Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Hakeem"suna kallo"gaishesa sukayi ya wuce part d'insu Khadija..bbu kowa aparlourn ,hakan yasa yawuce kitchen inda yakejin motsin mutane"
Khadija natsaye ta bawa k'ofar kitchen d'in baya"tana had'a coslow!sanye take doguwar riga ta kanti"tafito Mata da coka cola shape nata"kanta sanye da hula, tayi acuci da gashin kanta"
kalonta yaketa yi tunda k'afar ta harzuwa kanta"itakuwa ajikinta taji ana kallonta"da sauri ta juyo tashak'i k'amshin turaren sa"hakan yasa tahane shine.janye idanunsa yyi Yana gyaran Murya"gaba d'aya duk saitaji kunya"juyawa tayi da sauri bata bari sun had'a ido ba.
"angama shirya komai ne?"muryarta na kirma tace". eh" amma ga coslow nan dana manta banyiba"okay inkingama saikije ki kaimana acan"banaso nadawo nasameki ad'akin kigama da wuri....um um..dama Yaya kayi hakuri, hjy tace" nadaina zuwa ai.hmmmm!Abba yace komai yawuce karki damu kije kinjiko?hjy ta bazatasan kinjeba.dato ta amsa "shikuma yajuya Yana barin kitchen d'in.ajiyar zuciya yasaki sbd bbu kowa aparlourn."yafice zuwa parking space yashiga mota yafita.

Khadija kuwa komai ta had'a acikin trays 3 "harda drinks d cups"fitowa tayi ta wuce waiting parlour"cikin sa'a taga maryam"nahad'awa Yaya Hakeem abinci agabansa"ta zauna kan kujera tana jiran maryam ta gama.saiga hafsat ta shigo" da alama Yaya Yusuf tazo taga ko Yana nan.


"xama tayi kusada Khadija suka Fara fira"har Maryam tagama ,tazo ta zauna kusadasu.alfarmar sukama mata kayan takai sashen Yaya mahmod"ta nema agurinsu"suka ce to suna tashi...

Duk abinda yadace itadasu suka kai" suka kuma kama mata ta gyara bed room d'in da parlourn...kafin suka fito ta rufe d'akin"k'ok'arin tafiya sukeyi"hafsat ta hango Yaya Yusuf zai nufo nan"da alama dg wani gurin yake zai zo yabud'e d'akinsa.

Hafsat tace" lah kujirani dan Allah ga Yaya Yusuf can"Maryam tace." ah ah kedai kitsaya yazo d'in"haka kawai kayi mistake kad'an amaka masifa."ni wlh da Abba zai yarda da hostel nakoma !sai duk yayunmu sunyi aure nadawo"gaba d'aya suka saka dariya...Yaya Yusuf dake k'ara sowa "yabi hafsat da kallo Yana gulmarsu aransa. akan me sukema dariya?Yaya sannu da dawowa !duk suka fad'a atare"fuska bbu yabo bbu fallasa ya amsa.yana nufar k'ofar d'akinsa...wucewa Khadija da Maryam sukayi"hafsat tayi saurin cewa" Yaya wani waje kaje ko?"naga banganka ba."
Yace "eh "d'aurin auren abokin Yaya mahmod naje."gama sak'onki"yafad'a Yana saka hannu a aljihun gaban rigar sa"yazaro waya toch screem.zaro ido tayi had'e da cewa"wow Masha Allah!yaya nidai ko baby nokia zaka siyamun"dg baya kabani babba.yanzun mama zata tambayeni bansan mezanceba?"in Nokia ce kaga saina kashe inmungama waya"inzan kiraka sai inkuna ko?"k'afeta yyi da ido yanata kallonta"aransa yana mamakin wayonta"sannan yagama fahimta mama jummai batasanshi da hafsat kenan..Yaya kayi shiru? "tafad'a tana kallon sa"sunkuyadda kanta k'asa tayi sbd ganin irin kallon dayake mata.

Ahankali yace"kinfison Nokia d'in?"

Tace" eh"
Yana bud'e k'ofar d'akin yace".to shikenan zansiyamiki da dare"dama nasiya miki sim card"yeeeeeeeeee! tafad'a tana tsallen murna "sai dariya takeyi"dukda tasan wayar ba babba bace"amma tanason tayi ko nokia sbd waya na burgeta inta ganta ahannun Yaya zee"ayanzunma tsoron mama yasa zata hak'ura da babbar"kobayan tayi SSCE saitayi babban...

