Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

raju'un"meya farune ?cewar inno arud'e.yyinda hankalin hjy yyi mugun tashi.abba yashiga sanar musu komai.....anty ,mama jummai da Abba sune kawai basuyi kukaba.nura rungume amininsa yayi Yana kuka.gaba d'aya samarin gidan da y'an matan gidan kuka sukeyi" Zee hankalinta yayi mugun tashi sbd atsorace take rayuwa"dama sauk'in inta tuna Yaya mahmod Koda ansaceta yataimaka Mata "gashi abinda yasameshi.
Cikin kuka da tashin hankali hjy tace".tayaya hakan yafaru mahmod da yaushe kadena gani??cikin wani yanayi yace".nidai hjy nafarajin idona kamar wani abu yaf'ada "dg nan nafarajin Yana zafi da k'aik'ayi"nafara murzawa sai Kuma nafara gani biji biji dg nan nadinga ganin duhu ko yanzun duhu nake gani...Abba ya karb'e zancen da cewa duk wani tambaye tambaye bashi bane.ayi hakuri mudage da addua"sbd makamin muminice"duk abinda yafaru da mutum marar kyau.ya ambaci sunan Allah to zaizo da sauk'i insha ALLAH.lokacin dakaji bak'on yanayi a idonka sai furta qalu innalillahi wa inna ilaihir raju'un! Allah yasa mudace.gaba d'aya suka amsa da ameen.abba yadubi nura dake rungume da Yaya mahmod Yana kuka"yace kayi hakuri abokinka zai samu lfy insha Allah.ka kula dakomai nashi a office "sannan duk Wanda yatambayeka Ina yake? Yana gida bayajin dad'i..Nura yace" insha ALLAH Abba.

Abba yadubi Khadija daketa kuka"ahankali yace"Khadija inaso kifad'amun gsky tsakanin ki da Allah! Zaki iya Zama da mahmod Yana tare da wannan lalurar ki kula dashi matsayinsa na mijinki??
Tsit parlourn yayi kowa Yana kallon Khadija dajiran amsar dazata bada"hjy kuwa tuni ta yanke shawara aranta inma Khadija bazata iya Zama da Yaya mahmod ba"sai acikin satin a d'aura auren su da khairat.tasandai ita dolensa ce bazata gujeshiba....Abba Ina tare da Yaya mahmod ko wuya ko dad'i insha ALLAH.fatanmu Allah yabashi lfy.... Muryar Khadija ta katsewa hjy tunanin ta"Abba da daddy sukace Masha Allah!kincika y'ar halak khadija"Allah yayimiki albarka yaba mijinki lfy.
Batace komai ba kanta ak'asa"yyinda Yaya mohmod yasaki murmushi batare daya saniba.yanajin son Khadija da k'aunarta nabin duka sassan jikinsa.ita kanta anty taji dad'in yadda Khadija tace.

Hjy kuwa bata tab'a zaton Khadija zata aminceba.sbd azatonta sbd kud'in Yaya mahmod da d'aukakarsa ta yarda da aurensa.amma ko yanzun bazata yadda ace ita d'aya zata zauna dashiba.dole asake auramishi kairat sukula dashi tare.dukda tana ganin khadijar bazata iya kulawa dashi ba.
Daddy yace to alhmdllh yanzun zakibishi da Kamal "Kamal yakwana a parlourn sbd buk'atar taimakon wani abu" sai sukuma su wuce ciki.ina fatan hakan yyi wa koya daidai?gaba d'aya suka amsa da cewa hakan yayi"sab'anin hjy..Abba yace"kowa zai iya tafiya"

Yaya Nura yataimaka makawa mahmod yatashi tsaye"suka fita tare da kamal.yayinda anty ta dubi Khadija tace".ke mekike jira dabazaki bisuba?

Inno na k'ok'arin fita tace"ah ah abi ahankali dan ALLAH !tashiga ciki Koda akwai abinda zata d'auka saita tafi.batajira cewar anty ba ta fice..

Khadija ta tashi ta wuce sashensu"hjy kuwa ta ayyana aranta da safe zata Kira hjy rabi tasanar da ita tazo "intazo sai suyi mgn akan yaushe za'a yi d'aurin auren khairat da mahmod?da wannan tunanin ta wuce d'akin ta sbd tanason yin nafilfili tarok'awa yaronta sauk'i agun ubangiji...

