Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

🌹A GIDA D'AYA🌹
🏘️🏘️

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾


Story& written by mmn fareesa


*GODIYA*
Alhmdllh ala kulli halin🙏tsira da amincin Allah su tabbata ga shugabanmu annabi Muhammad (S W A) da ahlayensa da sahabbansa. ALLAH nagode maka daka bani ikon Fara wannan book. Yadda nafara lfy Allah kasa na idar lafiya.


*Gargad'i*
Banyarda wani ko wata ba su canza mun novel ta kowace siga ba. In kunne yaji jiki ya tsira.

*Abin lura*
Ya kamata ace muna d'aukar abinda ya dace muna yin amfani dashi, muna yin watsi dana banza.


BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM

🅿️1&2

Kyawawan y'an mata ne zaune su ukku acikin mota a back sit, yayin da wata guda ke zaune a front sit kusa da driver, kasancewar sun dawo daga skul zasu koma gida ne.
Budurwar dake atsakkiyar su ce tayi ajiyar zuciya had'e da kallon ta kusa da ita tace. "Hmmmm! Wallahi *Khadija* fargabar dawowar Yaya *mahmud* na keyi, sabo da nasan mun shiga ukku agida, sai mun zama bamu da wani sukuni wallahi."
Ummi ta karb'e zancen da cewar. "Kin san fa ko ƙarshen wata inya dawo yayi two days walllahi jinina akan akaifa yake, balle kuma ace anmai doshi aiki nan gaba d'aya."

*Khadija* ba tace komai ba, tayi dai shiru kawai tana ta sauraron su. sabo da ita wanda ma suke zancen akansa bata san shi ba.

Zee dake front sit ta tab'e baki ba tare da tace komai ba, sai dai ak'asan ranta murnar dawowar shi take yi.. Cikin isa da raini ta cewa driver d'in. "Kai dallah yi parking."

Bai ce komai ba yayi parking agefen hanya.
Ummi ta kalli Maryam suka tab'e baki sbd ganin zee ta fita sun tsaya da wani boy friend d'in ta ibbi suna magana.
Ahankali khadija ta d'ago dara daren Golden eyes ɗin ta ta azasu afuskar ummi, tukun ta buɗe baki cikin siririyar muryar ta tace. "Ko dai asauke ni na shiga adai-dai ta ne? Dan wallahi inada uzuri agida in mun koma."

Ummi tace. "Ah ah wlh Abba ba zaiji dad'i ba, ya ga mun fito tare wani ya koma daban bari na mata magana." Tana fad'in hakan ta bud'e k'ofar ta fice zuwa gurin da zee suke atsaye
Rumntse idanunwan ta Khadija tayi sabo da fitsari ne sosai ya kama ta tun a skul, amma sabo da tana da k'yan-k'yami yasa bata shiga toilet d'in skul d'in ba.
Maryam ta dube ta tace. "Lafiya dai ko?"
Khadija tace. "Lafiya lau fitsari ne nake ji sosai..." kafin Maryam tace wani abu ummi da zee sun shigo cikin motar.
Maryam tace. "Dan Allah isah muje khadija ce keda uzuri wallahi." Mitss! Zee ta doka tsaki had'e da cewa. "Aikin banza da wofi, dama akan wannan *agolar* ce aka matsa mun? Wato uzurin ta yafi nawa kenan?" Banza sukai Mata, yayin da isah yaja motar suka nufi gida, dama duk cikin yaran gidan ya tsani zee sabo da ba tada mutunci da girmama manya, ko gemun ka najan k'asa indai kana ak'ark'ashin gidan su to ba zata girmama ka ba daga ita har mama *jummai* (mahaifiyarta).