Shima murmushin yayi yace."gobe fane tafiyar da safe"kai Yaya kabari sai marece mana dan Allah! tak'are maganar da shagwab'a.
Hafsat kiyi hakuri natafi da safen kinga banaso nayi dare ahanya"kin yarda? yafad'a cikin wata muryar dabatasanshi da itaba"batare data kallesa ba tace". Allah yakaimu to.yace "ameen to kisaki fuskarki mana!nifa wlh Yaya banaso katafi kabarni .kasan dama duk acikinku kafisu sauk'i"d'an murmushi yayi yace" to kibi kowa ahankali karkiyi laifin daza'a miki hukunci"Kuma kimaida hankali a skul. "kinga Kuna last term naku, befi 2 month kuyi exams ba..hafsat dake saurarensa tace." to Yaya insha Allah zanyi duk yadda kace"bara nakoma Kar anemeni.yana murmushi yace" to shikenan k'anwar yayanta"tunda kingama firan dani"lah Yaya bahaka bane wlh"ai zanzo anjima gurinsu Maryam da dare nasan zanganka ko?eh Zaki ganni "yafad'a Yana shiga cikin d'akin.yyinda itakuma ta wucewarta...

##########

Gaba d'aya yaran gidan sun fito zasu tafi islamiyya"adedenan kuma Yaya mahmod yayi horn" me gadi yabud'e mishi get".
Nurane agdn gaba"sai friends nasu su biyu a back sit..nura yyi murmushi had'e da cewa lah kaga gasu baby (Khadija)can "islamiyya ma zasu tafi kenan?"banza Yaya mahmod yamishi Yana sake had'e fuska"
shikuwa nura tsokanace sarai yakeyi,sbd yagano cewa Khadija ba Abba bane mahaifinta"y'ar amaryarsace"sannan yanaso yatabbatar da cewa ko Yaya mahmod nasonta ne"shiyasa bayason yakulata"danshi nurama yanada wacce zai aura.

Fitowa sukayi dg cikin motar"alokacin kuma harsu Khadija sunficema dg gidan."
part d'in mazan gidan suka wuce"Yaya mahmod yamusu iso parlourn sa.bayan yabud'e k'ofar duk suka shigo.komai yana ajere inda Khadija ta shirya"bud'e komai Yaya mahmod yyi"Yana cewa"kumatso kuyi seving kanku,bbu d'an iskan k'aton dazan zubama komai...Nura yyi dariyar shakiyanci yace harda kaima k'atonne tunda bakada mata"garani tawa matar tana anan gidan"tsaki Yaya mahmod yaja had'e da cewa to namamajo!sarkin sin mata" kayi mana shiru dan Allah.Nura yace"to yayanmu,yyinda Yaya mohmod yamishi banza kawai..bayan yazuma kansa komai yaja gefe yafara kaiwa cikinsa...musbahu d'aya acikin bak'in yakalli mahmod yace ohni abokina halinka na nan?banza Yaya mahmod yamishi ,duk suka saka dariya suna fad'in matarka taga takanta wlh"nura na dariya yace ai anbadashi tuni...

Gaba d'aya kwasar girkin sukeyi sunata santi"nura yace nasanma baby ce tayi girkin nan"musbahu da ahmed sukace gsky ta iya "wannan irin delicious haka"uffan Yaya mahmod bece musuba harsuka kammala cin abincin"sukad'an huta tukum suka mishi sallama"nura nacewa su had'e a office ranar Monday...

Gurin karfe 6:15 Khadija ta nufi d'akin Yaya mahmod sbd ta kwaso kayan abincin dayaci shida abokansa...saidai tana k'ok'arin shiga parlourn sa"zee data fito dg d'akin Yaya Kamal taganta"saidai ita khadijar bataganta ba..wani irin girgiza Kai zee tayi"ta wuce sashensu bakinta fal da mgn.

Khadija kuwa tana shiga parlourn "baya ciki hakan yasa ta share kawai ta tattare kayan zata fito ,shikuma yashigo cikin parlourn"had'a ido sukayi,tayi saurin sunku yadda da kanta ak'asa"tana wasa da yatsun hannunta"zama yyi akujerar dake kallon ta yace".gobe Zaki rakani anguwa bayan kundawo dg islamiyya"dato ta amsa.yace khairat ta sake tsokanarkine?kanta ak'asa tace".ah ah" yace okay.itakuma ta wuce,yabita da kallo Yana lumshe ido...

Zee na zuwa tasami mama jummai a parlour"Zama ta tashi sbd lokacin sallar magrib yyi"ta zauna jiki asanyaye tace" .mama wlh abinda nake gudu zai faru"da idona naga y'ar iskar yarinyar nan Khadija ta shiga d'akin Yaya mahmod"zaro ido mama jummai tayi had'e da cewa"da gske?

