Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Asabi Kanwar Mama ce 'yan wa da k'ani suke)

turus tayi tana fad'in "na shiga uku ni Asabi wannan wani bak'in zuwa ne!

Yaya mi ya sami ta haka"?

kowa ya kasa cewa da ita komai, k'arfin hali tayi taje da sauri firij d'in Mama ta d'auko ruwa masu sanyi, ta dawo d'akin da gudu , tana zuwa ta bud'i marfin goran ruwan, ta kwararasu jikin Balkisu,

ajiyar zuciya mai k'arfe Balkisu tayi, dukansu sukayi hamdala, Mama Asabi ta d'agota ta rungumi ta jikinta tana cewa

"Yaya wai mi ke faruwa ne haka"?

sosai Balkisu ta fashe da kuka, cikin damuwa Mama taiwa Kanwarta bayanin komai,

cikin takaici tace "amma shikuwa malam mi zaisa ya aikata wannan d'anyen hukuncin?

ai wannan tsohon yayi ni, tuni mun fito wannan k'arnin na yiwa yara auren dole, gaskiya ba zamu yarda ba, ai muma muna da hakk'i akanta ba wai shi kad'ai ne mai hakk'in ba"

"Uhm Mama wallahi nima nayi iya k'ok'arina Abba ya fahimci ILLAR aubunda ya keso yayi amma sam yak'i"!

ya k'arasa cikin fitar da huce mai ciki da k'unci,

"Ai kuwa ina gidanan sai ya dawo ayi wacce za ayi, dan wallahi ba zamu yarda a cucemu ba"!

Mama da take zaune kan kujera tana saurarnsu sai yanzu ta iya cewa

"Asabi dan Allah ki kyale maganar nan haka, ko kinwa malam ita ba ganewa zaiyi ba, dan akan wannan maganar komai ma zai iyayi,

taruwa dai za muyi muyi addu'a da neman zab'in Allah, dan tabbas tunda yace eh d'in ba canzawa zaiyi ba,

sai wani ikon Allah kawai"

sosai suka shiga lallashin Balkisun da lokaci d'aya ta fad'a ta zabge, Ahmad sai da yaga ta daina kukan sannan ya bar gidan cikin damuwa,

yayin da Mama Asabi take ta sababi da mita, dan sam bata da hak'uri,

Balkisu ta janye jikinta ahankali daga jikin Mama Asabi, ta mik'i tsaye cikin tsananin ciwon kai ta sa kai zata fita,

"ina zaki auta"? Mama tayi mata tambayar tana kallonta ciki da tausayawa,

Ahankali cikin sanyin murya tace "Mama zanje d'aki ne"

bata ko ji abunda maman take fad'a ba ta fice d'akin,

"Uhm" ajiyar zuciya Mama tayi kafin tace "wallahi Asabi na rasa yanda zanyi da wannan al'amarin"

cikin gyara zama akan senter kafet din da ke shimfid'i a falon ta mik'i k'afafunta tana cewa

"Yaya laifinki ne fa, ki tirje masa ki kwatuwa yarinya 'yanci,

amma idan kika sa sanyin halin nan naki wallahi kina ji kina gani zai sata amatsala"

cikin tagumi tace "Asabi duk yanda kike tsammanin lamarin ya wucinan,

ayanda malm ya nuna man ko aurena zai iya tsinkewa akan maganar auren auta"

cikin mamaki Asabi tace "ikon Allah anya kuwa ba mai kud'i bane wannan abokin nasa"?

murmushi mai kama da na yak'i tace "kayya Asabi nasan halin malam kud'i ba za su rud'e shi ba,

k'arfin aminta ne dai da kuma irin yanda yayi masa halacce lokacin yarintar su, shine kawai"

sun jima sosai suna tattauna maganar auren, sai yamma sosai ta tafi tana k'ara lallashi da ban hakuri ga Balkisu.


