Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

saurin duk'awa tace"hjy Ina wuni?lfy qlau"ta amsa atakaice.

Hakan yasa Khadija barin parlourn ta wuce waje kawai.hjy ta fashe da kuka tashiga sanar mishi abinda hjy rabi da khairat suka mata.wani farinciki sosai yaji da hakan yafaru"kodan sbd gujewa auren khairat d'in.amma beji dad'in da suka Zama sanadin zubar hawayen mahaifiyar Saba"bedai nuna yaji dad'in abinda sukayiba"saima nuna haushi yayi.hjy tace"bbu damuwa kabarni dasu..yanzun alh yasameni da zancen zuwa dare zaku tafi gidan mlm ko?Yaya mahmod yace" eh hjy.
Tace"kushirya komai da komai da kuke buk'ata .bayan sallar isha'i alh da nura zasu kaiku.sunama can ana gyara muku dakin dazaku sauka.da to ya amsa "aransa Yana jin dad'in hjy tafara saduda.tunda bata kyari khadijaba.

Tashi tsaye tayi tace"nawuce ciki ni"yace" to"
ta fiita.

Khadija na hangen wucewarta ta nufo parlourn"Yana nan azaune inda ta barshi"amsa sallamar ta yayi yanatashi tsaye"Murya k'asa k'asa yace"zonan Khadija!Babu musu ta matso kusada shi tana mik'o mishi hannunta.kama hannun yayi yakai bakinsa yasumbata"kafin yace"banji Yana k'amshin lalleba meyasa bakyayine?Yaya tun bayan na biki bansakeba.ko kanaso nadinga yine?Ina so Khadija "Amma yanzun ko anmiki bbu amfani tuda ba gani zanyiba"wani irin tausayi taji yabata sosai.bata auneba taji ya rungumota ta baya ajikinsa"Yana sakin ajiyar zuciya had'e da sinsinar wuyanta zuwa fuskarta.yanata faman lalubar Mata jiki.ita kuwa uwar y'an tsoro tanata zare ido"sbd tsikar jikinta ta tashi.rike mishi hannuwa tayi"cikin sark'ewar Murya tace"Yaya ankusafa magrib Kar akirafa.kin iya wayo ko? yafad'a Yana goga Mata lallausan sajensa a baby face nata"ta lumshe ido"Murya can ciki yace"muje kishiryamana kayanmu to.da sauri tabar jikin sa, ta Kama hannunsa suka wuce bed room d'in sa..

B'angaren hjy rabi da khairat kuwa"suna a mota"kharat ta dubi hjy rabi tace"Kinga mama tunda ga Jamil dabamufi 1month da had'uwa ba.gara nafitar dashi kawai tunda ko jiya yacemun shifa da gaske yakeyi yaushe zai turo magabatansa?to sbd Yaya mahmod sainace mishi zan yi tunani.baki washe mama rabi tace"shine wanda yamiki shopping jiya ? kharat tace"eh shine mama"
Mama tace"kai alhmdllh naji dad'i sosai wlh.zasuga kin auri d'an gidan masu dashi.kice yaturo wlh tunda da gaske yakeyi.insha Allah sai su Yaya hakeema sunji haushi akatashi bikinki.tana goranta Miki"d'anta bece yana sonkiba.to ga wani dg Allah"kharat sai smile aketayi da fari da ido"har suka iso gida"saiga kiran Jamil yafishigo awayarta"ta d'auka tana kashe Murya...suka nufi cikin gida.

***************

Tafe suke acikin soron gidan mlm na Allah"Khadija na rik'e da hannun Yaya mahmod sunjero suna tafiya.yayinda Abba da nura ke bayansu dauke da trolley d'in su..
Kai tsaye cikin gidan suka shiga.mlm matsalar gida.ya amsa sallamar su"Yana cewa su shiga d'akin su.babu musu suka wuce ciki."matar mlm Inna yelwa da y'ar sa'adiyya.suka shigo suka gaisa dasu Abba da Yaya mahmod.gaba d'aya sai Khadija taji zafin yadda sa'adiyya takafe Yaya mahmod da ido tana kallo"harda cewa mamanta"Inna wannan ne marar lafiyar? kasancewar ankawo nefa da haske d'akin.duk aka Mata banza.hakan yasa ta fice dg d'akin.mlm yashigo suka sake mgn da abba.kafin shima nura suka tattauna sosai da Yaya mahmod.kafin suka musu sallama suka tafi..Khadija ta k'arewa d'akin kallo"bayan katifar dasuke zaune akai sai carpet da toilet ad'akin sai k'ofar me net ce da labulaye .sai trolley d'in kayansu.wani Imani da tsoron Allah Khadija tasake ji"sbd bata tab'a zaton wai itada Yaya mahmod zasu rayu ahakaba...kinyi shiru Khadija lfy daiko?"yafad'a cikin damuwa.da sauri tace"lah Yaya bbu komai"kaga 9pm ya wuce muje ka kwanta tunda dama kayi wanka agida ko?to my khady, yafad'a Yana tashi tsaye"hakan yasa ta tashi itama ta taimaka mishi yacire kayan jikinsa.dg shi sai boxer da vest "yakwanta kan katifar Yana cewa kizo mu kwanta kishafamun maganin da mlm yace "da to ta amsa.

