Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ni har babanku bama goyun bayan ka, mace ce ita ina laifin ma tayi sakandiri,

daga nan sai tayi Aure, wanda tayi kuma Allah yasa masa albarka"

"Mama yanzu fa ilimi ba maza kad'ai ne suke yin sa ba har mata, yana da matuk'ar amfani musamman karatun likita, dan Allah Mama ki fahimci ne"

"bafa zan fahimci ka ba, garama ka daina wahalar da bakin ka, ke Balkisu maza tashi kije, saura kuma kije ki masa halin, wallahi ni da ke ne gidanan"!

kallon Yaya Ahmad tayi da ransa ya mugun b'ace duk burinsa akan tilon k'anwar sa yana so ya tashi abanza,

kallonsa take kamar tayi kuka, shima kallonta yake yana mata alama ta ido ta kura ko waye,

Mama da ta kula tace "bisimillar wallahi daga kai har ita inaga sai na fita yamma da hankalin ku,

tashi kije tun muna sheda juna"!

ta fad'a cikin tsawa, tashi Balkisu tayi tana zubar da hawaye ta janyo Hijab dinta da ke ratayi k'ofar Mama tayi hanyar aure, aranta tana tunanin kalau cin mutuncin da zata masa wanda ba zai sa ya k'ara marmarin k'ara zuwa wajanta ba.

tana fita Mama ta jiyo tana k'ara wanke Yaya Ahmad da fad'a, hak'uri dai yake bata, mik'ewa tsaye yayi yana kallon agogo "Mama ni zan wuce"

Hararsa tayi tana fad'in dawo ka zauna, wato ni zaka mayar k'aramar k'anwar cikinka k?

so kake kuje ku taro kuci mutuncin bak'in "?

"wayyo Mama ba fa haka bane, Allah gidan zanje"

"ahaf ko ina ba zaka ba sai ta dawo"

dole haka ya zauna ba dan yaso ba, aransa yana tunanin yanda zaiyi ya cikawa k'anwar sa burinta.

cikin kuka Balkisu ta k'arasa suron gidan cikin....


*Karku manta kuna tare da Aisha A Yabo Fulani ta Annabi S.A.W nake maku fatan Alkhairi*
[8/28, 9:08 PM] Aisha A Yabo: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*ILLAR AUREN DOLE*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


*Daga alk'alamin Aisha A Yabo Fulani*


*Β© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUMπŸ„*
β˜†We the best β˜†

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* realhausafulaniwriters@gmail.com

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1


*MANUFARMU ANNABINMU*

*Ina sonka, ina jin sonka da kaunarka acikin jinin jikina, ya Rasulullahi wallahi ina jin sonka fiye da babana mamata,*

*Ina jin sonka fiye da kaina fiye da mijina fiye da 'YA'YANA*

*Komaina naka ne ya Manzon Allah S.A.W, tunanina kukana yaushe ne zamu gana, yaushe ne zan ganka Mustafa abun nema,*

*Ya Habibullah ya khairil kanzillah ya aba Zhara ya kakan Hasan da Husaini, ya kakan shek Ahmad tijjani,*

*Dan girma son da maulana shehu Ibrahim inyees yake ma, Annabi ka dubi ni ka yarda dani acikin masoyanka, ka sakani hannun damanka, ka yarje mun na rayu da sonka na rayu da kai duniya da lahira*

*Naita jin kaunarka tana kara narkewa acikin jinin jikina da ruhina, alfarmar Babar sharifai uwa wace babu kamarta, macen da babu irinta ba kuma za atab'a yin kamarta ba sayyada Nana FAD'IMA Alaihassalam,*


_ina taya junanmu ga batuwar sallah Ubangiji Allah ya sadamu da albarka da ke ciki, Allah yasa ayi bukukuwan sallah lafiya agama lafiya, kar dai amanta damu wajan naman sallah_πŸ˜‚