tana zuwa d'aki ta fad'a kan katifa tana jin wani irin abu mai dafi azuciyarta,

aranta tana tunanin taya zata iya rayuwa da wanda bata so?

taya zata iya rayuwa ba tare da mahamod dinta ba, miyasa abba ya kasa fahimtar ta?

miyasa ya zab'i ya farantawa wasu, nata farin cikin yayi fatali da shi?

kiran waya ne ya dawo d ita daga duniyar tunanin da ta fad'a,

tsurawa wayar ido tayi kamar mai neman wani abun acikin wayar,

harta kusa tsinkewa sannan ta iya danna koren sai dai ta kasa cewa komai saboda wani irin kuka da yazo mata,

ajiyar zuciya yayi kafin daga bisani yace "haba haba shalele ina kika shiga inata kiranki baki d'aga ba?

k'iris ya rage zuciyata ta buga, kinga shikenan kin rasa d'an kyakyawan mijin nan naki"

ya k'arasa cikin zolaya, wani irin kuka ne yazo mata, har bata san sanda ta bud'a baki tana yi ba,

cikin tashin hankali da kid'ima yace "Balkisu mi ya same ki kiki kuka?

ko baki da lafiya ne? ko maganata ce ta b'ata maki rai?

ba amsa saima sautin da kukan nata ya k'ara,

ga ba d'aya ta d'aga masa hankali shima ji yake kamar yayi kukan yace

"dan Allah ki taimake ni ki daina kukanan Shalele ki fad'aman damuwarki,

wallahi bana son jin kukanan nan naki yana d'aga man hankali tamkar saukar dalma haka nake ji"

ya k'arasa maganar cikin lallashi,

cikin kuka tace "ya zanyi ya zanyi, karka hanani kuka Mahamod ko zanji sanyi,

Ina cikin tashin hankali mutuwa zanyi wallahi Mahamod"!

da sauri ya tashi tsaye daga kan katifa da ya ke zaune, yace

"Mi yayi zafi haka shalele, kinga share hawayen ki, ki daina kukan, ganinan zuwa yanzu naji damuwar shalelena,

inma so kike a d'aura mana aure anayin sallah asuba, ai babu matsala shalele, sai ayi, kinga sai ace kai wannan Balkisun saboda ta k'agara ta barsu Abba da Mama ta ganta agidan mahamod a k'ir.... au a inama shalele tuna mun"?

yayi maganar cikin son ya kawar da kukan ya sata dariya,

sai dai akasin hakan sai kukan nata ya k'aru,

cikin dafa kai yace "ya salam shalelena ba za ki daina kukan ba ko, shikenan gani nan zuwa kiji shalelena"?

ba tare da ya jira cewarta ba ya tsinki kiran,

rigarsa da ya cire ya janyo yana sawa, ya zura takalmi ya fito d'akin,

hajiya da take duk'i tana k'ok'arin had'a masa abinci jin mutsin sa ya sata d'aguwa tana murmushi tace

"yawwa yaron kirki harka fito? ga abinci yau mutumin ka nama d'anwake da manja"

cikin son mahaifiyar tasu yace "Mama ki ajiye man zan d'an fita na dawo"

cikin mamaki tace "haba mai babban suna yaushe ka dawo garin ko hutawa bakayi ba kuma zaka fita"?

cikin karyar da kai yace "Hajiyanmu ina naga ta zama shalele na kira tana tamun kuka,

tama tsaya tamun bayani amma tak'i, sai kuka take, shine nake so naje naganta"

cikin jimami tace "ah maza kaje dan Allah, kuka Allah dai yasa to lafiya"

"Amin na tafi"
"to Allah ya tsare ka gaisheta, Allah ya tsare"
"Amin Hajiyanmu" yayi maganar yana fita daga gidan.

kasancewar dare ne yasa da kyar ya samu abun hawa, sai dai fad'uwar gaban da yayi kusan sati yana ji,

na yau ya d'ara na ko yaushe, ga tashin hankalin mi yake damun shalele, sai Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un yake ta fad'a.


