Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1


*MANUFARMU ANNABINMU*

*IDAN BAN NUNA SOYAYYATA GA Y'AR ANNABI BA GAWA ZAN NUNA SOYAYYATA*

*NASAN DAI CEWA ALLAH BAI HALICCI WANI ABUBA DA YAFI NA ANNABI BA*

*SAYYADA KO SAI IMANI,IMANINMA BA NA KOWA BA*


*ITACE TSOKAR SHUGABA*
*ITACE ZUCIYAR SHUGABA*
*ITACE RUHIN SHUGABA*

*NA TABBATA BA ILIMIN SANIN WANI ABU NA SHUGABA ANAN DUNIYA*

*ALLAH INA ROQONKA KA WANZAR DA GIRMAMAWA GA MAFI DARAJAR DARAJA SAYYIDATUN-NISA'IL'ALAMINA*


*WALLAHI QAUNAR FAD'IMA ITACE RAYUWARMU*


*9 to 10*


Da safe bayan fitar Abba Mama takira yaya Ahmad,

Alokacin yana shirin zai fita yaga kiran Maman, sai da ta tsinki sannan yabi kiran,

ta d'auki kiran bakinta d'auki da sallama,
cikin ladabi ya amsa da "Amin alaiki Salam, Mama Ina kwana kun tashi lafiya"?
"Lafiya kalau, ya yaran da mamansu"?

"Lafiya suki, dama anjima zan shigo na kawusu sun matsa su zo"

"ba laifi, Allah ya nuna mana ya kawu Ku lafiya"

"Amin Mama, Ina auta?"

"tana d'aki lafiya k'alau taki, dama Ina so muyi magana kanta ne, dan babanku ya zo man da wata magana, da nake tunanin da damuwa aciki, amma dai sai kazo sai muyi maganar"

"cikin damuwa yace Mama gani nan zuwa yanzu"

"Aa yayanta ba wajan aiki zakaje ba? Ba komai ka bari kawai sai ka dawo"
"Mama ba komai zanzo ko naje ba zan iya samun natsuwar aikin ba, gara kawai nazo naji"

sanin irin shakuwar da ke tsakanin su, da irin son da yakewa Kanwar tasa ne yasa tace

"to sai ka zo d'in" daga haka sukayi sallama, tana jin farin ciki sosai yanda yaran nata suke kaunar junansu,

fatan ta su dure har dukan zuri'ar su.


Balkisu tana kammala ayukanta, ta d'auki wayar Mama zata shige d'aki Mama da take fitowa ban d'aki tana ajiye bota tace

"wai mi ya sa meki na danni dannin waya?, ke da ada ba ruwanki da daukar wayar, amma yanzu in kin dauka ko mutsinki bana ji"

Murmushi tayi kafin tace "bakomai Mama gem zanyi"

"k'arya ko auta?, ki dai kula sosai auta, ki kuma san irin kalan firan da kike da shi, saboda mutuncin ki"

"Insha Allah Mama zan kula, ba zan aikita abunda ya sabawa Ubangiji ba"

"yawwa auta Allah yayi maku albarka"

"Amin ta fad'a tana mai shige wa d'aki"

tana zuwa ta kwanta kan katifa tana mai dannawa Mahamod Kira,

kamar jira yake yayi pikeng "shalele yanzu muka isu, Ina ciro wayar aljihu da niyar kiran ki sai ga kiran ki"

cikin farin ciki tace "da fatan kun isa lafiya"

"Lafiya kalau shalele, nagodi sosai da kulawa"

"haba bakomai Nurul kalb'i,"

basu jima suna fira ba sukai sallama akan sai zai taso ko zasuyi waya, dan akwai aiki agabansa.


da sallama ya shiga gidan nasu, daga d'aki Mama ta amsa masa tana cewa "shigo Ina ciki"