Zee tace "wlh"

Mama tace"d'azunfa nasami labarin cewa yamari khairat akanta"karfa ace son yarinyar nan yakeyi"hmmmm to wlh saidai Kar ak'ara cewar zee cikin k'unar rai.

Mama jummai tace gobe zuwa Gurin mlm nahayin gada yakamani wlh"amma kafin naje goben saina san yadda nacusawa hjy hakima zancen nan.zee tace"dadai yafi wlh...

*washe gari*
Tunda aka gama sallar asuba "hafsat ta wuce kitchen"tayiwa Yaya Yusuf cake da dambun naman kaza.sai Gurin karfe 8:3O ta Gama"mama jummai dakebinta da kallon tambaya tace "ke uwar kilbibi duk waye yasaki wannan aikin haka" kin kwashemun nama a freeza?"uhmmmm! Yaya Kamal ne"tab'e baki mama jummai tayi had'e da cigaba da abinda takeyi"hafsat tayi rapping komai ta d'auka ta fito dashi"tana k'ok'arin fita suka had'u da Yaya Yusuf zaishigo yamusu sallama"
turus tayi ta tsaya tace"Yaya harka shirya ne?Yana kallon ta da kayan hannunta yace "eh "Ina zakije haka?tana murmushi tace".gurinka manah....tsab acikin kunnan mama jummai"muraya k'asa yace kije parking space kijirani nayi wasu mama sallama.dato ta amsa ta wuce ,shikuma ya Ida shigowa parlourn.yaga mama tsaye tana jera kayan break fast kan table"har k'asa yaduk'a yagaida ita"yasanarmata zaitafi"d'an Jim tayi kafin tace". Allah yataimaka ya tsare hanya"ya amsa Yana fitowa.tsaki mama jummai taja had'e da cewa wlh jikinki zqi gayamiki inkindawo"dama shinekikayiwa kayan dad'i haka?
kikamun k'aryar Kamal yasakaki".

Khadija kuwa yau Yaya mahmod baice takaimishi komaiba"duk saitaji tanason zuwa ko gaidashi tayine"hijab nata ta saka iya gwiwa ta nufi d'akin sa"
tana k'ok'arin shiga ta hango khairat nata kallonta"gabanta taji yafad'i"tanajin kodai tafasa shiga kawai...
Yana zaune kan carpet da laptop agabansa Yana latsawa"jikinsa sanye da farar jallabiya.tayi sallama akofar parlourn"kasancewar a bud'e k'ofar take.amsawa yyi batare daya d'ago kansa ba.nesa dashi ta tsaya tace".Yaya Ina kwana?lfy qlau"yanzun da zanma saka akiraki munke girkin jiya yayi dad'i nagode..tayi mamakinsa sosai"murmushi kawai tayi kanta ak'asa tace".bara nakoma dama gaidakai nazo nayi ne"kafin yace wani abu sukaji muryan hjy tana cewa gsky khairat innaje Naga yarinyar nan bata ad'akin nan Zan sab'amiki" sbd jiyama haka kika Mana k'arya"shiyasa nace bara nazo da kaina....โœ๏ธ๐Ÿ˜ณ๐Ÿฅฑ๐Ÿ™„

Comments kawai guys๐Ÿฅฐ๐Ÿค—๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

๐ŸŒนA GIDA D'AYA๐ŸŒน
๐Ÿ˜๏ธ๐Ÿ˜๏ธ

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ



Story & written by mmn fareesa

Wannan shafin nakine halak malak mmn bilkisu๐Ÿฅฐ๐Ÿ’–


๐Ÿ…ฟ๏ธ11&12

.....Wani irin mugun bugawa k'irjin Khadija yyi"tana kallon Yaya mahmoud cikin mugun tsoro da fargaba. k'ok'arin mgn takeyi"yyi saurin mik'ewa tsaye yafinciki hannunta suka shige bedroom d'insa.... adedenan kuma hjy da khairat suka shigo".
adede wani corridor dayake ajiye basket d'in kayan wankinsa" anan yajanye kwandon da sauri yace".kitsaya anan karkiyi motsi kinji?babu abinda zai faru.bejira cewartaba,ya ajiye basket d'in agaban inda ta tsuguna.hakan yyi daidai da shigowar hjy tana cewa".wai kana Ina ne?"inata sallama a parlourn ka"murmushin k'arfin hali yyi yace".hjy keda kanki?basai kisaka akiraniba"hjy tace hmmmm!ancemun algungumar yarinyar nan Khadija na nan d'akinka!shine nazo nagani da idona in raina mgn ta kayine."ta k'are maganar tana y'an kalle kalle ad'akin"Yaya mahmod yadubeta yace "haba hjy meyasa kike d'aukar maganar jita jita?"waye ma yafad'a mikine?"hjy ta tab'e baki had'e da cewa".khairat Mana"yace tana Ina?gatacan parlou.cikin borin kunya yafara mgn da cewa" Allah hjy darajarki wannan sakaryar yarinyar keci"bara naganta saita fad'amun inni sa'an wasantane... yafad'a yana k'ok'arin fita"sbd yanason janye hankalin hjy ta fito dg bed room d'in...

