Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kayi basai kaji tabakina ba.nagode k'warai da zab'inka"tafad'a muryarta na rawa.
Abba yace". alhmdllh Masha Allah!insha allahu zakiyi alfahari da wannan auren kinjiko? Allah yayimiki albarka yasa alkhairi.batace komaiba ta tashi ta fice jikinta asanyaye...

Abba yabita da kallo na tausayi"tsab yafahimci batason auren sbd bbu yadda zatayi ta amince kawai.sab'anin shi Yaya mahmod daya fahimci yanason auren.

Tana fitowa sukayi clash da Yaya mahmod zai shigo parlourn"kafeta yyi golden eyes nashi yana kallo dajiran kota mishi mgn"saiyaga tarab'a gefensa ta wuce tana share hawayenta.gabansa yafad'i"musammun dayasan batasan shine zata auraba".gashi da alama Abba yasanar Mata kenan tunda gashi ta fito dg parlourn sa.. kukanta yatabbatar Masa da cewa batasonsa kenan?"yatambayi kansa.fasa shiga parlourn yyi yajuya yanufi part d'in mazan gidan"cikin wasi wasin k'ila wa k'ala..

Anty na zaune a parlourn ta"tanajiran shigowar Khadija taga Yaya mood nata ? saigashi ta shigo da gudu tana kuka wiwi...anty tace". Subahanallahi! Kunya zaki bamu Khadija?ni wlh banasonshi anty"shine dama ya hanani kowa da kula Yaya Tahir?harya dakesa"sbd yagammu tare. Khadija tafad'a cikin gunjin kuka"cikin tsawa anty tace".rufemin baki kiji abinda zan fad'a Miki shashashar banza dabatasan ciwon kantaba.
Ke yanzun bazakiyi farinciki da samun mahmod amatsayin mijiba?" mahmod yanada halayen k'warai dasanin yakamata "yanada aikinyi"uwa uba gata da cikakken asali.ga kyawun dayake dashi.nasan kinsan irin yanda mata kecewa suna sonshi amma duk bayaso.ko khairat ita da uwarta ke haukansu ,amma bayasonta.saike da mahaifinsa yaga dacewarku yahad'a ku!zakice bakisonsa.ainazata murna zakiyi ,kikoyi yadda zakiyi ta hanyar hikimarki ta y'a mace ki koya mishi sonki.sannan kimanta da uwarsa batasonki.natabbatar muddin kikayi hak'uri da juriya Khadija saikinci riba arayuwarki."uwarsa nasan bata k'aunar mu nidake"amma karki duba hakan"uwa uwace !ki girmamata kimutunta "shima zaiji dad'i.sannan karki sake kinuna wa mahmod da mutane bakisan auren nan.kitsaya kadaran kadahan.kebaki nuna kina soba" bakuma kinuna k'iba.ina fatan kin fahimceni?"

Ajiyar zuciya Khadija tasaki"jiki asanyaye tace".naji Kuma zanyi aiki da abinda kikace insha Allah.

Anty tace". dadai yafimiki alkhairi wlh"kina ganidai ubanki daba mutuncine dashiba"besanki besan darajar haihuwa ba" dasukaje neman aurenki gurinsa"cewa yyi shibema tab'a haihuwaba .mi hakan ke nufi?salon yatozartaki, yanuna hanyar da ko kinyi auren bazakiyi darajaba "komasu neman auren suyi zaton bakida ubah.ke yanzun indaba alh bane sukaje ,mekike tunanin zai faru?"sbd haka ki nutsu kibawa Mara d'a kunya kodan sbd mak'iyanmu.

Gaba d'aya kalaman anty sunyi tasiri k'warai azuciyar Khadija"taji Kuma zata iya auren Yaya mahmod ta zauna dashi bbu tsoro ko shakkar kowaye..

D'akin ta ta wuce ta kwanta kan katifarta.ta Lula tunani akan abubuwa sosai gameda Yaya mahmod"saitama Fara zargin kodai kishine to yake nunawa akantane?gefe guda Kuma tanajin zafin yadda Wai ace mahaifinta baya k'aunarta "Yana nunawa duniya ita tamkar ba jininsa bace.tunawa tayi da mutumin dasuka Fara chats dashi"da haryanzun takasa gane ko waye.wayarta ta d'akko tashiga what's app"taga kwana 3 baya online saita mayar da wayar kawai... tafad'a duniyar tunanin makomarta a auren Yaya mahmod? dakuma metayiwa mahaifinta yatsaneta.

