Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ganin d'an nata,
"Deen ka dawo"
"Eh Momy na dawo yunwa nake ji"

yayi maganar yana shafan cikinsa, "zo muje abincin ka na falon k'asa, dama yanzu nake shirin cewa Hasan ya kaima"

falon suka tafe zaunawa yayi k'asan kafet da Hasan ya shimfid'a masa darduma,

hannu ya wanke ya fara cin tuwon samo miyar kub'ewa busasshi da aka burge da nama, da busasshin kife, sai k'amshi take,

sosai yaci dan abincin da yake so ne,

yana gamawa ya d'an tab'a fira da Momy kafin daga bisani ya wuce masallaci jin anfara kiran magarib shida su Husain.



Yau asabar yana d'aki yana aikin cike wasu takardu, wanka kawai yayi ya zauna aikin,

dan yana so ya rage aiki kafin zuwa Monday, wajan 12 Momy ta kira shi, da murmushi a fuskarsa ya d'aga kiran,

"Deen duk mun fito zamu karya kai kad'ai muke jira"

"To Momy ganinan zuwa" ya kashi kiran tare da ajiye wayan, mik'ewa yaye yana mik'a tare da salati, kafin daga bisani ya fito zuwa sashin iyayansa.

bayan sun kammala Karin kumallo Dady ya d'auke tisho yana goge bakinsa yace

" 'yan biyun Dady kuje ku duba littafan ku zan magana da yayanku"

"to Dady" suka fad'a atare suna mik'ewa tsaye, bayan tafiyan su, suka kuma cikin falo,

Ladi mai aiki ta gyara wajan da suka ci abincin, Momy tana zaune gefen Dady yayinda Deen yake zaune k'asa wajan k'afan Dady,

ragi muryar TV Dady yayi kafin daga bisani ya kalli Deen ya kira sunabsa

"Nuradeen"
jin Dady ya kira ai nahin sunansa yasan lallai maganar mai muhimmanci ce,

ahankali yace "na'am Dady"
"Kasan aminina Billo na KAITA"

"eh Dady tun muna yara kana bamu labarin sa, har hotanan ku kana nuna mana"

"yawwa zuwan da nayi KAITA mun had'u da shi wanda munyi shekaru kafin mu had'u,

ganin zumuncin namu yayi nisa da neman rugujewa yasa mukayi alk'awarin had'a aure a tsakanin zuri'ar mu, dan k'arfafa zumuncin mu"

shiru yayi yana mai jan numfashi kafin daga bisani yace "za matsayina na uba mahaifi awajan ka, Nurudeen na maka matar aure, wato Balkisu 'yar aminina,

Ina fatan ba zaka bad'a man k'asa a idanu ba"
ya k'arasa maganar yana mai zubawa d'an nasa idanu,

wanda tun sanda yaji zancin anmasa mata hankalinsa ya matuk'ar tashi,

nan take kamanninsa suka canza, yana jin wani irin zafi a zuciyarsa,

"kamar shi ba yaro ba za a masa auren had'i, ai ko azamanin da an daina irin wannan ballatana basu zamanin,

kuma ma k'aramar yarinya, gaskiya da sake"!

yayi maganar azuciyarsa da zafi, Momy ce ta katse masa tunani da cewa

"Deen kayi shiru ko ba kaji abunda Dadyn ka ya fad'a ba"?

cikin wata irin murya yace "Dady Momy naji, amma ku gafarci ni Dady,

gaskiya ni sam bana sha'awar auren had'i, ko auren k'aramar yarinya, a gafarce ni"

ya k'arasa maganar yana mai k'arayin k'asa da kansa,

cikin bacin rai Dady yace "ba shawara nake neman ba Nurudeen umurni ne nake maka"

daga haka ya haye sama, itama Momy bin bayan mijinta tayi suka bar Deen zaune zuciyarsa na tafasa, ya jima awajan kafin ya koma d'akinsa,

aikin da bai k'arasa ba kenan, ya zauna cikin k'unci da tafasar zuciya, shi kam ba wanda zai masa AUREN DOLE tunda Shi ba k'aramin yaro bane.

