Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na yarda na fad'amaki,

amma ai yanzu dai komai ya wuce, nama had'u da Mahamod d'inki agidan Mama, ina ganinsa nace komai nomal kenan, shima sai da yamun k'urrafi"

cikin turo baki tace "ai dama ya dakar mun ke ko na huce haushi"

dariya Ummu ta kyalkyace da ita kafin tace "tab yana ma farawa, ni dai yanzu ba wannan ba yaushe za ki shigo makaranta"?

"tab ba rana ba wata"
"lallai su soyayya manya, wallah ki ajiye soyayyar nan gefe ki nimi ilimi yarinya"

"uhm to k'atuwa" dukansu sukayi dariya, "ke ni inawa hubby na k'albina girki mayi magana daga baya"

"to dad'in abun dai nima na kusa shiga inda kika shiga bare amun gurin K'ALBI"

"oho dai kafin dai wata ta shiga an rigata"

tana gama fad'a ta kashi waya dan tasan halin besty idan ta biye mata na k'are wayar za suyi ba, ta koma kitchen wajan girkin ta.

zaune yake gaban Hajiyanmu kuka yake sosai kamar k'aramin yaro,

Hajiyanmu ta shafa kansa cikin k'auna tace "autana mi ya faru kake kuka"? tayi tambayar cikin tashin hankali,

cikin muryar kuka yace "Hajiyanmu bansan da wani baki zan gode maki da 'yan uwana ba, kun bani zab'ina da na jima da ciri rai da zan samu,

kun bani farin cikina, Hajiyanmu na gode sosai Allah ya k'ara lafiya da nisan kwana, Allah ya saka da alkhairi,"

murmushi tayi cikin farin ciki tace "haba autana dan wannan kake kuka ka tayar mun da hankali,

Ai ba mune muka baka Balkisu ba, Allah ne ya baka, fatana Ubangiji Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a mai albarka,

sannan ka rik'i abokinka Adamu da amana, domin shine ya zo har gida ya fad'amun Balkisu na gida, ya kawu shawarar a nima ma aurenta"

sosai yayi godeya ya jima agidan suna fira irin ta d'a da uwa da suka shak'u da juna da soyayya.

daga gidan Hajiyanmu ya wuce gidansu Balkisu, ya jima gidan dan ya tarar da Yaya Ahmad, yana fitowa gudan ya wuce wajan Adamu da sukayi waya ya tarar da shi gidansa.

rayuwa suke mai ciki da k'aunar juna, Balkisu sosai take kyautata masa da nuna masa tsantsar soyayya bata kaunar abunda zai b'ata masa rai,

kamar yanda yake gudun b'ace ranta, ko yaushe za ka tarar da gidan nasu tsab yana fitar da k'amshi mai dad'i da sanyi,

dan Allah yayi mata tsabta, shiyasa jikinta baya rabu da k'amshi, bata da kwalliyar da ta wuce k'ananan kaya ko 'yan kanti, ko kayanmu na Hausa Fulani, wanda duk suke fito da jikinta,

sai dai idan za ta fita unguwa ne take sa manyan tufafi, kwanciyar hankali da natsuwa ya saukarwa masoyan,

'yan uwa da abokanai sai tsiya suke masu, basa kuma rasa amsar basu.

"Nasir yanzu dan mahamod ya ga na mutu a sonsa shiyasa yake gara ni yana mun wulak'anci"

ta k'arasa maganar cikin muryar kuka, cikin tsananin tausayinta na son ma so wani da Allah ya jarabce ta yace

"kiyi hak'uri Muhibbat gaskiyar zance abu ne mai wahala ki samu Mahamod, idan ba ki manta ba abaya ya baki labarin soyayyar sa da Balkisu,

to atakaici dai Allah yayi nufinsa yanzu ita d'in ce matarsa"

wani irin dum taji tamkar anbuga mata guduma a tsakkiyar zuciyarta, kashi wayar tayi tare da fad'awa kan gadonta,

ta fashi da wani irin kuka ciki da tausayin kanta ta furta "shikenan na rasa shi har abada, ya sure zab'insa na tabbata ya manta da ni"!

haka ranar ta wuni cikin d'aki cikin tsananin damuwa, ba yanda mahaifiyar ta bata yi ba akan ta fad'a mata damuwarta sai dai tace ba komai kawai bata da lafiya amsar da take bata kenan.

dukansu suna d'aure da tawul ajikinsu, da alama wajan wanka suka fito, ta d'auko mai sai da ta shafa masa shima ya karb'a ya shafa mata,

sun d'au lokaci suna shirya junansu wanda kusan wasanni yafi shirin yawa,

bayan ya k'arasa sa mata dugowar riga ta atamfa ta zauna bakin gado shima zama yayi kusa da ita ya rik'u hannunta,

yana murza hannunta yace "ya dai ko jikin ne"?

