Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

munyi waya ko"?

"Insha Allah" daga haka bai saki cewa da ita komai ba yasa kai yayi tafiyarsa tabi bayansa da kallo, Allah ya jarabce ta da sonsa.

sanyi take cikin Les ta fito hannunta riki da jikka sai mayafin da take shirin yafawa, sukayi kicib'is da Halima da dawowarta kenan daga gidan kakanninta,


"Aunty ba dai makaranta za ki ba"?
"kin san ai cam zanje tunda ba wani wajan nake zuwa ba, har kin dawo, ya su Hajiya"?

"lafiya k'alau take, tace a gaishe ki, amma Aunty kin manta yau Baba k'arami zai dawo"?
cikin dakewa tace "eh na sani, amma ai har naje na dawo ba zai isu ba, tunda zuwan dare zaiyi"

za tayi Magana sai ga Ummu da Inna Asabi sun shigo, "wannan shirin fa sai ina"?

Ummu ta tambaye ta tana kallonta, duk sai ta rasa abunda za tace, so tayi ta fita ko za taji sassaucin abunda take ji a zuciyarta, sai dare ta dawo, dan bata da wani txs a makaranta,
Gashi su Inna sun rushe mata fitar,

cikin basar da tambayar Ummu ta washe baki da fara'a tana cewa "sannunku da zuwa Inna ku shigo"

ta fad'a tana juyawa ciki bin bayanta sukayi Halima tayi murmushi da ban san ko na miye ba ta shige.

"Halima ta kawu masu abun sha bayan sun gaisa ta fita ta basu waje,

"Auta ya gidan da fatan ba wani damuwa ko"?
"humm damuwa har za a tambaye ta Ta tana ji, bayan sun san sun kaita gidan damuwan" Ummu ce ta katse mata tunanin da cewa
"Bari naje wajan Halima"

Bayan fitar ta Inna ta gyara zamanta kafin tace "fita da za kiyi ko, wallahi ina gudan maki yin aikin da nasani auta"
"kai Inna ni fa ba fita zanyi ba"

"ke dai kika sani, gara ki kwantar da hankalin ki aure ne an riga da anyi, idan kikace za kiyi k'ok'arin kashi wannan auren shikenan sai ashiga k'irga maki aure,

kuma rashin mutunci ko k'ok'arin kashe auren ki zai haifar maki da nasani marar yankewa,

idan kinyi biyayya za kiyi farin ciki da sanyawa iyayanki albarka, ungu wannan maza canye"

ta fad'a tana fito da wata kula acikin Leda, sai kuka take tak'i kallon ko kolan bare yasan miye aciki,

"wai za kiyi abunda nace ne ko sai na nuna maki Halina, kin dai sanni sarai"!
tayi maganar cikin tsawa,

ba shiri ta janyo kolan gabanta, tana bud'ewa da faffan kaza ce, da taji magani, tana ya tsina fuska ta fara ci, sam ba wani dandano mai dadi amma Inna tasa ta gaba sai da ta canye tsab,

ji tayi yana tasu mata kamar za tayi amai, tana cikin yanayin Inna ta bata wani ruwa sai da aka cika
da suke cikin gora, haka tasa ta ta sha rabi ruwan sam ba dad'i sai bauri,

Ummu ce ta shigo da sallama tana fad'in "Inna ga mai zanin lallen nan ta zo"

"yawwa aikuwa tayi sauri muje auta ta zana maki lalle" wani irin abu ne ya tsaya mata a rai ji take kamar taita rusa ihu ko za taji sassaucin abunda take ji,

haka ta tashi suka koma falo sai antayawa Besty harara take, ita kuwa tama k'i yarda su had'a ido sai dariyar da take k'unshewa,

ranar su Inna basu bar gidan ba sai yamma sai da suka sake gyara gidan ya sake fitowa Fes, ranar kam tasha gyara sosai, ta cika fum, koda su Inna suka tashi tafiya ko arzik'in rakiya basu samu ba, ba wanda yace da ita komai,

Halima anayin sallah magarib ta fito da 'yar akwatin kayanta, Balkisu da take fitowa falo da plet d'in abinci a hannunta ta dubeta da mamaki tace