kwana biyu sam sun kasa gani kansa, baya zuwa cin abinci ya k'aurace masu, awajan aikin ma sam baya tab'uka wani abun kirkin,

abokinsa Muhusin yayi lallashi da nasiha abanza kamar yana zugashi,

ranar dai da abun ya ishi Momy tace sami Dady d'akinsa yana wani aiki a laptop,

zama tayi kusa da shi kafin tace "alhaji magana nake so muyi"

ture laptop d'in yayi tare da janyota jikinsa yana cewa "uwargida sarautar mata, amarya ba kya laifi koda kin kashi d'an masu gida,

dariya tayi cikin kissa tace duk ni kad'ai mai gida"?

"eh mana kece uwar gida kece amarya,
wace magana kike tafe da ita"?

cikin damuwa tace "alhaji akan zancin Deen ne, kana ganin tun fara zancin auren nan yanda duk ya koma wani iri"?

"Uhm haka ne, ni kaina abun ya fara damuna sosai, yanzu mi kike ganin ya dace"

cikin kissa da wasa da gashin da yake kwanci lof akirjinsa tace "kaga aurena nan dan k'arfafa zumunci ne yasa ake son ayi shi,

kaga ya nuna baya so, da azo ayi auren matsaloli su taso zumuncin ya lalace gara tun farko kar ayi, nasan Billo zai fahimci ka"

"hakane Maimuna, nima na fara tunanin, amma kinga Billo ya kirani jiya akan zancin tsayar da rana, har munyi maganan zuwa Katsina can KAITA wajan su Yaya,

sannan munyi sati nai zuwa Nura zaije su gana da Balkisun,

amma zanyi shawara zuwa safe naga abunda ya dace"
"to alhaji adai duba kamarin saboda gudun yin abun da na sani"

daganan aka rufe firan aka fad'a love.

(kunsan ance so baya tsofa sai dai masu yinta su tsofa, kamar dai Aisa lol😜)


Washe gari Dady ya fad'awa Momy shawara da ya yanki, har cikin ranta taji dad'i sosai da jin hakan,

dan tana son farin cikin d'ansu, Husain Dady yasa ya kira masa Deen.


*TofaπŸ€” shin ko addu'an Balkisu da mahamod ce take shirin ci, ko dai biyu dan jin shawaran da Dady yayi*


*Karku manta kuna tare da Aisha A Yabo Fulani ta Annabi S.A.W*
[9/28, 8:22 AM] Aisha A Yabo: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*ILLAR AUREN DOLE*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*Daga alkalamin Aisha A Yabo Fulani*


*Β© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUMπŸ„*
β˜†We the best β˜†

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* realhausafulaniwriters@gmail.com

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1



*MANUFARMU ANNABINMU*


*IDAN BAN NUNA SOYAYYATA GA Y'AR ANNABI BA GAWA ZAN NUNA SOYAYYATA*

*NASAN DAI CEWA ALLAH BAI HALICCI WANI ABUBA DA YAFI NA ANNABIBA*

*SAYYADA KO SAI IMANI,IMANINMA BA NA KOWA BA*


*ITACE TSOKAR SHUGABA*
*ITACE ZUCIYAR SHUGABA*
*ITACE RUHIN SHUGABA*

*NA TABBATA BA ILIMIN SANIN WANI ABU NA SHUGABA ANAN DUNIYA*

*ALLAH INA ROQONKA KA WANZAR DA GIRMAMAWA GA MAFI DARAJAR DARAJA SAYYIDATUN-NISA'IL'ALAMINA*


*WALLAHI QAUNAR FAD'IMA ITACE RAYUWARMU*


RANDAWA MEDIA CONCEPT
*Kunaso ahadamaku ring tone da sunayenku?
*Kunaso ayimaku sound track da sunan masoyanku ko kuma lakanin sunayenku?
*Kunaso kuji wayarku tana kiran sunayenku alokacin da akayi kiranku awayoyinku na salula?

