Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah ka
fada min mana,ban san wasa da irin wannan
maganar,haba yaya na na kai na! Jabir na dariya ya ce na
ji wannan social bribe din,toh ka shirya nan da sati biyu
za mu kai gaisuwa da kuma sa ranar auren ka da
Hajjo....baki Khalid ya bude kamar zai yi magana,sai
kuma ya rufe,ya kara budewa ya na rufewa kusan sau
uku,Jabir ya ce fadi ma na,Khalid ya ce Alhamdulillahi
rabbi alamin!Jabir ya ce ko kai fa! Murna ce ta lullube
Khalid,fiye da tunanin kuwa,gani ya ke ya haihu ma ya
gama dan daga ganin Hajjo za ta yi kwayaye,baze bari ta
yi fmly planing ba,yara za ta jero ma sa kamar bene. Ya
ce Jabir wlh da na isa na ma ka kyauta da na ma
ka,maganar da ka fada min ta yaye min rabin matsala ta.
Jabir ya ce ka min mana,girman ka ne. Khalid ya ce ni din
banza,me na isa na baka. Jabir na murmushi ya shige
motar shi ya na fadin sauran mtsalar ta ka,ka yi saurin
kau da shi,ka kuma tuna ma ta Allah ne ya bamu damar
mu yi,kar ta yi jayayya da fadar Allah. Darawa Khalid ya
yi,ba shakka Jabir ya san sa kwarai ya na iya karantar
sa,ya ce madallah da wannan yaya nawa,na gode,Allah ya
bar zumunci. Ya tada motar shi ya ce ameen dan
rasulillahi,kar fa ka fara ma ta jiji da kan sosai,ka bari a
daura kar ta ce ta fasa! Ya na dariya ya figi motar
sa,Khalid na daga ma sa hannu,sannan ya juyu gida,ya
fara tsara wasikar da zai karantowa uwar gida Hauwa.
Kwance jikin shi,bayan ya gama nuna ma ta duk duniya
ba diya mace kamar ita. Ya kira sunan ta,Hauwa?Jin ya
kira ta ba tare da ya ce baby-luv din da ya saba fada ba
musammam lokaci irin yanzu ta san da wani abu. Ta
amsa da na'am. Ya ce kin san shekaran mu nawa da aure?
Ta ce sha daya. Ya murmusa tare da fadin,ol those years
da san ki ke kadai na ke kwana na ke tashi,haka ma har
tsawan shekarun da Allah ya kindaya ma na,you ar d love
of my lyf. Maganar ta sa tai ma ta dadi,ta dada kwanciya
jikin sa,tare da fadin tell me more,ba ta san more din ba
mai dadi ba ne. Sai da yayi shiru,sannan ya ce kin san dai
Allah ba ya cutar da bayin sa,sai dai bawa ya cutar da kan
sa,Hauwa ta ce haka ne. Ya ce kin san kuma kowa akwai
kaddarar rayuwar sa..gaban ta ya fara faduwa,ta ce haka.
Ya kara da kin san Allah na jin kunyar macen da be bawa
haihuwa ba? Hauwa ta gyada kai,ta ce eh,ki tabbatar Allah
na tare da ku,ya kuma san da ku,ku din ma mata masu
daraja ne. Ya sake yin shiru,Hauwa ta ce ina jin ka. Ya ce
Hauwa ki saurare ni da kyau dan Allah,wlh ban taba san
kowace diya mace ba sai ke...zuciyar Hauwa ya fara
kaduwa,ta ce dan Allah fada min,menene wai. Khalid ya
nisa,ya ce aure n ke son na kara.......a razane ta dago daga
jikin sa ta na kallan sa kamar wanda ya yi sabo,ta ce aure?