Duk abinda tasan zata buk'ata saida ta d'auka "saidai ranta fargaba da tsoro takeji "Wai yau zata kwana d'aki guda da Yaya mahmod.da wannan tunanin ta nufi d'akin sa"
Dg shi sai Yaya Kamal "da alama Nura yatafi gida.amsa sallamarta Kamal yayi"Yana cewa yauwa Khadija kibawa Yaya abinci "nace zanbashi bayaso , k'ila ke zai amince.to kawai tace tana k'ok'arin shiga k'ofar bed room d'in sa.bayan shigarta"Yaya mahmod yatashi tsaye yace"Kamal nunamin hanyar da bed room d'in yake! Da to ya amsa Yana Kama hannunsa"Saida yashiga sannan yasakesa.khadija na k'ok'arin fitowa yashigo"hakan yasa tayi baya k'adan.ahankali tace"Yaya sannu da jiki! d'an murmushi yayi yace"Khadija kina Ina?zoki kamani na kwanta"yafad'a Yana lalubanta.matsowa tayi kusada dashi tana cewa" Yaya abincinfa?Khadija bazan iya cin komaiba.yafada Yana rik'e ta jikinsa.gefen bed ta nufa dashi.bayan sun zauna tace"nidai karka kwana da yunwa dan Allah Yaya banaso nidai...Khadija idan naci abincin zakiyi farin ciki da hakan?"da sauri tace"eh zanyi wlh!inkuma bakaciba zantayin kukan.my khady kin iya rigima ko?toke meson naci abinci"ke kinci ko?nifa Yaya Bata tawa akeyiba"ta taka akeyi ai"murmushi yyi yace"ah ah ni Kuma Bata kaina nakeyiba ta Taki nakeyi khadija.to yanzun bayan kagama cin abincin kayi wanka ka kwanta sainaci nawa"hakan yayi ?beyiba my khady! d'an turo baki tayi had'e da cewa to yaza'ayi?"muci abinci atare shine kawai"konace nafasa cin abincin.dan shiru tayi tana tunanin sunan dayacanza Mata yanzun"
*my khady*
Hannunta dake cikin nashi ya d'an matsa Yana cewa"kinyi shiru to!ajiyar zuciya tasaki had'e da cewa na amince ai"tashi muje ko anan zamuci abincin.yauwa my khady kokefa"anan zamuci gsky.janye hannunta tayi had'e da cewa to baranaje na maido shi anan...

Yana nan azaune yarda ta barshi"amsa sallamar ta yayi"bayan ta ajiye tray d'in abincin akan carpet d'in dake tsakkiyar parlourn ta nufi gurinsa.yaya sakko muci abincin"tafad'a tana k'ok'arin Kama hannun sa"tashi tsaye yyi had'e da cewa sannunki khadija nagode da k'ok'arin ki..nidai Yaya banyi wani k'ok'ariba"Kuma kadena mun godiya.hmmm!kinganki ko my khady"yafad'a suna Zama"hannunta guda yarik'e da duka hannayensa Yana shafawa da murzawa ahankali sbd taushin hannun nata...ita kuwa bak'on yanayi na rashin sabo takeji da hakan...jikinta duk yayi lakwas"daurewa kawai taji ta jawo tray d'in gabansu..k'arar cokulla yaji"hakan yasa yace" nifa da hannunki zaki bani!batayi musuba"ta motsa abincin shinkafa da Miya da coslow tayi bissimillah ta nufi bakinsa"ahankali yabud'e bakinsa dayaji hannunta kusa dashi"Koda ya hadiye"cewa yyi my khady nima nizan Baki da kaina"tamkar tace kaida baka gani!saitaga rashin dacewar hakan"hannunsa na dama tasaka acikin abinci "bayan yadebo tana rik'e da hannun takai bakinta.sannan itama tabashi"

Sunjima suna shiriritar cin abincin"hannunsa rik'e da hannun ta guda"gab dazasu gama sukajiyo muryar hjy"saida gaban Khadija yafad'i"shikansa mahmod daurewa kawai yyi"Yana adduar Allah yasa kartayiwa Khadija fad'a da gaya maganganu masu zafi.ba shakka Ashe dukda be ganin sbd jaraba tare kukecin abinci ko?kin wani zo kinshige mishi haka harda rik'e hannu!Kai wannan yarinya kin bani..muryar hjy ta katsewa mahmod tunani.kan khadija ak'asa batace komai ba"zaki tashi kibamu wuri zanyi mgn da d'ana ko kuwa?"da sauri Yaya mahmod yacika Mata hannu"batace komai ba ta tashi ta d'auki tray d'in ta fita.