Ba anan kad'ai muka tsaya ba har wak'ok'in bikin aure bikin suna, ko wak'ar birthday.

Cikin aminci da karamci zaku samu wanga farinciki da farashi mai sauki, zaku iya samunmu ashafinmu na wasapp dandalin sada zumunta ta wannan lamba 08032176520. Don hudda ta kasuwanci kamar kyautane farashin aikinmu, tsada bata nuna inganci aiki akamfaninmu. Kada Ku manta, Namu dabanne! Domin kuwa aciki zamuyi yanda za'agane cewa lallai kaidinne ko kuma kedindaice akenufi. Ku gwada aiki da sabuwar fasaharmu zakuji dadin tsarin. Mungode mungode mungode.
Isah Randawa ke cewa muzama lafiya da alheri.


*20 to 21*

Kwanci yake kan kafet yayi filo da hannayansa, yana kallo rufin d'akin,

sosai ya fad'a tunanin mafita akan wannan auren da Dady ya jajibo masa,

Husaini ya jima yana bungun k'ofan shiru kamar ba kowa,

Deen na jinsa yayi banza da shi, jin ank'i daina buga k'ofan yasa shi mik'ewa tsaye yana tsaki,

bud'i k'ofan yayi cikin b'acin rai yace "miye zaka zo kana damuna"?

cikin tsoro yace "Dady ne yace na kira ka"

"to naji ji ganinan zuwa"
zura takalmi yayi ya nufi sashin nasu.


kallonsa Dady ya kiye cikin nazarin sa, sosai yaga raman d'an nasa, da zallar damuwa acikin kwayar idanunsa,

duk sai yaji ba dad'i, ahankali ya saukar da ajiyar zuciya kafin daga bisani yace

"Nuradeen yanzu saboda zancin auren ne duk ka shiga damuwa har kake guje mana"?

cikin susa kansa yace "Aa Dady kuyi hak'uri"

"to naji, yanzu dai munyi shawara ni da maman ka akan ka shirya kaje Katsina ranar asabar"

da sauri ya d'ago kansa yana kallon iyayan nasa ciki da nuna firgici da jin zancin tafiyan,

Murmushi Dady yayi kafin yace "wannan tashin hankali sai kace nace kaje wajan mutuwar ka"

Deen aransa yace "ai Dady kusan hakane"

"Kaga kaje kaga yarinyar idan har batama ba, nama alk'awarin janye maganar auren, sai ka kawu wace kake so,

amma ka sani matuk'ar wannan bata ma ba, dole zaka kawu wata"

Momy tace "ka daiji da kyau, ba zaiyu mu zauna muna zubama idanu ba, ka isa aure ga sa'anninka nan duk sunyi aure harda masu 'ya'ya, amma kai na rasa mi yake damunka da ka kasa tsayar da tunaninka waje d'aya, ka ajiye iyali"

Momy tayi maganar cikin nuna lallai abun yana dumunta,

cikin farin ciki yace "insha Allah Dady zanyi yanda kuke so"

"Yawwa Allah yayi ma albarka"

"Amin" nan ya tsaya yayi karin kumallo, cikin farin ciki.

da yamma suna tare da Muhusin awajan aiki, Muhusin yace "mutumin ya naga yau kana ta farin ciki, ko an kusa kawu amarya ne"?

yayi maganar yana dariya, harara Deen ya b'alla masa kafin yace

"Malam bana son iskanci, ai malam Allah ne ya ciro ni daga cikin k'angin da na fara fad'awa"

da mamaki Muhusin yace "fahimtar dani"

nan ya bashi labarin komai,

kallon Deen yayi yana gyad'a kai kafin yace "to kai idan aka janye maganar 'yar Katsina, kana da wacce zaka kawu ne"?

dum! yaji gabansa ya fad'i cikin wani irin yanayi yace "share da wannan, ai anyi mai wuyar, ahankali zan dinga lallab'asu har su bar zancin wata yarinya"