Hjy tadakatar dashi da cewa"karka Mata komai nace ko?"bece komaiba yabar d'akin ,hakan yasa hjy tabi bayansa.

Khadija datayi sharkaf da gumi sbd fargaba da tsoro" tasaki ajiyar zuciya.afili tace ohni Khadija nashiga ukku!anya zansake shigowa d'akin nan kuwa"wannan wace irin masiface??Mena tsarewa wasu agidan nan?"tunda take bata tab'a tsayawa ba,taji tana son amata aure sai yau"azuciyar ta ta aiyana muddin tasami mai sonta" gara tayi aure ta huta da wannan abin da ake mata acikin gidan...

Khairat dake tsaye a parlourn tanajin maganar sa"tayi wuf ta fice da gudu dg parlourn"Koda ya fito yaga batanan.yaja tsaki had'e da zama gefen kujera.hjy data biyosa tace"dan Allah karage saurin fushin nan"hmmmm!amma hjy fisabilillahi hakan daidaine?banaso kina shiga harkan yarinyar nan"Abba yamiki mgn banaso asami matsala dan Allah".cikin fad'a hjy tace".sokake yadda uwarta ta mallake ubanka" kaima su mallakemun Kai kome?"yace "hjy dan ALLAH kidena fad'in hakan"nifa amatsayin kanwa nad'auketa."inama iya kwana2 ban gantaba! ko kwana 2 banmata mgn ba"kuma dama gyaran d'akine nake sata wani lokacin, sai ko tadafamun wani abu...hjy ta tab'e baki had'e da cewa to nahana dg yau"kome kakeso zannce gasu ummi da Maryam nan ko?cikin marairai cewa yace".amma hjy kinsan inada k'yank'yami ko?"sannan yaran nan me suka iya? inba abasu kud'i su karb'e ba.yakamata hjy kiduba kyautatawar anty agareni kidena nuna hakan akan y'arta"sannan duk Wanda zaice miki kaza to kiyi bincike kafin kid'auki mataki"hakafa yarinyar nan jiya tamana k'arya"inda kinnuna mata ranki yab'aci aibazata sake wata k'aryarba"amma wlh hjy kisani sbd ke kawai zan auri khairat"amma wlh anawa tsarin batamun ba...duk wacce ke mutuniyar arzik'i bazatayi abinda tayiba"sharrifa tamana hjy nida khadija.inhar bamu yafeba sai Allah yabi mana hak'k'inmu.yanzun me wannan halin hjy kike ganin tadace data zama suruka agareki?"

Shiru kawai hjy tayi jikinta asanyaye"sbd maganganun Yaya mahmod sunyi tasiri aranta".tana kallonsa tace".kayi hakuri zan tsawatar Mata sosai.abinda yasa kaga na nace ka aureta"yarinyar nan ta nuna duk duniya bbu Wanda takeso saikai.
"kasan zumuncin dake tsakanin mu da mahaifiyarta.kuma mamanta ta rok'i alfarmar nasaka ka auri khairat" sbd ita kad'ai ta mallaka aduniya.nikuma nasan duk cikinku kafi kowa yimun biyayya dagudun b'acinraina.hakan yasa nabaka umarnin aurenta!namiji mijin mace 4 ne"dg baya saika auri wacce kakeso bayan aurenku da ita..badan yasoba yace"nafahimta hjy Allah yakyauta.

Hjy tace "ameen tana fita da nufin tayiwa khairat tas sbd itama ta bata haushi"

Hjy na fita Yaya mahmod yasaki ajiyar zuciya"yatashi ya wuce bed room d'in.