"ah miye haka, ina za ki da jaka"?
"kai Aunty har sai kin tambaya? to gidan kaka zanje"

cikin harara tace "ai bama za ki fara ba Allah"
"aunty Momy ce fa tace na tattara na koma can tunda Abba k'arami zai dawo"

hawaye ne masu zafe suka biyu fuskarta da sauri ta bar wajan, Halima ta bita da ido, sosai take jin tausayinta,

sai dai ba daman ta zauna, wannan yasa tayi tafiyar ta, sa sasaanta daga baya.

tana zuwa d'aki ta fad'a kan gado tana kuka sosai, fad'uwar gabanta yana tsananta, yanzu shikenan haka za ta zauna da wanda bata so,

k'ilama Yaya Deen ya fishi dama dama, ta rasa Mahamod kenan har abada, Haka zuciyarta taita mata sak'i sak'i, har barci ya d'auke ta, abincin da bata ce ba kenan.

k'arfe shiddan yamma suka sauka filin jirgin Katsina, 'yan uwansa suka zo d'aukarsa,

kowa kagani acikinsu fuskarsu ciki da farin cikin had'uwar su, "kai anya zan gane ka idan a hanya muka had'u"

cikin murmushi yace "haba Yaya ai ko ya na zama ba za ku kasa gane ni ba, bare ma na rame saboda kewarku"

"ahakan ka rame, lallai idan da babu kewa a tare da kai ina ga ko k'ofar Katsina sai tama kad'an"

yayarsa ta fad'a tana dariya,

dukansu sukayi dariya kafin duka shiga motucinsu, d'aya 'yan uwansa mata, d'aya kuma shida yayyansa maza.

kai tsaye gidan iyayansa suka nufa, ko pakeng basu k'arasa ba gajiya ta fito tana

"lale marhabin da autana, marhababika"

da sauri ya fito mota ya rungumeta itama rungumeshi tayi suna farin ciki, harda hawaye,

"Hajiyanmu nayi kewarki sosai"
"auta kewa kam ai ba a magana, alhmdlh da Allah ya dawo man da kai lafiya"

"oh Hajiyanmu tun awaje ba za kiyi hak'uri ya shigo ba"?

"barni Ummi yaushe rabu, ai nayi k'ok'ari da ban biku filin jirgin ba"

haka suka shiga ciki suna ta farin ciki, a gida sukayi jam'i, bayan sunyi sallah isha suka zauna k'ofar d'akin Hajiyanmu sukaci abinci, ana ta fira ciki da k'aunar juna,

"Abba albishirinka"
"goru Sadiya ko nayi siriki" ya fad'a yana kallonta ciki da murmushi"

rufi fuskarta tayi tana dariya k'asa k'asa kafin tace "kai Abba ba fa wannan ba, wani kyakyawan albishirin ne zanma"

"to ina jinki"
Ummi ce ta bugi bakinta tana fad'in "to gan d'uki, fad'i ba a tambaye ki ba, idan na sake jin bakin ki anan sai na bubbugi bakin naki"

mik'ewa tayi tabar wajan tana tunzurin baki,

"Yaya miyasa za ki kura man 'yata"?
"kai surutu ne bana so wallahi"

Hajiyanmu ce tayi gyaran murya kafin tace "to alhmdlh auta na godewa Ubangiji da ya dawo mana da kai gida lafiya ciki da nasarar abunda akaje nema,

sai dai auta nama wani karambani, ina kuma fatan za ka fahimci ni, na kuma yi hakan ne saboda sanin ban tab'a saka ko hanaka ba kak'i,

da ni da 'yan uwanka mukayi hukunci d'aura ma aure, ba tare da mun nemi shawaran ka ba,

wanda yanzu haka tana zaune acikin gidanka da 'yan uwanka suka saya ma, ina fatan za ka mana biyayya"?

