Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ya ce ya ki ka zauna a kasa? Dawo nan mana ya
nuna kujerar da ke kusa da shi. Hajjo ta
murmusa,dimpol ya bayya wanda ke kara ma ta kyau,no
am owk nan ma. Ina wuni? Ya aiki? Ya amsa da lfy lau,ya
na ki aiki? Ta ce Alhamdulillah. Sai kuma su ka yi
shiru,Khalid ya zuba ma ta ido,kawai Neena ce zaune. Ya
ce shez jst lyk you. Ta daga ma sa gira tare da fadin sorry?
Ya ce diyar ki Neena,is precisely lyk you. Hajjo ta
murmusa,ta ce na sani,is dat y u called me? To tell me am
jst lyk her ko kuma wani abu ne ya same ta? Khalid ya
dara,shi kawai mamaki ta ke bashi,child abuse ce haka ta
ke iya kallan sa ido cikin ido ta bashi amsa daidai da ta
shi,har wani sa'in ta watsa ma sa da yar magana? Kai
gaskiya boko yayi,jami'a ba wasa ba ce. Ya ce no,ba ma
saboda ita na ke neman ki ba,it is abt us,maganar mu ce
ni da ke. Gaban Hajjo ya fadi,amma sai ta basar dan kar
ya gane,ta ce us? Ni da kai? Hope all is well. Ya ce yes ol is
well,na yanke shawarar auren ki ne a matsayin ki na
mahaifiyar diyar da na ke so.
A hankali ta daga ido ta kalle shi,maganar ta ma ta kama
da tatsuniya,be yi mamakin ganin ta sa dariya ba,dariyar
ta ta mai ban sha'awa,wushirta da dimpol din ta du su ka
bayyana su ka kara kyawata kyan ta. tsayawa ya yi ya na
duban ta kawai fuskar shi dauke da mischievous
smile,dama ya sani,ya san she will celebrat idan ya ce zai
aure ta,ko wace mace za ta yi,dama dai Jabir ya na nan ya
gani da idanun sa. Ga mamakin sa da dariyar ta ta ta
tsaya sai ya ga ta tashi ta na nufin juyawa ta fita,yayi zatan
tsabar farin ciki ne ya sa za ta koma daki dan ta yi
celebratn da kyau,ya ce wait,ba shi kenan ba ai
Hajiya,wen za a fara maganar aure? Ta juyo ta na
murmushi,Khalid? A karo na farko da ta kira sunan
shi,wanda shi kan shi be lura da haka ba sai a
yanzu,hakan kuma ya sa shi shiga wani yanayi na kasa
gane shin wai ina matar nan ta dosa ne? Lokacin kuwa ta
fahimtar da shi.
Ta ci gaba da fadin wannan shi ake kira expensive joke,pls
ina respect din ka,for d fact dat diya ta consider u a
father,nd kai kuma ka yi taking responsbility din ta as if
kai ne mahaifin ta,so i beg of u let us maintain dat,nxt
tym in ka na da jest try someone else nt me,ta kare da
murmushi. Gwiwar sa ta fara sanyi,wato shasha ma ta
dauke shi ashe,hw dare her! Shi ma din tashi ya yi,ya
tsaya gaban ta,ya ce expensive joke? Jest? Tin da mu ke
na taba mi ki wasa ne Hajara? Hajjo ta ce Hajjo,kira ni da
Hajjo ba Hajara ba pls,haka kowa ya ke kira na. Zan cen
tin da mu ke babu,dan ba mu ta zama tare ba,daga nesa
nesa dai jst lyk now,dax y na ce kar ka soma. Khalid ya ce
ba wasa na ke ba toh,i mean it,marry me. Hajjo ta
murmusa ta ce y should i of all people marry d mighty
Khalid? Duk da ya san zolayar sa ta ke,ya gyara tsayuwa
ya ce saboda Neena,nd ina so na sami yara nawa na kai
na su zama tsatson su daya da Neena,kin san mata ta ba
ta haihuwa,i want u to bear my kids. Hajjo ta dara,ta ce
toh bazan aure ka ba. Cike da mamaki ya ce wannan
amsa haka kiri kiri? Saboda me ya sa? Ta ce saboda you
ar nt my type,i can't even manege someone lyk you.