"tube takalminsa yayi tare da shigewa falon mahaifiyar tasu,


sai da suka sake gaisawa kafin daga bisani Mama ta fara yi masa maganar,

"kaga auta ta gama makaranta, to yaron da ke zuwa wajanta ne ya nemi da ya turo iyayansa anema masa aurenta,

to najewa babanku da maganar ya watsar yace Bai san zance ba"

cikin farin ciki ya gyara zamansa yana cewa "yawwa Mama kinga ko baba ya fahimci ilimi yana da dad'i da amfani awajan mace,

shiyasa tun farko naso ki fahimta, amma Mama kika k'i, hakan da yayi shine dai dai"

cikin hararsa tace "to aku sarkin surutu ai sai ka bari na k'arasa zancin nawa kafin kayi naka sharhin ko"?

sosai Kai yayi yana cewa "yi hakuri Mama ina jinki"

nan ta masa bayanin duk yanda sukayi da Abba Daren jiya, tun kan ta k'arasa gumi ya wanke masa fuska cikin tashin hankali yace

"Mama ko ni da nake namiji ai ba amun irin wannan auren had'in ba ballatana mace,

miyasa Abba zai amimce ba tare da yardar auta ba, ai ko mu muna da hakk'in mu sani,

yau she Abban zai dawo"?

"yace dai ba zai jima ba, nan gidan Malam iliya yaje wajan jana'izar jikansa da ya rasu"

"Allah sarki Allah ya jikan musulmi, bari na jira shi tunda ba nisa yayi ba, Ina ita autan"?

"tana d'akinta, nasan ba zai wuce tana waya da Mahamod d'in ba"


jinjina Kai yayi tare da kwala mata Kira,

jin muryar yayanta yasa tayi saurin ajiye wayar da tun baysn gama wayar su suka ci gaba da magana ta tx,

dama haka suke idan Bai zo ba waya, idan kuma yana wajan aiki sai suyi ta musayar kalamai ta hanyar yuwa juna tx, sai da ta tura masa Yaya Ahmad yazo karyaji ta shiru, sannan ta fito,

suna ta firarsu cikin shak'uwa yana tambayar ta labarin Mahmod d'in, tun tana jin. kunya har ta sake tana zuba masa zance,

ad'an lokacin ya fahimci tana matuk'ar son saurayin nata, sosai yaji tausayin su, lallai ya zama dole yasan duk yanda yayi Abba ya barta da zab'insa.


sai wajan 11 Abba ya shigo gida, bayan su Auta sun masa sannu da zuwa, Yaya Ahmad ya gaishe shi, ya amsa da fara'a yana tambayar yara,

kafin daga bisani yace "ya naganka gida irin wannan lokacin, ko ba aiki ne"?

yayi maganar yana mai zubawa yaron nasa idanu,

cikin ladabi yace "daman Abba Ina jiran ka dawo ne"

"to madalla lafiya dai ko"?
"eh lafiya k'alau Abba, ke Auta tashi kije" yayi maganar yana mayar da kallonsa gareta,

"to" ta fad'a tana mai mik'ewa tsaye, haka ta bar d'akin cikin sanyin jiki, hakanan take jin fad'uwar gaba,


k'ara tank'washe k'afa yayi cikin ladabi yace "Abba dama akan maganar Auta ne,

sai nake ga hakan bai dace ba, saboda yanzu an daina irin wannan auren, kuma Abba kaga tana da wanda take so, kar a tilasta mata auren wanda bata so, saboda *AUREN DOLE YANA DA MATUK'AR ILLA*

dan Allah Abba ka fahimci ni"

wani kallo ya watsar masu daga shi har Maman kafin daga bisani yace

"to sannu babana, ai dole na fahimci ka tunda Kai ka haifini, shiyasa ma aka Kawo k'arana wajanka"

cikin sauri Mama tace "Aa Malam ni ba k'ara na kawu masa ba, magana ce dai mukayi, amma Allah ya baka hak'uri"

cikin damuwa yace "kayi hak'uri Abba, ba hakan muke nufi ba, amma abb.....


Abba ne ya katse shi ta hanyar cewa "komai zaku fad'a daga Kai har Maman taku ba d'auka zanyi ba,

dan ni nake iko da Ku ba ko ne kuke iko da ni ba, magana ce nayi balkisu bata da mijin da ya wuce nurudeen,

koma babu wanda ya isa ya can za man ra'ayi"!