Suna shigowa get isah yayi parking suka fito.
Zee tayi hanyar sashen su yayin da ummi, Maryam, Khadija suka nufi suma nasu sashen atare.
Khadija dake ta sauri sabo da fitsarin daya kama ta,l ko sallama batayi ba ta shiga waiting parlour tana mai wucewa k'ofar sashen su.
Hajiya hakimah dake zaune kan kujera taja tsaki had'e da cewa. "Ke zonan dan uwar ki baki iya sallama ba?"
Jikin Khadija har rawa yake yi ta nufo gurin ta. Cike da tausayawa ummi da suke k'ok'arin zama tace. "Ayya hajiya tayifa sallama k'arar TV ce tasa bakiji ba." Wata uwar harara hajiya ta watsowa ummi, hakan yasa ummi Jan bakin ta tayi shiru suka zauna ita da maryam akan kujerun dake parlourn.
Ahankali Khadija ta duk'a nesa da ita tana cewa. "Kiyi haƙuri hajiya dan Allah." Hakan ko yayi dai dai da fitowar Aunty (mahaifiyar Khadija). Kallon ta anty keyi cike da mamaki sabo da ganin ta tsigunne agaban hajiya hakimah kuma tasan yanzun taji k'arar anbuɗe get sun dawo daga skul.
Cikin shan k'amshi hajiya hakimah tace. "Ki kiyaye rashin k'in yin sallama aguri ga mutum, domin ko hakan na nuna bashi da tarbiyya, dan haka tashi kije." Jiki babu laka Khadija ta tashi ta kalli anty ba tare da tace komai ba ta nufi wata k'ofa. Anty bata ce komai ba ta dubi su ummi tace. "Kun dawo daga skul d'in?"
Atare gaba ɗaya suka amsa mata da. "Eh anty sannu da gida."
Tace. "Yauwa." Tana barin parlourn.

Tab'e baki hajiya hakimah tayi had'e da cewa. "Kilibabbun banza, zaku tashi kuje ku had'a kayan guga da aka kawo kujeran ko gulmar zaku tsaya yi ne? Ai gara wannan yaron ya dawo koya gyara muku zama! (mahmud).
Tashi sukayi ummi tace. "Dan Allah hajiya da gaske gobe Yaya zai dawo?" Banza ta musu basu kuma cewa komai ba suka bar parlourn.
Hajiya kuwa Sai da aka Kira magrib tukun ta tashi ta shiga ciki.

***********
Khadija na nufar shashen anty toilet ta wuce tayi buk'atar ta, kafin ta fito anty dake zaune kan bed ta dube ta had'e da cewa. "Laifin me kikayiwa hajiya?"
Sun kuyarda kanta tayi had'e da cewa. "Na shigo banyi sallama ba!"
"Daga yau karki kuma hakan sabo da ba dai-dai bane kina jina?" Ahankali tace. "Eh."
Anty tace. "Khadija bana son fitina ko kad'an, wllahi inba cin alhaji yace ki dawo nan da zama tunda umma ta rasu naso ace gidan yaya Abbas kika koma, bazan iya matsa musu ba tunda ya damu da ke k'in amincewa ta ba dai-dai bane zaiji bbu dad'i, dan haka Allah ki zauna da kowa lfy agidan nan babu ruwan ki da kowa." Ahankali tace. "To insha ALLAH."

Anty tace Kin ga gobe yayan su zai dawo daga Abuja acan yake aiki, amma yanzun anmai doshi nan. Nasan halinshi baya shiga harkar kowa agidan nan, tunda nazo Yana bani girma inhar yazo ƙarshen wata yayi week end, sabo da haka ki girmama shi shima yayan ki ne." Ahankali tace. "To" kawai.
Anty tace. "Yaya karatun naki to, kina dai ganewa ko?"
Cikin sanyayyar muryar ta tace. "Eh anty alhmdllh Ina ganewa, kinga yaune zuwa na na ukku a skul d'in amma alhmdllh wlh."

Anty tace. "Masha Allah! Ai haka akeso."
Kiran Sallar magrib ya saka su yin shiru, khadija ta wuce toilet sabo da tayi alwallah..

*Asalin labarin*

Alhaji Adam d'an asalin k'auyen shema ne dake jihar katsina. Su ukku ne agurin iyayen su. Adamu sai bello da k'anwar su binta.
Sun taso da tarbiyya tare da ilimin addini dana zamani.
Binta primary skul tayi aka mata aure a kano. Yayin da Adam da bello suka cigaba da karatu had'e da kasuwancin su na siyar da kayan gwanjo. Bayan Adam yyi diploma mahaifinsu ya rasu, hakan yasa suka siyar da gidan su da gonakin su suka dawo kaduna da zama tare da mahaifiyar su (inno).