Tsayawa yayi ya na kallanta,ya ma rasa amsar da zai ba ta
har ta juya ta fice. Komawa yayi ya zauna,Hajjo ta ma sa
bazata matuka,shin dama akwai macen da zai ce ya na so
ya aura ta ki? Kai ko Hauwa da ta hadau ten over ten ba ta
ma sa aji ba,bare kuma karan kada miya Hajjo. Ya saki
ajiyar zuciya,obviously Hajjon da ya sani a da wato child
abuse da wannan Hajjon ar two differant worlds! Rai
bace ya tashi ba tare da ya yiwa Hajiya sallama ba ya bar
gidan.
Tin shigar ta daki ta haye gado ta yi kwanciyar ta,wai ita
Khalid zai kalla ya ce zai aura tsabar ya yi niyyar ya
wulakanta ta,shi kan shi ya fi ta kyau bare matar shi da
Allah ya bawa baiwar kyau,mtws ta ja tsaki,in har
wulakanci ne d toh wlh sai dai kar ta san kar,dan ita ba
kowa ba ce,ba kuma ta isa a kira ta kowa ba ba za ta
zauna a wulkantata ba. NO WAY!
DEDICATED to The Women Of Virtue (group)
[7:49pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE
Ganin Khalid ya tafi ba sallama Hajiya ta san ba a yi ta
dadi ba,dan haka sai ta nuna kamar ba ta ma san zancen
ba. Hakan ya sa Hajjo sakewa,ta ma mance da maganar
ta da Khalid. Da ranar da ya kamata su dawo da Neena ya
yi su ka ji shiru sai Hajiya ta fara fada,za ta yi kiran Khalid
din ta ma sa tatas Hajjo ta ce wlh Hajiya da kin kyale su,ki
bar su zuwa sanda zan yi aure ta dawo wajan nawa,tin da
da nan din da can duk daya ne,Hajiya ta ce anya kuwa
Hajjo? A biye yanda su ke so? Dama fa nufin na su kenan.
Hajjo ta ce ba komai Hajiya,mai san na ka ai ya gama ma
ka komai,tsakanina da su sai fatan alkhairi. Hajiya ta ce
toh madallah. Ta kira wayar Khalid,ya na dagawa ya ce
Hajiya yi hakuri,kin ji ni shiru Hauwa ce ba ta jin dadi na
ce zan bari zuwa gobe...Hajiya ta ce toh ai abunda ku ke
so ne ya faru,Hajjo ta ce ku kyale ta har zuwa auren ta sai
ta dawo gurin maman ta. Saukar numfashin shi har sai da
ya fito ta bangaran Hajiya,ya ce kai amma ta kyauta,zan
fadawa Hauwar,a mana godiya,Hajiya ta kashe waya ta na
fadawa Hajjo yanda Khalid ya hau murna. Murmushi
kawai ta yi,ikon Allah wani diyoyi ma ta ya tsana,ga wani
kuma ko diya macen be samu ba,sai kwalafacin ta wani
ya ke,Allah mai yanda ya so.
Ranar lahadi gidan Jabir Hajjo ta wuni,ta na can suna
shan hira da Nabeela,ta zama kamar yayar ta,kamar
yanda Jabir ya zama yayan ta. Suna zaune a falo sai ga
Khalid ya aje Jabir,ya na mitar idan ba zai sake mota ba
da ga yau ba zai sake dana shi a tasa motar ba diyar Jabir
ta fito da gudu ta ba Baba Anty Hajjo ta siyo min
choculate,ai kuwa sai Khalid ya ce ina ta ke Anty Hajjon?
Ta ce ta na ciki ai,ta ce sai Baba ya dawo za ta tafi. Be yi
niyar tsayawa ba saboda hadari da ya ga ya taso,amma
jin haka sai ya faka ya fito,Jabir na fadin shegen
maza,yanzun ai ga shi ka fito. Ya na murmushi ya ce my
wife to b a gidan ka,dole na shiga. Diyar Jabir ta shiga da
gudu ta na Mama ga Baba har da uncle Khalid!
Jin haka gaban Hajjo ya fadi,tini ta nutsu ta ja mayafin ta
ta rufe kan ta,Khalid? Ba ta yi niyar sake ganin shi
ba,raban ta da shi tin ranar da ya zo ma ta da yashasshan
zance,wlh da ta san zai zo da ba ta tsaya jiran Jabir
ba....Nabeela ta na fadin yau Khalid a gidan nan,tin
dawowar sa ban sa shi a ido ba,gwara ma dai Hauwa da
Inna sun zo,babbar diyar Nabeela ta ce mama Neena ake
cewa ba Inna ba. Nabeela ta ce aw Inna fa ta koma
Neena,duk dariya su ka sa,sallamar Khalid da Jabir da
shigowar su lokaci daya ne. Ya na shiga idanun sa su ka
isa izuwa inda ta ke,be da buri da ya wuce ya kalle ta ya
ga yanda ta ke reactn duk sanda ya san ya idanun sa cikin
na ta,gashi d more ya ke ganin ta d more ta ke kara ma sa
kyau,ganin ta ya yi cikin riga da wando na pakistan
ja,mayafin yane bisa kanta gashi gashin goshin ta yayi
lublub abun sha'awa ka yi zatan irin gashin nan ne na
gaske. Kamar ta sani sai ta ki kallan ma in da ya ke,ta na
murmushi ta ke yiwa Jabir sannu da zuwa,ya na yauwa
Sannu my sister,ya na fama da yara da maman su,wata
ruke da hannun sa na hagu,wata na dama,wata kafa,ga
maman su ruge da jakar sa da ta karba,sauran yaran biye
da su su ka shige ciki kowa na nashi surutun, aka bar
Hajjo da Khalid a falon. Sai a sannan Hajjo ta daga ido ta
kalle shi,ganin yanda hankalin sa gaba daya ya karkata ga
inda su Jabir su ka shiga,ta ga yanayin da ya ke ciki,ta
tabbata Jabir da yaransa ne su ka bashi sha'awa,rashin
'ya'ya sam be da dadi,sai ta dan tausaya ma sa,amma na
kankanin lokaci saboda ita ta shagala ta na kallan sa,har
ya kama ta,sai ji ta yi yace am i dat handsum suger? Ta yi
sauri kau da kai cikin jin kunya ta ce sannu da zuwa,ya
aiki? Ya murmusa,yan da ya ga ta na kallan na sa ne ya
ma sa dadi kwarai,ya ce hamdan.
Jabir ya fito biye da Nabeela,sun hada yara da kayan dadi
sun rabu da su a daki. Nan ya zauna tare da Khalid
Nabeela ta kawo mu su abunci,Hajjo ta tashi za ta ba su
wuri Jabir ya ce ta zauna abun ta,yay ta jan ta da
hira,yanda ya ga ta sake da shi ya sosawa Khalid rai,wato
shi ne dai ba ta so,ba ta ra'ayi,ko ya sa baki a zancen sai
ka ji ta yi shiru,Nabeela ce ma mai kokarin sa shi cikin
hirar.
Sanda su ka gama cin abunci Hajjo ta fara shirin
tafiya,Khalid ya ce dama dai gida za shi bari su tafi tare.
Hajjo ta ce ah ah,ita ba gida za ta ba,Khalid ya ce ko ina za
ta ba damu,he is free. Nabeela ta kalli Jabir da alamar
tambaya irin wats up wit dem,ya daga kafada ya aje lyk i
donno. Jabir ya gyara murya ya ce my sister gwara ya aje
ki din,ga hadari kar ruwa ya taba ki. Da ke ta na jin
maganar Jabir,ba mu su ta ce tam yaya na. Khalid ya kalle
shi tare da fadin toh yayan ta da fatan xa a gyara ko a
canza mota,Madam ki dena hawa motan sai ya sake wata.
Nabeela ta sa dariya,Jabir da Hajjo kuwa ba wanda ya
dara,sai ma Jabir da ke fadin na ki na canza din,ta dena
hawa,diyoyi na sa hau. Da haka da haka ayi sallama, ya
sanya Hajarar sa gaban mota,su ka dau hanya. Sai shan
kam shi ta ke,shi kuwa zuciyar shi tas,ga iska da ke
tashi,gari yayi baki,hadari ya hadu sai kugi yake. Ana
yayyafi kadan kadan,kamshin ta da ya mamaye motar
gami da yanda AC ke ratsa cikin ba karamin nishadi ya
kara ma da ba.