wani irin gumi ne yaji ya wanki dukan ilahirin jikinsa, bugun zuciyarsa ya k'aru, yana ji kamar za ta fasu k'irjinsa ta fito,

kowa da yake wajan yayi shiru sai kallonsa suke, da k'yar ya iya bud'a baki yace "insha Allah kamar yanda kuke tsammani ba zan maku akasin hakan ba,

na karb'i auren Allah ya sanya alkhairi, na gode sosai"

dukansu suka amsa da amin, suna kallonsa ciki da tausayawa,

"ka tashi ka kimtsa zuwa anjima Adamu zai zo sai ya rakaka gidan naka, dukanmu muna maka fatan alkhairi"
cewar yayansa,

Hajiyanmu cikin farin ciki tace Allah yayi maku albarka, Allah ya k'ara had'a kawunanku"
"Amin Hajiyanmu" suka amsa cikin farin ciki, idan aka ciri auta da tun da yaji maganar an masa aure bai sake d'ago kansa da yake a duk'i,

wannan yasa ba za a tab'a fahimtar yanayin da yake ciki ba.

k'arfe 9 suna tare da Adamu, dai sam ya k'i bashi fuska daga gaisuwar babu abunda ya sake shiga tsakaninsu,

"kai ni fa malam na gaji da zaman kurami kawai ka tashi muje na rakaka wajan amaryar ka, na tabbata kana ganin amarya ba sunana ba ni kaina mantawa za kayi dani"

Ya fad'a yana dariya, banza ya masa, dan baya jin zai iya cewa da shi komai, wani irin fad'uwar gaba yake ji,

sai Inna lillahi wa Inna ilaihi raji'un yake ta fad'a acikin zuciyarsa,

mik'ewa tsaye yayi yana fad'in"bari na fad'awa Hajiyanmu idan ita tama magana ai za kaji"

mik'ewa Mahamod yayi da sauri yana hararar Adamu, suka fice d'akin, kai tsaye wajan da Adamu ya ajiye motarsa suka nufa adamu ya ya bud'e masa k'ofar mai zaman banza sannan ya juya d'aya b'angarin ya shiga, yayiwa motar key.

har suka isa ba wanda yacewa wani ko ci kanka, yana tsayawa yace "to ranka ya dad'i ango mun zo gidan, sai ka k'arasa daga ciki,

sai na dawo gaida amarya da karb'ar tsarabata" bud'i motar kawai yayi ya wuce dariya kawai Adamu yayi ya ja motarsa ya bar wajan,

dama ya san gidan yana nan aka fara ginin gidan,

yana zuwa falon ya lumshi idanunsa dan wani ni'imtaccin k'amshi ne yaji ya ziyarci hancinsa, ga wata irin natsuwa da yaji ta saukar masa,

fad'awa yayi kan kujeran da aka k'awata babban falon da su,

ciri hulan kansa yayi tare da jingina bayansa da bayan kujeran, lumshi idanunsa yayi yana jin wani iri a ransa,

yau wai shine yayi aure, gashi gida d'aya da wata ba Shalelensa ba, wani irin son Balkisu yaji yana tasu masa tamkar yau ne ya fara jinta aransa,

tunawa tana gidan wani wani irin kishi ya tasu masa, "har abada ba zan daina sonki ba Balkisu"!

ranar a falon ya kwana dan baisan wani d'akin ne nasa ba, kuma baya ko son ganin matar gidan bare ya dudduba.

washe gari kiran farko ya tashi "mts"! tsaki yayi yana tunanin ina zaiga ban d'aki,

bai da mafita da ya wuce ya dudduba, d'aki biyu ne ya gani jire da juna, cikin sa'a yana bud'i d'aya ba kowa ko alamar mutum, babbar, katifa ce da kujeri hud'u, sai k'aramin firij da yake gifen k'ofar shigowa, sai wadurop d'in bango, da ban d'aki,

shiga ban d'akin yayi bayan yayi lalurarsa yayi wanka tare da d'auro alwala, masallacin unguwar ya nufa dan gabatar da farilla.