****************
Tafe suke hanyar zuwa islamiyya" suna firar bikin Yaya mahmod da Khadija akan yadda zai kasance.sbd yau yakama satday.itadai Khadija batace komai ba "sauraron su kawai takeyi.ummi tace" antynmu kenan "kink'i mgn ko?yanzun xaki Fara shamana k'amshi tunda xaki auri yaya.murmushi kawai Khadija tayi had'e da cewa"hmmm!nice yau nazama anty Kuma?Maryam ta karb'e zancen da cewa" ai wlh lokacin da naji labarin cewa shizaki aura har rawa nayi wlh.dama banaso ya auri wannan khairat d'in Maison kud'i da k'aryar tsiya.hafsat dake gefensu ta na murmushi tace" nidai duk nafiku sani sbd sweet heart yasanarmun Allah!shiru kawai nayi bansanarmuku ba.ummi na murmurshi tace". ohni hafsat ta Yaya yusuf.hafsat kaitsaye bara nagaya masa"cewar hafsat cikin zolaya" "dariya suka kwashe da ita su duka.maryam tace". ikon Allah! Lallai ma Hafsat wlh"aidama tuni na lura Yaya Yusuf namugun sonki wlh.murmushi hafsat tayi tana jujjuya idanuwa tace" hmmm!jiyama wlh nayi kewarsa Yana busy bamuyi wayar dareba.amma nasan inmundawo zai kira.ummi tace".nidai pls karfa ki had'a mu dashi kinji?dariya hafsat tayi tana cewa" hmmm!wasafa nakeyi wlh"Allah yatsareni da had'a Yaya da k'anwarsa.duk suka saka dariya suna shiga get d'in islamiyyar.

Zaune zee take ak'asan sumunti ta jingina da bangon cel d'in"ta fige ta Yi bak'i sbd wahala da yunwa dakuma fargaba.kallon kunun kanwar dake gabanta tayi"Wanda tun d'azun aka kamata shi tayi kalacin safe.amma bazata iya shaba sbd k'yank'yami.ga wari da zauri dake tashi agurin.gaba d'aya taji ta tsani rayuwa ma gabad'aya"sannan rashin zuwan kowa nata yaganta"yasata jin k'aruwar fargaba da tsanar kanta da rayuwarta ma gaba d'aya.idanunta harsun sauya kala dg fari zuwa jajaye sbd kuka.tsawon satinta 5 kenan agurin Babu Wanda yazo nata yaganta.hakan bak'aramin ciwo da sakata kuka yakeba.sbd tana ganin tamkar batada gata yanzun...sau2 tana k'ok'arin gwada guduwa amma bata samu nassaraba.

jitakeyi inama itace su ummi da hafsat"sunacan gida hankali kwance sunacin abinda suka gadama"su kwanta inda sukeso"ita kuw gashi ak'asa take kwana ga zafi da sauro har zazzab'i tayi ta warke batasha maganiba.ko yanzun jikinta cizon saurone.hawaye masu zafi suka wanke Mata fuska.data tuna rabonta da wanka sati2" sau3 tayi wanka tunda tazo cel d'in... shaid'an ke raya Mata kawai takashe kanta tunda Babu me k'aunarta.

Tashi tsaye tayi ta taka karfen k'ofar "kasancewar duk wad'an suke tare acel d'in sunfita aiki ,itace arufe sbd zazzabin datayi yasa batafita aikinba.tasaka d'an kwalinta zata daure ta sama ta sarkafe kanta"wani jami'i Yana zagaye yahangota.cikin tashin hankali yanufi k'ofar cel d'in Yana daka Mata tsawa"Amma bata saurareshiba ta sarkafe kanta.da sauri yasaka key ya bud'e k'ofar"har idanunta sunfara juyewa"yanufeta da sauri"ya kwanceta.ajikinsa tafad'o sumammiyya..yayi waya wa commissioner akan azo abada taimakon gaggawa ga zee.

Acikin minti 3 akayi asibiti da ita"bayan ansanarwa su Abba da daddy halin datake ciki.

*************
Gaba d'aya nsu su goma suke tsaye gaban gadon da zee ke kwance suna binta da kallon tausayi.sbd canzawar da jikinta da fuskarta tayi.inno da mama jummai kuka sukeyi sbd tausayi.abba da daddy nadai gefe suna kallon zee dake bacci and'aura Mata drip"
Yyinda hjy da anty ke gefe guda zaune.

