Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

nuna tasan da ita take maganar bama.

Ak'ule mama jummai tace. "Maza kije da ya gama miki ki dawo, kinji ko ba kiji ba?"
"Eh naji mama." Cewar hafsat tana tashi tsaye ta kalli khadija tace tukun tace. "Muje to."
Ba tare da tace komai ba ta bita suka fuce, yayin da zee kuma ta raka su da harara tana tab'e baki.
Mama jummai tace. "Masha Allah tawan kinyi kyau, ki bari sai gurin k'arfe 2:30 pm sai kije ciki ki masa sannu da zuwa, kinga alokacin yaci abinci ya huta ko?"
Zee na murmushi tace. "To." Yayin da bilkisu ƴar 13 years da yake zaune tana ta kallon su tace. "Indai yayane gaki gashinan wallahi." acikin ranta.

Ahankali ya saka hannun sa ya bud'e k'ofar motar. Santala santalan k'afafuwan sa ya fara fitowa da su, kafin daga bisani kuma ya fito gaba d'ayan sa. Masha Allah!
Tsaye yayi yana k'arewa harabar gidan kallo, tukun ya zuk'i iska ya fesar had'e da tsotsar lip ɗin shi na k'asa.
Sanye yake cikin suit dark blue, takalmi saw ciki da suke sanye aƙafar sa suma dark blue, yayin da sumar kansa zuwa sajen dake zagaye da fuskarsa suka kwanta sukayi luf-luf sabo da gyaran da suke samu. Ga wani irin ƙamshi na mussaman da jikinsa ke fitarwa, yayin da fuskar sa kuma take a had'e babu far'a.
Agogon dake ɗaure antsintsiyar hannun sa ya duba, tukun ya tab'e baki yana kallon kamal da shine yayo ɗin driving motar. Ckin kamilalliyar muryar sa yace. "Bro time fa yaja ko?"
"Eh yaya kusan fa 12:48 yanzun." Kamal ya faɗa yana kallon sa.
"Okay muje ciki to."
Boot isah driver ya bud'e ya fito da duk wasu trolley's yana mai bin bayan su dasu zuwa babban parlourn gidan.

Cikin takun sa na wanda ya amsa sunan sa namiji yake tafiya kamal na binsa abaya.
Can k'asan maloshi yayi sallama kamar wanda baya son yin magana.
Gaba d'aya hajiya hakimah da yaran ta suna a parlourn. Cikin farin ciki ta tashi tsaye had'e da cewa. "Sannuku da zuwa."
Sakin fuska *Mahmoud* yayi yana mai nufar hajiya yayi hugging ɗin ta. Murmushi tayi had'e da shafa kansa. Yayin da salim da yusuf suka fara mishi sannu da zuwa, kamal kuwa shida isah suka wuce sashen mahmud dan sukai masa kayan sa.

Zama yayi akan kujera fuska asake sabo da ya ga mahaifiyar'sa cikin farin ciki. Yayin da ummi da maryam da suke zaune anutse suka mishi sannu had'e da gaida sa, kafin ya amsa khadija da hafsat suka shigo parlourn.

Wani irin bugawa k'irjin khadija yayi sabo da k'amshin turaren da ya daki ahancin ta, wani irin girma taji parlon ya mata, gaba d'aya jikinta asanyaye yake, takasa kallon direction d'in da mutanen parlourn suke zaune.k
Ƙokarin bin hanyar da zata sada ta da sashen su take yi hafsat tayi saurin rik'o ta murya can k'asa tace. "Muje mu gaida yaya pls Kar hjy taga ba kiyi dai-dai ba."
Gabanta taji ya kuma fad'uwa ba tare da tace komai ba.
Acikin rashin sa'a ta d'ago kanta dan ta kalli mutanan dake cikin parlourn idanunta suka hasko mata yaya mahmod yana amsa gaisuwar dasu maryam da ummi ke masa.
Nutsuwa ta jawo tasawa ranta, tukun ahankali suka zauna akan carpet ɗin, sannan hafsat tace. "Yaya sannu da dawowa ya hanya?"
Sai a sannan ya juyo ya gansu zaune kan carpet su biyu. "lfy qlau alhmdllh!." Ya fad'a ataƙaice.
"In Ina wuni ya hanyan?"
Siririyar muryar ta ta daki dodon kunnen sa, ba tare da yasan ko wacece ba.ba kuma kalle ta ba yace. "Lafiya!" Ataƙaice yana kallon hajiya, tukun yace. "Bara naje na watsa ruwa nayi sallar azahar."
Hajiya tace. "To shikenan na san alhaji da dadyn ku suma yanzun sun dawo." Bece komai ba yayin da har lokacin idanunsa suke alumshe.