Wasa ka ke ki Khalid! Aure fa? Kai ba da gaske ba ne! Yi
shiru kawai mu kwanta mu yi bacci. Shi ma tashi yayi
zaune gami da ruko hannun ta,ya ce ba wasa na ke ba,ba
kuma ba dan ba na san ki ba ne....idanu cike da kwalla ta
ce Khalid,me ka ke fada haka,ba ka san abunda ka ke fada
ba! Ta ficge hannun ta,ya ce Hauwa ki saurare ni! Ta ce
me za ka ce min? Ina jin ka! Ya ce Hauwa ki tausaya
min,tsufa na ke,wlh duk yanda na so na hakura na
kasa,ina san yara......sai ta fashe da kuka,ta na fadin dama
na sani,dama na sani. Ka kasa hakuri? Dole ka kasa mana
tunda ba kai ba ne da ralural ba! Bambamcin diya mace
da namiji kenan,da kai ne da matsalar ka san haka zan
hakura na zauna da kai ba ma me ji,amma yau dan ni ce
gashi za ka tuzar ta ni....ya yi saurin rufe ma ta baki,ya ce
haba Hauwa,kar ki manta bambamcin diya mace da
namijin har da umarnin ubangiji da ya ce mu auri
hudu,ko uku ko biyu har zuwa daya,manzo sallallahu
alaihiwasallam be zauna da daya ba Hauwa,ya ce mu auri
fiye da daya har zuwa hudu in har za mu iya adalci.
Hauwa manzo sallallahu'alaihiwasallam ya ce mu
hayayyafa dan mu zamo abun alfahari a gare shi ranar
gobe kiyama,shin da wannan damar Hauwa na cigaba da
ruyuwa yanda mu ke ki na gani na yiwa kai na adalci
kenan? 'Ya 'ya na ai na ki ne Hauwa...ta na hawaye ta ce ni
da ban haifa ba,ta yaya za su zamo nawa? Sanin kan ka ne
Neenan da na ke gani kamar tawa ma an kusa raba ni da
ita. Ya ruko hannun ta tare da fadin babu mai raba ki da
ita,saboda na tabbatar da hakan ya sa na zabi na auri
mahaifiyar ta.....dif Hauwa ta ji ta dai na ji,ta daga ido ta
kalli fuskar Khalid da ke ma ta haske duk sanda ta daura
idanun ta akai,yau sai gashi ya ma ta duhu dulum. Hauwa
ba ta ji ba ta gani ta cire hannun ta daga na Khalid. Ta
tashi za ta fita,shi ma din tashi yayi da sauri ya na
Hauwa,Hauwa! Ina ba ta tsaya ba,ya bi bayan ta da
sauri,ganin haka sai ma ta sa gudu,ya na biye da ita,ta yi
saurin shiga bankaranta ta kulle. Sai ta zube kasa ta na
kuka mai ban tausayi. Khalid yayi yayi ta bude ta ki,dan
haka shi ma sai ya sami waje ya zauna daga jikin kofar,ya
na jiyo kukan ta,ya rasa me ke ma sa dadi nan duniya.
DEDICATED to The Women Of Virtue (group)
[12:02am, 6/11/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE
Hajjo ma a na ta bangaran bacci nan ba ta yi ba. Tin da ta
amince da auran Khalid ta kasa nutsuwa. Sai da ta dage
da karatun alqur'ani,da kuma nafilfilu Allah ya sa hakan
alkhairi ne. sannan ta samu idanun ta su ka rufe.
Washagari da sassafe Hauwa ta tafi gidan su. Da ke iyayen
ta na arziki ne sai su ka ma ta tatas,su ka zarge ta da san
kanta,mutum ya iya zama da ita tsahon shekarunnan ba
haihuwa,dan ya ce zai kara sai ta tada hankalin ta,ita ba
mai ba shi shawarar ya kara ba ne! Yayyar Hauwa mai
suna Zeena wacce bayan iyayen Hauwa sun gama ma ta
fada ta zo,tare da kanan ta ne su ka ta zuga Hauwa,wai
wlh ta bari ya auri yar aikin gidan su ta fado,duk matan
da ke garin nan in ma kishi za su yi auro ma ta class din ta
mana! Hauwa ta ce da ta ke mai aiki,yanzu fa doctor ce.
Zeena ta ce sai me? Kowa dai ya san asalin ta,turan gini
ran zane! Ke ce ma kin dau diya kin manne kamar ta ki!
Yanzu kya gane kuran ki! Daya daga cikin kannan ta su ka
ta ce Hajjon mummana ma da ita! Dayar ta ce ai kamar
ta daya da Neena! Wlh kar ki kara kawo ma na yarinyar
gidan nan. Ita kuwa Hauwa har lokacin jin Neena ta ke
har ranta,dan haka ta ce ah ah fa,ba ruwan yarinya,ku dai
taya ni bakin ciki amma kar ku kyarar min Neena! Hada
baki su ka yi su ka ja tsaki. Mahaifiyar Hauwa ta shigo,da
ke ta dan cinci maganar,ta ce maza ki biye mu su ki yi
biyu babu,su zuga ki Neenan ma ki rasa,kin dai ji
shawarar da mu ka baki! Hauwa ta ce uhum.