*4*


Ranar juma'a da yamma taci ado tana zaune d'akin Mama tana cin waina da miyar taushe da aunty matar Yaya Ahmad ta aiko masu,

sai santi take Mama na dariyar ta, "Allah Mama Yaya yayi dacin mata, ga kyau kirki iya girki, gaskiya sun more abun su"

cikin dariya Mama tace "oh auta duk santin ne haka, aikuwa dai yayi dacin mata Allah dai ya k'ara had'i kansu, Allah yayi masu albarka,

ki kuma Allah yasa kiyi koyi da ita, ki zamo mace tagari"

"Amin" ta fad'a tana mai b'oye fuskarta, wani yarone yayi sallama tun kan a amsa masa yace

"wai Mahamod yace yana sallama da Balkisu"

wani irin sanyi taji yana sauka a k'irjinta, sai dai kunyar Mama ya sa ta kasa ko mutsi bare ta bada amsa,

Mama tsab take kallonta ko bata ce komai ba, ta fahimci tana farin ciki da zuwan bak'on,

murmushi tayi irin nasu na manya kafin tacewa yaron "ji kace ga tanan zuwa"

ta juyo tana kallon Balkisu tana fad'in "idan kin gama sunnu sunnin sai ki tashi kije"

ciki da jin kunya ta tashi tabar d'akin da gudu,

sai da ta wanki hannunta da bakinta sannan taje d'akinta ta d'auko Hijab tasa ya sauko mata har k'asa, dama da kwalliya ta, ta nufi sauron gidan su.


da sallama ta shigo amsawa yayi cikin fara'a, zaune yaki kan bancin da ke ajiye a cikin soron, yasha dakakkiyar shadda fara k'al, sai k'amshi yake zubawa,

d'an nesa da shi ta sunkuya tana gaishe shi, "ina wuni"?

"lafiya k'alau da fatan na samiki lafiya"?

"lafiya k'alau,
"ya mutan gidan"
"Lafiya k'alau" ta amsa a takaici,

kallonta yayi fuskarsa d'auke da murmushi yace "kinyi zak'unni ba zaki gaji ba"?

k'asa tayi da kanta kafin tace "Aa"

gaskiya ban yarda ba, kinga dawo nan ni sai na koma kan wancan dutsin na zauna"

ya fad'a yana mai nuna wajan da yake zaune,

nan ta masa ya dage ganin ya dage yasa ta koma wajan dutsin yana da girma da fad'i, yana daga k'ofan shiga cikin gidan, zama tayi tana fad'in "bari na zauna anan d'in"


"kiyi hak'uri kin jini shiru ko? nama san aranki kinyi tunanin dama ba da gaski nake ba ko?"

yayi tambayar yana kallonta, sunkuyar da kai tayi tana wasa da zoben hannunta,

"kinyi shiru"?

"Aa" ta bashi amsa a tak'aici,
"na gode da bakiyi wannan tunanin ba,
tafiya ce ta same ni bayan na bar nan, ina zuwa gida

na tarar ankira yayanmu da yake Kaduna baya da lafiya yana asibiti,

to shine naje, ni nayi jinyarsa, sai jiya aka bamu sallama, yau da safe nan nan na dawo, na kasa hak'ura dare yayi,

dan na k'agara naga kyakyawar fuskar ki Mai d'auki da kyakyawan murmushin ki Mai d'aukar hankali"

b'oye fuskarta tayi da hannayan ta cikin jimami tace "ayya ya jikin nasa"

"Alhmdlh yaji sauki sosai"

"Allah ya k'ara sauk'i, yasa kaffar ce"

"Amin nagodi sosai da kulawa,

"to ina muka kwana da zancin mu, da gaski Balkisu wallahi sonki nake, so ba na wasa ba, auren ki nake so, burina ki zama matata uwar 'ya'yana , da fatan zaki amince da ni"?