"Ke Balkisu Balkisu Balkisu"!

ya dinga kwala mata kira da k'arfi wanda yasata fitowa d'akinta a tsorace dan bata tab'a jin irin wannan kiran daga bakin mahaifin nata ba,

cikin tsoro ta k'arasa gaban Abba musamman ya nayin fuskan Maman ta da yayanta da tayi,

cikin rawar murya tace "gani Abba"

cikin gyaran murya ya fara magana "Balkisu waye ni awajan ki"?

cikin mamaki ta kalleshi kafin tace "Abba mahaifina ne Kai"

"Yawwa shin na isa da ke? na isa na saki ko na hanaki? na isa nayi maki umurni kiyi"?

zuwa lokacin ta gama tsorata nan ta shiga canki canki mi Abba ke so ta masa sai dai ta kasa ganu ko miye,

ta shiga duban su Mama da suke mata kallo idanunsu ciki da zallar tausayin ta,

saki mayar da duban ta tayi wajan Abba da ya zuba mata idanu yana jiran amsarta,

cikin sanyin jiki " tace "Abba duk ka isa har ka zarce"

cikin murmushi yace "madallah naji dad'i sosai Auta Allah yayi maki albarka,

auta kinsan alhaji Nasir aminina"
cikin tsananin fad'uwar gaba tace

eh Ina dai yawan jin labarin sa abakin ka, amma ban tab'a ganinsa ba"

"gaskiya ne, to naje KAITA mun had'u da shi har munyi shawaran had'aku aure tare da d'ansa Nurudeen, dan haka ki bawa shi saurayin naki hak'uri ki fada masa an maki miji"

tamkar saukar aradu haka taji zancin Abba, firgice ta matsa wajan Abba tana wani irin kuka mai ciki da tashin hankali tace

"dan Allah Abba kamun rai wallahi ban son sa ni Mahamod nake so idan aka rabamu mutuwa zanyi wallahi"

fincika k'afafunsa yayi ya mik'e tsaye yana fad'in "Balkisu wannan umurni ne ba shawara ba, dan haka garama ki sawa zuciyarki salama"

"Abba ba zan iya rayuwa ba Mahamod mutuwa zanyi Abba dan Allah karka yanke mun farin cikina Abba dan Annabi"!


tayi maganar cikin fizgar numfashi,

cikin tsawa yace "Balkisu ki mutu sai mi kanki farau ne, wallahi ko gawarki ne sai ankai gidan, ko bayan raina ban yafe ba idan aka fasa wannan auren,

idan yaso idan an kaiki ki had'iye zuciya ki mutu"!

ko saurarin ban hak'urin da Mama ke bashi baiyi ba ya fice gidan,

Yaya Ahmad ne ya janyota jikinsa yana lallashi "kiyi hak'uri auta muyi addu'a Allah ya zab'a mana mafi alkhairi kinki"?

cikin tashin hankali ta rik'i shi tana cewa "yaya Ahmad *AUREN DOLE* miye alkhairin sa aciki?

bayan tarin matsaloli, dan Allah ku taimake ni kar Abba ya yanki man farin ciki wallahi mutuwa zanyi idan narasa Mahamod"

Mama ta shiga lallashin ta amma kamar tana k'ara zugata mik'ewa tayi tsaye kamar mahaukaciya sabon kamu ta d'aga labulen zata fita kawai sai gani sukayi ta yanki jiki ta fad'i,

cikin k'araje su Mama suka yo kanta suna kiran sunan ta, Ina rai yay.......



*Karku manta kuna tare da Aisha A Yabo Fulani ta Annabi S.A.W*


[9/28, 8:22 AM] Aisha A Yabo: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*ILLAR AUREN DOLE*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


*Tare da alk'alamin Aisha A Yabo Fulani*


*Β© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUMπŸ„*
β˜†We the best β˜†

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* realhausafulaniwriters@gmail.com

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1


*MANUFARMU ANNABINMU*


*WANDA YA CIKA CIF KAFIN YA BAYYANA DAYA NE SHINE ABBAN BATULA*

*AMINCIN ALLAH YA TABBATA GARE DAIDAI CIKARKA YA NAJAMUL'HUDA*


RANDAWA MEDIA CONCEPT
*Kunaso ahadamaku ring tone da sunayenku?
*Kunaso ayimaku sound track da sunan masoyanku ko kuma lakanin sunayenku?
*Kunaso kuji wayarku tana kiran sunayenku alokacin da ayi kiranku awayoyinku na salula?

ba anan kad'ai muka tsaya ba, muna yin wak'ok'in bikin aure ko suna har wak'ar bthdy,


Cikin aminci da karamci zaku samu wanga farinciki da farashi mai sauki, zaku iya samunmu ashafinmu na wasapp dandalin sada zumunta ta wannan lamba 08032176520. Don hudda ta kasuwanci kamar kyautane farashin aikinmu, tsada bata nuna inganci aiki akamfaninmu. Kada Ku manta, Namu dabanne! Domin kuwa aciki zamuyi yanda za'agane cewa lallai kaidinne ko kuma kedindaice akenufi. Ku gwada aiki da sabuwar fasaharmu zakuji dadin tsarin. Mungode mungode mungode.
Isah Randawa ke cewa muzama lafiya da alheri.

*14 to 15*

Gani yake d'an acab'an baya sauri, ya k'agara ya ganshi gabanta,

yana zuwa ya sallami mai acab'an, ya ciro wayarsa da ke aljihun wandunsa ya kira ta,

tana d'agawa yace "shalele ki fito ina waje ina jiranki"

cikin shak'kk'iya murya da taci kuka tace "to"

hijab d'inta ta d'auko tana sawa ta nufi d'akin Mama,

zaune ta tarar da ita tana lazimi, "Mama Mahamod ne yazo"

d'ago kanta tayi tana kallon 'yarta cikin tausayi tace "to auta kije, amma karki dad'i dan kar abbanku ya dawo ya tarar da Ku,

ki kuma fad'a masa gaskiyar abunda ke faruwa, kuyi hak'uri ba komai ne kake so ya zama alkhairi ba"

gyad'a kai kawai tayi, haka ta fita tana sa bayan hannunta tana share hawayen da ke ta zarya afuskarta babu kakkautawa kamar lalataccin fanfu,

yana hango fitowarta cikin sauri ya k'arasa cikin surun gidan,

gabanta ya tsaya da d'an tazara kad'an, sanda idanunsa suka sauka kan fuskarta sosai yaji hankalinsa ya k'ara tashi,

cikin damuwa yace "shalele wani irin ciwo kikayi wuni d'aya kin take sosai kin danki kuwa"

kallonsa tayi cikin wani irin sonsa da take jin yana k'ara fizgarta,

duniyar da kai tayi ta kasa cewa da shi kumai, aranta tunani take ta inda zata fara,

gyara tsayuwarsa yayi kafin yace "dan Allah shalele ki fad'aman damuwarki, wallahi bakiji ya nake ji a zuciyata ba"

"Mahamod ina sonka, kaini namiji na farko da na fara so a rayuwata, har abada ba zan so wani bayan ka ba,

banda burin da ya wuce rayuwa a k'ark'ashin inuwarka ba, k'ark'ashin ikon ka, ka zamo Baban 'ya'yana"

shiru tayi ta kasa ci gaba da maganar da take sakamakon kukan da yazo mata,

cikin tashin hankali da tsoron da ya shige shi na rashin sanin dalilin kukan nata,

yace "na sani shalele nima hakanne, ke ce macen da na fara so daga ke babu wace zata samu muhalli a zuciyata,


ke ce kad'ai macen da zan iya rayuwar aure da ita cikin farin ciki, ko a aljanna kece nake fatan ki zamo shuganar matana na aljanna,

fad'aman damuwarki ko Abba ne yace wani abu akan maganata"?

yayi tambayar cikin zullumin amsar da zaiji,

cikin kad'a kai tace "eh Mahamod kayi hak'uri Abba ne naje masa da zancin ka, bai amince ba,

ba dan baya sonka ba sai dan wai yayiwa wani amininsa alk'awarin bawa d'ansa aurena,

Mahamod nayi iyakar yina Abba ya fahimci rabamu tamkar rabani da rayuwata ne"

ta k'arasa zancen cikin durk'shewa awajan tana shisshik'an kuka,

shima durk'shewa yayi agabanta cikin wani irin yanayi mai ciki da tashin hankali,

zuciyarsa na bugawa tamkar zata fasu kirjinsa ta fito, sun jima cikin yanayi na shiru kafin daga bisani mahamod ya katsi shirun da fad'in

"Balkisu dan Allah karki bari arabamu, wallahi ba zan iya rayuwar farin ciki Idan ba ke ba,

rayuwata ce ke, na riga na mace akan sonki Balkisu ba zan iya jure rashinki a tare dani ba Balkisu"

"ba laifina bane Mahamod, Abba ne, Abba ne Mahamod wallahi nima idan na rasaka mutuwa zanyi"!

lumshi idanunsa yayi cikin wani irin yanayi gaba d'aya jikinsa cira yake kamar namijin zaki,

idanunsa an sauya kala daga farare zuwa ja, jikinsa sai gumi yake tsifuwa,

yayin da ta cigaba da rera masa kuka da yake jin zafinsa kamar saukar garwashe a zuciyarsa,

zaiyi magana suka jiyo muryar Abba cikin tsawa yace

"ke auta mi kikeyi anan"?
cikin tsoro da kid'emiwa ta mik'e tsaye tana kirma tama kasa cewa komai dan tsoro,

saboda tun tashinta bata tab'a ganin bacin ran abba irin yanzu ba,

bai tab'a yi mata tsawa ba tun wayunta,. "ba da ke naki ba, ko ba kyajina ne, mi kike anan"?

cikin kirma da rawan murya tace "dama dama ab..b...a M...h..a..M

wani irin mari ya kaimata wanda ya hanata k'arasa maganar,

cikin kid'ima Mahamod da ke shirin yi masa magana ya mik'i yana dafi da fuskarsa da yake jin kamar shi akawa,

Abba ya d'aga hannu zai k'ara kaimata marin mahamod yayi saurin shan gabansa tare da druk'usawa awajan

ya rik'i k'afan Abba yana kuka kamar k'aramin yaro yace "dan Allah Abba kayi hak'uri wallahi ba laifinta bane,

nini da laifi kaman komai ka kyaleta dan Allah Abba"

Abba yayi sururu yana kallonsa cikin mamaki yace

"oh wato kai kace taman rashin kunya ta bijirewa maganata ko"?

da sauri yace "Aa Abba, kayi hak'uri dan Allah, ba bujirewa tayi ba, dan Allah kayi hak'uri"

"to naji tashi kabar gidanan, Balkisu dai 'yata ce, na mata miji, ba zan sauya ba, kuma kai baka isa kazo ka hure mata kunni ba,

karka kuskura na koma ganin k'afarka gidanan, kana jina ko"?!


"dan Allah ka man rai karka rabamu muna son junanmu, wallahi ba da yaudara nazo gun Balkisu ba"

fizge k'afansa yayi tare da fizgo hannun Balkisu da take durk'she awajan tana kuka,

sukai cikin gida suka bar Mahamod a zukunni.

tun a suron yake kwalawa Mama kira "Asma'u, Asma'u, kina ina fito fito naji da yawun wa kika barta ta fita, wato kun mayar dani wanda ban da mutunci da kima ko"?

cikin fad'uwar gaba da tsoro ta fito dan ko shakka ba tayi Abba ya tarar da auta da Mahmod,

aikuwa hasashinta ya zama gaskiya tayi turus tana kallonsa,

cikin dakeya tace "sannu da zuwa malam lafiya naji kana kirana haka"

cikin kallon kin raina man hankali yace "ah kya fad'i haka, wato Asma'u ban isa nayi magana agidanan abi ba ko?

