anyi abun kirki, nazo ban tsaya jira ba, kin shirya"

fuskarta d'auki da murmushi tace "oho maki dai ni yau bana jin fad'a,

"aikam dai naga alama, har wani annuri naga fuskarki tana yi, miye sirrin"?

tana d'aukar jakkar makarnta tace "indai gulma ke cinki komai ba za kiji ba, sai dai tasan yanda tayi da ke"

dariya Ummu tayi "lallai Bste wallahi ban yarda da ke ba"


dariya Balkisu tayi ba tare da tace komai ba, sukaiwa su Mama sallama.

a hanya sai dubi dubi take kamar mai neman wani abu,

"wai bste miye ne naga kina ta dubi dubi"?

"wayyo bste yaushe kika iya sanya ido? to ba komai, yawwa ga napep nan bara mu tara, Allah yasa ba kuwa"

"Amin" cewar Ummu, sunyi sa'a ba kowa suka shiga, tare da fad'a masa inda zai kaisu.


da dare taita zuba ido ko zai zo shiru, ko mutsin yara taji sai ta lek'o da tunanin ko shine ya aiko su,

Mama da take kule da ita tace wai ke mi yake damunki? Sam bakya cikin natsuwa"

cikin inda inda tace "bakomai fa Mama"
"ai shikenan tunda kince ba komai"

Mama ta fad'a ba dan ta gamsu da amsar ba,

"kinga tashi kije ki d'auko fura a firj ki damawa Babanku, nasan yanzu yana hanyar dawowa"

"to Mama, da nono za adama ko da yagot"?

"Aa yagot na nan da yayanki ya kawu da safe, ki damasa da shi".


tsawon sati da zuwansa amma ko mai kama da shi bata sake gani ba, idan akazo sallama da ita ba gardama take zuwa,

har mama na mamaki, yarinyar da ko yaushe sai tayi da gaski da kuka take zuwa jin kira, amma yanzu ana zuwa take fita,

sai dai da taje taga ba shi bane zata dawo tana tunziri tunziri,

ita dai mama idone nata.


*Karku manta kuna tare da Aisha A Yabo Fulani ta Annabi S.A.W*
[8/28, 9:08 PM] Aisha A Yabo: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*ILLAR AUREN DOLE*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


*Tare da alk'alamin Aisha A Yabo Fulani*


*Β© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUMπŸ„*
β˜†We the best β˜†

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* [email protected]

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1


*MANUFARMU ANNABINMU*


*WANDA YA CIKA CIF KAFIN YA BAYYANA DAYA NE SHINE ABBAN BATULA*

*AMINCIN ALLAH YA TABBATA GARE DAIDAI CIKARKA YA NAJAMUL'HUDA*

*WANDA YA SAN KOMAI KAFIN SANI YA SAMU SHI KADAI NE SHINE ABBAN SAYYADA ZAHRA'U*

*AMINCIN ALLAH YA QARA TABBATA GARE KA ADADIN YAWAN SANINKA YA BAHARUN-NADA*


*Ga b d'aya Nvl d'inan sadaukarwa ne ga duk matan da suka tsinci kansu a AUREN DOLE, Allah Ubangiji ya baku hak'uri da juriyar cinye wannan babban jarabawan, Allah ya kawu sauyi da HASKE arayuwaeku ta duniya da lahira*πŸ˜­πŸ™πŸ»

*ina mai baku hak'uri kuskuren da nayi pj1 Abba yake cewa ina alfahari da ke ke days na haifa kin zame man ya d'aya tamkar dubu, su biyu ne suka haifa*


*2*

Ranar lahadi koda k'arfe takwas tayi har ta gama aikinta ta shirya,

d'akin Mama ta shiga tana walwale farin Hijab d'inta da sallama ta shiga,

sai da aka mata izini sannan ta shiga, "mama na shirya zan wuce islamiya"

"to Balkisu Allah ya tsare, sai kin dawo, dan Allah ki kula da kanki sosai kinji"?

"eh Mama insha Allah, Umma ina Abba ba dai bai dawo ba"?