"eh, Allah ya zab'a mana mafi Alkhairi" ta fad'a ciki da kunya,

cikin farin ciki ya amsa da amin,

sosai ya jima suna fira, tun tana kasa sakin jiki har dai yasa ta sakin jiki da shi, dan Mahamod mutum ne mai yawan raha, komai nasa da zolaya ne, ko baka son dariya sai ya saka, shiyasa yake da saurin shiga rai,

sai wajan shidda ya mata sallama suka rabu ciki da so da kewar juna.


sosai shakuwa ya shiga tsakanin su, suna jin son juna matuk'a, har suna jin ba za su iya rayuwa ba tare da juna ba,

idan bai zo ba to suna mak'ale awayar Mama, sosai Mama tayi farin ciki da ganin Auta ta tsayar da hankalinta ta tsayar da mutum d'aya,

kullum nasiharta ta riki mutuncin kanta da na gidan su, karta yarda so ya rinjaye ta, tayi abunda ya sab'awa Ubangiji.

sanda ummu taji labarin tsiya kam tasha agun Ummu kamar tayi kuka.


da dare suna waya da Mahamod yace "shalele ni fa na k'agara naga an shafa fatiha, wai ko dai na tattaru famili na muzo yanzu ashafa fatihar nan asambad'u man ke gidanan"?

ya k'arasa maganar kamar gaski, cikin dariya Balkisu tace "kai ko, hum farin cikina kawai ma hakan ya kamata ayi shawara mai kyau"

"yawwa yawwa ta hannun damana, shiyasa nake sonki, akwai saurin fahimta, zo zo kawu hannunki mu gaisa"🀝🏻

itama mik'a masa hannun tayi🀝🏻kamar suna tare,

"kinga Shalele idan muna tare ba wani ba, ni kaina manta kaina nake, ke har sunana fa mantawa nake wai miye sirrin ne"?

dariya tayi "wallahi farin cikina kana sani dariya, ina jin farin ciki duk sanda muke tare, koda ina zaune sai dai nata murmushi,

wani lokacin na har dariya nake idan ina betar firanmu"


cikin farin ciki yace "burina kenan 'yan matana ki yi ta farin ciki sosai sosai, kin san ni fa gaba daya farin ciki abokina ne, sam ban sani wani abu b'acin rai ba,

Kin san mi"?
cikin gyara kwanciyar ta tace "Aa sai ka fad'a,
"uhm gaskiya tana din da naiwa rayuwar aurenmu ko, har wasu sai sunzo suna d'aukar karatu,

gaba d'aya rayuwar auren mu farin ciki soyayya kula da juna, girki atare zamuyi da duk wani aikin gida, uhm dama miyeπŸ€” hum suna fa da yawa 'yan matana, Allah dai ya nuna mana anshafa fatihar nan"

ya k'arasa maganar yana dariya, cikin murmushi mai nuna tsantsar farin ciki tace "amin farin cikina"

kallon agogo yayi kafin yace "kai kai shalele kinga fa har 11 tayi" cikin shagwaba tace "uhm kai dare yayi, amma dai ai tayi sauri gaskiya"

"ah sosai kuwa shalele muna zuba love ina zamu san dare yayi, yanzu dai kije ki kwanta, gobe akwai makaranta, karkiyi lati,

dan ba bari zanyi adakar mun shalele ba, har makarnta zan zo nace wa malamin, kai kuwa malam kowa fa na love dinan, na san kaima kanayi,

to kaga ni tawa love ne ya hanata barci da wuri, muna ta shek'a love sai kawai mukaga dare yayi sosai, kuma bayan tayi barci mafarkin love yasa bata tashi da wuri ba, shiyasa ta makara, ai bai kamata adake ta ba"


sosai tayi dariya shima yana tayaya haka dai suka rabu cikin shauk'i.