Auta tana tashi sai da tayi wanka ta d'auro alwala, bayan ta idar ta shirya ko Karin kumallo batayi ba ta fito ta bar gidan, dan dama Allah _Allah take gari ya waye tabar gidan ko zuciyarta za ta ragi zugi da yawan fad'uwar gaban da take ji,

duk kuwa da sai k'arfe tara take da karatu hakan bai hanata yin sammaku ba.

kusan sati d'aya da dawowarsa, bai tab'a damuwa da sanin wacece matarsa ba, baya dawowa gida sai dare yayi sosai,

gari na wayewa zai fita ya bar gidan, yana yawu gidan 'yan uwa yana rabun tsaraba, ko yaushe tunaninsa taya zai rabu da wannan matar da ta Zame masa alak'ak'ai?

a wajan wa zai samu labarin Balkisu? koda wasa bai zai nufi gidan iyayanta ko wajan besty da sunan neman labarin shalelensa ba,

bai san agunwa zai ji labarin ta ba, idan ya dawo gida da dare ya d'auko awarwaronta yana kallo yana jin wani irin sonta na sake shigarsa,

akwati babba kullum sai ya duba kayan da ke ciki wanda ya saya da sunan Balkisu, komai ya gani ya burgi shi sai yaga zai mata kyau,

hakan yasa yayi ta jibgu mata kaya iri iri, sai dai ya rasa ya ina za su kai gareta, wannan tunanin kam ya zame masa jiki.

Auta ko yaushe tana cikin damuwa da kuka, ko yaushe cikin b'oye kanta take gudun kar su had'u, ta daina zaman falon komai cikin sauri take yinsa tabar wajan dan kar su had'u.

Bayan wata biyu da dawowarsa, ranar Juma'a ya dawo masallacin Juma'a, da matsinacin ciwon kai wanda ya haddasa masa dawowa gidan da wuri,

yana zuwa ya kwanta kan kujeran da take d'aukar mutum uku, Ya dafa kansa da hannunsa idonsa a rufi, yaji wayarsa tana ringing, ba tare da ya bud'i idanunsa ba yasa hannu cikin aljihu ya ciro wayar d'aga kiran yayi ba tare da ya duba mai kiran ba,

sallama yayi jin muryar yasa ya saki murmushi cikin farin ciki yace "Nasir"

"na'am Mahamod ykk"?
"lafiya k'alau wallahi tun jiya nake so na kira ka abubuwa sun mun yawa"
"d'an rainin wayau ai ba za ka kirani ba, dan kasan ina ciki da kai"

Mahamod ya shafa sajen da yake fuskarsa yana murmushi kafin daga bisani yace

"ka fiye k'urrafi wallahi, yanzu kuma mi akayi"?

"Hm ai za kace haka, yanzu dai na shigo cikin garin Katsina" da sauri ya tashi zaune yana fad'in "wai dan Allah da gaski kake"?

"Na tab'a yi ma irin wannan wasan ne?
dan Allah fad'amun ina zan sameka"
"Bari na zo na k'arasu da kai fad'amun kana wani wajan"?

nan ya fad'a masa inda yaki ya tashi da sauri ya bar gidan yana fitowa ya fad'a cikin sabowar motarsa da ko wata bata bai rufi da sayenta ba.

suna zaune falo suna gaisawa Nasir yace "wai ya naji gidan shiru ina su Hajiya ne"?

jingina bayansa yayi da bayan kujera yana cewa "Hajiyanmu tana gidanta"

da mamaki yace "kamar ya, to nan ina ne"?
"bari na kawu ma abunsha, ya mik'i yana mai basar da tambayar,

shigarsa ko minti biyu ba ayi ba suka shigo gidan suna dariya da shewa, sukayi turus sanda sukaga wani zaune yana latsar waya,

yayinda bugun zuciyarta ya tsananta, wayyo Allah! ji take kamar ta koma baya, duk b'oye b'oyen da take yau sun had'u,

ita kuma besty da murmushi tace masa "ina wuni"?

d'ago idanunsa yayi yana kallonsu da mamaki ya amsa da "lafiya k'alau, sann....

maganarsa ce ta mak'ale sanda yayi ido biyu da Balkisu, tabbas koda bai tab'a ganinta ba yasan wannan Balkisun da amininsa ya mutu kanta ne,

to ya haka mi ya kawu ta gidan" ?
gaba d'aya kansa ya k'ulle,

auta da sauri ta bar falon ta shige d'aki har da turo k'ofar da k'arfe, murmushi Ummu tayi tabi bayanta,

tana zuwa ta tarar da ita kwanci kan gado tana kuka wannan kad'ai zai tabbatar mata har yanzu Balkisu bata san waye mijinta ba,

zama tayi gefen gado tana fad'in "wai miye haka besty"?