Zama hjy tayi gefen mahmod tace".bance kasaki jiki da yarinyar nan ba sbd banyarda dasuba da uwarta.nayi mamakin amincewarta zata zauna dakai"karka damu gobe insha Allah! hjy rabi zatazo nakirata tazo da safe"Zan sanar Mata sati me zuwa atsaida mgn" a'daura auren ku da khairat.nabari saitazo mungama mgn saina tuntubi alh da maganar.. Allah yakaimu lfy"iya abinda yace" Yana mamakin me Khadija da anty suka tsarewa hjy aduniya ta tsanesu haka.yanzun ya d'auka zata godewa Khadija akan kula dashi dazatayi da Kuma zab'ar Zama dashi.amma zai barta da hjy Rabin da khairat yaga yazasu kwashe..kadage da addua dan Allah inzaka kwanta.kakumayi k'ok'arin tashi sallar asuba"kayita Azkhar da karatun alk'ur'ani mai girma" aikanada hadda ko?"da eh ya amsa"cike da tausayi race babu komai Allah yasan damu.kayi hakuri "tafad'a tana tashi tsaye had'e da cewa" saida safen zanshigo insha Allah.to hjy Allah yakaimu"yanajin muryar ta bayan fitarta tana gayawa Khadija mgn.ya gigiza Kai kawai cike da tausayin Khadija"yarinya Mai kawaici da kamun Kai"sallamar ta ce ta katse mishi tunaninsa.agabansa ta duk'a tana cewa Yaya ga ruwa kasha"ta nufi bakinsa da da robar ruwan.lalibo hannuwanta yayi yarik'e cikin nasa.saida yagama shan ruwan"tukum yace"matso nan gurin Khadija kinjiko? yafad'a Yana janyo hannunta ta fad'o jikinsa"yyi saurin rungumota"kuka sosai tasaki tana k'ankamesa"Murya ahankali tace".dan Allah menayiwa hjy dabata sona ta tsaneni?"
Khadija nima bansaniba!Kuma banason tana Miki hakan.kiyi hakuri dan Allah banason jin kukanki.insha Allah zata Dena wata rana.muyi Mata addua"Kinga mahaifiyata ce ita!banida kamarta aduniya karki rik'eta aranki kinji my khady nah.yafada Yana shafa kanta da bayanta"tana shashshekar kuka ta kwantar da kanta a kirjinsa"sunkai kusan 10 minit a haka kafin tadena ajiyar zuciya.
Ahankali yace"kin hakura ko?"cikin sanyin murya tace aibanyi fushiba"yace"yauwa tawan"yanzun muyi wanka saimu kwanta bacci ko?gabanta taji yafad'i.aranta tace to yanzun yazanyi da wankansa?"my khady miye abin jin tsoro ?inkika kaini toilet nashiga 🛁 bath tub saiki fito"bayan kin ajiyemun towel.inna Gama zanmiki gyaran Murya saikizo kifito Dani"ajiyar zuciya tasaki harta fito fili"uhmmm!tsorona kikeji kome?da har wani ajiyar zuciya kikeyi"Allah dai yabani lafiya yarinya tare zamu dinga yin wanka duk zancire Miki wannan kunyar ai.itadai batace komai ba"tana mamakin yadda yau yaketa bak'in abubuwa.barin jikinsa tayi ta wuce toilet.lokacin data fito Yana tsaye "dg shi sai boxer yarage kayan jikinsa"da faffad'an kirjinsa tafara cin karo."mai cike da gargasan gashi bak'i sidik"saida takomajin wani tsoro sbd bata tab'a ganin babba namiji ahakaba.motsinta dayaji yasakashi cewa duba a sip nawa kibani towel"Gurin sip d'in ta nufa.taga towel kusan 7jere ta d'auki guda ta rufe sip d'in.

Ahankali tace".gashi Yaya"my khady kimatso kibani ,k'ofa motsinki banaji"yafad'a Yana lalubenta.hakan yasa ta k'ara matsowa kusada da shi.karban towel d'in yayi yahad'e da hannunta yarik'e.yana cewa muje toilet d'in"saida tayi addau suka shiga.bayan yashiga 🛁 bath tub d'in.ta fito taja wani stool ta zauna gab da toilet d'in.