*Karku manta kuna tare da Aisha A Yabo Fulani ta Annabi S.A.W*
[8/28, 9:10 PM] Aisha A Yabo: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*Illar AUREN DOLE*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


*Daga alk'alamin Aisha A Yabo Fulani*


*Β© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUMπŸ„*
β˜†We the best β˜†

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* realhausafulaniwriters@gmail.com

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1


*MANUFARMU ANNABNMU*

*ASSALATU WASSALAMU ALAIKA YA MAJIBINCIN RAYUWAR HALITTA*


*NA TABBATA DAKAI ANNABAWA DA MANZONNI SUKA CIMMA BURIKANSU*

*NA TABBATA DAKAI ALLAH YAKE SAURARAN BAYINSA SUKE SAMUN ABUN NEMANSU*

*NA TABBATA SHIRIYA DA ARZIQIN HALITTUN ALLAH DAGA GUNKA SUKE*

*YA ANNABIN RAHMA KA BAMU TABBATA CIKIN QAUNARKA TA HAQIQA*

*YA ANNABIN RAHMA KA BAMU TABBBATA CIKIN HIDIMA GA AHLIN GIDANKA*

*YA ANNABIN RAHMA KA BAMU TABBATA CIKIN GIRMAMA SAHABBANKA*

*YA ANNABIN ALLAH DAN IRIN HIMMAR NANA FAD'IMA CIKIN BIYAYYAR ALLAH*

*YA ANNABIN ALLAH DAN SAUKAR HAWAYE NANA FAD'IMA CIKIN TSORANTA GA ALLAH*

*YA ANNABIN ALLAH DAN YAQININ NANA FAD'IMA CIKIN ADDU'ARTA*

*YA RASULALLAHI DAN SAYYIDI BABBA DA SAYYADA BABBA KA MUN BAIWAR YAWAN KALLONKA*

*YA RASULALLAHI DAN RAHMARKA GA BAYIN ALLAH KA GOGE LAIFI KANMU*

*YA RASULALLAH DAN MARTABAR MASAUKINKA A ALLAH KA YASSARE MANA ZUWA ZIYARARKA*

*YA SAYYIDA FAD'IMA TUBA MUKE*
*YA SUTURA MAGANIN TSIRAICIN HALITTUN ALLAH*

*KI SUTURTA BAWANKI*
*KI TSARKAKE MU*
*KI GWADA MANA QASAITARKI*


*Ina mai mik'a sak'on barka da sallah ga dukan musulmi Ubangiji Allah ya karb'i ibadunmu Allah ya maimaita mana, alfarmar Annabi SALLALLAHU ALAIHI WSSALAM*

*Ina mik'a sak'on ta'aziya ta zuwa ga iyaya maigidanta, tare da 'yan grp d'in Aisha A Yabo HAUSA nvl, Ubangiji Allah ya jikan Fatima zahra (Maman haidar) da rahama, shugaban halitta ya karb'i bakuncin ta, Allah ya albakaci abunda ta bari, Allah ya bawa iyayanta damu kanmu hak'uri wannan babban rashin da mukayi*


*5 to 6*


Ranar da akayi bikin kammala makarantar su, an rabu da k'awaye anata kukan rabuwa, d'aya b'angarin kuwa ana murnar kammala makaranta.


Yaya Ahmad kuwa ya shirya masu k'ayataccin biki a harabar gidansa, inda suka gayyatu k'awayen su, dama komai tare sukeyi da Ummu tamkar tagwaye, anci ansha anraba abubuwa, anyi lafiya an waste lafiya, kowa na san barka.


da dare Mahamod yazo suka sha firarsu mai ciki da tsantsar so da shak'uwa,

"shalele kinga saura wata biyu ayi bikin hardar ku, ya kamata iyayanmu su shiga maganar mu, ko ya kika ce"?

cikin jin kunya tace "duk yanda kace banda ja"

cikin jin dad'i yace "nagodi sosai da yanda kike man BIYAYYA, wannan ya tabbatar mun ko aure mukayi zanji dad'in zama da ke shalele

Ina jin sonki sosai acikin zuciyata, ke d'in jinin jikina ce"