Cikin hukuncin Allah Adam ya had'u da hakimah sukayi aure, kasancewar babban gida ne ya sata agidan su aka jamusu ƙofar su daban.
Ahankali kasuwancin su ya fara haɓɓaka har suna zuwa garuruwa sarin kaya.
Bayan wani lokaci hakimah ta haifi mahmod, alokacin Kuma bello ya had'u da jimmai. Itama dai anan aka kawo ta bayan auren su aka ja musu katanga.
Babu laifi suna zaune lfy da juna duk inno Bata shiga harkan su sai dai agaisa amutunce. Sai dai kuma Allah yayiwa jummai hassada duk abinda mazajen su zasuyi musu indai taga na hakimah yafi nata sai taji haushi aranta, amma afili bata nunawa. Ana ahaka hakima ta haifi d'anta na biyu yusuf, akuma lokacin jummai ke kwaikwan cikin ta na fari.
Zuwa lokacin data haifi kamal duk mazajen su sun Sami aikin gwamnati.
Acikin wasu shekaru aka canza ginin gidan zuwa na zamani, akayiwa kowa sashen sa daban, itama inno sashen ta daban.
Ayanzun haka alhaji Adam (Abba) yana da ƴaƴa Mahmoud, yusuf, kabir, ummi, maryam, sai auta salim....

*Mahmoud*
Saurayi ne d'an kimanin 35yrs. Ya kammala karatun sa na mass com (d'an jarida) har an d'auke shi aiki a Abuja duk karshen month yake zuwa kaduna yayi 2 days kafin ya koma.
Mahmoud kyakykyawane ajin farko, akwai class da miskilanci had'e da shank'amshi. Dogo ne wankan tarwad'a, yana da k'atuwar sallaya atsakkiyar goshin sa dake k'aramishi kyau, bai cika dariya ba saita Kama, murmushin sa kuwa sai ya ga dama yake yi, inya had'e rai saika d'auka besan meye dariya ba.
gaba d'aya yaran gidan najin shakkar sa da tsoron sa sosai, sabo da baya wasa da yaro ko ya sakar musu fuska, in kuwa kama sa laifi to ka shiga ukku aranar.
Har yanxun beyi aure ba, be kuma da niya, asalima beda wata budurwa duk da kuwa tururuwar y'an matan dake cewa suna sonsa, kasan cewar sa d'an jarida mai farin jini.
Mahmoud yana son hajiya hakimah mahaifiyar sa tamkar ransa, da wannan damar tayi amfani wurin cusa mishi *khairat*
d'iyar k'anwarta ce uwa d'aya uba d'aya, ba dan yana so ba ya amince zai aure ta. Ayanzun an ajiye magana data kammala degree d'in ta nan da shekara ɗaya za'a yi auren su.
Wannan kenan!

*Alhaji bello* da mama jummai yaran su biyar. Kamal ,Hakeem sai zainab(zee), hafsat,sai auta bilkisu.
duk cikin yaran mama jumai tafi son zainab sosai, kasancewar duk wasu halaye na zainab duk na mama jummai ne, sannan ayan zun haka burin mama jummai mahmud ya auri zainab, sabo da tana son shi, sannan gefe guda Kuma Mahmoud yana da kud'i sosai, yana taimakon iyayen su duk da suma suna da shi.
Dukda Yana aiki Amma Yana business nasa shima. Zainab nada son kwalliya da fafa (k'arya), ko acikin friends nata nunawa takeyi Abba shine mahaifinta ba daddy ba. Ayanzu haka tana lavel 3.
Kaf samarin gidan sashen su daban, suma.kuma akwai kyakykyawar fahimta da had'in Kai atsakanin yaran gidan.

