Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ai bama sai kin man son ko d'aya ba, nawa son ya ishemu rayuwa, dan haka kima daina zancin na janye,

ina sonki ba kuma zan iya hak'ura da ke ba ayanda naje jinki azuciyar nan tawa ba"

ya fad'a yana dafa saitin zuciyarsa, cikin b'acin rai tace "gaskiya kai kana da sonkai, idan har kana jin son da Baja Jima da fara jinsa ba, ba za ka iya barinsa ba,

kayi tunani sosai akan son da aka jima anayinsa ciki da shak'uwa za a rabashi lokaci d'aya, ya masoyan za suji"!

cikin d'aga ka fad'a yace "komai zaki fad'a ki fad'a, ni dai ina sonki, kuma aure ni, ba makawa sai anyi, dan haka ki shirya fara son nawa, da cire wancan banzan aranki, dan karma ki yarda ki zo man gida da wani a zuciyarki"

za tayi Magana ta jiyo muryar Abba cikin gida, da sauri ta koma baya ta zauna kan kujera tana kuka ahankali,


sai ya ji tausayin ta sosai, ina ma zai iya da ya hak'ura da ita, sai dai a yanda yake jin sonta acikin d'an k'ank'anin lokaci, ba, zai iya hak'ura da ita ba,

kamar wace aka muntsini ta tashi tana goge hawayen fuskanta da bayan hannunta, kafin tace "ni dai ina k'ara fad'ama, kai ba zab'ina bane,

Ina da wanda nake so, karka tursasa ni akan sai na aure ka, domin babu wani farin ciki aciki,

gara kaje tun wuri kace kaima ba kayi, idan ba haka ba, wallahi ka rik'i wannan a ranka, GANGAN JIKINA NE ZAKA AURA, AMMA ZUCIYATA TANA WANI WAJAN BA KUMA ZA KA TAB'A SAMUN FARIN CIKI BA, KAMAT YANDA NIMA NA RASA NAWA FARIN CIKIN"!

tana k'arasa fad'a ta bar falon, rik'i kansa yayi da yake jin yana Sara masa, idanunsa sunyi jawur, sosai yake jin ciwon maganganunta,

miyasa so ya masa haka, miyasa zai so inda bai dace ya so ba, ya Allah! inama zan iya da na barki bari na har abada!.

tun awaje Abba ya gaisa da Muhusin, Ummu na ganin Abba ta shige cikin gida dama a takuri take, bayan sun gaisa da tambayar hanya, Abba ya shiga gida.

gajiya da zama shiru yayi ya duba a gogon hannunsa lokaci ya tafi gashi za su KAITA, ya kamata Deen ya fito haka su tafi,

shiga yayi falon inda ya tarar da Deen cikin wani yanayi, duk sai ya had'iye zolayar da ya zo masa da ita da tambayar

"Deen lafiya naganka haka"?
k'ok'arin daidaita natsuwarsa yayi kafin yace "ba komai, ya kamata mu gaisa da Abba mu tafi"

zubawa abokin nasa idanu yayi yana nazari dan bai yarda da bakomai ba,

dole da matsala, to ko bata masa bane? sanin ba zai bashi amsa ba yasa shi cewa "nima tunanin da nayi kenan, ina Balkisun"?

"ta shiga ciki" ya bashi amsa a takaici, suna haka Abba yayi sallama, sosai suka gaisa ciki da mutuntawa,

Abba na ta jin dad'in samun siriki na gari,

"Abba zamu tafi, dan zamu KAITA acan zamu kwana gobe da sassafi zamu dawo, daganan zamu wuce Legos" Deen yayi maganar cikin ladabi,

"to ba laifi, Allah ya tsare a gaishe da mutanan gida"

Muhusin yace Abba akwai sak'on Dady da yace a kawuma, da kuma sakon Balkisu"

"harda wahala haka, angode sosai, amma daga yau karka koma wahalar da kanka, komai bama bukata, fatanmu dai Allah yasa alkhairi da albarka,"

"Amin" suka amsa cikin jin kaunar dattijon,

Suna zuwa mota wanda abokin Dady ne ya turo masu motar da direva,

suka fito da sak'on Muhusin ya kai har cikin falon sannan suka kara sallama da Abba yana tasa masu albarka,

ko a mota duk yanda Muhusin yaso jin abunda ke faruwa Deen yaki ya fad'a masa,

dan da kunya yace mace kuma wace ya gama cika bakin baya sonta, yanzu ya dawo yana sonta ita kuma tana nuna masa zallar k'i.