"yanzu wannan ne mijina wayyo Allah na, ina zan sa kaina, wallahi ya cuceni, shikenan da gaski na rasa Mahamod"!

ta k'arasa maganar cikin shisshik'an kuka, cikin had'iye dariyar da take zo mata tace "kai besty wannan fa ya fi Mahamod kyau da had'uwa,

kawai ki manta da wani mahamod ki rungumi kyakyawan mijinki hannu bibbiyu"

afusace ta mik'e daga kwanciyar da tayi ta zauna tana hararar Ummu kamar za ta zazzagu idanun,

"Besty bana son haka ki daina had'ani da wannan da ko k'afan Hubby bai kamu ba a kyau da had'uwa"!

"Allah ya baki hak'uri, ni kinga yunwa nake ji wallahi"

"ai gidan ba bak'onki bane ko"! ta fad'a a fusace, murmushi Ummu tayi ta tashi ta nufi firj, ta d'auko drink tare da dunot, ta dawo ta zauna tana ce ba tare da tace da ita komai ba.

Mahamod ya fito da lemon kwali da goran faro yana fad'in "fara da wannan kafin a kawu mana abinci daga gidan Hajiyanmu"

Nasir da tun bayan shigarsu auta d'aki yake tsaye awajan da suka barshi tamkar an dasa icce,


kumawa yayi ya zauna inda ya tashi yana kallon Mahamod da mamaki ciki a fuskarsa yace

"wai ni kam nan gidan waye ka kawu ni"?

"Ina kake tsammanin zan kawu ka"?

"dan Allah ni ka bani amsa wallahi kaina a k'ulle yaki"

"kana da matsala, to gidana ne, ranar da na dawo na tarar Hajiyanmu da yayyena sun mun aure, shikenan kaji abunda kake son ji"?

"Hum! to wacece matar taka"?
"nima ban sani ba, dan ba damuwa nayi da nasan ko wacece ba"

Nasir zaiyi magana mahamod yayi saurin taran numfashinsa da fad'in "kaga malam ba fa za ka sani gaba da tambaya kamar muna kuto ba"

shiru Nasir yayi tunaninsa d'aya wacece matar acikin su biyun, Balkisun ko ta tare da ita, ko kuma matar tana ciki, to miye alak'ar matar Mahamod da Balkisu??

sake nisawa yayi kafin yace "to yanzu ya zancin Muhibbat, dan ta dame ni da kira, tace tun dawowarmu baka tab'a kiranta ba,

numbarka ma da na bata tunda ka daga sau d'aya kaji itace baka sake d'aga kiranta ba,

ta damini shiyasa ma na tasu naji dalili"

fuskarsa ba walwala yace "kawai ina cikin damuwar wannan auren ne shiyasa sam na manta da ita,

bana son damuwa ne shiyasa bana kulata, ka kuma san halinta da nacin masifa".

"besty ni kam zan tafi gida"
"tun yanzu?" cewar auta,

"eh kinsan fa na fad'amaki akwai bikin Hajara 'yar islamiyar mu da akeyi yau ake walima,

"Allah sarki kinji dad'inki besty kije duk inda kike so aduk lokacin da kika ga dama ba wanda zai hanaki"

"kema kinji dad'in ai, anan gaba za ki tabbatar kin fini jin dad'i da farin ciki insha Allah"

"hmm, ke dai ki gaida su Inna da Mamana, kiyi hak'uri ban girka mana abinci ba, ba zan iya fitowa falo ba wannan mutumin na nan"

"ke dai kika sani kawai kin hanani tafiya gida kinsa na biyu ki kin barni da yunwa" ta fad'a tana murmushi tare da mik'ewa tsaye tana d'aukar mayafinta,

daganan sukayi sallama dama bata sa ran za ta samu rakiya ba daga gun auta.