Hankali kwance yayi wanka da lalube da dubara yagama"yafito dg bathtub d'in"bayan yad'aura towel d'in" yamata gyaran murya..da sauri ta turo k'ofar ta shigo"Yana tsaye "tamkar Yana gani haka takeji.sbd hasken dakecikin toilet d'in"hannunsa ta Kama ahankali"yadafata Yana yarfomata ruwan hannunsa. bayan sun fito tace"dafa sanyi ruwan Yaya ka yarfomun"Yana murmushi yace".eh Mana kozaki iya ramawa ?nasandai ke matsoraciya ce"hmmm!Yaya tsorofa halak ne ko?injiwa to? zaunar dashi gefen bed tayi"tanacewa zaka saka kayan bacci?ah ah kiduba asip din katana gida na 3 akwai boxers ki kamun guda nasaka .amma Yaya ko vest bazaka sakaba?keko my khady? Allah nakamaki Zaki gayamusu.kibani kawai"turo baki tayi ta wuce ta d'akko tazo gabanshi tanacewa gashi to"hannunsa yasaka ya karb'a"Yana k'ok'arin ruk'ota ta zille tana murmushi.shima murmushin yayi had'e da cewa zankamakine"hmmm nide wanka zanyi nima "nasan sadda Zan fito kayi bacciko?"k'ila to"yafad'a Yana tashi zai janye towel nasa"da sauri ta wuce toilet d'in.

Acan tasami wani towel guntu ta d'aura"bayan tagama ta fito.yana kwance kan bed d'in idonsa alumshe.doguwar riga tasaka da hijab.takabbara sallar shafa'i da wuturi.my khadi mekikeyi ne wai? yafad'a sbd yadena jin motsinta.gyaran Murya tamishi,hakan yagane cewa Sallah takeyi.

Bayan ta sallame tace "Yaya salla nakabbara kayi hakuri dan Allah.mekake buk'ata ne?Babu komai Khadija"inkin idar kizo mu kwanta anan.da acanma ai Zan kwanta.sbd me?Babu komai"hmmmm!ki kwanta inda kikeso sbd bakisona bazaki iya kwanciya shimfid'a daniba.

Dan ALLAH Yaya kadena nifa ba haka bane wlh.bece komaiba yajuya bayansa yayi kwanciyarsa.sbd shi aganinsa miye nacewa bazata kwanta tare dashiba?inma wani abu take gudu"shibazai mata komaiba.

Khadija kuwa ta lura dabeji dad'i ba"hakan yasa ta shafa addua "ta cire hijab da kayan.tasaka riga iya gwiwa ta bacci.tafeshe jikinta da turare.gaba d'aya nauyi da kunya had'e da tsoro duk suka durarmata.aranta tace "ohni yau nice Zan kwanta da namiji a shimfid'a guda.

Daurewa tayi ta hau kan bed d'in"bayan tarage hasken d'akin"ta kwanta nesa dashi.ahankali take komai.saidai batasan Babu wani baccin dayakeyi duk yanajinta.saida tamusu addu'a tukum ta kwanta"Yaya mahmod yayi saurin murginowa saidai kafinma ta juyo yahaye samanta Yana cewa wa nakama?kingama yimun abinda kikeso ko?cikin zaro ido tace".Dan Allah kayi hakuri ka kwanta"tafad'a cikin tsoro dasakin nishi sbd yamata nauyi sosai.uhummm baccima zanyi anan yafad'a Yana laluba kirjinta.cikin rashin sa'a yatab'o nashanunta.saurin rik'e hannun sa "tayi tana turesa.mirginawa yayi yadawo k'asa ita tadawo sama .baby khady kinutsu bacci zamuyi ba wani abuba sarkin tsoro.shiru tayi batace komai ba sbd tsoro.da haka yarungume ta sosai ajikinsa.batada zab'in dayawuce ta kwantar da kanta akirjinsa.ahaka bacci yyi awon gaba dasu....

Washe gari da safe"Yaya kamal yataimaka mishi sukaje masjid suka dawo"Koda yadawo Azkhar yazauna sukayi da khadija.sai kusan 7 am yace Mata tashi muje mu kwanta.har zatayi musu ta tunada bayason musu.ahankali tace"Yaya Ina kwana ya k'arfin jikin?"Yana murmushi yace "kece me jinya my khady sbd haka ke za'a tambaya yamai jikiko?to nidai lfy qlau nike"ya tsoron dakika kwana dashi cike da shagwaba tace".nide Yaya kadena tsokanata.murmushi yayi Yana cewa matso nan kiji wata mgn.babu musu ta matso jikinsa"yarungume ta.suka nufi kan bed"tana rungume ajikinsa suka kwanta.cikin sanyin Murya tace"bacci zamuyi?hmmm!labari Zaki bani"Amma kafin nan hau online kidubamun messages Dana wasu grps sai ki duba face book.dato ta amsa"tana jawo wayar dg k'asan pillow...

