Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

๐Ÿ˜๏ธ๐Ÿ˜๏ธ

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ



Story & written by mmn fareesa

Wannan shafin nakine halak malak mmn nurul huda๐Ÿฅฐ


๐Ÿ…ฟ๏ธ19&20


Atake jikin Khadija yafara rawa,sbd yadda ta lura da fuskarsa tamkar besan miye dariyaba". atsorace ta dubi Tahir dake cewa"Khadija nalura bakisan kulani ne kawai...kaga dan Allah mlm kayi hakuri "(lacturer d'insu ne)ko a skul bana kula kowa balle agida.ga yayanmu nan tafe,nasan nizai Kira...shiru tayi sbd k'amshin turaren sa yashaida Mata zuwansa.dago kansa Tahir yayi yakoyi arba da Yaya mahmod daya had'e fuska tamkar hadarin gabas.
shikanshi Tahir yaji shakkarsa da kwarjininsa.kallonsu yyi .hakan yasa Khadija saurin jada baya tanacewa "wlh Yaya shine yatareni akan Dole natsaya"wlh nadena bazan komaba..cikin muryansa dake bawa marar gsky tsoro yace".K!wuce kishiga cikin gida"jikin Khadija nakirma ,tana hard'e k'afafuwanta ta juya da nufin ta wuce"mlm Tahir yayi saurin shan gabanta Yana cewa" haba yayanmu pls amatsayi na namalaminsu a sk....wawan marin daya mahmod yad'auke shi dashine" yasakashi yinshiru ,bek'arasa mgn ba." da sauri ya shafa hancinsa dayaji Alamar ruwa....wani mugun kallo Yaya mahmod yawatsamishi"cikin kakkausar muryansa yace".this is the first &last dazaka sakewa wata mace hakan"mitssww lusari kawai.... yafad'a Yana finciko Khadija da k'arfi da hannunsa.yamaidota bayansa"Yana adduar Allah yasa Tahir yayi yunk'urin cewa zairama marinsa.yafitar Masa da hakora...Tahir kuwa ransa yab'aci dayaga jini ahancinsa"yakuma lura mahmod bawani girmansa yyiba.cikin zafin zuciya yace ".aiba marina zakayiba katafi"kamata yyi mugwada k'wanji da juna.yaya mahmod na huci "ya juyo azuciye yamatso kusada Tahir yana cewa "nafi buk'atar hakan "asannan kuma Tahir yagane fusakarsa (d'an jarida Mai gsky da ake yayi)azuciye yashak'i wuyan Tahir yabashi wani wawan punch... k'arar azaba Tahir yasaki Yana k'ok'arin ramawa"yasake kawo wani punch d'in..anan suka fara gwada k'wanji. adedenan kuma Abba suka shigo layin "Yana back sit isah driver najansa..Khadija kuwa innalillahi wa inna ilaihir raju'un kawai take maimaita arud'e"sbd ganin gaba d'aya Yaya Mahmoud yafi k'arfin Tahir"kafin tahir yakai duk'a 2, ya mahmud yakai 3"sbd Yaya mahmod jikinsa ya horu da training...dan Allah kayi hakuri karabu dashi "karkayi kisan Kai mushiga ukku! khadija tafad'a tana k'ok'arin matsawa kusa dasu ,sbd taga bbu kowa alayin...horn d'in da isah driver yyi yaja hankalin Khadija "tana kallon motar,da sauri ta iso sbd hango Abba ta glass datayi"cewa take Abba Kar Yaya yyi kisan Kai yaya mahmod...asukwane Abba yafito Yana kallon su mahmod da Tahir dake artabu...cikin tsawa Abba yace". mahmod karabu dashi nace!karkayiwa d'an mutane illah...

Yaya mahmod na huci ya hank'ad'a Tahir ,kansa yabugi motarsa"cikin fushi yace muddin nakoma ganinku atare da ita" saina canzamaka kamanni.
"mittww! Yanafadin hakan yanufi Gurin Khadija dake tsaye yafinciki hannunta cikin rufewar ido"suka nufi k'ofar shiga get d'in gidan.sbd yamanta da Abba nagurin..

Abba kuwa girgiza Kai kawai yyi"sbd yasan Dole saiya sauka dg dokin zuciya tukum. yatambayeshi meya had'ashi da wannan saurayi?