"ahankali zee ta bud'e idanunta dasuka canja kala akan fuskokin family d'in ta.wani kukan farinciki tasaki tanason ta tabbatar da cewa ba mafarki bane takeyi."inno ce ta katse mata tunani Gurin cewa" zainab sannu ya jikin?"
daddy Abba Dan Allah kuyafemin" natuba da kuskuran Dana aikata dan Allah...tana fad'in hakan tana kuka maiban tausayi.abba yace" babu damuwa ki kwantar da hankalinki bazaki koma a cel ba kinji ko?" sannan dg yanzun kome zai faru dake matsayin ki na musulma" datayi Imani da kaddara me kyau ko marar kyau.karki koma gigin cewa Zaki kashe kanki.duk Wanda yakashe kanshi da gangan yamutu kafiri.insha Allah Abba nadena nagode "Ina alfahari daku amatsayin iyayena.matsowa mama jummai tayi tana Kama zee ta taimaka Mata ta tashi zaune.hjy ta had'a tea Mai kauri aka bata da abinci"hannu baka hannu k'warya zee ta take abincin da tea d'in.sai kallon tausayi mama jummai Kevin y'ar ta dashi....Koda aka basu sallama Yaya mahmod ne yazo yad'aukesu"tunda zee ta gaishedashi ya amsa da lfy" bekoma kallonta ba.gaba d'aya tsanarta yakeji sbd tanason b'atawa family nasu suna.koda aka koma gida yaran gidan bbu laifi sun nuna damuwarsu akan zee"wanka tayi ta kwanta tacigaba da bacci cikin kwanciyar hankali"kasancewar rabonta da bacci me dad'i tun kafin arufeta.

*Bayan sati d'aya*

Ayau yakama saura kwana 12 bikin Yaya mahmod da Khadija "akuma jiya aka Kai lefenta gidan alh mukhtar yayan mahaifinta.akwati6 da Ghana"Khadija kuwa anata Mata gyaran jiki dukda batarewa zasuyiba Amma anaso tayi kyau na fitar biki.
Duk da walima ce kawai za'a yi anan cikin gidan. Babu wata bidi'ar daza'ayi.kuma Khadija bawasu k'awaye gareta sosaiba.dama k'awarta naja'atu (k'anwar Yaya auwal)tafi shak'uwa da sakin jiki da ita...gefe guda hjy rabi da khairat sun saka ido akan komai sbd sunfiso abikin mahmod da khairat komai yafita daban Dana khadija.ko Kai lefe ance maza zasukai Amma sai da hjy rabi tazo"saidai hjy ta kaita parlorn Abba tagani "sbd maza zasukai.komai nacikin lefen Saida ta k'irga...

Khadija kuwa wasan y'ar buya takeyi da Yaya mahmod"duk Yana hankalce da ita yashare "Yana nuna tamkar besan metakeyiba.

Ahankali Khadija ta fito cikin gayunta na d'aukar hankali"zataje amso d'inkunan biki"shine zataje gidansu naja ta biya Mata su wuce.sanye take da doguwar riga ta yellow d'in lace"tabuga d'aurin d'an kwalin ta.dayafito mata da kyawun fuskarta.ta yafa gyale akafad'arta.sai wayarta da hand bag nata dake hannunta.jikinta nafitar da sansanyan k'amshin turare.gaba d'aya hankalinta nakan wayarta zata fito da number d'in naja ta kirata "sbd tafito su wuce kawai.
Gam taji ta yi Karo da mutum"da sauri ta d'ago kanta.idanunta tsab acikin na Yaya mahmod.fuskarsa amatuk'ar had'e.hakan yasata saurin jada baya tana cewa" Yaya kayi hakuri ban luraba wlh.ina wuni?"dama kin iya gaisuwa ne?Aida ciga da nunawa kika rikayi Baki sanniba.Ina Kuma zaki haka kikayi wannan kwalliyar?kanta ak'asa tace".d'inkuna na zanje na karb'o"keda wa?aranta tace dama ai d'an jarida halittarsace tambaya.ki amsamin, kafin kicigaba da gulmar tawa cikin zuciya.cikin sanyin Murya tace".nifa Yaya ba haka bane"
Hmmmm!kingama guje gujen inkin ganni ki b'uya?duk lokacin da kikakoma hakan nidakene.kedawa zakuje karb'an d'inkin.nida naja ne! had'e girar sama data k'asa yyi"yace "okay k'anwar saurayinki kenan(auwal)shiru tayi batace komai ba.tanadai y'an kalle kalle"dg yau karnakoma ganinki kinshiga gidansu koyiwa auwal mgn Koda gaisuwace.kinji kobakijiba?jikinta asanyaye tace naji"kayi hakuri nama fasa fitar zankira telan yakawo anan.tafada muryanta na rawa...inkika sake kikamun kuka anan wlh d'akina zantafi dake sai dare kidawo....gum tayi batayi mgn ba"bani number d'in telan !sannan kigoge number shi dg phone naki "komeye naje na karb'o nabiyashi"inma wani d'inkin Zaki bada kimun mgn.da to kawai ta amsa .tana fito da number d'in alk'aseem tela "ta mik'a mishi wayar.yanata kallonta ya amsa.saidai yad'an saki fuskarsa"bayan yagama saka number d'in yabata wayar"kafin yace".kikoma gida bance kije ko inaba.bejira cewartaba yajuya yayi tafiyarsa.tarakashi da harara tana turo baki ta wuce cikin parlourn gidan...