"lallaima Deen, to wai kai mi kake nufi, ba za kayi aure ba ko mi, anya ma kuwa kana da lafiya"?

afusace yace "ba lafiya ba asibiti ne ni"

"Hahahaha Allah ya baka hak'uri abokina"

Muhusin yayi maganar yana dariya ganin yanda Deen lokaci d'aya ya fusata,

"Mts"! Deen yayi tsaki tare da tattara ina shi ina shi zai bar office d'in, yace "idan kaga dama ka rufe man office d'in"

mikewa Muhusin yayi cikin k'ara tura haushi yace "ah mijin 'yar Katsina ai ba zaka barni ba,
shin yaushe ne zamu je wajan amaryar mu"?


"ban sani ba"! yayi maganar afusace, haka suka bar office d'in sai tsiya Muhusin yake masa.


sam ya manta da zancin tafiyan Katsina, sai ranar juma'a da yamma Dady yake k'ara tuna masa,

To kawai yace, amma sam baya son tafiyar, sai dai sanin itace damarsa ta kub'ucewa auren yasa ya amsa.


Wahe gari ana idar da azahar suka nufi hanya Katsina, ta jirgi, ciki da tsarabar da Dady ya bayar akaiwa Abba,

Momy ta bashi akwati d'aya da zai kaiwa Balkisu.

Yaya Ahmad ya shigo gidan bayan sun gama gaisawa da Mama yace "wai ina auta"?

cikin ajiyar zuciya Mama tace "tana d'aki, tun sanda maganar auren nan ya tashi ta mayar da zaman d'aki abokin firanta,

wallahi abun yana damuna, gaba d'aya ta zama wata iri"

cikin damuwa ya jingina bayansa da kujera kafin yace "narasa miyasa Abba zai dage da maganar auren nan wallahi,

ni da ban san halin Abba ba da sai nace ko dan kudin Dady ne ya nacewa wannan had'in"?

"Aa sam ka ciri wannan tunanin aranka, kawai aminci ne da irin kauna da taimakon sa da yayi lokacin k'urciya,

amma ba wai dukiyarsa ba, ai kasan halin Abbanku sam kudi basa rufe masa idanu"

"hakane, amma Mama bai kamata Abba ya nace haka ba, musamman saboda rayuwarta"

"To babu yanda muka iya, tunda yace eh, babu wanda ya isa yasa shi tace Aa,

kaga yanzu ma fa har yasa lokacin auren, wata biyu"

"haddar tata fa"?
"tunda kaga yayi haka ai babu zancin karatun, tayi hak'uri kawai, Allah ya amfana wanda tayi,

yau ma suna hanya zasu zo, shiyasa nake so kaje ka lallab'a man ita"

"to Mama" ya fad'a cikin damuwa sosai.

Kwanci ya tarar da ita idanun ta suna tsiyayar da hawaye,

zama yayi gefin ta tare da kiran sunanta ahankali yace "autar Mama"

tana jin myryarsa ta tashi da sauri ta fad'a jikinsa tana wani irin kuka mai cin rai,

shafa bayanta yayi cikin lallashi tace "mi ya faru kuma auta?
miyasa kike sawa kanki da kuwa damu, kiyi hak'uri da k'addarar ki, damuwa ba zai maki magani ba"

cikin shisshik'an kuka tace "haba Yaya Ahmad dan Allah mi nawa Abba zai mun wannan tsatstsauran hukuncin,

Yaya aure fa anayin sani da burin samun zaman lafy da farin ciki, rayuwace da ake burin yinta har mutuwa,

amma Yaya Abba yake son turani mahalaka, bana son sa taya zan iya yi masa biyayya, taya zuciyata zata daina tunanin wanda take so, Abba wuta fa yake shirin kaini"

da sauri Yaya Ahmad ya rufe mata baki cikin gyad'a kai yace "bana son kina irin wad'anan maganganun,