cikin shagwab'a tace "Aa farin cikina amma idan mun fito asibiti za ka ajiye ni gidansu Besty ko? kaga yau saura sati biyu ayi bikinta, ina so mu fara shiri da wuri"

ta k'arasa maganar tana shigewa k'irjinsa tana shafa gashin k'irjinsa da yayi kwanci luf luf,

zef d'in rigarta ya janyo yasa mata kafin yace "Aa karma mu fara kinsan ba zan barku yawu ba, ki wahalar mun da kanki da babyna,

haihuwa yau ko gobe zan barki kiyi yawu?
kiyi hak'uri na maki alk'awari insha Allah idan Allah ya sauke ki lafiya bayan kin haihu zan kaiki har kaduna gidanta,

kuma ai kinga zanje idan naje tamkar kinje ji ko,"?

had'iye hawayen da suke k'ok'arin zubu mata tayi kafin tace "Allah ya kaimu"

"Amin na gode sosai Allah yayi maki albarka, ina sonki har abada ba zan daina k'iunarki ba shalele,

baki tab'a mun musu akan duk abunda na gindaya maki, ko yaushe k'ok'arin ki ki faranta mun,

da ace dukan mataa sunayin abunda matata take mun hak'ik'a da mace macen aure da yawan matsalolin aure sun ragu matuk'a,

ba zan hanaki zuwa hidimar besty ba, amma ki mun hak'urin yau, kinga za muke gidan Yaya Ahmad mu duba 'yan kaciya,

yawun zaiyi yawa, amma insha Allah jibi ranar litinin zan kaiki da kaina"

cikin farin ciki ta sake shigewa jikinsa suka rungumi juna, "ina sonka Hubbyna, ba zan tab'a daina k'aunar ka na


hak'ik'a na keri mata, na zama mace mai matuk'ar sa'a da samun nagartaccen miji irinka,

Ina alfahari da samunka, hubby na Allah ya barmu tare abadan da'iman"
"amin matata uwar 'ya'yana, maza tashi muje karki makara dan naga wajan awun naku yana cika akwai jira"

ya fad'a yana mik'ewa tsaye tare da mik'ar da ita tsaye, ya d'auko hijab ya sa mata rabin jikinta kwanci a kafad'ansa,

ahankali yake bi da ita har wajan motarsa, ya bud'i mata ta shiga sannan ya koma ma zaunin direva ya zauna,

yana tuk'i da d'aya hannu, d'ayan kuma na kan cikinta d'an wata takwas yana shafa ciki da k'auna.


Mama tana had'awa Abba kayan da zaiyi tafiya Legos wajan auren Deen, tace

"ikon Allah kenan, wani bai tab'a auren matar wani kamar yanda babu mai haihuwar d'an wani,

ka duba tunda akayi auren auta da Mahamod hankalinmu akwanci,

ba mu tab'a jin wani abu na sab'ani ko tashin hankali a tsakaninsu ba, gashi har rabu ya ratsa"

"Hmm bari ke dai ai har kullum ina k'ara godewa Ubangiji da rabu bai kashi ni ba, akan auta kuma na tabbatar AUREN DOLE ba shi da amfani,

ki duba aurenta da Deen sam bamu da kwanciyar hankali, amma yanzu da ya zama zab'in ta ne gashi shiru muke ji,

gaskiya AUREN DOLE baya da amfani, ba zanyi fatan ko da mak'iyina ya shiga halinda na shiga ba sanadin yiwa 'yata AUREN DOLE"

"ai komai muk'addari ni fatanmu dai Allah ta basu zaman lafiya da zuri'a mai albarka"

"Amin bari na tashi Ahmad na gidan mai yana jirana, sai Allah yayi mana dawowa"

"to malam Allah ya tsare ya kai lafiya ya dawo daku lafiya, dan Allah muna masu Allah sanya alkhairi"

"Insha Allah za su ji.



*Alhamdulillah*
*Alhamdulillah*
*Alhamdulillah*

Ina matuk'ar godeya ga Ubangiji da ya nuna man na kammala littafina mai suna ILLAR AUREN DOLE, fatana Allah yasa ayi amfani da abunda yake mai kyau, marar kyan kuma ayi watsi da shi,

kura kuran da suke ciki Ubangiji Allah ya yafe mun alfarmar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wasallam, Allah ya sadani da alkhairin da.yake ciki dan isar Ummu Abiha,
tsira da amincin Allah su tabbata ga cika makin annabawa Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wasallam, da ahalin gidansa

*Had'in kanku shine zai tabbatar mun da soyayyar da kuke mun*

Takun dai ce mai k'aunarku, mai burin farin cikinku, Aisha Abdullahi Yabo Fulani,

Marubuciyar
*Amal*
*Mukula 'yan matan zamani*
*Karka guje ni*
*M'aurata*
*Randawa makiyayi*
*Mummunan furuci*

*Mai fitowa*
____________________
*AJIYAR ALLAH*


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment