Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gurinsu...โœ๏ธ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

๐ŸŒนA GIDA D'AYA๐ŸŒน
๐Ÿ˜๏ธ๐Ÿ˜๏ธ

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ



Story & written by mmn fareesa

Wannan shafin nakine kyauta๐Ÿ‘Œ HAFSAT SALISU๐Ÿฅฐ๐Ÿ˜˜ nagoge k'warai Allah yabar mutum da masoyinsa.ina yinki over๐Ÿ˜



๐Ÿ…ฟ๏ธ 53&54


Ahankali nura yace"ga abokina nan tafe my zee!da sauri ta d'ago kanta suka had'a ido da Yaya mahmod.gimtse fusakarsa yyi sosai Yana bankowa nura harara"nura yadinga mishi murmushi kawai"Yaya Yusuf atare shida hafsat suka ce Yaya sannu da dawowa.da yauwa ya amsa Yana wuto su ummi"Tahir ne yayi saurin cewa Yaya barka da dawowa.yauwa sannunku Yaya mahmod yafad'a Yana shiga k'ofar dazata sadaka da waiting parlour na gidan...Khadija na dining area tana shirya komai.yyinda Maryam tana kitchen tana Mata wanke wanken kayan dasukayi amfani dasu....k'amshin turaren sa yashaida Mata Yana a parlourn.d'ago Kanta tayi "adedenan yyi sallama Yana sakar Mata wani tattausan murmushi.itama maidamishi da murmushin takeyi tana amsa sallamar dsa had'e da cewa sannu da dawowa yaya.hannayensa ya ware Mata Yana cewa"irin wannan sannu da zuwan nakeso ba irin wannan ta bakiba.... d'an zaro ido tayi tana nuna mishi kitchen"Wai akwai mejinsu aciki"girgiza Mata Kai yyi alamar shifa inbatazoba bbu inda zai matsa.tana murmushi ta iso gurinsa"ahankali tayi hugging nasa"Yana lumshe ido yyi hugging nata back"ajiyar zuciya yasaki Yana d'ago kanta yafara sinsinar wuyanta zuwa baby face nata...uhmmm!Maryam tana kitchen fa"kada taganmu cewar Khadija tana k'ok'arin barin jikinsa.my khady itama sbd batada saurayi shiyasa ta tsaya akitchen ko?lahh Yaya bafa haka bane tanada Yaya Kamal mana.tabe baki yyi had'e da cewa" yatsaya kallon ruwa kwad'o yamishi k'afa.najima da fahimtar sonta yakeyi "amma yak'i ya furta.sbd haka damuwarsa.yanafadin hakan yaja hannun ta suka wuce bed room d'in sa"Yana cewa wanka zata mishi yaje yyi sallar magrib.yakuma k'udurta aransa muddin yarancan magrib ta musu anan sai jikinsu yagaya musu tunda Yusuf da hankalinsa yabiye musu...

Maryam kuwa duk tanajinsu tana a kitchen"tana ayyana itama Allah yasa Yaya Kamal yanuna Mata irin wannan soyayyar.saurin goge kitchen d'in tayi ta fito"mayafinta ta d'auka da hand bag nata.bata tsaya yiwa Khadija sallama ba sbd tasan suna tare da gwaninta.fitowa tayi sbd tacewa Yaya Yusuf yakaisu gida tunda yaya yadawo"tana fitowa ta gansu atsatstsaye"zee tace"mery mutafi gida ko?Maryam tace wlh kuwa"kinsan halin Yaya wlh.nura na murmushi yace"saidai ku zaiyiwa wani abu Amma Banda my zee"ita ai matar abokinsace...ummi na murmushi tace"hmmm Yaya Nura kenan ai wlh ko anty Khadija ta mishi laifi indai yayane duk son dayake Mata zai hukuntata...yaya Yusuf ne yakatse musu zance da cewa ke kuzo namaidaku gida"bata fuska hafsat tayi tana cewa"nidai Yaya banaso murabu.kilama sai safe zankoma ganinka saidai kawai ka kirani..Murya can k'asa yace"to my angel kece bakyaso kizama amaryata ne.dayanzun Muna tare any time ko office atare zamuje tunda nadawo nan da aiki ko?"nidai banaso inajin kunya"hmmm !innikuma natashi zanje nacewa Abba kawai ayi mgn ta aurenmu kawai...Yana fad'in hakan yace" muje sbd yaga befi 20 minit Akira magrib ba...front sit tashiga ,yashiga driver sit"yyinda zee ummi da maryam suka shiga back sit"yaja motar..

nura ma motarsa yashiga ,shima Tahir haka.