"tashi muje gun Hajiyan..... maganar sa ce ta mak'ale sanda yayi ido biyu da Ummu, itama kallonsa take cikin fito da ido irin na mamaki d'inan,

"Mahamod"!
"Ummu mafarki nake ko kuma gaski"

cikin murmushi tace "gaskin dai ne, kwana da yawa ganin ka yayi wahala"

"Hmm kinsan ban jima da dawowa ba, sannan ban tab'a tsammanin zan ganki ba, amma mi kika zo yi anan d'in"?

cikin murmushi tace "k'awata ce take aure a gidanan, hala abokin ango ne kai"?

wani irin dum yaji a zuciyarsa, murmushi yayi mata mai kama da na yak'i ba tare da ta iya ce mata komai ba,

"to ni kam zan tafi gida" tayi taku d'aya zuwa na biyu taji ya jihu mata tambayar da dama tasa ran zai mata,

"Ya labarin Balkisu ina fatan tana lafiya? amma yanzu ta haihu ko?

juyowa tayi tana murmushi tace masa "lafiya k'alau taki, Aa bata haihu ba, ai aurenta na farko ya mutum,

harma anyi mata wani auren, wata biyu kenan da auren"

wani irin jiri ne yaji wanda ya haddasa masa saurin zamewa kan kafet, da sauri ta fice gidan dan dariyar da take cinta,

yana gida d'aya da abu amma sun kasa fahimtar suna tare,

Nasir murmushi yayi mai ciki da farin ciki da taya amininsa murnan cikar burinsa, hawaye ne masu zafe suka zubo masa a idanu,

cikin wata irin murya yace "Nasir wannan wani irin rashin rabu ne, wallahi da nasan haka da ba zan bar k'asarnan ba,

auren ta ya mutu har tayi wani auren ba dani ba, kai gaskiya na cika marar rabu"!

yayi maganar da k'arfe zuciyarsa na masa wani irin zafe tamkar rashin wuta, yanayinsa ya sauya cikin 'yan mintuta,

kallonsa ya ke da tausayawa kafin yace "kana da rabu Mahamod rabunma mai girma, sai dai idan kayi sake har ya sub'uce ma shine babban rashin rabu,

ni zan wuce amma ina mai baka shawara da ka gaggauta sanin wace ce matarka, ka sauki nauyin da yake kanka,

ka kuma dinga tuna akwai mutuwa akwai hisabi, kana da ilimi kasan hukuncin mijin da ya danni hakk'in matarsa"

daga nan ya tashi ya fice gidan, Mahamod ya kasa ko mutsawa bare tashi ya raka amininsa, zuciyarsa yana jinta a cunkushi,

da kyar ya iya jan jiki ya nufi d'akinsa, ya d'auro alwala, ya fito da nufin zuwa masallaci sai yaji har sun sallami, hakan yasa ya tsaya falon dan gabatar da sallah la'asar.

wata irin yunwa ce ta tasu mata tana ji tamkar 'ya'yan hanjinta za su fitu, wannan yasa tana idar da sallah ta cire hijab d'inta ta nufi kitchen da yake cikin babban falo,

kansa na a sunkuyi yaji mutsi hakan yasa ya d'ago kansa yana kallon inda yake jin mutsin,

wata irin zabura yayi ya mik'i tsaye kallonta yake yana murza idanunsa, shin mafarki ne ya ke yi ko miye?

itama d'in daskarewa tayi awajan, idanu waje tana kallonsa,

matsuwa yayi gab da ita cikin wani irin yanayi yace "shalele da gaski ki d'in ce ko dai gamu nayi"?

cikin fargaba da tsoro tace "nice farin cikina, mi kakeyi anan"?

tayi tambayar ciki da fargaba amsar da za taji, dan abunda ranta ke bata abokin mijinta ne,

"Shalele ai ke zan tambaya mi kikeyi anan"?

sunkuyar da kanta k'asa tayi idanunta suna zubar da hawaye masu zafi kafin tace "aure na kiye, karu na biyu an saki yimun auren dole,

dan Allah farin cikina tunda abokinka ne shi ka masa magana ya sake ni muyi aure wallahi kai nake so Kaine farin cikina"!