A hankali khadija ta tashi tayi tafiyar ta.

Hafsat ta saci kallon yaya yusuf suka had'a ido. Sunkuyar da kanta k'asa tayi, yayin da shi kuma ahankali yace. "Zonan muga assignment d'in da aka dameni ba'a gane ba."
Batace komai ba ta tashi ta nufi kusa da shi book d'in ta ɗauke ahannun ta.
Yayin da yaya mahmod kuma ya tashi ya nufi hanyar sashen mazan gidan..

**************
Ahankali yake takowa zuwa cikin parlourn, sanye yake da farar jallabiya ajikin sa. Masha Allah! Kallo d'aya zaka masa kasan hutu da jin dad'i had'e da kwanciyar hankali sun ratsa jikin sa.
Hajiya ce kawai zaune, fuska asake tace ."Abincin zakaci ko?" Yayin da shi kuma yace. "Eh mma kiyi zaman ki hjy zan zuba komai da kaina, ina yaran gidan nan suke?"
Hajy tace ."duk suna ciki." Bece komai ba ya wuce dining area.
Kujera yaja ya zauna yana duba komai har idanun sa suka sauka akan food flux d'in da khadija ta kawo d'azun.
Ahankali ya bud'e yana mai lumshe ido sabo da k'amshin girkin daya daki hancin sa.

Dambu shinkafa ne yaji kayan had'i, ai kuwa ba tare da ya tsaya b'ata lokaci ba ya zuba, kasancewar yana son abincin gargajiya sosai.
Saida ya cinye plate guda tas tukun ya ƙara da kunun aya. Lol.
Tukun yaci pepper chicken da hjy ta mishi, k'ok'arin barin dining area d'in ya keyi su ummi suka shigo parlourn.
Sakkowa yayi yana kallon hajiya tamkar ba zaice komai ba.
Zama yayi akujerar dake kallon tata tukun ahankali yace. "Girkin nan yayi dad'i hjy ta, especially dambun shinkafar, agaskiya nayi missing ɗin girkin ki."
"Dambun shinkafa kuma?" Hajiya ta tambaya aranta. kafin tayi murmushi tace."K'ila acikin abinciccikan da zainab ta kawo ne, dan ni banyi da dambun shinkafa ba."
Tuni ya gimtse fuska sabo sa jin kalamun, yayin da hajiya ummi tayi saurin cewa. "Ah ah hajiya anty amarya ce ta aiko khadija ta kawo abawa yaya."
Shiru kawai hajiya tayi ba tare da tace komai ba.

Yaya mahmod kuwa yama manta da wata anty amarya sai yanzun ya tuna da ita, aransa yace. "Wacece kuma khadija agidan nan?"
Fasa zama yayi ya tashi ahankali yana mai faɗin. "hjy bara naje mu gaisa da ita." (anty)
Hjy tace ."To shikenan itama jummai kaje kagai da ita." Da to ya amsa yana mai bin haryar da zata sadashi da part d'in anty.