Rufe motar Abba yyi"yanufi Gurin Tahir dake shafa kunburarrar fuskarsa.abba yace" subahanallahi meya had'ashi da Kai yaro?kasa cewa komai Tahir yayi,illa kawai yyi k'ok'arin bud'e mota zaishiga.abba yyi saurin rik'emishi hannu Yana cewa"kayi hakuri yaro kaji?ni mahaifinsane zankuma d'auki mataki.amma meya had'aku?innabarka katafi kana haka aida damuwa ko?karkayi driving jikinka bbu dad'i, gakuma b'acin rai.
nasan halin waye mahmod baya shishshigi ko fad'a inba mak'ura aka kaishiba...inkuwa hakan yafaru za'ayi bbu dad'i.yanzun kaga ankusa magrib"ga chemist can bayanmu.muje adubamun kai."gaba d'aya sai Tahir yaji zuciyar sa tasaki dg fushi da b'acin ran dayakeji" tunani yakeyi aransa Abba wane irin mutum ne na k'warai haka?kwata kwata be goyi bayan d'ansaba "gashi yanabashi kulawar dakoshine yahaifesa sai hakan.muje Mana kayi shiru" rufe k'ofar motar d key Tahir yayi.hakan yasa Abba yajuya yafara tafiya,Tahir yabi bayansa...yyinda isah driver yawuce ciki da motar...

Ya mahmod suna shiga cikin get"maimakon yasake mata hannu, ta wuce part nasu "saiyajata zuwa d'akin sa."kuka kawai Khadija keyi tana mishi magiyar yayi hakuri karya daketa"sbd azatonta dukanta zaiyi.shikuwa har cikin ransa yakejin kukanta"cikin husky voice yace"inbakiyimun shiruba !zanbige Miki wannan bakin naki...tsit kakeji tayi shiru,jikinta sai rawa yakeyi cike da tsoro.da hannu 1 yasaka key ya bud'e d'akin"suka shiga Yana rik'e da tafin hannunta.sakinta yyi ta zauna kan carpet ad'od'ane..

Khadijaaaaaaa!yakirata cikin wata iriyar murya "yace"
da gaske wannan guy d'in malaminku ne?Murya na rawa tace".eh wlh"
Tun yaushe yafara Miki mgn?um um jiya ne... tsaki yaja yalumshe ido Yana dafe kansa.dukan dayayiwa Tahir besaka yaji sanyi aransaba.khadija ban hanaki kula samariba?cikin sanyin Murya tace".Yaya ka hanani"
shine Kuma kika tsaya sbd raini ko?tace"wlh ah ah Yaya"shine yasha gabana"Dole natsaya su ummi Basu tsayaniba suka shigo gd. kayi hakuri dan Allah bazan komaba.sannan dan Allah zantafi Kar wani yaganni anan"tab'e baki yyi had'e da cewa"Babu inda zakije saikin karb'i hukuncinki"sbd meyasa yanzun bakizowa kimun gyaran d'aki?kanta ak'asa tace"bansan laifin menamaka ba yaya!Inna gaidakai baka amsawa" koyimaka sannu d xuwa Yaya saika shareni "kuma banjin dad'i araina ...wani sanyi yaji aransa"sbd ko Yaya tadamu dashi.waye yaja Khadija?kecefa"yafad'a cikin cool voice Yana kallon ta.kanta ta d'ago taga ita yake kallo"janye idanunta tayi tace" nadena dan Allah.

Khadija meyasa kikafison kib'atan raine?kwanaki nakiraki naga kinmayi blocking nawa meyasa kiyin hakan?
Zancire block d'in Yaya yanzun dan Allah !gayacanma ana kiran magrib...hmmmm nagane wayonki yarinya"kije kiyi sallah,inkin gadama karki cire block d'in nawa da kikayi.hukunci kuma zan hukuntaki akan laifinki"da sauri ta d'ago kanta ta kallesa.taga Yama mike tsaye da nufin yashiga bed room d'in sa..yayaaaaaa!uhummm Khadija bazanfa hakuraba " gara kije kawai..hakan yasa ta tashi tafice batare data ce komaiba...

****************

bayan sallar isha'i"Abba ne zaune da mahmod da Tahir akusa dashi"Abba yadubi Tahir yace".kayi hakuri my son kaji ?Khadija itace wacce mahmod zai aura,ita kanta batasaniba.dg yanzun inkayi yunk'urin tsaida mace bata tsayaba"to kaje gurin magaba tanta ka nemi izini.mahmod kishine yasashi aikata hakan.sbd haka kubawa juna hakuri"kuma dg yau kunzama abokai na had'a abotar da kaina.abba yafad'a Yana murmushi.