Insha Allah wannan auren ba zai tab'a kaiki wuta ba sai dai aljanna mad'aukakiya,

ki daina tunanin Abba zai saki a halaka, Abba na sonki, kawai dai abune da Allah ya rubutu sai ya faru, bawa kuma bai isa ya sauya shi ba,

yanzu kinga yanda kika sa Mama damuwa, kuma duk dan tana ganin kin k'i ki kwantar da hankalinki,

kiyi hak'uri ki kwantar da hankalin ki, kibarwa Allah komai kinji autar mu"

gyad'a kanta kawai tayi, "yawwa auta kinga kina da bak'o zai zo yau, dan Allah karki bari ya fahimci komai, karki kunyata Abba dan Allah"

ya jima yana lallashinta kafin yayi mata sallama, ya barta cikin tashin hankali da tunanin taya za ta iya tsayawa da wani da sunan zance ba Mahamod ba.

Mama ta kira ta d'akinta tana ci gaba da lallashinta kawai dai tayi k'ok'arin boye damuwarta ne saboda ganin yanda Maman take damuwa,

suna haka Ummu tazo, Mama ta fita, "iyye kinga amaryar Legos, kingan ki kuwa, duk dai dai kin rame amma kin k'ara kyau da haske"

duka ta kaimata da sauri ta kauce tana dariya "besty matsalarki wallahi yanzu kin iya saurin fushi, daga fadan gaskiya sai duka"

cikin rawar muryar da take son yin kuka tace "besty kema kin daina sona wallahi"

kawai sai ta fashe da kuka, cikin sauri Ummu ta dawo kusa da ita tare da dafa kafad'anta cikin damuwa tace

"haba besty kema dai kin san kina fad'a ne kawai, amma daga Abba da kuwa ma har ni muna sonki ba kuma zamu daina ba,

kawai dai ina maki haka ne dan mu dara, sam bana jin dad'in sauyin da kikayi,

yanzu kin zama miskilan k'arfi da yaji, dan Allah besty ki mayar da komai ba komai ba kinji"?

"wai miyasa kowa ya kasa fahimtar ciwon da ke zuciyata ne?

besty kinfi kowa sanin irin yanda nake son mahamod, kinsan irin shakuwar da mukayi da shi,

shin taya rana tsaka za azo arabani da shi, kuma ace wai karna damu, na mayar da komai ba komai ba, taya taya ki fad'aman besty taya zan cire shi"!?

ta kifi kanta kan cinyoyinta tana kuka gwanin tausayi, wani irin son mahamod ne yake k'ara fizgarta tamkar yau ne ta fara jin sonsa,

itama Ummu hawaye ne suke zuba afuskarta ciki da tausayin aminiyarta tace "na sani besty amma damuwa da tashin hankali ba zasu cika maki birinki ba,

saima ciwon da za ki iya janyowa kanki, kiyi hak'uri muyi ta addu'a, mu nemi zab'in Allah"

shiru Balkisu ta mata tana ta sauke ajiyar zuciya, Ummu duk sai take jin ba dad'i.


zaune suke a falon Abba Ummu ta gabatar masu da abinci cikin mutuntawa,

aranta tana fad'in gaskiya dan dai kawai so na so amma Deen kyakyawa ne, ga alamar Hutu atare da shi,

duk da dai tsakanin Muhusin da Deen bata san waye saurayin bestyn ba, amma dukansu kyawawa ne.

"ki tashi kije Auta dan Allah karki bamu kunya kinji"

narai narai tayi da fuska za tayi kuka Mama ta girgiza mata kai "Aa karmuyi haka da ke, na sani ke yarinya ce mai biyayya, karki kunyata abbanki, karkiyi kuka, ki k'arfafa zuciyarki kinji,

ga Ummu nan zata rakaki, kuma bama dadewa zakiyi ba, tunda Abbanki na nan zuwa"

Ummu tace "Mama haka zata je ba za tayi kulliyar ba"

cikin harara tace "eh d'in ba zanyi ba, zo ki danni ni kiyi man"!