Idanun sa kan titi ya ce an gama jan ajin ko da saura? Ba
tare da ta kalle shi ba ta ce ban gane ba. Ya ce har yanzu
ajin ba a gama jan sa ba? Ar u still nt ready to obey ur
hrt? Dan na san deep inside u ki na so ki aure ni,am every
woman type,so don't give dat clumsy excuse dat am ur
type! Hajjo ta kalle shi tare da fadin nt every woman,nd
mind you am nt in ur dat "every woman" Khalid ya ce big
lie! Yayyafi ya karu sosai,ya kara da na sani Suger,ko ya ki
ka so ki boye feelns din ki na sani,i can read u lyk a novel!
U hav feelns for me,you hav crush on me. Rai bace Hajjo
ta ce ka manta diabates ba Suger ba,i hav no feeln or wat
so ever for you,so stop mistaking! Shiru ya ma ta,har ta
na tunanin ya rasa ta cewa,sai kuma ya kallo ta ta hanyar
danna idanun sa cikin na ta,yanayin fitar numfashin ta
tini ya dan tsagaita,ya ce wat abt d way u catch ur breath
wen i look at u? Ya saki murmushi mischievously tare da
mai da idanun sa bisa titi,ya ce let it go Suger,ke ma kin
san u lyk me! Rai bace,bakin cikin yanda da ta yi reactn ya
sa ta fadin tsayar da motar ka! Fita zan yi! Cike da mamaki
ya ce ki fita ki je ina kuma cikin ruwan nan? Ta ce da
zama guri daya da kai gwara dukan ruwa,ka tsaya ko na
bude na fita a haka. Ganin fuskar ta ba wasa,sai ya sauka
gefe ya yi parkn. Ta yunkura za ta bude motar ya danna
lock,wai ina zaki? Shin in kin fita ina za ki sami abun hawa
cikin ruwan nan. Ta ce ina ruwan ka? Zan fita kuma zan
sami abun hawa ba tare da bata lokaci ba,idan kuma ban
samu ba zan taka daganan har hotoro GRA a kafa.. ya ce
no way! A fusace idanun ta har spark su ke dan bacin rai
ta ce way! Bude ka gani! A kasalance ya rangwadar da kai
bisa kan kujerar sa,ya ce Suger....ta ce Hajjo! Ba suger
sunana ba,kowa da Hajjo ya ke kira na,so ka kira ni Hajjo
ko ma child abuse da ka saba kira ko ka yi shiru! Ya
murmusa ya ce child abuse is no more,wannan zaune
gabana is a strong woman! Khalid ba kowa ba ne,Khalid is
unique dax y zai kira ki da sunan da ba kowa ke kiran ki
da shi ba Suger! Ta ja hannun kofa,tare da fadin ka bude
min. Ganin ta matsa sai ya bude ma ta kofar ya ga iyakan
gudun ruwan ta. Ta ko sa kai ta fito,yayya fi ya zama
ruwa,wani irin iska mai sanyi ya buso jikin ta,kayan ta ya
fara bin jikin ta,ta ja daga jikin motar Khalid ta sami wata
yar lemar ma su sayir da recharge cards ta kebe,amma
duk da haka ruwan na taba ta.
Daga mota ya ke kallan ta,he love d view,ta yi ma sa kyau
kwarai,ba dan ya na tsoran kar ta kamu da sanyi ba da ya
kyale ta yay ta kallan ta a haka. Ya yunkura zai fito kenan
sai ya ga wata mota ta tsaya a gaban ta,an sauke glass din
motar,abun da ya dada kular da shi yanda ya ga ta na ma
mai motar murmushi mai kayatarwa!