tana zuwa d'akin Mama ta fad'a kanta tana k'ara sautin kukanta, Mama tun tana lallashi harta zuba mata idanu, sai dai har cikin ranta tana kin ciwon abun,
. Abba kuwa da ya zo ya tarar tana kuka fad'a ya dinga yi,

"wallahi Balkisu ki shiga taiyayinki, kika kuskura naji kin yin masa rashin ta ido ni da ke ni a gidan nan"

kuka take sosai aranta tana tunanin mi yasa Abba baya fahimtar ta, miyasa baya tunanin irin halin da za ta shiga sanadin *AUREN DOLE*?

fita yayi dan gaisawa da su Deen, alokacin Ummu tazo itama dai lallashin dai take mata.

sun baru KAITA ciki da farin ciki musamman Deen da ya jima sosai rabunsa da mahaifar Dadyn sa,

sosai yaji dad'in zuwan, irin yanda kakanninsa da famili suka nuna masa kauna,

koda goma tayi suna Katsina, kai tsaye gidan Abba suka nufa, inda suka tarar an had'a masu karin kumallo naji da gani,


basu wani ci sosai ba dan a koshi suki,

yauma dai da aka turomasa ita ko Muhusin bai samu kallon kirki daga gun auta ba, bare kuma uban gayya,

nan take Muhusin yasha jinin jikinsa, lallai in har tunaninsa gaskiya ne, Balkisu bata son abokinsa, da matsala babba kuwa,

haka ya fita d'akin cikin sanyin jiki, Deen ma dai ba wani abun dad'i da ya tsinta daga wajan ta, da ta wuce magana marar dad'i,

haka ya mata sallama cikin sanyin jiki,

awaje suka had'u da Yaya Ahmad da zuwansa kenan, Abba ya gabatar da shi, sun gaisa cikin mutuntawa, daganan suka shiga mota zuwa filin jirgi.


*Karku manta kuna tare da Aisha A Yabo Fulani ta Annabi S.A.W*
[9/28, 8:22 AM] Aisha A Yabo: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*ILLAR AUREN DOLE*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


*Tare da alk'alamin Aisha A Yabo Fulani*

*Β© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUMπŸ„*
β˜†We the best β˜†

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* realhausafulaniwriters@gmail.com

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1


*MANUFARMU ANNABINMU*

*TSARKI YA TABBATA GA SARKIN DA ANNABI MUHAMMADU (S. A. W)YA ZAMA BAWANSA*

*YA ALLAH KA D'AN'DANA MANA ZAQIN QAUNAR ANNABIN KA*

*YA ALLAH KA MANTAR DAMU KOMAI SABODA TUNANIN ANNABIN KA*

*YA ALLAH KA HASKA MANA HASKEN FUSKAR ANNABIN KA MAI TAFI DA HANKALI CIKIN HALARARKA*

*YA ALLAH KAIMANA HAKA ACIKIN ALFARMAR SAYYIDATUN-NISA'IL'ALAMINA*


RANDAWA MEDIA CONCEPT
*Kunaso ahadamaku ring tone da sunayenku?
*Kunaso ayimaku sound track da sunan masoyanku ko kuma lakanin sunayenku?
*Kunaso kuji wayarku tana kiran sunayenku alokacin da akayi kiranku awayoyinku na salula?

Ba anan kad'ai muka tsaya ba har wak'ok'in bikin aure bikin suna, ko wak'ar birthday.

Cikin aminci da karamci zaku samu wanga farinciki da farashi mai sauki, zaku iya samunmu ashafinmu na wasapp dandalin sada zumunta ta wannan lamba 08032176520. Don hudda ta kasuwanci kamar kyautane farashin aikinmu, tsada bata nuna inganci aiki akamfaninmu. Kada Ku manta, Namu dabanne! Domin kuwa aciki zamuyi yanda za'agane cewa lallai kaidinne ko kuma kedindaice akenufi. Ku gwada aiki da sabuwar fasaharmu zakuji dadin tsarin. Mungode mungode mungode.
Isah Randawa ke cewa muzama lafiya da alheri.