"hakane farin cikina ban tab'a tsammanin zan waye gari na tsinci kaina da son wani irin haka ba,

sosai nake jin sonka, ina ji kai d'in farin cikina ne, rayuwata ne kai Mahamod"

cikin jin gard'in zancin ta yace "kalaman ki ako yaushe sukan sani cikin farin ciki da shauki, ina ji tamkar yanzu akaimun ke gidana amatsayin matata"

ya k'arasa maganar yana mai zuba mata mayatattun idanunsa da zallar sone ne aciki,

da sauri ta rufe fuskarta tana murmushi dan bata iya juran kallon cikin idonsa,

cikin murmushi yace "kunya ko zakiyi ba yani 'yan mata,

kinga ki fad'awa Baba idan sun bada lokaci sai na turo, ko ayi ashafan fatiha na ganki gidana, agidan nawa ma ad'akina, ad'akin nawa ma a ina ma zance 'yan matana"?

yayi maganar cikin alamar tambaya yana mai kashe mata idanu,

hararsa tayi cikin so tace "kai ko zaka fara ko"?

shafa sajen fuskarsa yayi yana fad'in "haba 'yan matana ina zan fara yanzu, ai sai asamu matsala, zan dai fara idan lokaci yayi"

"hum kai ko" ta fad'a tana mai k'ara b'oye fuskarta cikin mayafi,


"sarkin jin kunya kawai, kinga ina so mu gaisa da Baba gashi muna samun sab'ani had'uwa"

"wallahi kuwa, amma insha Allah yana dawowa da wuri ko zuwa gobe ni sai na kira ka na fad'ama kazo ku gaisa,

zan fad'awa Mama sak'on ka sai ta fad'a masa"

"yawwa kin kuwa kyauta, zan tafi ga tawa 'yar kyautar ba yawa, kinsan abunka da talaka"

ya fad'a yana bata wani abu da bata san ko miye ba, k'in karb'a tayi tana cewa "ka barshi Allah nagodi sosai"

tashi tsaye yayi yana cewa "bama 'yar haka da ke tawan, idan kuma ba kya son kyautar tawa dan ni talaka ne to"

d'auka tayi tace "bafa nason haka miye zaka ce ce haka, kaima kasan ba zan tab'a wannan tunanin ba"

"eh yanzu na yarda tunda kin karb'a" ya fad'a fuskarsa ciki da murmushi,

itama murmushin tayi tana cewa "nagodi sosai Ubangiji Allah ya kara bud'i, Allah ya kara lafiya"

Amin tawan nagodi nima da wannan kyakyawan addu'a, zan tafi sai munyi waya"

Daga nan sukayi sallama ciki da kewar juna.

tana shiga gida tayi sa'a Mama bata tsakar gida sai tayi shigewarta d'akinta, mayafinta ta ajiye tare gateway kan katifa cikin d'auki ta bud'i ledar,

Katina ne masu kyau da d'aukar ido guda biyu, kwanciya tayi rigingini ta fara karantawa cikin shauk'i,

kalamai ne masu tsantsar nuna so da k'aunar wanda akabawa, tana kammala karantawa wasu hawaye masu sanyi suka zubo mata a fuska,

tana jin wani irin sonsa na yawu tundaga zuciyarta har sassan jikinta,

wani d'an k'aramin akwai ta gani d'auka tayi, zobe ne na azurfa irin na mata mai kyau sai kyallen yake,

da sauri ta ciro shi daga mazaunin sa ta rik'i ahannunta tana kallon zoben sai murmushi take tamkar Mahamod ne agabanta,

Kafin daga bisani tayi bismillah tasa a kyakyawan hannunta na hagu da yasha zanin lalle,

sunbatar hannun tayi kuma sai tayi saurin rufe fuskarta tana murmushi

"wayyo Mahamod ina sonka, Allah nuna man ranar auren mu wayyo Allah za aga soyayya rayuwar farin ciki zalla, Allah dan Annabi S.A.W Allah kasa Mahamod rabona, ne mijina uban 'ya'yana ne"

haka tai ta sabbatu ciki da magagin love ita kad'ai tamkar zautacciya, au wa ya sani dan da alama son Mahamod yasa ta zauce lol.