Khalid da ya tashi ya ga Hauwa ba ta nan ya san za a yi
haka. Sai cewa yayi da Neena maman na ta ta je gida ta
yiwa dady sallama dan ba ya so ta gane ta yi abunda ba ta
taba yi ba,wato yaji,shi zai kai ta makaranta,da ke Hauwa
ke kai ta kulli yaumin,ko ya ce zai kai ta hanawa ta ke. Duk
da hakan ya yiwa Neena wani iri,sai ta amsa da toh. Da ya
sauke ta makarantar ya biya ta gidan su Hauwa. Iyayen ta
su ka ce ta fito ta bi mijin ta,har da bashi hakuri,tare da
mu su dan nasiha. A hanyar komawan su gida ba wanda
ya ce da dan uwan sa kala. Sai da su ka shiga gida,Hauwa
ta ce da Khalid me ya sa Hajjo? Me ya sa za ka zabi Hajjo
maimakon wacce ta isa,na san yes isasshiya ce zan iya
kira da sunan kishiya?yayi mamakin maganar na ta,dan
shi zaman sa da Hauwa ya san mace ce wacce ba ruwanta
da arziki ko rashin arzikin mutum,mace ce mai saukin
kai,amma kishi na neman sauya ma ta hanya. Murmushi
kawai yayi ya ce ki yi hakuri Hauwa. Zai wuce ta shagaban
sa,ta ce me ya sa ita? San ta ka ke? Ya girgiza kai,alamar
ah ah,ya ce ke kadai na ke so. Ta ce toh ka sake wata! Ya
ce ba zan iya ba! Ta ce y her? Ya ce ita zuciya ta ta zaba,ki
yi hakuri Hauwa. Yayi saurin shige ta ya shiga bangaran sa
gudun ganin saukar hawayen ta. Nan ta zube ta na
kuka,ta na fadin wlh san ta ya ke! Mayaudari! Makaryaci!
Santa ya ke wlh!!!nan ta karaci kukan ta ta koshi. Jin
Khalid shiru ta san ya bi ta kofar baya ya fice,ita ma ta
lallaba ta shige dakin ta ta kwanta,tuni ta fita da ga
hayyacin ta.
Da azahar ta na tunanin Neena a makaranta dan ba ta ji
za ta iya fita,sai ga ta ta shigo dakin sanye da kayan
makarantar ta,da alama dawowar ta kenan. Ta ce
Momma sannu da gida,ya ba ki zo dauka na ba sai dady?
Ba ki da lfy? Ta zauna gaban ta kamar za ta shige cikin ta.
Hauwa ta kau da kai ta na ban da lfy,Neena ta yi saurin
ruko hannun ta,Dady ya kai ki asibiti? Cikin ranta cewa ta
yi ai shi ne asibitin tinda shi ya daura min,azahiri kuma
hawaye ne su ka fara zuba daga idanun ta,ganin haka
Neena ta rude,tuni ta fara kuka ita ma,ta na pls Momma
ki yi shiru na kira Dady mu je hosptal,bara na kira Uncle
Jabir. Hauwa na hawaye ta ce rashin lfy na ba na hosptal
ba ne Neena,ki min addua kawai dan na kusa
zaucewa,aure Dadyn ki zai kara... a razane ta ce aure? Me
ya sa? Ya dai na san mu? Hauwa ta ce ki tambaye shi da
kan ki. Ai kuwa sai ta tashi fuuuuu ta fice,a falon sa ta
tadda shi,ganin yanda ta shigo ga fuska shabe shabe da
hawaye sai ya tsuke fuska,ya ce ya dai? Ta dan yi kasa da
murya ta ce Dady wai za ka kara aure? Ya ce haka ne. Ta
ce Dady saboda me ya sa? Ya ce kin yi kankanta,ba za ki
fahimce ni ba yanzu. Ta ce ka dai na san mu ne? Ya ce na
fi san ku akan kowa...ta ce plss Dady idan ka na san mu
kar ka yi. Ba ta taba rokansa abu ya ki ba,amma wannan
karan ta zo da maganar da ba wacce ta isa fadan ta ya
amince idan ba Hajiyar sa ba. Ya ce ki yi hakuri Neena,it is
for your own gud,dukkan ku,ina san ku,amma dole sai na
yi. Idanun ta cike da kwalla,yayi mamakin yanda yar
yarinya wai itama ta san ta ya wacce ta dauka mahaifiyar
ta kishi,kai kishin mata daban ya ke. Juyawa ta yi za ta
koma,sai kuma ta dawo ta ce wa za ka aura Dady? Ba tare
da ya ji komai cikin ran sa ya ce Hajara ce wacce ake kira
Hajjo,ta ce Anty Hajjo ta gidan Hajiya? Ya ce eh. Ta ce
Momma ba ta so,Allah ya sa ka fasa Dady. Kallan ta ya ke
kawai,Hajjo kawai a tsaye,da ta san matsayin Hajjo a
rayuwar ta,da ta fi kowa farin ciki,amma a sannu za ta
fahimta,har yanzu yarinya ce. Sai da ta fice,sannan ya
koma ya kishingida.