Lokacin da Yaya mahmod yafito da jallabiya ajikinsa zai tafi masjeed yaga bbu kowa agurin.yaja tsaki had'e da cewa"kinceci kanku wlh..Yana fad'in hakan yyi tafiyarsa.

********************
Zaune suke gaban dining table suna dinner"Yaya mahmod nabata abincin abaki shima Yana cin nasa.gaba d'aya tana ajikinsa tana mishi shogwab'a"shikuma yanata biye mata.har suka kammala cin abincin.kafin sudawo parlou"tana zaune a tsakkiyar cinyoyinsa ya matseta ajikinsa suna kallon news atv
Basu tashiba sai 10:15pm "bbu kunya Yaya mahmod yace"atare zasuyi wanka.badan tasoba ta bishi dukda kunyar sa datakeji....Dole khadija ta rufe idanunta sbd shi bbu ruwansa yatube agabanta hankali kwance yafara watsa Mata ruwan kunfa.yana cud'a Mata jikinta Yana k'arewa suran jikinta kallo"sunjima kafin su fito suka shirya suka kwanta....saida yajagwalgwale ta son ranshi tukum yamusu addua suna rungume da juna bacci yyi awon gaba dasu.

Bayan sati 2

Masha Allah wannan family suna cikin farin ciki"yyinda Khadija tasami sauk'i sosai harma Takoma skul"abdallah ma awata tsadaddar University Yaya mahmod yasakashi .yana zaune a hostel..gefe guda Kuma Mahmoud da Khadija anata zuba love, gashi har hutunsa na angunci yak'are"ranar Monday zai koma office.haryanzun Kuma bbu abinda yakoma shiga tsakanin su shida Khadija.tun bayan first night d'insu..

Zaune kharat take tayi uban tagumi dukta fige ta rame sbd tunani"Takoma tamkar ba itaba"bbu gayun nan da kwarkwasa da d'aukar wankan nan "yanzun duk batayi.hawayene kawai ke zarya akumatunta.inhar tatuna Abu 3 "saitaji damuwa da tashin hankali yak'aru aranta.
na farko inta tuna cewa Jamil ne uban d'anta ko y'arta dazata haifa.sai na2 Yaya mahmod yak'ubuce mata.na 3 ,auren muhseen"dukda tasan muhseen beda wata makusa "Amma yanzun wata zazzafar soyayyar Yaya mahmod takeji aranta..tana share hawayenta Abba yashigo d'akin.wani irin tausayi yaji tabashi"ganin dukta fige ta fita hayyacinta.abba sannu da zuwa"tafad'a Kanta ak'asa.yauwa khairat! ungo duba kiga message d'in da matsiyacin yaron nan yaturomun...hannunta na kirma ta karb'i wayar abban ta duba kamar haka...
*kusani inma y'arku ta haihu to kuta haifarmawa baniba" zan b'ace b'at aduniyarku.abu nagaba muddin ta haifi y'a ko d'a dodo zai zuk'e jininsa...*
Iya nan takaran ta tadafe kanta sbd juyawar dayakeyi mata.abba nacewa subahanallahi! miye abin damuwa?wayarsa ta mik'a mishi.adedenan hjy rabi ta shigo sbd muhseen na parlour yazo gurin kharat d'in.kasancewar tunda yakecewa Yana sonta bata tab'a bashi fuskar zuwa tad'i aguntaba".yauma kewarta ce tamishi yawa yazo yaganta" sbd shidai dukda tana a hakan na matsayinta na bazawara" Yana sonta ahaka...hjy rabi tace"lfy take dafe Kai alh?"kafin Abba yabata amsa khairat ta saki k'ara jini Yana bin k'afafunta.ta sulale k'asa sumammiyya"
arikice hjy rabi tace"nashiga ukku! kharat karki mutu dan Allah ke kad'ai na mallaka aduniya.abba ne yyi jarumtar d'aukar khairat d'in Yana cewa saka hijabi kisameni a parking space mukaita asibiti.

Abba na fitowa yasami muhseen zaune kan kujera"yasha wankan k'ananun Kaya Yana ta zabga k'amshi"arikece ya mik'e tsaye Yana cewa" Abba Mike damunta naga kamar bata numfashi ko?Abba yace"muje asibiti muhseen ta sumane....

Tsatstsaye suke abakin k'ofar shiga emergency room "abba muhseen da mama rabi"bud'e k'ofar akayi.da sauri suka nufi gurin doctor d'in.. doctor yace tayi miscarriage ne, sannan ta zubar da jini sosai sai ank'ara Mata jini leda 2 . Allah Mai yadda yaso"Allah yasa hakan shiyafi alkhairi ga rayuwarki khairat.cewar Abba cike da tausayinta"muhseen cike da tausayawa yace"muje ad'ibi jinina asamata zaiyi mata.doctor yace okay suna barin Gurin shida muhseen.