Bayan ta saka kayan bacci"taje ta saka sakatar d'in dake jikin net d'in"kafin ta hau kan katifar ahankali tafara k'ok'arin shafa mishi maganin" aduka jikinsa.saidama ta cire mishi vest d'in"saidaifa ita har yanzun tsoron ganinsa haka takeyi"dukda tasan be ganinta"yayinda shikuma yanayinta da motsinta yatabbatar mishi da akwai sauran lokaci kafin tasake dashi sosai"dukda bbu laifi dg jiya zuwa yau.tasaki jiki dashi.bayan ta gama Yana kwance rigingine"ta musu addu'a ta kwanta nesa dashi.

Ahankali yafara lalubonta"hakan yasa ta juyo da sauri"murginowa yayi saitinta Yana cewa kina Ina?Yaya ganifa akusada Kai "hannunta yakama yajanyota jikinsa yarungume"ahankali yafara shafarta dg kirjinta zuwa bayanta"yafara k'ok'arin had'e bakinsu "da sauri ta janye kanta"tana cewa dan Allah kayi hakuri mu kwanta...banza yamata yafara romancing d'in ta azafafe"....saima yamirgonota yadawo yasamanta yahad'e bakinsu gu d'aya"rigar baccinta daya rabata da ita"yasaka ta janye bakinta ta saki kuka.ga nishin datakeyi sbd yamata nauyi sosai..d'agata yayi ya kwanta gefenta bece komaiba Yana maida numfashi"sunkai kusan minti 5 ahaka"saima yajuya Mata baya sbd beji dad'in yadda take nuna mishi tsoro hakaba.
Ita kuwa rigar baccinta ta maida ta kwanta.saidai takasa bacci sbd tana ganin fushi yayi d ita.

"Ahankali tace"Yaya"banza yamata Yana jinta.

Batasan lokacin data mirgino ta kwanta asaman kirjinsa ba "tasaki kukan shagwab'a"rintse idanunsa yyi sbd jin nashanunta yadaki kirjinsa.....โœ๏ธ

Kuyi break fast da lunch harma da dinner๐Ÿ˜Š

Inhar Banga ruwan comments ba bbu update Koda nayi ma to saidai Yan grp nawa su karanta.๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

๐ŸŒนA GIDA D'AYA๐ŸŒน
๐Ÿ˜๏ธ๐Ÿ˜๏ธ

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ



Story & written by mmn fareesa




๐Ÿ…ฟ๏ธ 37&38


"Acikin wani yanayi yace"menene kike kuka?"ai nadena Miki abinda bakyaso ko?"cikin marairai cewa tace"amma Yaya agidan mutanefa muke"kuma naga kayi fushi dani.hmmm!banyi fushi dakeba my Khady "Koda nan gaba kinmun laifi da baya "duk na yafemiki"sbd banaso Allah yayi fushi dake.maganar Muna agidan mutane betasoba.tunda bawani abu zanmiki ba"romancing ma kina nuna tsoro balle kuma wanc...da sauri tasaka tafin hannunta ta rufe mishi baki"yakuwa gartsa Mata cizo"tasaki k'aramar k'ara tana yarfe hannunta.had'e da cewa"Allah saina rama nima"murmushi yyi yace"kidai rame yarinya..jikinsa ta haye sosai tana k'ok'arin Kama mishi hannu ta rama.amma yak'i Bari sai haki takeyi da nishi..khadija kuwa duk yanda taso ta rama kasawa tayi"sbd kokawa suka dingayi kan katifar"dg karshe tasaki kukan shagwab'a tana dukansa a kirji"Yana murmushi yace"wata yarinya dai ragguwa ce"inta tankamun saita ji jiki agurina.sarai tasan da ita yake saita shareshi. tagyara kwanciyar ta akirjinsa ....har bacci yyi awon gaba dasu.