DEDICATED to The Women Of Virtue (group)
[4:22PM, 6/6/2015] AAG: [10:56pm, 6/5/2015] Khadija
Sidi: DIYA MACE
Ganin frnd din ta da ya dade da nace ma ta na yafuce
shi,farin ciki ya lullube ta,a asibiti daya su ke aiki,amma
shi a admin block ya ke aiki.Cikin jin dadin ganin sa Hajjo
ta ce KB na ji dadin ganin ka wlh! KB ya dara tare da fadin
maza shigo toh kar ruwa ya zane min ke. Dama tayin da
ta ke jira kenan,dan ta fara jikewa sosai,ta yi saurin bude
motar ta shige. A fusace Khalid ya fito daga ta shi
motar,ya nufi motar KB amma ina KB be ma san da
shi,tini ya karya kan mota ya haye kan kwalta abun sa. Rai
bace ya bi motar da kallo,ruwa ne ke dukan sa amma
sam be damu ba saboda zafin da kuna da ransa ke yi ya fi
dukan ruwan. Sai da ya dau kusan minti biyar a tsaye,ya
jike jagab,Hajjo sai dan waiwayen sa ta ke ta motar KB
har sai da ya ce ko kin yi mantuwa ne? Ah ah,ta yi saurin
ba shi amsa,mu je ba komai.
A fusace ya juya ya koma motar shi,da juyawa zai yi
kawai ya tafi gidan sa,amma kishin ganin Hajjo ta shiga
motar wani,wanda ba mamaki ma ba ta san shi ba dan ta
kuntata ma sa ta bishi ya sa zuciyar shi tafasa,a dole ya bi
bayan su dan ya tabbatar ya sauke ta lfy. Har su ka kai
kofar gida ba su san Khalid na biye da su ba,can gefe ya
faka,ya na ji ana ta horn maigadi ya ki ya zo ya bude
gate,shi ma ruwa ya buye shi,dan haka sai Hajjo da KB su
ka tsaya shawara,ya na ta zauna a gama ruwan,ta na bari
dai na shiga yanda ruwan nan yayi yawa Allah kadai ya
san lokacin tsayawan sa.
Khalid da ga na shi motar ya cika ya yi fam! Wai shin mai
Hajjo ta ke nufi za ta zauna a motar wani kato! Ta na
zaune motar wani cikin ruwan sama,sai shakar gamshin
ta ya ke! Mtsw ya ja tsaki! Hakurin sa ya kare,ya yanke
hukunci zuwa ya fito da ita da kan sa kenan sai ya ga ta
bude mota ta fito,ta shige gida da sauri. Ajiyar zuciya ya
saki tare da bin motar da kallo da ta zo shige shi ya na
fadin Allah ya taimake ka kai dai,amma ka kuskura na
kara ganin ka kusa da Suger ba za ka ji da dadi. Be shiga
gidan Hajiyar ba ya tada motar shi cikin bacin rai da
hanzari ya bar wajan. A hanya yayiwa Sani waya,ya ce da
shi gobe kafin ya taho kano yayi jiran shi,zai shigo
kumurya. Cike da mamaki Sani ya ce toh Allah ya kai mu.
Ya amsa da amen. Yanda Hauwa ta ganshi jike rai a bace
ta san ba lfy,ta yi kokarin jin musabbabin bacin ran na
sa,ya ce da ita ta dan bar shi ya na so ya ji shi kadai,ta ce
toh,Allah ya kyauta. Ta ja diyar ta ta bar shi ya ci kan
sa,binibini sai ka ji ya ja tsaki,mtws! Ranar dai haka ya
kwan da takaicin Hajjo wanda hakan shi ne karo na biyu.
Washagari da sassafe sai ga Khalid a kumurya. A tsakar
gida Sani ya sa ma sa kujerar da ya ke bawa bakin sa na
albarma ya zauna. Bayan ya gaisa da Indo,ya ke ce ma ta
ta fa dan so ta yi kama da Hajjo,dan dai ta fi Hajjon
kyau,dadi har ran Indo,kyakkyawa kamar Khalid ya ce ta
na da kyau. Zaman shi da Sani ya ke fada ma sa dalilin
zuwan sa,so ya ke a kai shi gurin iyayen Hajara. Sani ya ce
toh fa. Ai mahaifiyar Hajara Allah ya ma ta rasuwa
shekara goma sha uku kenan. Khalid ya ce Allah
sarki,Allah ya ji kanta,sunan ta Neena ta ci kenan shi ne
Hajara ke kiran ta Inna. Mahaifin ta fa? Sani yayi jum.