Mama rabi nata share hawaye"Abba nabata baki ,da Mata nasihar tabi y'arta da addu'ar samun lfy kawai...

###########

Zaune suke awani tsakar gida"da girman sa bazai wuce zaman mutum 10 ba.daki 2 ne sai kitchen da toilet"gidan fas share k'al dukda simintine bbu tayis"alh Ayuba dake zaune tsakar gida ya jingina da bango"hannunsa rik'e da tasbaha yanata lazumi"yyinda hjy Amina(mmn ibbi) tana kwance kan katifarta tana sauraren redio"cikinsa ne yaji ya juya sosai.gashi ibbi Yana gurin aiki"sbd wannan aiki shine rufin asirinsu. sai zob'o da ruwan sanyi da hjy amina kesiyarwa sbd anguwar ta jama'a ce sosai....ehemmm!alh Ayuba yyi gyaran Murya say 2.tabe baki tayi tamkar batasan meyake nufiba.saima ta shareshi sbd aganinta zaman datakeyi dashi taimaka mishi tayi ai.bbu dole saita k'ara inda dare yamata.
Amina kina jina Ina mgn zaki share? kaga mlm makaho banason takura fa.ta Yaya zaka matsamun da mgn bacin Ina hutawata.ai makantar taka Kaine ka d'orawa kanka ita.sbd asiri kayiwa wani saiya dawo maka ko? Kaga kuwa kaika azawa kanka masifa.ina cewa ai sbd nafad'a maka gsky ka rabu da alh mudi.cewa kayi akan hakan saimu rabu .kaga gashi yanxun kunrabu badan Allah ba ko?nidai banason wasu surutai kodai minene ai ke matatace inada ikon saki abu"sbd haka iรฑ bazakiyiba shikenan"Yana fad'in hakan yatashi yana laluben bango har ya iso bakin toilet d'in"Yana aza kafarsa sulb'in sabili da aka zunda yajashi.jikake timmm!yasaki k'arar azaba.asukwane ibbi dake shigowa yanufesa yataimaka mishi yatashi"Yana mishi sannu"kafin yakaishi toilet d'in"yakaimishi buta ya ajiye cike da ruwa"bayan ya ajiye yasami umma kwance tana sauraron redio.

Idanunsa sunyi jajir sbd b'acin rai"ahankali yace"wlh umma bakyayiwa daddy adalci"meyasa bakya tausaya mishi be?inda banzoba aidayaji ciwo dan Allah kidinga taimaka Masa idan baninan...Ibrahim abinda kuka shuka kaida ubanka shine kuke girba.sauk'insa guda"da Allah yasa kana tausayinsa da taimaka masa.inbacin hakan nadamarsa ma saitafi haka.sbd haka Allah yakyauta Zan gyara"sannan mgn tagaba nadai hanaka neman Mata kacemun kadena.nakuma yarda da hakan "sbd haka kasamu wata ka aura.cikin sanyin jiki yace"nima naso hakan umma "Amma mudaku mufara samun ingantacciyar rayuwa tukum.hakane Allah yyimaka albarka yak'ara shiryaku kaida mahaifinka.yace ameen ummana.

Tashi yyi yad'akko ludayi da gidauniya" yazauna yadama fura da nono da yogurt yasaka k'ank'ara.alh Ayuba na fitowa yazaunar dashi yafara bashi furar"hawaye nacika mishi idonsa.umma dake lek'ensu ta window taji ibbi yabata tausayi sosai.hakan yasa ta fito ta karb'e furan .tana cewa jeka kitchen abincika na nan akula kazauna kaci kayi wanka.nizan bashi yasha din.

Cikin jin dad'in kalamanta yace"yauwa ummanah"yatashi yabarsu anan zaune kan tabarmar.

Alh mudi kuwa lokacinda yabar asibiti shida wani yaronsa.da akewa kirari da (goga)har gidansa yakaisa"saidai Kuma duk wani abu Mai mahinmanci goga bbu tsoron Allah ya kwashe" harda wayoyin alh mudi da wasu kudad'e da agoguna masu tsada da takalminsa.alh mudi yayi zaton kashe Masa yakeyi,Saida yagama kwasar komai tukum yace". alh makaho nima na yagi rabona "sainace ayi yawo atiti lfy.alh mudi yace"goga amanata zakaci bazaka kula daniba kodan zaman tare?wata dariyar rainin hankali goga yyi"ashek'e yace" inada abin yi nima,azatonka sadda nace Ina bayanka d'ari bisa d'ari a asibiti.kad'auka har cikin rainane?"
To sbd nabiyoka na yagi rabona nima" sbd haka nabarka lfy ,bakada dai idon gani balle ko atiti inkana bara kaganni ka ganeni...Yana fad'in hakan yajuya ya bar gidan... kukan bak'in ciki alh mudi yafashe dashi..