Da asuba da taimakon mlm Yaya mahmod suka tafi masjid"bayan sun dawo ,yasami khadiya nata Azkhar nata"tashi tsaye tayi ahankali tana cewa"Yaya har kadawo ne ?"eh Khadija yanzunma zanyi karatun alk'ur'ani mai girma ne"da to ta amsa tana Kama hannun sa. ta zaunar kusada inda take zaune ta tashi"zama tayi kusada dashi tana cewa "Yaya Ina kwana?lfy lau Mrs mahmod yahidima da hakuri dani?hmmm Yaya inbayi zolayaba bakajin dad'i.yanzun zaka fara karatun ko?Yana sakin guntun murmushi yace"hmmm meyi dan Allah bayaso ana fad'a.Allah yayimiki albarka yabarmu tare"tana murmushi tace"ameen Yaya"

sun jima anan suna karatun alk'ur'ani Mai girma.har saida rana ta fito tukunna" sukayi addu o insu suka tashi dg kan prayer mat d'in..gefen katifar ta zaunar dashi"Yana cewa Khadija kiramun hjy ta waya inyashiga kibani nagaisheta...kafin tace wani abu"sa'a diyya ta turo k'ofar net din ta shigo d'akin"bbu ko knocking.akule Khadija ke kallonta batace komai ba"sai Yaya mahmod ne ya amsa sallamar ta "tace Ina kwana ?lfy lau "yajikinka?yace"alhmdllh!kallon Khadija tayi tace"Inna tace"ko akwai abinda kuke buk'ata?fuska bbu walwala Khadija tace"ah ah"
Kallon Yaya mahmod sa'adiyya tayi tace"dan Allah yasunanka?wlh kanada kyau.... sa'a diyya! sa'adiyya!!!Inna ta k'wala Mata kira"yyinda Yaya mohmod yayi murmushi kawai"Khadija taja tsaki had'e da cewa meke damun ki nadole saikinsan sunansa?to mijin watane nan dakike gani"tana fad'in hakan taja tsaki ta wuce toilet.uffan Yaya mahmod beceba saima juya baya yyi"hakan yasa sa'adiyya fita sbd Kiran da Inna ke mata...amma ta ayyana aranta saitaji sunansa.
K'arar rufe k'ofar yasaka yagane ta fice"yasaki wani killer smile "sbd jin dad'in yanzun yasan yanada gurbi acikin zuciyar Khadija "dukda Yana makaho hakan besa ta nuna bata kishinsaba.kai gsky Yana alfahari da ita...motsin fitowarta yadawo dashi tunaninsa.
"Ahankali yace"my khady zonan"turo baki tayi had'e da cewa nazo kakoma cizo na.besan lokacin daya saki dariyar da fararen hak'oransa suka bayyana ba.yace"hmmm aibakimun abinda zancijekinba ko? kizo Mana inba ga tsoroba".hmmm !ta fad'a tana kallon sa"yamata mugun kyau"wani zafi taji aranta data tuna kalaman sa'adiyya.batasan lokacin da tace"nidai gsky banason wannan yarinyar maizubin maza" kana Mata mgn ba" Koda ita ta maka zan bata amsa.
Mekikace?maimaita mun banjiba"shiru kuma tayi aranta tace"karfa yaga Kona rainashi sbd nasanshi da son girma.yana dariyar maganarta Wai Mai zubin maza"my khady kidena kishi da yarinyar da bawani nutsuwa da wayone da itaba sai yarinta"ko hafsat ta girmeta"banaso kina gaya Mata mgn" Kinga agidansu mukazo"kuma zata iya yuyuwa ko iyayen ta in sun lura bazasuji dad'i ba.amma karki damu da kishi da ita"matan dasuka fita sunce mijinki sukeso" bekulasuba sai ita. sbd haka kece kawai matar mijinki....shiru kawai tayi sbd kunya. gaba d'aya kalamansa suka sakata"yanzun har yamata fassara da kishinsa takeyi kenan?"
Ki kiramun hjy pls"to Yaya ta fad'a tana k'ok'arin d'aukar wayar sa.
Ringing 2 tayi ta mik'a mishi wayar"hjy tayi sallama"hakan yasa Khadija saurin fita dataga Yana mgn da ita.