Tahir yana murmushi yace". nagode k'warai da karamcinka Abba"insha Allah nayafe masa komai ya wuce"mahmod kayi hakuri bansan asaka muku rana da Khadija ba "da wlh bazan tsaida itaba.na lura a skul bata kula kowa shine nabiyota har gida..
Yaya mahmod fuskarsa bbu yabo bbu fallasa yace ".bbu komai Allah yakyauta gaba"Tahir yace Abba kayi hakuri bazan iya abota da wanda yafi k'arfina ba! yadakeni kuma"dariya Abba da Yaya mahmod sukayi atare.
Abba yace" ah ah aina kullah abotarku"sbd haka asannu zaku saba da juna"mik'ewa tsaye Tahir yayi Yana cewa"to shikenan Abba nagode zan wuce gida.
Abba yadubi Tahir yace" kasan ummi da Maryam dasuke tare da Khadija?โ€tahir yace"ah ah bazan iya shaidasuba Abba! inadai ganinsu su ukku"amma bazan iya shaidasuba"sbd banfi sati d'aya da Fara lacturing a skul nasuba.kuma a department d'in su Khadija nike koyawa.abba yace" to shikenan Inka dawo wani lokacin zanturo maka ummi da Maryam "acikinsu kazab'i wacce tamaka tunda karasa khadija.naji ka kwantamun arai"inkuma acikinsu bbu wacce tamaka bbu damuwa.tahir na murmushi da yaba kyawun halin Abba aransa yace". insha Allah Abba !jibi Friday zandawo nagode k'warai" Allah yak'ara girma.daga hakan sukayi sallama yafice"

Abba yadubi mahmod ,Wanda beji dad'in had'in da abba yace zaiyiba da tahir acikin yaran.ahankali yafara mishi nasiha akan yarage zafin zuciya da kishi haka"sannan yace" insha Allah dakaina zansanarwa Khadija maganar aurenku nabari adan kwana2 ne...Yaya mahmod kansa ak'asa yace" to shikenan Abba.

b'angaren zee kuwa"tunda ibbi yafara driving d'in tafarajin fad'uwar gaba,sai surutu yake janta dashi "saidai tayi murmushi kawai bata cika mgn ba.sannan ta lura yau ibbi yanacikin farinciki sosai.

Yana k'ok'arin yin parking ta dubeshi tace".Wai sweet heart yau farin cikin da murnar mekakeyine?โ€wani shu'umin kallo yamata "kafin yyi murmushi yace".ayau wani buri nawa nakesaka ran cikarsa.gabanta taji yafad'i"batace komai ba ta alak'anta abun da tsoron komawa gidane takeyi "sbd Kar daddy ko Yaya Kamal yarawo.
Hotel ne inda za'a yi birthday party d'in,acan wani fili akayi decoration's.acan suka nufa sai shishshige mata ibbi keyi tanaja da baya"har suka iso gurinda za'a yi party suka zauna.

Anata rawa dabawa me birthday d'in gift...har aka Fara Kiran magrib,yyinda zee keta damun ibbi ita gida zataje.
Kallonta yyi yace". muje akwai siyayya danayi miki nabawa abokina ajiya muje kirakani nakarba.batace komaiba saima murna datayi aranta tabi bayanshi.

Acan saman bene room12 suka tsaya"amamakinta saitaga yasaka key yabud'e k'ofar"kallonsa tayi ,kafin tayi mgn yace muje ciki Mana "abokinane yakama d'akin ,yakuma bani key d'in yace" mudakko shopping d'in.nidai gsky bazan shiga d'aki na hotelba amatsayina na budurwa"inwani yaganmu yazargemufa? d'an Jim ibbi yyi,kafin yace ".shikenan shiga suna gefen bed ki d'akko ,saimu wuce namaidamishi key d'insa nakaiki gida ko kuwa?โ€

batakawo komai arantaba ta shiga cikin room d'in"ibbi yyi saurin binta abaya,yarufo k'ofar da k'arfi yadanna key....๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

๐ŸŒนA GIDA D'AYA๐ŸŒน
๐Ÿ˜๏ธ๐Ÿ˜๏ธ

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ



Story & written by mmn fareesa

Alast page ansami matsala Gurin number nasaka 12&22 inaso nasaka 21&22 Ina fatan angane...


Wannan shafin nakune
mmn fareesa fans page,YAU DA GOBE paid grp,mmn shukra novels,zumanta novels grp & A GIDA D'AYA fans Ina yinku sosai guys acigaba da zazzafan comments๐Ÿฅฐ๐Ÿ’–๐Ÿ’”


๐Ÿ…ฟ๏ธ23&24

.....Ayanzun haka zainab na cell atsare anyanke Mata hukuncin wata 3 agidan yari tareda horo Mai tsanani".ko tarar naira dubu dari 300"sannan kotu ta buk'aci da iyayen zainab Dole sukula da lafiyar Ibrahim."sannan inhar Ibrahim yaji sauk'i kotu zata hukuntashi akan yunk'urin fyad'en dayaso yiwa zainab...sbd abokan Ibrahim sunzo Sunbada shaidar dama yanada mummunan k'udirinshi akan zainab" nason b'ata Mata rayuwa.wannan shaidar itace ta wanke zainab da fitowarta sai Allah wlh....cikin kuka mama jummai tace"amma Yaya basai a biya dubu dari 300K d'inba afito da ita.

Wani mugun kallo natsana da takaici daddy ya watsawa mama jummai."yanajan doguwar tsuk'a yace".ko yanzun bata b'aciba saikije da kanki kibiya kifito da ita.aikin banza da wofi kawai..Abba yadakatarshi sbd ganin akwai yara acikin parlourn bbu dad'i aci Mata mutunci gaban y'ayanta.mama jummai batace komai ba"saidai ta Lula tunani akan mlm d'aya sanar Mata tashin hankali zai tunkaro gidan babba!Ashe wannan ne?inkuwa haka be bazata koma zuwa girin mlm ko boka ba..... mahmoud shine yad'auki nauyin rashin lafiyar Ibrahim"cewar Abba daya katsewa mama jummai tunanin ta.

Abba yaci gaba da cewa"nikuma zanbada dubu dari 300 "akan tarar, sai daddynku yahana"nakuma fahimceshi dayamun bayanai sosai.da ido mama jummai ta kafe Daddy tana mishi wani irin kallo...inno ta karb'e zancen da cewa"ai gara abar y'ar iskar marar kunyar ta horu agidan kaso"dg baya intadawo tacanza hanya tadawo mik'akk'iya"amma bello kamun daidai wlh daka Hana adamu yabada kud'in"Kuma intadawo guna zata koma nina kula da tarbiyyar jikokina!tunda keda kikayi nak'udarsu kin kasa.ke yanzun inda ya haikemata fa?ba fata akeyiba takamiki guzirin jika shege fa?dukda ana cikin wani yanayi saida su Abba suka murmusa.abba yace yanzun dai ayi hakuri,kekuma jummai hakan ya Zama iznah agareki "inzaki nutsu kiyi hankali da kyakykyawan tunani to"inkuma bazakiyiba ruwanki.kowa yatafi na sallami kowa"cewar inno tana k'ok'arin barin parlourn.yaya mahmod dake zaune yanata aikin kallon Khadija da kanta ke duk'e" sbd hararar da hjy ke aikamata.soyakeyi su had'a ido"ita kuwa batama san yana kallon ta ba.
Hafsat kuwa itama ta k'asa sakewa sbd Yaya Yusuf na gurin"da d'ad'd'aya da d'ad'd'aya sukayita ficewa dg parlourn "khadija ma ta yunk'ura da niyar tashi sbd taga anty ta tashi"tana waigowa d nufin taduba khalifa ta d'aukeshi su wuce.tahangoshi jikin Yaya mahmod" yanata wasa da fuskar Yaya mahmod yanajan tattasan sajensa daya zagaye fuskarsa yak'ara mishi kyau.janye idanunta tayi ta juya da nufin ta fice" sbd taga su maryam harsun mik'e suma zasu shiga sashen hjy.parlourn yarage dg ita sai Yaya mahmod da Yaya kabeer dasu Yaya Yusuf.

"zoki karb'esa"tattausan muryansa yadaki dodon kunnen ta.
"Ahankali ta juyo tana tafiya ,ta iso gurunsu"kallonta yyi Murya can k'asa yace".meyasa baki dawoba jiya?"wato ga abokin wasanki ko?kasa cewa komai tayi"kawai ta mik'a hannu da karb'i khalifa"shikuma yak'i zuwa saima yasaki kuka"d'agowa tayi daga dukawar datayi"ahankali tace".kayi hakuri dan Allah abinda yasa banjeba hjy ta hanani zuwa wajenka!batajira cewar saba ta juya ta fice ,yabita da kallo Yana lumshe ido had'e da kissima abubuwa aransa"

*******************
Bayan wasu kwanaki...

Hjy rabice (mmn khairat)zaune kan kujera itada hjy iklima"hjy ta dubeta tace". gsky rabi dakamar wuya alh ya yarda ace bikin su su biyu za'a yi"kidai bari ayi wannan d'in " bayan wasu watanni ko shekara 1 sai ayi nasu da khairat d'in. sbd ni band'auki bikinsa da muguwar yarinyar nan ba biki"bikinsu da khairat shine biki... khairat dake zaune kan carpet" tawani juya idanuwa tana fari dasu.