*Karku manta kuna tare da Aisha A Yabo Fulani ta Annabi S.A.W*
[9/28, 8:22 AM] Aisha A Yabo: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*ILLAR AUREN DOLE*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*Daga alkalamin Aisha A Yabo Fulani*

*Β© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUMπŸ„*
β˜†We the best β˜†

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* realhausafulaniwriters@gmail.com

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1


*MANUFARMU ANNABINMU*

*NA KASA MALLAKAR HAQURINA*

*MADINA TAYI SANSANI AQIRJINA*

*INAMA YAQININA YA GASGATA BURINA*

*KAMAR AJALINA YANA CIKIN RASHIN ZUWA NA MADINA*

*YA ALLAH KA GAFARCEMU KA WANKE DAUDARMU TA RUHI DATA ZUCIYA KA SADAMU DA SHUGABA KALAMUNCE MANA ZIYARAR MAI GIDA KAFIN ZUWAN AJALINMU*

*sak'o daga shugabanmu Sayyadi zainul abideen*

*SOYAYYA NANA FAD'IMA BA AIBU BANE*
*DARAJACE GA MAI RABO*

RANDAWA MEDIA CONCEPT
*Kunaso ahadamaku ring tone da sunayenku?
*Kunaso ayimaku sound track da sunan masoyanku ko kuma lakanin sunayenku?
*Kunaso kuji wayarku tana kiran sunayenku alokacin da akayi kiranku awayoyinku na salula?

Ba anan kad'ai muka tsaya ba muna yin wak'ok'in bikin aure ko suna har wak'ar bathdy,

Cikin aminci da karamci zaku samu wanga farinciki da farashi mai sauki, zaku iya samunmu ashafinmu na wasapp dandalin sada zumunta ta wannan lamba 08032176520. Don hudda ta kasuwanci kamar kyautane farashin aikinmu, tsada bata nuna inganci aiki akamfaninmu. Kada Ku manta, Namu dabanne! Domin kuwa aciki zamuyi yanda za'agane cewa lallai kaidinne ko kuma kedindaice akenufi. Ku gwada aiki da sabuwar fasaharmu zakuji dadin tsarin. Mungode mungode mungode.
Isah Randawa ke cewa muzama lafiya da alheri.


*13 to 14*


*Asalinsu*

Malam Billo d'an asalin garin katsina a karamar hukumar KAITA,
Baban malam Billo babban manomi ne, yana da mata biyu, Baba Haule, da gwaggo Laure,

Baba hauli itace uwar gida 'ya'yanta uku duka maza, Auwal Nuhu, Isma'il,

Gwaggo Laure yaranta biyu, Billo Nafisa,

gidan zamu iya cewa noma shine sana'ar su kuma arzikin su,

dukan yaran gidan kansu ahad'i yaki, sanadin had'in kan iyayan nasu,

karatun islamiya kawai sukeyi, Billo ne dai Allah ya nufa da yin boko, silar abokin sa Nasir,

Nasiru makwata ne mahaifin Nasiru Alhji Mamuda yana da kud'i yana sana'ar zuwa kurmi,

Nasiru kad'ai ne d'an da suka Haifa, shiyasa suka d'auke son duniya suka d'ura mai,

sosai suke shiri da Nasiru da Billo, tare suke komai, barci ni kawai ke rabasu,

har abotarsu ta janyo alk'a ta mutunci tsakanin iyayan nasu,

sanda za a asaka Nasiru makaranta kuka ya dinga yi yana ihun shi ba za shi ba,

cikin tashin hankali Baba Mamman yace "Nasiru miyasa baka son zuwa makaranta, ko baka so watarana ana nunaka ga TV"?

cikin turo baki yace "ni bana so"

da mamaki mahaifiyarsa hajiya Ladi take kallon yarun nata da ko yaushe yake cewa "Mama yaushe Baba zai sani makaranta nima indinga fitowa a TV tamkar kawu Usman"?

shine kuma yau zaice baya so, janyo shi tayi cikin lallashi tace "d'an Baba fad'aman miyasa baka so"?