Ya shedawa Hajiya,har ta fadawa yayye da kannen Baban
maza,su za su yi komai har sa rana da kai lefe,lokaci ya
canja,ya fi san mazan su kai dan a rage bidi'a.
Sati biyu su ka dauka kafin Sani ya mu su jagora zuwa
wajan Baba,da ke dama Baban ya san Khalid sosai,sai
gashi har da gayyato yayan sa da kuma Alhaji Baso baban
Garbati,duk da kuwa ba wai warkewa yayi garau ba,jikin
na sa na tashi lokaci lokaci,karfin hali ya ke kawai. Lokaci
guda su ka bada kudin na gani ina so,ga kuma kayan sa
rana da lefe,su ka ce wata uku su ke so a sa,ba mu su su
Baba su ka amince,musamman yayan Baba da ya gaji da
surutan jama'a wai kanin sa ya bar yarinya ta lalace ta
zama yar boko ta ki aure. Lefe ma na gani na fada da
Khalid ya hada cikin gaggawa su ka sauke su gaban su
Baba. Su Baba sun yi mamakin yawan akwaitinan,ko da
bakin su ka tafi bayan an basu tukwicin su daga kudin da
su ka kawo bisa al'ada tuni magana ya fara zagaye gari,an
kawo laifen birni gidan Alhaji Mamman,an sauke arziki
gidan Alhaji Mamaman. Shiko Baba da ya san wacece
Hajjo da irin rayuwar da ta yi a baya ya san kadan ma ya
gani daga sakayyar alkhairi da Allah ke yiwa Hajjo.
DEDICATED to The Women Of Virtue (group)
[12:17am, 6/11/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE
Hajjo ta na zaune tsakar gida,ta cika ta yi fam,fashewa ne
kawai ba ta yi ba. Sai ga Indo ta shigo ta na guda,wato ta
gano kayan Hajjo kenan,har da takawa,ta na rai dai,rai
dai,rai dai! Ina ma Inna ta na raye ta ga arzikin autar
ta,Hajjo? Tin da na ke ban taba ganin kaya,kaya dai irin na
akwatin lefan ki ba!anjiman nan ma Baba ya ce a zo a
kwasa a kawo mi ki idan Sani ya sami lokaci. Ko a jikin
ta,Hajjo ta ce hmmm. Indo ta kara da wata uku aka sanya
ranar ma.....nan Hajjo ta fusata,ta ce na fasa auren na shi!
Indo ta ce iyye? Hajjo ta ce eh na fasa! Indo ta na tafa
hannu ta ce ku ga wacce ba a yiwa abun arziki dangin
gidan maza! Akan wani dalili? Dan an sa rana wata uku?
Hajjo ta ce haba Indo,ki na fa gani tun da na amince da
auren mutumin nan be sa kafa ya tako ya zo gidan nan
ba,ko waya ma be min ba,ba shawara ta ba komai an
tashi an samin aure wata uku,na san Baba zai iya sa awa
uku ma ba wata uku ba tinda dama ba kauna ta ya ke
ba,amma shi ba sai ya tambayi shawara ta ba!!
Indo ta ce gaskiya be kyauta ba,ai na zaci kun yi shawara
ne,amma ki ma sa uziri be kai ga a fasa aure ba,ki yi kiran
sa mana....Allah ya sauwake! Hajjo ta katse ta,wlh ba zan
kira shi ba Indo! Indo ta ce toh sai ki yi hakuri tin da ke
ma na ki jin kan ya hana ki neme shi,maganar fasa aure
babu...ta na magana ta shige ciki ta bar Hajjo na ta faman
kwafa.