Karfe 8:da wasu mintina hjy rabi da khairat suka iso gidan...✍️


Comments kawai🥰🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

🌹A GIDA D'AYA🌹
🏘️🏘️

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾



Story & written by mmn fareesa




🅿️35&36


........"Kaitsaye sashen hjy sukayi"hjy nata jera break fast itada asabe Mai aiki"hjy rabi da khairat suka shigo parlourn.hjy naganinsu tace"sannunku da zuwa! hjy rabi tace"meye yafaru dan Allah ?wlh hankalina yatashi ko karyawa bamuyiba" nacewa khairat muzodai mugani.hjy tace"hmmm!gsky babu lafiya muje ciki kuji....
Suna zama kan bed "hjy tafara matsar k'wallah.kafin tasanarmusu komai.innalillahi wa inna ilaihir raju'un!suka fad'a atare.khairat tace ayya Yaya mahmod annakasa to Allah yasa hakan shiyafi alkhairi.wani kallo hjy tamata kafin tace"wace irin addua ce wannan khairat?rok'a mishi lfy yakamata kiyi ko?hjy rabi tace"hakane gsky Allah yabashi lfy.mubari muwuce gida"ah ah dama harda maganar aurensu da khairat yasa nace kizo muyi mgn .sbd a wannan satin nakeso ad'aura aurensu dashi.....sbd Yar uwarsace zata iya mishi komai.banaso ace yarinyar nan yana tare da ita wlh.gara yazauna da jininsa akan bare.cikin k'ank'ance ido hjy rabi tace".bangane yaren dakikeyiba ?Wai kina nufin y'ata khairat son kowa k'in wanda yarasa zata auri nakashashshe?"Kuma makaho"mmmm! saidai inbana numfashi hakan zai faru...Baki bud'e hjy hakeema ke kallon hjy rabi cikin tsantsar mamaki da al'ajabi.khairat ta karb'e zancen da cewa ai wlh mama kobakida Rai bazan auri nakashashshe ba.kuma makaho"bacin acikin nakasa ,makanta yafi komai ciwo.shida Allah yad'orama saiyaji da ita Allah yasawak'e...ke wawiya jahila !kin Isa kigayama hjy mgn agidanta....cewar ummi cikin fushi tana nufo khairat"sbd tana toilet tanajin komai.shine tafito Afusace....cikin b'acin rai marar musaltuwa hjy tace"ummi fita waje bance kimata komaiba.ran ummi ab'ace ta juya tana cewa akoma islamiyya gsky "tabyaya za'arik'a gayawa Wanda Allah yajaraba da lalura mgn.

Bayan fitar ummi"hjy ta dubi hjy rabi tace"bantab'a zaton haka daga garekiba"Ashe bare zaifi jinina?nanuwa y'ar mutane k'i da tsangama sbd zugarki"Ashe ko bayan Raina bazaki iya kulamun da zuri'ata ba?"Babu damuwa nagode!sai yanzun Nagano maganganun mahmod nacewa" sai wani abu yasameka kake gane masoyinka na gsky"inda nagodewa Allah mahmod bayason y'ar ki"itace ta manne mishi ,hakan yasa na tursasashi ya aureta"kuma ya amince da zab'ina badan yasoba.... tab'e baki hjy rabi tayi had'e da cewa"saidai kiyi hakuri Yaya hakeema! Amma bazan cutar da kaina akan waniba.ita khadijar saita zauna tare dashi "dama ai y'ar wahalace ita.tunda ta yadda zata zauna da naka....kimun shiru kija y'ar ki kubarmun gida.marar mutuncin banza da wofi.kirubuta ki ajiye ko bayan Raina Babu maganar had'a zuri'a ta dataki wlh.murmushi hjy rabi tayi had'e da tashi tsaye itada khairat tace".Babu komai naji Allah yabashi lfy.nabarki lfy"batajira cewar hjy ba suka fice dg bed room d'in.

Ummi da Maryam suna tsaye a parlourn"ummi tagama bawa Maryam labarin abinda hjy rabi da khairat suka yi"saiga su sunfito"Maryam ta dubi kharat tace".kinbani mamaki khairat butulu kawai"insha Allah saikinyi nadamar maganganun dakikayi.ke dan uwarki nikike gayawa mgn.angayamaki ko akwai abinda Zaki iya yine?cewar ummi cikin fushi"hjy rabi tace"ke wuce muje rabu dasu kimusu uzuri nahaushin d'an uwansu yamakance.tanafin hakan sukayi hanyar waje"ummi tace aidakin tsaya jikinki yagayamiki yarinya.

