Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Yusuf "harda zazzab'i tayi..acikin sa'a kuma hjy taji muryan hafsat nagaida ita"da yuni foam na skul ajikinta."fuska asake hjy ta amsa,tana cewa yauwa hafsat zonan" kikiramun yayanku Yusuf"bangane number saba.da to hafsat ta amsa tana karb'an wayar tashiga contact ta fito da numbesa.kallon hjy tayi tace".akira shi?"eh kirashi manah"bugu 2 yad'auka Yana cewa hjy!hafsat tace hjy yad'aga ai"hjy ta tashi tsaye tace kugaisa Mana bara nazo"batajira cewar hafsat ba,ta wuce part nata.yyinda su ummi da maryam suka k'unshe dariyarsu.kasancewar suna zaune a parlour...

cikin turo baki tace".Yaya Ina kwana?"Yana murmushi yace".bazan amsaba hafsat!sbd kin rainani shine kika kashemun waya ko?tashi tsaye hafsat tayi tana k'ok'arin fita tace".bafa haka bane Yaya"to menene gayamun"cike da shagwaba tace".bakaine kaketa zancen wannan taslim d'in ba.hmmm !nadena zancenta "tunda bakyaso.amma Yaya anan Kano take?"
Yace"eh"a anguwarmu ma!kokinaso kisanta ne?"da sauri tace".eh Mana"
Hmmmm!kibari ranar Dana dawo zannuna Miki pic nata karki damu.jikin hafsat asanyaye sukayi sallama.shikuwa yanata dariya abinsa.sbd yamata wayo"

Komawa tayi parlourn"tasami su ummi da hjy"ta dubi hjy tace".gashi hjy ,yayan yace"zaikiraki yanzun.hjy tace ".to tana karb'an wayar.nikuwa nace lallai hjy kinso kanki da yawa"meyasa ita Khadija bakya sonta.โ˜น๏ธ

Gaba d'aya Yaya Mahmoud Yana cikin damuwa"tun Daren dasukayi waya da Khadija.ak'agare yake yazo gida.hakan yasa yabarwa nura motar yataho da ita"shikuma yabiyo ta jirgi.gurin karfe 12:35 pm ya iso gida.kai tsaye part d'in su hjy ya wuce"bayan yasaka isah driver yakaimishi kayansa abakin k'ofar d'akin sa..
Cikin kamilalliyar muryansa yyi sallama"Yana shiga acikin parlourn"su ummi d Maryam dake zaune suka amsa.suna mishi sannu da zuwa.kallon ummi yayi yace".hjy fa?"
Ummi tace" tana ciki.part d'in hjy ya wuce"tana kwance kan bed d'in ta"tayi zurfi atunani taji muryansa yana sallama.tashi zaune tayi fuskarta bbu walwala ta amsa sallamar.gabansa yaji yafad'i dayaga fuskarta"hjy sannu da hutawa"yafad'a Yana k'ok'arin Zama kan kujerar dake gaban gadon.

Hjy tace".yauwa" shigo war wuri kayine?"yace eh"
Tace".dama kuwa inason nafara ganinka ,kafin alh yaganka"dakewa yyi yace lfy dai ko hjy?"tab'e baki tayi had'e da cewa dadai sauk'i"tashiga kora mishi bayani akan komai.tsabar farin ciki. jiyake tamkar yataka rawa".saidai Koda wasa be nuna hakanba"wani k'in mama jummai yak'ara d'arsuwa aransa"inbacin darajarsu Kamal ,wlh shima da kanshi sai yyi maganinta...meye mafita yanzun?"muryan hjy takatse mishi tunani"kallon ta yyi cikin taushin Murya yace".hjy kiyi hakuri kibar Abba yyi komai game dani"nibanason yarinyar nan"kinsan halina banason raini.inma ya auramun ita dg baya nasan yadda nayi narabu da ita.amma yanzun inna bujure bazai ji dad'iba"zaiyi zaton dasaka hannunki.sannan hjy dan Allah kidena d'aukar jita jita"sbd gudun irin wannan matsalar.gashi inno tazo taga laifinki,hakan yyi sanadin daza'a auramun wannan yarinyar ko? tab'e baki hjy tayi tace".waye yajawo ?inba kaiba!na hanaka sakata aiki kak'i ji"aigashi ammanna maka agola ko?"kiyi hakuri hjy dan Allah zanyi .aganinta"hjy tace"ni yanzun bansan Yaya halima zata d'auki wannan maganarba gsky.(mmn khairat)
Tab'e baki yyi yace"yoyafa hjy?tsoronta kikeyine ?"iyaka kisanar Mata komai ko?hmmmm! mahmod kenan"Allah ya kyau ta.amma Ina sanar dakai karka sake kasakarwa yarinyar nan Khadija fuska.dato ya amsa" Yana cewa"bara naje hjy na watsa ruwa!da haka ya wuce zuwa part d'in su na mazan gidan.yyinda ransa fal farin ciki"Yana yiwa Allah godiya"hade da addu'a, Allah ya Ida nufi khady tazama mallakinsa.