*24 to 25*

Sosai su Dady sukayi farin ciki da jin ya amince da auren Balkisu.

cikin d'an k'ank'anin lokaci, aka kai kud'in aure har lefe naji da gani,

tun zuwansa na farko bai sake marmarin zuwa wajan Balkisu ba, abun da yasa ransa duk k'in da take masa da zarar anyi auren komai zai zama tarihi.

yana yawan waya da Abba, tare da bashi hak'uri rashin zuwansa akan aiki ne ya hana shi dawowa, sam Abban bai damu da rashin zuwan nasa ba, kasancewar dama shi mutum be da baya da ra'ayin yawan zance wajan yarinya.

Muhusin duk yanda yaso yasan damuwar Deen ya k'i bashi damar, dan aganinsa abun kunya ne ace wai mace na k'insa, shiyasa ya barshi amatsayin sirrinsa,

sosai ya shiga damuwa dan Allah ya jarabci shi da sonta, sosai maganganunta suka tsaya masa arai.

Mahamod sosai ya k'ara shiga damuwa, ya rami duk yayi wani iri, kamar ba shi ne d'an kwalisa mai yawan fara'a da haba haba da juma'a,

yanzu duk ba fara'a ba ya shiga mutane, daga wajan aiki sai gida, awajan aikin ma aikin kawai ya keyi, amma yawan damuwa da tunani yasa sam baya da maida hankalinsa kan aiki kamar da,

da yake da kwazo da mayar da hankalinsa wajan aiki.

abincin ma sai hajiya tayi da gaski yake ci, sosai sauyin nasa yake damun 'yan uwanasa da abokanan sa.


Balkisu duk da dama can ba mai jiki bace sai ta k'ara zubewa, sosai ta rame sai fari da manyan idanunta da suka k'ara fitowa,

ko yaushe zaka ganta cikin damuwa da yawan tunani da kuka take, Mama tayi lallashi tayi nasihan tayi fad'a amma kamar ba tayi.

yau saura sati biyu biki, Ummu tazo gidan k'arfe goma na safe, bayan sun gaisa da Mama ta shiga d'akin Balkisu ta tarar da ita akan sallaya tana karatun k'ur'ani mai tsalki,

zama tayi kan katifar ta d'auki wani littafin addu'oi da yake ajiye gefin filo, tana dubawa,

sai da ta kai aya sannan ta sadaki tare da yin addu'a,

suka shafa tare, cikin murmushi Balkisu tace "Allah kamar kin san ina son ganin ki"

"Ta samu kenan" Ummu tayi maganar tana dariya,

"ba wani ta samu kawai nayi kewarki ne kwana biyu ban ganki ba, kuma ni an wani kulli ni agida kamar matar aure, matar auren ma ta kulle"

tayi maganar idanunta sunyi raurau kamar za tayi kuka, dan yanzu abun kuka awajan Balkisu baya da kad'an,

cikin tausayi Ummu tace "Allah besty bana jin Dad'in yanda nake samunki cikin damuwa ne, shiyasa na d'auke k'afata da zuwa gidanan, ko mutum yazo ki sa shi gaba da kuka"

"ya zanyi nima ai ba son damuwan nake yi ba, kawai dai banda yanda zanyi ne, wallahi besty wani irin son Mahamod nake ji kamar zan mutu idan na rasa shi"

ta k'arasa maganar tana kuka, kallonta Ummu tayi cikin damuwa tace "kingani ko, Allah idan kuka za kiyi sai na tafiyata,

miyasa ba za ki d'auki k'addara bane"?

"Haba besty idan kowa ya kasa fahimtata ban zaci kema ba za ki fahimci ni ba,

da banyarda da k'addara ba wallahi da tuni na jima da zama abayan k'asa, da na kashe kaina, ko na gudu na bar gida na shiga duniya, dan haka kima daina wannan zancin"

"Uhm kiyi hak'uri sam ba hakan nake nufi ba, ni dai bana so ina ganinki cikin damuwa ne, ki duba yanda Mama ta shiga damuwa saboda damuwarki, kalli yanda Yaya Ahmad ya shiga damuwa, har rama yayi, duk saboda ke,

miyasa ba za kiyi k'ok'arin kwantar da hankalinki ba, ko dan mu masu sonki"

"Hum ba za ki gani ba besty, dan haka mubar zancin, yasu Inna"?

"lafiya k'alau suki, tace na gaishe ki"

"Ina amsawa"
Ummu kwanciya tayi tare da mayar da dubanta ga Balkisu tace
"wai besty wani shiri ya kamata muyiwa bikinan"?

cikin hararata tace "ban sani ba"

"hahahaha ai wallahi garama ki sani, ko kina nufin bikin lami za muyi shi ne"?

"kin bawa kanki amsa, ni komai ba zanyi ba"

ta fad'a yana cire hijab d'in jikinta, ta cire kayan jikinta ta rage daga ita sai zani, tayi d'auri gaba, tace "besty bari nayi wanka dan Allah"

"bama sai kin had'ani da Allah ba, ina nan ina jiranki, dole ki zo mu san abunyi, biki saura wata d'aya"

komai bata ce da ita ba, ta fita,

ita kuma Ummu ta nufi d'akin Mama, suna fira har take cewa "Mama za mu fitar da anko, kuma muna son mu fara shirye shiryen abubuwan da za muyi a bikin, amma besty tak'i ta bani had'in kai"

"karki damu Ummu, kiyi komai karki bi takan k'awarki, yanzu nawa kuke so dan fitar da ankon"?

"atamfa roba 'yar dubu biyu, sai matiriyarl na k'awaye, shi kuma duk yadi dubu d'aya"

"shikenan insha Allah, idan Abbanku ya dawo zan fad'a masa, sai ya baku kud'in kuje kasuwa, ku d'auko"

koda Balkisu ta fito bata fad'amata yanda sukayi da Mama ba, ta cigaba da janta da fira.


Ranar laraba, da yamma Ummu tazo, Mama ta d'auko kud'i ta bata "gashi harna fad'awa abbunku, sai yayanku ya bayar, sai kuje ku sayo, amma dan Allah karkuyi dare,

kinga da kyar Abba ya amince ta fita, da cewa yayi kije keda Nafisa 'yar wajan Asabi, da kyar na shawo kansa ya amince"

"to Mama insha Allah ba zamu jima ba"

Balkisu da take gefinsu, sai yanzu tasa bakinta,

"wai ina zamu"?
"anko zamuje saya"

cikin muryar da take son yin kuka tace "nifa ba ankon da zanyi, kuma ni ba zanje ba"

cikin fushi da fara gajiya da halin Balkisu Mama tace

"Balkisu bana son shashanci, so kike ki nunawa duniya irin auren da za amaki ko?
inhar na isa da ke, to ki shirya kuje,

ki sani tashin hankali da damuwa basu isa su yayi maki matsalarki ba, addu'a zaki rik'i itace makamin mumini"

sosai ta mata fad'a, haka ta tashi tana kuka ta canza kaya daga 'yan kanti zuwa atamfa, ta d'auko hijab kalar kayan tasa,

tana fitowa saiga Maijidda, 'yar Kanwar Mama, tazo, suka dunguma tare, zuwa kasuwa,

su kad'ai suke firansu, tak'i kukasu, sai cika take tana batsewa, suma d'in ba wanda ya kulata.

ko da suka shiga cikin kasuwa, gefe ta koma kamar ba tare suka zo ba, tabarsu suna zab'e,

k'amshin turare ta jiyu, wanda take mararin sake shak'arsa, tana son k'amshin sosai, saboda mahamod d'inta turarensa kenan,

lumshi idanunta tayi ciki da jin shauk'i da son mahamod, da take ji yana yawo acikin jinin jikinta,

k'amshin sai k'ara kusantuta yake, tana k'ara lumshi idanunta, tare da k'ara shaku kamshin,

sunan da taji ankira ne yasa ta saurin bud'i idanunta, fis suka fad'a kan hasken idaniyarta, FARIN CIKINTa,

"Mahamod miyasa zaka tsaya daga waje, muje ciki dan Allah ka tayani zab'i"

"Aa aunty kije kawai, mata sunyi yawa awajan,

zan jiraki anan gefen kantin"

"Kada Allah yasa ka zo d'in, yaro sai shigen kwalafuci, tun da akace an hanaka aure yarinya, kabi ka sukurkurci, ka koma wani iri, sai kace itace autar mata da ba zaka cireta aranka ba,

da Kabir na nan ko cewa ka rako ni ba zanyi ba"!