Hjy rabi tadaiyi shiru kawai Amma ba hakan tasoba"saidai Tasha alwashin muddin akayi auren khairat da mahmod tofa Dole khadija tabarwa y'arta mahmod..

Yau yakama Friday Kuma kwana 9 kenan da zuwan Tahir"ayau Kuma yakira mahmod yasanar mishi zaizo bayan tasowar juma'a.yaya mahmod kuwa yasanarwa Abba"
Abba yasaka Maryam ta gyara parlourn bak'i"kafin yace mata taje itada ummi su shirya zai aikesu wani waje driver zai kaisu bayan andawo sallar juma'a.
tahir dg masjid yanufo gidan Abba"har cikin ransa yaji yanason Abba zaikuma iya zab'ar guda aciki Koda bayaso sbd mutuncin abba.sbd Mata shi badamuwarsa bace gasunan ma .akwai masu cewa suna sonsa Yana kaucewa...da wannan tunanin ya iso gidan"Yaya mahmod yaimishi iso zuwa parlourn bak'i"bayan sun gama gaisawa"yawuce yasami ummi da maryam yace".guda ta d'auki drinks takai parlourn bak'i" guda ta shirya abincin mutum1 takai acan.
Ummi tazunbula hijab har k'asa"Maryam ma haka suka fice"Abba dake kallonsu yyi murmushi kawai"Amma ransa Yana bashi Koda Tahir zaizab'a to k'ila Maryam zai d'auka sbd tafi sakin jiki da mutane da sakin fuska..

Tahir na zaune kan kujera yayi k'ofa k'uri da ido"ummi dake gaba tayi sallama"tashigo Maryam nabayanta.ajiye tray d'in hannunta ummi tayi"batare data kallesa ba tace Ina wuni?kallonsu yyi su duka Yana cewa lfy lau sannunku"ummi batace komai ba ta juya sbd tagane shine wanda yazo Gurin Khadija" Kuma malaminsune tana ganinsa a department d'in su Khadija..Maryam tace "ya gida ya aiki??yace" alhamdullh!Masha Allah Akira maka itane?tana nufin Khadija ,sbd kosu basusan cewa itace Yaya mahmod zai auraba.yana murmushi yace".ai waccan data fita ita nazo gurinta"Kuma tatafi.d'an Jim Maryam tayi kafin tace".to bara naturota "okay yace Yana lumshe ido.tunani yakeyi har ransa yaji ummi ta Masa"sbd yanason mace Mai aji marar hayaniya"yalura tunda ta shigo sau1 tayi mgn.

Maryam nafitowa ta nufi part d'insu"Abba na zaune inda tabarshi"yakalleta yace".bak'on yatafine?Maryam tace".ah ah Abba cewa yyi Gurin ummi yazofa! murmushi kawai Abba yyi "afili yace ikon Allah!banyi zaton ummi zaiceba wlh "jeki kice mata nace taje tanada bak'o...

Ahankali ummi tashiga"ranta fal da tarin tambayoyi tamishi sallama.ya amsa cikeda nutsuwa ,zama tayi nesa dashi.
"Ahankali yace "Masha Allah my baby dafatan kina lfy"nasan kinada tarin tambayoyi fal aranki"sbd kinganni da Khadija ko?dama. zuwan nakine nazo kwanaki tamun hanyar zuwa gurinki sbd ni malaminsu ne. ajiyar zuciya tasaki aranta.dama ita tun wancan lokacin data gansu tare taji gabanta yafad'i"
kinyi shiru baby koban Miki bane?uhummm!kawai tace "tana sunkuyadda kanta k'asa.acikin Yan mintina saigashi duk miskilancin ummi tafara sakewa da Tahir hardasu murmushi.koda zai tafi har get tamishi rakkiya. bayan yace zai kirata da wayar hjy databashi number d'in"zata rik'e wayar da dare saiya Kira"kafin yakamata tata wayar.abba na zaune kan bene Yana hangensu yasaki murmushi afili"Yana kissima zaiyi binkice a skul nasu Khadija gameda halayen tahir"dama tun kafin yazo yagano mahaifinsa Ashe abokinsane...