ta k'arasa maganar tana mai durk'ushewa awajan sautin kukanta yana k'aruwa,

da sauri ya sunkuya yayi sujjada, yana mai godeya ga Ubangiji, kafin daga bisani ya d'ago cikin farin ciki ya d'auketa yana juye da ita yana ta sabbatu, cikin mayen so

"Allah na gode ma, shalele Allah ya cika mana burinmu, Allah yayi za muyi aure, za mu rayu acikin inuwa d'aya,

Allah ya sakawa su Hajiyanmu da su Abba da alkhairi, sun bani farin cikina"

rasa tayi mi za tayi kuka ko dariya za tayi, mak'alk'aleshi tayi tana jin wani irin farin ciki da tun da take a rayuwarta bata tab'a ji ba,

rungume juna sukayi tamkar zasu mayar da juna ciki, zaunawa sukayi kan kujera ya d'aurata kan cinyoyinsa, wata irin kunyarsa ce ta rufeta tayi saurin b'oye kanta cikin faffad'an k'irjinsa,

d'ago kanta yayi yana kallonta cikin so yace "daina boye man kyakyawar fuskarki da na ke cikin matuk'ar kewarta,

rufi idanu tayi tana murmushi mai ciki da tsantsar farin ciki, "kin san mi"? Ya cigaba da magana ba tare da ya jira amsar ta ba,

gaskiya ba k'aramin d'ibu ni akayi agida ba, wata biyu ina tare da ke a gida d'aya ban sani ba, gaskiya anshammatu ni"

"wai kuma besty ta sani amma aka had'a baki da ita tak'i fad'amun, d'azun fa da naga wani na d'auka shine mijina, bakaji yanda hankalina ya tashi ba"

"oh Nasir ne fa, abokina ni" haka suka kasance ranar manni da juna sallah ce kawai take tashinsu.

*K'arshe*
kwanci yaki akan gado ya d'aurata akan faffad'an k'irjinsa yana wasa da jelar kitsonta yace "shalele ya akayi kuka rabu da wancan d'in"?

nan ta shiga bashi labarin duk abunda ya faru, ta k'arasa da fad'in "ashe duk wannan rabun za muyi aure ne,

Gaskiya ina godewa Ubangiji da ya cika man burina, ina fatan yanda ka zama mijina anan duniya har aljanna fiddausi ka zamau mijina"

"Hum"! Ajiyar zuciya yayi kafin yace "Allah sarki shalele kiyi hak'uri kinji nasan duk sona ne ya janyo maki wannan wahala,

Insha Allah zan mantar da ke duk wata wahala da kika sha abaya, zan baki kulawa soyayya k'auna mai ciki da aminci da farin ciki da yarda Ubangiji,

Allah ya bani ikon yi maki halacce kamar yanda kika mun halacce shalele ina k'aunar ki sosai"

ranar kam ankwana soyayya dan bai iya d'aga mata k'afa fa, aranar ya mayar da ita cikakkiyar mace.

"Allah ya tsare hanya, Allah ya dawo da kai lafiya, agaida su Hajiyanmu"

"za su ji insha Allah, mi kike so na sayu maki"?

"banda zab'i da ya wuci naka farin cikina"

Kiss ya manna mata a gushi yana fad'in I love you" sannan ya shige mota, sai da ya wuce sannan ta rufi get d'in ta shige gida tana murmushi.

tana kitchen da yamma tana masu girkin dare, wayarta tayi ringing alamar kira ya shigo,

sai da ta gama wanki naman ta d'aura a wuta sannan ta wanki hannu ta fito falo inda wayarta da ke ajiye kan kujera ta nufa,

tana d'auka taga besty ta mata kira biyu, da murmushi a fuskarta tabi kiran,

ba ajima ba aka d'aga kiran, "amarya kinsha k'amshi, shikenan tunda baka shiga amarci anmanta damu ba waya ba zuwa makaranta"

" 'yar rainin hankali, ai ni fad'ama nake da ke wallahi, yanzu besty da ke za a had'a baki ak'i fad'amun Gaskiyar zance,

kina kallona ina kuka ina damuwa, amma duk kikayi biris dani"

"oh yi hak'uri kinsan Allah sanda akayi zancin Abba da Mama suka kirani sukaja kunnina sosai akan kar

Please Login or Register in order to submit comment