Goga befi 20 minit da tafiyaba" saiga police sunxo bbu tausayi sukayo waje da alh mudi da kayansa duka na sawa. suka saka mishi atroley"yanata zaginsu da tsinemusu suka watsoshi waje...

Cikin bak'in ciki da gajiya da rayuwarsa ya nufi titi acewarsa gara yaje mota ta takesa yamutu ya huta da wannan k'untacciyar rayuwar...

Shidai yanzun besan inda zasushiba.dama anan garin yatashi Gurin marik'ansa dasuka d'akko shi gidan marayu.bayan ya girma yabujire musu ta hanyar yiwa y'arsu fyad'e.hakan yasa suka rabu dashi cikin tozartashi...bakin titi yanufa da lalube da tambaya" kaitsaye yahau titi.....mashin da wata mota sukabi ta samansa...atake kansa yafashe k'afarsa guda ta fita ko shurawa beyiba ya mutu.mutuwar wulak'anci atiti...bbu wani dayyi yunk'urin d'auke gawarsa.illa wad'anda suka yi bankan suka janyesa dg saman titi... Allah yasa muyi kyakykyawan k'arshe.

***************

Yau yakasance Friday"da misalin karfe 12:00pm Yaya mahmod yashigo gidan.kasan cewar tun 9 am yafita Abba na kiransa"sai yanzun yadawo da nufin yyi Shirin zuwa Sallar juma'a.

Khadija na kwance tana bacci"mafarki tayi da( jafar mahaifinta) gashinan yanata kuka Yana kiranta itada abdallah.yana cewa suzo su taimaka mishi..wani mugun kallo suke mishi Khadija na cewa bazanzoba natsaneka!bazanzoba natsaneka!!!iyanan Yaya mahmod daya shigo a bed room d'in yaganta kwance bakinta na furta hakan.kuma idanunta arufe"subahanallahi! yafad'a Yana hawa akan bed d'in.yarik'eta yanamata addua.bude idonta tayi.ahankali yace"my khady mafarkine kikayi ko?d'agamishi kanta tayi.kinyi addua dazaki kwanta ne?eh Yaya Saida nayi.bara naje nayi fitsari"sakinta yyi ta tashi ta wuce toilet.

Saida ta wanke bakinta tukum tayi fitsarin ta fito.

Had'a ido sukayi"yasakar Mata murmushi itama mayar Masa tayi"hannunsa ya mik'amata bbu musu ta nufesa tana kwanciya ajikinsa ta fashe da kuka...my khady Mike damunki pls? kisanarmun banason kukanki Kuma kinsani ko?"batare data d'ago kanta ba tace"Yaya abbanmu nayi mafarki da Abdallah...tasanar dashi mafarkin" ta h'ada da cewa natsaneshi banason ganinsa.sbd bedamu da rayuwarmu ba!ko lafiyarmu da farincikinmu...toshe Mata Baki yyi had'e da cewa ya isa my khady kinji?kiyi hakuri uba uba ne ba'a canzashi.adduar shiriya yakamata muyi mishi"insha Allah YAU DA GOBE zatayi aiki akansa...shiru kawai tayi tana sakin ajiyar zuciya"

Ahankali yace"kin hakura ko?d'aga mishi kanta tayi,alamar eh"zuge zip din doguwar rigar dake jikinta yyi Yana cewa muje muyi wanka my khady...shiru yyi sbd ganin nashanunta sun bayyana sbd bbu bra ajikinta"rufe idonta tayi hakan yabashi damar dagota yahad'e bakinsu Yana bata hot kiss"shafa kansa zuwa kirjinsa tafara yi hakan yasa yacikata yarage kayan jikinsa.