Atsakar gida ta fita ta samu Inna na dama Koko"har k'asa ta duk'a ta gaida ita cikin girmamawa"kafin ta amsa tana tambayarta Mai jiki"tana bata amsar da sauk'i"yyinda sa'adiyya dake zaune gefe tadinga kallonta.khadija tanuna tamkar batasan da itaba"tana anan mlm yashigo suka gaisa dashi"tana k'ok'arin tashi ta koma d'aki Yaya Kamal yayi sallama yashigo."hannunsa d'auke da basket babba"shak'e da kayan break fast...

Fuska asake tace"sannu da zuwa Yaya Kamal kawo kayan"Yana murmushi yace"ah ah Khadija kece da sannu wlh"kinata kula mana da yaya.yafad'a Yana tsayawa suka gaisa da Inna yelwa "kafin ya wuce d'akin dasu Khadija suka sauka."Khadija tabi bayan sa.

Yaya mahmod na zaune "idanunsa abud'e kaikace Yana gani azahiri.amma abad'ini duhu yake gani.amsa sallamar Kamal yayi"bayan ya ajiye basket d'in" yagaidashi had'e da sanar mishi Abba da daddy nanan tafe anjima dubashi..
Yaya Kamal bejimaba yamusu sallama yafita.kafin Khadija ta taimaka mishi yayi wanka.bayan tayi itama. sukayi breakfast atare"
Mlm yashigo yabada magani akan ashafa mishi a fuska kawai...ba'ajima da shafa mishi maganin ba"bacci ya d'aukesa...

Zaune suke gaban wani mashirikin boka"yatasa tukunyar tsafin sa agaba"Yana wani surkulle Yaya mahmod ya bayyana"saikuma yab'ace.yyi hakan kusan sau3.dg baya ruwan suka dinga hayak'i da tururi...kallonsu alh mudi yayi yace"wannan yaron yanada ruk'o da ibada da addinin musulinci sosai.bana zaton zakuyi nassara akanshi sai sa'ar gaske"sbd natura aljannu kafirai bak'ake Kuma"Amma Basu iya rab'arsa sbd k'arfin adduo I, da kafe kafe dake jikinsa"Koda zasuci galaba akansa sai Yana tare da janaba"inkuma kukace zaku matsa tofa kome yabiyo baya kuyi kuka da kanku...alh mudi yace"saida nace abar maganar tura aljannunnan" Amma yace shidai atura"alh Ayuba yace"shikenan ai abarsu sai Yana tare da janaba d'in sbd ai yanada iyali ko?"alh mudi yace" eh bejima da aureba.
Boka yace"karku damu maganar zab'e Kaine zakaci d'an majalissa.shikuma mataimakinka.muddinkun binne jakki da mage da ransu...cikin farin ciki sukace ai tuni tun jiya komai yakankama angama....iya nan Yaya mahmod yabud'e idonsa"Yana salati yatashi zaune sbd muryar Nura dayaji.. innalillahi wa inna ilaihir raju'un kawai yake fad'a aransa.yana mamakin meyasa yayi mafarki dasu Alh Ayuba?kodai hakan na nuna cewa sune manyan mak'iyansa?kuma suna binsa da sharri??"my man katashine?
Eh wlh yanzun kashigone?nura yace"eh sai Kuma Khadija tace bacci kakeyi"nace bara najira ka sbd nazo muyi mgn Mai mahimmanci..

Yaya mahmod yace"Ina jinka!Allah yasa lfy dai"nura yace"Babu damuwa indai mukasan mafita...Yaya mahmod yace"Ina khadija take?nura yace"tana tsakar gida"bayan nazauna ta fita ta barni...
Ohk kawai yace yayi shiru..

Nura yace dg jiya zuwa yau"nasha tambayoyi a office akan Ina kake?" sauk'ina guda ka kashe layinka dasuka sani"nace musu baka gari"kunje wani gari kaida family naka"zaku jima kafin kudawo.abin mamaki alh mudi dasu is'hak'a da salis damuke zargin suna d'aukar sirrin campany dinmu" suna gayamishi Yana biyansu" Ashe da gaskene.sai gashi sunzomun da zance Wai karnasaki jaridar da akayi fira da alh mudi" zai cigaba da takarar d'an majalissa.ayanzun haka angama zab'e"next week za'a Fad'i Wanda yaci.sun buk'aci nayi hakan zasu biyani kud'i mak'udai "sainace musu saina binciko jaridar sbd anbugata.abin mamaki Wai ancireka dg aiki" agidan TV da redio"sukuma campany dinmu"sunaso kota waya kasanarmusu inda kake ko kaje"ko kuwa su baka takardar sallama.nura yafad'a cikin damuwa....amamakinsa saiyaga Yaya mahmod na murmushi"yace tabbas inaji ajikina banida wani babban mak'iyi aduniya d'aya wuce alh mudi.kabarsu kawai ka b'oye jaridar inhar nasami sauk'i nida kaina zanfito da ita"Ina fatan kagane? nura yace"to shikenan inkuma sunbani kud'i gsky bazan karb'a sbd alh mudi kudinsa na tsafine.yaya mahmod yace"hakane gsky"maganar sun koreni dg aiki da saisunyi mgn dani kasharesu kawai"Allah yabani lfy shine fatana.
Nura yace"ameen yah Allah...