Ahankali yayi sallama cikin kamilalliyar muryar sa. Yayin da anty dake zaune khalifa na acinyar ta ta amsa sallamar.
Da sauri khadija dake zaune kanta babu d'ankwali kalbar kanta duk ta zubo mata agadan baya tayi yunk'urin tashi ta shiga ciki, sai dai ta makara domin ko tuni k'amshin turaren sa ya shaida mata shigowar sa cikin parlourn.
Kallo d'aya ya mata ya d'auke kansa kasancewar ta bada baya, da hanzari tayi cikin bed room d'in anty.
Zama yyi fuska asake yace."Anty ina wuni na sameku lfy?"
Anty tace. "Lafiya qlau mahmoud ya hanya?"
Kansa aduk'e yace. "Alhadilillah." yayin da khalifa kera kiciniyar sauka daga jikin ta, anty tace."Ikon Allah Ina zakaje to?"
Ɗago kansa yayi ya kalli khalifa yana mai faɗin. "Zonan!" Ya fad'a yana mik'a mishi hannun sa.
Sakkoshi tayi ya rarrafa gurin shi, anty tace. "Ko akawo maka abinci ne?" Mahmod yace. "Ah ah naci abincin da kika aikamun dashi ma."
Anty tace. "Masha Allah!" Yayin da shi kuma ya tashi tsaye had'e da sab'ar khalifa ya mata sallama yana mai fita da yaron ahannun sa.

Yana ta kallon yaron had'e da mishi murmushi suka nufi part d'in mama jummai.
Cikin taushin murya yayi sallama acikin parlourn.
Bilkisu ta amsa tana kallon sa tace."Yaya sannu da zuwa, da yanzun zanje na gaishe ka wallahi."
Hararar ta yayi kasancewar itace k'arama ayaran gidan, kuma yana d'an sakar Mata fuska, tukun yace. "Kisha zaman ki auta." Ya fad'a yana kallon mama jummai dake zaune tayi kicin kicin da fuska sabo da ta ganshi da khalil a hannu.
Tab'e baki yayi aransa yana cewa. "Mai hali dai baya fasa halinsa." (kasancewar yasan halin mama jummai.) tukun daga bisani yace. "Mama Ina wuni na sameku lafiya?"
Fuska asake. "Tace lfy lau alhmdllh!"
Ƙwas! Ƙwas!! Ƙwas!!! Kakeji k'arar takun takalmin zee na tashi.
Dago kansa yayi suka had'a ido. Hakan yasa ya hade rai sbd ganin yadda zee ta kafeshi da ido babu ko k'iftawa da yay.
Cikin kissa ta nufi kusa dashi zata zauna tana cewa. "Yaya sannu da zuwa, yanzufa zanje nakai gaisuwa sai gashi kazo ma." Ta fad'a tana Zama.
Yo ai basai kuje canba ku sake gaisawar! "Cewar mama jummai" tana washe baki.
Yayin da haushi sosai ya turnik'e zuciyar yaya mahmod, in bacin yasan idan ya mata wani abu agaban mahaifiyar ta be kyauta ba da taga ne kuran ta, dama tun wancan tafiyar da yayi sadda yazo ya gane zee na sonsa, amma zaiyi maganin ta, domin ko soyayya da k'aramar yarinya baya a tsarin sa, dan ko ko khairat darajar hjy taci wallahi, kuma ko da hakan bazai d'auki raini agurin ta ba.

"Yaya kayi shirufa." Zee ta fad'a cikin kashe murya.
Sake tamke fuska yayi, tukun yace kinga karb'i khalifa ki mayar dashi kizo na baki sak'o.
Canza fuska tayi sabo da ita rabon data d'auki wani yaroma arayuwar ta har ta manta, ba tada son yara, atsarinta ma yara biyu zatayi intayi aure."

"Ke bilkisu zoki karb'e shi ki maidashi mana." Cewar mama fuska babu yabo babu fallasa, sabo da ita dai bata san asma'u da y'a'yan (anty) bakuma suyi Mata komai ba.

Yaya mahmod ya kai k'ololuwar fusa ta, sbd besan raini, amma ya daure yamik'awa zee khalifa murya akausashe yana mai faɗin. "Ke na aika ki kaisl shi, inba zakije ba kuma sai kiyar dashi!"
Be jira cewarta ba ya sakar mata khalifan yana mai tashi tsaye yabar parlourn.

Missttw! Zee ta doka tsaki had'e da hankad'a khalifa cikin rashin sa'a ya fad'o daga kan kujerar kansa ya gwaru da tayis!
Wata k'arar azaba yaron ya saki. Da sauri bilkisu ta matso tana k'ok'arin d'aukar sa sbd taga zee da mama jummai ko a jikin su da fad'uwar yaron.