Hayewa yyi samanta Yana romancing d'in ta"yyinda tayi luf tana k'arb'an sak'onsa.gaba d'aya Yama fita ahaiyacinsa ,dama abuk'ace yake yabarta ne sbd ta warke sosai"duk itama yasata a network Amma tanajin tsoro aranta.sbd Bata mance wahalar datashaba.rabasu da komai na jikinsu yyi" cikin wata iriyar murya yace" my khady zaki yarda?bazanmiki da zafiba kinji ko?d'aga mishi kanta tayi alamar to...hmmmm fad'in yadda yaya mahmod yatumurmushi khadinsa b'ata bakine.bewar Allah taji ajikinta"dukda wahala datasha baikai na first night nasuba...shikansa yaga k'ok'arin ta daya dawo hayyacinsa.tana rungume ajikinsa yarufesu jikinsu. wayansu da kansune awaje"agogo ya kallah yaga 2:15pm"
Subahanallahi!wlh antaso dg juma'a my khady kinsa nayi latti wlh"cikin k'arfin halin boyemishi yanayinta tace"to ai saikayita Agida dandai yau kawai.amma my khady ba'aso mumini na k'warai Sallar juma'a na wucesa"hakane Yaya"
Tashi muje muyi wankan Fatima(k'anwar nura) zankaiki tamiki lalle ja"Amma sai munje anmiki saloon"nifa kitso bawani cika burgeni yyiba .garama amiki kalba ko?nima Yaya wlh banason kitso zafinsa nakeji"to shikenan sai agyara Miki gashin kawai.. yafad'a Yana janyeta dg jikinsa yakwantar da ita gefensa"tashi tsaye yyi yamaida boxer d'insa.kafin yaja hancinta Yana cewa bud'e idon sarkin kunya.nasaka wando to"bud'e ido tayi tana murmushi tace"nidai kakamun towel na d'aura"to shikenan tunda bazaki iya tashi ahaka agabanaba.amma Dole kiyi wankan agabana ,Kuma bbu komai ajikinki.batace komaiba"ya wuce toilet.ta rintse idanunta sbd rad'ad'in datakeji agabanta.bata auneba taji ya sureta yyi toile d'in da ita.

Cikin bathtub d'aya cika da ruwan zafi yasakata aciki"sbd tagasa jikinta"ayadda yakejin khadynsa ko zuwa dare ko safe saiya sake yi. gsky ya ayyana aransa.

Bayan sunyi Sallar suka shirya cikin milk d'in gizna iri d'aya"sai k'amshi suke yi.sunyi kyau gwanin sha'awa da burgewa.kama hannunta yyi"
fita sukayi wani tsadaddan restaurant sukaje sukayi lunch acan..dg nan suka wuce inda za'a Mata saloon...

zaune suke awaiting parlourn gidan"Yaya Yusuf da hafsat kan 2seeter"sai zee da Yaya nura.naja da Yaya kabeer anata zance hankalinsu kwance.

Ummi da Maryam suna d'akin hjy tareda hjy" hjy tana jiran dawowar abban ta mishi mgn yasan nayi da yaran nan".Kar cikinsu wani yafara yunk'urin tab'a wata.gara ร musu aure"dg waya sai zuwa fira shine aikinsu.gaba d'aya yaran gidan bilkisu ce kawai batada saurayi...sallamar salimce ta katsewa hjy tunanin ta."yace anty Maryam Wai Yaya Kamal yace ki kaimishi abinci"dato Maryam ta amsa ta d'auki k'aramin gyale ta aza saman gyaran gashinta datayi bbu jumawa.dama da shirinta ajikinta"hjy aranta tace"hmmm shikuma da Kamal Gurin Maryam yasauka kenan.

Itadai ummi dariyar shakiyanci kawai takeyi"dukda maryamce babba 2yrs tsakanin su"Amma sbd ummi nada jikin girma suke Kai d'aya. wasuma nazaton ko twins me.

su Yaya Yusuf na nan azaune ta gaidasu ta wuce dining area ta had'a abinci plate guda ta nufi sashen mazan gidan.

Yaya Kamal na zaune yayiwa k'ofa zuru Yana tuna shawarar da Yaya Yusuf yabashi jiya da dare.wlh inhar kanasonta gara kasanar Mata tun kafin wani yahure Mata kunne.nasan Maryam Bata kula samari"Amma kaga duk ko wacce agidan nan tanada saurayi.hakan zaisa taji itama tana sha'awar yin nata... sallamar Maryam ce tadawo dashi duniyar daya Lula.