"Mama ni bana so na rabu da Billo"

Alhji Mamman da yake kallonsa yayi dariya kafin daga bisani yace "yanzu dan wannan ne kake d'aga mana hankali"?

gyad'a kai kawai yayi, "to shikenan harshi sai nasaku tare, ai shikenan kukan ya k'are"

da murna ya bar gidan zuwa gidan su billo,

zaune ya tarar da Billo yana cin d'umamin tuwon gero da miyar kuka,

Yana zuwa ya tsuma hannu dan Nasiru akwai son dumami, suna ci yace "albishirinka".
"Goro" Billo ya fad'a cikin murmushi,

nan ya sheda masa zancin makaranta, aikuwa abincin da bai k'arasa ci ba ya hau murna.

sanda Baban Nasiru yajewa Baban Billo da zancin da kyar ya amince dan mutum ne da yake da wadatar zuci baya son zurewa mai kudin gudun wulakanci, sai da Baban Nasiru yayi da kyar kafin ya amince.

wannan shine silar karatun Billo, wanda Baban amininsa ya d'auke nauyin karatunsa.

bayan sun kammala furamari, sukaci makaranta kwana Katsina, duk da taimakon iyayan Nasiru, duo da shima nasa iyayan suna iya nasu k'ok'arin iya k'arfin su.

Bayan sun kamala makaranta ne suk'a rabu da juna sanadin d'an uwan mahaifin Nasiru da ya d'auke shi zuwa Legos, inda acan yayi jami'a,

shi kuma Billo Baba Mamman ya nema masa gurbin karatu jami'an katsina, sun rabu da juna cikin kewa da alhini.


Asma'u itama 'yar KAITA ce, sanda akai bikin yayi d'alibbai sakandiri, Billo ya raka wani abokin sa bikin wanda k'anwarsa ce zata gama makaranta,

anan Allah ya hadashi da Asma'u nan soyayya mai k'arfi ya shiga sakanin billo da Asma'a, basu dauki d'ogon lokaci ba aka yi aurensu,

bayan bikinsu da sati uku ya koma makaranta yaci gaba da karatunsa ,Asma'u ta nuna damuwarta a lokacin da zai koma da kyar ya lalabata ya tafi cike da kaunar matarsa.
****** *******
Bayan shekara da abubuwa da dama Sun faru ciki kuwa harda fara aikin malam Billo, kuma a cikin shekarar Allah ya abarci Asma'u da yaronta mai kama da mahaifinsa sak, ranar suna yaron yaci sunan Ahmad, daga nan haihuwa ta tsaya ma Asma'u haka dai suka cigaba da addu'a suna kulawa da Ahmad,


Ahmad nada shekara hud'u suka bar gidansu na gadu da mahaifarsu zuwa garin Katsina.

ganin aiki yayi wahar samu sai ya cigaba da kasuwancin sa, wanda mahaifin sa da 'yan uwanasa suka bashi jari,

dai dai gwargwadu yana taimakawa iyayansa da 'yan uwanasa,

duk lokacin da zaije KAITA yakan je wajan iyayan Nasiru ya gaishe su da alkhairi iri iri, suyi ta godiya da sanya masa albarka.

Tun rabuwarsu da Nasiru sau biyu kawai suka had'u, zuwansa na farko gida, da kuma zuwan da yayi bikin Billo,

shi dai billon sosai yazo zuwa bikin auren amininsa da wata Maimuna 'yar asalin Kano, wace suke zaune Legos,
Allah bai nufa ba,

har sun samu k'aruwa Nurudeen, da Fatima Hasan da Hussain.

Allah mai amsa addu'ar bayinsa, Ahmad nada shekara goma, dai dai sanda ya gama furamari Asma'u ta sake haihuwar diyarta kyakyawa da ita, ranar suna yarinyar ta ci sunan Bilkisu.