sai da ta gama sabbatu kafin daga bisani ta tashi taje d'akin Mama, bayan ta b'oye katukan.

k'iris ya rage suyi karu da Maman da ke shirin fitowa d'akin,

"yawwa dama fitar nan zanje na kwala maki kira ne, naga kin dad'i fira har 11"

tayi maganar cikin fad'a, tana mai komawa ciki,

binta Balkisu tayi tare da kwantawa jikin Mama cikin shagwab'a tace "ayya Mama tun d'azun fa na dawo ina d'aki"

"aho ai na d'auka kina can kuna firan, dan ni fa yawan zuwan ya ma fara isata, gara ya turo ayi magana yawan firan sam babu amfani hakan kesa azo tun ana fad'an gaskiya har azo ana fad'an k'arya,

daganan kuma komai zai iya faruwa, na maganganu marar ma'ana"

cikin b'oye fuskarta jikin Mama tace "dama yace na fad'a idan ansa masa lokaci sai ya turo iyayansa"

cikin farin ciki Mama tace "yawwa yayi tunani ai shiyasa ina yaba hankalin yaron, babanku na dawowa zan fad'a masa,

dama ko yaushe ina so na fad'a masa zancen yaron sai ina sha'afa, amma yau Insha Allah yana dawowa zan fad'a masa auta fa tayi miji"

ta k'arasa maganar cikin dariya irin tasu ts manya, k'ara b'oye fuskarta tayi jikin Mama tana murmushi,

tace "Mama kinga abunda ya kawu man"

ta fad'a tana nuna mata zoben da ke hannunta,

ture ta Mama tayi daga jikinta cikin fad'a tace "wato hannunki kika bashi ya sa maki zobe"?

cikin tashin hankali ta durk'usa gaban Mama nan take ta fara kuka tana rantsuwa "wallahi Mama ba shi yasa mun ba,

hasalima ban san miye ba acikin ledar gef ya bani sai da naje na bud'e naga ko miye, Wallahi ki yarda dani ko kusa dani bai tab'a zuwa ba bare har hannunsa ya kai jikina wallahi Mama"!

ta k'arasa maganar cikin k'ara fashewa da kuka,

cikin tausayin 'yarta ta janyo ta jikinta tana mai share hauwayen da ke fuskarta tace "shikenan naji na kuma yarda dake,

kawai dai ina maki hakan ne saboda ki kula ki kare mutuncin kanki da namu, sannan uwa uba ko a addinan ce kinsan haramun ne namiji da ba muharramin ki ba ya tab'a ko da d'an ya tsanki ko"?

cikin gyad'a kai tace "eh Mama nasani kuma ana fad'amana a islamiya,

insha Allah Mama zan kiyayi matuk'a wajan kiyayewa"

"yawwa Allah ya maki albarka"
"amin mama" ta fad'a cikin farin ciki, daganan suka fad'a wata firan.

*Karku manta kuna tare da Aisha A Yabo Fulani ta Annabi S.A.A*
[8/28, 9:10 PM] Aisha A Yabo: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*Illar AUREN DOLE*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*Daga alkalamin Aisha A Yabo Fulani*


*Β© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUMπŸ„*
β˜†We the best β˜†

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* realhausafulaniwriters@gmail.com

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1

*WANDA YA CIKA CIF KAFIN YA BAYYANA DAYA NE SHINE ABBAN BATULA*

*AMINCIN ALLAH YA TABBATA GARE DAIDAI CIKARKA YA NAJAMUL'HUDA*

*WANDA YA SAN KOMAI KAFIN SANI YA SAMU SHI KADAI NE SHINE ABBAN SAYYADA ZAHRA'U*

*AMINCIN ALLAH YA QARA TABBATA GARE KA ADADIN YAWAN SANINKA YA BAHARUN-NADA*

*WANDA RAHMA TA SAMU DAGA KANSA SHINE SANADIN RAYUWAR KOMAI*

*AMINCIN ALLAH YA QARA TABBATA GARE KA YA SARIMUL-IDA*


*7 to 8*


11:pm

a lokacin Balkisu tana d'aki suna waya da Mahamod kamar ba d'azun d'azun ya bar gidan ba.