Lumshe ido yyi Yana amsawa"ta ajiye plate d'in agabansa tace"Yaya Ina wuni?hmmm bazan amsaba"kanta ak'asa tace"meyasa?sbd Baki damu daniba.nayi zazzab'i jiya bakimun ya jikiba.dago kanta tayi suka had'a ido.....saurin janye idanunta tayi sbd ganin yadda yake binta da wani irin kallo Mai wuyar fassara.wata kasalama taji ajikinta..ahankali tace aibansaniba ne shiyasa"yajikin yanzun?nasamu lfy kodan sbd ganinki danayi ayanzun.amma inasu ummi suke?sunacan zance"Amma ita ummin nabarta ad'akin hjy"to ke Ina naki saurayin ne?rufe fuskarta tayi tana murmushi tace"nibana kula kowane saurayi.to idan yayankine saurayin naki Zaki kulashi?eh Mana tunda d'an uwanane.tafada still fuskarta arufe"matsowa yyi kusada ita"cikin wata iriyar murya yace"my habibaty kindad'e araina Maryam"inamiki zaton tun kafin Yusuf yafara son hafsat nake sonki"Ina gudun kada na furta kik'i amincewa dani.kuma banason raini shinefa"Amma inasonki sosai my mery"fatana mukasance da juna har abada.ina fatan baza'a jamun aji ba za'a amsamun.tashi tayi da gudu ta fice tana dariya.suka yyi kan kujera cikin farin cikin yasauke abinda kedamunsa azuciyar sa.yanzun Maryam tashice....

Ahankali Abba yashigo parlourn...gaba d'aya Baki yakama sbd ganin ammaida mishi parlourn gida dandalin fira"aransa yace"zanyi maganinku.wata 2 zansaka aurenku na huta insha Allah...gaba d'aya suka hau gaisheshi anata sinne sinnan Kai... murmushi kawai Abba yyi Yana amsawa.ya d'auki khalifa dayanzun ya iya tafiya yanata tete a parlourn.

Yanufi part d'in hjy akan yatambayeta waye keson Maryam?sbd betab'a ganinta da waniba...


Da misalin karfe 11:pm khadija na kwance jikin Yaya mahmod"yagama Tara Mata gajiya"tamkar ta kurma ihu"ko fitar da sukayi d'azun wlh daurewa tayi"gashi da darenma bbu d'aga k'afa...wayar khadijar ce tayi ringing"da mamaki shida ita suke bin wayar da kallo harta katse.

Wani kiran yakoma shigowa"Yaya mahmod ne yamik'a hannunsa ya d'auki wayar dake kan bed side drower.
*baba mukhtar*
sunan dayagani akan screen d'in wayar.kallon Khadija dake kwance ajikinsa yyi yamik'a Mata wayar yace ki d'auka Abba ne.....โœ๏ธ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

๐ŸŒนA GIDA D'AYA๐ŸŒน
๐Ÿ˜๏ธ๐Ÿ˜๏ธ

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ



Story & written by mmn fareesa



๐Ÿ…ฟ๏ธ 55&56


......Ahankali ta karb'i wayar ta kara akunnan ta"tayi sallama gabanta nata fad'uwa sbd tasan bbu lfy" ace baba yakirata dadare haka.... assalamu alaikum Khadija kina jina kuwa?eh baba Ina wuni?lfy lau yamai gidan naki?Yana lfy baba"to madallah kiyi hakuri nakiraki da dare"Khadija inaso gobe idan Allah yakaimu lfy da safe kuje keda mijinki .a asibitin A&S INTERNATIONAL HOSPITAL.zaki duba jikin wani bawan Allah.shima Abdallah nakirashi akan yazo da wuri"yabar kome yakeyi amakarantar...amm...banason jinkomai Khadija karki damu saidai safe"kashe wayar tayi tana kallon Yaya mahmoud.murmushi yamata sbd yaji duka maganganun da sukayi da baba.yana shafa kanta yace"karki damu my khady Allah yakaimu goben lfy ai week end ne mako?saimuje kinji"tashi muje muyi wanka"bbu musu ta tashi ta mayar da rigar baccinta suka wuce bath room...

Washe gari sbd fargaba ko break fast Khadija kasayi tayi"duk yadda Yaya mahmod yaso yatursasata.saima tasakarmishi kukan shagwab'a"hakan yasa yarabu da ita.yana rarrashinta kawai"shima tea yasha suka shige mota...suna ahanya yadubeta yace" kinsan kome A&S take nufi?girgiza kanta tayi had'e da cewa ah ah Yaya"kinaso kisani my khady?eh Yaya .ALIYU& SUMAYYA take nufi"kanta ta aza akafad'arsa tace tokai ta Yaya kasani?hmm !my khady asibitin abokinane fa.Allah sarki saiku gaisa dashi ai inmunje"eh to in matar tashi tabarshi yafito da wuriba.hmmm my man kaganka akwaika dason basarwa"murmushi yasaki har fararen hak'oransa suka bayyana.my khady kenan wlh soyayyar kice ta canzani sosai"shikansa ALIYU danake gayamiki"matarsa Yana Mata son dabayayiwa kansa wlh...komai yace my summy.ita Kuma my Lion take kiransa dashi.khadija na murmushi tace"aidai mijina yafi sona akan yadda mijinta keson ta ko?tofa masu karatu ga tambaya tsakanin sumayya da Khadija wace mijinta yafi sonta?