Shiru yaratsa tsakani.kafin Yaya mahmod yaja ajiyar zuciya yace nayi wani mummunan mafarki wlh ayanzun"Amma duba in mlm nanan kace inason ganinsa...nura yace" subahanallahi! Amma karka damu mafarki ba gsky bane ai"Yaya mahmod yace hakane.tashi yayi yafita"bbu jumawa saiga su sundawo d'akin tare da mlm.bayan sun zauna Yaya mahmod yamusu bayanin mafarkin da yayi...mlm yayi gyaran Murya had'e da cewa"dama nasan insha ALLAHU zakayi mafarki sbd maganin da aka shafa maka"sannan jiya banyi bacciba nayi istahara nagani "tabbas koma su wayene to Basu nemanka da alkhairi sai sharri"abinda nakeso dakai shine"kadage da addua bbu Rana bbu dare.sannan kayi hakuri dayin wani abu na auratayya da iyalinka sai bayan samun lafiyarka.inka fahimta mafarkinka iznane"Kuma ubangiji nasonka daya nuna maka...domin bbu tamtama dukda kana ahaka wani sharrin suke kullamaka..Allah yakaremu dg duk kan sharri da masu sharri...gaba d'aya sukace ameen.bayan mlm yasake bashi shawarwari"sannan yafita,shima nura wucewa yayi jikinsa asanyaye.hakan yaba Khadija dake zaune da Inna yelwa suna fira jefi jefi damar tashi ta shiga cikin d'akin.

Yana nan azaune yanata tunanin wace iriyar zuciya su alh mudi keda ita"meye laifinsa?sbd yanuna shi Yana akan gsky baya zalinci.shine suka tsaneshi ,bacin Allah ne yaharamta zalincin...Yaya !Yaya!!harka tashi dg baccin ne?natashi ! yafad'a atakaice Yana mik'ewa tsaye"yace muje da maganin nan nasake wanka.saiki bani Wanda yace Ashe sau 3 arana.dato ta amsa .ta taimaka mishi yacire kayan jikinsa.khadija kiduba awayata ki kunna suratul bak'ara..da to amsa"bayan ta kunna suka wuce toilet...

*Bayan sati 2*

Jikin Yaya mahmod saidai ace alhmdllh! Amma har yanxun baya gani"yyinda mlm da Khadija dashi kansa Yaya mahmod din.sundage da addua da kulawa dashi sosai....gefe guda Kuma Abba da daddy da Yaya Kamal kullum saisunzo dubashi.yaya Yusuf ma yazo yayi kwana2 yakoma cike da damuwar halin da d'an uwanshi yake ciki"
Hjy , Mama jummai,inno da anty had'e da y'an matan gidan duk sunzo sunganshi da jiki.kowa yabon k'ok'arin Khadija yakeyi akan kula da Mai irin wannan ciwo.sbd sai anyi hakuri andaure.bewar Allah har Rama tayi "hjy yanzun kuwa nauyin anty da Khadija takeyi"Koda sukazo sau d'aya sukayi mgn da Khadija data gaisheta ta amsa.mama jummai ita kanta yanzun tayi siranda anshiryu ta tausayawa Yaya mahmod akan halin dayake ciki..su ummi har kuka Saida suka sake Yi"Abba yace baza'a sake zuwa da kowaba....


B'angaren su alh mudi kuwa"duniya tadawo musu sabuwa"musammun ma alh Ayuba.sbd anfidda ibbi waje amishi aiki akansa.suna Egypt shida amintaccen yaron alh Ayuba.ayanzun haka sunci zab'e saura rantsarwa kawai da abasu office...shagali bbu Kama hannun yaro"suna bushasha da facaka da kud'i...kafin abasu office nasu...