murmushin yak'i hauru kawai ya mata, yayi saurin barin wajan dan karta tara masu jama'a,

kuka mai k'arfi ya zo mata, da sauri ta tushi bakinta da mayafi tare da rufi fuskarta, wani irin son sa da tausayan juna take ji,

ji yanda ya koma ya rame, duk asanadin ta,

wani tunani tayi wanda yasa ta saurin tunkarar wajan da Mahamod yake tsayi yana danni danni waya,

tanayi tana waigin bayanta tana jin tsoron karsu Ummu su ganta har su biyu bayanta, kasancewar da d'an tazara daga inda ya tsaya, zuwa inda take tsaye,



wani irin abu yaji ya dakar masa zuciya da ya haddasa masa d'ago kyawawa idanunsa,

sukayi ido biyu da ita, da sauri ya k'arasa wajanta, suka zubawa junansu idanu k'im ba ko k'ibtawa.


_kuyi hak'uri da wannan, bana jin dadi, kunsan jiki da jini_

*Karku manta kuna tare da Aisha A Yabo Fulani ta Annabi S.A.W*

aranar suka koma Legos, Ummu har dare tana gidan tana k'ara kwantar da hankalin Balkisu.

ba laifi yanzu Abba yana sake mata sai dai ba kamar fa ba, ko yaushe cikin tunanin Mahmod take, sai dai awajan kowa ta rasa labarinsa,

Abba ya samu mata gurbin karatu cikin Katsina, wannan yasa sam bata da lokaci.

"Ya aboki kwana biyu na daina jinka zaune cikin dare, ko ka daina mafarkin"?

Murmushi Mahmod yayi kafin yace "eh na daina, ina ji ajikina Shalele tana cikin farin ciki aduk inda take a yanzu"

dariya Naseer yayi kafin yace "eh ai kai kullum baka da zance sai na shalele, kwanan baya kace kana mafarki tana cikin damuwa yanzu kuma tana cikin farin ciki,

su Baban soyayya, to wata k'ila sun samu k'aruwa, tana da juna biyu"

mik'ewa Mahmod yayi ya d'auki jikkar laptop d'insa, ya fita aji da sauri Nasir yabiyu shi, "kai aboki fushi, to Allah ya baka hak'uri, ni da wasa na fad'a"

"ko da gaski ka fad'a ai ba laifi bane tunda da aurenta" ya fad'a fuska ba walwala, murmushi kawai Nasir yayi dan yasan kishi ne kawai ki nunnugarsa.

Hajiya da take fitowa daga ban d'aki tana ajiye bota tace "ah wa nake gani kamar Adamu"?

yana susa kai yace "wallahi kuwa Hajiyanmu"
"bisimillah shigo daga ciki"

bayan sun zauna kan kujera hajiya tace "shikenan tunda abokinka ya tafi saduwa tayi wuya"

"ayya Hajiyanmu wallahi ayyuka ne sukayi yawa, ayi hak'uri, ina wuni"?
"lafiya k'alau, ya gida ya aiki"?

"alhamdulillah"
"Bari nasa akawu ma abinci"
"Aa na gode Hajiyanmu, dama akwai abunda ke ta fi dani" nan ya shiga yi mata bayani, sai da ta gama jinsa tsab

"Uhm anya Adamu hakan zaiyu kuwa"?
"zaiyi insha Allah Hajiyanmu, kuma dukanmu za muyi farin ciki da hakan"

"to Allah ya tabbatar mana da alkhairi, bari yayanku ya shigo muyi magana muji ta bakinsa"

"to Allah yasa ya amince, zan tafi"
"Amin, ka gaida gida".

Ranar litinin ta dawo daga makaranta agajiye ga yunwa ta kwasu, tana zuwa ta ajiye mayafinta tana fad'in

"Mama angama abinci yunwa nake ji"

"Aa da saura dai auta, da alama yau kin kwasu gajiya"
"wallahi kuwa Mama, mts anyi rana yau, gashi tun abincin da naci da safe ban sake cin komai ba, ga txs d'in yau yayi zafi"

"to Allah ya taimaka, dama ba a samun karatu a banza dole sai anci wahala"

"Bari naje nayi wanka kafin nan abincin ya k'arasa, mi aka girka mana"?

tayi tambayar tana wucewa d'akinta, "kuskus na mana da miyar kife"

Mama ta bata amsa tana shifa kitchen.