Khadija kuwa duk tanajin magan ganunsu da hjy.tanajin fitarta tayi wuf ta fito dg mab'oyarta"duktayi gumi,tana goge gumin da gefen hijab nata yashigo"
satar kallon sa tayi ,suka had'a ido"ta duk'ar da kanta ak'asa...zo muje parlour "yafad'a Yana juyawa yafita"

saida yasakawa k'ofar parlourn key"tukum yajuyo danufin yadawo yazauna"hakan yyi daidai da fitowarta dg bed room d'in"atsorace tace".Yaya kabud'emun nafita dan Allah!zama yyi kafin yace".kizauna muyi mgn"sannan saiki tafin ko? yafad'a fuska agimtse .hakan yasa ta k'araso ta zauna kan carpet.

Inaso kimanta da abinda khairat keyi"kikuma d'auki abinda hjy kenunuwa amatsayin kuskure.duk wani abu danake sakaki kimun bazai canzaba zaki cigaba damun..
Itadai tana aikin saurarensa"amma batace komai ba.wace irin waya kikeso?"yatambayeta Yana tsareta da idanunsa masu haske....uhumm!nifa banida zab'i "duk wacce akabani nagode.
Ok to shikenan inkindawo islamiyya Gurin 11am" kisameni a parking space,sai muje nakaiki ki zab'a.da sauri ta d'ago kanta suka had'a ido"janye idanunta tayi tace".kayi hakuri Yaya dan Allah karwani yaganni yasanarwa hjy...zakije koba zakijeba?yatambayeta cikin muryansa maiba mararjin mgn tsoro"jikinta nakirma tace zanje.tab'e baki yyi had'e da tashi yabud'e k'ofar"yad'an lek'a kansa waje ,kafin yace".zokitafi!da sauri ta tashi ta fice.yagirgiza kansa kawai Yana rufe k'ofar...

Yaya Yusuf na fita"directly inda motarsa ke fake yanufa"yyinda hafsat na back sit tana jiransa suyi sallama.
back sit d'in yabud'e yashiga"yabar murfin abud'e".
Hafsat tayi saurin cewa"Yaya gashi namaka, ka ajiye amasaukin kadunka ci..Yana kallon ta Yana murmushi yace".gsky hafsat d'ina tanaji dani"miye aciki to?"hmmmm!Yaya saikaje zaka ganidai"to shikenan nagode sosai, yafad'a Yana mik'o Mata baby nokia yace". gashi mudunga gaisawa kullum ko?ko bakyasan jin murya tane? yafad'a cikin wata iriyar murya"shiru kawai tayi tana murmushi"kud'ine yafito dasu "yasaka Mata atafin hannunata.tadubi kud'in ta girgiza Kai tana cewa"nifa yaya bazan karb'i kud'in nan"tunda kaima yakamata ace akwai kud'i sosai awajenka tunda wani gari zakaje.amma inaso ace first salary naka mu raba nidakai"tafad'a cikin tsokana.ita dashi duk sukayi y'ar dariya.Yaya Yusuf yace".kinsan banason shirme ko?kayan kwalliya zaki siya kidinkayi agida "ba inzaki fitaba".ki kula da kanki kinjiko? yafad'a Yana Kara saka mata kud'in ahannunta"kallon kud'in tayi"ta k'irgi 5K tace". Allah Yaya sun isheni kayi hakuri kaje dasu kaji ?ta fad'a cikin shagwaba"Yana kallon ta cikin murmushi yace".yanzun to first salary nawa zamu raba kamar yadda kikace kin yarda?"tana murmushi tace". Eh"
hafsat kikoma ciki" bara natafi kinji?"narai narai tayi da ido ,ta yunk'ura zata fita"yyi saurin cewa"karkiyi kuka kinji?2 weeks zanyi nadawo"Kuma zamuyi waya Dana sauka kinjiko?"d'aga mishi kanta tayi tana ficewa"yalumshe ido Yana jin tamkar yakamota yarungume..da haka yakoma driver sit"yaja motar yabar gidan..

Hafsat kuwa sak'e wayar tayi ajikinta"ta rik'e kud'in ahannunta"ta wuce sashensu".

Mama jummai nakan kujera zaune tana dakon shigowar hafsat".saidai lokacin da hafsat ta shigo"idanun mama jummai sukahasko Mata kud'in dake hannunta"
K``!zonan dan uwarki"
Tuni hafsat Tasha jinin jikinta"ke y'ar iska narabaki da yaron nan Yusuf bakiji ko?shine kikamun k'aryar Kamal yasaki aiki ashe shine kikamawa? Saikace kece kika siyi kajin kika samun a freezar.zaki sani wlh"dan Allah mama kiyi hakuri"cewar hafsat tana kuka da hawaye.