Hjy kuwa sbd bak'in ciki da b'acin rai"saida tayi hawaye .bata tab'a zaton hjy rabi zata Mata hakaba.toilet ta wuce ta wanke fuskarta "tasaka hijab ta nufi part d'in su Yaya mahmod.

Cak ta tsaya agefen window d'in bed room d'in shi"tana hangosu....

Zaune suke gefen bed"tana shafa mishi mai"da alama dg wanka yafito"hjy tayi tsaye ta window tana hangensu Bata shigaba.ahankali Khadija tace" Yaya bara naje nakamaka kayan ko?ah ah muje gurin sip d'in narakaki"tana murmushi tace"to.kamashi tayi yatashi tsaye yadafata suna tafiya ahankali har suka iso gurin sip d'in kayansa.dubawa tayi tace "mezaka saka?"my khady duk kayan dakikeso kikabani suzan saka .to tafad'a tana k'ok'arin ciro mishi t shart da 3 Quarter"ita ta taimaka mishi yasaka"kasancewar da boxer ajikinsa.sannan taja hannunsa yazauna gefen bed"tajawo kayan break first da Kamal yakawo bbu jumawa tafara k'ok'arin had'a mishi...hjy dake lab'e ta window gaba d'aya jikinta yayi sanyi.tasha mamakin ganin yadda Khadija ke mishi hidima "babu wata hantara konuna gajiyawa dashi "saima wani lokacin harda murmushi takeyi"Bata auneba taga tana bashi tea da cheeps yanaci"suna magana da murmushi da alama fira sukeyi.....sannan atare suke break fast d'in...jikinta asanyaye ta juya kawai Takoma sashensu" sbd yanzun nauyin Khadija ma takeji..

A parlour tasami ummi da Maryam zaune jigum jigum"zama tayi tana cewa"kunyi kalacin kuwa?ummi tace". ah ah hjy!
Maryam tace".hjy kiyi hakuri dan Allah akan abinda mama rabi da khairat suka yi"hjy na murmushin takaici tace".inban hakuraba mezanyi Maryam?ummi tace"ai hjy gashinan Kinga halin d'an Adam"dama ni wlh tuni nasan badan Allah takeson yayaba"hjy harda taimakon mama rabi Gurin hura wutar k'iyayyar Khadija aranki"wlh hjy Khadija mutuniyar arzik'i ce.kuma nituni nafahimci Yaya yanasonta !sbd ke yak'i furtawa ko nunawa.ummi tace "k'warai kuwa nima shaidace.wlh Khadija nada kyawawan halaye hjy.kuma ita ba butulu bace "ta zauna da Yaya da kula dashi dan Allah..ajiyar zuciya hjy tasaki tana sauraren maganganun duka yaran nata "Kuma da alama sunyi tasiri sosai aranta.
Batace komai ba" ta tashi ta wuce bed room d'in ta"....

Da misalin k'arfe 11:30 "matasan y'an jarida guda 3 suka bayyana abakin get d'in gidan su Yaya mahmod.(alh mudi da alh Ayuba suka sanar musu komai"dansu zo su d'auki ruhoto su watsa. sbd har yanxun bbu Wanda yasan wani abu yafaru da Yaya mahmod awaje.)
Sunje office nashi kusan sau2 "sai Nura yace"baya gari ai.hakan yasa suka canza shawarar suzo anan kawai..baba Mai gadi yace" dg Ina suke Kuma wasuke nema??"sbd yaga zasu shiga cikin get din gidan..
Babbansu yace"munason ganin mahmod ne !mu abokan abokinsane mu"k'ok'arin mgn baba Mai gadi yakeyi...muryar Yaya Kamal tadaki dodon kunnen sa"Gurin cewa"in Kuna nemansa sai akace Dole agidansu zaku zone ?to baya nan yayi tafiya zaku iya tafiya"babbansu yace".miyayi zafi abokina?kozaka iya sanar Mana inda yatafi ne?"wani kallo yamishi dayasa yaji mugun shakkarsa.fuska a had'e yace ".malamai kubar nan dallah!basuce komaiba suka juya suka shige motarshi.yaya Kamal yadubi baba me gadi yace"inda banzoba meye zaka cemusu ne?"yakamata ace kana rik'e Mana sirrin gida tsawon shekarun dakayi anan gidan. baba Mai gadi yace"ayi hakuri zan kiyaye insha Allah.kafin Kamal yace"wani abu "isah driver yayi horn "su Abba da mlm na Allah na back sit.cikin get d'in kawai Yaya Kamal yashiga"

Bayan su Abba sun fito dg motar"Yaya Kamal yagaidasu, suka wuce sashen su Yaya mahmod.yyinda Kamal yad'aga wayarsa sbd ganin kiran Yaya Yusuf.
Bayan sun gama gaisawa "Yaya Yusuf yashiga mishi jajen abinda yafaru" sbd hafsat da safe tasanarmishi dayakirata.
Kafin dg karshe yace"gobe Yana hanyar dawowa gida insha Allah.