*****************

Kwanci tashi bbu wuya agurin Allah"agobe ake d'aura auren Khadija da Yaya mahmod.gida bbu laifi yacika da bak'i na nesa Dana kusa.ko khairat anan aka tare tun jiya"Yaya Yusuf ma ayau zaidawo Yana hanya.hafsat tamkar ammata albishir da gidan aljannah sbd murna.zee ma Babu laifi ta murmuje Kuma tayi nadamar gsky.sannan ta rage izzar datakewa masu aikin gidan dakuma k'annanta sbd duka y'anmatan tagirmesu.ita kanta yanzun haushin abinda ta aikata abaya takeyi"ga Kuma wani irin son Yaya mahmod dake shigarta kullum.gashi tana ganin yamata nisa fintin kau.

Zazzaune suke awaiting parlourn gidan.kusan su 16 y'an matan gidan su 5 da k'awayensu su 11.sai maiyin zanen lalle"tana zanawa zee "da angama Mata za'a yi wa hafsat.svd anyiwa ummi da maryam.khadija dake zaune kusada naja ,tayi Shar gwanin burgewa duk Wanda yakalleta yasan itace amaryar.ita kuwa ganima takeyi anya ba wata zata mataba?sbd Kar lokaci yatafi...ringing d'in wayar hafsat iPhone 7+"da Yaya Yusuf yasiya Mata tafara ringing.adedenan Kuma khairat ta shigo parlourn.tana wani yauk'i da yatsina.babu Wanda yatankata"hafsat ta d'auki wayarta tana k'ok'arin barin parlourn.ummi na dariya tace oh angel d'in Yaya Yusuf miye abin jin kunya aisaikiyi gabanmu ko? hafsat tayi murmushi kawai tana d'aga Kiran...saigashi itama ummi Babu jumawa Tahir yakirata"naja na murmushi ta dubi Maryam tace".ohni k'awata yakamata mu aje makamammu nak'in kula samari akan sai mun Gama karatu.muzo muma mu shiga sahu.maryam nadariya tace." hmmm!k'awata so ko wahala?"bazan iyaba.inzaki iya babu damuwa" dama wlh na lura Yaya kabeer Yana ciki.duk suka saka dariya.itadai Khadija murmushi kawai tayi... tsit akayi da sauri Khadija ta d'ago kanta.tashaki k'amshin turaren Yaya mahmod.gabanta taji yafad'i dataga fuskarsa ad'aure..yayi kyau naban mamaki cikin suit farare da takalmi sawu ciki suma farare.ammishi askin angunci.lolx..gaba d'aya y'anmatan k'awayensu suka bishi da kallo.khadija kuwa addua takeyi aranta karya disgata konuna bayason auren agaban k'awayensu ya kunyatata..amamakinta saitaga yanufo gurinta.khairat tayi saurin cewa sweet heart sannu da dawowa....wani zafi Khadija taji ak'irjinta"da k'afa naja ta zungureta.suka had'a ido.da hannu ta Mata alamar tanajin khairat?"
Yaya mahmod banza yyi yashare kairat tamkar badashi takeba.yanufi Gurin Khadija"sunkuyawa yyi gefenta fuskarsa.gab danata yakai bakinsa saitin kunnen ta.yace"kitashi muje sashen inno gamai lalle zata miki. Banason wannan ta miki.naja duk tana saurarensu sbd tana kusada khadija.tayi murmushi aranta tana cewa Khadija kinyi sa'a komai nashi dabanne.samun kanta Khadija tayi da shagwab'e fuska "ahankali tace".nifa Yaya inajin kunyar tashi har naje can.okay Babu damuwa bara nad'aukeki kawai ko? yafad'a Yana tashi dg sunkuyawar dayyi.gaba d'aya mutanan dake cikin parlourn sunmaita attention d'insu agurinsu.khairat kuwa tamkar ta had'iyi zuciya ta mutu sbd bak'in ciki..