ab'ngarin Mama kuwa tun dawowar Abba ba da jimawa ba, ta kawo masa abinci da ruwan sha, sai da ya kammala, ya watsa ruwa, sannan ta gabatar masa da zancin,

tana daddanna masa k'afafu tace "Malam wallahi ko yaushe ina so na fad'ama, to sai abuwa abuwa suna sa abun ya shafe mun,

"to Allah dai yasa lafiya" cewar Abba,
"Aa lafiya k'alau, Alkhairi ne abun farin ciki ne ya sami mu"

kallonta yayi fuskarsa d'auke da murmushi y"Masha Allah to abani nasha, ko dai auta ce zatayi kanwa ko Kane"?

yayi maganar cikin zolaya, dariya tayi tana fad'in

"haba malam tsufai tsufai dani, Aa na barwa yara, wad'anda Allah ya bamu Allah ya sanya masu albarka"

"Amin" ya amsa yana dariya,

lakutu wani mai da kullum idan zata masa danna ak'afa take shafa masa saboda ciwon k'afan da yake fama Da shi,

"Malam auta fa Allah ya karb'i addu'armu, ta samu yaron kirki, harma yana neman izini akan yana son iyayansa suzo nema masa auren ta"

tayi maganar cikin farin ciki, sai dai nan take farin cikinta ya juya zuwa mamaki,

ganin yanda Abba ya zabura daga kwanci zuwa zaune

yana mata wani kallo mai kama da na tuhuma, sai tasha jinin jikinta,

cikin kakkausar murya yace "ina matsayin ubanta acikin gidanan har wani yazo wajanta ba tare da ya nemi izinina ba, dan kun mayar da ni sullub'un uba"?!

cikin kwantar da murya tace "kayi hak'uri Malam gaskiya ne anyi kuskure,

amma wallahi murna ta kulashi ne yasa ban kawu wannan tunanin ba,

kuma kaga kwanakkinan kana jimawa kafin ka dawo shiyasa ban fad'ama ba, amma dan Annabi S.A.W kamun aikin gafara"

ganin yanda tayi maganar cikin sanyi da kwantar da kai, sai kuma yaji kamar bai kyauta ba, tunda ta fad'i uzurinta tun farko, "uhm"

ajiyar zuciya yayi kafin yace "naji ya wuce,

sai dai ina so ki bani arun hankalinki, ki kuma fahimci ni sosai akan abun da zan fad'a"

yayi maganar cikin nuna maganar mai muhimmanci ce,

cikin sanyin jiki tace "insha Allah zan fahimci ka Malam"

saukuwa yayi daga kan gadon ya koma kan kafet ya zauna tare da jingina bayan sa da jikin gadon,

itama dawowa tayi kusa da shi ta zauna,


"Asma'u zaki dai tuna Nasiru abokina tun k'urciya ko"?

cikin gyad'a kai tace "eh ya za ayi na manta shi, ba shine naji kwanakki kace man kun had'u a zuwan da kayi DUTSINMA wajan su gwaggo ba"?

"yawwa sosai kuwa, baki manta ba ashe" ba tare da ya jira cewarta ba ya cigaba da cewa,

tun alokacin mukayi wata magana da shi akan yanda zumuncin namu yayi rauni,

sam bama ziyartar juna awaya ma mun gagara yin magana,

wannan yasa mukaga mi zai hana mu had'a yaranmu aure, wanda shine zumunci mai k'arfi zai d'ure a tsakanin mu,

a tak'aici dai na yanki hukunci ba tare da neman shawaranku ba ko jin ta bakin auta saboda sanin bata kula kuwa, babban d'ansa Nuradeen zai aure balkisu"

wani irin tausayin 'yarta taji saboda yanda ta fahimci irin soyayya da shak'uwa da ke tsakanin 'yarta da yaron, yanzu ya zata ji idan taji wannan zancin?