"oh Allah mayar da wukar amaryar Deen"

"Mama kina jinta ko" ta fad'a cikin shagab'a, "kyaleta auta tashi kuje.

zuciyarta wani irin zafe da radad'i take mata lokacin da suka zo k'ofan da zata sadaka da falon.

Muhusin tunda aka kawu abinci ya budi tumbinsa ya bararraki abinci yana ta santi

"kai mutumin aradun Allah zaka kwashi girki, wannan dadi haka, inaga ko sati da aure ba za arufe ba, zaka mulla k'iba harda taib'a"

filon kujeran Deen ya dauka ya buga masa "wallahi Muhusin zanci mutincinka, ai sai ka bari sai tamun sannan ka samu abun man fad'e"

"Hahahaha ai kamar ma tayi insha Allah, yanda naga 'yar uwarnan tata kyakyawa, ai nasan itama haka kilama har ta fita, nifa ina jiye ma karka ganta ka rud'e"

"Mts Allah ya sawwak'a, ai idan nace No ba na dawo nace yees, kuma ka sani sarai mi zanyi da k'aramar yarinya, ni ko aciki manyan mata ma da suka ansa sunansu nafi k'arfinsu ballatana 'yar k'uwaila"

"Uhm to yayi gamu dai gani, wallahi Allah ka shiga uku dani idan ka dawo ka sauya tunani"

shiru ya masa yana hararsa,

"oho idanunka sai dai su zazzagi malam kazo kaci abincin nan kar abarka baya wajan kwasar dadi"

"ba zan ci ba, banza mayen ci"

"kada Allah yasa kaci, ai kayiwa kanka"

Muhusin sai da yayi k'at yasha ruwa, sannan ya mayar da kayan abincin gefi ta dawo ya zauna kan d'aya daga cikin kujeran, yana daddanna wayarsa, yayiwa Deen banza.

da sallama suka shiga d'akin, kanta na k'asa ta janyo mayafi ta rufe fuskarta tamkar amarya,

d'ago kansa yayi daga kan wayarsa da yake danna zuwa wajan da Ummu da Balkisu suke zaune.


Hajiya ta tasa shi agaba cikin alhini tace "mahamod so kake ciwo ya shige ni saboda kai ko"?

cikin sauri ya d'ago yana kallon mahaifiyarsa yace "Hajiyanmu kiyi hak'uri bana fatan hakan"

"ba gaskiya bane Mahamod, ka duba yanda ka kuma, ka rami ka koma wani kala, ko yaushe cikin ciwo uhm,

wajan aikin naka ma sam baka mayar da hankali, duk saboda mace, shin ita kad'ai ce autar mata da zaka sa kanka a damuwa, k'ilama ita ta manta ka"

zamewa yayi daga kan katifa ya dawo wajan da take zaune ya d'ura kansa akan k'afafunta yace

"Hajiyanmu kiyi hak'uri, nima ba ason raina bane nake damuwa, wallahi ita kad'ai zuciyata take so,

ban san taya zan iya cireta daga zuciyata ba, na sani itama tana cikin damuwa kwatankwacin wacce nake ciki,

ki taya ni addu'a Hajiyanmu ba zan iya juran ganin Balkisu zata aure wani na ba wallahi, mutuwa zanyi Hajiyanmu"

cikin tashin hankali tace "na shige su ni Maijidda, Allah ka kawu man dauki ya Allah ka cirewa yaronan wannan karabar son"

d'ago kansa tayi daga jikinta ga mamakinta kuka yake,

hannu tasa tana share masa hawayen da ke ta zarya afuskarsa tace "kayi hak'uri autana addu'a makamin mumini ce, ka rikita insha Allah komai sai yazo cikin sauki,

"tashi muje kaci abinci, kuma bana son musu"

haka yabi hajiya d'akinta ba dan ransa na bukar abincin ba.