Ruwa ya watsa ,ya kwanta yanata tunanin zuci"kiranta yasake gwadawa yaji wayar akashe.

Afili yace toko tasan da zancen aurenmu ne?"wata zuciyar tace ah ah gsky"kaima inbacin hjy ai bazaka saniba...wayarsa tayi ringing"Yana dubawa yaga Abba ne.cike da girmamawa yyi sallama"abba yace" kana hanya koka iso gida?Yaya mahmod yace".nadawo Abba kusan awa guda kenan.abba yace ok kasameni a parlour na.

Abba na zaune kan kujera"Yaya mahmod yashigo da sallama"yanemi guri akan carpet yazauna.
Bayan yagama gaida Abba"Abba yakora mishi bayanin komai da komai"Yaya mahmod na murmushi yace"nagode k'warai Abba"Allah yabani ikon rik'eta Amana"Abba na murmushi yace"ameen...dama Abba tuni ya fahimci Yaya mahmod nason Khadija" yak'i nunawane sbd hjy...Abba yace munyi mgn da daddynku sati na sama zamuje nema maka aurenta.ai gara kafara auren ,kafin nan da shekara gudan yyi"kayita zama bbu iyali"iyali su suke k'ara ma mutum mutunci da kima.kuma insha Allah zakayi alfahari da auren nan.yaya mahmod kansa ak'asa bece komaiba.abba yaci gaba da cewa kaga ba'a kaiga sanarma Khadija ba"nabari sai iyayenta sun baka ita.sannan inaso kayi d'an baya da ita"ko aikin dakake sakata kadena.kafahimceni?"Yaya mahmod yace ".eh Abba na fahimta.
Abba yace". Allah yyimiki albarka"Yana amsawa yatashi ya fita.sbd anfara kiran sallar azahar.

Yaya mahmod nak'ok'arin shiga cikin gidan"su Khadija na k'ok'arin shiga mota"driver yakaisu skul"da ita yahad'a ido"tamke fuskarsa yyi , had'e da d'auke kanshi yawuce.khadija kuwa batayi mamaki ba"sbd tasan ta mishi laifin kashe mishi waya..

Koda suka dawo dg skul"boye kanta Khadija tayi .sbd batason su had'u balle yasakata aiki"sannan gefe guda ko waiting parlour tadena zama.inta gaisheda hjy bata amsawa "saima tayita zaginta da aibatata.hakan yasa dg khadijar har anty suna cikin damuwa"

*************

Zaune mama jummai take"abin duniya yataru yamata yawa.gaba d'aya daddy yafita harkanta"fushi sosai yakeyi da ita,ko girkinta baya ci"kwana 3 kenan"sannan yasaka Yaya Kamal yyiwa zee mugun duka"akan tanutsu .bayan yace karta sake zuwa o ko Ina sai skul kawai..
Tashi tsaye tayi "ta nufi d'akin daddy.kokarin fitama yakeyi ta shigo" had'e Rai yyi had'e da cewa meyakawoki d'akina?haba alh !wlh bakamun adalci"shin waye kebe kuskure arayuwa ne wai?Dan Allah kayi hakuri koami ya wuce dan allah.murmushi daddy yyi,yace "nahakura ai tuni"tunda mun daidaita da tsohuwar baza warata....tuni mama jummai ta gimtse fuska"cikin b'acin rai tace".banganeba?cikin ko inkula yace abinda kikaji.๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