"Kinyi shiru Asma'u"
cikin sauki numfashi tace "uhm ba shiru nayi ba Malam, ina dai tunanin lamarin ne kawai,

amma malam kamar bai dace ayi wannan hukuncin ba tare da sanin yaran ba, ka fa san yanzu zamani ya canza,

sam yaran yanzu ba kamar na da bane da suke da kawaici da ya kana,

kuma an daina irin wannan had'in malam, sannan na fahimci sosai Auta ke son yaronan Mahamod"

cikin ko oho yace "naji yanzu mi kike so? ko so kike naje nace masa na fasa saboda anfi k'arfina agidana ko"

"Aa malam ba haka nake nufi ba, Allah ya baka hak'uri, Allah ya sanya alkhairi"

"yawwa hakan nake son ji matata" ya fad'a cikin farin ciki, haka suka kwanta kowa da nashi tunani.


sosai sukayi fira har k'arfe 12 30:am "kai shalele dare fa yayi kije ki kwanta hakanan"

cikin murmushi da jin kewa tace "Allah idan muna tare sai naita ganin lokaci na gudu"

"aifa dole muna zuba love ai komai ma gudu zai mana,

gobe zanyi tafiya da sassafi, k'ila ko da zan tafi kina barci"

cikin shagwab'a tace "haba yanzu sai ka tafi ba muyi magana ba, bayan nasan duk sanda ka bar gari ba zanji ka ba sai magarib"?

cikin dariya yace "ayya tawan ni na isa na tafi ban jin daddad'ar muryar nan taki ba,

ai ni ba dan kar su Abba suga haukata da sai nazo naga kyakyawar fuskar MASOYIYATA kafin na tafi"

"yawwa kawai ma ka biyu komai safe su Abba komai ba za suce ba"

"ah wayo ko tawan, nazo Abba yace kai wannan wani zararrin ne yake mana sammako da uwar sa fiya? kinsan mi zance masa?"

cikin murmushi mai ciki da farin ciki tace "Aa sai ka fad'a"

"cemasa zanyi yi ai kuwa Abba tsab ka ganu ko waye, ai ni indai akan Balkisu ne nafi ma zararri zarewa, tab'abb'ini lambar d'aya"

cikin dariya tace "oh Allah na nurul k'albina kai ko, hum Wallahi zaka cika mun ciki da dariya, ina sonka sosai marar iyaka"

"burina kenan balkisu kiyita farin ciki, sosai nima nake jin ki acikin heart d'ina,

kece mace ta farko da na fara so arayuwata, kuma insha Allah daga ke babu wace zata sake samun koda masak'ar tsinke acikin zuciyata,

sosai nake jinki acikin jinin jikina balkisu"

juye tayi cikin lumshi idanu tace "Mahmoud ban san ya rayuwata zata kasance ba idan kayi nesa dani? Zuciyata ba k'aramin kamuwa tayi da sonka ba"

K'ara rungumi fillon da ke k'irjinsa yayi yana jin wani irin yanayi da ba yace ga kalansa ba, kafin daga bisani ya saukar da ajiyar zuciya yace

"Insha Allah Balkisu ba zan barki ba, karfa ki manta ke rayuwata ce, kice farin cikina, ina tare da ke ako wani yanayi kisha kuruminki kinji shalelena"

sun jima suna amayar da kalaman K'auna wa junansu kafin daga bisani sukayi sai da safe,

tana ajiye wayar alwala tayi, ta fara nafila, kamar yanda ta saba duk dare sai tayi na fila da karatun k'ur'ani kafin ta kwanta barci.


*Daga alkalamin Aisha A Yabo Fulani*
[8/28, 9:10 PM] Aisha A Yabo: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*Illar AUREN DOLE*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


*Daga alkalamin Aisha A Yabo Fulani*



*Β© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUMπŸ„*
β˜†We the best β˜†

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* realhausafulaniwriters@gmail.com

*Web Page:*

Please Login or Register in order to submit comment