"Barshi bilkisu karki tab'a shi!" Muryar yaya mahmod ta karad'e parlourn.
Ɗago kanta zee tayi atsorace ta kalle sa. Gaba ɗaya danunsa harsun fara sauya kala, bece komai ba ya duk'a ya d'auki khalifa dake kuka kamar ransa zai fita, yayin da goshin sa yayi kumburi had'e da yin ja.
Uffan bece musu ba ya fice daga parlourn.
Bilkisu tace. "Wallahi yaya zee kin shiga ukku agurin yaya, me khalifa ya miki da zak..." Zanci ubanki ko kiyimun shiru. "Cewar zee" cikin masifa!
Tsaki mama jummai tayi had'e da bankowa bilkisu harara tace." "Ba shiga ukku tayi ba tara ta shiga kinibabbar banza."

Ya mahmod ransa ab'ace ya fita da yaron, dama yasan baza'a rasa mugunta ko wasu maganganu da zasuyi ba bayan fitar sa shi yasa yana fitowa yad'an tsaya, sai kuma yaji k'arar khalifa shine ya koma aransa yana mamakin wace irin uwace mama jummai, su yanzun ahaukan su itada zee sonshi zee keyi.
Rumse ido yayi sabo da baya fatan hakan ya kasance. Jijjiga khalifa ya hauyi da rarrashinsa duk da besan komai ba akan kula da yara.
Part nasu na mazan gidan ya wuce"l da shi, bed room nashi ya nufa da khalifa yana rarrashin sa har ya samu dak'yar yaron yayi bacci akan bed ɗin shi.
Cikin b'acin rai yake kallon goshin yaron da sauraron yadda yaron keta ajiyar zuciya, aransa yana mamakin rashin imanin zee da mama, sai dai k'asan ranshi yana tunanin meze cewa anty akan fushin da goshin khalifa yayi.
Wayoyin sa dake kan bed side drower suna caji ya duba sbd jin guda d'aya na ringing.
Kallon fuskar wayar yayi tare da tab'e baki had'e da Jan tsaki sbd ganin kiran khairat ne. Yayin da aransa kuma yake mamakin irin rawar kan dake d'awainiya da y'an matan yanzu.

Wani kiran ya sake shigowa akaro na biyu, tsaki yaja yana rejecting d'in kiran, kafin ya daga bisani ya shiga contact ya fito da number din kamal yayi calling nashi.
Yana jin ya d'aga yace. "Kana Ina ne, okay kazomun da zainab yanzun a parlou na ina jiran ku."
Bejira jin amsar kamal ba ya kashe wayar yana huci.