kinsan na raba yarinyar nan da wancan yaron na mata miji, shini zaki barta ta fita wajansa"


"kayi hak'uri Malam ba hakan bane, ta fad'aman yazo, nace taje ta fad'amasa abunda ke faruwa, amma ba dan na tozarta maganar ka ba"

"naji koma miye daga yau ban yarda ta sake zuwa wajan sa ba, naga so kuke ku mayar dani k'aramin mutum zan kira Nasir, ayi maganar auren cikin kwanakkinan, tun kan ku janyo man abunda zai sani jin kunya agun aminina"

yana gama fad'an hakan ya sa kai d'akin sa,

Mama ta janyo Balkisu d'akinta tana lallashin ta tare da yi mata nasiha,

"auta kuka ba shine zai maki maganin damuwarki ba, ki ci gaba da addu'a da rukun ubangiji akan yayi maki zab'i na alkhairi,

kamar yanda nake fad'amaki ba komai ni kake so ya ke zame maka alkhairi ba,

da yawa abun da ba ka so sai kiga shine alkhairi agare ki, kuma cikin ikon Allah sai kiga kina son sa"

da sauri Balkisu ta d'ago kanta tana kallon Mama tace "Mama so fa? hum Mama har abada ba zan so shi ba wallahi, so d'aya tak mahamod nakewa,

zanyiwa Abba biyayya ne kawai dan ban isa na kaucewa umurnin sa ba, amma nasan auren nan ajalina ne"

a tsoraci Mama ta kalleta tana cewa "subhanallah, auta kar na koma jin hakan daga bakin ki kinji?

naji dad'i da har zakiwa mahaifin ki biyayya, insha Allah zaki ci riban biyayyan da kikayi,

ki saki ranki ki daina yawan damuwa auta, kuka ko damuwa ba za su sauya maki k'addarar ki ba,

wani bai isa ya aure matar wani ba, idan har mijinki ne Nurudeen babu makawa sai anyi,

idan Allah bai rubutu aurenki da Mahamod ko duk duniyar nan za su taru su so auren wallahi ba za ayi ba,

dan haka ki sawa ranki komai sai Allah ya nufa akeyin sa, sai kiga zuciyarki ta samu salama"

sosai ta mata nasiha kafin ta rakata d'akinta ta kwanta,

sannan ta fito takaiwa Abba abinci, sai da taga ya gama yasha ruwa sannan ta dube shi cikin kwantar da murya tace

"Malam miyasa ba zaka hak'ura da maganar nan ba?

tunda tana da wanda take so, nasan Nasir zai fahimci ka"

cikin d'aure fuskar da fad'a yace "Asma'u ina k'ara fad'a maki ki fitar da kanki acikin maganar aurenan,

idan har ba zaki goye bayana ba, to karki ce zaki kawu man wani salon,

kuma wallahi akan maganar aurenan zan maki abunda baki tab'a zato ba,

yarinya 'yata ce nayi hukunci ba wanda ya isa yasa na sauya, idan kuma za kusa ta bujire man to bisimillah"

cikin wani yanayi da ba zaka tab'a fahimtar komiye ba, tace "Allah ya huci zuciyarka,

dama naga da azo ayi abunda za adawo ana da nasani har ya kai ga b'ata zumuncin da ake k'ok'arin k'ara k'ullawa, gara tun farko ba ayi ba,

amma tunda kana ganin bayanta nake bi insha Allah ba zan sake cewa komai ba, amma ka tuna ko mu ba auren had'i aka mana ba,

kai ka ganni kana so, sai da na amince kafin ka turo magabatan ka gidanmu, har muka kawu wannan matsayin,

karka d'aukaka farin cikin amininka fiye da na 'yarka, kayi tunani sosai"

daga haka bata
sake cewa komai ba, tunda ta kula akan auren komai ma zaiyi, gara ta zuba ido tabi 'yarta da addu'a, gudun kar suyi abun kunya agaban 'ya'yansu,