Anty asma'u (maman Khadija)
Basufi shekara 1 da watanni ba da auren su da Abba (alh Adam) bayan ansha fitina da hajiya hakimah akan bata yarda ba, daga baya dole ta haƙura sabo da be fasa ba.
Anty sun rabu da baban Khadija sabo da baya san haihuwa, bayan ta haifi khadija ta sake haihuwar namiji Abdullah, da gashi sai inta samu ciki ya rik'a b'arewa, ashe shine ke zubar mata, sai da tayi b'ari yakai kusan sau biyar tukun taje asibiti aka bincike ta, anan suka shaida Mata komai, itama kuwa takoma ta shaidawa iyayen ta, yayan ta Abbas yace dole araba auren.
wannan shine dalilin rabuwar asma'u da jafar (mahaifin Khadija), sai jafar ya amshi abdallah, ita kuma Khadija ta zauna awurin anty agaban iyayen ta, bayan sunyi aure da alhaji sai ruk'on khadija ya dawo wurin kakar ta hajiya, shine last week ta rasu sai Abba yace khadijar ta dawo nan da Zama.
Ayanzun haka anty nada d'a guda agidan alhaji Adam, (Adam khalifa ake kiran yaran dashi bazai wuce 8 month ba). Wannan kenan.

Khadija yarin ya ce y'ar kimanin shekara shatakwas. Ayanzun haka suna label 1 ita da ummi, yayin da Maryam ke label 2 kasancewar yanzun atare suke tafiya skul sbd duk skul d'aya suke.
Aweek end Kuma suje islamiyya safe da marece, sauran rana kun Kuma da dare ƙarfe 8 malamin su ke zuwa su zauna karatun hadisai da sauran littattafai na addini, sai 10 suke komawa cikin gida su kwanta.
Hakan kuma duk aikin Yaya Mahmoud ne, shine ya turo mutumin Yana biyan sa duk wata, acewar sa babu wacce zatayi fira ko chats gara suyi abinda zai amfane su.
Zee kuwa ba wani zuwa take yi ba sai in yaya Mahmoud na gidan. To ko yanzun da zuwan khadija gidan ba tafi 5days ba, haka tasamu anayi kuma anty tace itama ta rik'a fita d'aukan karatun duk da khadija tamayi saukan alk'ur'ani Mai girma tun last year.
Khadija na da hankali da nutsuwa had'e da sanyin hali, sai dai bata san raini da wulaƙanci ko kad'an, shiya sa tunda tazo gidan jinin su be had'u da zee da mama jummai ba.
Khadija farace ba za'a kira ta gajera ba kuma baza'a kira ta doguwa ba. Kyakykyawace sabo da ta gado kyawun agurin mahaifinta bafulatani ne...

*Cigaban labarin*

b'angaren zee kuwa tana shiga parlour ta Sami mama jummai azaune sai yaya Kamal dake kallo a parlourn.
Zama tayi tana sauke numfashi, kafin daga bisani mama tace. "Harkun dawo kenan?"
"Eh mama ai yau munjima wallahi, kinsan wannan banzar yarin yar da ummi sune muka tsaya suka gama lacture guda da tuni ƙarfe 5 anan zata Mana."

Tsaki Yaya Kamal yaja had'e da kallon zee yace. "Waike wace iriyar yarinya ce? Baki da mutunci ko? Wallahi yanzun inba kiyi sannu ba jikinki zai faɗa miki, Ina ruwanki da yarinyar da dududu ba tafi 5 days agidan nan ba, ko zaman ki take yi ne? To kiiyi k'ok'ari Abba yasan kin sawa rayuwar ta ido." Mittsssw! Ya doka tsaki had'e da tashi ya fice.
Taɓe baki mama jummai tayi had'e da cewa. "Ai dama su maza basu san wani abu kishin kai ba, ke dallah rabu dashi shiya sani."

Zee tace. "Wallahi mama na rasa me yasa na tsani yarinyar nan, dana ganta sai inji gabana ya fad'i, uwa uba Kuma kyawunta na bani tsoro wallahi!"
Hmmmm! "Ke kuwa Ina ruwan ki da kyawun ta?"
"Ba zaki gane ba mama, amma abardai maganar kawai.