Kamal dama Yana a haraban gidan, suna gama waya ya nufo cikin gidan.
Zee na nan zaune inda ya barta, kamal ya had'e fuska sbd yasan tabbas wani mugun abu zee tayi.
Dining area ya nufa ya had'a abinci a plate ya rufe, tukun yace. "Ke zonan ki ɗauko wannan biyoni da shi.
Yayi hakanne sbd yasan halin mama in har yace zee taje Yaya mohmod na kiran ta kuma tasan tayi laifi ba zata yadda taje ba.
Zee bata kawo komai aranta ba ta tashi ta d'auki plate d'in abincin tabi bayan sa zuwa sashensu na mazan gidan.
Suna zuwa d'akin yaya Kamal ya karb'i abincin, tukun yace bani hannunki nan." Ya fad'a fuska babu alamar wasa.
Hakan yasa ta mik'a mishi hannun, tukun yafinciki hannun nata suka nufi parlourn yaya mahmod.
Gabanta taji yayi mugun fad'uwa sbd tasan tabbas akwai wata ak'asa.
Yana zaune hakimce kan kujera fuskar sa babu annuri ko kad'an, idanunsa sunyi jajir ya d'ago ya kalli zee!
Saida takusa sakin fitsari awando sbd tsorata da fargaba, sakin ta yaya Kamal yayi had'e da juyawa ya fice.
Kneeling tayi agaban sa tare da had'e hannunta duka biyu alamar rok'o, tukun tace. "Dan ALLAH yaya kayi haƙuri na tuba bazan kuma ba..."
Wani kallo ya mata da yasa taja bakin ta ta tsuke jikin ta na rawa.
Tashi tsaye yylayi had'e da d'age carpet ya zaro belt. Azabure tayi baya tana k'ok'arin tashi.
Yayin da shi kuma ya buɗe baki cikin cool voice ɗin sa yace. "Inhar kikayi yunk'urin guduwa ko kikamun ihu kin k'arawa kanki laifi marar kunyar k'arya, ai na zata tunda zaki iya cin zalin yaro k'arami kamar wannan to zaki iya jure duka ma, ashe ke k'aramar marar kunyace ko?"
Girgiza kai kawai ta keyi ta kasa cewa komai. Yayin da shi kuma ya matso kusa da ita bata ankara ba ya fara tsula mata guda!
Ƙara tasaki shi kuma ya cigaba da jibgar ta duk kwalliyar ta ta goge, d'aurin d'an kwalin ya cire gashin kanta duk ya yamutse.
Kuka da ihu had'e da magiya kawai take mishi amma yak'i dena dukan ta.
Sai da ya mata lilis tukun ya saki belt d'in yana cewa daga yau ki sake k'ok'arin yin zalinci ki gani wawiya k'azama kawai, sannan inaso kisani duk ranar dana kuma kamaki kina kallo na ko k'ok'arin zama kusa dani da wasu kalamanki na hauka you should be in trouble, kinji ko baki jiba?" Ya fad'a atsawace.
Jiki na rawa tace. "Naji wlh." Yana huci yace. "Get out of my parlour."
Jikin ta na kyarma ta d'auki d'ankwalin ta ta fice, fuska jage l-jage da hawaye da majina ta nufi part ɗin su

Tsaki yaja had'e da cewa. "Zan saitawa duk yarinyar kanta ke rawa acikin ku, ai naji dad'i sosai dana dawo aiki anan." Kukan khalifa da yaji ya saka shi yin shiru.
Bed room d'in ya koma, da sauri ya nufi kan bed d'in cike da tausayawa ya d'auki yaron.
Aparlour ya fito da shi ya bashi ruwa yasha, tukun ya saɓa shi akafad'ar sa ya nufi sashensu hjy hakimah da shi.

Abba na zaune da hjy hakimah adining area yana cin abinci kasancewar girkin hjy ne yau, mahmod ya shigo d'auke da khalifa.

Tab'e baki hajiya tayi saboda aganin ta meye auin wani kama d'aukar yaro yana yawo shi dashi.
Isowa yayi gurinsu ya duk'a yana gaida abba.
Amsawa Abba yayi fuska asake yana kallon khalifa da goshin sa.
Abba yace. "Subahanallahi meya sami goshin khalifa haka?" Kafin Yaya Mohmod yace wani abu mama jummai ta shigo parlourn tare da zee rik'e ahannun ta.

Kallo d'aya yaya Mahmoud ya musu ya d'auke kansa, tukun yace Abba zan maka bayani gameda fad'uwar khalifa." Ya fad'a yana mai mik'ewa tsaye, yayin da abba ya ajiye cokalin dake hannunsa sabo da ya fahimci wani abu game da mama jummai data shigo yanzun.
Yaya mahmod kuwa sakkowa yayi daga dining area d'in yana k'ok'arin shiga parlourn hajiya sbd ya samu ko ummi ya bata khalifa ta mayar da shi.
Mama jummai tayi k'ok'arin saita kanta, kafin ta zauna gefen kujera, yayin da zainab ke tsaye tana ta kuka idanuwa sunyi jajir.
Mama tace. "Mahmoud gunka nazo zaka kuma tafi." Tamkar yayi tafiyarsa yaji sai dai hakan bazai faru ba kodan sbd y'a'yan ta dole ya bata girma.
Yayin sa hajiya da Abba suka sakko parlourn atare, mahmod kuma ya juyo fuska babu walwala yace. "Gani mama!"
Cikin munafurci mama jummai ta duk'a ta gaida abba dake tambayar zainab lfy take kuka?
Mama jummai tace. "Eh wallahi alhaji kasan yaran nan basa jin magana, laifi tayiwa yayan su Mahmoud shine na taso ta gaba ta bashi haƙuri ya kuma sake mata hukunci yadda gobe ba zata kuma ba."
Shiru kawai yaya mahmod yyi aransa yana mamakin makircin mama jummai. Yayin da abba kuma yace. "Kai sarkin zuciya yanzu daga zuwan ka yau zaka Fara dokar mun yara sabo da ALLAH."