Mama jummai ta mik'e tsaye tana nufo hafsat"aikuwa tasaki kud'in hannunta zata gudu"taji an rik'eta ta baya"tana juyowa taga zee ce.kafin tace wani abu" mama jummai ta fincikota tafara duka da takalmi...duk yadda hafsat ke tsoron duka" hakan besa tayi shure shuren da wayar zata fad'o ajikinta ba.tana ihu dabawa mama jummai hakuri"saida tagaji ta k'yaleta "tana huci tace dg yau kicigaba da mun k'arya"nasan wa'ancan kud'in shine yabaki"bazaki Kuma amfana dako bicika ba.zee na zaune tana yatsina fuska tana kallon hafsat...itadai hafsat batace komai ba!tana share hawayenta ta rarrafa ta wuce d'akin su"itada bilkisu inda suke kwana"ta fito da wayar tanata kallo tana kuka"gwanin ban tausayi...

Tunani takeyi aranta me Yaya Yusuf yakashewa mama aduniya?dabata sanshine"tasandai duk iyaye nagari nason mutumin dake kyautatawa d'ansa"iya bakin gwargwado Yaya Yusuf yana kyautata mata..

share hawayenta tayi"ta d'auki wayar tamata b'oye acikin ward rope nata"

Toilet ta wuce sbd tagasa jikinta dake rad'ad'in duka...

***************
Hjy na fita ta sami khairat har bed room d'in ta"tayimata rashe rashe akan bed"hjy tayi tsaki aranta.tana ganin rashin tarbiyya irin na khairat koda ita y'ar hjy ce"ai akwai kunya ta sarakuta ... zama tayi kan stool tace".ke tashi muyi mgn"turo baki tayi had'e da tashi, sbd gaba d'aya taji zama gidan yafita aranta"
Hjy tace kisaurareni da kyau kiji abinda Zan fad'a miki.dg yau karki koma zuwa kicemun anyi kaza bacin kinsan k'arya kikeyi".keko kunyar k'arya bakiji?wlh hjy ba karya nakeyiba"da idona naganta!rufemin baki sokike sai mahmod yaji kinfice mishi arai kokuwa?namiji sakaraine duk inda ake kulawa dashi ake tarairayarsa to hankalinsa yafi raja'a acan"amatsayinki na y'a mace kebazakiyi hakanba.saiki dinga abubuwan dasuke zubar miki da k'ima kina b'ata kanki agurinsa"kicanza tun wuri kinji abinda nagaya maki...

Khairat tace".hmmmm!hjy yaya yatsaroki ko?amma bbu komai "zanyi yadda kikace shikenan."

b'angaren Khadija kuwa"gani takeyi Yaya mahmod natakurata ne .da wannan tunanin ta iso part nasu.... d'akin da anty t ware Mata take kwana acan ta shiga ta zauna" tayi tagumi ta Lula tunani..yanxun damuwarta shine" Yaya auwal kwata kwata yanxun bbu ruwanshi da ita. Ko ganinta yyi saiya d'auke kanshi"intagaisheshi itadasu ummi wani lokacin saiya d'auke kanshi yake amsawa.ita inda zaizo yace yana sonta! data amince kodan tabar gidan nan."sbd tasan dai aurene zai rabata da gidan..jikinta asanyaye tayi Shirin zuwa islamiyya.

Kamar yadda yafad'a Mata 11 am"tasameshi a parking space.shirywa tayi cikin farin las doguwar riga"tayane kanta da veil fari.tayiwa anty bayanin inda zasu tafi.anty tamata gargad'in ta rik'e mutuncinta takuma Kama kanta akona zasuje.kafin ta fito dg part nasu"hjy da khairat na zaune a waiting parlour suna kallo.batace musu komaiba ta fice"khairat ta ja tsaki aranta tana jin tamkar ta finciko Khadija ta mata mugun duka...

Yaya mahmod kuwa shima becika son african time ba"tana fitowa tahangoshi da alama dg sashen mazan gidan yake"aranta tana yaba kyawunsa da iya dressing nashi"duk wankan dazai d'auka saiya mishi kyau..ayanzun haka sanye yake cikin k'ananun Kaya riga da wando jeans sai takalmi sawu ciki"kansa yasha gyara sai k'yalli yakeyi.ga k'amshin da inya gifta tagaban mutum yake sakar mishi"agogon dake daure antsintsiyar hannunsa ya duba"11:12am .

saidai Kuma Yana k'ok'arin shiga shashensu hjy yahangota tana nufar parking space"hakan yasa yabi bayanta"saigashi yacimmata kasancewar tak'in nmj da mace ba d'aya ba.dukda shi cikin nutsuwa da kasaita yake tafiyar tashi...