Khadija kuwa atunaninta wasa yakeyi"saitaji yace".madam kitashi kosaina d'aukekine ?"sai asannan sauran mutanan sukaji tattausan muryanshi.zee datakejin inama itace hakan yafaru akan ta.tace Yaya Ina wuni?"hakan yaba sauran y'anmatan damar gaidashi.be kalli kowacensuba"ya amsa da lfy qlau sannunku! yafad'a atakaice Yana Kama hannun khadija ta tashi tsaye"yajata suka fita.aikuwa parlourn ya hargitse da shewa da hayaniyarsu.kasancewar wasunsu naganinsa agidan TV.yau sunganshi zahiri da jin muryansa.... khairat sbd b'acin rai barin parlourn tayi"yayinda ummi da hafsat suka dawo bayan sungama wayarsu.
Naja itama! jitakeyi inama Yaya kabeer yafurta mata yanasonta"aida babu abinda zai hanata amsar soyayyar sa.sbd talura duk mazan gidan kyawawane" saidai wani yafi wani kyau.ga Kuma kyawun hali babu laifi"dukda taji ummi nafadar Yaya kabeer bayada hayaniya dayawan mgn sosai.koda agabanshi za'ayi Abu baya kulawa...

Ahanya kuwa tafe suke....✍️


Kuyi break fast harda lunch da dinner maπŸ˜œπŸƒβ€β™€οΈπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎπŸΎ

🌹A GIDA D'AYA🌹
🏘️🏘️

🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾🐾



Story & written by mmn fareesa


πŸ…ΏοΈ27&28


"Ahanya kuwa tafe suke Yana rik'e da hannunta guda"cikin sanyin Murya tace ".pls Yaya ka cikani naga gidan da jama'a!shareta yyi yacigaba da tafiyarsa.shiru tayi batace komai ba.

Can ciki yayi sallama a parlourn inno"kasancewar Mai lallen k'anwar nura(abokinsa) ce ita.

Hakan yasa nuran yakawota."
Amsawa khairiyya tayi tanata kallon su tana murmushi"

Yaya mahmod yace".khairiyya ga antynki nan kimata lalle Mai kyau Wanda yafi na Fatima(budurwar nura) y'ar dariya tayi tace".to shikenan Yaya mahmod "kallon Khadija yyi ido cikin ido yace" madam najira konatafi ?k'asa cewa komai Khadija tayi sai murmushi kawai.hannunta dake cikin nashi ya mintsina Yana cewa" to bara natafi smiler!zanje nadawo kimun addua.tana Zama kusada Fatima dake had'a komai na lallen tace". Allah yatsare yadawo da Kai lfy Yaya..fuska asake yace".ameen Yana fita dg parlourn.

Gaisawa sosai sukayi da juna"kafin Fatima tahau yiwa Khadija lalle nagani na fad'a...

**************
Tsaye yake gaban mirror d'in sa "Yana taje sumar kansa.ahankali ya ajiye cum d'in Yana shafa cikinsa.wayarsa yad'auka yayi Kiran Khadija"

Cikin siririyar muryarta tamishi sallama.saida ya lumshe ido sbd kasalar da muryarta ta haddasa mishi .cikin cool voice yace".angama Miki lallen?"okay kikamun abinci naci yanzun"tunda sainace kikula dani zaki kula ko?Yana fad'in hakan yakashe wayar.

Fitowa yyi zuwa parlourn sa yazauna.cikin shigar k'ananun Kaya....

Khadija kuwa ko mak'iyi yaganta yasan tayi "musammun yadda lallen yasake haska farar fatarta da gyaran jiki."gata ma'abociyar son gayu da kwalliya"sai abun yayi gwanin burgewa.tayi d'as da ita" sai kallonta jama'a keyi.
Riga da siket ne na atamfa tasaka sai mayafi yellow ta yafa akan gyaran gashin da aka mata...tana shafa lips stick Yaya mahmod yakirata.

Fitowa tayi ta nufi kitchen"food flux tasamu me 2 sama da k'asa " kasa tasaka sinasir ,dg sama ta zuba niyar kaji dataji alaiyahu.kafin ta rufe ta d'auki plux din da wayarta ta fice zuwasashen Yaya mahmod.tana k'ok'arin shiga hjy rabi dake bayanta taganta.