Wallahi Abba khalifa yaya zee ta ture ya fad'o daga kan kujera kansa ya bugu da tayis, shi ne zan d'auke shi sai yaya yazo ya dauke shi. "Cewar bilkisu" da shigowar ta parlourn kenan da unifoam d'in islamiyya ta la'asar ajikin ta, tazo ta biyowa salim sutafi islamiyya kasancewar sa'annin junane ita da shi.

Wata kunya da dana sani had'e da nadamar zuwa sashen ya dabai-baye mama jummai.
Cikin inda l-inda tace. "Oh d'an yau ai maganin ki kenan gara daya dake ki."

Yaya mahmod kuwa murmushi yayi aransa yana jin bilkisu ta burgeshi, dolema ya mata kyauta duk da yasan yau sai mama jummai ta dake ta, sabo da yasan munafurci ya kawo su danta had'a shi da Abba shine tazo da wannan makircin.

Abba kuwa sarai ya gano makirci mama jummai taso ta had'a, amma sai bai nuna mata ba ko a fuska yace kawai. "Allah ya kyau ta to." Tukun ama jummai da zee suka fice suka bar bilkisu nan na jiran salim ya fito sutafi islamiyya sabo da har 3:30 pm tayi.
Abba ya girgiza kai had'e da kallon mahmoud yace. "Kawo khalifan."
Bbu musu ya nufi gurin sa ya mik'o mishi.
Taɓe baki hjy tayi ko ajikin ta da fad'uwar khalifan balle ta tausaya mishi, saima haushin mahmood taji akan sbd wannan yaron zai yiwa zainab irin wannan dukan.
Yayin da abba kuma yay ta masa wasa, tukun daga bisani ya tashi dashi ya nufi sashen anty.

Tsaki hjy taja had'e da cewa. "Daga yanzun karna kuma ganin ka d'auki yaron nan, akan me zaka kama wani d'aukan sa?"
Shiru kawai yayi bece komai ba, domin ko yasan k'ila kishi hajiya keyi da uwar khalifa.
Ahankali yace. "Kiyi haƙuri hajiya ta bara naje gurin nura (Babban abokin sa Kuma shima d'an jarida ne.) Yana parking space yana jirana."
"Sai ka dawo to" ta fad'a tana k'wala wa salim Kira akan ya fito bilkisu na jiran sa, adai-dai nan kuma Abba ya shigo parlourn, yayin da yaya mohmod kuma ya futa.

Hijab nata take k'ok'arin sakawa ummi, maryam da naja'atu(y'ar makotan su ce kuma tana son k'awance da khadija tunda suka Fara had'uwa a islamiyya)
Duk suka shigo parlourn khadija na murmushi tace. "Ina ta sauri karku jira ni saiga kuma."
Naja'atu tace. "Kin san kuwa ana dukan makara." Cikin zaro ido khadija tace. "Da gaske Dan Allah?" Kasancewar tana da tsoron duka.
Dariya suka saka gaba d'aya suna fitowa sukayi waje.
Ahanya naja'atu ta dubi khadija tace. "Yaya auwal yace yana gaida ke." Kicin kicin da fuska khadija tayi had'e da cewa. "Waye haka Kuma?"
Hmmmm! "Yayana ne khadija"
"A ina ya sanni to?"
"Yana ganin wucewar mu atare cikin y'an kwanakin nan."
Shiru kawai khadija tayi. Yayin da ummi da maryam kuma sukayi murmushi.
Basu jima ahanya ba suka isa islamiyya sabo da babu nisa sosai dasu.