Khadija kuwa tayi mamakin ganin harya wuceta"sauri tayi ta iso gurin motar dataga Yana k'ok'arin bud'ewa.

"Ahankali yabude Mata front sit yace"kishiga ciki"yana fad'in hakan ,yazagaya yashiga driver sit.batace komai ba itama tayi bissimillah ta shiga.wani sanyayyen k'amshi had'e da sanyin AC yadaki hancinta"ta lumshe ido tana yaba kyawun motar aranta .yaya Ina wuni? tafad'a lokacin daya bawa motar wuta suka fice dg get d'in gidan...yatsina fuska yyi,kafin yace". yini ko kwana?"uhumm!kawai tace" dg nan taja bakinta ta tsuk'e"shima bece komaiba" Yana sauraren wa'azin marigayi shakh jafar...da haka har suka iso safa da marwa communication!
Parking yyi yafito "itama ta bud'e k'ofar ta fito tana kallon gurin".sai asannan yasami damar k'arewa dressing nata kallo!muje ciki"yafad'a yana k'ok'arin shiga k'ofar dazata sadaka da cikin Gurin..bin bayansa tayi"suka tsaya layin dakeda wayoyi manya masu tsada...hii baby!zoki duba anan"koba waya zaki siyaba?cewar wani acikin masu siyarda wayoyin. Yana tsaye abayansu...Shiru
tayi tana satar kallon Yaya mahmoud "dake tsaye yana duba wasu wayoyi.taga yanabin guy d'in da wani irin kallo"tuni yasha jinin jikinsa.WOW!
*mahmod Adam shema* "wlh shine k'awata"wasu y'anmata dasuka shigo gurin suke fad'a suna kallon Yaya mahmoud...sosai suka bawa Khadija mamaki sbd ganin sunnufi gurinsa"shikuwa wannan guy d'in basarwa yyi yanatadai kallon Khadija.

Assalamu Alaikumlaikum ! yarinyar dake gaba ta fad'a tana kallon Yaya mahmoud".yatsina fuska yyi"sbd yasan bewuce tace" tana ganinsa gidan TV ko a jarida ba.sbd hakan yasa be cika yawan fita irin haka ba...juyowa yyi fuska agimtse Yana amsawa"gaba d'aya sai sukaji yamusu kwarjini.tagaban tace". I'm happy to see you wlh!munajin dad'in shirinku akan matsalolin mata.batare daya kalletaba yace nagode"Yana kallon Khadija yamaka Mata harara had'e da cewa" zonan!

Jikinsu asanyaye y'an matan suka wuce gaba abinsu.

"Khadija ta tab'e baki ,aranta tana ganin k'arfin halin su na tare namiji harsuce suna farin cikin ganinsa.bakya jinane? yafad'a Yana kallon ta"da sauri ta juyo da nufin ta Isa gurinshi"k'afar ta ta turje..tasaki k'ara tana rintse ido"sbd tasanma fad'uwa zatayi"saidai kawai tajita anyi saurin ruk'o ta"tafad'o jikinsa.da sauri ta bud'e idonta"taganta jikin Yaya mahmod....cike da mamaki take k'ok'arin barin jikinsa"taji yace kidinga kulawa yarinya dakinsha k'asa.matsawa tayi cike da kunya"yamik'o mata kwalin wayar dake hannunsa" iPhone 7+ .cike da kunya ta karb'a"tafara k'ok'arin dubawa"saidai kafin tayi wani abu taga yabasu ATM card d'in sa sucire kud'in...gaba d'aya tsoro yakamata Ina ita Ina rik'e wannan wayar...

tanadai tsaye har akagama cire kud'in"yajuyo yakalleta cike da kulawa yace".tayimiki ko acanja ne?"sunkuyadda kanta k'asa tayi"ahankali tace"amma Yaya wayar tamun tsadafa"hmmm! muje kawai "yafad'a Yana kallon ta.hakan yasa batace komai ba tayi gaba yanabinta abaya"wasu y'an mata3 suka bisu da kallo suna kus kus...

Suna shiga mota"maimakon taga sunyi hanyar gida.saitaga yacanza hanya"tanaso ta tambayesa Ina zasuje ?amma tana shakku"shikuwa yagama fahimtar abinda ke ranta.yana tuk'insa yace".office nawa zankaiki kije kigani yau"tunda baki tab'a tambayata Yaya meye aikin kaba ko??"d'an murmushi tayi kafin tace".ai Yaya baka fira da yara "shiyasa bantam bayeka ba.