Balkisu kyakyawa ce yarinya mai wayo da shiga rai,

Bilkisu tana da k'awa mai suna Ummu, wace suka had'u amakaranta, daga baya ne ma suka fahimci unguwarsu daya.

halayansu d'aya ,komai nasu daya suna son junansu sosai, kawancan nasu yasa har uwayan nasu suke Zumunci,A unguwar alkali suke Zaune.


Mahmod saurayin bilkisu ne dan asalin dutsinmma ne, suna zaune katsina, mahaifinsa ya rasu tun yana yaro, mahaifiyar sa ce da yan uwansa suka tsaya tsayin daka ganin ya samu ingantacan ilimi, shine auta a gidansu yana da yayyan maza uku mata biyu,

yana da digiri yanzu haka yana aiki a wani kamfani na sarafa takalma nan cikin katsina.
Mahmod yana zaune ne a kofar kura, Abba malam billo baban bilkisu yana kasuwanci a yar katungu yanzu Alhamdulillah yana da rufin asiri.

Kakar Balkisu ta rasu tun Balkisu nashan mama,

shekara uku tsakani Baban Billo yarasu, mutuwar sosai ta tab'asu,

haka suke zumuncin su shida 'yan uwansa, sosai yake kulawa da matar babansa da tilon kanwarsa inna Nafisa da ke aure wani malamin makaranta funtuwa.

*Cigaban labarin*

Wasge gari tana d'aki kwance bayan Mama ta bata maganin zazzab'i,

so take ta cire komai aranta ta daina damuwar ko ta samu salama kamar yanda ya Ahmad ya ruketa zuwan da yayi da safe,

sai dai kash ta kasa, taya zata cire komai taya zata manta Mahamod farat d'aya?

harta fara tunanin wani, abune da ba zai tab'a yuwa ba, son mahamod bada wasa ya shige ta ba,

taya za tayi farin ciki bayan farin cikin nata ana neman a nisanta ta da shi,

haka ta wuni d'aki cikin damuwa da k'unci, Mama tayi lallashi har ta gaji ta zuba mata idanu.

da yamma Ummu ta shigo gidan a tsakar gida ta sami Mama tana wanke wanke,

bayan sun gaisa tace "Mama wanki wanki da kanki, ko bsty batanan"?

cikin murmushi Mama tace "tana nan, 'yar uwar taki ce ba lafiya, shiga tana d'aki"

da sauri ta mik'i tana fad'in "subhanallah mi ya sameta"? tayi tambayar ba tare da ta jira amsar ba ta fad'a d'akin,

"Bestyna mi ya same ki?"
juyo da kanta tayi tana kallon k'awarta ta, sai ga hawaye shar suna ambaliya afuskarta,

akid'imi Ummu ta zauna bakin gadon tana cewa "Balkisu lafiya mi yasame ki haka, kingan ki kuwa? kin fad'a sosai"

cikin kuka tace "Ummu komai ma gani za kiyi dani, tunda Abba ya zab'i nayi bankwana da farin cikina"?

da mamaki Ummu ta zuba mata idanu tana kallonta kafin daga bisani tace
"ban gane ba Balkisu, mi Abban ya maki da zafi haka"?

nan ta shiga bata labarin abunda ke faruwa cikin kuka, ko kafin tagama bata labari Ummu ta fara kuka kamar wacce akaiwa mutuwa,

Mama da take zuba mage cikin miyar su ta dare ta fito kitchen d'in da mamaki ta nufi d'akin Balkisu,

sanda ta d'aga labulen d'akin ta tarar dasu rungumi da juna suna kuka ba mai lallashin wani,

kanta ta gyad'a ba abun mamaki bane dan tasan amintarsu farin ciki da bakin ciki duk suna rabawa juna ne,

"to ke Ummu har ke zama za kiyi kiyi kukan?

to wa zai lallashi wani tsakanin ku?
Ina jin dadin kinzo ki taushe zaciyarta, sai kuma ki biye mata ku taru kunayi"