bayan ta k'arasa cin abinci Mama ta dube ta kafin tace "Auta idan sai har lissafina yana dai dai yau wata biyar kenan da mutuwar aurenki,

Ya kamata ace kin fito da wani ko da ba a d'aura auren ba ak'alla dai ayi bakon ku,

amma shiru ba dan kuma ba ki da mane ma ba, ko yau she ana aikuwa kiranki kina k'in zuwa, to abunda dai dai ko yaushe nake fad'a maki ki fitar da miji tunkan mahaifin ki ya waiwaye ki kika k'i,

dan haka sai kiyi hak'uri yau da zai fita ya bani sak'o na fad'a maki ya maki miji kuma umurni yake baki ba shawara ba,

an tsayar da ranar aurenki sati biyu masu zuwa, saura kuma wannan Karun ki kunya ta shi"
gabanta taji ya bada dum! ba ta san ya za ta kwatanta irin tashin hankalin da take ciki ba,

sai dai tayi k'ok'arin danni abunda take ji ta hanyar boye damuwar cikin murmushi tace "to Mama insha Allah ba zan bashi kunya ba"

cikin murmushi Mama tace yawwa Auta Allah yayi maki albarka"
"Amin" ta fad'a tana mik'ewa tsaye d'akinta ta nufa,

tana zuwa ta fad'a kan gado ji take kamar taita rusa ihu ko za ta ragi jin rad'ad'in da take ji a zuciyarta,

sauk'i, "na rasa Mahmod a karu na biyu, tawa k'addarar kenan, ya Allah ka bani ikon yiwa iyayana biyayya"

ta rushi da wani irin kuka mai ban tausayi.

suna fitowa makaranta a hanyar su ta dawowa gida Ummu da suke makaranta d'aya sai dai kowani b'angarinsa daban,

tace "wai besty mi yake damunki kwana biyu nan bana gane maki"?

"Uhm! besty ina cikin damuwa, karu na biyu Abba zai mun auren dole, karu na biyu zan rasa farin cikina" ta k'arasa maganar kamar za tayi kuka,

dafa kafad'an ta Ummu tayi cikin tausayi tace "ayya besty kiyi hak'uri gaskiya ba dad'i, amma ya muka iya ita k'addara bawa bai isa ya sauya ta ba, sai dai k'arfin addu'a yasa k'arfinta ya sassauta,

ki d'auka dama can Allah bai rubuta Mahmod a matsayin mijinki ba, kiyi k'ok'arin manta shi, hakan zai baki k'warin gwaiwan biyayya wa mijinki, da kuma iyayanki,

wata k'ila shima mahamod ya manta da ke yana rayuwar sa a wani wajan, ba mamaki ma ace yayi aure, dan haka kema kiyi k'ok'arin manta shi"
harara ta danna mata idanunta sunyi jajir saboda kishi, "idan ba za ki kwantar man da hankali ba malama karki ce za ki tashi hankalina"!

"oh Allah ya baki hak'uri, daga fad'an gaskiya" ta fad'a tana b'oye dariyar da ta zo mata, suka tari napep zuwa gida.

"Auta kiyi ki k'arasa gogan ki zo zan aike ki gidan Asabi"
"to Mama ai na kusa k'arasawa, yawwa Mama zanje har gidan Yaya Ahmad, amma sai na biya ta gidansu Besty ta rakani"

"to shikenan, yawwa kinga na manta Abbanki yace na fad'a maki angon ba zai samu damar zuwa ba saboda yayi tafiya,

shine yace ko za a nuna maki hotonsa, kinga lokaci ya k'ure gara ki ganshi ko"?

gabanta ya shiga dukan uku uku da kyar ta iya cewa "Aa Mama ba sai na ganshi ba tunda ya maku shikenan"

"Aa gara dai ki ganshi"
"Aa Mama ku barshi kawai ai zan ganshi ne"

"Allah yayi maki albarka"
"Amin ta fad'a tana k'ok'arin b'oye hawayen da ya zubu mata.