To yanzun zamuje har office nawa kigani"ko bakyasan zuwane?
Lah! "Ah ah "
bece komaiba"Yacigaba da driving d'in sa"yyinda k'asan ran Khadija na fargabar yadda mutanan gidan zasu fassara ta"intace Yaya mahmod ne yasiya Mata wannan tsadaddar wayar..
Parking yyi yana cewa".fito muje agurguje"dato ta amsa suna fitowa dg motar suka shige gidan TV d'in.gaba d'aya sai Khadija ta koma wata bak'auya "dukda bbu mutanema sosai sbd yau week end"sai kallonsu akeyi"Yana gaisawa da mutane jifa jifa"har suka iso office nashi .ya bud'e Mata suka shiga.tana d'an murmushi tace".Masha Allah! Allah yatsare yasa albarka.fuska asake yace ameen...wasu files yaduba,bayan yayi y'an rubuce rubucensa yamaida yarufe.kafin yakalleta yace muje to"tunda kink'i Zama ko?"batace komai ba suka fito"aranta tana yaba tsarin Gurin da haduwar office nashi...da wannan tunanin suka iso gd.

Yaya mahmod na Danna hancin motarsa cikin gidan"idanunsa suka hasko mishi zee da ibbi tsaye suna fira.

Parking yyi,ko sauraren Khadija dake mishi godiya beyiba"yanufi gurinsu....zee data d'ago da nufin yin mgn ta hangoshi yanufosu.fuskarsa bbu annuri"atake antar cikinta ta kad'a.atsorace ta dubi ibbi tace".nashiga ukku!yayanmu yaganka ,dan Allah kagaidashi koyamun hukunci Mai sauk'i...kafin ibbi yace wani abu sunga Yaya mahmod tsaye agabansu ,Yana jifansu da wani irin kallo"kafin yadubi ibbi ,cikin dakakkiyar muryansayace".dg yau karnakoma ganin k'afafunka agidan nan"inba hakaba kuwa"yafad'a Yana girgiza Kai had'e da nuna mishi yatsunshi 2"yanabinshi da wani irin kallo...dg bosani yace". get aut! gaba d'aya ibbi yasha jinin jikinsa "sbd Yaya mahmod yamishi kwarjini sosai.bece komaiba yajuya ya fice... yyinda zee sbd tsabar tsoro kanta aduk'e yake...marar kunyar banza da wofi"duk kirasa Wanda zaki tsaya dashi sai wannan marar tarbiyyar.dan Allah kayi hakuri Yaya natuba"tsaki yaja had'e da cewa duk ranar danakoma ganinki dashi Zaki gane bakida wayo"kije kisaka broom kishare duka compaund d'in gidan nan"inma bakiyiva Zan tambayi isag driver.yana fad'in hakan yawuce yaje ya rufe motar sa"ya wuce sashensu na samarin gidan...

Zee kuwa tasan Bata Isa tak'iyin abinda yace ba".dolenta taje ta d'akko broom tafara sharewa"tanajin zafi aranta.sbd aganinta ita tagirmewa hakan.kuma ajinta zai zube inma wani yashigo gidan yaganta tana shara"hakan yasa tak'ara bada himma"k'asan ranta Tasha alwashin bazata rabu da ibbi ba...

Khadija kuwa ganin be saurareta ba"kawai saita fito ta wuce cikin gida kawai"a parlour ta tami anty"anty tace".sai yanzun Khadija?"
Tace"eh wlh kinsan Yaya Mai jama'ane gashi da farin jini wlh...tashiga bawa anty labari...kafin ta nuna Mata wayar"ita kanta anty tayi mamakin d'aya siya Mata wayar"hakan yasa tace zankaiwa alh wayar yagani zuwa gobe inyadawo anan.naji ta bakinsa"amma Ina tsoron nabaki wayar nan Khadija"

Khadija tace"hakane anty Allah ya kyau ta...

Washe gari kasancewar yau Monday duk wasuna skul,wasu na office.

Yaya mahmod na zaune a office nashi"aka turo k'ofar da k'arfi"hakan yasa yad'ago kansa sbd yaga wane marar kunyar ne.alh mudine tsaye !Yana bin Yaya mahmod da wani irin matsiyacin kallo"daka gansa kasan ransa ab'ace yake...

Maida kansa Yaya mahmod yyi "yacigaba da abinda yakeyi.

Cikin k'unar rai alh mudi yace"wlh !wlh!!kaji na rantse saina

Please Login or Register in order to submit comment