๐ŸŒนA GIDA D'AYA๐ŸŒน
๐Ÿ˜๏ธ๐Ÿ˜๏ธ

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ



Story & written by mmn fareesa

Happy Sallah my fans๐Ÿฅฐ Allah yamaimaita Mana ๐Ÿ‘

Wannan shafin na team d'in zee ne da mama jummai๐Ÿ˜œ๐Ÿƒโ€โ™€๏ธ


๐Ÿ…ฟ๏ธ17&18


mama jummai tace"haba alh! tunda k'uruciya meyasa baka k'ara aureba sai yanzun damuka Fara tsufa?"wani kallo daddy yamata kafin yace".kece kika Fara tsufan?toko Yaya adamu (abba)be wuce k'ara aure ba"tunda asma'u basufi 2 yrs tareba. balle ni!inbaki saniba" kisani, budurwa Zan aura...dangirman Allah! karufan asiri karka auri koma wacece "kina wahalar da kanki wlh"bbu abinda zai hanani k'ara aure.dama hakuri nakeyi dake"amma yau kin kaini bango.kokin manta nida gidana innashigo muddin baki ganni da ledaba"to bakimun sannu da zuwa "balle nasami fara'a a fuskarki.ke gaki me bakin kwad'ayi ko?"sbd haka inno Tama bani izinin nak'ara "Kinga bbu fashi kuwa"inzaki nutsu kidawo hanya kidawo.inkuma bazaki canzaba "tonima bazaki tab'a jin dad'in zama daniba"kima sani yanzun ma darajar mahaifinyata da yaranki kikaci.amma wlh datuni kina gidanku"amma muddin kika sake had'a husuma kima d'auka munrabu har abada...Yana fad'in hakan yafito dg d'akin"Yana cewa"kifito narufe d'akina.uffan batace ba" tafito jikinta asanyaye"shikuma ya rufe yayi wucewarsa...

Kwance yake kan katafaren bed nashi"dg shi sai boxer ajikinsa"yyinda idanunsa suke alumshe"bbu abinda yake tunawa sai wai khadinsa tazama tashi da yardan ALLAH."
Tunawa yyi da yadda take abubuwan ta"cikin sanyi da nutsuwa.wani juyi yyi ya rungume pillows akirjinsa"Yana tuna ranar da khadinsa zata Zama madadin pillow d'in.saidai fa shikanshi yasan mahafiyar khairat" mama ba Imani ne da itaba.tacika son kanta da yawa"muddin sukaji abinda kenan akwai fitina wlh"yasan abun nadamun hjy sosai"tunawa yyi da karatun Khadija,afili yace"zaki cigaba da karatunki insha Allah.amma dukda hakan Dole nasa ido akanki"karwani yazo yacusa maki sonshi"wayarsa yajawo yashiga Kira" amma bata shiga.dg bayama suka sanar mishi anyi blocking nashine".har cikin ransa yaji zafin hakan sosai"dukda yasan tanada dalili akan hjy ne.amma shi meye nashi laifin dazata sashi black list?"
Layinsa na sirri da bakowa yasanshi dashiba".yasaka number d'inta aciki "Yana shiga ta what's app yaganta online"

Magana yamata kamar haka".

Assalamu alaikum!

Khadija kuwa tagani"amma bata bud'e message d'in ba.saita share sbd taga bak'uwar number ce.yaya mahmod kuwa Yana chats Yana dubata" yaga kozata mishi reply saiyaga bata bud'e message d'in ba"tama sauka gaba d'aya dg online d'in..

Hmmmm!my khadi kenan"bbu kyau shariya fa "yakamata ki kulani..indai nakai matsayin daza'a kulanin..yana Gama typing yatura mata..

******************
Zaune mama da hjy hakima suke a parlourn ta"hjy tafara mgn kamar haka" dama ba wani Abu bane yasani cewa kizo muyi mgn. sai game da khairat da mahmod "kiyi hakuri rabi !bbu yanda zanyi da alh"yarigada yazab'awa mahmod Khadija" amatsayin matarsa.kamar yadda nazab'a mishi khairat amatsayin Mata."yace "muddin nahana mahmod auren Khadija" to shima zai hanashi auren khairat....wani mitsitstsike idanuwa mama tafarayi"kafin cikin fad'uwar gaba tace".nashiga ukku ni rabi!wannan matsiyaciyar matar da y'arta"sunyiwa rayuwarmu Karan tsaye.mekike nufi Yaya hakima da wannan mummunan zancen ?"hjy tace".abinda dai kikaji"ninafiki jin bak'in cikin auren.shiyasa tun farko naso ayi auren khairat da mahmod" kukace saita gama karatunta "kunga ga abinda yafaru.amma mahmod yace "zaisan yadda zaiyi da ita bayan auren".
tab'e baki mama tayi,kafin tace".yayime ?kezai tsara" amma wlh yanason auren"hjy tace". ah ah bayasofa.mama tace" hmmm!

Amma wlh muzuba muda asma'u take kowacece?muddin tace "y'arta zataja da tawa y'ar"zata fad'i k'asa warwas...Yaya mahmod dake k'ok'arin shigowa cikin parlourn yatsaya cak.aransa yace "Allah yarabamu dason zuciya"mummunan kalamai kawai mama kefad'i akan Khadija da anty"har mahmod yashigo batasaniba..

Mama ina wuni?"shine abinda Yaya mahmod yafad'a Yana k'ok'arin zama kan carpet.shiru mama tayi ,tana kallon mahmod"fuska bbu walwala tace".lfy qlau"ranan saikak'i kashigo kagaidani ko mahmod?"