*Karku manta kuna tare da Aisha A Yabo Fulani ta Annabi S.A.W*
[9/28, 8:22 AM] Aisha A Yabo: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*ILLAR AUREN DOLE*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


*Tare da alk'alamin Aisha A Yabo Fulani*

*Β© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUMπŸ„*
β˜†We the best β˜†

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* realhausafulaniwriters@gmail.com

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1

*🌲MANUFARMU ANNABINMU 🌲*

*MAI KATA FARIYAR KYAUTA ZAHRA'U YAR'SHUGABA*

*WANDA YACE YANAYI DA ITA WALLAHI ITACE TAKEYI DASHI*

*WANDA YACE BAYAYI DA ITA ITACE BATAYI DASHI*

*NANA FAD'IMA MUN GODE*
*NANA FAD'IMA MADALLAH*

*ALLAH KA WADA TAMU DA QAUNAR UWA GA SHARIFAI*

*DARAJAR ANNABI AGUNKA*

*DA SOYAYYAR ANNABI AKE ADO*

RANDAWA MEDIA CONCEPT
*Kunaso ahadamaku ring tone da sunayenku?
*Kunaso ayimaku sound track da sunan masoyanku ko kuma lakanin sunayenku?
*Kunaso kuji wayarku tana kiran sunayenku alokacin da akayi kiranku awayoyinku na salula?

Cikin aminci da karamci zaku samu wanga farinciki da farashi mai sauki, zaku iya samunmu ashafinmu na wasapp dandalin sada zumunta ta wannan lamba 08032176520. Don hudda ta kasuwanci kamar kyautane farashin aikinmu, tsada bata nuna inganci aiki akamfaninmu. Kada Ku manta, Namu dabanne! Domin kuwa aciki zamuyi yanda za'agane cewa lallai kaidinne ko kuma kedindaice akenufi. Ku gwada aiki da sabuwar fasaharmu zakuji dadin tsarin. Mungode mungode mungode.
Isah Randawa ke cewa muzama lafiya da alheri.


*22 to 23*

"Barka da fituwa gimbiyar mata" Muhusin yayi maganar yana mai son kallon fuskar budurwar abokin nasa,

sai sai sam tak'i kanta asunkuyi yaki ta rufe da mayafi, ba dan tana jin kunya ba sai dan kawai bata muradin ganinsa,

cikin fara'a Ummu ta gaishe su, wannan katunma dai Muhusin ne ya amsa, da fara'a yace

"kawar amarya zance ko 'yar uwar amarya, ya gida ya karatu"?

"lafiya k'alau alhmdlh, duka zaka iya kirana dasu"

ganin Balkisu tak'i tayi magana, yasa Ummu cikin yin k'asa da murya tace "kin manta maganar Mama ko"?

Balkisu zuciyarta halbawa take wani irin k'unci take ji, ga wani irin kuka da ya zo mata, tana so ta tilasta kanta ta gaishe su,

sai dai kukan da take k'ok'arin had'iyewa ba makawa duk tace za tayi Magana kukan zai fallasata,

hakan yasa tayi shiru tare da k'ara b'oye fuskarta,

muntsini Ummu ta mata a cinyarta, aikuwa ba shiri ta d'ago kanta tana sakin k'ara dan taji shi sosai,

k'ararta yasa Deen da yake danna wayarsa kamar ba kowa a falon, wanda hakan ba k'aramin haushi ya bawa Muhusin ba,

k'ararta da d'aguwar kanta yayi dai da d'ago tasa fuskar da sauri,

idanunsa suka fad'a cikin nata, wani Harara ta masa,

wani irin bugawar zuciya yaji, hararan sai ya masa kyau tamkar wani kallon love take masa,

gaba d'aya cikin 'yan sakanni ta gama ta fiya da imaninsa, sam ya kasa d'auki idanunsa daga kanta,

cikin rawan murya tace "ina wuninku"