Parking yyisuka fito"yakama hannunta suka jero"wata dake kallonsu batasan lokacin da tace".wow nice couples! had'e rai Yaya mahmod yayi"yyinda Khadija tayi murmushi kawai suka wuce cikin asibitin"

A reception suka had'u da baba mukhtar da mahseen dayake famanzarya a asibitin.sbd har yanzun kharat na nan akwance..k'ila abata sallama yau"gaisawa sukayi sosai da juna"suna k'ok'arin tafiya saiga hjy rabi da Abba sun shigo ciki"Yaya mahmod yad'an matsa hannun Khadija dake tsaye gabansa yace" ga mama rabi can muje mu gaisa...kafin Khadija tayi mgn"mama rabi ta gaida alh mukhtar Yana tambayanta jikin kharat.kafin suyi musabuha da abba.matsawa Khadija tayi kusada ita suka gaisa amutunce"Khadija tace"mama dama khairat batajin dad'i ne?hjy rabi fuska asake tace eh wlh B'ari tayi.yaya mahmod yace"subahanallahi!baba mukhtar yace"kunsan junane mahmod? mahmod na murmushi yace"mama k'anwar mahaifiyata ce uwa d'aya uba d'aya.baki washe baba mukhtar yace Kai Masha Allah.ashe muhseen duk Yan uwane?to muje ciki saimu dubata kafin muje inda zamu"sai a sannan abdallah ya shigo Yana hangensu yace anty Khadija...juyowa tayi suka had'a ido.da sauri ya k'araso.gaba d'aya acikin sati 3 zuwa sati4 Khadija taga Abdallah yyimugun canzawa.yyi haske yyi kyau da wayewa "uwa uba sutura da k'amshin daketa tashi ajikinsa" gaidasu yyi suka nufi d'akin da khairat take..

Khairat na ma zaune ta jingina da pillow"dukta rame sai haske data k'ara"idanunta sunyi haske da k'ara girma sosai and ramar datayi"ancire Mata drip d'in dake d'aure a hannunta"tunanin irin hidimar da muhseen kawai yakeyi akanta take.kuma Wai har jininsa yanada aka sakamata...ita yanzun gani takeyi kamar baikamata Yana saurayin Saba ya auri bazawara... s anty salma k'anwar abbanta dake agefenta tace"khairat yakamata kiyi karatun ta nutsu kisaki jikinki da yaron nan muhseen sai rawar jiki yakeyi akanki"Wanda baisaniba sai yad'auka cikin ma nashine.wlh yabani tausayi sosai"kafin khairat tayi mgn su Abba da Yaya mahmod duk sun shigo..gabanta taji yafad'i lokacin da idanunawanta suka sauka akan hannun yaya mahmod Yana rik'e da hannun Khadija dayasha Jan lalle.

Kauda kanta tayi had'e da sunkuyadda shi k'asa"sbd ganin yadda muhseen kebinta da wani mayen kallon.abba Ina kwananku?duk suka amsa da Mata da tambayarta ya jiki"mahmod suka matsa kusada ita"Khadija yace"sannu khairat!yajikin? Allah yak'ara lfy"tana murmushi na yak'e ta amsa"shima Yaya mahmod yamata ya jiki"kafin yacewa mama rabi tazo zasuyi mgn.khadija na k'ok'arin janye hannunta"Amma saiya rik'eta suka fito dg d'akin..

Murya can k'asa tace".Yaya bazataji dad'i ba"kaje kuyi maganar saina tsaya anan pls"sakar Mata hannu yyi Yana murmushi"kafin yanufi Gurin hjy rabi data biyo bayansu suka fito dg room d'in... tambayarta yyi Ina mijin khairat d'in.dukda yasan waye ta aura.bbu wani b'oye b'oye hjy rabi tasanar Masa da komai da guduwar jamil da text message d'in dayaturo.wanda shine sanadin zubewar cikin...cikin b'acin rai Yaya mahmod yace"karyabari muyi arba dashi wlh!aigara da shegen cikin nashi yazube"Amma me muhseen kenufi da khairat?anan tasanar mishi shine Wanda zata aura.murmushi yyi yace alhmdllh!ai mutumin kirkine Allah yabata lfy"hjy rabi tace"wani kukazo dubawane?eh mama abban khadijane yyi accident wlh shine mukazo dubashi.dukda ita batasaniba anboye Mata sai yanzun inta ganshi zata sani.subahanallahi! Allah yakyauta gaba yabashi lfy.
Yaya mahmod ya amsa da ameen... adedenan su Abba mukhtar dasu abdallah suka fito"Khadija ita ta k'araso sbd Kiran da Yaya mahmod yamata da hannu alamar tazo...