Zaune Khadija take akan 3 seeter"Yaya mahmod yayi matashin kai da cinyarta.hannunta guda saman sumar kanshi ta na shafawa"yyinda hannunsu guda ke sark'e da juna.
gaba d'aya dg jiya zuwa yau"d'an zaman dasukayi sun sake shak'uwa d juna.da kuma sabo da juna"gaba d'aya k'amshin jikinsu iri d'ayane "inhar baka saniba zaka d'auka yaya mahmod Yana gani sbd idanunsa abud'e suke"
Ahankali yace"my khady kibani wani labari Mana"uhummm!Yaya nibanida labari inba na hausa novels ba"ko English novels...Ashe kinason ki iya soyayya my khady? rufe idonta tayi tana murmushi tace"nifq badan hakaba Yaya"to sbd menene?sbd nak'aru da sanin abubuwa masu mahimmanci na rayuwar yau da kullum.zan ilmantu na wa'azantu nakuma nishad'antu wlh.yar dariya yayi"yace"har wani ilmantuwa da wa'azantuwa akeyi acikin novels?"
Eh Mana Yaya"wlh akwai wani book Dana karanta YAU DA GOBE....hmmm book d'in nan yayi 💯"wlh Yaya na k'aru ga Kuma bantausayi"Kai my khady zaki karantamun ne?me zai hana yaya?insha Allah kuwa..(karki Bari yau da gobe na mmn fareesa yawuceki"paid book kibiya hjy ki karanta cikin nutsuwa)
knocking d'in k'ofar da akayi yasaka Yaya mahmod cewa waye?Abba yace"mune"da sauri Khadija tayi k'ok'arin janye kan Yaya mahmod dg kan cinyarta.amma sai cewa yyi meye haka?"k'auyanci kome?Abba kushigo "yafad'a cikin ihu.hakan yasa Abba yayi sallama yashigo"yyinda mlm na waje sbd asanar musu kafin yashigo.cike da kunya Khadija ta gaida Abba kanta ak'asa"Yaya mahmod nakan cinyarta yagaida abba.yana mintsinin Khadija a hannunta.ramawa tayi itama agefen wuyansa"Abba yace"dama nace maka zamuzo da mlm .sbd haka Yana waje zanje nace yashigo.yaya mahmod yace"to Abba.bayan fitar Abba Khadija tasaka hijab nata dake kusa da ita. Yaya mahmod na murmushi yace" wakika mintsina? turo baki tayi tamkar Yana ganinta tace"ba ramawa nayiba!nidai ko my khady?zamu had'u anjima...kafin tayi mgn mlm da Abba sun shigo parlourn.

Amsa sallamar su Yaya mahmod yayi Yana tashi zaune"hakan yasa Khadija ta gaida mlm tana k'ok'arin barin parlourn.abba yace" dawo ki zauna kinjiko?ai keda mahmod Babu zancen b'oye b'oye.zama tayi kan kujera" mlm suka gaisa da Yaya mahmod ,yamishi tambayoyi akan yadda yakeji ajikinsa.yana bashi amsa"wata robar faro ce cike da magani"yamik'awa Abba yace"suje yanzun yayi wanka da ruwan ciki"sannan yayi alwallah sai suzo inajiransu.abba ya karb'a Yana k'ok'arin mikawa Khadija"ta karb'a ta Kama hannun Yaya mahmod suka nufi bed room d'in sa.