Jiyake tamkar yace"eh baza'a zoba"sbd yadda yaji tana aibata mishi khadinshin .amma sai ya daure yace ".Ina saurine shiyasa ban shigo ba.tabe baki mama tayi had'e da kauda kanta.
Girgiza Kai Yaya mahmod yyi"Yana kallon hjy yace".hjy sannu da hutawa"hjy tace yauwa"tashi tsaye yyi Yana cewa nina wuce ciki"dama dg office nake.bejira cewarsuba yayi ficewarsa"zuciyar sa najin zafin abinda maman khairat ke fad'a akan Khadija.

Yana fitowa dg parlourn hjy"yafito babban parlourn gidan"sukayi clash d Khadija.da alama daga islamiyya take"sbd da yunifoam ajikinta....fad'uwa gaban Khadija yyi"datashak'i turarensa"d'ago kanta tayi ta saci kallon sa.fuskarsa ahad'e"yyi wani kyau na musammun.cike da tsoro tace".Yaya Ina wuni?"tafad'a tana waige waige and gudun Kar hjy taji"tab'e baki yyi bece komaiba"itakuma ta wuce ,aranta tana tunanin tabbas hjy ce ta hanashi ya kulata "tunda gashi tamishi mgn.yamata banza"gaba d'aya sai Khadija taji zafin abun aranta sosai..jikinta asanyaye tawuce part nasu.

Yaya mahmod kuwa bed room nashi ya wuce.yazauna Yana jawo wayarsa yakira nura"bayan sun gama mgn "yahau online yahango Khadija itama a online d'in"
Messages nata yagani kamar haka"
wslm
wake mgn pls banganeba??"

Murmushi yyi "yaturamata "

๐Ÿคจ๐Ÿ™๐Ÿ˜”
My khady nine ma Baki ganeba?yakamata ace zuciyar ki tasanarmiki da wanene ni"karki damu da sannu Zaki sanni.

Fad'uwa gabanta yyi"afili tace".gsky koma wanene yasanni to"gashi Yana fad'in sunana.
Tura mishi tayi da cewa...

"Inabazaka fad'amun wanene kaiba "to bazan koma kulaka ba!

Yana gani "sai kawai yayi calling nata....Khadija naganin voice call nashi yashigo" taji wani tsoro yakamata.harta tsinke bata d'agaba"sake K
kira yyi akaro na2."
"Ahankali ta d'aga tana sallama"lumshe ido yyi"yacanza muryansa daban wajen cewa".my khady na! sai anjamun aji sannan ad'aga ?cikin sanyin Murya tace".lah bahaka bane fa"daba zanma d'agaba ai"gyara kwanciyarsa yyi yace".sbd me?"tace "hmmm!sbd bansan dawanake mgn ba"amma Raina nabani cewa kanada information akaina".very soon zaki sanni nan kusa Khadijaaaaaa!mekikeyi yanzun?"ajiyar zuciya tasaki had'e da cewa"ina online kakirani"amma zanyi alwallah" lokacin magrib yakusa.amma inbabu damuwa inaso natambayeka pls?hmmmm!nasan be wuce kice wanene niba ko?kokuma tayaya nasami number ki da sanin sunanki?"ahankali tace".hakane gsky.yace "karki damu zaki sani nan gaba"inaso nazo muyi fira"sbd gidanku asan dani! Amma inatsoron wannan yayan naku d'in nan wlh... d'an murmushi tayi had'e da cewa "hmmm!mezai Hana kaje gurinsa kanemi izinin zuwa muyi mgn"amma akanme zakazo muyi mgn?my khady kenan"fad'in kalaman yadda kike araina k'auyancine "saidai kigani a aikace da Kuma zahiri"bazan boyemiki ba Khadija"tun ranar da naganki nagane Ina *sonki*
gabanta taji yafad'i"ahankali tace".kayi hakuri dan Allah!kazo kanemi izinin mgn da ni"indai da gaske kakeyi. nibana kula kowane saurayi...shiru kawai tayi sbd shigowar anty d'akin"tayi sallama ,hakan yasa tayi saurin kashe wayar...

Anty ta dubeta tace".lfy najiki kina mgn ke d'aya?"

"Anty bbu komai fa"baranaje nayi alwallah.batajira cewar antyn ba tabar parlourn.

Yaya mahmod kuwa "yaji muryar anty "yasan sbd ita takashe wayar.wani killer smile yasaki" kafin ya ajiye wayar ya wuce toilet...