"haba Mama dan Allah miyasa Abba zaiyi haka?
dan Allah Mama kiyiwa Abba magana ya janye zancin nan,

wallahi *AUREN DOLE ILLAR* ne da shi ko da baka da wanda kake so, bare kuma tana da wanda take so"

shigowa ciki tayi ta zauna gefen su, kafin daga bisani tace "hakane Ummu, amma gaskiyar magana,

Abbanku ba zai tab'a sauyawa, magana d'aya yake yi ba zai canza ba, dan haka hak'uri dai shi za ayi,

ki kuma lallashi kawarki, ku sani bawa bai isa ya sauya k'addarar sa ba"

daga haka ta tashi tabar d'akin, "uhm"!

ajiyar zuciya mai k'arfi Ummu tayi kafin ta sake duban Balkisu tace

"Bestyna amatsayina na aminiyarki shawarar da zan baki shine kiyiwa mahaifin ki biyayya,

tunda har kikaga Mama tace haka to hak'urin shi ne yafi,

Insha Allah silar biyayyan sai kiga Allah ya cire maki son Mahamod d'in ya sa maki son zab'in Abba,

dama ba komai ne kake so yake zamuwa alkhairi agare ka ba, sai kiga abunda baka so shine alkhairin"

cikin wani kallo da taiwa Ummu tace "hum Ummu kenan, banyi zaton kema za ki kasa fahimta ta ba,

shin so wasan yara ne da zan daina shi farat d'aya, bare ma ba irin Mahamod ne ake so adaina ba wallahi"

"na fahimci ki mana Balkisu, amma abunda nake so ki sani bijirewa iyayi ba abune mai kyau ko amfani arayuwa ba"

"hakane nima ba zan bijirewa Abba ba, zan masa biyayya, amma tabbas wannan auren shine yankewar farin cikina, shine yankewar numfashi na"!

a tsoraci Ummu tace "mi kike nufi Balkisu, ba dai kashi kanki za kiyi ba ko"?

"Hum sai kace wace bata da ilimi, ba zan kashe kaina ba Ummu, amma tabbas an d'auko hanyar tafiya ya, dan an yake man rayuwata"

shiru Ummu tayi, sai sai kam zuciyarta ciki take da tsoron kalaman Balkisu, har aka kusan kiran magarib tana gidan sai da Mama tace "Ummu tashi kije gida kar anemiki ga magarib ta sawu kai"

"to Mama" ta fad'a cikin sanyin jiki tace "zan tafi dan Allah bestyna kiyi hak'uri kiyi ta addu'a da karatun k'ur'ani insha Allah

Allah zai kawu maki mafita, nasanki dama ba baya ba wajan yin ibada"

"Nagode ki gaida su Inna"
"Zasu ji"
daganan ta fita.

da dare ma sai da Mama tayi da gaski taci abinci ko shi ganin b'acin ran Mama ne yasa ta d'an tsatssakura,

ranar kwana tayi nafila sa da karatun k'ur'ani tare da salatin Annabi.

Mahamod da zazzab'i sosai ya wuni Hajiya tayi tayi suje asibiti yak'i,

cikin damuwa tace "auta wai ina aka tab'a zama da ciwo ba magani sabida Allah"

d'ura kansa yayi kan k'afafunta yana hawaye yace "Hajiyanmu asibiti basu da maganin ciwona,

Balkisu fa zan rasa wani na ake shirin aura mata, taya lafiya zata zauna a jikina?

Hajiyanmu itafa rayuwata ce, idan na rasata tamkar na rasa rayuwata ne"

shafa kansa Hajiya tayi kafin daga bisani tace "miyasa ba za kayi tawakkali ba uhm Mahamod,

idan matarka ce kana nan zaka ga Allah yayi ikonsa, idan kuma ba matarka bace damuwa bai isa ya baka ba,

ka tashi ko magani kasha dan Allah sai kaci abinci, karku ma kace Aa indai ba kana so ka ganni cikin damuwa ba"

ba yanda ya iya haka ya tashi ya bi umurnin ta, ba dan ransa ya so ba.

zuwa azahar zazzabin ya sauka sai dai rashin k'arfin jiki, da kuma damuwar da ki zuciyarsa,

ya kira number Mama ba adadi amma a rufi ake cewa, so yake yaji muryarta, ya sani tana cikin damuwa, tuna hakan yana tab'a masa zuciya.