Khalid kuwa Hauwa ce ta ke gasa ma sa gurasa danya a
hannu,gaba daya ta birkita shi,ta hana shi kwanciyar
hankali,tashin hankalin yau da ban na gobe da ban. Har
ya gwammaci zaman Abuja akan kano,ba dan ya na so ba
sai dan ya ba ta lokaci ya yi nesa da ita ko ta huce. Idan ya
zo kano shirye shiryen auren sa ya kai shi ko kuma ya
leka site din sa ne,inda ake dankara ma sa hadadden
gidan sa da ya yi designing da kwakwalwar sa dan zaman
mata biyu. Hajjo na ransa kwarai,ya na son zuwa ya
ganta,amma ba dama saboda abubuwa sun cude ma
sa,gashi ya daga waya yay ta kiran ta,amma ba a
dagawa,ashe wayar ta ta faduwa ta yi. Har ya yi fushi ya
ce shi ma ya dai na kiran na ta,ta zo gidan sa sa na
gaisawa gaba daya. In dan zai aika ma ta da sako Sani
kawai ya ke bawa,idan aka kai ma ta ta ki karba,sai Sani
da Indo sun ma ta ca ta ke hakura.
Ana saura wata guda biki,su Doc Hussaina da yan uwanta
likitoci aka kawowa Hajjo kayan gyara,su cikwaidi,zuman
mata,tsumi har da turarukan tsugunno. Doc Hussaina ta
ce matso nan ki ji diya ta,dan ni fa Hajara diya na ke da
ke ba abokiyar aiki ba. Cikin jin kunya ta matsa kusa da
ita,sauran matan ma matsowa su ka yi dan sun san Doc
Hussaina ba da ga nan ba. Ta gyara murya ta ce Hajara
kin shirya yin aure kin shirya zaman aure? Hajjo ta yi
shiru,Doc Hussaina ta ce amsa min mana. Hajjo ta gyada
kai alamar eh. Ta ce toh saurare ni da kyau,auren dai kin
taba yi,amma ki sani wanda ki ka yi da da na yanzu ba
daya ba ne,da bambamci,da ba ki san ciwan kan ki
ba,yanzu kuwa kin san wacece ke,kuma kin san wa za ki
aura,toh fa Hajara sai kin yi hakuri,dan hakuri shi ke
zaunar da ko wace diya mace gidan mijin ta,Hajara da ba
hakuri da aure dayawa tuni ya mutu,ki yi hakuri,ki toshe
kunnuwan ki,ki kuma runtse idanun ki,ki sai ta harshen
ki,ki ji ki ji,Hajara ki gani ki ki gani,kar ya hau ki hau,idan
ya hau,shafawa zuciyar ki salama ta hanyar ambaton
ubangiji,ki tuna Allah ki ke bautawa,ba wai dan shi wanda
ya aje ki gidan na sa za ki yi ba,sai ki ga ke kin sauko,da
iyaye ma sai an yi hakurin zama bare wani can da ya
ganki da hakoran ki ras da wayan ki. Sauran su ka ce ba
shakka. Doc Hussaina ta ce kin ga watannin farko na
aure,nan su ke fara nuna isa,su a lalle sai sun gwada
wannan ikon da Allah ya ba su kan mace tin da ta zama
mallakin su,ke kuma daure ki gwada wannan sallamawar
da Allah ya yassare mi ki,kwantar da kai,ba komai ba shi
girman sa,girmama shi,yi ma sa ladabi da biyayya
muddin be wuce gona da iri ba,kar ki yarda ki yi abunda
zai rai na ki,duk da ba ke bace matar sa ta farko,dole da
tambiyar uwar gida zai tafiyar da ke,da kin ga abunda be
dace ba a musulunce da dabi'ance gyara ma sa a
dabarance. Kar ki taba yarda wai kin zama daya da miji ki