**************
Anty ce tsaye aharaban gidan"suna mgn da Yaya Abbas "sai abdallah tsaye agefensu Yana rik'e da khalifa.(inme karatu be mantaba abdallah k'anin Khadija da anty ta haifesu)
Yaya Abbas yace"karki damu tunda inada rai zan rik'e abdallah tunda yamaidoshi yace bazai iyaba.
Cikin k'unar rai anty tace"tsakanina da jafar Allah ya isa(baban su Khadija) wlh yaguji haduwarshi da Allah akan hakk'in yaransa.yanzun abdallan zai maido yace "bazai iya rikeshiba.kasan ko yanzun nayi k'ararsa Dole amasa hukunci. Mai tsanani.yaya Abbas yace" ah ah baza'ayi hakanba.ko alh mukhtar besaniba.nade share kawai sbd nasan wlh watarana sai jafar yayi kuka da hawayensa akan wofintar da rayuwar y'ayansa.sbd haka kishare da zancen.dg nan zamuje can inda kika Mana kwatancen saimu ganoshi.shima abdallah yaga y'ar uwarsa....cikin farinciki abdallah yace"lah zanga anty khadija? murmushi kawai anty tayi tace"eh zaka ganta.yanata murmushi yace"to.. abdallah k'anin Khadija ne tabashi 2yrs"yanzun 16 yrs gareshi.bayan sun Gama mgn anty ta karb'i khalifa sukuma suka fice ...

Zaune hjy take a parlourn ta.tayi tagumi tana tunanin halin da mahmod yake ciki" kusan sati 3 kenan yanacikin wannan lalurar."aranta tana ganin laifinta abaya na nuna wa Khadija k'iyayya.ashe itace zata Mata Rana "yanzun inda ba'a yi aurensuba to waye zai kula dashi ?"tunda kharat ta nuna batayinsa... sallamar hjy rabice ta katse mata tunani"kallonta tayi ta amsa.tamkar race mekikazo yimun Agida?saikuma ta share kawai.

Bayan sun gaisa"fuskar hjy Babu yabo bbu fallasa. tayi shiru tanajiran jin dame Kuma hjy rabi tazone yau?
Zuge zip din hand bag nata hjy rabi tayi"ta fito da leda bak'a me daure da wani Abu aciki.ajiyewa gaban hjy hakeema tayi kafin tace". Gashi kayan saka ranar auren khairat ne. nanda wata 1 za'a sha biki insha Allah....โœ๏ธ


Comments kawai guys๐Ÿฅฐ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ

๐ŸŒนA GIDA D'AYA๐ŸŒน
๐Ÿ˜๏ธ๐Ÿ˜๏ธ

๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ๐Ÿพ



Story & written by mmn fareesa




๐Ÿ…ฟ๏ธ39&40



.......Da ido kawai hjy hakeema takebin hjy rabi dashi"ak'asan ranta tsantsar mamaki ne aciki"Allah yasa alkhairi!iya abinda hjy ta fad'a kenan ta mik'e tashige cikin bedroom nata.sbd kukan bak'in ciki dake cinta"inbatayiba bazataji dad'i ba..
Tab'e baki hjy rabi tayi ta tashi ta fice dg parlourn....

Zaune Khadija take kan katifarsu"sai gyangyad'i takeyi.sbd batasamun isasshen lokaci sosai..yyinda Yaya mahmod na toilet Yana wanka"wayar Yaya mahmod dake gefenta tayi ringing"gabanta taji yafad'i sbd ganin number d'in *hajiyata*
Rasa Yaya zatayi ma tayi har wayar ta tsink'e aka koma wani Kiran"badan tasoba ta d'aga cikin kirman jiki"hjy tafashe da kuka gwanin ban tausayi tace"mahmod kaji abinda rabi da y'arta suka Mana ko?rasa mezatace Khadija tayi "kafin tayi mgn hjy tacigaba da cewa"bacin maganganun data gayan masu d'aci"shine kana cikin wannan lalurar za'a saka bikin khairat nan da wata d'aya.kamutu koka rayu badamuwarta bace"sbd abin duniya...wlh mahmod kunyar Khadija da mamanta nakeyi akan abinda nayi abaya... k'arar knocking d'in k'ofar toilet da Yaya mahmod yayi"yasaka Khadija kashe wayar kawai.ta ajiye kan katifar da sauri ta nufi toilet d'in...
bayan sun fito"tace Yaya hjy ta Kira kana wanka"kusan sau2 tona d'auka tafara mgn banaji sosai sai naji motsinka sainakashe... okay my khady kiramun ita to.dato ta amsa tana d'aukar wayar"bayan ta shiga ta mik'a mishi yakara akunnansa.sallama yamata"kafin yace"hjy kinkira banaji sosai"Amma yanzun inajinki.hjy ta shiga kora mishi bayani kamar yadda tayi ad'azun"ajiyar zuciya yasaki.kafin yace karki damu hjy Khadija bata rik'e kiba.amatsayin uwa kike agurinta.fatana kija anty ajikinki kuzauna lfy.batun mama rabi ki ajiyeshi gefe sbd
*Kowa yasiyi rariya saita tafkamishi asarar ruwa*
Banaso kina nuna Mata kindamu da abinda ta aikata"kibarta ai duniyace karkuma ki yanke zumunci da ita"ah ah kibarta kuciigaba da zumuncinku...insha Allah hjy sai anjima zansake Kira Allah yak'ara girma...janye wayar yyi sbd kin takashe.