*Bayan sati d'aya*

dukan masoyan har maguya bayansu suna cikin damuwa da alhini, daga Mahamod har Balkisu suna jin wannan kwanakkin tamkar shekaru,

basuga juna ba basu ji muryar juna ba, ba k'aramin jigita sukayi ba,

Mahamod yasha zuwa unguwar dan ya ganta sai dai ko mai kama da ita baya gani,

yana tsoron yaje gida su had'u da Abba ya janyo wa shakelensa duka gun Abba, dan bai manta marin da akai mata agabansa ba,

har wajan Ummu yaje tana fitowa suka gaisa

kafin daga bisani yace "Ummu dan Allah ki taimaka man naga shalele na kasa samunta ko ta waya,

Na kasa juri tashinta dan Allah ki taimake ni na ganta"

kallinsa take cike tausayi ganin yanda cikin kwana bakwai yayi wannan uban raman, kallo d'aya za ka masa ka fahimci yana cikin damuwa wacce sam bata b'oyuwa,

k'walla suka ciko mata idanu cikin k'ok'arin mayar da k'wallan tace "kayi hak'uri Mahamod, Abba ya hana Balkisu fita har zuwa islamiya ya hanata, kuma ya karb'e wayar Mama"

dafa kansa yayi da ya Sara masa tare da jingina jikinsa da bungub surun,

cikin damuwa yace "nagode Ummu yanzu ba yanda za ayi na ganta"

cikin gyad'a kai tace "gaskiya babu Mahamod kayi hak'uri ku rungumi wannan k'addarar hannu biyu, zaiyu rabuwar taku ce alkhairi"

"Uhm"? wani irin gwarron numfashi yaja kafin daga bisani yace "shikenan zan tafi nagode sosai, amma dan Allah ki dinga lallashin ta, ta daina damuwa dan Allah"

"Insha Allah zanyi Mahamod"

daga nan sukai sallama.


Ranar juma'a da dare bayan Abba ya gama cin abinci yana kallon TV tashar arewa25,

bayan angama shirin da yake kallo ya kalli Mama da take had'a masa hulunan da yace a had'a da safe zai kai wanki yace

"Asma'u ki fad'awa Balkisu gobe insha Allah tana da bak'o Nurudeen zai zo,

dan munyi magana da Alhji Nasiru, wata biyu masu zuwa za a yi bikin, duk da dai munyi shawara aje can KAITA wajan su Yaya a nemi auren,

amma dai insha Allah ba zai wuce wata biyu ba, sai ki fara shiri,

zai zo su fahimci juna kafin lokacin bikin"

ajiye hulan hannunta tayi tana kallon Abba cikin fad'uwar gaba, wato dai malam ba zai bar maganar ba,

"To" kawai tace ba tare da ta k'arasa cewa komai ba ta cigaba da abunda take,

cikin jin haushi yace "wato na gani Asma'u kina goyon bayan Balkisu ko,

wato ba za ki tayani fitar kunyar aminina ba, bayan 'yarki za ki bi,

to wallahi daga ke har ita Baku isa ba, kuma zan sab'a maki matuk'a akan maganar auren nan"!


"Malam sabida Allah yanzu mi nace"?

"au mi ma kikace kike tambayata ko? Na fad'a maki magana mai muhimmaci akan auren 'yarmu kice to, ba komai bane kenan"?!

"Allah ya baka hak'uri, naga dai sak'o ka bani na fad'a mata shiyasa nace to"

"naji idan na baki sak'o maganar auren fa"?