saki jiki,ki na zama anyhw,idan an yi abun dariya ki saki
baki ki ta dariya kamar shashasha! Ah ah Hajara raini ya
ke kawowa,wlh ba ko wani irin sakin jiki za ki yi da shi
ba,kar ki yarda idea din an zama daya ta shiga ran ki,idan
ki ka bari ya rai na ki kin shiga uku,ki yi yanda zai yi
respectn din ki,ja girman ki ki ja ajin ki,yan da za ki yi
reapectn din sa yayi respectn din ki,reapect beget
respect. Uwar gidan sa gaba ta ke da ke,ko da kuwa kin
girme ta,ita ma ba ta girmanta, tare ki ganta da mijin
ta,kar ki yarda daidai da rana daya tunanin ki fitar da ita
ya tsurga cikin zuciyar ki,ke ma diya mace,kuma ki na da
diya diya mace,ki na da yan uwa,ba za ki so a yi mi ki ko
na ki haka ba,ke ma ki yi adalci kar ki yiwa wata,amma fa
kar ki yarda ta raina ki. Haka dangin miji,zama da su sai
da dabara,zama da su iyawa ne,ki saki jiki a raina ki,ki ja
jiki a ce kin ki su,toh sai dai ki ti kaffa kaffa da su,ko uwa
tushe daya ku ke sai kin iya takun ki,bare ke zama ki ka
taba yi sa su,da kin auri na su toh sun zama dangin
miji,tsakanin ki da su kyautatawa,ki bude hannu,ba su,ke
dai ba su,kyauta ta na raba ki da su,kar ki zura jiki,kar
kuma ki janye jikin ki gaba daya,sama sama,sai wa kanki
mutunci kar ki yarda a rai na ki. Tsakanin ki da facalolin ki
mutunci,wacce ta ku ta zo daya sai ku yi,wacce ta ku ba
ta zo daya ba ruwan ki da ita,kowa ya tsaya matsayin sa,I
keep repeatn dis,kar ki yarda a raina ki,kar ki raina kowa.
Ki zama mai tsafta,mai kula,mai tattali,mai boye
sirri,Hajjo ki rufa sirrin mijin ki,ban da tona sirri,kin san
duk abunda ya fita daga bakin ki zuwa kunnan wata ya
tashi daga sirri,sirrin ma iri iri ne,akwai na dakin mijin
ki,akwai na aljuhun shi,akwai kuma na tsakanin ku,akwai
kuma na zamantakewa. Na zamantakewa ne mai wuyan
boyewa,yau da gobe dole akwai randa za ki bukaci ki yi
sharing abunda ke damun ki akan yanayin zaman auren
na ku,ko da kuwa ba solution za a baki ba,ke dai ki fada ki
sami sauki,wannan ba laifi idan kin sami wacce za ki yi
sharing da ita,toh amma me? Ba kowa za ki fadawa
ba,ban da ma iyaye,ke za ki manta,su ba sa
mantawa,rukewa su ke a ransu,kawaye ba ko wacce kawa
ba ce mai ruke sirri,wasu rashin ruke sirri ma a hilittar su
ya ke musammam wacce ta fiya surutu,dan ko gawa za a
wanka ba a yi a gaban mai surutu ko wanda ba na ka ba
saboda kar ta ga wani abu suruta ya sa ta furta,dan uwa
sai kin sami wacce ta ke very close da ke kuma kun saba
sharing problems dinki,san samu ki sami mace wacce ta
ke ta manyanta,cikin yan uwa ne kawayen mamanki
ne,aunties ko ma maman kawar ki,idan kuma kawayen
na ki ma akwai ta sirri wacce ki ka aminta da ita shi ma
din ba laifi,dan ba a rasa na kwarai,kafin a same su ne
aikin,inshaAllahu sai ki ga kin sami mafita asirin ki a rufe...