Hakan yasa ta juya ta koma ciki sbd ta shaidawa hjy hakeemah.kasancewar taga lokacin da khadijar ta fito taga kayan dake hannunta.shine ta biyota sbd taga Ina zata tafi"sbd ranta yabata a d'akin Yaya mahmod zata shiga..

Khadija kuwa batamasan hjy rabi nayiba"ta shigewarta d'akin bayan ta murd'a k'ofar.

Ahankali tayi sallama"yad'ago kansa dg latsa wayarsa dayakeyi ya amsa"yanamata wani irin kallo, jiyakeyi tamkar yaje yayi hugging nata.k'unshinta yayimugun yimishi kyau"yanata kallonta besan lokacin dayace zonan naga lallen naki"da sauri ta d'ago kanta tana ajiye food flux d'in agabansa kan carpet.

kasa cewa komai tayi sbd kunya dakuma fad'uwar da gabanta keyi"saima ta sunkuyadda kanta k'asa.sakkowa yyi Yana cewa shikenan tunda bazaki zoba"ke kinci abincin?
Yafad'a Yana Zama kusada da ita.batare data kallesa ba tace".ah ah rabona da abinci tun break fast"meyasa to?banajin yunwane ai"
Hmmmm! yafad'a Yana bud'e food flux d'in.fork d'in dake hannunta yamik'a hannunsa ya karb'a"yanata kallon hannayenta gwanin sha'awa.

Ahankali yafara yin Loma guda ,kafin yace Mrs mahmod bissimillah!girgiza kanta tayi"tana ce wa nak'oshi Yaya.

in har kinason samuna yadda kikeso to karkimun musu ko gaddama!Yana fad'in hakan yacigaba da cin abincin sa. Ita kuwa nauyi da kunya takeji sosai.
gyara zamanta tayi ta juyo suna fuskantar juna"yyinda shitabashi dariya sbd yagano kunya da nauyinsa takeji.gudan fork d'in ta d'auka zata diba a marfin food flux d'in sbd bbu Plate"yayi saurin cewa meyasa bakyajin mgn?kije kawai tunda bazaki iya cin abinci tareda da Wanda aka tursasaki ki aura agobe in Muna raye..

Saurin kallonsa tayi"yad'age gira guda"yace yes !kauda kanta tayi"ahankali tace".wlh Yaya nifa bahaka bane"hmmm!muci abinci kawai"shiru tayi tafara cin abincin tamkar wata y'ar yaye"shikuwa yanabinta da kallon k'asan ido"caraf taji yayi da hannunta guda Yana cewa "Masha Allah yayi kyau tunda nace kizo nagani kink'i zuwa ko?tsikar jikinta taji ta tashi "k'ok'arin janye hannunta guda takeyi"aka banko k'ofar Afusace.

Innalillahi wa inna ilaihir raju'un!hjy rabi ta fad'a tana kallon hjy hakimah da suka shigo parlourn tare.ta k'ara da cewa"kinganidai ko?gani yakori ji,in wani yagansu ance k'arya ne to gashi kingani da idonki...

Gaban Khadija inbacin dukan Tara Tara ,Babu abinda yakeyi sbd tsabar tsoro da fargaba.k'ok'arin k'wace hannunta takeyi"yak'i sake Mata"yanacin abincin sa hankali kwance ko ajikinsa.aransa yanajin tsanar hjy rabi na d'arsuwa aransa.

Mahmod dama abinda kuke aikatawa kenan?har dasu cin abinci tare ?Anya maganar khairat ta baya ba'a bun dubawa bace?"cewar hjy tana binsu da kallo "sai asannan yasaki hannun khadija Yana cewa tashi kije cikin gida.babu inda zataje sai anyi agabanta.cewar hjy rabi tana yiwa Khadija wani mugun kallo.

Gaba d'aya mahmod ransa yakai k'ololuwar b'aci akan hjy rabi da kalaman hjy itama.idanunsa harsun sauya kala bece komaiba" ya rufe food flux d'in.yana kallon Khadija dake k'ok'arin tashi.

Hjy ta dubesa tace".ban hanaka kula y'ar iskar yarinyar nan ba?"

Batare daya kalletaba yace".kiyi hakuri hjy abinci takawomun"shine kukeci tare ko?ke Kuma bak'ar daga ! tarbiyyar da uwarki tabaki kenan ko?tunda gashi kin lik'ema namiji daba a kaiga d'aura muku aureba.hjy tafad'a cikin tsawa tana hararar khadija.