Mama tace. "To Allah ya kyauta, kin san gobe mahmud zai dawo ko?"
Washe Baki tayi had'e da cewa. "Eh wallahi mama, gaskiya wannan karan ya kama ta kiyiwa dady magana ko da zai auri y'ar iskar yarinyar nan ( khairat) to afara bikin mu da shi, inyaso sai ita tazo ata biyu mana."
"Kamar kin san abin da ke raina kuwa, amma wlh ba zai aure ta ba muddin bokaye da malamai na rayuwa, yadda ban zauna da kishiya ba haka kuma ƴaƴa na ma ba zasu zauna da ita ba, indai Ina numfashi aduniya shi kuma Mahmoud d'in muddin zai Mana gaddama ko yanuna girman kan ba zai soki ba to zamu gama dashi da uwarshi."
"Wayyo Allah na dad'i mama! Ina sonki Ina alfahari dake amatsayin uwata!"

Mama jummai tayi murmushi had'e da cewa. "Ke dai Allah ya kaimu goben lafiya har girki da wuri zamu shirya kije kikaiwa sakaran uwar shi abashi."
Kafin zee tace wani abu hafsat ta shigo da unifoam d'in islamiyya ajikin ta, hakan yasa suka yi shiru sabo da gaba d'aya yaran mama jummai basa son abinda takeyi itada zee.

Hafsat ta dubi zee tace. "Yaya zee ga assignment ɗina kimun anjima please."
"Bazan yi ba, haka kawai, nima naji da nawa assignments d'in mana, kina ss3 har sai anmiki assignment ke ba zaki iya ba?"
"Allah ya baki haƙuri ban gane ba ne shiya sa, kuma naga duk yau banga yaya yusuf ba dama shine nake tambaya in bangane abuba ko yaya kamal." Tab'e baki mama jummai tayi ak'asan ranta tana jin inama zainab ce keda kyawun hafsat, amma tana so ta takewa hafsat burki kar shak'uwa ta shiga tsakanin su da yusuf, domin ko kaf ayaran ta mata hafsat tafi su kyau, me yusuf yake da shi, bata tunanin hakan ma ya kasance, mahmoud kawai take ganin zai iya auren cikin yaran ta ta amince, sabo da kyawun sa da d'aukakar sa abin alfahari ne ace y'arta na auren sa, gashi kuma yana da kud'i... Sallamar Daddy ce ta katsewa mama jumai tinanin ta.

"Daddy sannu da zuwa." Hafsat da zee suka fad'a atare.

Fuska asake ya amsa yana cewa. "Kuje kuyi alwallah lokacin Sallah ya kusa." Da to suka amsa suna masu tashi sukabar parlourn.
Mama jummai kuwa fuska babu yabo bbu fallasa tace. "Sannu alhaji, ka dawo ne?"
"Eh." Yace yana nufar k'ofar sashen sa ba tare daya damu da yanayin ta ba, tunda taga ya shigo babu leda ahannun sa yasan ba zai samu sakin fuska agunta ba...

*Washe gari.*

Yau ta kama asabar week end, ƙememe zee tak'i zuwa islamiyya suka shiga kitchen ita da mama suka had'a abinciccika masu dad'i sabo da dawowar Mahmoud.
Gurin karfe 12 suka gama komai, zee jikin ta na kirma ta had'a komai a trays guda biyu, ita ta d'auki guda hafsat ta d'aukar mata ɗayan ta bita da shi part d'in su hjy hakimah.

Babu kowa a parlourn sai k'amshin girki dana air frishner ke tashi a cikin parlourn.
Ƙofar parlourn hajiya suka shiga. Tana zaune tana yanke farce, fuska asake ta amsa sallamar su tana kallo nsu da kaya.
Gaishe ta sukayi kafin zee tace. "Hajiya gashi abawa yaya inya dawo."

"Kai Masha Allah angode sosai zainab, dama abinci kala biyu na mishi kinga sai aƙara mishi da wannan ɗin, ki cewa jummai nace angode." Da to suka amsa suna masu fita. Yayin da ita kuma hajiya ta cigaba da yanke farcenta sabo da ita azaton ta kawai mutunci ne ya saka suka aiko da girkin, musamman tunda ta sanma halin mahmud baya sakarwa ko wane yaro fuska agidan balle harta hasaso manufar zee da mama jummai.