Bayan an idar da sallar isha'i"Khadija nakwance"tanata murmushi ita d'aya"data tuna firansu da mutumin dabata sani ba.sannan ita tanajin muryansa namata Kama da wata muryar data sani.saidai tarasa ganewa inda tasan muryan"online ta hau sbd akwai assignment d'in da za'a turo mata.
hannunta har kirma yakeyi Gurin dubashi"taga Koyana online....saidai taga be online,kuma ba'a ganin last seen nashi.
chat nata ta cigaba da yi"zuwa kamar minti 7"yamata mgn"

my khady!keda suwaye kike chats?"

d'an murmushi tayi"ta maida mishi reply da cewa "friends nawa mana"sannan inhar bakasanar mun kokai waye ba? zandena kulaka.
Dubawa yyi yamata reply da"
Hmmmm!banaso kisanni yanzun sai nan gaba"inkuma zaki iya k'in kulani ,bbu damuwa my khady".
amma kisani kullum saina ganki"inzakije skul.

hmmmm! Haba Yaya auwal naganeka fa"ta turamishi.

Reply yamata da"

๐Ÿ™๐Ÿ˜”
Inkinaso mu b'ata dake" to kicigaba da maganar auwal mak'o cinku".inkuma kinason farin cikina" to kidena maganar sa.yana gama typing yatura mata "kafin yasauka dg online d'in rai bace...

gaba d'aya ransa b'aci yayi"tabbas Khadija nason auwal kenan".tunda gashi ta rik'esa aranta"dole yyi wani abu akai"ita kanta khadijar saiyaji tabashi haushi" sbd kishinta yakeyi sosae.hakan yasa besake hawama online d'in ba" harya kwanta bacci.

Khadija Koda ta duba messages nashi"yabata mamaki da al'ajabi"takuma san koshi wanene to "yasanta sosae.saidai abun yatsaya Mata arai sosai"saita mishi reply da"
Hmmmm!
dg haka har washe gari bata sake ganin
Messages nashiba.

*Bayan kwana2*

Abba ne zaune aparlourn sa"yyinda anty ke gefensa suna fira Yana cin abinci.bayan ya idarne yadubeta yace". alhmdllh! asma'u ,ayau aka saka ranar auren mahmod da Khadija "kimanin wata 2"munje danida bello(daddy)gurin mahaifinta"saima yanuna Mana cewa shibeda y'a Khadija "Kuma betab'a haihuwa bama"cikin b'acin rai anty tace".au abinda yafad'a kenan sbd bashida mutunci?"Abba yace".karki damu ,ai rayuwace ko?wata rana yau da gobe zata koya mishi hankali.k'yaleshi mukayi"mukaje gurin alh abbas.yakaimu Gurin yayansa"shine yabamu aurenta "alh mukhtar kenan.cewar anty tana sakin ajiyar zuciya.abba yace"eh shifa "yanada kirki gsky"yamana godiya akan ruk'on khadija danakeyi" dakuma zab'amata mahmod danayi amatsayin miji.yace" kuma insha Allah! duk abinda za'a yi na hidimar biki dashi za'a yi."yama karb'i number ta"dukda nace mishi bbu bidi'ar da za'a yi"
*Agida d'aya*
zamu zauna dasu" kafin sukoma can gidanshi daya gama gini kwanannan.saisu tare acan"amma zata cigaba da karatunta.anty tace".bangane ba AGIDA D'AYA zamu zauna?"
Abba na murmushi yace".eh za'a d'aura aure,amma bazasu tareba" sai bayan wata 5 .zata cigaba da zuwa skul"in anyi aurensu da khairat saisu tare bak'i d'aya...shiru kawai anty tayi"sbd ita sai yanzunma ta tuna dasu khairat da mamanta..taji gabanta yafad'i.saidai bbu yadda zatayi"saidai tabi y'arta da addua da fatan alkhairi.gaba d'aya tausayin Khadija anty taji yakamata"fatanta Kar alh yasanarwa mahmod yadda sukayi da mahaifinta"karwata Rana yagoranta Mata".musammun tunda bashi yace yanasonta ba....kinyi shiru asma'u ko tsarin bemiki bane?"girgiza Kai kawai tayi had'e da cewa" Allah yatabbatar da alkhairi.yana murmushi yace" ameen yah Allah"ahankali tace" alh dan ALLAH karka sanarwa mahmod yadda kukayi da baban Khadija...haba asma'u! Allah yasawak'a nayi hakan.saikace wani k'aramin yaro"karki damu,muyita addua...karki sanarwa Khadija dakaina zansanar mata "acikin satin nan insha Allah.