Komai bai ce da ita ba, ya cigaba da kallon TV, aransa yana k'wafa.


haka yaja k'afafunsa cikin wani irin yanayi ya samu acab'a ya hau zuwa unguwar su,

hajiyansu da take zaune zugum tana jin damuwar jinsa shiru, yayansa yace

"haba Hajiyanmu Mahmod fa ba yaro ne k'arami ba da zaki damu dan ya jima bai dawo ba"

kallonsa tayi cikin damuwa tace "haba K'asim ka fa san mahamod duk tsanani baya wuci goma baya gida indai har yana gari,

amma sha d'aya fa yanzu, duk da ya fad'aman inda zaije amma ai ba yau ya saba zuwa wajan ta ba, bai tab'a kaiwa haka ba,

amma kace karna damu"

cikin sanyin jiki yace "gaskiya ne Hajiyanmu, to Allah yasa dai lafiya"

kafin tayi magana suka jiyo sallamarsa cikin dariya K'asim yace "to Hajiyanmu hankalin ki ya kwanta ga auta..

maganarsa ce ta mak'ali ganin yanayin da ya shigo gidan kamar d'an maye,

tabbas da ba dan yasan waye k'anin nasa ba, da sai yace abugi yaki,

"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, Mahamod lafiyan ka kuwa"?

Hajiya tayi maganar tana mai mik'ewa tsaye ta taro shi,

fad'awa tayi jikinta yana fitar da shed'a sama sama kamar wanda yayi gudun fanfalak'i,

K'asim ya rik'o hannunsa yana tambayar sa abun da ya same shi,

cikin wani irin yanayi yace "Hajiyanmu zuciyata zuciyata fashewa za tayi dafa kiji yanda take yi"

ya fad'a yana mai d'aura hannunta akan kirjinsa kan saitin zuciyarsa,

a tsoraci ta janye hannunta, tana cewa "subhanallah, mi yake faruwa auta, mi ya sami zuciyar taka da bugun nata ya wuci k'a'ida"?!

cikin runtsi idanu ciki da radad'i yace "Abban Balkisu yace karna koma zuwan masa gida yawa Balkisu miji"

ya k'arasa maganar cikin sark'ewar murya,

Salati suka shigayi kafin daga bisani Hajiya tace "mi yayi zafi haka da zai datsi soyayyar ku?

ko yayi binciki ne yaga baka cancanta auren 'yarsa bane"?

"Aa ko d'aya wai d'an amininsa ne, kuma Allah Hajiyanmu Balkisu bata sonsa, ki taimake ni karna rasa ta"

sai a lokacin K'asim ya nisa kafin yace "hak'uri dai za kuyi tunda har auren na gida ne sai wani ikon Allah idan zai janye,

kayi hak'uri kacire ta kawai aranka, matar mutum k'abarinsa, matuk'ar matakar ce babu wanda ya isa ya hana tabbatuwar hakan,

koda kuwa duk duniyar nan zasu taru suna k'inka da Balkisu, dan haka damuwa ba mafita bace,

kayi addu'a da neman alkhairi kaji autan Hajiya"?

Hajiya ta d'ura da cewa "sosai kuwa auta, wani baya auren matar wani, idan matarka ce zaka aure ta, idan ba matarka bace babu wanda ya isa ya baka auren ta, komai nufi ne na Allah, muyi addu'a neman alkhairi acikin al'amarin"

sosai suka shiga lallashin sa da nasiha, saurarun su kawai yake, dan basu san ya yake ji ba ne,

abincinsa Hajiya ta bashi, sai dai ya kasa ci ya tasa abincin gaba yana kallo, Hajiya ta matsa ma da yaci,

"kiyi hak'uri Hajiyanmu ba zan iya ci bane" daga haka ya mik'e zuwa d'akinsa, Hajiya ta bishi da kallo ciki da tausayawa,

"K'asim kaje ka lallashi shi dan Allah yaci abincin nan"

"Hajiyanmu ko naje ba ci zaiyi ba awanan halin da yake ciki, mu dai kawai taya shi da addu'a"