DEDICATED to The Women Of Virtue (group)
[12:36am, 6/11/2015] Khadija Sidi: DIYA MACE
Waje yayi shiru,Doc Hussaina ta kara da batun gyara,kin
san dai ganyen magarya ko? Hajjo ta gyada kai. Doc
Hussaina ta ce toh ki ruke shi,ya na da amfani
matuka,musammam da aka hana amfani da soaps da
kuma antibacteria,saboda any thing antibacteria is
powerful,kuma ur private part is the most delicate part
of ur body a matsayin ki na diya mace,wajan akwai flora
wanda su ke da amfani,shi kuma antibacteria idan ki ka yi
using ba ya iya bambamce tsakanin flora da
bacteria,duka ya ke hadawa ya kashe,kin ga anyi ba a yi
ba,haka kuma ya na sane mace yawan amfani da su,plus
soap wari ma ya ke sawa. Shi ko ganyen magarya na
tsaftace jiki kwarai,ya na hana warin gaba,ya na matsi,ya
na maganin toilet infections, ya na kuma kara ni'ima,tin
daga yanzu ki same she danye ko busasshe, ki fara
daurayewa,sannan ki tafasa ki ta ce ki na tsarki da shi da
dumin sa ba da sanyi ba. Haka farin almiski,dan kin ga shi
ana ma kiransa miski Aisha,wanda ya samo asali daga
wajan Nana Aysha Allah ya kara yarda da ita,duk san da
ta gama period ta ke amfani da shi,ya na matsi kuma ya
dauke wannan karni da gaifi na period. Kin ga ni duk
juma'ar duniya na kan yi amfani da shi. Ni yara na da sun
fara period na ke koya mu su amfani da ganyen magarya
da miski badan komai ba sai dan period kadai kara
budurwa ya ke,musamma idan ya na fita da yawan
nan,tashi guda ka ji bulum ya sauka,gasu yawancin su
suna shiga toilet na makaranta,akwai every possibility na
kwasar toilet infection,so da sun gama sai na ba su
ganyan magarya su kama ruwa sannan na ba su miski su
shafa,ba wai sai sun zo aure ko sun yi ba. Daya daga cikin
Docs din ta ce Anty Hussaina tin da kin ce period kadai ya
na bude budurwa,ba laifi kenan budurwa ta yi amfani da
abun matsai idan ta tashi aure? Doc Hussaina ta ce eh ba
wai ba laifi ba ne,kamata ya yi ayi daidai ruwa daidai
tsaki,kin ga lokacin mu dake at our tender age ake ma na
aure,da yawa dakin mijin mu mu ke fara period,so idan
aka tashi mana aure ba wani maganin matsi da mu ke
bukata,amma yan matan mu na yanzu an yi period na
kusan shekara da shekaru,ga daukan abu mai nauyi,ga
tsallake tsallaken kwata mai girma dadai sauran su ya sa
mu ke dan bawa yaran mu kayan matsi,shi ma din ba wai
na matsi sosai ba,irin su ganyan magarya,ake tsarki da
shi,da miski,dama kuma idan za ta yi gyaran jiki za ai
mata dukkan da dirot ko farar kaya,wannan ma ya
wadatar,ba a dinga tsugonno a wannan,a waccan, a shafa
waccan,tusa waccan,garin neman gira a rasa ido,ku ga
yarin ta matse gam kamar bango,wata dama a matsen ta
ke sosai ba ta san kanta ta kara,sai daga baya a zo ana
jinya,wasu har dinki ma,toh ina amfanin haka? In ma
matsin sosai za ki yi gwara ki jira a kai ki ki san kan ki,ki
gane irin ki sai ki yi matsin da hujja.
Toh ga gudun mawata gare ki Hajara amarya. Doctors su
ka ce ita kadai ko har mu? Doc Hussaina ta ce har ku da
ma da ku ke gidajan ku za ku iya yi,amma yanzu da ita na
ke magana ta,duk su ka sa dariya. Doc Hussaina ta ce ki
na ji na Hajara? Hajara ta ce eh. Ta ce idan biki ya matso
kusa sosai,kafin a fara sai ki sami kankanar ki wanda ki ka
san za ki iya shayewa kwallo guda,sai ki yi sallah raka'a
biyu nafila,ki fafaye saman kankanan,ki dan caccaki cikin
yanda ruwan zai tsatso,sai ki karanta suratul
Khafi,Maryam da Rahman ki tofa ciki,ruwan da ya tsotso
na kankanan sai ki disa cikin turaren ki da ki ka ware dan
amfanin ki ke kadai,kamar humrah,bayan ki tabbata
ruwan kankanan ya zuba ciki sai ki aje kayan ki. Ki shanye
kankanar ki tsaf ki koshi,turaren ki kuma ki na amfani da
shi,inshaAllahu mijin ki zai girmama ki,ya martaba ki,yayi
respect din ki,za kuma ki sami daukaka wajan sa wanda
shi ake fata. Gaba daya kowa ya fara kai gaskiya ni ma zan
yi,ni ma zan yi. Hajara ta ce na gode Anty Hussaina,Allah
ya kara girma. Doc Hussaina ta ce

Please Login or Register in order to submit comment