Acikin kwana2 Tahir yyi wata iriyar shak'uwa da ummi.suna zuba soyewarsu son ransu.ayanzun haka antsayar d mgn bayan 2 yrs za'a bashi ummi.yyinda Yaya Yusuf yakoma Gurin aikinsa"suna zuba love shida hafsat.

Ayanzun haka daddy ya hana kowa zuwa duba zee"acewarsa saitakai 3 month kafin asakota gaba d'aya.data dawo Kuma sure zai Mata wlh Babu d'aga k'afa..
Gefe guda Kuma Mahmoud yanata k'ok'arin yin duk abinda yadace akan ibbi yasami lfy kodan sbd a hukuntashi akan abinda yaso yiwa zainab "Kuma antabbatar hakan halaiyarsace..ubansa alh Ayuba yad'aure mishi gindi.har Yana ikrarin Dole zee ta auri d'ansa tunda ita ta illatashi"Yaya mahmod kuwa yalashi takobin Koda abinda yamallaka zaik'are zee bazata auri d'an alh Ayuba ba".da ake zargin Yana k'ungiyar asiri ,Kuma gashi d'an siyasa ne...wannan kena.

**************
Zaune alh mudi da alh Ayuba suke gaban wata k'atuwar tukunya.mai fad'i da ruwa bak'i k'irin aciki"jikinsu sanye da wasu bak'aken Kaya da Jan hula"wani hayak'i yafito dg cikin ruwan ,sunawani irin bullllllll!kamar suna tafasa" fuskar Yaya mahmod ta bayyana"saikuma wani haske aciki yafito.hakan yasa fuskar ta b'ace"
wani surkulle alh mudi yyi"saiga wani mutum tamkar dodo bango yatsage ya bayyana agabansu. Yatsun k'afafunsa irin na doki"ga k'wala k'walan idanuwa,yawatse hakora tamkar na horo"alh Ayuba saida yatsorata.๐Ÿคฃ๐Ÿ˜‚ cikin wata iriyar murya yafara mgn kamar haka!jininsa yanada k'arfi"wajen tsoro da addua"hakan yasa bazan iya kashesheba!ta hanyar shanye jininsa"yanada ruk'o da adduo in tsari da karatun alk'ur'ani"sbd haka yanzun yafi k'arfinmu kashesa.saidai wancan nufin naku na farko k'ila ya tabbata.
shima Kuma sai in Yana cikin b'acin rai Mai tsanani ko yanajin sha'awar mace ,Koda janaba ajikinsa shine zamuci galaba sosai akanshi.kasancewarsa mutumne shi dabai iya fushiba.hhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhhh!!!yakece da wata iriyar mahaukaciyar dariya"hayak'i yagauraye d'akin tare da wata tsawa"fit yab'ace agabansu...

Wata dariya alh mudi da alh Ayuba suka saki.

Alh mudi yace".aidama nayi alk'awari kozanyi yawo tsirara sainaga bayan matsiyacin yaron nan "daya b'atamun suna,hakan yasa banci zab'en d'an majalissaba"nayi asaran lokacina da kud'ina da Kuma mutuncina.hakan yasa nalashi takobin kassara mishi rayuwa kota halin kak'a..alh Ayuba yakarb'e zancen da cewa nima haka "tunda y'ar uwarsa ta lalata wa yarona d'aya Tak Dana mallaka aduniya rayuwa.nabukaci inta fito dg gidan yari t aureshi"yahana tare da gayan mgn.naci burin sainaga bayanshi...

Bayan sati 2

Mama jummai ce zaune tayi tagumi.dukta rame tayi bak'i sbd damuwar halin da zainab take dakuma watsar da itadin da daddy yyi.baya amsa gaisuwarta baya cin abincin ta,baya kiranta shimfid'arsa.ga hafsat da bilkisu inno ta karb'e.gaba d'aya batajin motsin kowa agidan.dama Kamal da Hakeem banan sashen sukeba.sunacan sashen mazan gidan"sai cin abincin ke kawosu da gaisheta da safe zuwa sashen.dg ita sai aikinta kawai kezama parlourn.abin gwanin ban tausayi"daddy kuwa duk yana lura da ita da komai nata"yabarta ne kawai sbd ta saduda. amma shikanshi Yana tausayin halin datakeciki ,fatansa ta gyara rayuwarta da yaranta. "duk Mai Imani dole yatausaya mata.fitowa yyi dg d'akin sa"yanufi parlourn ta...dakatawa yayi sbd jin maganar ta ta waya"tana cewa"na cuci kaina halima ,mijina yatsaneni gaba d'aya nayi nadamar kuskuran Dana aikata "kiduba kiga yarana duka bbu ko guda agurina suna hannu inno"yazanyi da raina ,bansan halin da zainab keciba acell"alh yahana kowa zuwa dubata"tafad'i hakan tana sakin kukan bak'in ciki.