****************

k'arfe 6:pm aka tasosu daga islamiyya.
Tafe suke suna sauri sabo da hadarin daya taso da iska had'e da buji. Su duka suke tafiya harda bilkisu da salim da hafsat. Gaba d'aya khadija atsorace take sabo da tana tsoron walk'iya da tsawa.
Basu ankara ba sakaji an fara yayyafi, sauri suke har suka iso layin su, naja'atu ko sallama bata musu ba ta tura get d'in su ta shige gida.
Yadda ruwan ya sakko sosai duk ya jiƙa musu jikin su. Suma su khadija da sauri suka tura get suka shige. Babu kowa aharaban gidan, hafsat ce kawai ta wuce part nasu, yayin da bilkisu ta wuce part d'in kakar su sabo da tasan inta koma me k'watarta gurin mama jummai sai Allah. Yayin da su kuma gaba d'aya suka shige babban parlourn gidan.

Wata uwar tsawa had'e da walk'iya aka saki tare da cida.
Wata uwar k'ara Khadija ta saki, afirgice tayi k'ok'arin guduwa tana ture su ummi dake gaban ta. Akuma dai-dai lokacin aka d'auke nefa.
k'ara ta kuma saki, bata ankara ba taji ta tayi karo da mutum, atsorace ta cikwikwiye ko waye, sabo tsabar tsoro da firgita da tayi. Sai dai kuma lokacin da hancinta ya shak'o mata k'amshin turaren sa ta gane ko waye.
Zaro ido tayi atsorace tana k'ok'arin janye jikin ta taji anficiko ta. Adai- dai nan kuma aka tada injin parlourn ya gauraye duka da haske....✍🏼

🥰😝🤔 waye to wannan???

Bana post week end muhade Monday in Sha Allah.inkuma naga zafafan comments kuga update..🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾

🌹A GIDA D'AYA🌹
🏘️🏘️

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾


Story& written by mmn fareesa


🅿️5&6

"You are very stupid!"meke damun kune Wai?"Yaya mahmod yafad'a cikin kakkausar muryansa "yana janye ta dg jikinsa"inbacin rawa bbu abinda jikin Khadija keyi sbd tsabar tsoro akan abinda tayi."
Ummi kuwa da Maryam "sun tausayawa Khadija datayi gigin yiwa Yaya Mahmoud laifi"jikinsu na kirma suka Fara k'ok'arin barin parlourn "sbd ganin irin kallon dayake binsu dashi.gashi har yanzun ruwa akeyi"bbu kowama a parlourn duk suna ciki"cikin marairai cewa tamkar zatayi kuka taja da baya,kanta aduk'e tace". dan ALLAH kayi hakur....keep quiet!zaki karb'i hukuncin laifinki! sbd gobe inkina tafiya kirik'a kallon gabanki."zaku wuce kubawa mutane guri ko kuwa?"yafad'a Yana kallon su ummi dake tafiya suna waiwayen khadija.azabure sukabar parlourn"kallon Khadija yyi yaga tana sharan k'wallah yaja tsaki had'e da cewa muje"zaro ido tayi azuciyar tace".
naje Ina Kuma?nidai nashiga ukku wlh"batada zab'in dayawuce tabi bayan sa."

"binsa tayi tana sauri sbd ganin yamata nisa "ga ruwa anayi har lokacin.tunani takeyi aranta anya zata iya zama agidan nan?"sbd kawai ta bangajesa batasaniba ".shine yazama wani laifi babba"
" A bakin wani corridor suka tsaya, taga yabud'e k'ofar yashiga.gabanta yafad'i sbd itadai gsky batasan Zama da namijin daba maharraminta ba.bakin k'ofar ta tsaya tayi kneeling down."

Yaya mahmod kuwa Zama yyi kan kujera Yana latsa waya"Yana d'ago kansa yaganta tana kneeling down.tab'e baki yyi had'e da cewa K``zonan"!
kayi hakuri dan Allah bazan iya Ida shigowaba.zaro ido yyi Yana nuna kansa had'e da cewa kina nufin nizanzo kenan?girgiza kanta tayi had'e da tashi....adedenan aka saki tsawa" "wata k'ara Takoma saki.mamakinta na tsoron tsawa yakamashi"saidai yadanganta abun da

Please Login or Register in order to submit comment