Muhusin ne dai ya amsa yana mata barkwanci, komai bata ce ba, sai ma kawar da kan da tayi,

cikin k'asa k'asa da murya yace "malam janye idanun haka da kan 'yar mutane karka cinye masu ita,

ni tashi ma mu tafi sam batayi ba Allah"

ya k'arasa maganar cikin k'ok'arin had'iye dariyar da tazo masa,

ahankali ya janye idanun sa daga kanta, ya jingina bayansa da kujera yana murmushi ba tare da yace komai ba,


aransa yana tunanin sam bai san haka zai sami yarinyar ba, da sam bai wahalar da kansa da cewar baya so ba, bare har ya hana kansa sukuni,

ajiyar zuciya yayi ahankali yanda ba mai jinsa, kafin daga bisani ya d'ago cikin sanyin murya yace

"barka ku da fitowa, mun same ku lafiya"

"lafiya k'alau" cewar Ummu da take wasa da mayafinta aranta tana cewa "ji dan rainin hankali sai yanzu zai mana magana,

to ko dai d'an gidan sarauta ne? Aa ba wani sarauta kawai iskanci ni, amma fa besty tayi dace, yana da kyau dai dai misali, gashi da ganinsa ya iya saukar wanka"

Muhusin ne ya katse mata tunani, "kanwata muje ki tayani fira, dan naga wad'anan basa son zaman namu,

bakiga har harararmu suke ba"

cikin murmushi tace "aikuwa naga alama" ta mik'i tsaye cikin saure Balkisu ta rik'i mayafinta,

cikin dabara ta fizgi tare da wucewa ta k'ofar waje, inda tuni Muhusin ya fita,

kamar jira yake su fita ya d'ago daga ginshidin da yayi yana kallonta yace

"Balkisu daga ni har ke ba bak'in juna muke ba, ta fuskar jin labarin juna awajan iyayanmu,

sai dai azahiri ne dai ba musan juna ba,

iyayanmu sun zab'a mana rayuwa da juna a matsayin abokan rayuwa na har abada"

ya d'anja numfashi kafin ya cigaba da cewa

"ni dai kin mun, aganin farko da na maki sonki ya shigini ba da wasa ba, ina fatan kema haka"?

yayi mata tambayar cikin k'ara zuba mata idanu ciki da son jin amsarta, da mararin k'ara son jin muryarta,


saukowa tayi daga kan kujeran ta durk'usa agabansa gwaiyuyinta ak'asa cikin kuka tace


"dan Allah Yaya Nura ka taimake ni ka cici rayuwata, wallahi ina da wanda nake so"

nan take yaji wani irin abu marar dad'i ya tsaya masa a zuciya, idanunsa sunyi jajir,

Ina da wanda nake so, yake ta masa kururuwa cikin kunnuwansa wani irin kishi ne ya taso masa, numfashi yaja tare da furzarwa,

cikin wani irin yanayi yace "kina nufin ba kya sona, wani na ne kike so,

cikin sauri tace "eh indai son aure ne ba kai nakewa ba, ina dai sonka so na zumunci, ka taimake ni ka fahimtar da Abba, wallahi mutuwa zanyi idan na rasa Mahamod,

shine farin cikina, shine rayuwata, ba zan iya rayuwa ba sh...

"ya isa"! ya fad'a da k'arfe, tare da mik'ewa tsaye, hannunsa cikin aljihu, yana kallonta cikin tsananin b'acin rai yace

"ni kinmun, ina kuma sonki, ko da ba kya sona, babu matsala, ai akwai son zumunci, ya ishemu, tunda ba sona ne ba kyayi gaba d'aya ba"

cikin sauri ta mik'i tsaye taje gabansa ta tsaya ido cikin ido tace,

"ni har na zumuncin bana ma wallahi, ban sanka ba, ban tab'a ganinka ba sai yau, dan haka ko d'aya bana ma,

ka taimake ni, ka taimake rayuwata, ka dawo man da farin cikina, kace baka sona, na sani Abba zai janye matuk'ar kace ba kayi"

Murmushi yayi mai ciki da takaici, sosai yake jin zafin maganganunta, ji yake ina ma bai zo garin ba, ga ba d'aya, da bai ganta ba, ballatana har yaji sonta da zai d'aga masa hankali haka,

"shikenan

Please Login or Register in order to submit comment