Hjy rabi tace". Hmmm wama yasani ko uwarma da haka aka auro Miki itane"gashi ta lalata miki yaro.kuka sosai Khadija ta fashe dashi tana k'ok'arin barin parlourn.yayinda Yaya mahmod yakejin zuciya takaimishi iya wuya"cikin b'acin rai yace".hjy dan Allah kije part naku zanzo muyi mgn!yakamata ace kidena d'aukar jita jita na munafukai dabasaso ki zauna lafiya "kuma suna tare dakene sbd abun hannunki.inda bakidashi bakiganin Koda k'afarsuce...Yana fad'in hakan yatashi yabi bayan Khadija dake ficewa dg parlourn.

Hjy rabi ta tab'e baki sbd tasan ita Yaya mahmod yagaya ma mgn.kallon hjy tayi tace".hmmm!wlh inbakiyi da gaskeba sai sun rabaki da d'anki "nidai bara natafi tun kafin mahmod yakaimun duka sbd maganganunsa Ina zargin Dani yake"Kuma kin k'asa d'aukar mataki.shiru hjy tayi tana nazarin maganganun mahmod dana hjy rabi"fita tayi sbd ganin itama hjy rabi ta fita..

Mahmod na fita "cikin sauri yataddo khadija dake tafiya zuciyar ta na k'una"ta ayyanawa aranta inbacin darajar Abba dako Yaya mahmod shine autan maza Bata auresaba.ana aibata mahaifiyar ta damata sharri duk Dan kawai zata aureshi....Khadijaaaaaa!cak ta tsaya sbd jin muryar Yaya mahmod.bata juyoba" ahankali ya iso agabanta yace banason kukanki ki kishare hawayenki...bata Bari ya k'arasa mgn ba ta juya aguje tana kuka.

Tafe kansa yyi yace"Allah yakyauta yarabamu da sharrin shaid'anin mutane.

Yana fad'in hakan yyi saurin bin kwanar lambun gidan sbd hjy da hjy rabi daya hango...gaba d'aya ransa inyayi dubu b'ace yake"yaje yazauna yanata tunanin wace irin zuciya hjy kedashi"ita tunanin da yayi"Amma be gano me anty da Khadija sukayiwa hjy arayuwaba.saima ita hjy takemusu"ya lura sau kusan 2 hjy nazuwa tayi zaune d'akin abba ranan girkin anty.sannan agabansa ranar girkin hjy anty tatsaya bakin k'ofar parlourn Abba ta duk'a ta gaidashi"sbd gudun karta shigo hjy tace" ta b'ata mata....



***********
Khadija kuwa batabari wani ya lura da halin datake ciki ba"ta lallab'a ta wuce d'akin ta"saida taci kukanta Mai isarta ta wanke fuskarta"tayi alwallah sbd magrib tayi.

*Washe gari*

Da misalin k'arfe 11:am d'aruruwan jama'a suka shaida d'aurin auren mahmod da Khadija.akan sadakai dubu 50"

Yaya mahmod yasha wanka cikin farar shadda y'ar ciki da malun malun"kallo d'aya zaka masa kasan Yana cikin farin ciki.dukda baya dariya saidai murmushi.sai gaisawa yakeyi da jama'a suna mishi fatan alkhairi a aurensa.yyinda nura abokin ango suke tare da angon suka nufi cikin gidan.

Cike da tsokana nura dake kusadashi yace".mutumin naso ace fa ayau Khadija zata tare"nasan Babu abinda zai hanaka shiga dg ciki..tunba yanzunba nasan hanawar dakakeyi akulata kanka kakeyiwa tanadi.. yafad'a Yana. πŸ€£πŸ˜‚

Cikin basarwa Yaya mahmod yatab'e baki had'e da cewa d'an iska kawai"me zanji ajikin k'aramar yarinya?kaima kasan bazata iya daniba saina sake rainonta.tanadi Kuma"aikafi kowa sannun ta yadda aka sanarmun aurenta ko?

Nura na murmushi yace".hmmm! kadai fad'a ne kawai" amma wlh kanasonta sbd yadda kake nuna kishinta zahiri.. sannan inhar naganta da ciki kashiga ukku aguna wlh...banza Yaya mahmod yamishi suna Ida shiga cikin gidan.sashen hjy suka wuce.