Atare suka nufi room d'in da abbansu Khadija yake"gaba d'aya Khadija da Abdallah gabansu fad'uwa yakeyi"anty kuwa hanawa tayi asanar musu dakuma bazasuzoba..sbd aganinta Saida yaga yakusa mutuwa zai tuna dasu bacin yanunawa duniya besansu ya wofintar da rayuwarsu" shine yanzun and beda kunya zai nuna shine mahaifinsu....baba mukhtar ne yafara murd'a k'ofar yashiga saisu Yaya mahmod da Khadija sai abdallah dake bayansa suka shiga atare.

Yana kwance kan bed"kansa duka anzagayeshi da bandage.k'afarsa guda andatseta....kallo d'aya Khadija tamishi tagano mahaifinsune....da sauri tayi yunk'urin k'wace hannunta dake cikin na Yaya mahmod.rik'eta yyi Gam had'e da cewa meye haka?karki koma yunk'urin guduwa.... abdallah ma naganinsa yaganeshi dukda kamanninsa sun sauya.juyawa yyi da sauri zai fita"cikin tsawa yya mahmod yace"Abdallah inhar kafice dg d'akin nan ranka zai b'aci!dawowa Abdallah yyi sbd bazai iya musu da Yaya mahmod ba.kuka Khadija ta fashe dashi itada Abdallah.

Wani irin mugun tausayi duk jama'ar dake parlourn suka bashu....tqrin da marar lafiyar ne yyi yasaka kowa kallonsa...Yaya mukhtarrrr!dan Khadija da Abdallah basuzoba har yanxun?cikin tausayawa d'an uwansa yace"sunzo yanzun gasunan.

Khadija Abdallah kuyafemin natuba da abinda na aikata muku abaya.inaji ajikina ciwon nan bazan tashiba"kubawa asma'u hakuri ta yafemun dan Allah y'ayana kuyafemin... yafad'a Yana tari da hawaye"

Gaba d'aya Khadija saitaji yabata tausayi"Yaya mahmod da ido yamata alaman taje gurinsa...bbu musu ta matso kusada shi tana cewa baba sannu!khadijaaaaa!zonan kikama hannuna.Allah yyi muku albarka"Abdallah naganin taje shima yamatso kusada ita...gaba d'aya sunbawa mutanan dakecikin room d'in tausayi"Kama hannun ta yyi idanunsa arufe yace"kuyafemin Dan ALLAH badan niba da mugun halina..Yaya mukhtarrrr kasaka baki suyafemun dan Allah"Ina Abdallah?hannunsa abdallah yakama Yana cewa gani baba.Abdallah kunyafemun ?munyafemaka baba"yafad'a Yana share hawayensa"khadijama kukan takeyi,cikin tari yace"waye Wanda yahanaka tafiya yamaka tsawar kadawo gareni abdallah? ahankali yace"Yaya mahmod ne mijin anty Khadija.Mahmod kana Ina? Allah yyimaka albarka"Yaya mukhtar tasanarmun halaccinka akan y'a'yana...tari sosai yakeyi"su Khadija na mishi sannu"cike da tausayawa Yaya mahmod ya iso kusa da Khadija Yana cewa sannu baba insha ALLAH zaka Sami sauk'i...tarin dayakeyi yyi yawa hakan yasa akakira doctors"aka tafi da baban wani room.Yaya mahmod ya bi bayan doctors din" sukaje akayi mgn za'a fita da baba k'asar waje. zuwa jibi insha Allah...amma sai Mai asibitin yazo yyi singing"yaya mahmod yace"bbu komai bayaso kowa yasan yabiya afitar dashi waje....

Room d'in yakoma yasami Khadija nata kwara amai a toilet.

Arikice Yama manta da mutanan dake Gurin yabita yabita toilet d'in"sannu my khady.kinga saida nace kiyi break fast kika k'i" gashi yanzun yunwa tadameki... fad'awa jikinsa tayi ta kwantar da kanta ajikinsa tayi lamo"janye gyalenta yyi Yana tab'a jikinta yace"subahanallahi zafi naji"harda

Please Login or Register in order to submit comment