Zee suna zuwa sashen su wanka ta wuce tayi, tukun taci kwalliya ta kece raini tamkar zata gidan biki lol.. Ta feshe jikin ta da body sprays & parforme.
Hafsat da bilkisu dake zaune kan bed suna ta binta da kallo, hafsat aranta tana ganin k'arfin halin zee dake ikrarin tana son yaya mahmod.

"Nayi dai ko babu k'arya?" Cewar zee tana kallon hafsat.
Taɓe baki hafsat tayi had'e da cewa. "Eh kinyi." Wayarta zee ta jawo ta fara kashe selfi.

Khadija ce da khalifa yana zaune kan cinyar ta suna cin abinci, gaba d'aya ta rasa meke damun ta daga jiya zuwa yau sai fad'uwa gaban ta keyi.

"Ki tashi tunda kun gama kije kikaiwa hajiya wannan food flas d'in, kice abawa yayan ku mahmoud." Cewar anty dake zaune kan kujera tana kallo a tv.
"Me yasa nake jin tsoro da fad'uwar gaba in an anbaci sunan mutumin nan?" Khadija ta tambayi kanta acikin zuciyar ta.

Karb'an khalifa anty tayi ita kuma khadija ta wuce kitchen ta wanke hannun ta ta d'auki food flux d'in ta nufi parlon hajiya hakimah.

Maryma da ummi sai Salim ne kad'ai zaune a parlourn. Amsa sallamar Khadija sukayi tace. "Gashi inji anty abawa yaya mahmud."
Ummi tace. "To angode hajiya na ciki za'a fad'a mata."
Ita kuwa ummi tayi haka ne sabo da tasan indai hajiya ta gani zatayi ta baƙaƙen maganganu, kuma k'ila taƙi karb'an abun da aka kawo.
Maryam tace. "Anjima zan shigo khadija ki turamun novels pls."
Murmushi khadija tayi tukun tace. "To shikenan sai kinzo d'in." kafin maryam tace wani abu Yaya Yusuf ya shigo parlourn.
Sannu suka mishi ya amsa yana kallon khadija yace jeki sashen su mama ki kira mun hafsat.
Cikin fargaba Khadija tace to tana mai futa, sai dai tana jin tsoron zuwa sabo da ita bata tab'a zuwa sashen ba.
K'ok'arin nufar hanyar sashen takeyi taji k'arar buɗe get. Da sauri ta juya"ta hango motoci guda biyu suna yin parking. Wani fad'uwa gaban ta taji yayi......✍🏼


Comments kawai guys🥰😘🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

🌹A GIDA D'AYA🌹
🏘️🏘️

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾


Story& written by mmn fareesa


🅿️ 3&4


Jikin ta asanyaye ta nufi sashen su zee.
Ahankali khadija tayi sallama ta shiga, akuma dai dai wannan lokacin ita kuma zee ta fito tana ta zabga uban k'amshi.
Suna had'a ido da khadija ta had'e rai tana jifan ta da wani irin kallo, ɗauke kanta khadija tayi, yayin da bilkisu da hafsat da suke zaune a parlourn suka kalli khadija. Tukun hafsat tace. "Lah Yaya khadija kece yau kikazo?" Murmushi khadija ta saki had'e da cewa. "Eh wallahi yaya yusuf ne yace kizo yanzu."
Kafin hafsat tace wani abu mama jummai dake shigowa cikin parlourn ta karb'e zancen da cewa. "Uwar me zataasa idan taje ɗin?" Shiru duk suka yi, yayin da khadija kuma ta rusuna tana mai faɗin. "Ina wuni?"
"Ke bansan kinibibi da munafurci ki rik'e gaisuwar ki, sannan kuma kije kice masa bata nan."
Mama dan Allah kibari naje wallahi assignment zemin. "Cewar hafsat" tana mai marai-racewa tayi kalar tausayi.
Tsaki zee taja tana mai zama kan kujera, tukun ta dubi Khadija cikin raini tan mai faɗin. "Ke ai sai ki wuce kije ki sanarwa wanda ya aikoki ko."
Banza khadija tamata batare da ta

Please Login or Register in order to submit comment