Kayan jikinsa ta taimaka mishi yacire "yayi saura dg shi sai boxer"robar maganin ta mik'a mishi tana bud'e k'ofar toilet d'in tace".Yaya shiga ciki"Yana lalubenta yace" to my khady nikad'ai zanyi wankan Wai?eh Mana Yaya"kayi bissimillah saika zuba ajikinka ka cud'a ko Ina"shiru yyi bece komaiba ya shige toilet d'in"yamata shirune sbd yasan biyoshi zatayi"dan yalura bataso yayi fushi da ita ko ta mishi laifi.hakan kuwa yakasance .ta biyosa abaya"karb'an maganin tayi dg hannunsa. ta bud'e marfin"tun dg tsakkiyar kansa tazuba zuwa duka jikinsa shikuma Yana cud'awa"yyinda ta rage kad'an tana cewa Yaya nafita saika Ida zubawa indabejiba"murmushi yyi sbd yaganota.sotakeyi tace"yacire boxer nashi" shine tace" haka ,amma cike da zolaya yace" Kinga zoki ciremun boxer d'in nan saina zuba.da sauri ta fice tana cewa nidai Babu ruwana.yana murmushi yacire, ya zuba ko Ina ajikinsa.
Bayan yagama yajawo towel dake rataye akan k'ofar toilet d'in yad'aura.kafin yayi alwallah yafito".Khadija natsaye da jallabiyar sa da wani boxer d'in a hannunta" tayi saurin matsowa kusada shi tana cewa ga jallabiya kasaka Yaya"to my khady nagode kinji?batace komai ba ta taimaka mishi yasaka"kafin yacire towel d'in"suka fito parlourn atare.saida ta zaunar dashi tukum "itama ta zauna.abba yace" sannunki khadija! Allah yayimiki albarka"tana murmushi tace"ameen.

mlm ya matso kusada Yaya mahmod Yana mishi tofin wasu adduo in.yajima Yana mishisu"kafin yadubi Abba yace"a gsky sihirine ajikinsa !dubada yadda idanunsa suke abud'e Kuma baya gani.sannan gsky Dole mutafi dashi gidana yazauna muga Yaya Allah zaiyi.amma ko yanzun ana nufarshi da sharri wlh.sbd yadda jikinsa yanuna "bushewar ruwan maganin.nagane ne ta hakan... innalillahi wa inna ilaihir raju'un!Abba yafad'a cikin damuwa.yaya mahmod kuwa besan wani Jaye Jaye"shidai yad'auka ciwonsa dg Allah ne...

Abba yace to shikenan nagode k'warai mlm.zuwa anjima zamu zo tare dashi agidan naka.amma iyalinsafa?munatare abba.dg mlm har Abba Saida suka murmusa.mlm Yana murmushi yace"Babu damuwa ai nima iyalin tawa gudace"akwai d'aki Zan yi kaye Kaye saisu zauna ko zuwa sati d'aya mugani insha Allah.abba yace to shikenan nagode.sallama sukayi"mlm da Abba suka fita"

Yaya mahmod kuwa badan ransa yasoba zai amince atafin "saidai kawai sbd mahaifinsa bayason musu ko jayayya dashine.kallonsa Khadija tayi taga yayi tagumi yadafe kansa.tashi tayi anutse tanufi kusada shi ta zauna.jikinta danashi na gugar juna....

Cikin sanyin murya tace"Yaya menene naga kayi tagumi?"tafad'a tana saka hannunta tajanye mishi hannunsa"lalubota yayi "tadawo saman cinyarsa yarungumeta.cikin wani yanayi yace"banason zuwa gidan malamin ne my khady"banason Jaye Jaye "har azo ana zargin wani"nayi Imani bbu mahaluk'in daya Isa yamun abinda Allah bemunba.ahankali tace"hakane Yaya"Amma muyi hakuri muje can d'in ba'a san inda ake dacewaba"inaji ajikina ta sandin sa zaka warke" insha Allah bazamu dawo gidan nan ba saika warke.yana murmushi yace"aranar zanbaki ajiyar baby kuwa.hmmm!Yaya wane irin baby Kuma?"tafad'a sbd harga Allah Bata gane meyake nufiba!my khady kenan "baby nacikin ciki Mana "da Mata da miji ke haifarsa.tsit tayi sbd kunya,saima k'ok'arin guduwa datayi "yayi saurin rik'ota"Yana cewa zancire Miki wannan kunyar my khady"yafad'a Yana laluben cute face nata"janye kanta tayi tana mishi cakul kuli ,hakan yasa tayi saurin sakinta Yana dariya.itama dariyar takeyi tana cewa "yeeeeee!nayimaka wayo ai....kafin yace wani abu hjy ta murd'a k'ofar ta shigo da sallama"da sauri Khadija tadena dariyar"saima fad'uwar gaba data rik'a ji"Yaya mahmod ne ya amsa sallamar cikin fargaba "sbd yasan saita b'atawa Khadija rai.zama tayi kan kujera"Khadija tayi

Please Login or Register in order to submit comment