Shigowar dady parlourn Yasa takashe wayar.tana kallonsa yahad'e fuska"yajefeta da invitetion card na d'aurin auren da"sati biyu masu zuwa.kallonsa tayi tana girgiza Kai tace".nameye ?kiduba kigani"jikinta na kirma ta duba cikin fad'uwar gaba" (kasancewar tayi primary skul tayi aure)
Tana hawaye ta d'ago kanta suka had'a ido"tace Babu komai da sakayyar da kamun"Koda zakayi aure,nazata sai anfito da zainab daka tsana ayaranka"meyasa bakaga k'ok'arin ta nakare kantaba?"sbd tarbiyyar dakabata Bata Zama irin yaronba.tunda ance banbasu tarbiyyaba.banyi zaton haka daga garekaba.inamai tabbatar maka da cewa nagama Zama dakai Koda zanrasa abinda zansaka abakina...tana fad'in hakan ta tashi tsaye da nufin ta barin parlourn.saidai daddy dake sauraron kalamanta yyi tsaye yaganta tazube k'asa sumammiyya...

Hankalinsa tashe"yakira isah driver yafito da mota,yyinda shikuma ya d'auki mama jummai sukayi mota da ita zuwa asibiti.suna mota daddy ya Kira Abba yasanarmishi.abba yasaka hjy ta shirya suka wuce asibitin"


Anbata taimakon gaggawa"kafin a'daura Mata drip bayan sunsamu numfashinta yadawo.

Doctor yadubi Abba da daddy da hjy hakimah yace".muje office nawa zanmuku bayani"Babu musu sukabi bayansa Banda hjy hakimah da daddy yace "ta jirasu sbd Yana ganin bedace tasan sirrin mama jummai ba.doctor yadubesu Yana cewa alhmdllh da farko!amma wlh patient naku ta tsallake rijiya d baya baya "ayanzun haka tana d'auke da hawan jini"hawan jini??daddy da Abba suka fad'a atare.docto yace eh wlh"yakuma hau sosai"abincikena wani Abu na bacin rai aka gayamata har zuciyar ta ta buga"tafad'i ta suma.aAllah yasa bata tashi daciwon b'arin jikiba.
(paralise)
sannan yanzun takamu da ciwon zuciya"sbd haka gsky indai kunason rayuwarta ta inganta da lfy da farin ciki tofa Dole kunisanci b'acin ranta.ku kusanci farin cikin ta.inta farka zamu azata kan magunguna "Allah yak'ara lfy Mai amfani.jikin daddy yyi sanyi sosai wlh"damashi bbu wani auro dazai k'ara ,katin bogine yasaka aka bugo mishi.azatonsa zata bashi hakuri tasake nutsuwa da nadama. Ashe hakat abin xai zama ai shikenan.shi yanzunma bazai iya zuwa wajen wata da sunan yafurta Mata kalmar so.abba ne yakatse mishi tunani ta hanyar cewa"wato bakaji abinda nace makaba ko?zuwa kayi Kanata k'untata Mata da abubuwa ga abinda yazo yasameta ko?toka kyauta.kayi hakuri Yaya wlh wasu Abubuwan sbd ta shiryune ,Kuma alhmdllh!yalabarta mishi wayar dayaji tanayi da yayarta halima"dakuma katin bogi daya nuna mata.murmushi kawai abba yyi yace".baka kyautaba gsky,kaga sbd kishi ta kamu da hawan jini da ciwon zuciya"Koda kuwa da gske aurenne wlh Dole ka hakura sbd lafiyarta da farincikin y'ay'anta.daddy yace" hakane Yaya Allah yabata lfy.abba yace ameen sunayiwa doctor godiya suka fito.lokacin dasuka fito"mama jummai ta farka"hjy nabata Baki"tana rantse rantsen bazata zauna da daddyba tunda baya k'aunarta abinda zaimata kenan y'arta nacikin wannan halin... tafad'a lokacin dasu Abba suka shigo"tana kallon daddy daketa kallon yadda dukta fige ta rame ta fita hayyacinta sbd zaimata kishiya.tamkar yyi dariya saikuma yadake.cikin jin haushinsa tace mlm kabani takardar sakina nagaya maka. Subahanallahi !Abba yafad'a Yana cigaba da cewa" jummai kimun shiru inde na Isa dake"maganar aurece bbu ita tsokanarki yakeyi dama."gashinan sbd kishi kin kwanta gadon asibiti.abba nafad'in hakan yaja hannun daddy suka fice.wani sanyi mama jummai taji aranta"tana kallon hjy tace"da gske?d'aga Mata Kai hjy tayi"tana murmushi kawai"wani gefen zuciyarta tanajin haushin barin datayi Abba yak'ara aure.kasan ranta ta tuna dakuma Allah yarubuta hakan.sbd ko a baya Abba shine mecew bayada tsarin mace 2"daddynne mecewa zaiyi auren alokacin kuruciyarsu.gashi shid'inma beyiba.dan Allah hjy kiyafemun abinda na aikata abaya.insha Yusuf bashida Mata sai hafsat kiyi hakuri.hjy na murmushi tace"bbu komai ya wuce.amarya saiki Fara shiri asallameki tunda kinwarke bbu zancen kishiya.murmushi kawai mama jummai tayi...