"oh ni Maijidda ya Allah gani gare ka, Allah ka dubi yaranan ka kawu masu d'auki dan Annabi S.A.W"

"Amin zanje na kwanta sai da safe"
"to Allah ya bamu alkhairi"

"Amin ya amsa yana ficewa gidan.

ko kafin kace mi zazzab'i mai zafe ya rufeshi, sai karkarwan sanyi yake, zuciyarsa na masa zafi,

ganin tunani ba zai kawu masa mafita ba, ya tashi cikin rashin k'arfin jiki ya d'auro alwala ya shimfid'a darduma, ya fuskanci gabas yana kai kukansa ga mai komai mai kuwa Allah.

hakan dai ta kasance awajan Balkisu, zazzab'i hak'uranta suna gamiwa kaf kaf, alwala tayi tana kai damuwarta ga ubangiji.

ranar dukan gidajan biyu anyi barci ne marar dad'i ciki da damuwa.


*Karku manta kuna tare da Aisha A Yabo Fulani ta Annabi S.A.W*
[9/28, 8:22 AM] Aisha A Yabo: πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*ILLAR AUREN DOLE*
πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*Daga alkalamin Aisha A Yabo Fulani*

*Β© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUMπŸ„*
β˜†We the best β˜†

https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-R

*Email:* realhausafulaniwriters@gmail.com

*Web Page:*
http://www.hausafulaniwriters.blogspot.com

*Follow Us On Insta_gram*
https://www.instagram.com/p/BkZOMcIlfcw/?utm_source=ig_share_sheet&igshid=15q15b5oz4j2u&r=wa1


*MANUFARMU ANNABINMU*


*YA LUDUFIN HALITTA KA LAD'D'AFA MANA ZAFIN QAUNARKA YA ZAME MANA YAWAN GANAWA DAKAI*

*YA SANADIN RAYUWA KA WANZAR DA GANIN KA ACIKIN RAYUWARMU*

*YA MAI TABBATACCEN MULKI A DUNIYA DA LAHIRA KA TABBATAR DAMU CIKIN MASOYANKA NA HAQIQA*

*DAN HAQIQANIN NANA FAD'IMA*

*YA ADON GIDAN ANNABTA ZINARIYAR ANNNABI KI DUBI ROQON BAYINKU*


RANDAWA MEDIA CONCEPT
*Kunaso ahadamaku ring tone da sunayenku?
*Kunaso ayimaku sound track da sunan masoyanku ko kuma lakanin sunayenku?
*Kunaso kuji wayarku tana kiran sunayenku alokacin da akayi kiranku awayoyinku na salula?

Ba anan kad'ai muka tsaya ba, muna yin wak'ok'in bikin aure da na bikin suna, harda na bthdy,


Cikin aminci da karamci zaku samu wanga farinciki da farashi mai sauki, zaku iya samunmu ashafinmu na wasapp dandalin sada zumunta ta wannan lamba 08032176520. Don hudda ta kasuwanci kamar kyautane farashin aikinmu, tsada bata nuna inganci aiki akamfaninmu. Kada Ku manta, Namu dabanne! Domin kuwa aciki zamuyi yanda za'agane cewa lallai kaidinne ko kuma kedindaice akenufi. Ku gwada aiki da sabuwar fasaharmu zakuji dadin tsarin. Mungode mungode mungode.
Isah Randawa ke cewa muzama lafiya da alheri.

*11 to 12*


"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un, ta mutu, shikenan ya kasheta"!

Mama tayi maganar cikin wani irin yanayi na firgici tana girgiza Balkisu,

Yaya Ahmad durk'she yake agabanta yana kuka sosai kamar k'aramin yaro,

duk sun rud'e sai kuka suke an rasa mai lallashin wani acikin su,

tun daga suron gidan take ta kwad'a sallama shiru babu amsa, haka ta kunnu kai cikin gidan tana fad'in

"ba kowani agidan? Inata sallama shiru"

kukan da taji yana fita d'akin Mama yasa Asabi saurin fad'awa d'akin, (

Please Login or Register in order to submit comment