Anty nasakin ajiyar zuciya tace".to shikenan"

*************

Zaune mama jummai take"tayi uban tagumi,gaba d'aya duniyar tamata zafi.duk inta tuna daddy zai k'ara aure saitaji bak'in ciki da tashin hankali"gashi yak'i sake Mata fuska,balle tayi burga da hauka kodan yadena.duk tayi sanyi"hafsat dukta damu da halin da mahaifiyarta take ciki"ko yanzun duk suna zaune a parlour.amma gaba d'aya mama jummai ta lula duniyar tunani....tashi tsaye hafsat tayi"ta wuce d'akin su.wayarta ta fito ta kunna"text message d'in Yaya Yusuf yashigo kamar haka.

Baby rigima!kina Ina? gani nadawo....zaro ido hafsat tayi"tana cewa anya Yaya ba tsokanata yakeyi ba?kiransa ne yashigo awayarta"hakan yasa ta d'auka cike da shagwab'a tace".pls Yaya da gske kakeyi?
Hmmmm baby kenan!gani nan kusan awa 1 da dawowata".kina inane yanzun?"inafa d'akinmu"okay to kizo ga taslim nan zaku gaisa da ita".muna k'ofar d'akina...bejira cewartaba yakashe wayar yana dariya.

Hafsat kuwa tamkar tayi kuka "sbd kishin dake cinta arai bata sani ba.
ta ayyana aranta cewa"dataje taga wannan taslim d'in"bazata sake kulashiba"tsintar kanta tayi da canza kaya "sbd kar taslim ta rainata.๐Ÿ˜…kasancewar dama da wankanta"lip stick pink ta shafa ,bayan tasaka riga da siket na pink lace.veil pink tayi rolling dashi"tafeshe jikinta da turaruka masu sanyin k'amshi.wayar ta b'oye"ta zura plate shoe's ta fito"zainab dake zaune a parlourn tana chats" ta bita da kallo ,kafin tace".Ina zakije?"inda kika aikeni!cewar hafsat" sbd tunda zee ta rik'e ta mama jummai ta daketa,takejin haushinta"tsaki zee taja had'e da cewa wlh nasan gurin Yaya Yusuf zakije ko? sbd Yaya Kamal naji yace" yanzun yadawo.saina gayawa mama muddin kikaje wlh. uffan hafsat batace mataba tayi ficewarta kawai."sbd ta k'agu taga Yaya taslim d'in nan takene.

Tun daga nesa yahangota"jiyakeyi tamkar yaje yayi hugging nata.murmushi yasakar Mata lokacin data kusa isowa gareshi.saita kauda kanta tana turo baki"tana isowa ,tafara waige waige had'e da dube dube"kafin tace" Yaya Ina take taslim d'in ne?kicin kicin yyi da fuska "kafin yace".yanzun baby rigima bbu sannu da zuwa ko ya hanya ?sai wani zance daban ko?"sunkuyadda kanta k'asa tayi" tana wasa da yatsun hannunta.kafeta da ido yyi yanata kallonta"yanzun duk sbd kinaso kiga matata taslim kike wannan abun?"xoki ganta to awaya gata".da sauri hafsat ta matso kusada shi tana kallon wayar...atake photo d'in ta yafito "wanda yamata amota ranar dazai tafi.. d'ago kanta tayi,suka had'a ido"yajefeta dawani irin shu'umin kallo had'e da k'asaitaccen murmushi. da sauri ta rufe fuskarta tana murmushi "ta juya aguje.hakan yafaru akan idon Abba dake zaune asaman bene "dukda bejin mesuke cewa" amma yafahimci cewa sunason junansu.baby hafsi nah ,karki gudu kijira"inahhhhh!tuni tak'ara Mai aguje tana dariyar farinciki...

Murmushi Yaya Yusuf yasaki akaro na bbu adadi"afili yace". alhmdllh"nayi zaton zansha wahala kafin nashawo kanta ta karb'i soyayya ta"Ashe itama tana sona?"
mlm kamatsa dg can gurin "kayi shirmen surutunka.kazo kaida ita zaku cikamun kunne d mgn.da sauri Yaya Yusuf yad'ago kansa suka had'a ido da Yaya mahmod dake mishi mgn ta window.kasancewar k'ofar d'akinsa Yaya Yusuf ketsaye.
Murmushi Yaya Yusuf yayi"had'e da cewa tuba mukeyi babban yaya.tsaki kawai Yaya mahmod yaja yakoma yazauna ,har cikin ransa yaji yusuf d hafsat sunburgeshi"dama tuni yalura da Yusuf kamar son hafsat yake"yanaso yahanashi son k'aramar yarinya.saigashi shima soyayyar Khadija ta kutso acikin zuciyar sa.hakan yasa yagane SO Babu ruwanshi da shawara inyatashi shiga zuciya..