Khalid ya ce ya ka yi shiru ne? Sani ya ce ai abun ne,toh
mahaifin ta na nan,gidan nan gaba ne ba nisa. Khalid ya
ce toh mashaAllahu za ka iya raka ni gun sa? Sani ya yi
jugum,kamar mai shawara. Khalid ya ce kar ka
damu,tsakanin mu ne,ko matar ka ban so ta san za mu
wajan na shi,sai nan gaba,da alkhairi na zo,kamar yanda
na ma ka bayani a baya auren Hajara zan yi. Sani ya ce ba
komai,sai na raka ka din. Sani ya ce da Indo su na
zuwa,su ka fita ba su zame koina ba sai gidan su Hajjo.
Gidan ya koke ya lalace kamar ba Jama'a ciki,wai kuma a
haka Mudi ya yi aure ya aje matar shi ciki haka shi ma
Ayuba shi ma da matar sa cikin gidan. A waje su ka
tsaya,su ka tura yaro ya mu su sallama da Baba,Yaro na
shiga ya fito ya ce ai ga Alhaji Mamman din nan soro sai
nishi ya ke ina ga ba shi da lfy ne. Godiya su ka ma
yaro,tare su ka kutsa cikin soron,sai kuwa ga Baban nan
kwance a wulakance sai nishi ya ke,be ma san wa ke tsaye
kan sa ba. Subhanallahi,tare su ka yi saurin durkusawa
gaban Baba,Sani ya na fadin yaushe kuma haka ya faru?
Ko da wasa ba mu ji rashin lfyar ba! Shi kuwa Khalid ran
sa ne ya dada baci da al'amarin Hajjo,ya Baban ta mahaifi
na nan kwance cikin wannan wulakantacciyar rayuwa ba
gata,amma ita ko a jikin ta, ta na likita,haba wannan wata
irin duniya ce haka! Ya kalli Sani ya ce bayan Hajjo da
Indo bai da wasu 'ya'ya ne? Ya ce akwai Mudi da
Ayuba,nan su ke zaune da matan sa. Khalid ya leka ya
sami yaro ya ce ya yi sallama da Mudi ko Ayuba,dan tin
zuwan su ba wanda ya leko,da sun zo da wani mugun abu
ne da tuni sun aiwatar. Yaro ya dawo ya ce ba sa nan,sai
matan su. Khalid ya ce ace su su leko. Sai ga lantana
matar Mudi ta leko da daurin kirji ta na mita wai waye
maigida baya nan sa ya ce sai ya gan mu...Ganin Sani tare
da wani dandasheshen namiji sai ta shanye maganar ta.
Yanda ya ganta dukundukun,ga daurin kirji,Khalid ya ce
disgusting! Ita ko sai ta fara hannu,hannun ku,ashe Sani
ne,ai daga Mudi har Ayuban ba wanda ke gida,eh sun je
samo mana na afawa! Khalid ya ce sun san da rashin lfyar
mahaifin su? Lantana ta kalli inda Baba ke kwance ta ce
sun shi na mana,kullum cikin ba shi jike jike su ke ai,Mudi
ne ma ya kawo shi nan ya kwantar,dudu ma kwanan sa
nan uku kwance ba,sai dai a tayar a kwantar. Rai bace
Khalid ya ce Sani taimaka min mu sa wannan bawan Allah
mota mu kai asibiti,wa'yan nan ba su san darajar iyayen
su ba,da ga su har matan na su. Lantana ce yo ai dai mun
ma sa iya kan kokarin mu mu dai,so ka ke mu sa zani da
majanyi mu goya? Banza su ka ma ta,yayin da su ka kama
Baba,sai zarnin fitsarin da yayi a kwance ya ke su sa shi
mota. Sai da su ka biya gidan Sani,ganin halin da Baba ke
ciki Indo ta girgiza,Khalid ya ce ya aka yi ba ta zuwa ganin
sa har ya kai haka bai da lfy?Indo ta ce wlh ta na zuwa
duk da ko ta je din fada ya ke ma ta wai ta na damun shi
da yawan zuwa,ko kwana hudu da ya wuce ta je. Tare su
ka dunguma su ka taho kano,Indo ta bar babbar yarta
tare da yara.