"eh bai dawo ba, dama yace daga wajan zanin suna zai biya gidan malam Iliya karb'o wani sak'o"

"Allah ya dawo da shi lafiya na tafi"

"Amin, Allah ya tsare"

Hijab dinta tasa har k'asa sannan ta d'auki jikkarta da ta ke ajiye akan tagar d'akinta ta rataya, ta fita tana cewa Mama idan Abba ya dawo ta karb'ar mata kud'i akwai littafin da malam mai fik'ihu yace su saya.

gidansu Ummu ta wuce sai ta biya mata sannan su wuce tare dama islamiyar tana ta wajan layin su Ummu,

gab da zata kai gidan su Ummu ta wuce wasu maza su uku ko kallonsu batayi ba tayi wucewarsu,

dukansu suka bita da kallo, Mustafa yace "kai wannan yarinyar mugun haushi take bani wallahi"

"Wallahi kuwa nima haushin ta nake ji, yarinya sai shige iyayi" cewar K'asim,

da mamaki Mahamod ya kallesu yana fad'in "kukuwa mi ta tare maku ne haka?

naga dai ko da tazo ko kallon banza batayi maku bare kace haka"

"Hum kai mutumina yarinyar ce ta fiye ji da kai, ga rashin yiwa mutane magana"

murmushi Mahmoud yayi kafin daga bisani yace "ni kuwa kunga magana ta gaskiya burgini takeyi,

wannan ne karu na uku da nake ganinta, kuma cikin natsuwa da shiga ta kamala,

sannan abunda kuke gani ji da kai, gaskiya ba ji da kai bane, sanin kanta ne yasa ta haka, kuma hakan dai dai ne,

mace mai kamun kai itace mace tagari, tana burgini"

kusan atare K'asim da Mustafa suka k'yk'yace da dariya suna tab'awa, "lallai mutumin wannan dogon sharhi haka, ko dai kodai"?

cikin harar su yace "oho kudai kuka sani, ni dan Allah d'auko man takardun ina so na wuce, yau ina da abubuwa da yawa"

Mustafa ya shiga gida yana fad'in "Allah abokina ban yarda dakai ba, kawai ka fito ka fad'amana abun da ke zuciyar ka"

gyad'a kai kawai yayi yana saurarin shak'iyancin abokananan,

fitowar Mustafa yayi dai dai da fitowan Balkisu da Ummu,

suna tafe suna firansu da ka gansu kasan suna cikin farin ciki, karb'an takardun Mahamod yayi tare da yi masu sallama.


*Bayan sati biyu*

da dare bayan sallah Insha suna zaune suna fira Mama da Yaya Ahmad da yayi masu shigowar dare sai dai bai tarar da Abba ba,

Balkisu ta kwantu jikinsa tana zuba masa shagwaba,

Mama sai fad'a take yi mata, "wai ke Balkisu ba zaki barshi ya huta ba, daga zuwansa kin d'ani jikinsa, shigen son jiki kamar mage"

cikin turo baki tace "Yaya kana jin Mama ko"

yana shafa kanta ya kalli Mama fuskarsa d'auke da murmushi yace "Mama barta tayi abunta auta ce fa, kuma idan bata mun ba wa zatawa"

"ku dai ku ka sani ai wallahi kai da malam ku kuke sakanta ta tanawa mutane tab'ara"

Mama ta fad'a tana mai tab'i baki, Yaya zaiyi magana wani yaro ya shigo da sallama,

Mama ce ta amsa sallamar, "Maman Balki ina wuni"?

"lafiya k'alau Tijjani, ina ka fito da darenan, ince maminka bata san futowarka ba ko"?

"Aa ta sani itace ta aikini kantin Sani, to na dawo zan shiga gida shine wani saurayi yace dan Allah na shigo na masa sallama da Aunty Balki"

cikin sauri Balkisu ta tashi daga jikin Yaya Ahmad tana dafa k'irji tace "naga Rasulullahi ni Balkisu,

Wallahi Mama bani bace ni ban ma san shi ba Yaya"

tayi maganar kamar za tayi kuka,

"ke auta miye abun tashin hankali, daga cewa ana sallama da ke, bari yanzu naje na fatattake shi"

ya juya da kallonsa kan yaron da aka aiko "kai Tijjani je kace tana zuwa"

ya mik'i zai fita cikin b'acin rai Mama tace "dawo ka zauna, kai kake d'aurewa Balkisu tana k'in kula masu zuwa neman aurenta"

gyara zaman sa yayi kafin daga bisani yace "ba haka bane Mama karatu ba zai had'u da soyayya ba,

Ina so Auta tayi karatu sosai Mama fannin lafiya nake so tayi karatu, yans da matuk'ar wahala, ba yanda za ayi ta had'a abu biyu"

"sannu to ka sani daga

Please Login or Register in order to submit comment