Kallo d'aya zaka mata kasan tana cikin damuwa"sbd fuskarta bbu walwala.gaba d'aya sai Yaya mahmod yaji jikinsa yyi sanyi"murnansa ta koma ciki.sbd aganinsa tunda mahaifiyar'sa batayi farin ciki da aurensaba ai auren bazaiyi albarkaba dukda shi yanaso.lfy qlau...muryar hjy ta katse mishi tunaninsa tana amsa gaisuwar nura"kafin tayi suarin dakatar da nura ta hanyar cewa bawani photo d'in dazan d'auka tunda banason auren ku b'acemun da gani anan..gaba d'aya sai Yaya mahmod yaji ya kunyata yakuma ji nauyin nura"hakan da nura yalura dashi yasashi fahimtar hjy batason ya auri Khadija"yana murmushi yace".
ayimana hakuri hajiyarmu munfice.yana fad'in hakan yaja hannun Yaya mahmod suka fita.

Khadija najin anyi bud'a gabanta taji yafad'i domin ta tabbatar da cewa an d'aura auren kenan.

Tasha make up na musammun irin na amare masu gata.anata photuna ,daurewa kawai takeyi tana yak'e"saidai tayi mamakin har aka Gama pics babu ango da abokansa.gaba d'aya y'an matan gidan sunsha make up da kayansu na alfarma. Yaya Yusuf kuwa shida sahibarshi shadda lemon green suka saka iri d'aya.sai kallonsu akeyi ana kus kus..


da misalin karfe 4:30pm gaba d'aya y'an matan gidan be da k'awayensu a haraban gidan"Mai dj yasaki kid'a ana cashewa.itadai Khadija na zaune harta canza kaya.tana mamakin Ina Yaya mahmod yashige"wasu friends nasu batacewa Ina ango da abokansa"saidai ummi tace "ango big broth me baya bidia"hakanma datace yasaka zuciyar Khadija sanyi.saidai ranta yab'aci sosai" takuma sha alwashin Koda yanzun yazama mijinta zaiga Jan aji wlh da sharewa...duk abinda ke wakana khairat na lura da komai"Kuma tayi from ciki da hakan..

Yaya mahmod kuwa hankalinsa ba a kwanceba "sbd ganin mood d'in hajiyarsa"duk yadda yakeson Khadija zai iya hakura da ita indai hjy zatayi farin ciki da hakan.yanason mahaifiyar'sa dason kyautata Mata "shiyasa yashige d'akinsa bayan sun rabu da nura ya rufe yayi kwanciyar sa Yana tunani....har aka Gama hidimar da akeyi.aka Kira Sallar magrib.

Khadija ma share zancenshi tayi aranta sbd tasan ba yanzun zasu tareba.saidai ta ayyana aranta insun had'u zata nuna Masa tamkar batasanshiba.

Da safe yashigo waiting parlour d'in gidan"Yana sanye da jallabiya ajikinsa"yahango fitowar Khadija dg sashen Abba"tana juyowa suka had'a ido"d'auke kanta tayi fuskarta bbu walwala batace dashi kanzil ba.ta wuce ta gefensa tanufi sashen anty.

Be kawo komai aransa ba"sai ya alak'anta hakan da k'ila sbd har yanxun da jama'a agidan"dan yasanta da kunya.

Sashen hjy ya wuce"tana zaune itadasu ummi a bed room d'in ta.suka gaidashi suka fice"bayan sun gama gaisawa.ahankali cike da ladabi yace kiyi hakuri hjy dan Allah inhar nab'ata Miki akan aurena da khadija.tabe baki tayi had'e da cewa ubanka dai yabak'antamun daya aura maka ita.kuma Dole ka rabu da ita" bayan wani lokaci...bece komaiba ya tashi yafita..

Ayau yakama Friday"tunda wuri Khadija ta shirya sbd 11 am sunada lactures su duka. Zee ce kawai sai 2pm zata tafi"

Gaba d'aya sun shirya"Khadija da hijab har k'asa ajikinta"suna fitowa dg k'ofar parlourn suka hango Yaya mahmod da alama anan sai iso"da sauri Khadija ta dauke kanta ,tayi gaba abinta tana sauri"yayinda tsab yaganta"yakumayi mamakin meyasa take mishi haka?

Su ummi suma bin bayanta sukayi sbd dama sungaishe d'azun dayashigo.yanzun ma dg office yake...

Tafe suke zee itada isah driver"wata yarinya ta tsaidasu"harzasu wuce zee tace su tsaya sutaimaka Mata.

Ahankali ta k'araso ta tsaya kusada k'ofar baya inda zee take"tace dan Allah inyamma kukayi kitaimakamun ku

Please Login or Register in order to submit comment