Yaya Yusuf d'akin sa ya wuce"cike da farin ciki yasake gwada Kiran hafsat dayayi seving number ta da my Angel!

Hafsat kuwa tamkar ammata albishir da gidan aljannah"haka taji aranta.kwata kwata takasa gane Ashe tuni tanason yayanta.kawai ita awautar ta"yace yanasonta kenan ?Kuma zai aureta tunda yanuna photo d'in ta akan itace matarsa.da wannan farin cikin ta shigo parlourn"saidai Tasha jinin jikinta datayi arba da mama jummai tana jifanta da wani irin kallo.dayasa jikinta Fara rawa"zee da bilkisu ne kawai a parlourn.bilkisu tayi saurin cewa Yaya hafsat kigudu mama dukanki zatayi"anty zee tace kinje gurin Yaya yus...bige Mata bakin da zee tayine yasakata yin shiru"zee yace shegiyar yarinya keba'a sirri dake"wlh namanta nayi mgn agabanta.lallai bilkisu kinzama annoba agidan nan.mama jummai tana hararan bilkisu tace kibarni da munafuka zanyi maganinta.kafin tadubi hafsat dake tsaye har lokacin tace K dan uwarki banraba ki da matsiyacin yaron nanba?wawuya marar kishin uwarta"kokin manta cin fuskan da ubansa yamun?da ikrarin karnakoma zuwamishi sashe.to barikiji kiji babuke Babu Yusuf"zankumayi Miki maganin kunnan Kashi.tana fad'in hakan ta tashi tsaye tana tunkaro hafsat d'in.da sauri hafsat taja baya tana bada hakuri.wlh muddin kika fita sainamiki dukan danaji Miki ciwo tunda bakijin mgn ta.tana fad'in hakan ta jawo wayar adafto dake kusada ita.tafisgo hafsat d'in"ta fad'i agabanta. tafara tsulamata guda ,tanacewa kinsake zuwa gurinsa Dan ubanki?hafsat tasaki ihun azaba had'e da cewa ah ah...karki koma dukarmun yarinya!muryar daddy tadaki dodon kunnen mama jummai.da sauri tasaki hafsat tana huci.bilkisu ta tashi da gudu tafad'a jikin daddy"tace wlh daddy mama batasonmu nida Yaya hafsat tafison anty zee.kuma anty muguwace ,itace tasanarwa mama Yaya hafsat ta tafi Gurin Yaya Yusuf"shine mama take zaginta karta koma ganinta dashi"Kuma take dukanta.....ya Isa autan daddy"jeki zauna!sakin daddy bilkisu tayi "da gudu ta fice dg parlourn"sbd tasan muddin sai mama tadaketa tunda tatona...

Abba yayiwa zee wani irin mugun kallo"kafin yace"tashi kibawa mutane guri,zanyi maganinki wlh.sum sum sum zee ta tashi ta wuce...
Kallonsa yamaida akan hafsat yace"kiyi hakuri kinji ko?yanzun yusuf d'in yadawo?tana share hawayenta tace eh"Abba yace to umarni nabaki ba shawaraba!kicigaba da zumuncinki da d'an uwanki karki fasa kinajina?"kanta akasa tace".insha Allah.

Abba yace". madallah ,tashi kishiga ciki.

Bayan hafsat ta bar parlourn"yadubi mama jummai datayi kasak'e.yace dg yau ban amince kikoma dukarmun yaraba.kome sukayi kisanarmun Zan hukuntasu.maganar hanata zuwa Gurin Yusuf nasoketa"ke baki Isa kirabamana zumunciba.yusuf mutumin kirkine bashida aibu.sbd haka kiyayeni wlh.araina nayi niyar fasa auren danace Zan k'ara"Amma ayanzun bbu fashi wlh sbd bazaki tab'a canzawa.saima abinda yyi gaba amugun halayenki..alh katsaya dan Allah kafahimceni Mana!tashi tsaye yyi Yana cewa".banida lokacin tsayawa nafahimceki.saidai nace Allah yashiryemu"dg hakan yajuya yanufi part nashi...

Bilkisu kuwa nafita"kaitsaye d'akin Yaya Yusuf ta wuce.baya a parlourn,Yana bed room d'in sa yanata gwada Kiran hafsat tak'i shiga.yaji muryan bilkisu nacewa Yaya kana Ina?kafin yace wani abu tashigo bed room d'in.kallonta yyi fuska agimtse yace lfy kekuma?baya tad'an ja kafin tace Yaya zee tasanarwa mama Yaya hafsat tazo gunka"shine mama ta daketa.gashi canma tanata kuka,Kuma nagayama daddy dayashigo yasamu mama nadukanta...