"Allah ya sanya alkhairi"

"Amin" ya fad'a yana cin magani.



*Karku manta kuna tare da Aisha A Yabo Fulani ta Annabi S.A.W*
[9/28, 8:22 AM] Aisha A Yabo: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*ILLAR AUREN DOLE*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*Daga alkalamin Aisha A Yabo Fulani*

*Β© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUMπŸ„*
β˜†We the best β˜†

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* realhausafulaniwriters@gmail.com

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1


*MANUFARMU ANNABINMU*

*YA LUDUFIN HALITTA KA LAD'D'AFA MANA ZAFIN QAUNARKA YA ZAME MANA YAWAN GANAWA DAKAI*

*YA SANADIN RAYUWA KA WANZAR DA GANIN KA ACIKIN RAYUWARMU*

*YA MAI TABBATACCEN MULKI A DUNIYA DA LAHIRA KA TABBATAR DAMU CIKIN MASOYANKA NA HAQIQA*

*DAN HAQIQANIN NANA FAD'IMA*

*YA ADON GIDAN ANNABTA ZINARIYAR ANNNABI KI DUBI ROQON BAYINKU*


RANDAWA MEDIA CONCEPT
*Kunaso ahadamaku ring tone da sunayenku?
*Kunaso ayimaku sound track da sunan masoyanku ko kuma lakanin sunayenku?
*Kunaso kuji wayarku tana kiran sunayenku alokacin da akayi kiranku awayoyinku na salula?

Ba anan kad'ai muka tsaya ba har wak'ok'in bikin aure bikin suna, ko wak'ar birthday.

Cikin aminci da karamci zaku samu wanga farinciki da farashi mai sauki, zaku iya samunmu ashafinmu na wasapp dandalin sada zumunta ta wannan lamba 08032176520. Don hudda ta kasuwanci kamar kyautane farashin aikinmu, tsada bata nuna inganci aiki akamfaninmu. Kada Ku manta, Namu dabanne! Domin kuwa aciki zamuyi yanda za'agane cewa lallai kaidinne ko kuma kedindaice akenufi. Ku gwada aiki da sabuwar fasaharmu zakuji dadin tsarin. Mungode mungode mungode.
Isah Randawa ke cewa muzama lafiya da alheri.


*Ina bawa makaranta hak'uri da kuskurin da nayi a pej 13 to 14, 16 to 17 ne, FNS kuna raina*


*18 to 19*

Washe gari, sosai suka gyaran gidan da girki girki kala kala kamar yanda Abba yayi umurni,

dan tare da abokansa zai zo, duk abunda ake Balkisu bata da masaniyar zuwan bak'onta,

ba koma ta tambayi dalilin girki girkin ba, dan ba wannan ne agabanta ba, damuwarta ta wuce wannan,

suna kammalawa tayi wanka, bata yi kwalliya ba dugowar riga material kawai tasa, hakan bai hana kyanta fitowa ba, sallah azahar tayi Tare da yin askar, addu'a take akan Allah ya kawu mata mafita, idanunta suna zubar hawaye, sosai take jin son mahamod da kewarsa.


Mama ta kira number Yaya Ahmad tace tana son ganinsa, yace mata yana hanyar zuwa gidan,

sannan ta kira maman Ummu tace ta turo mata Ummu.


*Legos*

gajiye yau ya dawo wajan aiki yana rurrufi motarsa ya nufi sashinsa, wanka yayi sannan ya fito zuwa sashin iyayansa dan yaci abinci yunwa yake ji sosai,

yana zuwa ya tarar da Hasan ne kawai afalo, cikin ladabi yace "Yaya Deen sannu da zuwa"

cikin miskilanci yace "yawwa ina Husain"?

"yana d'aki"
"Momy fa"?
tana kitchen"
"Ok" kawai yace tare da nufar kitchen d'in,

yana zuwa suka had'u da ita k'ofar kitchen tana fitowa,

murmushi tayi

Please Login or Register in order to submit comment