Ahankali yace"khadijaaaa!shiru bbu motsinta"murmushi yyi yace"hmmm wannan halin naki na burgeni my khady "sab'anin wasu matan na lik'e d miji suna bimishi kwaf a al'amurran rayuwarsa.sallamarta ta katse mishi tunaninsa"ya amsa had'e da cewa my khady hjy na gaidake tunda kingudu saikace wani abu za'a ce ta wayar...tana murmushi tace"Ina amsawa Yaya "bara nashafa maka Mai ko?ah ah bani nashafa da kaina khadija"meyasa bakaso namaka?
my khady kinsan mlm yacemun naguji duk abinda zaisa nashiga wani yanayi(sha'awa)kibani kawai....itadai bata wani gane meyake nufiba.tajawo trolley d'in su ta fito da lotion d'insa .ta matsa kusadashi ta saka mishi ahannunsa.kafin ta zauna gefen sa"amamakinta saitaga Yana shafawa da lalube"tayi tagumi kawai"aranta tana tariyo maganganun hjy.tarasa meyasa taji dad'i da akace kharat wani zata aura ba Yaya mahmod ba.sannan ita kanta tayi mamakin butulci irin na hjy rabi da khairat.wato badan Allah sukeso Yaya mahmod ya aureta ba.... khadija karki gaji pls kayana kinjiko?"ahankali tace"aigasunan ma nafito dasu.tafada tana k'ok'arin mik'a mishi kayan..riga t-shirt da wando 3 quarter.ta taimaka mishi yasaka.yana Zama yace" wai Khadija wakike bawa wankinmu ne? sai yanzunma na tuna da wake Mana wanki?"
Ai Yaya nice kemana...cike da mamaki had'e tsakanin ganin ki'marta yace" haba khadija ai wahalar saita Miki yawa ko? Ga hidima dani ga Mana wanki"na zata koma Kamal ke kaiwa ai.dg yanzun bazaki sake wankiba"to dama wane lokaci kikeyin wankin be?
Shagwabe fuska tayi had'e da cewa nidai dan Allah kabarshi namana tunda bawani Mai yawa bane dan Allah..tunda sai in kana baccin safe nake wankemana."ke Kuma saiki hana naki idon baccin ko?to ai Yaya zansamu ladane ko?my khady haka kike dama? Allah yayimiki albarka Ina alfahari dake amatsayin matata.nagode Yayana"Yana murmushi yace"matso kusada dani nabaki tukwaicin farin cikin dakika sani ayanzun.d'an Jim tayi ,katin ta tashi ta matso kusada shi"janyota jikinsa yayi ya rungumeta sosai"kafin yace"Allah yabani lfy my khady na Miki alk'awari d'aukar karatun abdallah insha ALLAHU...sosai khadija ta rungumesa tana sabbatun godiya.nagode sosai Yayana"wlh kullum burina na inganta rayuwar abdallah sbd abbanmu baya sonmu... tafad'a tana sakin kuka.ah ah my khady karmuyi karmuyi haka dake Mana"addua zamuyi mishi kinjiko"dukda banga abdallah ba"amma dasukazo kwanaki naji muryansa, kuma d'an uwankine naji inajinsa tamkar salim..sbd haka karkidamu hakan nacikin jarabawarmu kinjiko my khady?"gyara kanta tayi akirjinsa tace"naji Yaya zanyi yanda kakeso"fatana Allah yabaka lfy"Yana shafa bayanta yace"ameen my khady...