"what's?"yya Yusuf yafad'a Yana tashi tsaye"cikin damuwa da fargaba yace " banason fa k'arya bilkisu.innagano k'arya kikeyi dukanki zanyi.
Bilkisu tace wlh Yaya da gske nake!komawa yyi yazauna ,Yana cewa jeki shikenan.dafe kansa yyi byn fitar bilkisu "Yana furta la'ilaha illah anta subbahanaka inni kuntu Minal zalim!wace irin uwace mama ?itace zatayiwa soyayyar mu karantsaye"yafad'a Yana lumshe ido"cike da tausayin hafsat.tunani yakeyi aransa"tunda mahaifiyarta batasan tagansu tare.gara yyi baya kawai"saiya dage da adduar zab'in alkhairi.insunada rabon mallakar junansu to!inkuma bbu , shikenan beson yazama sanadin da hafsat zata Sami matsala da mahaifiyar ta"uwa ba abin wasa bace...

****************
Yau yakama Wednesday"ayau Kuma ibbi yashirya mummunan k'udirinshi akan zee.
kiranta yyi ta waya"yasanar Mata inda zatazo su had'u .ta rakashi Gurin bathday d'in abokinsa da marece.

Kowa yyi Shirin zuwa islamiyya "dukda ranar Wednesday wa'azi kawai akeyi.amma banda zee "kuma mama bata tambayeta ba,kocemata ta tashi ta je" Saida kowa yatafi skul.tukum zee ta shirya cikin areviant gownt purple "Tasha make up "saita za hijab inta fita ta cire.hand bag nata ta d'auka da wayarta"bayan tayiwa mama jummai k'aryar zataje bathday d'in k'awarta kausar.(itada kausar close friends ne)

Tana fitowa get ta cire hijab nata "tayi rolling,kafin ta tari adaidaita ta hau...

Ibbi Yana tsaye agefen motarsa Yana latsa waya.mai adaidaita ya ajiyeta"bayan ta sallameshi ta nufi gurinshi.

Wani shu'umin kallo yake binta dashi,Yana aiyana yadda komai zai kasance aransa...hmmmm!baby love kenan"kinshafa kyau.yafada Yana bud'e Mata front sit"tana murmushi tace". thanks sweetheart.

Shiga driver sit yayi Yana cewa "ba yanzun zakimun godiyaba sai man gaba....


Yaya mahmod ne tsaye agaban dressing mirror"Yana gyara sajen daya kwanta luf agefen fuskarsa"sanye yake da mint blue shirt"me long sleeves da cufflinks"sai jeans ja.simple shirine amma yyi mugun karb'ansa"he is looking way smart.babu abinda jikinsa keyi sai tashin k'amshi.
Fuskarsa adauke yafito dg d'akin sa ya rufe"kasancewar dawowarsa kenan dg office yyi wanka zai fita yyi lunch.sbd girkin da hjy tayi ba choice d'insa bane.ak'afa yatako zuwa hanyar get"su hafsat dasu ummi suka shigo"tasowarsu kenan dg islamiyya"kallon su yyi Yana amsa gaisuwar dasu kemishi.yaga bbu Khadija acikinsu"

D'an Jim yyi,saikuma yaga harsun wuce bbu ita" hakan yasa yafasa zuwa Gurin motarsa yanufi get d'in "da nufin yafita yaga ko abaya akabarta.

wani sarawa kansa yyi sakamakon hango Khadija tsaye da wani matashin saurayi dazasuyi sa'annin juna dashi suna mgn...kafesu yyi da ido Yana kallon su "cikin zafin kishi da bugawar zuciya"besan lokacin da yanufi gurinsuba azuciye...Khadija na k'ok'arin juyowa ta nunawa Tahir harsu ummi sunshige gida sun barta"yyi hakuri Bata kula samari.tahango Yaya mahmod gadan gadan yanufosu...โœ๏ธ

๐Ÿ˜ฑ๐Ÿคซ๐Ÿƒโ€โ™€๏ธ


Comments kawai guys๐Ÿฅฐ

Kunsan bana post week end k'ila innaga ruwan comments kujini Sunday..

Masumin mgn a PC Kuma Muna agrp d'aya dasu kubari Dan Allah komeye kuyi mgn agrps...masu bina pc da tambayar acigaba ko page yyi k'adan damasu cewa asasu grps nawa duka kudena Dan Allah...grps nawa na kud'ine da anyiwa wasu zancen kud'i saikiji sunyi lakwas.sbd haka inbakida mgn mai mahimmanci Dan Allah karma kiyi wahalar mun mgn...๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

๐ŸŒนA GIDA D'AYA๐ŸŒน


Please Login or Register in order to submit comment