ranar juma'a aka d'aura auren Balkisu da mijin da bata tab'a gani ba, sosai akayi taru fiye da aurenta na farin, har su Dady da Yaya Deen sun zo da sha tara na arzik'i,

ba za ka tab'a fahimtar halin da amaryar take ciki ba, bayan sallah isha aka raka ta gidan Mijinta, wanda sai da aka fara kaita gidan iyayen mijinta sannan aka raka ta gidan Mijinta,

kowa ya watse an barta daga ita sai halinta, kuka take sosai, ga tsoro da ya cikata, ba yanda ba tayi ba akan besty ta tsaya amma fir tak'i, dukan k'awayen su sunyi tafiyar su,

tana cikin kuka taji an turo k'ofa firgici ta kallo k'afan wata mata ce kyakyawa da shiga ta kamala ta shigo bayanta wata matashiyar budurwa ce da ba za ta wuce sa'ar Balkisu ba,

kusa da auta matar ta zauna, cikin disasshiyar murya tace "ina wuni" da murmushi ta amsa da "lafiya k'alau amarsu, ana ta bak'unta ko?

kiyi hak'uri insha Allah jibi irin wannan lokacin kuna tare da angonki, ina ta cikaki da surutu ba tare da kinsan ko ni wacece ba,

sunana Hafsat matar babban yayan mijinki ce ni, ina fatan za ki d'auki ni tamkar yayarki"?

kanta kawai ta iya gyad'a mata murmushi tayi kafin tace "'yarki nan Halima za ta taya ki zama kafin mijinki ya dawo, da fatan za kiyi hak'uri da ita"

da farin ciki tace "na gode Aunty"
"ba komai karki damu kinji, ni zan tafi sai da safinku" ta fad'a tana mai mik'ewa bayan tafiyar ta Halima tace

"Aunty amarya ni dai barci nake ji bari na samu d'aki na kwanta"

"kina nufin ba anan d'akin za ki kwanta ba"?
"eh zan duba d'aya d'akin"
"tab bama zaiyi ba, kawai ki zo nan muyi kwanciyar mu, dan ya mun girma"
shikenan bari nayi shirin barci"

auta tashi tayi ta shiga ban d'aki baya ta fito ta sauya kaya zuwa na barci ta kwanta bayan ta shafi jikinta da addu'a, taja bargo ta rufi jikinta, itama Halima ta kwanta gefenta.

cikin kwana biyu sosai suka saba da Halima, saboda Halima mace ce mai barkwanci, haka ba ta da son jiki, tare sukeyin komai na aikin gida,

sosai take K'ok'arin b'oye damuwar da ke cinta a rai, ta rami sai farin da ta sa ki yi, zuciyar ta fal da zullumin wani irin miji ne ta aura, ya kalarsa take? sosai take jin wannan firgaban.

"Aunty wai duk kewar Abbana ne ya sa ki rama haka"?
Harara ta danna mata kafin tace "Halima kin raina ni wallahi"

"hahaha Aunty daga fad'an gaskiya"
"kya kaisu idan kaya ne, ni kin sanmi wallahi ina so naje makaranta ana tsirimun da karatu,

na kira Abba na masa zancin yace ba ruwansa na nimi izininsa"
"shi wa"?
"Ban sani ba Allah inaga sai na fara dukanki"

Halima ta kyalkyace da ita kafin tace "tab da ba sai nayi tafiya ta ba naga wacce za ta taya ki zama"

"to ya na iya tunda kin riga da kin ganu Laguna" dukansu sukayi dariya
"Aunty ki kira kaka ki fad'amata kinga idan tace kije sai kiyi tafiyar ki, mu dinga zuwa tare"

"yawwa Halima na shiyasa na keyi da ke, amma fa ina jin nauyi gaskiya, shiyasa ma ranar da muka je na kasa sakewa a gidan"
"Uhm to bari yau idan naje sai na fad'a mata"
"Yawwa na gode".

tunda sarakkuwarta ta mata izinin zuwa makaranta ta cigaba da zuwa makaranta wannan yasa damuwar ta sassauta mata, ko yaushe suna tare da besty da Halima.

zaune suki cikin wani lambun makarantar da aka k'awata sosai, Muhibbat tana zaune gefinsa kuka take sosai,

kallon ta yayi ransa duk ba dad'i yace "wai Muhibbat mi aka maki ne,?

kin nimi na zo nan na kuma zo kink'i kiyi magana, sai sani gaba da kikay kina kuka"

"Muhibbat kina dawo da zance baya ina ce mun wuce wannan ko"?
"Uhm shikenan kayi hak'uri, Allah ya tsare ya kaiku lafiya, sai

Please Login or Register in order to submit comment