Koda aka sallamesu suka koma gida"har k'asa mama jummai yaduk'a ta nemi gafarar Abba daddy da inno .sukace sun yafe mata.suka Kuma sake Mata nasiha sosai.inno tace zata maido Mata yaranta.


Kwanci tashi bbu wuya agurin Allah yau yakama bikin Khadija da mahmod saura sati3"har angama had'a lefe.gefe guda Kuma ya mahmod na it's fin sati besaka Khadija a idonsaba.ko ganinsa tayi saita buya.sbd tsoron hjy"ayanzun haka anty da Khadija sundena zuwa sashen hjy da safe gaida ita.sbd Bata amsawa saima tadinga jifarsu da k'ananun maganganu marasa dad'i.hakan yasa khadija yin nisa da mahmod sosai.sannan aranta tanajin zafin meyasa aka hanata soyayya da Tahir?Kuma gashi yadawo gurin ummi suna soyayya harya siya Mata waya.wannan abun yasaka Mata shakku da zarge zarge akan Yaya mahmod baya k'aunarta ,yanuna cewa ita agolace agidan.yarabata da Tahir ,yabar ummi kanwarsa suna soyayya.hakan yayiwa Khadija zafi arai sosai.shiyasa ta nisanci duk wani abu dayashafi Yaya mahmod.shikuwa Yaya mahmod bemasan tanayiba harga Allah!yanadai damuwa da rashin ganinta"dakuma kaucewa ganinsa datakeyi.

""""""""""""""""""
Abba ne zaune aparlourn sa"khadija nakan carpet zaune itama.ahankali Abba yace kiyi hakuri Khadija da abinda Zan fad'a Miki"kid'auka hakan shiyafi zama alkhairi.

Nasan kinsan ummi da Tahir suna son juna yanzun ko?
Kanta ak'asa tace".eh abba"

Abba yace madallah"nasan zakiyi zaton mahmod yayanku ,yyi sonkai na rabaki da Tahir yabarshi Yana kula ummi.to Khadija amatsayina na mijin mamanki Kuma uba agareki"na zab'a Miki miji mahmod d'ana dana haifa. Kuma yamun biyayya,nasan kema Zaki mun biyayya insha Allah.miye zab'in ki Khadija karki cuci kanki kimun bayani Zan fahimceki inbaki sonsa.ayanzun haka aurenku saura sati3 daidai...โœ๏ธ


Comments kawai guys๐Ÿƒโ€โ™€๏ธ๐Ÿฅฐ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

๐ŸŒนA GIDA D'AYA๐ŸŒน
๐Ÿ˜๏ธ๐Ÿ˜๏ธ

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ



Story & written by mmn fareesa


๐Ÿ…ฟ๏ธ25&26

..........."Wani irin mugun duka k'irjin Khadija yayi da k'arfi"tana jin maganganun Abba tamkar durar aradu acikin k'wakwalwarta.sai yanzun ta tuna da lokacin da anty tace"taje Abba na kiranta Yana a parlourn sa.sannan duk umarnin daya bata ta amince"Ashe auren Yaya mahmod ne za'a sanar Mata?shin Yaya mahmod Yana sonta kokuwa?"yakuma zatayi da hjy?gabanta yasake fad'uwa sbd tunawa datayi da khairat.innalillahi wa inna ilaihir raju'un! tafad'a cikin ranta.khadija kiyi mgn kinyi shiru kinajina kuwa?"muryar Abba ta katse mata tunaninta "batare data d'ago kanta ba tace ". Babu komai Abba duk abinda yadace dani

Please Login or Register in order to submit comment