Su na zuwa kano AKTH su ka wuce,nan da nan aka
kwantar da Baba emergency,darajar Jabir tuni likitoci su
ka rufa kan Baba su na duba shi,abu na su. Khalid da
Sani,da Indo su ka ja gefe,Har Khalid ya daga waya zai
kira wayar Hajjo,sai ya ja tsaki ya kashe,an sha fada ma sa
diya mace ta fi jin kan iyayen ta akan maza,amma sam ya
ga bambamci gun Hajjo,hw comes? Hw can she be so
cold to her biological father,ita ta yaya ta ke so na ta
'ya'yan su ji kanta har su tausaya mana. Kai daga
dowowar sa zuwa yanzu Hajjo ta tsaya ma sa a rai kan
abubuwan ta da dama. Sani ya sallama,kar Hajiya ta ji
shiru,ya ce kar ya fada ma ta sun kawo mara lfy,idan ya
dawo zai ma ta maganar,gudun kar Hajiya ta ji irin abun
da ya ke ji game da Hajjon.
Da wuri ta samu ta bar asibiti,hudu a gida ta mata,ta yi
saurin yin wanka ta shirya cikin english wears riga body
hug ruwan goro,da kuma free skirt bski,sai ta daura
bakar sweater da ke garin ana sanyin damina. KB ne ya
dame ta zai zo tin da ya sauke ta jiya,ita kuma ganin
kirkin da ya ma ta dan a ramawa kura aniyar ta sai ta
yarda yau daya dai yazo. Ta na kallan kanta a madubi,ta
dau humra ta na dan shafawa jikin mayafin da za ta yafa
wayar ta ya fara kara,ta duba ta ga sunan KB sai ta aje
humran ta daga,ya ce gashi cikin farfajiyar gidan. Ta ce
toh ga ta nan fitowa. Ta kuma kalle kanta a madubi,ta yi
kyau kamar diyar turawa,ta sanya takalmi ta je ta fadawa
Hajiya za ta fita.


[11:15pm, 6/5/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE
KB zaune kan motar shi ya na jiran fitowar Hajjo,wata
mota ta shigo gidan,ta faka gefe guda. Ganin Khalid ya
fito sai da ya sha jinin jikin shi duk da dai ba su taba
haduwa ba,be kuma san wanene shi ba. Shi ma Khalid tin
shigowar sa gidan ya gane KB,dan haka kai tsaye wajan
shi ya je,ganin ya nufo shi KB ya sauko daga kan mota
tare da mi ka ma sa hannun tare da fadin
salama'alaikum,fuska murtuke ya amsa wa'alaikumul
salam. Wajan wa ka zo ne? KB ya dan yi jim sannan ya ce
wajan Doctor Hajara. Khalid ya ce a matsayin ka na wa?
KB ya ce ban dai san kai wane ne ba,so dax y zan amsa
ma ka,a matsayi na na friend din ta. Khalid ji yayi kamar
ya buge bakin sa,ya ce matar tawa ce friend din ka? KB ya
gyara tsayuwa,tare da fadin matar ka,wlh ban san ta na
da aure ba,ba ta fada min ba,Khalid ya ce ba a daura ba
ne,wata biyu ya rage dax y ina ga ba ta fada ma ba,so ka
nemarwa kan ka arziki ka janye kafar ka daga gidan kuma
da ga wajen mata ta. Jin ba a daura auren ba sai hankalin
sa ya kwanta,ya ce ba damuwa,sure bazan sake zuwa ba.
Khalid ya ce madallah. Ya juya ya na tafiyar nan ta shi
cike da takama ya shige gida,KB ya ce ba shakka dan ma
su gida,shi gidan ma ya ke shiga kai tsaye,bara na ja
rayuwata na yi gefe guda! Be san gidan su Khalid din ba
ne. Ya shige motar sa ya ya fita lokaci guda kuma Hajjon
ta fito,sai gani korar motar ta yi,cike da mamaki ba ta ma
san Khalid na tahowa ba ta ke fadin me zai sa kuma KB ya
tafi,bari na dauko waya na kira shi. Da jin kamshin
turaren sa da ankarewa da shi lokaci guda ne,ta daga kai
ta kalle shi. Ya bi ta da kallo tin da ga sama har kasa,har
sai da ta kasa sakewa.
Fuska murtuke ya ce kar ki damu da ki kara kiran shi,na
sallame shi har a bada ba

Please Login or Register in order to submit comment