****************
Rayuwa haka tacigaba da tafiya a family d'in su Yaya mahmod"kowa burinsa samun lafiyar Yaya mahmod.amma jidai suke shiru"shikansa Yaya mahmod Yama cire Rai da samun lfy...ayanzun haka watansa na 2kenan Yana cikin lalurar"
gaba d'aya hankalinsa atashe yake sbd nura ya kirashi jiya"yasanar mishi ibbi yadawo dg igypt yasami lfy"yad'ora dg inda yatsaya gurin shashanci..."bbu wani zancen kamashi amishi hukunci.hakan ba k'aramin haushi da b'acin rai Yaya mahmod yashigaba.sbd ko sati 2 da suka wuce dayasami labarin an rantsar dasu Alh mudi,anbasu office bedamuba.sbd yasan watarana gsky zatayi halinta..gaba d'aya yaji yatsani wasu acikin mutanan Nigeria sbd rashin adalcinsu"sannan tashin hankalinsa"kada ibbi yasake kaima zainab farmaki.koda hakan yafaru yasan bbu abinda hukuma zatayi.sbd bbu wani tsayayye ko jajurtacce dazai tsaya a lamarin...gaba d'aya jiya da yau Khadija ta rasa gane kanshi.data mishi mgn saiyamata banza ko tsawa.hakan yasa tashiga damuwa"saima tarik'a zargin kodan sbd gobe ake d'aura auren khairat ne shiyasa yake Mata haka...

Da misalin karfe 9:30 na dare Khadija na k'ok'arin yin addua ta kwanta gefensa"sbd itama duktashareshi.nikuwa nace kishine.

Khadija fushinme kikeyi dani?gaba d'aya kinshareni kokema kingaji da zama dani ne?"hmmmm!amma nimena yimaka duk yau kaketa mun tsawa?saikaga laifina Dan na kaucewa abinda za'a hantareni.sau 3 yau inamaka mgn kana sharewa... tafad'a tana sakin kuka....yah salam!Khadija meyayi zafi haka?dan Allah kibarni naji da damuwata.karki sake kuka"kukanki natadan hankali... yafad'a Yana matsowa kusada ita Yana lalubenta.ni karabu dani!kinaso nayi fushi dake?shiru kawai tayi tana share hawayenta.bata auneba tajita ya rungumota.tasaki ajiyar zuciya.rarrashinta ya hauyi.saigashi harda murmushin ta suka fad'a duniyar bacci...

Washe gari da misalin karfe 11 na safe aka d'aura auren khairat da Jamil..yyinda hjy hakeema bataje Gurin bikiba"dg ita harsu ummi.duk event din da akayi basujeba.anyi kamu ,dinner mother's day....haka da marece akadauki kharat aka Kai anguwar G R A....gida abinda ke gida nagani na fad'a.kowa yaba gidan yakeyi"hjy rabi jinta take tamkar a ajanna take sbd murnar y'arta tasamu duniya...
Bayan kowa yawatse"Jamil ya iso gidan.shi d'aya bbu wasu abokansa"hakan bedami khairat ba"bayan sunci sunsha.suka Yi wanka batare da gabatar da nafila ba Jamil ya afkawa khairat.....

Bak'aramin azab'a Jamil yabawa kharat ba.bbu wani rarrashi ko nuna tausayi yake gudanar da komai.tayi kuka da ihu bbu iyaka.saida yasamu gamsuwa yabarta.ko yatsa bata iya d'agawa"batare daya kalli inda takeba ,yawuce toilet yawatso ruwa ya tsarkake jikinsa yafito.kallonta yyi sbd jin shashshekar kukan ta"tab'e baki yyi had'e da cewa inma Zaki dayaye ki dayaye wlh "sbd Zan k'ara nasafe in Allah yakaimu.dole na mori sadakina wlh bazanyi asaraba"kitashi kije kiyi wanka ga ruwa can na had'a Miki..ahankali ta d'ago kanta ta dubesa"Yana tsaye d'aure da towel ak'ugunsa.yanzun Jamil da abinda zaka sakamun dashi kenan?bazakaji dad'i nakamaka budurcinaba ,ka rarrasheni kabani kulawa kamar yadda kowane ango kebawa amaryasa a first night nasu...Kinga inbazaki iya tashiga nakaiki toilet kawai"banida lokacin tsayawa shirmen wani tarairayar mace.indai kina biyamun buk'ata Zaki samu komai waja waja agidan nan.amma hakan shirme nad'aukesa gara naje office Gurin neman kud'ina.inafatan karki koma mun wannan korafin banzan...mamaki sosai Jamil yabawa kharat.tasaki k'arar azaba"hakan yasa yasureta bbukomai ajikinta yadireta acikin bathtub"tana ihu da komai"yadinga gasata sosai"kusan sau3 Yana canza Mata ruwan zafi.sbd kuka har muryarta ta

Please Login or Register in order to submit comment